Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 7
zuwa Empire Clinic da 46 ke plot 132 Badawa layout. A can asibitin sun sami taimakon gagagwa, duk da hakan hankalin Hajiyan be kwanta ba sai da ta ga numfashinta ya daidaita, sannan ne ta sami nutsuwar zuciyarta. Hankalinsu duk a tashe yake saboda rashin sanin abin da ke wakana, Ambassador ne yake kokarin lallashin Aunty Na'ima, yayin da Heedaya da 'yan uwanta suke cikin tsananin damuwa. Gefin magariba ta kira su a waya ta sheda musu asibitin da suke, ba fata lokaci suka tgarzaya zuwa asibitin na mata (Clinic) rungume take jikin Hajiyan tana ba ta tatacciyar madara (fresh milk) kanta ta yi da sauri my sister me ya sa za ki tafi ki bar mu?" tashi donAlalh. Ta janyo yarinyar jikinta yayin da fa'iza da Fa'iz da ma Fiddausi suke kokawar daukar ta. Ambassador ne ya raba gardamar bayan da ya dauke ta amma duk da haka Heedaya na nanike da shi, tana kaunar yarinyar tamkar yadda take kaunarsu fa'iza. Aunty Na'ima na gefe sai hawayen dadi take ruskar diyarta da ta yi a halin numfashi a hannu daya kuma tana kunshe da farin cikin kaunar da ake gwadawa diyarta, haka abin yake a idonta ne ko a bayan idonta daya daga cikin abin da ke burge ta daga halayayr Hajiyan ke nan da 'ya'yanta, don haka ne ma take hakuri take kuma kyakkyawan fata ga Hajiyan, a duk irin cusgunawar da take mata. Tsaki ta ja bayan da ta buda kwanukan abincinta (food flaks) don mai ya sa ne Ladi mai aikinsu) za ta yi musu sakwara bayan ta san ba cimar ta ba ne duk wani abu da aka sarrafa shi da doya. Ta nufi sashen maşu aikin nasu dan bin bahasin hakan, amma ba ta tarar da ita ba domin tana bandaki, za mu gamu ne ta fada a zuciyarta, kai tsaye 47 key din motarta ta dauka ta nufi Bercast Daylight domin yin take away, ko dayake a duk dare ko kuma yamnaci takan ziyarci shagon na kayan kwalam. Hakan ce ma ta sa har suka yi sbo da ma'aikatan wajen. Misalin karfe tara da 'yan mintina na dare ta baro wajen, da yake lokacin damina ne garin ya yi shiru fetal tamkar babu jama'a, sai ko jefi-jefi masu shigewa a motocin gida. Sautin kaset din Mariah Carey cikin wakarta ta Have U Ever. Ke tashi a cikin motar, tana gyada kai gami da dan karkada sitiyarini motar da yatsun hannunta tabbatar sautin kidan na ratsa ta. Kamar a mafarki wata mota da ba za ta iya kiyaye kowace iri ba ce ta dumfaro ta gadan-gadan a dai-dai titin Maganda da ke Nassarawa G.R.A. Ko kafin ta ankara ta yi mata over taking gaba daya ta rude ta diririce har dai Allah ya taimaka ta taka birki ji kake kuuuuuu! cikin wani irin matsanancin sauri wani mutum sanye da bakaken kaya kai komai nashi a rufe yake ba ka ko iya ganin fuskarsa in ka cire shafin hannunsa da kuma kwayar idanunsa. Gilashin motar ya tarwatsa sannan ya bude murfin motar hannu ya sa ya fusgo ta ta shiga tutturjewa tare da neman agaji fadi ta ke barawo, Sarawo jama'a ku taimake ni amma shiru kake ji babu ko alamun motsin mutum.mari ya sakar mata wanda ya yi barazanar makantar da idanunta kai gaba daya ma dai sai ta nemı hankalinta ta rasa, ta ji dai an shigar da ita wata motar an kuina tashe ta kuka take tana ihu da kururuwa k oa jikinsa, domin babu wani alamun tsoro ko firgici a tare da shi, be wani damu da kururuwar da take yi ba tun da babu mai iya jin ta, gudu yake shararawa kamar me shirin barin doron Kasar. 