ko, ba wai na ce kar ki so Tahir ba
65
ne kin san ni ce ma mai dada karfafa maki gwiwa
kuma ban taba kawo miki wani kushe a kan Tahir ba.
yi.
Ki yi bayaninki kawai dan Allah. Kadai kai ta
Abin da nake so ki gane ba duka abin da namiji
yake so ne za ka yi mishi..... Sai abin da yake ki ko?
Ba ta dai tanka mata ba, ta ci gaba shi namiji idan ka
cika zake mishi har ma ka sake ya fahimci fifikon son
ka a kanshi to wallahi za ka shawu nan gaba kin ga
misali.....
Cikin kufula ta ce, Misali? Misalinki na banza,
to bari ki ji, babu wanda ya isa hana ni son Tahir, shi
nake so, shi ne kuma zabina, gaskiya ne ba karya ba
ina son shi, sai meye kuma? Aikin banza kawai, in ban
da sa ido ma ina ruwan mutum da kai?" ba ta saurare
ta ba domin ta san halinta ita me saurin daukar zafi ce
amma kuma ba ta da riko ko kankani, kai sum ma saba
yanzu za su haura an jima kadan kuma su shirya balle
fa yanzu da idonta ya rufe da son Tahir.
A harabar Zenith Bank Ambassador Sa'ad tare
da diyarshi Heedaya suka dumfari bankin, kimanin
minti arba'in da biyar suka kammala da abin da ya
kawo su, hannunta rike da briefcase din Dad din nata
ta yi shiga irinta alfarma, sakakken leshin Kasar
Malesia ne a jikinta, ta yi kyau ainun kai da gani ka ga
yarinyar da ake ji da ita. 96
Tana gefen mahaifin nata suka hadu da abokinshi. Musabaha suka fara yi tare da jinjina tsawon lokacin da suka dauka ba su hadu ba, iun hawan gwamnatin da ke ci a yanzu. A yawancin lokutu General Abdallah Usman ya fi zama a birninAbuja
wasu lokutan kuma yakankasance cikin yanayin aiki zuwa kasashe daban-daban, shi ko Ambassador Sa'ad al'amuranshi sun fi karkata ga Kano da Birnin Ikko. Russunawa ta yi da niyyar gaishe shi ya yi saurin riko hannunta, wace ce wannan? kada dai diyar
tawa ce ta girma haka? Lallai kam idan akan hanya ne
zan wuce in bar ſiyata.
A to kai ma ka fada gaba daya dai zumunci ya yanke a tsakaninmu, laifin wa? Cewar Gencral. Lefin kusan
dukanmu ne. A to ka fadi gaskiya dai. Cewar General. Zumunci dai ba abin wasa ba ne duk da cewa dai wasu al'amuran ne suka sha kawunanmu to amma dai duk da hakan babu wani uzuri a kan yada zumunci domin shi zumunci abu ne mai kyau, don haka ne ma nake neman iri
tun da ga diyata ta tasa sai mu dada inganta dankon
zumuncin da ke tsakaninmu. Kai da kaya duk mallakar
wuya ne, dukkansu kai mai iko a kansu ne, ni kam ina gefe idan kun gama kintsunku mu 'yan shafa fatiha ne. Dariya ya saka, kai kai sa'ad na yi farin ciki, na gode Alalh da ya sa zumuncinmu ba zai tafi a haka ba. diyata kishiryà kwanan nan za ki sami sabon Dady har ma
da Momy. Zuciyarta in ta yi dubu ta baci, amma dai ta kanne, ta shiga sunkui da kai tare da murmushin da ma iya kiran sa da yake. Ya ciro kudin Kasar Amurka (dollors)
67
masu dama ya ba ta, ta karba tana godiya. Ba ta wani sa
abun a zuciyarta ba, tunda ba ta dauke shi da muhimmanci
ba, kai ta ma mance da batun.
