zo kuwa? Ni ko na
sani domin ko be wuce wurin yarinyar da ake shirin kakaba
min ba. To a bar maganar cewar Samir.
Sauka cc aka yi musu irin ta gidan masu da shi, kai
ka ce an san da zuwansu, ko da yake galibin gidan masu da
shi ba ka raba su da cima ka me kyawu a kowane lokaci ne.
Duk da kayatuwar dakin babu ko wanda ya damu
da shi domin sun ga wanda ya fi shi haka nan kayan
alfarmar da aka dire musu ba a gabansu yake ba, Samir din
ne ma ya dan jika makoshinsa da tataccen ruwa mai sanyi.
Zaman duk ya ishe shi ji yake tamkar a kankaya
yake, zuciyarshi ta dada kawo wa wuya, kai ko ma wacece
ko 'yar uban wacece shi kam ba ya ra'ayinta, dan menene
za a wulakanta su a shanya su kamar kayan wanki? Gaba
daya ya gama kissima wacce za ta fisshe shi. Samir dai ya
yi shiru bai tanka ba, fatansa su fita lafiya kada ya tatawa
'yar mutane rashin arziki.
A can gidan ma Haj. Kaltum na can na fama da
diyarta ta rasa ta yandaza ta bullo mata, daraba ce ta fado
mata ta yi kokarin hada ta da Dadin nata a waya to shi din
ma lallashi ya shiga yi, Dady zan fita sai dai ina soka yi
min alkawarin cikar burina ko ma menene in dai bai wuce
Ka'ida ba zan miki.
80
Da haka ya lallaba ta har ta amince za ta je gurin bakin sai dai fa ba haka nan ta tafiba akwai tsiya takun da ta shiryo musu.
Ya ja tsaki ya fi sau a kirga, Samir dai bai iya cewa komai ba don kar ya zunguro shi.
Cikin isa da kasaita ta isa falon har ma da kyar ta iya yi musu sallama, kamshin turarenta gaba daya ya gama
gauraye dakin za ka so ka dauwama kana shakar daddadan Kamshin.
Kanshi a sunkuye yake ko alamun dagowa bai yi ba yayin da Səmir ya dago da niyyar yi mata barka da zuwa,
amma kuma sai ya kasa baki ya bude cike da mamaki, ba
wai tsabar kyawun da ake zugwigwitawa ba ne ya tsorata shi, a'a tsagwaron mamaki gami da taʼajibi ne. Daya daga cikin kujerun dakin ta samu a ta zauna
lokacin ne ya yi yunkurin dago fuskarshi, kamar hadin baki
ita ma a lokacin ta dago fuskarta, to fa! Idanunsu suka yi
arangama da junansu har ma a cikin dakikoki kankani suka shiga turawa junansu sakon da ke cikin zukatansu.
Mikewa ta yi cikin matsanancin bacin rai babu
alamar annuri a idanunta, ta ja gabansa ta tsaya kerere,
hannu ta sa ta nuna shi da yatsa ta dube shi da kallon raini,
Ka kuwa ba ni kunya ka kuwa ba ni mamaki, ashe jin kai
da isar na banza ne? ashe fangima da gadara duk na karya
ne? kamar dan General guda sai an yi kyautar sa? To bari
ka ji ko fitowar nan da ka ga na yi na fito ne'a kila-wakala
idan ya yi mini sai in so shi, idan kuwa be min ba babu cuta
bare cutarwa zan bayyana masa. Ta dan yi murmushi me
kama da yake to fa sai dai ka yi hakuri sam ba ka yi mini
ba, ba na son ka ba kuwa zan so ka ba, babu me iya sani
81
kuma in so ka, domin zabi a ka ba ni ka ga ko ba zan kwari
kaina ba ko don cewa har yanzun nan akwai mata masu
daraja wadanda ba a iya kyautarsu, ko da yake ko a mazan
ma akwai mazan na hakika masu nagarta da ba a iya
kyautar da su. Na bar ka lafiya Dan General. Ta yi ciki abin
ta yayin da ta bar shi da cizon yatsa.
