Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 8
murmushi uhm ko da yake an fa ce wanzami bai son jarfa. Hada inasu inasu suka shiga yi, ta dube su da gasken tafiya za ku yi tun yanzu? Anti gwanda mu hada inamu inamu karonmu dayaya ba zai yi kyau ba баббalla mu fa ya ce zai yi? Kin kwa san halin yaya? wane hali ne yake da shi? Ta tambaye su a duniya tana so ta ji wani abu da yake bakanta ransa domin ta sami damar aiwatar mishi, lubabatu ce ta fara ba ta amsa, kin ga yaya ba shi da yawan fada amma fa in ya yi fushi babu kyau don idonshi yakan 45 rufc har ma ki yi zaton yana hauka ne. Ba ya son kuma raini, kin san shi mutum ne me son girma ga zuciyar masifa shi kansa Dady yana yimishi fadan hakan balle kuma momy. Lubuan ce ta katse ta da sewa, ni kin san abin da ya fi damuna ma? Kar fa ya je ya hada mu da Dady ina jin koke da kika zo family namu kwanan nan kin fahimci halin dadin sam ba ya yi wa mutun ta dadi. Ta yi shru tana nazari, gaskiya ne ko waye ranshi zai baci, ita da kanta yanzu ta soma gano rashin kayutawar rayuwar da suka yi da Tahir, duk da dai iyakar mu'amularsu be wuce rike hannun juna -ba ko kuma dai irin su zauna guri guda, sau daya ne za ta taba tunawa ya hado ta da jikinsa shi ma din ba da son ran nata ba don dai ta cunkusawa abokin fadan nata ne (Waheed). Ta dan numfasa, to ai kuma dai ba ku kyauta ba irin abin dakuka yi haba da Allah? Na dai kare ku ne don in yi escape dinku a gurin yayanku amma dai ba ku kyauta ba Allah. Haba anti kamar ba ki san soyayyar zamani ba? Allah kin ji mun rantse ba fa wani abu da ya gudana irin dai wanda yaya yake nufi. Ko ma meye ba ku dai kyauta ba. Mun gode da kika cece mu gurin yayanmu kuma zamu yi kokarin kiyaye afkuwar hakan a gaba, to ainma anti ini tambaye ki? Cewar lubabatu. Me ya sa ne nake ganin kamar akwai matsala a tsakaninki da yayanmu? Ba ma kamar ba ne, akwai matsalar. Lubuna ta karashe mata. Murmushi ta yi na karfin hali babu komai ku ne dai kuke ganin hakan. A'a anti kar ki rufe mu, suka dai matsa mata ta dube su da kyau, me kuke so in ce muku? Ko ko za ku ce min ba ku san halin yayanku ba n? To anti ko ma meye ai 46 matsalar taki ce abin da kika so shi zai yi, amma ji bi fa antinmu sam fa ba kya ba shi kulawar da ta dace, irin meye da meye din nan duk ke ba ki iya ba? kada fa kimanta idan ke ba ki mishi ba ba ki kuma ba shi kulawar da ta dace ba akwai dubban matan da irin wannan damar kawai suke jira, Me kike ganin zai afku? Me take ganin zai afku ko kuma me yake afkuwa? A dan zaman da suka yi tana jin ta fi kowa sanin shi kwararren maneminmata ne, to tun yaushe ma ta san hakan? Ta bawa kanta amsa. Suka sa ta a gaba fa sai fada suke mata, dariya suke ba ta wai 'yan fici-ficin yaran nan su ne za su koyar da ita yadda za ta zauna damiji, suka ishe ta, kai ku kyale ni fana dai fahirnta ta ron dangi kuke son yi min ku dayayan naku baki faya. Dazu ya ce zai 6ab6alla ni yanzu kuma kun zo za ku cinye ni da baki. Dariya suka saka, haba Antinmu. Ko zama be yi ba ya faramita, ni meye ne za ka bi ka cika ni da waya, har ma kana barazanar kashe min