shi shi ke nan tashi ka je dama na dauka ko wata matsala ce ta faru dana ga kwana biyu bana ganin ka.
31
Ta yi tsai tana nazari, wai me ya kawo haka ma?
Mota da ba tata ba shi ya sa har zai gwada mata wannan
gadarar banza da wofi, ya mance cewa ba daga gidan tsiya
ta fito ba, meye ma dalilin da ya sa har yanzu ba a kawo
mata motar ta ba ko dan kaucewa irin wannan wulakancin?
Telephone kawai ta dauka ta nemi layin Dadinta,
tun da handset din nata ya yi mata sanadinta. Sállama ta yi
gami da gaishe shi ya amsa cikin tsananin farin ciki,
ummina in ce ko lafiya? Kuna dai zaune lafiya ko? Ta yi
kokarin tattara yawun bakinta lafiya lau Dad na kira ne in
gaishe ka, in kuma ji lafiyarka. Dariya ya sa umıni 'yar
gidan Dady, dadinki yana nan lafiya har ma da mom da
Antinki Na'ima.
Cikin shagwaba ta ce, af daman ina so in kawo
maka karar Mom sam ta ki ta zo gidan nan har yanzu ita
ma anti Na'iman sau biyu kacal ta zo su ko su fa'iza sai sun
ga damar zuwa ko na yi aiken su zo ne. Yana dariya ya ce,
lallai kam ba a kyauta wa ummina ba amma barizanyi
maganin abin. Shi ke nan ummina? Ta ce uhm... uhm. Fadi
mana ummina, akwai wani abu da za ki boye min ne? ta ji
kwarin gwiwa daman Dad maganar motata ce, ina bukatar
ta Dad ayyuka sun masa yawa ba ya samin zuwa dauka na
da wuri, kin tabbata haka ne ba wata matsalar ba ce ko? Ta
saki dariya haba Dad babu kormai komai fa ya wuce.
Ya ce to kisha kuruminki galleliyar motarkiatana
nan tafe a cikin kwanakin nan shiru na vieban gava
don kar ki ishe ni da buge-bugen waya Ta sa kaa wayyo
Dad thanks very much, I loye you nny Dad. Yana jin
hargowarta ya kife layın yanka dariya kamar yadda ya fada
a cikin satin motar ta zo wato 'Exclade Jap.
32
Ko da yake megidan nata ya ce a dankawa ba ta dai
so hakan ba, amma dai tun da ta gidan ubanta ce babu
yadda za a yi da ita, ranshi in ya yi dubu ya 6aci, wato ta
gayawa mahaifinta ba shi da arzikin motar da za a kai ta
ofis? ko ko ta gaya musu ya hana a dauke ta a motarsa?
Don daure karya gindi shi ne aka turo mata da sabuwar
mota, kowa za a gwada wa karyar arziki?" to ai dai sai ya
yi ra'ayi za a hau tan za ta ga lalata ya ayyana hakan.
Shiru-shiru har tsawon sati guda be ce mata komai
ba, wannan dai ta gidan ubanta ce don haka tana da
hurumin da za ta bi bahasin hakan. Ba ta taba shiga falon
ba muddun yana ciki sai fa yau. Kerere ta tsaya a kansa,
fuskarta a daure ta dube shi, Malam mai mota, na ga
bakuwar mota a gidanka ina tsammanin kuma tawa ce, so
in hali ya yi sai a ba ni, in ko ta yi maka ne sai na sanar a
kawo minwa ta? Curarriyar maganar ta yi mi shi ciwo. Ya
yi dai shiru bai ce komai ba
Ba ka ji ba ne? Ta sake fadi, ina tarbiyya a gurin
yarinyar nan ya ayyana hakan, tashi ya yi dan ya gawda
mata iyakar ta, "Ke ko wani naki ba ku da arzikin da za ku
ba ni wani abu na karbaj balle ma wata akwalar motar da
ko jakin dawa sai marat galihu ne zai shige ta. Mari ta
kawo nishi ya yi saurid tike hannunta, kanshi ya shiga
girgiza mata, kin yi kuskure, ni za ki mara? to bari ki gani.