Safiyar ranar asabar ta gurfana a gaban mahaifinta,
Hecdaya na sani ke yarinya ce me da'a da son duk abin da
nake so, ina so ki nuna wannan halayya taki, baki za mu yi
yau ki mutunta su ki kuma girmama su. Kamar me da. me
kuke bukata da za ku girka musu? idan kuma daga
restaurant za a yi order shi ke nan? Ta ba shi amsa Dady na
duk abin da kake so ni ma ina son shi, duk yadda kake so
haka za a yi, ko a girka musu ko kuma a yo take away,
fatana Dady wata rana ka cika min wannan burin nawa. Ве
fahimce ta ba ya ce to Allah ya nuna mana wannan rana
ummina.
Misalin karfe biyar na yammaci komai ya kammala
bakin kawai akejira. A can kuma ran General din in ya yi
dubu ya baci ya dubi matarsa Haj. Fatima, kin ga tsiyar da
yaron nan zai mana ko, karo na biyu fa ina fada masa a yau
din nan amma kuma ya yi kunnan uwar shegu da ni dan kar
in dame shi'ya ma rufe duka layukan nasa. Ita ma dai ran
nata a bace yake ta ce to ya za mu yi tilas mu tashi mu tafi
dan kar mu zama manyan kawai, dadinta ma da ba ka riga
ka shaida musu da shi zamu zo ba, daman ni Alhaji sam
ban so hakan ba, neman aure bayan iyaye har da shi kanshi
saurayin?
Ya daka mata tsawa kar ki kawo min zancen banza
mana, ko daman ke kika zuge shi ya yi min wannan
wulakancin? To bari ki ji ni da sa'adu duk daya muke in
kin mance na ki tuna babu wani banbanci. Sai menene dan
na tafi mishi da danshi ya nemi albarkarsa?
68
Haba Alhaji duk abin ba na haka ba ne, kana 1a saurin daukar zafi ne, amma yaushe zan ki zuri'ar sa'ad 1? Ya dan saki fuska ni ma dai abin da na duba ke nan. Kin
san ko babu me iya hana auren nan sai dai Sarki Allah idan
be kadarto ba, in ma dalilin da ya sa ya gudu ke nan to ko ya yi a banza.
Iyakacin karba ta karamci da girmama wa kam iyalan Ambassador sa'ad sun musu, a yau har da Aunty Na'ima da ita ake karbar bakin duk da dai fuskar Hajiyan ta
nuna ba ta so hakan ba to amma ya za ta yi tun da ba ta da mataimakiyar da ta fice ta.
Dukkansu sun hallara a falon Fa'iza, Fa'iz da ma mardiyay da fiddausi suka zo domin gaisar da bakin, Haj. Fatima fadi take ni ina diyar tawa ne? Na'ima ko ke kika boye min ita ne? murmushi ta saka, haba Hajiya mutum da diyarshi a hana shi ganinsa?" to ke Kaltume ko ke kika boye min diyar tawa ne? baki ta rike ni wa ce ni, nemi
uwarta ga ta nan dai ta nuno Na'iman, to ko ke Na'ima duk
inda diyata take maza je ki ki kawon ita. Kamar hadin baki
sai ga shi ta yo sallama sanye take cikin rantsattsan leshin Kasar Faransa (French Lace) amma fa firsrt class din, ko ina a jikinta sai sheki yake ya sha adon zinare hannunta rike da katon tray da aka rufe shi da abin rufe abinci na bature. Wannan abinci ne na musamman da ita da kanta ta shiryowa bakin dadin nata duk dan ta faranta zuciyarshi.
Russunawa ta yi ta ajiye a gabansu, cikin sassanyar
muryarta ta shiga gaishe su, riko hannunta ta yi taso diyata
zo nan ki zauna babu kunya ko ta dare abinta ko da yake ba
ta san wace ce ba, ta so sheda General din amma kuma
fuskar sai ta bace mata ta ma mance inda ta san shi.
69
Haj. Fatima tuni ta gama yabawa da zabin da
maigidanta ya yi wa dansu, yarinya ga kyawu, usuli da
kuma tarbiyya, take yarinyar ta shiga ranta haka nan shi ma
sai ya ba nutsuwarta yake ga Ambassador ko zuciyar nan
tashi kamar farar takarda dan haske a duniya, yana son duk
mutumin da yake kaunar diyar nan tashi diyar da son ta ya
fifita a zuciyarshi a duk cikin 'ya'yanshi.
