zan
siya ba duk gorin da za ka yi min, ina ni ina siyan wannan
dankareriyar motar? ko ko nima kana so a tuhume ni da
halin bera ne? Kallonshi ya yi kawai ya kau da kai idan ya
biye mishi sai ya saka masa ciwon zuciya.
Sam ba ya yin fushi da duk maganar da za ka gaya
mishi yayin da shi kuma zai dinga lailayo wacce ka iya sa
zuciyarka ta tarwatse saboda takaici.
Banza mara zuciya mai naci sai ka rufe motar mu
tafi. Yana dariyar dai ya ce, na ji dai ko ma menene da
sauki tun da ba a tuhume ni da halin 6era ba. Be tanka
mishi ba illa dogon tskai da ya ja, gami da kwada mishi
wata muguwar harara, You are very stupid, you are very
idiot. Shi ma ya mayar masa sai kuma gaba dayansu suka
kwashe da dariya. 30
Wahced da Samir abokanai ne tun suna kanana haka suke a yi fada a shirya tun zamanin Kuruciyarsu haka nan kusan daukacin rayuwarsu, karatunsu kai, dama komainasu tare suka yi shi, makwaftan juna ne, haka nan iyayansu aminan juna ne don haka in ma ba sanika yi ba za ka ıya tsamınanin 'yan uwan juna ne. Sun sami ilimi mai zurfi har zuwa matakin Degree a fannin Engineering. Shi dai Waheed va yi degree ne a Bulding Engineering shi ko Samir bangaen construction Enginecring ya karanta. Bayan karewar karatunsu sun fara aiki da gwamnati na kankanin lokaci to daga nan ne suka bude kamfani na Kashin kansu na yini ginc-gine tare da taimakon mahaifansu.
Mahaifin Waheed General Abdullahi Usman tsohon
soja ne har mataimakin shugaban kasa ya yi a zamanin da ake mulkin soja a kasar nan. A yanzu haka shi ke rike da Ministantsaro (Defence Minister). Shi ko mahaifin Samir Dr. Salim Ibrahim Kwararren ma'aikacin gwamnati ne, ya rike manya da kananan mukamai a kasar nan har kawo yanzu da yake rike da matsayin MD. Na Bankin Arewa (Bank Of The North), mahaifiyarsa kuwa ma'aikaciya ce a
ma'aikatar lafiya (Ministry of Health). Haj. Fatima wato mahaifiyar Abdulwaheed 'yar kasuwa ce tana gudanar da kasuwancin nata a tsakanin Saudi Archia dia kuma kasar ch ina, duk da cewa zamani ne da aka cigaba tana daga gida take gudanar da harkokin kasuwancinta ta cikin na'urar sadarwa ta zamani (Internet). Shi Waheed din shi ne da na farko a gurin iyayansa daga shi sai Abdulwahab, Abdurra'uf, Lubuna da kuma Lubabatu.
31
de to sh baste W
[[**************** hea
Suna tare da mahaifinta a babban falon gidan kowa
da kowa na gidan ya halarta cikin walwala da nishadi in ka
cire Aunty Na'ima da ke gefe cikin takurarko da yake in ba
Ambassador yana nan ba yaushe ta ga fuskar zuwa falon,
haka yake shi mutum ne me tattalin iyalinsa yana son
iyalinsa yana kuma bakin kokarinsu wajen kyautata musu
kowanne na rubuta list na abinudauyake bukataya duba
yagani sa'annan ya zana vek yasmikawa Hajiyan kowanne
a sai mishi abin da yake bukatay har su mardiyya a tambayi
ra'ayinsu.