dodon kunnuwana da karar wayar. Zancen dai be wuce zai tuina... Zeenatu.. wace се? Wace ce? To ni dai ka bar cika ni da maganar 'ya'yan nan iskan harkar arziki ce a gabana, haka kawai ina cikin kula wace za ta fisshe mu kawa ni ishi mutane da waya? Tun dakai da alama kudin sun sihe ka har ma sun maka yawa sai kuma ya ce ka ma mai da hankalinka ba zai yiwu ni ina can ina shan rana ba kai kokana can 'yan iskan bariki sun dauke maka hankali har ma kana yi musu facaka da naira kamar ya yi a bola saboda ba ka san zafin neman su ba. Eh! Na ji ko menene gwanda ni ina alheri ina cin kuma dukiyata son raina ba wai kadangarun barikin kadai 47 suke cin arzikina ba wani fa? ko cikinsa bai iya hiidimtawa sai dai fa Kadangarun barikin nan kadai ke cin arzikinsa. Kuma ka sani ba wannan maganar ce ta sani kiranka ba, na kirawo ka ne domin ka shedawa waccan mara kunyar yarinyar, nan fa ba bariki ba ne gidan aure ne, don haka ta bar taramin Karatan banza da wofi. Ban fahimce ka ba. Ya fada fuskarshi a yamutse, Tiryan tiryan ya labarto masa komai ya kuma kara da cewa, don haka ka sheda mata ka kuma gargade ta zaman aure fa ta zo ba zaman bariki ba. Au ka amince matar taka ce ke nan ko? Da matar uban wace ce? Ya fada cikin kufula. Kamar haka na ji ka cc abaya, amma tun dayanzu ka ımaince wa hakan shi ke nan sai mu shiga kokarin samo mafita. Shawara ta ka hakura ka sauke rawanin tsiyar nan da ke kanka ka nemi sulhu gurin matarka kuma ka nemi soyayyarta idan har an dace tana ra'ayinka sai ita ma ta so ka shi ke nan ka ga sai a yi sabon aure harına a bude sabon amarci. Cikin daga murya ya katse shi, never! Never!! Never!!! In so ta ballantana har in nemi soyayarta, bana sonta ba zan taba son ta ba. na tsani yarinyar nan ba na ra'ayinta don an ce mata ta ce ba wai hakan na nufin na so ta ko ina son ta ba, na tsane ta, na tsane ta ba zan so ta ba na ce. Ranshi ya yi mummunan 6aci, ai ban san wannan rashin mutuncin za ka shuka ba da ban zo ba, aikin banza kawai ka ajiye yarinya kana gasa ta, to ka sani Allah sai ya saka mata. Kuma abin daka yi wa wani shi za a yi wa naka, na san wata rana ba za ka so hakan ba, to saika shirya wa hakan tunda dai takidinka ne wulakanta ‘ya'yan jama'a. 48 Na ji dai kome za ka ce ka ce amma fa ka lura ka gane kafin ka yi min nasihar ka fara yi wakanka tukun, aikin banza kawai yaran jama'a nawa ka yaudara ka kuma ci zarafinsu abaya ko don shi gwano baya jin warin jikinsa. Ya mike ko dai me na yi bai dai kai naka ba, tunda kai macen sunan kake yi wa wannan wulakancin ni kuwa fa kadangarun bariki ne, meye ko aibun yi musu hakan? Ai kowa ya sai rariya yasan za ta zubar da ruwa ne. Zan kuma shiga in shaidawa 'yar mutane kar ta raga maka a duk lokacin da ka nemi keta ta. Ina jin dai lokacin da za a yi hakan ba ka nan, saboda haka zan ma samu damar cudada 'yar mutane ne. Ya tarar da ita ita kadai a falonta yi zugum da alama tunani take, kâwai sai ya ji ta ba shi tausayi, yau ba karatun ake yi ba ne? ta dago ta dube shi har yanzu dai babu wani sakinf uska a tare da ita suka gaisa na zo ne a cikan alkawarina. Na me? ta