48 Tsawon lokaci suna tafiya ba da jimawa ba kuma sai ta ji an tsaya an yi parking, finciko tan ya kara yi ta shiga kokarin turjewa, sabo ta ya yi a kafada tamkar karamar yarinya. Shfi ke nan tata ta kare cikin biyu daya, ko dai ta afka hannun yan fashi da makami kamar yadda hasashenta na farko ya ba ta, to amma a halin yanzu ta fi gasgata hannun masu yankan kawunan mutane ne, shi kenan ita da Momy da Dady sai dai a lahira. Ji ta yi ta hadu da garu ta kume, take bakinta ya fashe sai jini, jikinta na rawa hannunta na makyarkyata lokacin da 6arawon kawunan mutanen ya yi cilli da ita ya kuma shiga kokarin cire hular da ya saka a fuskarsa wacec ta kasa bayyana surarsa. Ja ta dinga yi da baya-baya cikin matsanancin tsoro lokacin da ta fahimci ko wanene, kallonta ya yi sama da kasa yana mai murmushin mugunta gami da ciza.lebe ko ina a jikinta rawa yake kamar an jona wutar lantar a jikinta (shocking) da fadawarta hannun wannan mugun mutumin hakika gwanda fadawarta hannun hasashenta na baya. Ta tsane shi ta tsani ko ganinshi kamar yadda ta hakikance haka gare shi, hakika wannan kam zai iya yi mata illar da danfashi ko dan yankan kai be ma taba, domin shi dan fashi zai raba ta da dukiyarka ne kawai, shii ko fan yankan kai sai dai ya raba ta da rayuwarka dingurungum, wannan kam ya rage tsakaninshi da mahaliccinsa ne. Cikin rawar murya ta shiga fadin, ka cece ni ka taimaki rayuwata ka sada ni daiyayena ko nawa kake nema za su baka, kome kake bukata a gare su za su yi maka. Hannayenshi ya saka ya harde a kirjinsa, fuskarshi dauke 49 da murmushin mugunta tun da shi daman ba ma'abocin dariyar bane. Ya nuno ta da yatsa, ke har kina ganin kuna da wani abin da za ku iya ba ni da ba ni da shi to in haka ne ya kada kai maza-ımaza canja tunaninki. Ka taimaka min don Allah ko me kake so Dady zai baka ko shi menene.... yauwa-yauwa ya yi saurin datse ta, ashe ma ta kwana gidan sauki ya nuno ta da yatsa only you. Ya karkada hananyensa nakc so ya ci gaba, amma fa a cikin daren nan kawai daga hakan ya shiga kada kai ko hanya ba na fatan in hadu da shi, you understand? Ja ta dinga yi da baya da baya yayin da shi kuma ya ja ya tsaya kyam banu alamun tsoro bare tausayi a tare da shi, magiya takc tana rokonshi tsawa ya daka mata, ke mara kunyar Karya, rufe baki ba na son jin wani abu daga gare ki, zuciya ta dada kawo shi wuya, lokacin da ya tunano.kaskanci da tijarar da yarinyar ta gwada mishi a gaban kuma mutumin da suke mutukar adawa da junansu wannan ta fi komai bakanta zuciyarshi. Ya ci gaba ke kin yi zaton abin da kika yi min kin sha ne? ya kada kai a'a, to ba haka ba ne, ni din nan da kika gani na isa ja da kowace 'yar iskar yarinya konai tsagerancinta. A yau kam zan koya miki darasin da za ki koyar da mata masu kokarin wuce gona da iri ga guyses. Kayanshi ya shiga kokarin cirewa wallahi a yau saí na dasa miki abin da har ki mutu ba zai taba barin zuciyarki ta huta ba. Ta fahimci manufarsa don haka ta dada rudewa ta ma birkice gaba daya