Ya juyo gare ta, na dawo rgaré ki ummina ta dauke
hannunta daga laptop computer ta main dad dubanta ga
mahaifinta. ya fara magana ummina aikin nan ya isa haka
kullum fatanki ki kare karátuoki lzáina cikakkiyar lauya
sannan ki yi aure duk dai na bivra'ayinkiedon dai kada in
tauye ki, amma kuma kehgal shinkina son bata min zuciya
tun yaushe nake miki wannan maganar amma kuma ma lura
yawo da hankatina kawai kike son yis 1
Dady yaushe zan so in 6ata ranka? Ai na ce maka
tuni maganar ta shige na bayyana maka ra'ayina.... Da sauri
ya katse ta ummi lamarinku davyaron nan ba mai yiwuwa
banc, na nunamiki hakan tun darfarkoki dai sauya tunani
in ba haka ba zan hada ki da duk wanda na yi ra'ayi. Ta
buda baki domin ba ita san abin ya kai thaka ba, Dady wai
don Allah mai ya sa ba kalson zabina ne? wallahi Tahir
yana kaunata Dady dan Allah kaso shi tun da yana kaunar
diyarka. Kai ya girgiza ummi ke yarinya ceiba za ki gane
32
abin da nake hange miki ba, kowane irin bayani zan miki ki dai yi hakurı ki cire yaronnan daga zuciyarki lamarinku ba
mar. yiwuwaha ne.
Kuka ta saka wayyo Dady ka cece ni don Allah ka
so Tahn wallahi shi kadai nake so. Ta zo ta tsuguna a
gabansa tana rokonsa. Kada kai ya yi ya fice ranshi a bace
sam ba ya son bacın ranta ba aon ya gan ta cikin bacin
rai balle har ya ga zubowar haw ayenta, yana yi mata wani
irin fifikon so a duk cikin zurı arsa, ba kuma ya taba hana
ta duk wani abu da take bukata daga gare shi. Ba ya fatan
wannan rana, to sai dai fa ga ranar nan ta zo ranar da zai
hana umminsa zabin ranta, sai dai kuma ya san hakan shi
ne mafi alheri don haka nema bai cika damuwa ba.
Cike fada kan da shagwaßa ta cinyar mahaifiyarta
tana kuka, yayin da momin ke lallashinta ita kanta ba ta
ra'ayin wannan aure, to amma tun da yarinyar ta kafe ta
nace ba sai a ba ta ra'ayinta ba, tana son farin cikin 'yarta
fiye da komai a duniya.
Kukan dai take a cikin kuryar dakinta, dan menene
Dady zai yi mata haka? me ya sa ne yake kokarin bijirewa
abin da shi ne mafi soyuwa a gare ta? Abin da Dady be
fahimta ba shi ne tana son Tahir son da ba za ta iya hakura
da shi ba.
Cikin talatainin daren ya kira ta a waya, "Hello my
sweet heart how are you? Ya fada cikin taushin harshe. Da
kyar ta iya ba shi amsa cikin rawar murya take ya fahimci
tana cikin matsala cike da damuwa ya ce menene Heedaya?
Wa ya taba min ke? Ta yi kokarin boye masa, ya ce a'a
Heedaya kar ma ki rufe ni muddun kina cikin damuwa ko
33
da ba na dubanki sai na sani, kin san da hakan? Don Allah
gaya min menene?,
Kuka ta saka mishi, ya dada rudewa kwarai da
gaske ta fahimci hakan nan da nan ta dada shiga cikin wani
damuwar gami da tausaya musu a bisa kudurin da ake
kokarin yi na shiga tsakaninsu, cikin muryar kuka ta ce
Tahir Dad na son raba tsakainmu, ni kam ban san me ya sa
ba ya son lamarinmu da kai ba, bayan ni nasan Dadin yana
son duk abin da nake so.
Shiru ya yi na wani lokaci ranshi in ya yi dubu ya
Baci da kyar ya iya furta ni kaina na rasa dalilin da ya sa
Dad ba ya ra ayina, ni kam in ya raba tsakaninmu ban san
inda rayuwata za ta kasance ba. Heedaya ina son ki son da
ban san iyakarsa ba, don Allah kar ki bari wani ya kwace ki
daga gare ni. ya zan yi ne ni Tahir? Da ganin wannan rana
gwanda mutuwa. Tofa kai ya kwance ya shiga yi mata
surutai barkatai har ta yi dakacen gaya masa. Sai ya
zamanto ita ce mai lallashin ma, da kyar da sidin goshı ta.
lallaba shi suka yi sallama.
Misalin karfe takwas da rabi dai-dai va sd
ofishın nata wanda isowarta ke nan ma Masinjanta ta
sa ya kawo mishi breakfast amma ko ya daga kai ya
dube su, saboda damuwar da yake ciki.