Ga Heedaya ba ta san me ke akwai ba ita dai duk ta
ji ta takura ko don ganin babu sa'anninta a wajen ne abin da
dai ta lura tsananin kulawar da bakin ke ba ta har ta kan yi
mamakin hakan, sai kuma ta ayyana kila sun san
matsayinta ga Dadynta ne shi ya sa suke mata wannan
kulawar, domin duk mai son farin cikin Dady toya so ta.
Kyauta ce a kai mata irin tasu ta manya har ita kanta
lamarin ya so ya ba ta mamaki.
A can guest house din General da ya kasance dan
nashi ke amfani da shi kusan ma ya zama mallakinsa.
Abdulwaheed ne ya yi dai-dai kan carpet yayin da Samir
din ke kishingide kan 2 seaters, ya dube shi ka san wani
abu ko Samir? Waheed din ya fada. A'a sai ka fada cewar
Samir. Murmushi ya yi sai kuma ya yi ajiyar zuciya sannan
ya ce, Wani abin dariya Dady yake shirin yi wai kamar ni
din nan zai nemawa macen aure. Ban gane ba? ya katse shi,
kai fa banza ne ka cika garaje to ina jin ka amma fa kar ka
kara ce min banza, da Allah ja can na fasa fada maka ya
diro daga kujerar kar mu yi haka dakai abokina ka sani
abokin kuka ba a boye mishi mutuwa.
Ya ci gaba wai Dady ne zai hada ni da wata 'yar
abokinshi har ma yake shirin kai ni gurinta kai ka ji fa?"
dariya ya saka kai amma fa da ba dan Dad bane da sai na се
70
ya yanke ka zan ce? Dadin ne zai kai ka zance? Ya saka dariya kai Allah ya kyauta.
Da Allah bari yi min dariya nan kai abin ma dariya ya ba ka ni fa duk haushi mana na ji wallahi shi ya sa ma yau duka na kashe wayoyina tun da ni dai ban isa na ce mishi ba za ni ba, ka san dad dai sarai ba sai na shaida maka shi ba. Ni kam Waheed a nema min macen da zan aura kai Allah yakyauta tamkar na makance. Shima Dad din da wata rigimaryake ka san ko ni ma haka muka yi da Abba (mahaifinsa) kwanaki, sai fa da kyar na kwaci kaina, wallahi fata-fata na yi wa yarinyar ba shiri na kwaci kaina, kai in ka ga yarinyar kamar wata 'yar shila sai shegen kyau
amma kuma sam badiri, ina jin kila ma auruwa ta ki yi shi ne a ka nemi likawa Abbana. Kai dai Waheed Allah ya fisshe ka domin Abba da Dady ba daya suke ba. Abba akwai saukin kai yayin da Dady bai daukar wargi ko Kankani.
Shiru ya yi yana nazari, maganar ka fa akwai kamshin gaskiya sai fa na yi da gaske, sai kuma ya ja tsaki mtsss, kai Allah ya tsare ni wa ya sani ma ko me kama da dan shilan ce? Ka ko san yarinyar arziki macen da ta isa ainsa sunanta na ma ce ba za a taba neman kai da ita ba,
don da ga ji ka san kwantai ce neman kai ake da ita ka san kuwa tsoffin nan namu sai dai a yi sha'ani kawai, amma
sam ba sa iya gane wa irin wadannan abubuwan. Samir din
ne ya dada ingizo shi sai kuma dariya ta ci karfinsa, Allah sarki yau dai ga ranar da idona zai gane mini kyautar sankacecen guy me ji da kansa, shi ke nan fa daga kanka sai fa rufe kyautar 'yan mata sai fa samari to amma fa dad
ban ji yana batun kawo k udin toshi, kudin zance, waye71
waye dai....Wani wawan duka ya kawo mishi da kafa yau
za ka gane cewa ni ba sa'an wasanka ba ne, bai same shi ba
sai jikin garun dakin da ya samu ya ji zafi har cikin
kashinsa bai san sanda ya ce wayyo Allana.