kawai neman mafita take, amma babu ko ina ta taba garam babu ko alamar motsi, ihu kuma ta shiga tare da neman agajin jama'a. Amına ko haushin kare ba ta jivo ba. illa ma wata tsawa da aka daka, sakamakon hadarin da yake ta hadowa 50 To fa duk fa ba haka nan ba ne a gurin Haj. Kaltum fada take mai kama da habaici, haba Alhaji ka bar damawa kanka lissafi ga abu nan a bayyane. Eh, mana kana tare da makiyinka da yake kokarin ganin bayanka ba dole ko meye ya aikata ba, tun da kwadayin zinar duniya ce dai ta kawo shi, zai iya yi maka komai don dai ya cimam burinsa. Muryarta ta daďa kaurara, ni kam Alhaji dole ne ma ka dau mataki ina ji ina gani ba zan dinga zama da makiyina ba alhalin na sani sarai ba kaunata yake ba. Cije lebe ya yi gami da takaicin halayyar Hajiyan a wasu lokutan, shi ko engineer faruk damai dakinsa Momy Maryam ban baki suke bawa Hajiyan amma tamkar ma kara zuga ta suke yi. Kada kai ta yi bayan da hawaye ke zubo mata sai kawai ta nufi 6angarenta, saboda Allah wannan daukan hakki har ina? Matar da tun daren jiyan da abin ya gudana ba ta iya ko rintsawa ba ta kasance cikin nafilfilu tare da shedawa sarki Allah ya kubuto da yarinyar a duk inda take amma kuma tashin farko sakamakon da Hajiyan za ta yi mata ke nan? Wai wane irin riko ne Hajiyan take mata? Duk wani kokari da za a yi na gano wanda ya tafka wannan ta'asar abin ya ci tura, amma duk da hakan be janye casc ba ana nan ana ci gaba da bincike. A lokacin da abin ya faru Tahir ba ya kasar ya je can kasar Canada wajen hada-hadar kasuwancinsu. Hankalinshi a tashe ya iso gidan, ya dade yana zaman jiranta kafin ta fito kamar ko yaushe zaune yake a cikin, motarsa, ta dan leko da kanta jikin tagar motar, Tahir shigo daga ciki mana. Kai ya girgiza mata, shigo ban jin zan iya fitowa, menene ya far ne? Wa yake kokarin sace min ke? 55 Wane mai kokarin dauko wa kansa tarar gawuna ne haka? Lokaci daya ya jero mata tambayoyin. Sai bayan da ta zauna sannan ta fara ba shi amsa, kwantar da hankalinka Tahir, ko ma menene ya riga ya shige. Ya dube ta da kyau ranshi a 6ace ina fa ya shige, kin san Allah kowane dan iskan ne zan gwada mishi kuskuranshi, mu za a yi wa wannan iskancin? bayyana min wanene? Wadanne mutane ne? Allah zan iya salwantar da rayuwar mutum a kanki Heedaya. Ta tsorata daga sambatun da yake, kai kamar ma ba Tahir din nata ba: ta godewa Allah da ya sa tun da farko ba ta bayyana gaskiyar lamarin ba, tabbas babu abin da zai hana shi daukar mummunan mataki a kansa musaınıman da yake ta lura akwai tsunammiya a tsakaninsu. Idan ko har ya aiwatar da wani abu a kanshi zai kara bakin jini ne kawai a gurin dadinta, ko a yanzun ma ya aka cika, da kyar dai ta iya shawo kansa bayan da ta nuna mishi komai ya shige tun da an kama wadanda suka yi abin. Ni dai kam ki amince min na turo magabatana gurin Dady tun da mun fara fuskantar wannan barazanar kin ga sai mu dage mu bar musu kasar ma baki dayanta. Mu dai kara hakuri takir, ka san komai lokaci ne idan lokacin ya zo sai ka ga kamar ba a yi hakaba har ma wata rana ya zama labari da haka dai ta kwantar da hankalinshi har ma ya ci gaba da bayyana mata tsagwaron kaunar da yake