"Heedaya." Ya ambata hakan ta dube shi bayan
da ta amsa mishi, "Idan dai kin amince kin kuma ba ni
hadin kai a yau din nan zan turo magabatana gurin
Dadinki. Meye ra'ayinki.?"
Kada kai ta yi, "Ko kusa kada kai haka."
34
Π
"Saboda ba kya so na ko? akwai wanda kike ra'ayi ko? To na gane na kuma gode." Ya tashi cikin Bacin rai da sauri ta dakatar da shi, “Zauna don Allah.
dadina da kai saurin fushi, amma in ban da hakan kai
da kanka har ka yi tunanin akwai wani namiji da ke
gabana a bayan kai? Kai ma ka sani sai dai kawai ka so
zuciyarka.
Hannu ya sa ya dafa kansa, "Ya kike so in vi
ne?" ta ce, "Yauwa ka gane ko kar ka yi garajen turo
magabatanka in ba haka ba za a bata goma dayaba ta
gyaru ba, ka dai bari na gama shawo kan Dady, ka san
Dad na so na yana son duk abinda nake so don haka
nake saka ran nan gaba kadan zamu cimma nasara.
Ajiyar zuciya ya yi, "Na fahimce ki Heedaya,
na kuma yarda da kaunar da kike min, sauran kokari
duk yana gurinki, ki dage ki cije ki turjewa Dady Tahir
finki shi ne ra'ayinki, zabinki." Kai ta daga mishi
gami da murmushi.
Yanayin dai yana ci gaba da tafiya a haka, yayin
da Dad dinta ya dage ya cije sa'ilin ne wutar sonsa
take dada ruruwa a zuciyarta, haka abin yake a
Bangaren Tahir, yana ji kamar wannan lokacin ne ma
ya fara son ta.
Ana tsaka da bikin faisal da amaryarsa Amal
yayin da Heedaya da Tahir dinta suka kasance kirjin
biki, yau ita ce rana ta karshe wajen gudanar da
35
shagulgulan bikin a kuma ranar ne za a gudanar da cin
abincin dare (Dinner) a Prince Hotel.
Ta kintsa ta hade cikin net (first class) na kasar
Faransa da akai mishi landing da saitin yard. Launin
Kwanduwar kwai komai na jikinta ma launin
kwanduwar kwai ne. hatta da yari da sarka da kuma
abin hannu wasu tsadaddun fasion earring ne masu
mutukar tsada samfurin 'Vivaldi.' kamar ko yaushe
dai hill din takalmi ne a kafarta yayin da ta bi ilahirin
jikinta ta feshe shi da 'Tommy Purfume).
Tsayawa ta yi a mudubi tana kallon mimar da
ubangiji ya yi mata, a yau kam ta dada gasgata sunan
nan da ake kirantta da shi (Queen of Beauty) Barrister
Heedaya ke nan yarinya me ji da kanta. Doguwa ce
sambal me kyawun sura idanunta manya ne masu
kyawun gani, gashin da ya yi wa kwayar idanunta
rumfa su suka dada fito da kyawunta, haka nan tana da
yalwar gashin gira, gazar-gazar gwanin ban sha'awa,
haka nan tana da yalwar gashinka baki sidik sai dai
yana da dan karfi to amma mayukan zamani da take
amfani da su sun mai da shi mai mutukar santsi da
sulbi, ta biyo kalar mahaifiyarta domin baka ce ba ta
da haske ko kalilan ko da yake ko a cikin kanurin ba
kasafai akan sami farare ba.
To sai dai ko kai farin idan ka dube ta za ka yi
fatan zamantowar launin fatarka irin tata saboda santsi
da sheki gami da laushi dafatarta ke da shi.