Tafe suke a motar kowannensu ya yi shiru babu
batun magana, maganganun yarinyar na shirin tarwatsa
zuciyarshi, ta gama da shi ta kuma yanke shi Dadin ne
kuma ya jawo mishi hakan. Ko da zato ko da tsammani bai
taba kawo cewa yarinyar ba ce ko da ko a turmi Dadin
nashi zai daka shi da bai yarda ya zo ba wannan rainin
hankali haka?
Ya fuskance shi ya shiga fadin wallahi a ranar da
duk tsautsayi ya gifto na ci karo da yarinyar nan sai na
karairaya ta, zan kuma nuna mata ita kucaka ce ko a cikin
'yan iskan. Cabdijan, ko waye ma ya yi wannan hadın ya
hada masifa da bala'i domin-hadin sam be yi ba, in ba haka
ba kuwa za a WAYI GARI a iske yarinyar mutane a
karairaye. Ya ma za a yi na auri wannan 'yar iskar
yarinyar? Never!!!
Na fada na kuma kara fadin hadin sam be yi ba.
Samir din na jin sa ya ja bakinsa ya yi gum har ya yi
tabotsansa ya gama, ko dayake kashi casa'in da tara da
digo tara yana bayan abokinshi, hadin kam sam be yi ba,
tabbas kam akwai kamshin gaskiya a maganarsa, ba don
komai ba sai dan tsinkayo irin zaman da za a yi idan har
aka naçe da wannan hadın,.
82
Kan cinyar mahaifiyarta ta fada da shigar ta ta shiga fadin na shiga uku momy ki taimake ni kada Dady ya hada ni da wannan mutumin, sam ba na son
sa ba na taba son sa domin maketaci ne sam ba shi da
halin kirki, shi ne fa wanda nake gaya miki ya mare ni
kwanakin baya, wallahi momy ba na son sa ba zan taba son sa ba.
To fa yau fa ake yin ta, ya a kai yi haka ta faru
ne? tambayar da Haj. Kaltum take wa kanta, to amma
duk wannan ba wani matsala ba ne rashin sani ne
kawai da kuma rashin fahimta don haka nake so ki
kwantar da hankalinki da zarar kun fahimci junanku
shi ke nan, amma ina! Ga Heedaya ta san matana yi,
tini zuciyarta ta gama yin nisa ga kiyayyar mutumin.
Ya yi sallama ya riske ta da kannansa lubabatu
da lubuna, ya samu waje yazauna yau dai babu alamar
wasa a tare da shi dan haka kowacce ta kama gabanta.
Ta dube shi ya daga zuwanka za ka korar min yara?
Kansa ya dafe momy bar ni kawai, ta mai da
hankalinta gare shi dan tana mutukar son dan nata.
Lafiya dai ko? Ina fa lafiya mum, ya ci gaba bayan
Dad yana shirin hada ni da wata fitsararriyar yarinya,
wallahi sam bana son ta, kai ba ma zan iya auren ta
ba.ta tattara hankalinta gaba daya a kansa ban fahimta
ba Abdul? (a mafi yawancin lokuta ta fi kiran shi da
wannan sunan) ba kunkya ya mursiye ya shiga
bayyana mata rashin kaunar dayake wa yarinyar....
83
Dakata, ta datse shi da hannu, ka ko san abin da kake
cewa, to in ma mafarki kake ka shirya ko kuma dan ni
ka raina ni ne shi ya sa ka zo min da wannan batun to
tun da ba ni na ba ka yarinyar ba sai ka je ka gayawa
wanda ya ba kan.
Marairaicewa ya yi haba momy na san kina son
duk abin da nake so, kina son kuma farin cikina ba za
ki so a hada ni da abin da bana soba, shi ya sa na biyo
ta hanyarki, don Allah ki taimaka ki yi wa Dady
bayanin komai, mur ta sha.
Dakata Abdul na dai fuskanci so kake ka
dagulan lissafi ka kukma janyo matsala tsakanina da
Dadinku, amma in ba haka ba me ya kawo wannan
magana? Ka fi kowa sanin mahaifinka ba a sa shi ba a
hana shi ni kam ba da ni ba in tare shi da wannan
maganar, ina ga in za ka iya tarar sa to bismilla amma
fa ba da yawuna ba, domin ni dai ban ga aibun
yarinyar nan ba, iyayenta mutanen kwarai ne masu
dattako, haka nan ga yadda na fuskanci yarinyar akwai
tarbiyya a gare ta, to meye kuma ya yi saura?