mata. Suna tsaka da hira Ambassador ya dawo dirarsa ke nan daga Kasar Thailand ta isa gare shi bayan da ta rikojakar hannunshi, hannunta ya riko yana fadin unmina 56 na same ku lafiya? Fuskarsa ta dan sauya lokacin da ya yi ido biyu da yaron. Karasowa ya yi ya giashe shi gami da yi mishi barka da zuwa. Me za a yi da irin wadannan yara marasa tarbiyya? Jibi inda yake gaishe ni a tsaye kikam tamkar da sa'an ubanshi yake Ambassador ya ayyana hakan. A nashi 6angaren (Tahir) yana ganin ya yi iya kokarinshi wajen mutunta surukinsa, kila da wani ne sai dai ya mika mishi hannu su gaisa. A nan ya barsu ya shige ciki abinsa. Heedaya don Allah me ya sa ne Dad bai yi min irin murmushin da yake miki?" a duk lokacin da muka hdu sai na ga kamar yana daure fuska. Kai haba, kai ma ka ji ka kana dai wani zance ne, bayan a duniya babu mutumin da Dad yake mutukar gani da daraja irin mutumin da ya kaunaci Heedayansa. Kai ya kada tare da tunanin samo hanyar da zai bi don dai ya karbu a wajen surukin nasa. Da shigarta gida ya fara fada. Ranshi a bace ya dube ta kina so ne mu sa kafar wando daya da ke ko ummina? Ni daddy? Ta tambaye shi. Kwarai kuwa, tund a kin kasa fita harkar yaron nan, na gaya miki ba daya ba biyu ba lamarinku da yaron nan ba zai yiwu ba, ba ta yanda za a yi idona ya rufe na hada tsakaninku sam-sam hakan ba zai yiwu ba. Kuka ta saka, wayyo Dady wannan kawai za ka yi min na san kana kaunata Dady, da zan iya hakura da Tahir da tuntuni na hakura, ka yi hakuri Dady kaso shi don Allah. Dafe kai ya yi gami da dogon tunanin damuwar da za ta shiga a lokacin da ta tabbatar da abin da yake fada mata babu sauyi a cikinsa, a duniya babu abinda yake gudu irin bacin ran diyarsa 'yar lele Heedaya amma kuma ga wani sanadi da zai sa ya jagula ranta domin komai kafewarta dole ne na ta hakura da wannan yaron. 57 A cikin daren ranar ta kasa ko runtsa idanunta sakamakon karan tsaye da Dad dinta ke shirin yi a rayuwarta, tana son Dad dinta tana son duk wani abu da zai saka shi farin ciki, to amma fa a wannan karon sun raba hanya, hanya kuwa me tsayi tana son Tahir ta na yi mishi wani irin so son da babu wani mahalukin da take wa irin sa. Yayin da shi kuma Ambassador ya kudurcewa zuciyarshi ko maza sun kare ba zai taba iya aura mata zabin nata ba. ba don komai ba sai don kiyayewar mutuncinsa da ma na diyar tasa. Zaune yake bisa kujerar hutu (resting chair) ya yi dai-dai akanta yayin da sassanyar iskar na'urar sanyaya dakin take kadawa gwanin ban sha'awa, hannunshi rike da farin kofin gilashi tare da sassanyar ruwa a cikinsa dayan kuma rike yake da jaridar This Day me dauke da labarin yunkurin sace diyar Ambassador Sa'ad Mohd da kuma makudan kudin da aka ware ga duk mutumin da ya bayyana mutanen da suka yi yunkurin sace tan a kwanakin baya. Murmushi ya saki bayan da ya tabbatar da ta ji kashedinsa, ai kuwa ta samawa kanta lafiya ta ma sakaya kanta, tun da babu wanda ya isa ja da su a kasar nan ko shi wanene? Gobe ma kya kara kya kuma san ba duka maza ne suke wawayen da suke daukar raini, rainin ma irin na mace ba. Tun da abin nan ya faru ta kasance cikin rashin kuzari da damuwa, sakamakon yankan kaunar