36
Katafaren hotel din na Prince ya cika ya batse
da zaratan samari da 'yan mata waje ne har waje da ya amshi bakuncin 'ya'yan hutu, 'ya'yan kuma masu da
shi, waje tuni ya gama tumbatsa, domin tuni amarya da
ango sun iso, a gefenta kuma babbar abokiyar amaryar
ce Barrister Heedaya Sa'ad Mohd, gaba daya hankalin
mafi akasarin guys da ke wajen ya tafi gare ta kai ita
me kyau ce kyawun ma irin mai daukar hankalin
jama'a, abin da kunnuwan Waheed ya jiye mishi ke
nan, be wani kokarin juyawa kallon ta ba, ta'adarsa ce
yarinya duk kyawunta duk matsayinta sai dai fa ta so
shi ba dai shi ya fara furta yana son ta ba. Samir din ne
ya zungure shi da kafa. Ya yi masa nuni da ido,
Waheed ga fa mutuniyar taka can. Wa ke nan? Ya
tambaye shi gami da waigawa lokacin ne idanunshi ya
gane mishi fuskar sarauniyar kyawun. Baki ya bude
cike da mamaki bayan da ya gane ta, kai hakika Allah
ya yi halitta a nan, yana cikin wannan tunani ne ya
dada zungurarsa. Meye ne haka kamar wani bakin
maye kakura mata ido. Shafa kai ya yi gami da sunkui
da kai Samir ina son yarinyar nan. Eh me ka ce?
Abinda kunnuwanka ya jiye maka, kada kai ya yi tofa
dara ta ci gida kamar yaya? ka fi ni sani ko da yake shi
ma din ya jinjina lamarin? Meye shawara ne Samir?
Ya dan yi nazari, kawai ka sa kai ka san da zafi-zafia
kan bugi karfe muddin ko ka yi sake ni sai na saka kai,
kai fa dan iska ne, ba a maganar kirki da kai dan Allah
37
ba ni mafita ka san ni dai ban iya wani zance da mace
ba saifa ka kowa a yau din nan in ba haka ba sai dai
idan za ka biya ni, ka san ni komai na kudi ne a gurina.
Dauke kai ya yi gami da jan tsaki, ya ki ya gane
lokacin wasa da lokacin da yake na zama serious.
A bangaren amare kuwa Barrister Heedaya ce
ta gabatar da jawabin amarya cikin tsararren turanci
tamkar baturiyar Ingila. Zazzakar muryarta ta dada tafi
da zuciyar guys din wajen ciki ko har da
Abdulwahecd. An fara gabatar da duk abubuwan da
aka tsara sai dai daga Heedayan har zuwa su kansu
amaren rayukansu a bace yake saboda rashin isowar
babban na hannun damar angon (Tahir). A dunıya
faisal ba shi da abokin da ya fice Tahir, ko meye
dalilin rashin isowar tasa? Wannan ne suka kasa sani,
ta neme shi a layi amma kuma is not available, amma
duk da hakan ta yi karfin hali wajen danne damuwarta
ko dan kar ta dada saka amaren a cikin damuwa.
Babu wasu masu kida da aka gayyata illa music
da aka saki. An ci an sha an gyatse samari da 'yanmata
suka fara dansewa wasunsu kuma suka fara kulla abota
da sababbin 'yan matan da suka yi. Yayin da su
Heedaya suka shiga hidima da da jama'a wajen
rarraba musu gift da aka tanada samari da dama sun
latsa ta amma ko ta kula bi ta ke tebir daya bayan daya
suna raba gift din ita da Samira da kuma Najeeba 'yar
uwar amaryar. 38
A can daya teburin da aka warcwa manya- manyan abokan ango Waheed ne da Samir suke
tattauan yanda za su shawo kan abokiyar fadan nasu, barka da hutawa kuna bukatar abokin hira ne? wata kyakykawar yarinya ta fada, kai da ganin ta ka san
cewa 'yar wani ce ban da ma kyawun da Allah yaba ta
a lokaci daya suka daga kai suka dube ta kallo daya ya
yi mata ya kau da kai gami da jan tsaki akara gaba dai
mun gode, Waheed din ne ya fada.
Ji ta yi wani abu ya tsirga mata, yayin da
matsananciyar kunya ta baibaye ta, musamman da ta
lura dariyar da guys din da ke kusa da wajen suke mata
cikin mutuwar jiki ta bar wajen..
Dunkule hannu ya yi ya daki tsakiyar teburin.
kai Allah ya isa Waheed, wulakancinka ya yi yawa,
haba mai ya sa kai mata haka? Harara ya sakar masa
donme ba zanmata haka ba, a bar ni man in ji da abin
da ke gabana saikumaa zo a ishe ni da wani
karuwancin banza, ka sani dai macen da take tallata
kanta ba kasafai take burge ni ba. Amma dai ko
mameye be cancanci ka yi mata haka ba, ko da yake
sabonka ne wulakanta 'ya'yan al'umma, sai fa in kai
ka yi ra'ayi.