tambaye shi na "BILKISU." murınushi ta yi, ayyah har yanzu na kasa kammala labarin, why? Aikin ofis ya hana ni sakat, idan na dawo kuma saika ga gajiya duk ta saukar min,to yanzu ba zan sami wani karin bayani ba a dangane da halin da Bilkisu ke ciki? Za ka dan sami karin haske amma kadan ne don iyaka ta Karshen kashi na biyun. To kafin a fara ba ni labarin BILKISU MAI GADON ZINARE a kawo min abinci tukun, yau ma dai da yunwar na iso,amma fa wannan karon kar a kawo min kwamacalar Bilkisu. Ta harare shi kana zolayar BILKISU wallahi zan gayawa safwan dinita ko dayake a karshen littafin yama ba ni haushi. A'a Hecdaya, kar ki min haka, ki hada ni da safwan, kin san fa abokinmu ne. 49 Da gaske? Ta-fada cikin sauri, da gaske mana, ya ba ta amsa. Kada kai ta yi kai haba gaskrya mana ashe abokanai kuke shi ya sa hali ya zo daya. Dariya ya saka kai Heedaya sai fa a bar ki, ina na san wani safwan a Kamaru a ka ce yake ko a ina ne to ina ma aka taba yin haka daga labarin alınara (kagagge) sai a ee an san mutum? Ajiyar zuciya ta yi gami da gano wautarta, ta dube shi, ka san Allah tun dana karanta labarin nan na ji kaunar bilkisun ta shige ni dama ita kanta kasar ta Kamaru, tunanina a ko da yaushe ta yaya za a yi na je kasar Kamaru cikin birnin Douwala ko na ga bilkisu, wallahi ji nake kamar in na je zan gan ta. Labarin ya tsaru, kana karanta shi kana hango hotunan abubuwan da ke wakana. Allah duk ranar da na sami dama sai naje kasar kamaru, a birnin Douwala cikin unguwar New-Bell, a yankin Marobiya mahaifar bilkisu, jinake da gasken zan ga bilkisun da ma mamanta Saudatu. Kada kai ya yi yana dariya, an gaishe ki Heedaya, abin ınaki baba ne to ni kuma na yi alkawarin duk ranar da aka tashi zuwa Kamarun nan zan biya kudin tikiti har ma da komai da komai na tsaraba. Kai ta kada lallai kam inda kuka tsąnenin nan yaushe za a yi haka. "Heedaya." Ya kira sunanta, a'a bari dai in je in hado maka abincin tun da yau ka ce ba ka cin kwamacalar bilkisu. Kitchen ta nufa ta fara hada mishi "Dillaf Rice wato a dafa shinkafa a tsane a sami yankakken koren tattasai, jan tattasai, albasa, a zuba a tukurya bayan an zuba butter a .ciki a soya sama-sama, a zuba talasasshen koda, karas, tumatur na gwangwani, gi magi, curry, thy me a 50 juya a a dauko soya sauce da kuma shinkafar da a ka tsane a zuba a yi ta juyawa, a rage wuta a bar ta ta turara a gefe guda kuma ta hado mishi chips and salad wato hadin salad me hade da soyayyan dankali, a bangaren abin sha kuma ta hado mishi mango drink. Yana ci yana zuba santi, har ya share abincin yanemi kari, tukunyar sukutum ta dire mishi da yake irintasu da 'yan gayu ceme murukin roba da murfi na tanaran launin kore (HappyHome) made in Germany. in maida ni rumbu, wallahi kaman fahimta kai rumbu ta'asss ne bama rumbu ba. Dariya yake sosai ta ce Allah gaskiya na fada matarka sai ta shirya. Wallahi ko kin yi gaskiya don in ba ta iya grki basaina lallasa ta har saista iya din.aikin ku ke nan dai duka-duka ku daki mace košku mare ta, shi ya sa har yanzu nake tunani anya ko ba da gasken ne Safwanun bilkisu ba