damutumin ya yi mata, har yau har kwanan gobe babu wanda ta 58 bayyanawa babu kuma wanda take fatan bayyanawa muddun rayuwarta, babbar damuwarta ranar da Tahir dinta zai fuskance ya riske ta a haka shin me za ta ce masa? M zai dauke ta? hakika mutumin nan ya gama kwara. rayuwarta, hakika ya yi gaskiya da ya ce zai dasa maia abin da ba zai taba barin zuciyarta ta huta ba, ashe ko haka ne, a kullu yaumin da wannan abu take kwana da shi kuma take tashi kamar yadda zafafan kalaman da ya yarfa mata ita da mahaifanta ya kasa barin zuciyarta ta huta, "Ke ko mahaifin naki ba ku da abin da za ku ba ni, me kuke da shi? Ku su wanene? Talakawa 'yan kauye, ko waye uban naki ki gaya masa ba shi da abin da zai iya bawa dan General Abdullah Usman." Wadannan kalamai sun tsaya mata a makoshinta. Waheed na tsane ka! na tsane ka!! tsana marar iyaka. Ta kasankce cikin damuwa har ma ta kai Tahir din ya fuskanta, a kowane lokaci cikin tuhumarta yake ta kan ce a zuciyarta har abada ba za ka taba jin wannan sirrin nawa ba Tahir, domin ban san da wata sigar za ka dauki lamarin ba, ina gudun tashin hankalin da zai biyo baya ina kuma gudun kar ka yi zuciya ka guje ni, da na rasa ka kam gwamma ba ni a duniyar. Ya kasance dai cikin lallashinta gami da nuna kaunar sa gare ta abin da kan tausasar da zuciyarta, sai dai duk da hakan abin ya ki barin zuciyarta, tare da tsagwaron tsanar mutumin da ke karuwa bayan dakika guda a zuciyarta. Misalin karfe hudu na yammaci suka yi da sameera za su je bikin nabila Ishak wata kawarsu da suka yi karatu tare tun daga secondary har zuwa 59 university a dai-dai lokacin ne Tahir din ya zo ta yi mishi rakiya gurin friend dinshi mutum kasar China da suke business tare. Sanye take cikin English Wears masu mutukar tsada launin madara takalmi kamar ko yaushe hill ne haka nan jakar da ke hannunta me kyawu kirar Kasar Italiya. Mayafin da ta dan yane kanta da shi wanda shi da babu kusan daya ne launin madara ne (milk colour), a wuyanta ma tsadaddun fashion earing ne na farin dutse masu mutukar tsada samfurin Atthood, ta bi ialhirin jikinta ta feshe da Hugo Women. Ta iske shi a mota shi ma din ya yi mutukar hadewa cikin suit bakake wuluk masu matukar tsada ya yi kyawu ainun. Bude murfin motar ta yi ta shiga ya dube ta ya kuma duban ta sannan ya tuka motar ya fice daga harabar gidan nasu. Duban nan ya ishe ni kar ka kifar da mu. Murmushi ya saka, shi ma din dai bai iya cika dariyar ba, ya shafa kai kin san wani abu? A'a sai ka fada. Wallahi da gangan wasu mutanen suke fifita kyawun fararen fata ko mai haskensu a kan jinsin bakaken fata, kin gan ki din nan wallahi sai an tara dubban mata masu haske kafin a sami guda daya kacal da za ta iya gogayya da ke. Hararar shi ta yi ya ishe ka ban da cin fuska, ni din nan ina na ga wani kyawu? Ai sai dai in babu fararebn mata a duniyar? Burki ya ja ya tsaya ta dube shi cike da mamaki, kai ya girgiza mata gami da 60 tabbatar da abind a zai fito daga bakinshi hakikatan gaskiya ne. Heedayah! Kamar yadda yake ambata sunanta. Kin san Allah daya ne ko shi mai jar fatar idan ya dube ki zai yi fatan shi ne da wannan baiwa da Allah ya yi miki. Ya shiga