Ta gabansu ta zo ta shige amma ko kallo ba su
ishe ta ba ta lura da su tun farkon shigowarsu kallo
daya ta yi musu ba ta kara ko son duban su ba kai da ta
san akwaiwata alaka a tsakanin su da shi faisal din da
39
ba babu abm da zai sa ta zo, duk da amincin da ke
tsakaninsu da amaryar, to amma tsanar mutumin ta
zarta komaia wajenta.
Samir jibi fa ta share ni ko kallon kirki ba mu
samu daga gare ta ba, ina shakkun tunkarar ta fa?
Samir din ne yake mishi magana cikin rada-rada da
Allah za namiji mana, meye kankanuwar yarinya za
ta firgi ar kai haka... shawara ta a gare ka kar ka
bari wannan lamar ta shige ka, maza je ka ga ta can
sun zauna ita da waccan kawar tata. Kallon shi ya yi
yavin da shi kuna ya kada kai.
Hannunsa sanye cikin aljihun coat dinsa yayin
da dayan yake a sake, ya isa teburinsu, barkanku da
hutawa. Ya tarfa cikin daddadar muryar nan tashi
maisace zukatan `yan mata Ta dube shi ta kara
dubanshi sai kuma ta kau da kai, yayin da ita kuma
samairan ta ce lafiya dai malam. Lafiyar ke nan ya ce
ya ci gata na son magana da kawarki ne. ta dube shi
ta dube ta sannan kunma ta girgiza kai, lallai kam
lamarin babba ne.ya dan matso daura da ita, barrister
Herdaya o zan sami mutsuguni a wajen nan? Wani
irin abu ta ji nai mata yawo a tsakar kanta, tsana da
kiyavyar nutumin ta motsa mata, ji yake jiya ma yau
ce ya zo ya ci mutuncinta, to ai ko zai gane ЛҮА ВА
YAU BA ce tun da zai amshi SAKAYYAR abin da ya
yi mata da hannunsa.
40
Matsowa ya kara yi kusa da ita yayin da yake
kokarin zama kusa da ita da yake kujerar mai cin
mutum biyu, zumbur ta yi ta mike yadda ka san
mutuwarta ce ta nufo ta, cikin shouting (daga murya)
abin da ya janyo hankulan mutanen wajen ta shiga
fadin, "Dan Allah malam ka saurara min, ka fita hanya
ta, domin kai ba tsarana ba ne, ba ka kai ko ajin da zan
tsaya dakai ballantana in kai ga yin soyayya da kai ba,
ba na son ka na sha gaya maka ba na sonka to menene
za ka dame ni?" cike da mamakin tuggun da take
shirin kulla mishi ya buda baki da niyyar magana,
cikin sauri ta tare shi, dama dai kada ka 6ata yawunka
domin ba zai yi tasiri a gurina ba, dan babu wani dadin
baki ko kalami da za ka yi min, domin bana son ka, kai
din nan ba ka isa in soka ba. Samawa kanka lafiya ka
sami dai-dai kai, ni kam na fi karfin tsayawa da kucaki
ka na kazami kamar ka.
Haaaaaaaaaa! Matasan wajen 'yan mata da
samari suka kwashe da dariya, wasunsu ma har danuno
shi da yatsa, musamman ma dai samarin da suka sa
abokin adawar ubangidansu ne ko da yake yawanci
abokanan faisal abokanan Tahir ne na kud da kud.
musamman da yake shi maliya ne ba ya tausayin kudi
ko kankani, amma kuma shi faisal din suna dan
dasawa da Waheed din.