abokinku ba ne? don komai naku daya ne. A'a kar ki mana sharri ina muke karatun wannan shirmen pallantana mu san wani safwan daga wasa kuma sai a ara a yafa har ma ya zama makamin yakarmu. Ya sauya maganar. Wai ko dan Allah ina mara kunyar kawar nan taki ne? ta bata rai wacce ke nan? Sameera ko samiha ko menene. Ta galla mishi harara abin ya soma gangarowa ga kawayera ne? ya ce a'a bahaka ba ne, yarinyar ce akwai tsiwa, wai ko kinga san da ake rikicin nan wani gatsine da aka dinga yi min da murgude-murguden baki kala-kala? To ya ishe ka dai cin zarafin naku kuma kada ya ta6a yar uwata. Ya yi murmushi, babu batun cin zarafi ni da za kiba ni ita rna da na gode miki. Baki ta rike ni wa! Allah ya 51 tsare ta da shig ahannun irin ku, ni din ma da na riga na fado addu'ar kubuta nake a kullu yaumin. Shi ma bakin ya bude lallai kam an tsangwame mu da yawa, me ya yi zafi haka har ake mana wannan bakar addu'ar? To duk ma daimu bar wannan maganar duk da daina gano wayon kar a bani Samiran ne bayan ko Samira ta Samiru ce a daura musu aure da Malam Sule dogo. Ya fara rera wakar har da dan tafi. D riya ta saka bayan da ta katse shi, ya isa da Allah za ka fara ko? Ya lura da kyau ta saki jiki da shi, don haka sai ya ce, to shi ke nan ah yi shiru din tun da wannan dinma ba a so. To ni sai a cika min alkawarina a karashe min labarin BILKISU MAI GADON ZINARE. Ta saki fuska yauwa, to yanzu na ji zance, kanaji ko..... ta fara ba shi labari tamkar tana karanto shi har zuwa inda littafi na biyu ya tsaya. Ta ciji lebe ka ga fa irin cin amanar taku, likitan ta ce fa? kai "Maza Ba Ku Da Tabbas." Cewar zainab Lawan, kai hakika kam ta yi gaskiya, wannan irin rashin tabbas haka? Hakika ya ci amanar bilkisu. Kada kai ya yi. Gaskiya kaım be kyauta wa bilkisu ba, to amma in ke ce ya za ki yi? Ta dan yi nazari zuwa can ta ce sai kawai in yi hakuri in ci gaba da tarairayarsa ina ba shi kulawa har zuwa lokacin da zai karkato gare ni tun da dai ina son sa. Ajiyar zuciya ya yi ya sami yadda yake so, ya kuma fahimce ta muddun yana son ta sake da shi su yi hira toya tabomaTahirar littafi, littafinma na hausa. Ya fuskance ta babu alamun wasa a tare da shi, "Heedaya." Ya ambata sunanta. Duban shi ta yi in miki wata tambaya mana. Ina 52 jin ka, ya ci gaba idan har za ki yi hasashen haka a dangane matsalar bilkisu menene zai sa ba za ki jarraba wannan hanyar ba a tsakaninki da maigidanki? Hcedaya duk da kasancewar ki kankanuwar yarinya Allah ya ba ki ilimime tarin yawa, kin fahimci matsalar al'umma har ma kuna iya tsaya musu domin kare hakkokinsu da kuma kwato musu 'yancinsu why? ba za ki jarraba hakan akanki ba? abin nufi tsakaninki da megidanki. Meye amfanin ilimi ne muddun ba za a yi aiki da shi ba? ba shi da wani amfani. Ki bawa kanki amsa karshe ma idan ba ki hankali ba ya kai ki ga halaka ranar gobe kiyama. Ki tsaya ki nutsu ki yi nazarin maganganuna kada ki yi dubayya da abin da ya faru abaya ballantana har ki sako shi a jerin abubuwan da ya hana ki kwantar da kai ki yi wa mijinki biyayya. Zama ne Allah ya riga ya hada shi ba fa wanda ya isa ya