suffanta kamanninta.... a dai-dai lokacin da ya zo kan bakinta sai kawai gani ta yi ya shammace ta yana kokarin janyo ta jikinsa, jikinta ne ya saki har ma ta kasa katabus, ta tsinci kanta a wata duniya. Wani tunani ne ya zo mata da sauri ta ture shi ba na so, ba na so Tahir ba na son irin haka. Lumshe ido ya yi Heedayah ina son ki ina kaunarki, me zan yi ne da zai sa Dady ya amince min aurenki? A irin hakan zai amince yaba ka diyarsa? Ta fada gami da hararar shi, jingina ya yi da jikin kujerar ya kwanta lamo bayan daya lumshe ido, ina son ki Heedayah, ya zan yi da kaunarki tun da kin ki ki fahimce ni? ta dauke kanta daga dubanshi bayan da yake kokarin narkar mata da zuciya ta sani a yawancin lokuta idanunta yakan rufe har ma ta kasa bijirewa umarninsa sam ba ta son irin haka na shiga tsakaninsu, idan a ka yi hakuri lokaci kankani za ta zama mallakinsa. Sun isa gidan Mr. Lee inda ya karbe su da karamci ya kuma yaba da zabin abokinshi a karshe ya ce idan dai ya tashi aure zai zo ya zabo mishi launin masoyiyarsa, be sani ba a cikin jinsin bakaken fata akwai kyawawa haka? Ya yi mata alheri mai yawa na 61 makudan dollors. Kai tsaye Royal garden suka wuce ita ke tuka motar yayin da shi kuma ke gefenta. Zaune suke a harabar wajen ya dube ta irin duban nan nashi na kurilla, ta dan kifta idonta da hannunta ka matsa min da kallon nan wai meye ne? ina son ki Heedayah, ina son ki Heedaya kullum-kullum. Bayan ni din na fi kaunarka? Karya kike, Allah kuwa da gaske nake to bari in gani inda gasken ne. da sauri ta kufce bayan da ta fahimci manufarsa dariya ya saka ita ma dariyar take. Wayarta ce ta shiga ruri ko da ta duba sai ta rike baki sannan kuma ta daga, kamar zatonta fadan ta hauta da shi, wai meye ne haka Heedaya za ki wani shanya ni ina zaman jiran ki, na neme ki a layi kin ki ki daga dan dai kawai wulakanci irin naki. Ta katse ta to ya isa haka kar a cika ni da bakar magana, mun danfita ne da Tahir kin san ko uzurinshi ya fice na kowa, idan kin so kina iya samuna a Royal garden Opposite Nassarawa Hospital. Ta dube shi bayan da ta mayar da wayar, yau fa na fa shiga uku da mita, shaf na mance da batun bikin Nabila. ya kashe mata idanu ko ma bikin waye uzurina ai ya fice na kowa ko? Ita ma duban nashi ta yi, "Tahir." Ta furta hakan sai kuma ta kada kai ina Raunarka, ina maka sonda baki ba zai iya fadarsa ba, kai ne dai ka kasa gane hakan. Ya ji dadin kalamanta lumshe ido ya yi gami da sauraronta ta ei gaba, a ranar da na wayi gari a 62 dakinka za ka gasgata hakan, zan gwada maka tsantsar so irin wanda ba ka taba mafarkinsa ba, don haka ne ma nake jin cewa zan iya ja da kowa zan iya ja da kowane ne in dai a kan son ka ne Tahir." Kamar daga sama ta jiyo tafi a saitin kunnuwanta, dukkaninsu ba su ankara da zuwan ta ba. ta fara fadin ya kamata Dady ya yi wani abu a kan lamarin nan kada yabari diyarshi ta zautu da son Tahir din nan, wannan so haka kullum kalmar ke nan Tahir! Tahir! Tahir shi ake so. Lumshe ido ya yi gami da harde hannayenshi a kirjinshi ya son ranki? Tun dake har yanzu ruwan idankunki ya hana ki fitar da gwaninki don haka sai a kyale Heedaya da Tahir dinta su soye abinsu. Abin