A na cikin haka ne mai gayya mai aikin ya iso
TAHIR DR. EL-HUSSAIN maliya sarkin ambaliya
41
kamar yadda akasarin abokanansu sukan kira shi, cikin
isa da gadara ya iso wajen kai da ka gan shi ka san
cewa wani ne kuma dan wani ne saboda tsadaddun
kaya na fariya da ya sa a jikinsa, da ko Baturen sai
isarsa ta kai isa yake iya saka su, ya dube shi da kallon
raini da kaskanci a gefe guda kuma yana me mamaki
gami da takaicin abin da ya' hada su da Heedayansa.
balbalin bala'i ya ayyana hakan aransa, wannan karon
kam Wahced ka yi kadan har ma ka yi kankanta na
tsane ka, gabarmu da kai ba za ta taba karewa duk dai
a zuciyarshi ya ayyana hakan.
Ya mai da dubanshi gare ta Sweet baby yana
mai dan bata fuskarsa,me ke faruwa ne a wajen nan?
Ta dube shi da sigar so yayin da shi kuma ya hado ta
da jikinsa tell me?" wani mutum ne dabba ko jaki zan
kira shi, ya takura min na gaya mishi ba na son sa, ba
na son sa, ya kasa fahimtar hakan, amma ban sani ba
ko da gasken jakin ne ko dabban? ta nuno shi da yatsa
ka shiga tsakanina da shi Darling Wani kallo ya sakar
masa na nuna tsantsar tsana da kiyayya cike da raini ya
shiga furta kakan, to kai ka ji sai ka gane ka fita
harkarta tun da ba ta ra'ayinka.
Zuciya ta kawo shi wuya ya fusata bayan da ya
kawo mata wawan mari sai dai ko kafin ya ankara tuni har
ta gama wanke mishi fuska har kashi biyu. Baki ya saki
haaaaa kamar wani soko, wanda tsabar takaici da bakin ciki
ya mai da shi haka har ma yake jin cewa kila jinin jikinshi
ya riga ya gama sandarewa har ba ya tunanin sake motsa
42
ga6ban jikinsa, wannan shi ne kashedi na karshe, idan ka kiyaye ka taimaki kanka. Da fadin haka ta bi shi da ruwan
lemon da ke hannunta zuwa fuskarsa, ta juya da zummar
tafiya yayin da take jingine da kafadar Tahir, wani irin
wawan raruma ya kawo mata cikin sa'a masu dan hankalin
cikinsu suka rike shi amma duk da hakan hankoro yake na
ya kwace sai zagi da ashare-ashare yake tamkar mutumin
da ya zautu. Ita ko ko a jikinta, wani murmushi ta bi shi da
shi, bayan da suka fice ita da Tahir dinta.
To fa manyan na hannun daman Tahir suka shiga
sowa, dariya har ma da tafi, barin kuma 'yan matan wajen
musamman wadanda suke ciki da shi ciki ko har da
yarinyar da ya bonsa yanzu-yanzun nan, tsakar kansa ta
tsaya tana ta yi mishi dariya, har ma da shegantaka. Ga
Samira ko tun da ta kifa kai a jikin teburin ba ta kara
dagowa ba ranta in ya yi dubu ya baci hakika kawarta ta
gwada haiin rasthin kirki, ba ta taßa sanin tunaninta ragagge
ba ne irin yau, har yaushe za ka tijara dan'adam irin haka,
shi kansa Samir din sandarewa ya yi a kujerar da yake
zaune sakamakon kaskancin da aka gwadawa abokinshi.
Karon farko ke nan da ya ji tsanar yarinyar, kai ko 'yar
uban wace ce sai sun yi maganinta.
Tun bayan rabuwarsu da Heedaya kai tsaye
mashaya ya wuce domin nuna farin cikinsa kai anya ko
akwai wata rana da ya taba riskar kansa cikin farin ciki
haka? In ma da akwai to ba ko ta kai wannan ranar ba.
Waheed ka shiga tara ka afka tarkona abin da na dade da
buri kodonkai ya zame min dole ma in auri Heedaya. Shin
akwai burin da nake da shi da ya wuce na kuntata maka?
Ya taınbayi kansa duk wanda yake a mashayar a ranar a
43
cikin aljihunsa ya sha saboda mutukar muhimmancin ranar,
ko da yake wani sa'in yakan yi hakan idan ya so nuna
bajintarsa.