Kafin ta ankara ya kawo mata wani wawan mari da har
tsakiyar kanta sai da ta ji shigar marin, ta rikice sai akwai ta
sa kuka ta zube a nan.
Kanta ya zo yana karkada mata mukullayen motar,
kin ga wannan haramiyarki ba dai a gidana ba, domin ni
din nan da kika gani na fi karfin a zo a gwada min karyar
33
arziki, don haka ma nake shawartarki da ki yi gaggawar
shawartar wadanda suka kawo miki wannan aimalanken su
fitar min ita daga gidana domin gidana ba bola ba ne
ballantana a nemi mayar min da shi jujin yasar da
amalanke. Idan kuma har kin yi kunnan kashi da maganata
na dawo na tarar da wannan amalanken to sai dai fa ke da
itan ku tattara ki gidanku, ko da yake ko yanzu ma kofa a
bude take, ya sa kai ya fice abinshi.
Zuciyarta ta shiga ayyana mata a kan me za ta tsaya
tana Gata lokaci kan mutumin da yake maketaci mugu me
cin'zarafin dan'adam ciki ko har da iyayanta, za ta iya jurar
komai amma fa ban da ya wulakanta mata iyaye: Shi wane
ne ma? Gidansa din menene? Cikin Rankanin lokaci ta
harhada kayanta sai kuma ta tsaya turus, bayan da ta tunano
da rashin goyon bayan da za ta fuskanta daga wurin
iyayenta, musmman ma Dadin, kai kila ma abin ya juyo
kanta tun da tun farko sai da ya bincike ta ta kuma nuna
masa babu wata matsala, mugun mutuinin kuwa yana iya
yin duk wani abu da ya san zai kare kansa ya kuma
tsunduma ta a ciki, harma a karshe ya hada ta da iyayenta
kamar yadda ya faru a baya.
Hannu ta sa a ka tana fadin, "Wayyo Allana." Kuka
take har da kururuwa takaicinta ya zo ya riske ta a wanran
gida bayan ya riga ya gaına yi mata gorin sa.
Wani abu ta ji ya tsurga mata mai sanyi lokacin da
tunano isoffin arzikin, wato iyayan mijinta, taboas su kzafai
nc za su iya share mata hawaye. Kai tsaye gidan General
Abdallah Usman ta nufa. A yadda Haj. Fatima ta aria ta
san ba lafiya. Ita da Abdulwahab. ne a dakin yena dan
zolayarta amıma sai ya lura ba ta cikin walwala, ya nutsu
34
lafiya anti to sarkin tambaya daga zuwan mutuin ba ruwa
ba komai sai a cika shida tambaya. Cewar Haj. Fatima.
Yana dariya ya ce, to a yi mina fuwa, momy na lura
dai antin Yaya (kamar yadda suke gaya mata) ta kwace
fadar kowa, a gurinki. Nan da nan ya cika da ta kayan
kwalam, ya kuma zauna a gabanta, to Anti ci ko hankaliná
ya kwanta, na ga duk kin bata ranki. Ya gutsuro cake ya
mik bakinta ci Antina kada ki janyo mana jangwam wurin
yayannu ya ce mun hana amaryarsa abinci, please ... Anti,
pleasccee! Ya yi kamar zai yi kuka kawai sai ya sa ta
dariya. duka ta kawo masa tashi ka ba mu waje. Ya fice
yana dariya koke fa antinmu. haka kawai da kin hada rai
kin san u damuwa, to ire-iren kulawar da 'yan uwan mijinta
da ma mahaifansa suke ba ta ta wuce wai.
ta nutsu tsam! Yata me ya faru ne? hawaye kawai
ta ji na zubo mata, ta dada shiga damuwa, me ya faru ne
Heedaya? Ni mahaifyarki ce kar ki rufe ni, wa ya taba min
ke? Tiryan-tiryan ta labarta mata komai, abin da kawai ba
ta bayyana mata Ba shi ne makasudin da ya hana ta zuwa
ofis wato wayarsu da Tahir.