Ta sami waje ta zauna daga cikin kayatattun
kujerun da ke dakin mahaifinta. Ya fito daga dakin
hannunsa rike da jarida. Ummina kin iso ko? Na iso
Dady. Yau wa to Allah ya yi miki albarka, kina ji ko?
Ya shiga bayyana mata makasudin kiran nata, dafe
kirji ta yi wayyo Dady ka cece ni ka yi min rai ni Tahir
kawai nake so shi kadai na za6a bana son kowa ba
shiba.
Tsawa ya daka mata ke ba na son rashin
hankali, tun yaushe na gargade ki da yaron nan, kina
zaton ko ban zo miki da wannan batu ba zan amince ki
aure shi ne? wannan kuskure ne babba. Ya sassauta
murya haba ummina kada ki ba ni kunya kinsanba zan
taba zabar miki abin da na san zai cutar da ke ba, ki yi
hakuri ki amshi zaßina.
Ba zan iya ba Dady. Ta fada tana kuka, dan
Allah ka ceci rayuwata kada ka hada ni da kowa ba
Tahir ba. Tahir kadai nake so Dady.
To fa duk iya lallami da lallashi ya bi amma fa
yarinyar ta kekashe, haka dai ya dinga binta sannu a
hankali har zuwa lokacin da yake tunanin shawo kanta,
kokadan ba ya son bacin ran 'yarshi kamar yadda ko
menene zai mata amma ban da ya ba ta Tahir.
72
To haka dai al'amura suka ci gaba da wanzuwa,
kull;um cikin lallashinta yake, ita ma Hajiyan na nata
kokarin, za ta yi mutukar farin ciki idan lamarin ya
tabbata zumuncinsu zai dada inganta da tsohuwar
aminiyar tata, burinta kuma zai cika na aurar da 'yar ta
gidan da za ta huta, domin dai Hajiya kaltum 'yar jari
hujja ce.
Soyayyarsu da Tahir sai dada karfafuwa take yi
yayinda kowannensu yake jin zai iya yin komai a
domin dayansa.
Ranshi a 6ace ya dube shi Abdulwaheed ka
kyauta abin da ka yi jiya? Zai dan fara magana ya
katse shi ya isa ba na son jin wani abu daga gare ka, ka
sami lokaci daga nan zuwa gobe ka je ka ku gaisa, ba
na son wani korafi domin mun gama magana
damahaifan yarinyar, ita kanta yarinyar na yaba da
nutsuwarta dan haka ka yi kokari ku fuskanci junanku,
nan da lokaci kankani.
Dad... ya yi nufin furta wani abu amma ya yi
saurin dakatar da shi, ka tunana sha yi maka maganar
auren nan amma sai ka share saboda ka mai da ni
dattijon banza, damarka ce ka riga ka saki don haka ba
ka da wani zabi da ya wuce zabin da na yi maka.
Yinin ranar dai cikin dacin rai ya yi shi don me
ya sa ne zai mishi haka kamar wani karamin yaro?
macen ma da zai aura zai kuma zauna da ita sai an
zaba mishi? Kai hąba sam ma ba zai yiwu ba dan haka
73
ya ma share maganar baki daya, ya yi sa'a a dai-dai
lokacin yana da tafiya zuwa birnin Amsterdam ta kasar
Netherland, abin sai ya zo mishi a dai-dai, ko da ya
dawo be ko kara tunawa da maganar ba kai ya ma
mance baki daya domin a lokacin macen da ba zai iya
hada son ta da kowa da ita ba take tashe a zuciyarshi
wato Zeenatu ga kuma 'yan matanshi na bayan fage da
suke jin dadin rayuwarsu da su, dan haka babu aure ko
maganarshi a zuciyarshi a dai wannan lokacin.
Ajiye wayar ya yi ranshi a bace bayan da suka
gama tattauna da amininshi Ambassador Sa'ad Mohd,
ya dubi mai dakinshi Fatima ashe yaron nan bai je
gurin yarinyar nan ba, ni na yi zatontuni komai
yakankama har nake rawar kafar tuntibar lokacin da za
a tsayar na auren nan. Ita ma din mamakin dai ta yi.