Zai yi magana ta dakatar da shi kar ka ce min
komai ni dai kam na gama magana ruwan ka ne ka bi
abin da na ce ruwanka ne ka bi son ranka.
Ji ya yi ya rasa me yake masa dadi, tun kan aje
ko ina ya soma fuskantar matsala a gurin wacce yake
ganin za ta share mishi hawaye. Ya kasance cikin
damuwa a bisa wannan gurmi da ake shirin hada mata,
84
to amma kuma zuciyarsa ta sanyaya lokacin da ya hango makasudin da ya sa Dadin nasa ya yi masa haka.
Take ya yanke shawarar magance matsalar. Tashin
farko tunaninsa ya tsaya a kan Zinatu yarinyar da yake
matukar so ko can baya ita ce zabinsa wadansu dalilai
ne yake ganin ba za iya auran ta, amma ko wadanne
dalilai ne sun kau da dai a hada shi da fitsararriyar
yarinyar nan.
Cike da kwarin gwiwa ya nufi gidansu, tare da tabbacin ba za ta watsa mishi kasa a idoba sakamakon
dimbin son da take masa, kamar dai ko yaushe sanye
take cikin shigar kananun kaya blue din jeans hade da
farar Bodyhug.
Wani murmushi ta sakar mishi lokacin da suka
yi arba da juna, hannunta ya riko ya janyo ta jikinsa
suka shiga salon gaisuwar da suka saba, tsawon lokaci
kafin su dai-daita hannunta na rike danasa ya dube ta
Zeenat! Ta dube shi ya a ka yi Abdulwaheed?
Ya lumshe ido yana jin dadin yadda take
ambata sunansa yana wasa da yatsun- hannunta ya ce. Zeenat idan dai zan sami hadin kanki ina so a cikins
atin nan iyayena za su zo da maganar aurenmu.
Lumshe ido ta yi, wani ni'imtaccen sanyi ya ratsa zuciyarta, abin da take mafarki ke shirin tabbata? Cike
da damuwa ya dago ta kin daina ra'ayina ko Zeenatu?
Murmushin nan nata ta sakar mishi ko daya Abdul
tsabar farin ciki, ne ya cika min zuciya, ina son ka
85
Abdul, kada ka bari na yi missing dinka Abdul. Ya
fuskance ta, ni naki ne Zeenat kar ki sa wani shakku a
zuciyarki, kadarta gaki can dauke da babin Abdul a
gidansa. Lumshe idon ta kara yi Allah ya nuna min
wannan rana Abdul.
General din yana birnin tarayya Abuja, haka
momin nashi a satin nan ta dage zuwa Kasar Emarat
(Dubai), kai tsaye Abujan ya shige. Bai sami damar
ganawa da baban nashi ba sai da dare, ya dube shi in
ce ko lafiya Abdul? lafiya kalau Dady har ma na zo
maka da wani batu ne, sai dai ina shakkun gaya maka.
Cikin dadin rai ya ce, haba Abdul ni fa mahaifinka ne
kar ka ji shakkun komai a kaina ko menene in dai bai
fi karfina ba zan maka shi.
Cike da kwarin gwiwa ya shiga fadin, Dady ba
wani abu ba ne da ya wuce maganar nan da kai min
kwanaki. Uhm. Ina jin ka. Ya fada cikin sakin fuska.
Ya ci gaba Dadyi na riga na gama gano lefina kuskure
ne kam na yi shi na sani ka fita hakkina har ma ka ba
ni damar fitar da yarinyar da nake ganin zan aura, to
Allah be nufae ni ba tun a lokacin, a halin yanzu kam
mun gama daidaitawa da yariniyar har ma na gayamata
magabatana na iya zuwa ko yaushe daga wannan
lokacin.
Fuskarshi a daure ya ce ban'fahimce ka ba fa?
kana nufin mata biyu za ka hada ka aura a lokaci
guda? To in haka ne ko ka yi kuskure?