datse shi sai fa ranar da Ubangiji ya so, idan kuma be Kadarto rabuwar ba hakan muke fata, to ya za ayi ke nan? Dole watan wata rana a hakurcewa juna, kila ma lokacin Allah ya ba da albarkar zuri'a bayan ko a baya abin da yaka mata a yi ke nan. Shiru ta yi tana sauraronsa, mutane sun kasa fahimtar ta ballantana su san matsalarta lefinta kawai a ke gani bayan ko ta cancanci daukar matakin da ya fice hakan, saboda babbar illar da inutumin ya yi mata da ba za ta taba barin zuciyarta ta huta ba, ya riga ya gama yi wa zuciyarta miki tun da ya zuba mata guba me wuyar sha'ani har abada ba za ta taba mancewa da mutumin ba, ba za ta taba ganin girman sa ba kamar yadda ta san ba zai taba ganin darajarta 53 ba tun da ya riga ya gama da ita, zamansu kam ba zai taba yin armashi ba haihata-haiha...... Da ke nake Heedaya? Ya dawo da ita hayyacinta, ki yarda ki amince wa zuciyarki ki so mijinki ki kuma Kaunace shi. Cikin tsananin Gacin rai ta ce, Never, sam-sam-sam ba zan taba Kaunatar shi ba duniya da lahira, ba na son shi, ba na son shi ba zan taba son shi ba, kama sheda mishi yaba ni takarda ta na tafi gurin ne kaunata. Tahir nake so shi kadia nake Kaunata don haka ba zai taba saınun farin ciki daga gare ni ba. Kallo kawai ya tsaya ya bi ta da shi cike da takaici. ji yake kamar ya tashi ya kwada mata mari wannan katobarar da ta yi. Kai wace irin kiyayya ce ke zukatan mutanen nan? Kiyayyar ta yi yawa, in ka yi kamar za ka shawo wancan sai ka ji har ma gwanda dayan. Mikewa ya yi cikin bacin rai na tafi kuma ba za ki kara ganina a gidanku ba, tun da kin kasa daukar shawarata har ma kina wadannan maganganu marar sa kyau. Tana fadin Samir, Samir amına ko ya juyo ya dube ta, kuka kawai ta saka, babu wanda zai fahince ta ita kuma ta yi alkawarin babu me taba nin wannan yankan kaunar da ya yi mata ballantana a daina ganin zafinta. Zaune take ita daya a ofis aiki ya kacame mata sallama ta jiyo ta dago da niyyar ansawa, cikin matsanancin mamaki ta buda baki tana kallon shi. Tahir. Tа ambata haka. Ya sami waje ya zauna, kina mamakin ganina ko? kina tsamımanin duk inda kike bana tare dake ne? aiko ban kasance da ke ba zuciyata na tare da ke Heedaya. 54 Heedaya na damu da ke na rasa yadda zanyi da kaunar ki dare da rana kaunarki ta hinaa ni sakat, ba na iya baccin kirki, bana walwala bare nishadi tun bayan rabuwarmu why Hecdaya kike neman saba alkawarin dake tsakaninmu, zamanme kike yi ne har yanzu Heedaya? Ta dube shi ya rame ya fada kai ya ma ba ta tausayi haka kawai ana neman yi musu karan tsaye a rayuwa, ta ji wani irin tausayinsa, "Ka yi hakuri Tahir ina bakin kokarina, ka san shi komai lokaci ne idan lokacin ya yi babu mai iya kara min ko da dakika guda ne, amma dai abin da nake so ka bar zuwa saboda gudun zargin mutane ka san yanzu an daina kiwon dabba sai dai fa mutum, duk abin da kake mutane na halkance da kai. Mikewa ya yi cikin 6acin rai to na gode Hcedaya, na kuma fahimta kin daina kauna ta ko? Shi ke nan kawai. Tahir! Tahir!! Da sauri ta shawo gaban shi, kada kai min haka, idan ka yi min haka ka yi min rashin adalci da me