Tafa hannaye ta dinga yi tana salati, kai... kai....
amma yaron nan be kyauta ba. Abdulwahab? Ta shiga
kwalla mishi kira, yi maza, yi maza. Lafiya mum? Ya fafa
a razane, yi maza na ce sarkin tambaya duk inda Abdul
yake nemo mini shi. Lallashinta take yi har zuwa lokacin
da ya iso yana ganinta jikinsa ya ba shi, tashi ta yi tsam ta shiga cikin fakin ko kalle be ishe ta ba.
Yana Kokarin gaishe ta ta fara fadin, yau bana bukatar gaisuwarka, tun da kai yaron banza ne, zai yi
magana ta dakatar da shi, kira mahaifinka a waya tukun
35
kafin na ji tsarin naka. Yana jin hakan kirjinshi yaba da
dam,! Ya san 'yar iskar yarinyar ta fano mishi bom. har ma
da bama-bamai.shi dai General din ba yanan yana can
Kasar Slovacia don haka ne Haj. Fatima ta yi saurin sanar
mishi don a yi gaggawar yi wa tufkar hanci. Yaji kain ba
dadi gurin mahaifin nashi kamar yadda ya yi tsammani, ko
kafin ya gama ajiye layin Hajiyan ita ma ta dauka, to inma
ban da rashin hankali ina aka taba haka? Kai ba ka sai mata
ba an kuma dauko an kawo mata sai ka hana ta abarta
saboda ikon banza da wofi har ma ka bi ta da cin mutuncin
iyayenta, to kai ina taka amalanken da ka sai mata? Mara
kirkin banza kawai, maza tashi ka ba ni waje ka dau
matarka ku tafi. Tashi ya yi ranshi in ya yi dubu ya baci ba
wai fadan da ta yi mishi ne ya fi 6ata mishi rai ba, domin
wanda dadin ya yi mishi nata lami ne ma. Takaicinsa yadda
aka ci zarafinsa a gaban mara kunyar yarinyar wanda hakan
na kara ba ta lagon raina shi.
A kan hanyarshi ta fita ne ya ci karo da
Abdulwahab da Ra'uf, wani kallo suke mishi na jin zafin
abin da ya yi wa Antinsu ya kuma fahimci dalilin da ya sa
suke masa wannan kallon, ashariya ya sakar musu ya kara
uban wa kuke wa wannan kallon? Ko ni sa'an ubanku ne?
da yake akwai 'yar tazara a tsakaninsu,babu wanda ya
tanka masa, domin sun san haushin kaza wuce a kan dami
kawai yake son yi musu bayan sunsan shi ya yi rashin
kyautawar.
Hajiyan ce ta shiga lallashinta ta je su tafi, ita dai
kaın ba haka ta so ba a zatonta za ta yi wani kwakkwaran
abu ne a kai (ya sake ta) sakamakon cin zarafin da ya yi wa
iyayanta, amıma da yake ba za ta iya musanta mata ba sai ta
36
mike, ko banza a wanke mata wani bangare na daga
takaicin da ya kunsa mata, tun da an ci zarafinsa kamar
yadda ya ci nata.
Kofar gidan baya ta bude ta shiga. Daga shigarta ya
fisgi motar alamar har yanzu yana cikin fusata, har suka
kai gida babu wanda ya cewa wani kala ta buđe murfin
motar ta fita ta fara tafiya taku daya biyu, sai ta ji ya tsai
da ita, ya fara fadin, kankanuwar yarinya kamar ki ba ki isa
in yi miki karya ba ballantana har inmusanta abin dana
fada, abin tambayar a nan me ya hana ki inda kika kai karar
ki fadi musababbin rikicin ba (wato kama ta da ya yi tana
waya da saurayi).; ci gaba ta yi da tafiyarta bayan da ta
fuskanci inda ya dosa, koma dai menene ita ce a sama tun
da ita ke da nasara.
Wayewar gari ta nufi wurin aikinta a cikin dalleliyar
motarta, tana jin wani irin farin ciki da nishadi tare da farin
cikin nasara a kan abokin hamayyarta da ta yi. Mu je dai
zuwa nan gaba kadan ni ke da bababr nasara. Ta ayyana
hakan a zuciyarta.