86
Ya yi saurin tarar numfashinsa, ba haka ba ne Dady ina nufin ita maganar waccen yarinyar a janye ta baki daya don gaskiya ba na son ta kuma..... Ji kake tasssssssss! Ya sharara mishi mari kə kafin ya amayar da abin da ya yi niyyar fadi cikin matsanancin bacin rai ya ce, ni din nan da ka gani ban haifi dan da ya isa na ce eh ayi ce a'a ba ko ka so ko ka ki auren nan babu fashi, kada ka kuskura ka kara
zuwar min eda maganar banza, mutumin banza tashi ka ba ni waje. To fa ran ‘yan mazan jiya ya baci, fada yake ba jiba gani.
Ranshi a 6ace ya dubi Abokinshi ka san Allah yarinyar nan sai ta dandana kudarta muddun ta sake ta shigo hannuna, aure dai? An kafe an nace ko? To duk mai hannu cikin wannan hadin hakika zai yi nadamar hadin har ma ya yi kuka da idanunshi.
Katse shi ya yi yana me jan tsaki kai ko wallahi ina rasa tunaninka wani zubin, har ka dinga fadar maganar da ba ta dace ga iyayenmu ba, shi aic ba lamari ne na Ubangiji ba, idan Allah ya kadarto aure tsakaninku da yarinyar nan ba ka isa ka kauce ba kamar yadda idan be kadarto ba babu wanda ya isa tilasta ka ka aure ta.
Oho iai ko ma meye yarinyar za ta dandana kudarta muddun ta sake ta shigo hannuna, a na me za a
sani yin abin da ba na so? kanka dai ake ji babu kuma yadda za ka yi idan har Allah ya kadarto aurenku.
87
a
Cikin kanknain lokaci magana ta kankama, an
kai kudin aure an kuma tsai da ranar aure watanni
hudu masu zuwa, to fa kamar an yafa mishi wuta haka
yake jin kansa, dan menene za a dage sai an kakaba
mishi yarinyar da ba ya so?
Aunty Na'ima na falon a rakube Hajiya, ni
kuma na gefen Ambassador ko da yake kiran Na'iman
ya sa a kai mishi da ba ta da ko hurumin zama a wajen,
Hajiyan dai ta hakimce kamar ko yaushe.
Ta shigo domin amsa kiran mahaifinta, kujera ta
samu ta zauna ta yi darere abinta, Dady an ce kana kira
na. Ya gyara zamansa haka ne ummina, ina so ki nutsu
ki kuma fhaicme ni bana so ki daga hankalinki ko
kuma ki kasance cikin damuwa, ummina ina ganin
cewa na isa da ke domin ke diyata ce da nake da iko da
ita a takaice. Na hanga na hango babu wani alheri a
tsakaninki da wannan yaro (Tahir) ba tun yau ba na
sha fada miki, a matsayina na mahaifinki na zaba miki
abokin rayuwar da nake ganin zai iya rike min ke bisa
amana har ma an kammala komai lokaci kaďai ya rage.
Me ka ce Dady? Ta fada cikin kidima. Ya ba ta
amsa abin dai da kunnuwan ummina ya jiye mata shi
ne ina fatan kuma ba za ki badan kasa a ido ba, domin
na yadda da tarbiyyar yaron, Abdulwaheed yaro ne me
hankali danutsuwa tun yana kankanin sa.
Kuka ta saka bayan da ta dada fahimtar inda ya
dosa, na shiga uku, wallahi bana son shi Dady sam
88
sam bana kaunar shi, wallahi bazan iya aurenshi ba. Ina! Wallahi a'a.
A'a ummina kar mu yi haka da ke ba na son
abin da zai sa in 6ata miki. Cikin kukan dai ta се, Allah Dady ba zan aure shi ba ko za a kashe ni ne, don
me za a hana ni zabina a hada ni da wannan dan iskan
mutumin..... Aunty Na'ima ta yi zugum tana ganin tsabar rashin TARBIYYA, ka yi magana a ga lefinka
kokafin su ankara tuni ya sakar mata mari cikin
matsanancin 6acin rai ya kara kawo mata wani marin,
Aunty Na'ima ce ta yi saurin rike shi, a'a Alhaji idan
rai ya baci hankali ke nemo shi, ya shiga bambami, kyale ni Na'ima in zane ja'irar yarinyar nan mara kunya kawai har ni za ki dubi tsabar idona ki gaya
mini wannan maganar, to bari ki ji aure ne ba fashi, in
ma da wanda yake daure miki gindi ne ya yi a banza. Ya sa kai ya fice cikin fusata.