zan ji ne? kuka ta samasa, jikinsa ya yi sanyi ya sami waje ya zauna,j to Heedaya ya kike so in yi ne? na ga ni ne kamar kin daina kaunata. Ba hakaba ne Tahir, kaunarka na nan daram а zuciyata babu abin da zai sa ta raunana balle ma in daina son ka, ka yadda komai lokaci ne, lokaci kuma nan nan zuwa in zama mallakinka Tahir. Lumshe ido yayi lokacin da yake kokarin tunano irin farin ciki da zai riski kansa a wannan rana. Ina son ki Hecdaya, son da ban san adadin sa ba, zan iya rasa rayuwata muddun na rasa ki. Runtse ido kawai ta yi sarai ta san akwai rashin da cewar zamansu ina ma lefin su tsaya a wayar, sai ta ji sam ita da kanta tana jin cewa ba su kyaut aba. 55 Karfe biyu dai-dai an tashi daga ofis zo mu je in sauke ki gida Heedaya. Ta dubeshi tana dogon tunani, akwai rashin da cewar hakan, to amma ba ta son 6ata ranshi sai kawai ta mike ya je ya sauke ta kawai ai ba lefi ba ne, inma ba ta bi shin ba ya za ta yi, domin da kyar ta iya kawo kanta zuwa ofis sakamakon imatsalar da notar take ba ta, akwai matsala a cikin injin motar, haka nan sharp dinmotar ya yi kasa. Ta kuma fada masa ko a safiyar yau amma ko ya daga kai ya dube ta. Yana tsaye a bakin motar yana kokarin budewa ita kuma tana daga daya 6arin tana haramar shiga da zarar ya bude suna daga tsayen suna tattaunawa a dangane da rikicin auren kawarta Sameera ya shiga zolayarta ku dai dukkaninku auren dole za ayi muku? Kai ma dai ka fada bayan tuni an daina wannan yayin, kai gaskiya ba a yi mana adalciba. Haka kawai ana shirin kashe mu da ranmu. Ya Karashe nata, dariya ta saka shi ma dariyar ya saka. Tahir ba ka da dama. To ina fa na gadamar tun dana rasa Heedaya, dukkansu dariyar suka dada sawa. Duk da kasancewar ayyuka sun kacame masa a ofis haka ya kawar da komai ya nufi dauko ta ko ba ta fada masa ba ya san motar ta akwai matsala mawuyacin abu ne ma ta iya dawo da ita. Rashin sani aka ce ya fi dare duhu, lokacin da Waheed ya yi parking da motarsa dab da ta abokin hamayyarsa, wani irin abu mai matukar tsini ya ji ya soki kahon zuciyarsa, lokacin da ya yi tozali da su, suna hirar su cikin nishadi har ma da kyakyata dariya. Ta kadu kwarai da gaske lokacin da ta yi ido biyu da shi to amma sai ta dake, sai menene don ya gan ta da 56 abin kaunar ta? Fakat ya sahale mata ta je ta auri abin kaunarta. Shi din ma ya lura da shi, kai ya ma riga ta ankara da shi amma sai ya dake ya basar ya ma shiga jan ta da hira duk dan ya cusguna masa. Ya gama bude motar ya shiga ita ma ta shiga sai da ya zo dai-dai saitin window sa ya dube shi da kallon raini kana jin cewa ka mallake ta har ka aure ta ba ka san cewa zuciya har ma da gangar jikin na wurin Tahir domin duka mallakinsa ne. Daga haka be kara cewa komai ba ya ja motar cikin matsanancin gudu, ko a jikinta kai Tahir din ma ya burge ta, idan ya yi fushi ya kuna tabbata shi mai zuciyar ne ya sake ta. Ko kafin su isa tuni har ya isa gidan, cikin matsanancin Gacin rai ya zama dole ya dau mataki na karshe a kanmara kunyar yarinyar nan. Tahir? Matarsa? Hannu ya sa aka ya dafe, za a yi balbalin bala'i zai sake tan don ya nuna