yi fatali da farin cikinta a
kan farin cikin wasu daban duk da tsagwaron Kaunar
da yake gwada mata wanda rabi-rabinsa 'yan uwanta
ba su samu ba, ita kanta ta san hakan, amma a yau wai
duk ya kau, har ma idanun dadin nata ya rufe yana
shirin hada ta da gagarumin makiyin da ba ma ita ba
shi da kansa ba shi da kamar sa, wai me ya sa ne ba za
96
ta bayyana yankan kaunar da mutumin ya yi mata ba?
babu tantama dadin nata zai janye daga wannan niyya tashi ko yanzun ta san rashin sani ne, to amma ina har
abada babu wanda za ta iya bayyanawa wannan yankan kaunar da ba za ta taba mancewa da shi a
rayuwarta ba. Ba don komai ba sai don dalilanta na
baya, tana son Tahir tana kuma taka tsantsan a kan duk
wani abu da ka iya kawo musu tarnaki, kamar yadda
ba za ta taba yin saken da za a hada ta da wannan
mugun mutumin ba. ta tsane shi, sam ba ta kaunar shi
ba za ta taba kaunatar shi ba.
Duk da kasancewar an riga an sa mata
takunkumi, sai da ta yi dabarar da suka hadu da
masoyin nata da yammacin ranar asabar a harabar
wurin shakatawar da ke cikin Nassarawa G.R.A. "Fish
Park".
Cikin yanayin damuwa ya dube ta, "Heedayah!
Wane hali zan riski kaina yayijn da na rasa ki? Hakika
rayuwata ba ta da amfani a lokacin ina son ki
Heedayah, ina son ki so mara iyaka, son da ban san
adadinsa ba, ki so ni Heedaya, kar ki bari wani ya
kwace min ke, wai shin wanene ma wannan mutumin?
Fada min ko na gargade shi ya fita hanyar a bar so na,
domin ni kadai na fi cancantana mallake ki.;
Runtse ido ta yi bayan da hawaye ke zubo mata
lokacin da ta tunano da kaddararran mutumin da ake
shirin kakaba mata da ko kaďan ba ta kaunar kuka ya
97
ei Karfinta, girgiza ta ya yi, Heedaya, menene? Ba kya
son sa ko? Ni kike so, gaya min wanene na jena
gargade shi.
Cikin tashin hankali ya ce, "What? Bayan da ya
fahimci inda ta dosa, waheeeeed..., karya kake, karya
kake wallahi, ba za ka taba cin galaba ba a wannan
karon, zan gwada maka kaskanci da wulakanci tun da
ka yi saken da ka kara shiga hrumina, never! Never!!
Wallahi never kai da Heedaya, Heedaya mallakina ce
ni daya. Kai ya birkice ya ma haukace sai sambatu
yake gaba daya ta bi ta tsorata, yanayinsa kamanninsa
kai komai nashi ya sauya, jikinta sai bari yake, lallai
kam. wannan wace irin adawa ce a tsakaninsu, ta
fahimci hakan tun karansu na farko.
Ta kasance cikin damuwa da bacin rai ta tashi
hankalinta ainun, kųkan safe daban narana daban, amma
babu abin da ya sauya daga kudurin mahaifinta, sai ma abin
da ya ci gaba, kamar ko yaushe yau ma kukan take gami da
bijirewa umarnin mahaifin nata, a lokacin da ta gurfana a
gabanshi domin nuna adawar ta da wannan aure.
Ya dube ta jiki a sanyaye Heedaya akwai wani abu
da kike nena a duniayr nan da ban taba yi miki ba? ko me
kike so komai tsadarsa bana gudun mallaka miki duk dan in
farantamiki, shin ma meye ne a duniyar nan ban yi miki ba?
ine kika taba nema a gurina kika rasa? Amma abu guda
kawai kin kasa yi min biyayya a kansa? To ina ba ki
shawara ki sawa kanki salama ki bar tayar da hankalinki
aure ne dai kam babu fashi. Cikin yanayin kuka ta ce, aah!