Aunty Na'iman na faman lallashin ta yayin da
take dada tutturjewa gami da maganganu marasa da'a, ita ko Hajiya Kaltum ranta in ya yi dubu ya baci, dan
menene Alhajin zai fadamata wannan kalmar a gaban
babbar makiyyarta, alhalin ba ta da lefi ko kankani. Ba
wai kalmar da ya fada ba ne ya fi kona mata rai a'a
fadin da ya yi ne a gaban makiyyarta shi ya fi komai
bata ranta, cikin daure fuskarka ta ce, ai sai ki tashi ki
ba mu waje ko?" buri ya cika sai a zuba ruwa a sha a
kasa dan farin ciki. Dago kai ta yi ta kalli Hajiyar sai
89
kuma ta kada kai ta fice cikin sanyin jiki. Ga Heddaya
kuka kam ta yi shi har ba adadi, tana ji tana gani Tahir
na kiran ta a waya amma ta gaza dauka, to me za ta се
mishi? Bayan ana shirin raba tsakaninsu.
Misalin karfe goma sha daya na dare ta kira shi
a waya kuka take tana bayyana mishi abin da ke
gudana, gaba daya shima hankalinshi ya tashi har ta yi
nadamar bayyana mishi. Sun yanke shawarar za su
hadu a dandalin mutanen Kasar Labanon "Labanon
Club" da sanyin safiyar gobe ko kadan ta kasa
runtsawa sakamakon kalubalen da ke gabanta, babbar
damuwarta be wuce mutum da ake shirin kakaba mata
mutumin da ya yi mata illar da ba za ta taba mancewa
da ita ba. Ya cuce ta ya gama da rayuwarta, komai
rintsi komai wuya ba za ta taba aurenshi ba, ko da za a
saka ta a turmi a kirba Tahir dinta kadai take so shi
kadai ne ya cancanci zama abokin rayuwarta.
Wai me ya sa ne dadinta kai har ma mominta ba
sa kaunar aurenta da abin kaunar ta? Menene dalili?
To bari dai mu ji meye dalilin?
Shi dai Tahir da ne gurin Dr. El-Hussain
babban gwamnan babban bankin kasa. Kwararren dan
boko ne ya rike manyań mukamai daban-daban har
zuwa yanzu da yake rike da wannan mukami. Sun yi
aure da matarshi Miss Diana mutuniyar kasar Afrika ta
Kudu (South Africa), ko da yake daga baya ta
musulunta har ma ana kiran ta da Dr. Maryam El90
Hussain, Allah ya hada aurensu ne a lokacin da yake aiki a can kasar Africa ta kudu har zuwa lokacin da ta
musulunta suka dawo gida Najeriya.
Sun haifi yaransu guda uku, Nasir, Nabil da kuma Tahir, dukkaninsu sun kwase kyawun mahaifiyarsu domin ko ita din ruwa biyu ce, mahaifinta bakar fata ne na Africa ta kudu,
mahaifiyarta kuwa ta fito nedaga jinsin fararen fatar kasar, domin usulunsu turawan kasar Sukotilan
(Scotland) ne shekaru aru-aru tun iyaye da kakanni
suka dawo kasar tun kafin fara wariyar launin fata.
Dr. El-Hussain cikakken bafulata ni ne don
haka yaransu suka gado kyau ta uwa da uba sai dai
abin kaico yaran sun tashi cikin TARBIYYA marar
kyau. Dabi'unsu, halayyarsu duk dai ababen kyamata
ne, duk da kasancewar mahaifinsu mutum na kwarai
mai halin dattako amma rashin katari da uwa ta gari
shi ya sa yaran suka tashi a sangarce, domin
musuluncin na mahaifiyarsu ga shi nan ga shi nan ne, domin sam ba ta riko da abin da addinin musulunci ya
zo da shi sai fa abin da ba a rasa ba.