Wallahi Alhaji ni ma din an zaci tuni sun gama daidaita kansu, ya yi kwafa, zai ci kaniyarshi kuwa
yashiga nemo shi a layi, bai yi wani mamakin kiran
ba, a zatonshi be wuce wasu al'amuran da suka jibanci
harkokinsu ba,tun da Dadin yana yi musu kokari
kwarai da gaske. Shi da Samir din suka iso da yake
suna tare, lokacin da ya yi yo wayar fuskarshi kawai
suka kalla suka san fa ba kanta.
Cike da girmamawa suka gaishe da mahaifan
nasu, ya dube shi fuska a daure sam babu walwala a
cikinta, kai dai kam mutumin banza ne ashe ko baka je
gurin yarinyar nan ba? gabanshi ne ya ba da dam!
74
Gaba
suka
daya ya mance da maganar kai tun lokacin da
la
yimaganar ma ya sa kafa ya shure ta ya ma share baki daya.
Da kai nake? General din ya fada cikin kufula, ya nuno shi da yatsa, to wallahi tun wuri ka shiga taitayinka dan ban haifi yaron da zai kunyata ni a idon duniya ba. auren nan babu fashi kai da yarinyar nan, sa'o'i biyu kacalna ba ka ka je ka gan ta. Shi da kansa yasan bai isa ya tankawa mahaifin nasa ba yadda ya dau zafin nan har ya yi fadansa ya kare kansa na sunkuye. Ya nuno da shi da dan yatsa, kai Samir kai na dorawa wannan nauyin ina jiran ku maza ku je kai mishi rakiya yanzun nan, kafin kai ma mu juyo kanka, domin dukkanku jirgi daya ne ya kwaso ku shashanci kawai kuka sa a gabanku.
Ya sunkui da kai gami da shafa keya, tuba muke Dady. Ya ci gaba kuma ai ba mu san yarinyar ba, amma dai ina jin kun san Ambassador Sa'ad Mohd in ma ba ku sani ba ku je ku bincika don ba boyayye
ba ne. kai soja masifar zuciya gare shi tga fadan tsiya
amma in ban da haka meye na gayamusu wannan
maganar daga tambaya tunanin Abdulwaheed ke nan. Sum-sum suka tashi ya sani sarai bai isa kawo masa wargi ba balle har ya ja da maganarsa.
Da fitarsu bayan sun hau kwalta ya faramtia
wallahi ko 'yar uban wace sai na ci ubanta 'yar iskar yarinya ta saka an ci zarafina. Ya dube shi ka san
75
meye? Be jira amsar tasa ba, wallahi tun katin in ga
yarinyar na ma tsane ta ba na son ta, kai ba ma zan so
ta ba, duk dai kai daya? Cewar Samir. Zai fara
shakiyancin nasa ya ga ba fuska sai shi ma ya gimtse.
Ka ga ko da za ka gane ka kuma dau shawarata
da sai na ce kada ka yi saurin yanke hukunci, mu jе
kawai mu ga yarinyar idan ta yi mana ta kuma kai ajin
da ya dace sai mu so ta, ba shi ke nan ba, ai ba a
kanmu a ka fara kyautar da saurayi ga mace ba.
Ya harare shi, wallahi ka maida hankalinka
kuma idan dai har kai ta yi maka to wallahi na
barmaka ita duniya da lahira. Baki ya buďe kai haba,
ai ka san har yanzu akwai gayu masu aji wadanda ba
su riga sunyi kwantai ba har ma a fara tunanin kyautar
su,ka ga ko ina cikinsu dan haka ni Abbana ba zai yi
kasassabar kyautar da ni ba. Dauke kai ya yi ya ci gaba
da tukinsa ya ma ki saurarar sa dan kada ya kara
hadamishiwani dumin.