Kallon shi ya yi ya dauke kai, aikin banza ma
malam, komaimutum sai ya yi wasa a cikinsa, in fa ba
neman kudi ba ne in ba haka ba tun yaushe nake zaman
jiran ka? Na dai ji ko ma me za ka ce. Ya fada yana dariya
a lokacin da ya zauna, dama ka shirya zaman jira domin ni
yunwa nake ji, mom ba ta gari ni kuma ba na iya cin
abincin kazaman masu aikin nan, ka kuma azalzale ni
ballantana na tsaya wurin abinci mai kyau in ci. Tabe baki
yayi ai ka ga tsiyar gwagwaren ke nan inda kana da mace
har ka tsaya neman abincin titi? Da dare ya yi kuma a shiga
kame-kame, ni da kai dinmeye banbanci? Ya ba shi amsa
37
ya ci gaba,babu wani abu da ya banbanta mu, kana yawan
gidajen abinci inayi, kana zaga gari har ma da bin dakunan
yaran jama'a ni ma ina yi....
Tsawa ya daka mishi ya ishe ka da Allah malam,
rufe mana baki. Kallon shi ya yi kana tsoron ta ne? ko kana
tsammanin ba ta san-abin da kake ciki ba ne? Ban sani ba.
yaba shi amsa da sauri ka rufen baki na ce kada anti amarya
ta ji ta rufe ni da duka. To to na rufe ya sa hannu ya toshe
bakinsa, kamar wani Karamin yaro, sai kuma ya ce, to ko za
ka gayamata ta miko mina binci dan ko na gaya maka
yinwa nake ji bana iya ko motsawa a nan da ka ganni. Ya
dan saki fuska gami da sassauta murya za ka iya cin
abincin kazamiyar yarinyar? Ya tambaye shi, kwarai kuwa,
me ma zai hana? Kai dai ba da umarni kawai ka ga aiki da
cikawa.
Fuska ya daure don ya fuskanci wulakanci yake son
yi mishi, ai ka san ba baiwarka ba ce? A'a kai dai fadi
gaskiya tsoron takake ji, to sai menene? Sai kawai ka daina
kira na da wanda ya yi yowa mata rakiya, domin kai rikon
jaka ka zo yi musu, ka ga ko ka fi ni.
Dauke kai kawai ya yi ya mayar da kallon shi ga
TV muddun ya biye mishi zai dada curo mishi wacce za ta
tafarfasa zuciyarshi.
Ya mike bari ni na je na karbo abincin da hannuna,
tun da ka san ni mace ba ta ba ni tsoro balle har in kasa
unkarar ta har ma na zamo dan rakiayrta. Be ce mishi
komai ba ya ci gaba da kallon sa fuska a daure tamau.
Tana jiyo su daga falonta dariya duk ta bi ta gama
cika ta, kai wannan mutum an yi shakiyi ashe bar abokin
nasa ma be bari ba? sai kawai ta ci gaba da karatunta ta ma
sha mur don kar ya kawo mata wargin da ya saba.
Assalamu alaiki amarsu ta ango, amaryar da ba ta
tsufa. Ya fada a lokacin da yake kokarin shigowa.
Kishingide take hannunta rike da hausa novel tana
karantawa. Ta dube shi cikin rashin sakin fuska suka gaisa,
to ni fa yunwa nake ji sai a tashi a nemo min abinci tun da
angor: naki marowaci ne yahana ni ko da dugon ruwa. Та
bata ra. ga shi kuma babu ya za a yi ke nan? Sai kawai ki
san yadoa za ki yi da ni. Ya ko zan yi da kai tun da babu?
Zai kar amagana ta yi saurin katse shi gami da daga littafin
hannunta, "Dan Allah Samir ka kyale ni bana son surutun
nan, ka bar ni in yi karatuna kawai, ai kuwa babu yadda za
ki yi dole ne ma yau na ci girkin amarya.
Ta dada 6ata rai ta san halinsa sarai da naci ga
rashin zuciya, ta dube shi yanzu saboda Allah sai ka hana
ni karanta "BILKISU"? bilkisu! wace bilkisu? "MAI
GADON ZINARE" ta ba shi amsa gami da nuno mishi
bangonlittafin. Ya tabe baki ke ma kina karatun shirmen
nan? ki bata lokacinki a banza a kan karance-karancen
shirme. Ta galla mishi harara shirme ma? Karatun littafin
shi ne shirme? To bari ka ji dubban mutane ne ke amfana
su fadaka su kuma ilmanta daga ire-iren littattafan da ka
kira su da na shirme. Har ma a wasu lokuta ka ga mutum
ya shiriya ya bar abin dayake mara kyau, to a nan me za ka
ce da wadannan littattafai da ka kira su da na shirme?