Shi kuma sakaci da baiwa sana'arsa (aiki) fifiko
da uwa uba tsananin son da yake wa yaran wanda ma
iya cewa ya wuce iyaka, ya makantar da shi ga ba su
tarbiyya ingantacciya, gata na duniya kam tun daga
kan ilimi (amma fa na zamani) da sauran kyalc-kyalen
91
duniya an gwadawa yaran amma kuma duk ya tashi a
banza saboda rashin samun ingantacciyar tarbiyya.
Dalili ko shi babban danshi wato Nasir ya
kasance shedani bayan neman matan banza da shaycshayen miyagun kwayoyi har ma da Damfara (419)
duk dai ta'adunsa ne, manya da kananun kasashen
duniyar nan babu inida ba sa zagawa haka nan a cikin
kasar nan har daurin ginidi suke da shi, duk da cewa
babu abin da ya rasa daga gurin mahaifinsa, amma
yajefa kansa cikin wannan sana'ar. Ka kam fuskanci
mummunan bacin rai a lokacin da ka je wa da Dr. ElHussaiin wannan batu, wanda tsabar son da yake musu
ne ya makantar da shi ganin hakan.
Tashin hankalin ya faro ne lokacin da rikici ya
hado Nasir da abokin shashancinsa a kan yarinyarsa ko
kuma mu ce karuwar da suke hamayya a tsakaninsu,
abinka da sangartacce dan masu da shi me kuma
daurin gindi take ya sakar masa bullet (karamin
harsashi) ko shurawa be yi ba ya mace, to tun daga
lokacin ya gudu ya bar kasar babu ko wanda ya san
inda yake, dominshi kansa ya san ya tabowa kansa
jidali, gata da komai da daurin gindi yaron ya fishi,
shi ne da kwaya daya a gurin mahaifinshi, don haka ya
fahimci zai iya fuskantar duk hukuncin da bai
tsammani, shi ko me biye masa wato Nabil rikakken
mashayi ne da ba ka iya kwatanta kamarsa ga kuma
Garnar da yake wa mahaifinsu, account dinshi ne ko ko
92
a gida ne ba shi da damar ajiyar kudi zai bi ya zare,
domin shi sangartar shi ta fi ta kowa har ma ba ya iya
neman na kansa, sai dai a ajiye ya dauka, komai
yawansu kuma ya batar da su ga ababan shaye-shaye
domin shi matama sam basa yabansa, bala'insa dai
shaye-shayen, shaye-shayen ma na muggan kwayoyi,
wanda a karshe suka gusar mishi da hankali yarasa
tunaninshi baki daya, shi ke na rayuwa ta riga
tawaya.
ta
Shi ko Tahir shi a ke gani me dan dama-dama,
to amma a rashin sani, domin gwani ne a wajen
neman matan banza, caca da kuma shan ababen maye,
duk dai ta'adarsa ce barasa ko tamkar ruwan korawa
ya dauke ta.
Dadinta dai shi ya iya neman na kanshi kuma
yana da mutukar hangen nesa ba ya yadda ya yi abin
da zai iya cutar da shi wani sa'in haka nan kuma yana
mutukar son iyayenshi, don haka ne ma yake takunsa
sannu a hankali, ko da yake sun fahimci halayyarsa, to
amma ba su fahimce shi yadda yake na hakika ba, a
halin yanzu shi Tahir shi ke rike da kamfanin
.mahaifinsa na sarrafa kayan abinci, haka nan yana gudanar da harkokin kasuwanci don haka kudi tamkar
yayi suke a gurinsa, a dangane da dangantakar Tahir
da Abdulwaheed kuwa muna iya cewa abokanan juna
ne na kud da kud kasancewar halayyarsu ta zamo
daya (dama hausawa na cewa sai hali ya zo daya ake
93
school suke tare, Tahir, abota) tunsuna secondary
Abdulwaheed, Samir da kuma Faisal tun suna a
socondary din suka fara lalata 'ya'yan al'umma, har
zuwa lokacin da suka shiga jami'a sai likkafa ta cі
gaba, shi dai Samir ya fi kwarancewa ne wajen neman
mata, shi ko Waheed a fannin caca ya fi kaurin suna
duk da cewa neman matan ma a na tabawa, shi kuma
Faisal a fagen shaye-shaye ya yi musu zarra duk da
cewar shi ma din gwani ne a fagen neman matan yayin
da Oga kwata-kwatan (Tahir) ya yi musu zarra a
dukkanin wadannan ta'adu. A bayan shi din ma iya
cewa Abdulwaheed din ne ke rufa masa baya duk da
cewa shi ba ya shaye-shaye kai ko karan sigari ba ya
zuka.