Tunaninshi ya kasu kashi-kashi, ya ki bin
umarnin mahaifinsa ya ko gane kuransa, ya fi kowa
sanin halinshi, to amma kuma ya za a yi ya kai kansa
gurin yarinyar da aka ci zarafinsa a kanta, ba ma
wannan ba ya ma za a yi a ce kamar shi hadaddden
gaye ya kasa za6o matar da zai aura duk da tarin 'yan
matan da suke sonshi ga kuma uwa uba rabinranshi
Zeenat to amma a wani bangaren hudubar abokinnashi
ta soma shigarshi, me zai hana idan har ta yi masa sat
76
ya hakura ya sota har ma yaaure ta in ya so daga baya
ya auri zabinsa, idankuma ba ta yi masa ba fa? ya tambayi kansa, to anan fa zuciyarshi ta dagule kila ma mai suffar dan shilan ce irin wace Samir yake ba shi
labari, don wace macen kirki ce za a tsaya ana kyautar
da ita, kai in ko haka ne Dadin ya gama da shi, ya sani sarai taurin zuciyyar mahaifinshi.
Wai ina za mu je ne? Samir ya tambaye shi,
gurin ta mana. Wa? Ya tambaye shi. Ban sani ba. Ya ja
tsaki banza kawai. Ya lura so yake ya dada jagula
zuciyarshi, dakata dan Allah, juya mu koma gida.
Haba da Allah ji bi shigar da ke jikinmu sam be dace
mu je haka ba, neman aure fa ba wasa ba ne, har
gwanda ma ni T.Shirt ce da dan faffadan wando kai
kuwa fa? ji fa wasu matsattsun kaya da kasa, ka wani
hadu ka tsuke kamar wani lemon da ya motse. Kar fa
ka ci min mutunci a kank wata 'yar iska.
Ai gaskiya ce dole in fada. Ya ma za a yi mu
jemusu a haka, ai iyayen yarinyar ma sai su hana ta
fitowa. Da kwa sun kyauta mini. Ya fahimta da gaske
yake, a hakan yake nufin su je. Dakata ya fada
fuskarshi ba wasa, sauke ni kawai na fasa rakiyar,
daman ni zuwan bai zame mini wajibi ba idan Dad ya
tuhume ni sai na sheda masa dalili na san kuwa ba zai
ga laifina ba. Ciza labbansa ya yi da hakoransa, cikin
fusata ya juya akalar motar zuwa gida, tun da dai in ba
Samir din bai iya jin zai iya zuwa.
77
Da kyar da sudin goshi ya iya sa shi saka 'kayan
kirki, wato tsadaddiyar Ghalila launin alawar cakuleti
(Chocolate Colour), ai kuwa kayan sun amshe shi ya yi
kyau ainun, shi ma Samir din Galilar ya saka 'yar
ubansu.
Misalin karfe biyar na yammaci suna Rofar
gidan Ambassador Sa'ad Mohd cikfin unguwar
Nassarawa kan titin Abbas Road. Duka-duka ba wani
nisa ne a tsakaninsu ba.
Kyawun gidan dai kam ba sai an fada ba, mai
gadin gidan ne ya russuna ya gaishe su suna daga
cikin motar, Waheed din ya yi karfin hali, Baba mutan
gidan muke magana da su. Wa? Hajiyan ke nan? Samir
din ya yi saurin gyara zancen. A'a diyar Alhajin muke
nufi tun daga shi har abokin nashi babu wanda ya san
sunanta. Dariya ya saka baba mai gadin lallai kam 'yan
yara kun yi gaskiya, ran gidan gaba daya kuke nufi, in
dai 'yar lele HEEDAYA ke nan. Ta gaban goshin Oga
kwata-kawta zai fara yi musu hari gidansa kasancewar
mutum ne me shegen surutu. Waheed din ne ya yi
saurin katse shi taimaka dai ka kira ta baba, ko da ta
kuryar keya ce. Mintsini Samir din ya sakar mishi, kai,
kai, kai kar ka kuskura bakinka yaro kada wani
tsautsayin ya sa wani ya ji ya isar da wannan sako
zuwa ga Alhaji, ka san fa Alhajin zai iya yadda da
komai na batanci a gare shi amma fa ban da taba 'yar
lele ta gaban goshi, kana uwar dakin mu Hcedaya
78
ya hakura ya sota har ma yaaure ta in ya so daga baya
ya auri zabinsa, idankuma ba ta yi masa ba fa? ya tambayi kansa, to anan fa zuciyarshi ta dagule kila ma
mai suffar dan shilan ce irin wace Samir yake ba shi labari, don wacec macen kirki ce za a tsaya ana kyautar
da ita, kai in ko haka ne Dadin ya gama da shi, ya sani
sarai taurin zuciyyar mahaifinshi.