mata ita ba wata tsiyar ba ce, to amma fa sai bayan ya gwada mata kaskancin da ya fi nata, cuta ce dại an riga an yi mishi, iyayansa kuma suka ja masa, shi daman tuni ya san yarinyar ba ta da tarbiyya kokankani. Karar mota ya jiyo ko da ya leka sai abin ya ba shi mamaki ita ce ya ajiye ta, ya tafi kamar ba ya so ba, abin ma sai ya ba shi mamaki lallai ma ta tabbata yarinyar tantiriyar mara kunya ce, bayan ma zamewarta mara tarbiyya in ban da haka har ta iya dawowa gidan shi zai kwa gwada mata ko a cikin tsagerun ita kankanuwa ce. Tun kafin ta gama shigowa cikin ainihin baban falonsu ya tare ta fuskar nan tashi babu sauran mutunci, ya dube ta ina jin cewa gidan nan mallakina ne ba da uban 57 kowa na gina shi ba? ballantana har wani ya yi tunanin akwai kason sa a ciki. Kau da kai ta yi ya ci gaba da ke nake karamar 'yar iska me ya hana ki juyawa inda kika fito. Ya je ya sa ma miki daki domin nan kin san ba bariki ba ne balle ya zama dandalin 'ya'yan iska. Ta dueb shi ranta a Gace kai bari ka ji ka kuma sani, abin da kake zargi hakan ne? ba haka ba ne? duk dai-dai ne domin shi nake kauna shi ne kuma zabina, saboda haka shi kadai ne wanda zan iya mallakawa zuciya har gangar jiki baki faya..... ji kake kauuuuuuuu! Ya wanke ta da mari. Ai ba sai kin yi hakan ba za ki nuna min ke yarinya ce marar tarbiyya. Cikin masifa ta ce, na ji na yadda to amma in ka yi fushi ka sahale min, dominni dai na gaya maka na kuma kara gaya maka bana son ka ba zan taba son ka ba, bana ma fatan na so kan. Ya nuno ta da yatsa, kin yi abanza domin kin da nake miki ya shallake tunanin dan adam ki ji ki sani, ki kuma sani kiyayarki a jinina take, shashashar yarinya mara tarbiyya. -Ta dada fusata, Eh daina ji ko me za ka ce na kuma yi farin ciki da hakan, zan kasance cikin kaiconrayuwa yayin dana fahinci burbushin so na a zuciyarka, to sai a ka sami akasin haka, na kuma gode Allah, domin ba ni da wani kaico a rayuwata, babu abin da ya fi kaico irin soyayar mutumin da kai kake mutukar kiyayyarsa, kawai ka sake ni ka hutawa kanka dama rayuwarka baki daya. Ko ba ki fada ba na sani na kuma fahimta ba tun yau ba manufarki ke nan har ma kike gwada min halayyar rashin tarbiyiya, don haka na kudurcewa zuciyata ba zan sahale mikin ba don kar na ba ki farin ciki, na fi so ki gasu 58 ki kuma gashe, har ma zuwa lokacin da masoyin naki z daina yayinki tun da akwai wanda da suka fi ki a tare da shi, yanzu dai yana kan yayinki ne kafin ya gama sidin kwanon ya 6aro sabo dallele. Karya kake na fi gaban haka gurin Tahir, duk hassadarka sai deai ka buga ka kyale,. Dariya ya ska yarinya na fi karfin na yi miki karya na gani da idanuna ne. Ta hayayyako mishi sai dai ya sake ta so take ayi ta ta kare hannu ya sa ya dakatar da ita, ke dakata, kar fa ki dauka ke wata tsiya ce yaki ce ki ba komai ba ne, kar fa ki manta babu fa wani abu da za ki yi min tunkaho da shi, meye bakona ne? wane dare ne jemage be gani ba? Don haka ki iya bakinki, ke da fankon ashana daya na dauke ku, kin san ko fankon da ba shi ashana a cikinsa ba shi da wani sauran amfani da

Chapter 4 of 8