Shi dai Tàhir ma iya kiranshi da mayen mata,
kamar yadda abokanansa suke ce inasa, domin dai ba
ya gajiya da mace, duk inda kyakkyawar mace take
yana wajen ya kuma san duk hanyar da zai bi ya
mallake ta komai jan ajinta, shi da kansa yana alfahari
da kyawun da Allah ya yi masa, wanda yake rudar
'yan mata da shi. Shi ko Waheed ga ta'adarsa sai dai a
gani a ce ana so, in ko har ya furta yana yi da ke lallai
ba karamin aji ne da ke ba.
Sabani ya shiga tsakaninsu ne bayan da Zeenatu
yarinyar da shi Tahir din yake inu.ar ji da ita kai a
duk cikin 'yan matansa ma ta cni tma domin yana
mutukar alfahari da n3. ta mallakı dak wani abu da
94
kyakkyawar mace za ta yi takama da shi. Dare daya Zcenatu ta kekashe idanunta ta nuna babu wanda take
so take kuma yi da shi irin babban na hannun daman masoyinta, to fa gaba me tsanani ta shiga a tsaknain Tahir da Waheed, domin shi Tahir mutum ne mai mutukar dagawa da dan banzan kishi, ba karamin
kasawa ba ne yarinya ta guje shi, ta kuma komawa abokinshi alhalin yana ganin komai da komai ya fi shi
tun daga kyawun sura har zuwa duk wani abu da yake takama da shi.
Ko da yake shi Waheed din be wani dauki abun
serious ba, domin ba wani son yarinyar yake can ba,
amma irin yadda shi Tahir din ya dinga nuna mishi ya tilastawa zuciyarshi son yarinyar har ma ta bi ta kankame zuciyarsa kazalika ita ma ta mallaka masa zuciya har ma da gangar jikin baki daya. A bangaren abokai ma sai ra'ayi ya banbanta shi dai Samir yana
goyon bayan dan uwanshi Waheed, ko dan kusancin
da ke tsakaninsu, shi ko Faisal ya fi karkata ga Tahir
don ganin shi a ka yiwa rashin kyautawar, sai dai
hakan bai 6ata dangantakar da ke tsakaninsu ba, illa dai dangantarkar ta raunana kowannensu ya kama gabansa, Tahir da faisal, Waheed kuma da Samir. Shi dai Tahir ba wai tsantsar son da yake wa
yarinyar neja haddasa haka ba, illa tsabar kishi da
dugawa da kuma jin shi ya fi kowa shi ya haddasa
mishi wannan tsantsaradawa gami da kiyayyar tsohon
95
abokin nashi, a karo na biyu sun kara haduwa a kan
mace guda, ko ya za ta karke musu? To bari dai mu
bar su sannu a hankali dan jin yadda za ta kaya. Sa'ad Idan muka koma bangaren Ambassador
kuwa, za mu ga cewa babban dalilinsa na kin auren
`yarsa da Tahir be wuce tsabar rashin tarbiyyar ahalin
gidan El-Hussain da kuma uwa uba matsalar da ta
danganci matarshi domin kowa ya riga ya san cewa ko
kadan ba ta riko da addinin Islama, duk da tana amsa
sunan musulmar, wato irin kalmar nan dai da malam
bahaushc ke cewa 'Musulmiya', wato mutumin da
yake amsa sunan musulunci amma kuma ba ya riko da
abin da musuluncin ya zo da shi, wasu tsirarun mutane
kuma suna rade-radin har yanzu tana riko da addininta
na Almasihu.
Shirye-shiryen aure na ci gaba da kankama
yayin da amaren ke ci gaba da bijirewa musamman ma
daga bangaren amarya, tsiya-kala-kala, ta yi kuka ta yi
tambotsanta duk dai a banza, aure ne babu fashi,
wannan abu namutukar kona zuciyarta, ganin yadda
Abban nata ya mursiyeya