Haka ko?" ya ci gaba, to in ma hakan ne ni kam ban
gani a kasa ba. tamke fuska ta yi ta san shagube yake mata,
ta sauya zancen, so yanzu dai mę zan kawo maka tun da ka
rantse saika wahalar da ni? ko ma menene a kawo min.
39
murmu;shi ta yi to bari ka ga, yanzun nan zan hado maka
irin kwamacalar "BILKISU". WACE BILKISUN? Ya kara
tambaya "MAI GADON ZINARE" ita ma ta kara ba shi
amsa, murmushi ya yi, to-to-to na gane cewa za ki min
Bilkisu cikinlittafin Shirme.
To nì dai don Allah kar a hado irin kwamacalar
bilkisun, kin san ni cikina special ne, mikewa ta yi tana
hararar shi, ka ma ji da shi, ni dai babu ruwa na
kwamacalar bilkisun zan hado maka wato Indomie Jollop
da akai wa hadi da baked beans salad creams and sirdine a
gefe guda kuma ga tacaccen ruwaj inibi da strawberry. Ci
yake yana zuba santi lalaoi ki ce "Kayataccen girkin"
bilkisu zan ci ba kwamacala ba. ta dan saki fuska ah to na
gya maka akwai alfanu a cikin littattafan da ka kira su da
shirme. Lallai kam tun da ga shi ni mana amfana daga
kayataccen girkin bilkisu. ta yi murmushi har cikin
zuciyarta.
Ya dai fahimci tana son littafin, sai ya ce, to ni ma a
dan ba ni labarin BILKISU MAI GADON ZINARE na ji.
Cikin dadin rai ta shiga labarta mishi, ya yi kasake yana
sauraro, har zuwa inda ta dakata daga karatun littafin, ya
dube ta to sai a ka yi yaya bayan ta gama dafa mishi
indomin? oho ba kai ka datse ni ba ina cikin karantawa. Ya
ce ayya lallai kam ban kyauta ba, so ina fatan next time
idan na zo za ki karshemin labarin dan jin yadda za ta
karke musu? Sai kuma ya ce, kai amma fa guy din nan ya
yi wa sauran guys din keta, barin shi Aminun ko da yake
ya burge ni ko banza ya yi maganin irin wadannan kucakan
samarin da ba su kai su so yarinya ba har ma su ce za su
gwada gogayya da wanda ba tsaransu ba.
40
Daure fuska ta yi ta san magana ya cillo mata. Ya
fan yi murmushi domin ya san ta fahimci manufarsa. Ya
mike tun kafin su fara hauro ta, ni zan yi gaba na bar
angonki na jira na sai na dawo. Jin karshen labarin bilkisu.
Ba ta cc mishi komai ba saboda maganar da ya cillo mata
wanda ta taba masoyinta duk ko mutumin da zai taba
masoyinta koshi waye ba za ta taba ganin kirkin sa ba kо
me zai mata ko me zai ba ta.
Har ya kai bakin kofa ya dube ta kin san meye? Ta
ce a'a. yauwa to kin gane ko idan ni ne safwan a kai min
wannan kwamacalar zane yarinyar zan yi. Ai ko za ku
aikata, ko bakomai hali ya zo daya kai kila ma
akwainasaba. Shi ya sa ma nake kokarin harhada inawainawa tun kan a kai wannan matsayin. Dariya ya saka ya
fice yana fadin Barrister Heedaya.
Wani banzan kallo ya sakar mishi banza marar
zuciya yarinya na wulakan takata na kyarar ka amma kana
wani shige mata har ma ka mance da abinda ke gabanka.