A nata 6angaren ta kasa bacci tana jin wani irin
farin ciki da nishadi, takan yi murmushi ta runtse idonta a
duk lokacin da ta hango abin da ya gudana a dazun nan,
musamman wajen da ta wanke mishi fuska, hakika ta yi
bajinta ya ci kuma a yaba mata tun da ta yi nasarar kunyata
shi kai har ma da kaskantar da sankacecen saurayin da yake
mutukar ji da kansa ya kuma saka rayuwarta cikin kunci ba
sidi ba sadada. Da wannan tunani bacci ya dauke ta.
44
<>
bin da Waheed yake fada ke nan ga abekinshi, ya A daga dan yatsansa gami da nuni da shi wallahi
Samir na rantse da sarkin da ya halicce ni sai na
wulakanta rayuwar yarinyar nan za ta yi dakacen abin da ta
yi min nan ba da jimawa ba. Ni Waheed a ka yi wa
wannan? a kuma gurin mutumin da gaba da kiyayya ce a
tsakaninmu? Ya yi kwafa Tahir zan maka illar da ba za ka
taba mancewa da ita rayuwarka ba, za kuma ka gane
kuskurenka a karo na biyu, ni Waheed wane kai Tahir? Ya
ambata hakan da Karfi.
Samir din ya yi shiru be ce komai ba, rashin
kyautawa kam yarinyar ta yi har ma ta wuce mun shairin, to
amma ya ci a ce an manta da komaí an kyale, domin su dai
ba kananun yara ba ne, laifi ne kowa ya yi wa kowa, shi ke
nan kalas!
Kwana daya, biyu, shiru kai har tsawon sati babu
Samira ba ta ko neme ta a waya ba, idan kuma ta neme ta a
layi sam ba ta dagawa, matar da ba sa iya kwanaki biyu ba
tare da daya ya ziyarei daya ba. Daga office gidansu ta
wuce.
Ta yi sa'a ta same ta domin ita mahaifinta ya ki
lamince mata yin aiki ba tare da ta fitar da mijin aure ba,
abin da kuma ya gagare ta, ba wai dan babu samarin ba a'a
illa dai sangartar da ta tashi cikinsa a tunaninta aure ba
komai ba ne face takura da tsangwama.
Sun gaisa da maman Saınira Haj. Maryam, amma
daga nan ta huce fakin mutuniyar tata, kai ta dago ta dube
45
ta sai kawai ta mayar da dubanta ga abin da take, hannu ta
sa ta kwace magazine din da ke hannunta meye wani za kı
wani kallę ni ki basar? Sakar min takardata, dan Allah
Samiran ta fada fuskarta a daure, ba zan sakar miki ba sai
kin fada min abinda na yi miki kike sha min kunu haka.
Ta dube ta ta kara dubanta, sai kuma ta ja tsaki, kin
ba ni mamaki Heedaya sam ban taba sanin za ki iya cin
zarafin n n haka ba, haba me ya sa kikai wa mutumin
nan hakа.
Harara ta sakar mata, makure ni sai in gaya miki
dalili tun da ba ki da masaniyar hakan. Ta fara magana
cikin fada-fada aikin banza kawai ą kan wannan banzan
mutumin har za ki dinga 6ata rai kina wani share ni, ko ma
dai me za ki ce na ji dai na kuma fada na kuma kara ba ki
kyauta ba, ba kuma ki nuna halin kirki ba.
Karya kwana ta yi da niyyar fita, ni na tafi amma
kuma kafin nan ina shaida miki ki je ki nemo kuma ki
binciko duk inda mutumin nan yake sai ki so shi kuma ki
aure shi, shi ke nan ko?
Hankalinta a tashe ta shigo falon rungume da
mardiya, gaba dayansu hankalinsu ya dawo kanta, Alhajin
ne ya fara magana lafiya Na'ima?" me ke faruwa ne cikin
muryar kuka ta ce Dady (kamar yadda sauran 'ya'yanta
suke fada masa) mardiyya za ta mutu taimake ni don Allah
suma take, da sauri Haj. Kaltum ta yo kanta ko kafin ta iso
ma tuni su Heedaya da 'yan uwanta sun yo kanta.
Mardiyya, mardiyya, me ya same ki? Ta fada a lokacin da
ta karbe ta daga hannun Na'ima. Babu alamun numfashi a
tare da ita. Cikin matsanancin hanzari ta zari key din mota
ko kafin a yi wani abu tuni ta fice