Wai ina za mu je ne? Samir ya tambaye shi,
gurin ta mana. Wa? Ya tambaye shi. Ban sani ba. Ya ja
tsaki banza kawai. Ya lura so yake ya dada jagula
zuciyarshi, dakata dan Allah, juya mu koma gida.
Haba da Allah ji bi shigar da ke jikinmu sam be dace
mu je haka ba, neman aure fa ba wasa ba ne, har
gwanda ma ni T.Shirt ce da dan faffadan wando kai
kuwa fa? ji fa wasu matsattsun kaya da kasa, ka wani
hadu ka tsuke kamar wani lemon da ya motse. Kar fa
ka ci min mutunci a kank wata 'yar iska.
Ai gaskiya ce dole in fada. Ya ma za a yi mu
jemusu a haka, ai iyayen yarinyar ma sai su hana ta
fitowa. Da kwa sun kyauta mini., Ya fahimta da gaske
yake, a hakan yake nufin su je. Dakata ya fada
fuskarshi ba wasa, sauke ni kawai na fasa rakiyar,
daman ni zuwan bai zame mini wajibi ba idan Dad ya
tuhume ni sai na sheda masa dalili na san kuwa ba zai
ga laifina ba. Ciza labbansa ya yi da hakoransa, cikin
fusata ya juya akalar motar zuwa gida, tun da dai in ba
Samir din bai iya jin zai iya zuwa.
77
Da kyar da sudin goshi ya iya sa shi saka kayan
kirki, wato tsadaddiyar Ghalila launin alawar cakuleti
(Chocolate Colour), ai kuwa kayan sun amshe shi ya yi
kyau ainun, shi ma Samir din Galilar ya saka 'yar
ubansu.
Misalin karfe biyar na yammaci suna Kofar
gidan Ambassador Sa'ad Mohd cikfin unguwar
Nassarawa kan titin Abbas Road. Duka-duka ba wani
nisa ne a tsakaninsu ba.
Kyawun gidan dai kam ba sai an fada ba, mai
gadin gidan ne ya russuna ya gaishe su suna daga
cikin motar, Waheed din ya yi karfin hali, Baba mutan
gidan muke magana da su. Wa? Hajiyan ke nan? Samir
din ya yi saurin gyara zancen. A'a diyar Alhajin muke
nufi tun daga shi har abokin nashi babu wanda ya san
sunanta. Dariya ya saka baba mai gadin lallai kam 'yan
yara kun yi gaskiya, ran gidan gaba daya kuke nufi, in
dai 'yar lele HEEDAYA ke nan. Ta gaban goshin Oga
kwata-kawta zai fara yi musu hari gidansa kasancewar
mutum ne me shegen surutu. Waheed din ne ya yi
saurin katse shi taimaka dai ka kira ta baba, ko da ta
Kuryar keya ce. Mintsini Samir din ya sakar mishi, kai,
kai, kai kar ka kuskura bakinka yaro kada wani
tsautsayin ya sa wani ya ji ya isar da wannan sako
zuwa ga Alhaji, ka san fa Alhajin zai iya yadda da
komai na batanci a gare shi amma fe ban da taba 'yar
lele ta gaban goshi, kana uwar dakin mu Heedaya
78
A katafaren dakin saukar bakin Alhaji aka sauke su,
baban ya russuna gami da yi musu sallama, amma fa 'yan
samari a daure kada a sami firgici a lokacin da kuka yi
tozali da 'yar kyakkyawar diyar tamu.
To nagode baba amma a dinga saka linzami a bakin
musamman ga bakon ido. Cewar Waheed. Kai kan ba ka
da mutunci, wai ko ka san ko inda muka