ma har da gori ta yi kwafa, dukanku za ku raina kanku ranar da kuka ga gwarzon nawa hadadden gaye. Duk haduwarshi be ko kama kafar Tahir dina ba. ta ba ta amsa, wane shi wannan kucakin naki? Mu dai rufe wannan babin tun da na fahimta kin yi nisa a cikinsa idan kin shirya kin kuma yi ra'ayi sai ki taso mu tafi. Ta dube shi da son ya yarje mata, dauke kai yayi alamar ba ya son hakan, ta dai daure zan wuce Tahir. Ya dada faure fuska yawon biki ya fiye miki zama da ni? da sauri ta dube shi haba Tahir me ya sa zaka ce lianа? Tun zuwan ka fa na gaya maka maganar bikin nan, nabila ce fa ka ko san yadda muke da ita? 63 Tashi ki je kar ki gaya min bakar magana, nabila ta fi Tahir shi ke nan kawai, tashi je ki. Jikinta a sanyaye ta koma ta zauna, na hakura je ki kawai samecra. Baki ta bude cike da mamaki, sha'anin naki azimun ne ya girmama kina ko tare da wahala in dai a kan da namiji ne, batun yau ba ta fahimci haka ba ta iya ketare maganarsa, kamar yadda ba ta taba iya kaucewa abin da yake so, ta sani Tahir yana son ta babu wani makusa a tare da shi daga irin tsabar son da yake gwadamata to amma fa gaskiyar magana son da take mishi take kuma bayyana mishi ya dari nashi tunanin Samira. Ki je fa na ce babu abin da za ki ce min, kawa ta fi Tahir a gu rinki. Sunkuyar da kai ta yi bayan da hawaye ke zubo mata me ya sa za ka yi min haka Tahir? Na lura da kyau a wasu lokutan tamkar ba ka son farin cikina.yanuna damuwarshi a fili haba Heedaya kada ki ce haka sam-sam ba hakaba ne, kin san dai ina son ki ina kaunarki don haka nake kishin duk wani abu da zai yi tarayya da ni. Yanayin yadda kikai lafazinki sai nake ganin kamar kin fifita kawarki a kan ni masoyinki da nake fatan shimfida rayuwa da ke (aure) ki yi hakuri kin sanni ba sai na bayyana miki ba ina da kishi musamman a kanki. Ya shiga lallashinta ta ce shi ke nan ya shige amma dai ba zani ba sai ko wani jikon. 64 Tahir ina son ka ba na son duk wani abu da za zamanto zai saba maka ballantana ni na saba maka. Tashi mu je in raka ki mota kada wannan mai manyan idanun ta cinye ni. Hararar shi ta yi na cinye ka ko ka cinyic ni? ina jin nan gaba ni kaina sai an tuhume ni, wannan kishi haka? Kishin ma har da kawa? Bugu ya kawo mata, ta yi saurin kaucewa, kai fa mugu ne Tahir sako ta ya yi a motar ya leko da kanshi jikin tagar motar, to uwar kankanba ki kula ki kuma kiyaye kada ki yar min da amarya. Su amarya manya, ta fada gami da yi mishi gwalo bayan da ta ja motar. In gaya miki wani abu mana Heedaya? Ta dube ta sai kuma ta dauke kai domin ta sank duk abinda zai fito daga bakinta bai wuce mitar bata lokacin da ta yi musu ba, daman ita gwanar mita ce. Ta ci gaba, Heedaya! Kin san dai ni 'yar uwarki ce ko?" domin na wuce matsayin kawa ko abokiya, tun muna kankana muke tare don haka ba zan ga wańi abu da zai cutar da ke ba na kau da kai. Ki gane wani abu daya, shi namiji ba a yi mishi haka komai irin kaunar da kake mishi na lura da kyau-zahirin abin da ke zuciyarki kike bayyana mishi, ita ko mace kara da alkunya aka santa. Abin nufi na ga kamar kina zakewa da yawa..... Cikin faure fuska ta datse ta ban gane ba? yauwa tokin gane

Chapter 4 of 7