98
Dady, aa! Walla а gаye maka ko me
za a yi min Allah ba zan a
zan kashe kaina in huta, ba na so.
aure shi ba Tahir nake so, shi ne kawai zaon l Kitu
ta rike baki sakato "Aah! Alhaji a na me za
sabauta 'yarmu a kan son ran wani? Sam-sam haka ma ba
za: y.u ba. ta fada tana me kada hannu, ta ci gaba a ba ta
zabinta kawai ba shi ke nan ba mu za mu zauna mata da
mijin? Tun da ta ji ta gani ai sai a ba ta zabinta sabo da
Allah.
Ko da yake ita ma Haj. Kaltum din ba son Tahir din
take ba, to amma tun da abu ya kai ga haka ai sai a hakura
da dai su rasa 'ya mafi soyuwa a duk cikin 'yayansu tana
son diyarta fifikon son ta ya rinjayi na dukkanin
'ya'yayenta, tana kuma son duk abin da take so don haka
ına ya zama dole ta cusa son yaron a zuciyarta domin shi ne
cikar farin cikin diyarta.
Cikin matsanancin 6acin rai ya dube ta, "Ban san ba
ki da dogon tunani da hangen gaba ba sai a yau, ina ce ni da
ke duk mun san makasudin kKiyayar aurenta da wannna
yaron....." ta datse shi to Alhaji ba sai a janye ba tun da dai
yarinya ta ce ta ji ta gani shi take so.
Ya nuno ta da yatsa, ke ko diyarki ba ku isa
saka ni abin da ba na ra'ayi ba, kamar yadda ba ku isa
saka ni abin da ba kwa ra'ayi ba, dogon tsaki ya ja sai
kuma ya fice karan farko ya yi nufin isa sassan Na'ima
ko ya sami sassaucin zuciyarsa, amma wani hucin zafi
ne ya bugo shi, irin hucin da yake ji a duk lokacin da
ya yi nufin isa sassanta why? Ya tambayi kansa.
99
yarda da wannan sangartar, koma wane ne ta aura komai
son da yake mata. Ai ita tarbiyya a hannun iyaye take, kar
ku mance gaba daya yarana na haife su ne a cikin kudancin
Kasar nan inda wani gurin ma ko 6irbishin addinin
Musulunci babu amma wa kuka ga yana irin wannan
rayuwa? Me ya janyo hakan? Saboda sun sami
ingantacciyar tarbiyya tun daga tushe ba sai rana tsaka ba
ka ce za ka ga garayaro ka tankwara shi yin abin da tun da
fari ba ka riga ka haska masa ba (biyayya).
Hannu ta sa ta dafe kanta ya isa, yaya yanzu dai
meye mafita? ban san yadda zan yi in shawo kan yarinyar
nan ba, ta kafe ta nace ba ta ra'ayin yaron nan. Ah! To, ai
irin abin da nake nuna nuna miki ke nan tun kan “GARI
YA WAYE" yanzu kam da "GARI YA RIGA YA WAYE”
kya san yadda za ki yi, in ba ki da gaske ba ma nan gaba
kadan a barki da kalmar nan ta "ME GARI YA WAYA."
Makwanni kadan ya rage a daura auren abokanan
radawara hannu guda kowannensu na kulla wacce za ta
fisshe shi, haka nan Samir na bakin kokarinsa wajen shawo
kan abokinshi amma tamkar yana kara ingiza shi ne, har
Ima ya fahimta tun zuwan nan da suka yi be kara taka kafa
gidanba, alhalin lokaci kadan ya rage don haka ya ga rashin
dacewar hakan, shi dai kam be isa funtubar shi da batun ba
musamman inda yake cikin, zafin nan sai ya yi mishi me
gaba dayan ya hada shi da General din, to fa bacin rai kam
ya fuskance shi daga wurin General din har ma bai son tuna IIKO KALIN LICO Я К
-kalaman da ya gargasa masa.