Murmushi ya yi irin na tura haushin na, na dai ji ko me za a
kira ni amma dai ni ban zana matsoraci ba ballantana har
in zamanto dan rikon jakar mata. Sai kuma ya sauya
maganar, wallahi kana ba ni mamaki Waheed, sam ka ki ka
kwantar da hankalinka ka tsaya ku fahimci juna da yarinyar
nan, kullum sai tsiya kala-kala kake tata mata, to ka dai bi a
hankali in ba haka ba wata rana za ka yi ba wan ba kanin,
ka yi batan 6aka tantan a lokacin ne za ka ga ME GARI
YA WAYA? Alheri, alheri zai wayar min insha Allahu. Ya
fada cikin zafin rai.
Yanayin zamansu dai yana ci gaba da tafiya a haka,
babu girma barc arziki babu kuma maishiga hurumin wani,
41
tana ji kamar a kan wuta take muddin yana gidan, haka nan
ana sa bangaren yana jin wani irin tururi me zafin gaske a
zuciyarsa yayin da ya tunkari gidansa saboda tunanin
wacce zai je ya gani wai kuma a matsayin matarsa. Ba ya
son yarinyar sam ba zai taba son ta ba.
Al'amuransu da yake gudana a tsakaninsa da
Zeenatu babu abin daya sauya takan debe mishii kewa
harma wani sa'in ta mantar da shi duk damuwar da yake
ciki, me kamar Zecnatu me zai yi da wata kucakar yarinya.
A 6angaren ta ma babu abin da ya sauya daga cikin
al'amarinta da Tanir kuilum cikin huduba yake mata ta
kashe aurenta domin shine ya fi cancanta da ita, don haka
take zuba masa rashin arziki kala-kala ko da yake yakan
mayar mata da martani ninkin ba ninkin abin da take masa
ko kankani ba ya ragamata. Zaman dai ya ki dadi domin
tuni zukatansu sun riga sun tsumu da kiyayyar junansu.
dadin rai a dalilin Yinin yau ta yi shiri ne cikin
zuwan su Lubu sun saba da yaran tamkar tun fil'azal da
sanayya a tsakaninsu, ita dai lubabatu daliba ce a Jami'ar
Bayero (BUK) tana karantar Accounting. Shekarunta ba za
su gaza ishirin ba, ita ko lubuna daluba cc a kwalejin
tarayya (F.C.E) tana nazartar Hausa/SOS. Ita ma
shekarunta ba za su gaza ishirin ba dan tazarar da ke
tsakaninsu kadan се.
Da yammaci a ka shiga girki. kala-kala saboda
zuwan samarinsu, ita ko yayar tasu tia ta fi kowa zakewa,
suna tare dukkansu ababban falon gidan, sanyie take da riga
da wando na kasar Malesiya ta yi kyau ainun, halifa ne ya
dube ta wato saurayin lubabatu,Lo antinmu kina burge
ni kin iya karbar baki da karamci har ina nake addua'r
42
Allah ya sa kannannaki su yi koyi dake. Amir me son
lubuna yace, gaskiya ne Antinmu akwai kirki sai dai kuma
ina rokon a yi training kannanki yadda ya dace kosa zama
masu kirki kamar ki.
Kai-kai-kai, ku bar fa koda antin nan namu kada a
yi rashins a'a yayanmu ya ji ya ce kuna koda mishi mata
har ma ya fatattake ku, kunsan yayan namu akwai kishi.
Cewar lubabatu. kuma yana mutukar kishin antin nan namu
Kila ya hada mu da ku baki daya ya yi waje road da mu. Та
yi nunı da hannutna zuwa bakkin kofa, ai ko ta nuno shi
din a dai-dai saitin kofar fuskar nan tashi babu alamar
annuri a tare da ita, ba su ankara ba dariya suke har da
kyakyacewa, kai Heedayan ta fi kowa ma kyakyacewa. Ita
da ta riga ta gan shin ne dai ta gan shi.
Kai tsaye ya sa kai ya shigo.; to fa kowanen ya sha
jininjikins yayinda surukansa suka yi gaggawar zubewa
kasa domin gaishe shi, ba karamin daurewa ya yi ba ya iya
amsawa saidai fuskarshi babu walwala bare fara'a, ita kam
ko a jikinta, domin kalloma be ishe ta ba. sabanin shi da
yake mata wani bala'ya'yan kallo don kar a fahimci wani
abu da shi ta yi kamar ta bhi shi tsawon lokaci sannan ta
dawo suka ci gaba da hira.