Babu yadda zai yii domin shi kam be isa ja da
mahaifinsa ba Samir din ne ya lallába shi suka tafishi ne
レ
ma ke jan motar ranshi daí duk a bace yake, tákidin tsiya ne
101
Komawa ya yi da baya zuwa harabar gidan kai ya hada
da gwiwa yana me tagumi bacin ran abin da 'yarshi ta
yi mishi duk ya addabi zuciyarshi wai yau 'yar da ya
tsuguna ya haifa ya kuma nuna mata fifikon so, take ja
da shi har ma ta kasa yi rnishi biyayya me yasa ne?
(a'a to, shi dai itace tun yana danye ake tankwara shi
yayin da ko ya riga ya bushe mawuyaci ne ka tankwara
shi, domin idan ka matsa shi zai balle baki daya ne,
kukan kurciya jawabi ne me hankali.....).
Janyo ta ta yi jikinta tana ci gaba da sababi
kan menene za a nemi salwantar mata da yarinya?
a
Haj. Mariya yaya ce a gurin Haj. Kaltum tana auren
wani babban sojan sama a can birnin Ikko. Ta muskuta
bayan da ta gama jin damuwar 'yar uwarta ni kam ina
mamakin ki Kaltum, halinki sam ya banbanta da namu in
ban dahaka mahaifinta ya ce eh ki ce a'ah, a ina aka taba
haka? Saboda Allah ai shi mahaifi shi ke da iko fiye da
mahaifiya don menene za ki yi masa katsalandan....? ta
katse ta a'ah, yaya ba ki fahimce ni ba fa, ba fa wai ba na
son wannan aure ba ne kar fa ki manta Haj. Fatima
tsohuwar aminiyata ce, ina dai duba sha'anin yarinyar ne
tun da ga wanda take ra'ayi ba sai a bata ba.
Tun da kuma ita ta tsuguna ta haife ku ba ku kuka
haife ta ba? ta fara sababi, haba duk kun bi kun sangarta
yarinya ba dole ta yi muku wannan tsiyar ba, abin da
yarinya take so shi za a yi mata babu kwaba bare tsawatar
wa? Batun yau ba ina nuna miki illolin hakan, to bari ki ji
wannan ba gata ba ne ba kuma so ba ne, sai ma kokarin
cutar da rayuwar ta da kuke yi, domin babu namijin da zai
100
kala-kala a zuciyarshi, ya kuma shirya mata a duk irin
yadda za ta zo mishi.
Baki ya washe ya kuma hangame kamar yadda ya
hangame musu kofar ya russuno jikin motar domin ya
shaida su, barka da zuwa an iso lafiya? Sai kuma kuka бace
ko kasa ko sama? Har na fara tunanin ko dai kun hada iri
da jinsin mutanen Sulaimanu? Ashe ba haka ba ne
sannunku, sannunku da zuwa, duk dai baba mai gadini ya
fada a lokaci guda baya ko numfasa wa.
Yau 'dai babu wasa tamke fuska ya yi tun da yana
cikin bacin rai fiye da na baya Samir din ne ya yi kokarin
ba shi amsa, sannan ya ce Heedaya muke son gani. Ya
amsa to...to...to..., ashe dai yau ba mutan gidan kuke son
gani ba? wato ya mayar musu da martanin abin da shi
Waheed din ya fada a farkon zuwansu. Sai ya ci gaba, Si
dai fa abokin nawa yau babu annuri a tare da shi har ma ya
ki ya ce min komai, ko ko zulumin haduwa da ta gaban
goshin kake? Ai na gaya maka diyar tamu akwai kyau
tamkar ta hada iri ce da jinsin Sulaimanu, ko da yake kai
ma ba baya ba ne.