Yana can ya kasa zuane ya kasa tsaye zuciyarshi sai
tafarfasa take yana jinwani irin suya a zuciyarshi. Da ya
rufe idonshi hango ta yake yi tana dariya yayin da
kumatunta ke lotsawa, la66anshi ya hade ya cije yana jin
wani irin abu bayan da ya hango fuskokin kyawawan
samarin da sukai wa kawanya. Matata? Ya nana ta no, no,
no hannu ya sa ya dafe kai bayan da ya tabbatar dai matar
tasa ce. Why? Why? Why? Yake jin wani irin kishinta.
43
Tsaki ya yi saurin ja Allah ya tsare shi da kishinta. Abinda
kake so shi kake wa kishi, shi ko ba ya sonota ya yi
amannar hakan kai ba ma zai ta6a son nata ba.
To amma why har yanzu zuciyarshit ake dafa
azalzalarshi da wani abu me kuna kasancewar ta da wasu
mazan, mazanma samarin kannanesa me ya sa haka? Ya
tambayi kanshi.
Awanni biyu cur da dawowarshi ya kasa barin gidan
wanda da da ne ba zai yi wannan dadewar ba da ya yi
wanka ya gama abinda yake zai fice sai kuma dare wani
sa'in ma idan ya raba. Zuciya ta kawo shi ya nufi babban
falon nasu da niyyar cin zarafinsu baki dayansu a
kanmenene za a nemi mayar mishi da gida bariki saboda
kawai ya auri yarinya mara tarbiyya, ba ta falon kai tuni ma
ta yi ficewarta, ya iske su ana zuba soyayyar nan irin ta
yaran zamani, lubuna na kwance a kirjin masoyinta ita ko
lubabatu pillow ta yi da cinyar masoyin nata.
Ashariya ya fara saka wa sai kuma ya shiga
banbami mara sa mutunci masu ata yaran mutane, ku
shige ku ba mu waje kar na kara ko ganin kafarku a gidan
nan ko a can gidanmu, tun daku lalatattu ne marasa
tarbiyya, ku fice na ce kar-kuma na kara ganin kafar
kowanne dan iska a gidannan. A kan me? ta fada a
lokacind a take kokarin shigowa harara ya galla mata nan
fa ba gidan 'yan iska ba ne don me za a taramin karatai a na
yi min shakiyancin banza. Murmushi ta yi kai haba da Alha
kar ka bada ni mana, soyayya zamanin ce za ka ce ba ka
sani ba? ca na ke anyi wanda ya fi haka. Kai wasu ma sun
yi wanda ya shallake haka. Mari ya kawo mata saurin rike
shi ta yi, haba dai wannan yayin tuni ya wuce to ma meye
44
abin bugu daga fadar gaskiya, soyayar zamanin ce ba ka
sani ba? zan ko yi ınamaki idan ka ce ba ka san haka ba.
Anti ki ba wa yayanmu hakuri abin da yake nufi ba
haka ba ne. cewar khalifa masoyin lubuna. Ku je abinku
babu damuwa ai ba gona da iri kuka wuce ba domin wasun
gona da irin suke shigewa har ma su man ta su watsar da
irin a wurin dabe dace ba. Tsayawa ya yi galala yana
kallonta har matasan samarin suka fice ba tare da ya ce
komai ba.
Kansu ya yo da duka za ku ci ko ubanku a yau,
rukunkume ta suka yi Anti ki cece mu, wallahi ba wani abu
muka yi ba daga fa kawai munzauna waje daya. Kai da
Allah ku sha kuruminku na gaya muku ba wuce gonada iri
kuka yi ba ina ga masu wuce gona da irin?
Cikin fusata ya ce wallahi zan hada har ke har su
din in bab6alla yarinya, ko ki sake su. Ta dube shi sama da
kasa tana wani irin dariyar tura haushi, ni kam na kan rasa
tunanin wasu mutanen wani sa'in, wai ini tambaye ka
mana? Shin ka mance da cewa abin da ka yi shi za a yi
maka? To ina lefin suma su da ba su wuce gona da irin ba.
ta yi