Tsoho har tsoho amma ya kasa rike tsufansa. Cewar
Waheed cikin daurarriyar fuska, kunshe baki ya yi
a'aaaaah! Yau kuma curarriyar aka curo min, to bari dai in
je in turo ta tun kafin a curo min wacce za ta cunkushe mini
zuciya.
Ji mana. Ya fada a lokacin da ya dada cukwikwiye
fuska, ka fa shaida mata ba fa wani rawar katar ganin ta
muke ba idan ta fito a kan fokaci ta yi wa kanta suttura, don
mun bar kara yadda a shanya mu kamar tsummokara.
Rintse ido Samir ya yi gami da cıza labbansa, a lokacin ne
102
kuma baban ya shiga ba shi amsa, ai ko abokina ba ka yi
kama da ko tsohon zani ba balle fa tsumma?" ban ki ba dai
ko na hannun damanka (ya zunburo shi da baki) ya so yi
min kama da tsohon zanin kakata Delu har ma idan be yi da
gaske ba taki kadan ka iya zama tsumma har ma ya tsume.
Dariya ya saki hahahaha abin shi, shi ko Samir bakt ya
bude rashin mutuncin yau kuma kansa zai juyo? bai san
sanda ya ce kai wannan an yi dattijon banza, inda yake dan
Kwalisa sannan yake kuma jin kansa lambaya daya amma
yake mishi wannan sharrin, shi da yake raga mishi, kwafa
ya yi, abin har ya so bawa Waheed din dariya amma da ya
ke ba lokacin dariyar ba ne sai ya gintse.
Ba da jimawa ba ya dawo kun ci sa'a don ban yi
zaton tana iya sauraronku a wannan lokaci ba sai kuma ya
rankwafo da sigar gulma, kun san fa idan tana tare da
shegen yaron nan me kama da zabiya ba ta iya sauraron
kowa. Na tsani zuwan yarop nan firgitar da ni yake, domin
yakan tuna min da mutanen Sulaimanku, ko dayake akwai
shi da sallamar kirki, ba kamar wasu ba da sai dai a zage a
gudu don dai kar a yi min salanar arziki. Da su yake sun
fahimta.
Baba! Ka kwa binciki kalmar nan tawa? Waheed
din ya fada lokacin da yake kokarin fitowa daga motar.,
wacce fa nutumina? Ya ci gaba da tafiyarsa, bayan dayake
ba shi amsa, surutun nan na tsiya-tsiya. Buda baki ya yi ko
kafin ya ba shi amsa Samir din ne ya amshe, tsoho, tsoho
ne, amma wani tsohon na banza ne, har,ma da na wofi, shi
kuma Waheed ya karashe mishi suka yi ciki abinsu, suka
bar shì a nan yana sambatu. Za ku ci kaniyarku ni za iku
jawa janwuru? 103
Kayatattan lambun gidan suka nufa kamar yadda
baba maigadin ya nuno musu mutum biyu ne a zaune kan
kjcrun da aka tanada don lambun (garden) Mace ce da
namiji suna mutukar kusanci da junansu, sai dai ba sa iya
tantance fuskakinsu, domin baya suka ba su, ja ya yiyi ya
tsaya Ryam a lokacin da ya fahimci ko wanene ke tare da
ita, ya yi nufin Juyawa,a/Samir din ya yi hanzarin rike
hannunshi gagam. Cikin karfin hahjinya yi kokarin mika
mishi hannu amma Tahir din a dioy i mhi an
Easkantaccen kallov/be karaya bayya ce, Barka da hutawa
amaryarmu, in babu takura ango na san magana da ke.
Kalton da ta yi masa shi zai tabbatar maka da tsantsar
Kiyayyar da take wa abokin nasa.
Alhamdulillah!
A Nemi Kashi Na Biyu Wanda Suka Fito Lokaci Guda
Mai Kaunarku,
Zainab Kabir Biroman
104
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels