An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
ME GAR
YA WWAYG
ZALNAE KABIR BIROMAN
MRS SUNIŞU BRISCOE)
Sadiya Mukhtar Chairıman
Asına'u Mukhtar Chairman
GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI GA:
Fatima Aminu Baba (HAKA YA ISA)
Allah ya bar zumunci, ya kuma albarkanci zuri'a, amin.
GARGADI
Ban yi wannan littafi domin wani ko wata ba, ban
kuma ba da izinin amfani da slii ta kowacce siga ba batare
da izinin marubuciyar ba.
BUGAWA A NAʼURA
Mubarak Ahmad Kurawa
Yolawa Computers&Communications
Email: almubrak@yahoo.com
G.S.M: 08032929831
4
MAFARIN RIKICI
ammacin ranar Asabar garin ya yi kyawu babu Y
alamun zafi sai ni'imtacciyar iska da ke kadawa niai fauke da ni'imtaccen kamshi sakamakon korayen ganyayyaki da furrai da suka lullube zagayen unguwar ta masu fada a ji, unguwa mafi kyawu a duk cikin birnin na Dabo (Nassarawa G.R.A). Dan’adam zai kasance mai godewa Sarki. Allah a bisa wannan ni'ima da ya yi ımasa, alhalin a wasu kasashen ko kwayar gero ba ta iya tsirowa a
Rasa
t od iSannu a hankali motoci ne ke shigewa cikin lumana da kwanciyar rai, yanayin motocin da ke sakaraftu a kan shimfidadden titin kana kyakkyawa da ko a kasar turarai
nisai haka shi zai dada tabbatar maka da cewa ba fa unguwa
ce ta Ya-Ku-Bayi ba. A dai-dai junction (mahada) din in Ahmadu, Bello Way bayan an shige shataletalen Daula Hotel titin da zai sadar da kai har zuwa Tukur Road daga
nan har Abbas Road, wata kyakkyawar mota ne fauke da Rofa daya mazaunin ma na mutum biyu ne kawai, motar da nigalibin matasan Turawa ne ke amfani da ita ta kunno kai, ilahirin glasses din motar masu duhu ainun a kulle suke.
tk ,mo !dai-dai lokacin da. motar take kokarin karya kwana daga Ahmadu Bello Way zuwa Tukur Road a dai- dai kumay lokacin ne wata rantsattsiyar mota kirar m.Meroedesc 230), motar da akasari matasan 'yan mata yа yаn masu fada a ji suke kece raini da ita. Ta kuno kai Alaga, Tukur Road har suna shirin tawo mu gama da motar
5
da ta bullo daga Ahmadu Bello Way sakamakon gudun da
kowannensu yake yı, ya zamanto ba za su iya shigewa a
lokaci guda ba ke nan. Tilas sai daya ya budawa daya
amma hakan ta faskara. Tsawon minti biyar motocin biyu
sun kasa budawa junansu.
Abdulwaheed da ke cikin daya motar da ta fara
isowa wajen shi ke rike da akalar motar, dogon tsaki ya ja
gani da waiwayar abokinshi, wai shin wane me takamar
banza ne haka ya tsare mana hanya ne? Samir da ke gefe ya
dube shi shi ma gami da dan jan tsaki, Ni ma tunanin da
nake yi ke nan Waheed. Waigawa ya dan yi gami da duban
hanyar. lallai ma ko waye ma ya kwaso wa kansa jidali, za
mu kauce mu ba shi hanya ne alhalin mu ke bisa ka'ida?
(wato su suka riga shi isowa wajen). A'a kila dai ko ma
waye ke jan akalar motar yana da tawaya a idanunshi ne
cewar Wahced. Koma waye? Ko dai ko dai wace ce?" da
gani ba tambaya ka san motar mata ce, kila ma ta irin
tsagerun yaran nan masu jiji da kai da fangimar tsiya.
Tsakin ya kara ja gani da tabe baki ai ko ma wacece ni
babu abin da ya shalle ni, zan kuma nuna mata kuskuranta,
mutukar ba ta kauce ta ba mu hanya ba.
A can dayamotar 'yar kyakkyawar matashiyar kana
sarauniyar kyau (Quecn of Beauty) kamar yadda akasarin
friends dinta kan kira ta, ta cika ta yi fam tare hanyar da
take ganin an yi musu sautin kida ne ke tashi a motar kaset
din Tony Branton cikin wakarsa ta "Look 4 Me'.
Ta kai hannu ta rage sautin radio (volume) sannan
ta gyara zamanta a jikin kujerar gami da kishingida bayan
da take bin sautin wakar sannu a hankali, sameera dake
gefenta ta dube ta sannan kuma ta mai da dubanta izuwa
6
daya motar gayu na tsiyarsu a garini nan, ji fa iskancin da mai motar can ya yi mana. Ba tare da ta dube ta ba ta shiga ba ta amsa, shi ya sa ni ma zan gwada mishi ni dai-dai da shi ce. Ta ci gaba da jin sautinta ba tare da ta kara cewa
komai ba. Tsawon lokaci babu wanda ya yi kokarin kaucewa wani, ta fakaici idonta ta danna ham din motar har kashi uku. Samir ne ya sa hannu ya mayar musu da
martanin hakan, ya lura da kyau ba su da niyyar kauce
musu ya dube shi da Allah kau ce ka ba su hanya su shige kada su 6ata mana lokaci a banza, wani kallo ya sakar
mishi sai ka bari yayin da sitiyarin motar ya dawo
hannunka ka janye musun, tun da ka amince wa zuciyarka
mata ka yowa rakiya duniyar, ya harare shi ba na son cin fuska, sanin kanka ne babu yarinyar da ta isa na jera da ita balle har na zamanto dan rakiyarta. Abu daya dai da nake
so ka gane kuma ka san hakan, ba na wasa da lokacin da
duk na san wata karuwa za ta same ni, don haka yanzu haka lokaci ne da yake da matukar muhimmanci a
rayuwata, kauce ka ba su hanya dan Allah in ba so kake ka
cuce mu ka yi mana sanadin da za mu yi missing makudan dollars din da suke shirin shigo mana ba, tun da kai na lura da kyau ba sa gabanka, sau tari ka kan yi wasa da damarka. Ya dube shi ka san Allah ko nawa ne za mus amu na
gwammace wa asararsu da dai in kaucewa mamallakiyyar
motar da ta gwada min gadara da isa, ya dada nutsewa cikin kujera, Samir ya dube shi yana dan gunaguni dole ma
mu kauce mu ba su hanya in har su ba suba mun ba a kan
me za ka cuce ni? Wata da watanni muna neman kwangilar nan takuma samu shi ne za mu yi wasa da damarmu? Sanin kanka ne ketare lokacin da aka diba mana ka iya sawa mu
7
kasa ganawa da Director wanda hakan ke nufin mun saki
damarmu, a Jalilin me za ka cuce ni? Ya buda kofar gami
da fita yayin da shi kuma ya bi shi da harara banza mayen
kudi son kudi kamar tsohuwar karuwa.
Ya ja ya tsaya gami da knocking glass din motar
duk da cewa ba a iya ganin na ciki. Barrister Hecdayat ta
daga kai ta dube shi gami da kau da kai, Sameera ce ta yi
kokarin fita dan jin bahasin tsare musu hanya da aka yi.
fuskarshidaure gami da yi mata kallon raini ya ce meye
hujjarku na tsare mana hanya? Ta bi shi da irin duban raini,
may be kanka ya dace ka yi wa wannan tambaya, amma dai
bari in ba ka amsa, hujjarmu be wuce cewa mu mun isa har
ma mun wuce kaucewa wani Guy ba ko shi wanene. Haka
kika ce? Kwarai kuwa. Ta ba shi amsa. Tsawon lokaci suna
ce-ce-ku-се.
Waheed da ke mota duk haushin abokin nashi ya
kama shi, dan menene zai tsaya kankanuwar yarinya tana
bata musu lokaci haka? ya ja dogon tskai gami da ficewa
daga motar cikin fusata ko 'yar uban wanene za ta gane
kuranta. A cikin motar take ranta in ya yi dubu ya baci ta
hasala ta fusata da wannan wulakanci ko kuma gadarar da
ake gwada musu. Babar damuwarta be wuce batawa
sauravinta lokaci da za ta yi ba, a dai-dai wannan lokaci
suna hanyarsu ta zuwa Birthday partyi na fricnd dinta kana
budurwar babban abokin amsoyinta. Duk kokarin da za ta
vi na ta same shi a layi ta rasa samunsa completely wayar ta
Ki shiga tabbatar network problem.
Dauke da kallon ke ba ki isa ja da ni ba ya dube ta
ya kuına dubi motar ya dai fahimta ba ita ke jan motar ba,
ya kara yi mata kallon nan dai na raini, zai yi kyau ki
8
shawarci uwar gijiyarki ta ba mu hanya, domin ke na
fahimta matsayinki be wuce na rike mata jaka ba ko?" ta
galla mishi harara gami da jin dacin maganar shi. Ya gyara tsayuwarshi bayan da ya zira hannayenshi a aljihu ya yi irin
tsayuwar nan ta isa da gadara sannan ya dan kwankwasa
gilass din dai-dai saitin Driver, hankalinta ya dawo gare
shi ta kalle shi tsaf sama da kasa a zahirin gaskiya ba ta
taba ji m,o ganin matashin da tsarinshi ya yi mata ba
irinshi, sanye yake cikin English wears irin nasu na 'ya'yan
masu da shi kayan sun mutukar tsari da jikinshi tamkar
domin shi aka saka kayan. To sai dai fa duk wannan ba ya
gabanta ta ma ture shi gefe guda a memakon hakan sai ta
riski kanta da jin tsanarsa, sakamakon gadarar da yake
shirin gwada musu.
Cike da jin kai ta fito daga ickin motar, a duk iya
gane-ganensa da bibiyar 'yan mata da ya zamanto sana'arsu
be taba katari da kyakkyawar yarinya me kyawun fuska har
zuwa gangar jikinta irin wannan ba, dole ne ma ta yi jin kai
da isa, ya ayyana hakan a ransa. Sanye take cikin French
lace da ya amsa sunansa wato original din dan yadi daya
naira dubu goma zani da riga me dogon hannu, (buba)
kanta babu kallabi bare gyale sai fa uban gyaran da gashịn
ya sha, wanda ya yi mutukar kara fito da kyawunta.
fankwalin lace din ne ta yafa shi a gefen kafadarta yayin
da kunne da wuya har ma da kafafunta shake suke da
danyen gwal da babu sirki a cikinsa, kirar kasar Dubai a
kafafunta hill shoe ne da ya kara fito da tsarin kwalliyarta.
Ta dube shi ta kuma dubi abokinshi cikin kallon
raini a kan menene za a tare mana hanya? Ta fada cikin
daure fuska. Ya dube ta ya kara dubanta cikin kallon da ya
9
fi nata, ke ba ki kai ko matsayin da za a mayar miki da
amsar tambayarki ba. Samir fin ne ya karashe mishi da
cewa kuma ku yi kokarin janye motar nan cikin lokaci
Kankani. Ini ba haka ba fa? ta fada cikin tsiwa. Za ki gane
kuranki shi ma Waheed ya mayar mata.
Ji nan malam mun fi karfin mu tsaya ce-ce-ku-ce da
ku dan haka ku kauce ku ba mu hanya cewar sameera.
Ai na zaci ke 'yar rikon jaka ce babu da abin da za
ki iya tabukawa, ban sani ba ba haka ba ne ko ma menene
dai ba a gabana yake ba so ku kauce ku ba mu hanya ina
fatan kun gane.
Ya matso gab da gab da ita ku janye motarku tun
kan GARI YA WAYE MUKU. Ya waye mana har ma dare
ya yi mana, in dai har a kan in kauce muku ne never,
wallahi ba ku kai haka ba, kai ba ku isa komai ba ma. Ta
fada cikin daga murya.
"Ke wace ce? Wace ce ke? Ke 'yar uban wane ne za
ki zo kina gwada mini wannan gadarar?. "
"Ubana ya fi karfin a ce wanene? Ban san ba ko
naka?" ya fusata ya kawo mata mari ya kuma kawo mata
marin ya yi sa'a duk ya same ta. Cike da mamaki ta dafe
kuncinta ta kuma dafe kuncinta sannan ta kawo mishi mari
ko kafin ta kai tuni ya rike hannunta ya matse shi da karfin
gaske ya shiga nuni da yatsa, da kin sake hannunki ya isa
kuncina wallahi yau da kin gane kuskurenki, da kuma na
nuna miki ke karamar mara kunya ce.' Ya yi facali da
hannunta, ta zuciya ta kara kawo mishimarin, cikin sauri
sameera tayi saurin rike ta, yayin da shi ma Samir yake
kokarin rike shi, kan kace kwabo jama'a sun taru ana rabon
fada zaginsa take tana fadin ko shi dan uban wanene a yau
10
din nan sai ya ga kaskanci me tarin yawa, za ta ga gatanshi, za a ga mutumin da zai iya kwatarsa.
Shi dinma ban da an rike shi nufin dukanta yake waje yakacame da hargowa, yayin da go slow ya cika titin,
w da duk sun tsare hanya, kowannensu kuma ya nace ya kafe ba zai janye motarsa ba, to fa yau fa ake yin ta ilahirin
motocin da ke kan titin an saka su cikin halin ka-ka-ni-kayi babu dan ar gaba bare ja da baya.
Police station da ke gundumar wajen nan da nan
reporting ya iso musu ba bata lokaci suka garzayo da nufin
sasantawa amma kuma daga Waheed din har Heedayan sun
dau alwashin duk wanda ya taba musu mota zai gane
kuskuransa. Nambar motocin kawai suka gani suka shiga taitayinsu, fadan na manyansu ne, lallai kam matasan ba banza ba suka kafe kai da ka ji ka san akwai abin da kowannensu ya taka. Idan ka ji ana fa dan manyan giwaye
me iya shiga tsakani sai ko zaki da zakanya uwayen gijin naımin dawa.
Abu wasa-wasa ya dauke su har tsawonsa'a guda,
kowannensu ya kafe kan ra'ayinsa yayinda aka dau hakkin jama'ar da ke kokarin shigewa amma kuma babu damar hakan. Wani tunani ne ya fado mi shi nan da nan ya matsa
nambobin Dad din Waheed domin shi kadai ne zai iya kashe rikicin, ita ma wannan tunanin ne ya fadomata cikin kanknain lokaci ta lalubi nambar Momyn Heedaya tunda ta san dad din ba ya kasar.
Motocin gidajen biyu ne suka iso a lokaci guda a
lokacin gudan ne kuma suka janye motocin da ake rikici a
kansu. Bayan da kowannensu magabatansa suka sa aka yi
awon gaba da shi.
11
Da isarta gida ta ci karo da Aunty Na'ima kishiyar
mahaifiyarta, ta dube ta Heedaya lafiya dai?" ganin aydda
take a hargitse wani irin kallo ta yi mata sai kuma ta ja tsaki
ta shige abinta, kallon dai take bin ta da shi, kai wannan
rashin tarbiyya har ina? matar ubanka kake wa wannan
duba.
Fadawa ta yi kan mamanta sai kuma kuka ya biyo
baya, wallahi yau Momy wani mutum ya gwada mini
kaskanci, idan dai har ina da gata a wajenku ya zama dole a
nuna mishi iyakarshi, wai menene ya hada ku ne
Heedaya?" Tiryan-tiryan ta labarta mata. Baki ta rike ya
mare ki? Lallai kam zai ci kaniyarshi, yaron banza kawai, a
kan me zai kama diyata ya buga?" A na me?" Zai gane
kuskuransa kuwa. Bari Dadinku ya dawo ina sa ran zuwan
nashi daga yau zuwa gobe.
Ta dada narke mata yayin da ita kuma take ci gaba
da sababin fada, dakata malam. Waheed ya umarci direban
da ya tsaya dakata na ce, ya fada da karfi cikin fusata,
Malam Mudi direban mahaifinshi wanda a haife ya haife
shi har ma jika ya yi da shi. Ya ja ya tsaya fice kawai je ka
abinka zan karaso da kaina. Ya dube shi cike da ladabi ya
shiga fadin ranka ya dade Alhaji ne ya umarce nina dauke
ka na kaika gida. Ya gargade ni kar na sake na bar ka. To ai
ka rabo ni da wajen sai ka kama gabanka ka san dai ni ba
yaro ba ne da sai an yi min jagora zuwa gida. Ala huci
zuciyarka ranka ya dade, ya fada gami da mika mishi
mukullun motar.
Kai tsaye guest house suka shige, tsaki ya yi ya
zauna gami da ciza lebe na jin haushin kansa na sakacin da
ya riga ya yi, da bai tumurmusa yarinyar ba, ga Samir kuwa
12
ranshi in ya yi dubu ya faci sakamakon asarar da ya ja
musu suna ji sunagani, sun saki wannan dama tasu kai ya
cuce su. Banza kа cuce mu a kan wani dalili kankani, Allah
ya isana. Ya kalle shi yana harararshi na cuce ka ko ka cuce
ni da ka hana na lallasa mara kunyar yarinyar nan a kan son
kudinka na banza? Mu yi mu tafi kada mu rasa kwangila
ko? Key din motar ya dauka ya fice yana 'yan
gunaguninshi na ta leko ta komar da abokinshi ya jaza
musu.
Zaune yake gaban mahaifinshi yana mi shi fadan
sakarcinsa, "Ban da ma kai sakaraine har yaushe za ka
tsaya fada da mace, macen ma da watakila ba ta fi sa'ar
kanwarka ba, ni na rasa san da za ka yi hankali
Abdulwaheed? Sunkui da kai ya yi Dadi ka bar ganin lefina
wallahi yarinyar ce ba ta da kunya, haka kawai ta ja ta tsare
min hanya, alhalin ni na riga ta isa wajen, to sai menene?
Ba sai ka kauce mata ba faduwa ka yi idan ka yi hakan?"
ya fan 6ata fuska Dad..... zai ce wani abu ya datse shi ya
ishe ni bana son jin wani abu daga gare ka. Abin da kawai
zan ce maka, ya kamata ka hada hankalinka ka san ka riga
ka girma, har ma ka isa yi wa wasu fada, dan haka ne ma
nake dada tunasar da kai akan maganar aurenka na gaji da
ganin sa ban ga kaho ba, ya dan shafa keya yana
murınushi, ka yi hakuri Dad komai lokaci ne, lokaci ne
haka ne amıma kuma kai ka ki ka sa lokaci saboda kawai ka
sa kanka a shashanci. Ya dago kai da niyyar magana, yi
shiru kar ka yi min wata magana ko kana nufin ban san
halin da kake ciki ba ne? na kyale ka ne idan tura ta kai
bango zan yi maganinka. 13
Kamar ko yaushe ya dawo kasar cikin iyalinsa cike
da nishiadi Haj. Kaltume ke gefenshi cikin isa da kasaita
yayin da ta hannun daman nashi, ya ma fi soyuwa a cikin
'ya'yanshi ke gefen hannund amanshi ragowar yaran gidan
kuwa suna warwatsc a falon tare da nuna farin cikin ganin
mahaifinsu. Aunty Na'ima kuwa abokiyar zaman Hajiyan
tana takure a gefen kujerar kuryar dakin ya rabawa kowa
tsarabarshi kamar ko yaushe dai tsarabar 'yar gata Heedaya
ta fifita, ya lura da kyau wannan karon ba ta murna da
dokin zuwan nashi, ummina menene ya same ki ne' wa ya
taba min ummina ne? ta 6ata rai Dad ba na sheda maka ba
tun a waya na gani ne ka zo sam ba ka dauki wani mataki a
kai ba. ya buda baki ah..., lallai kam shi kam wannan waye
ya dakar mini ummi?
Dady ni daiį kawai ina so ka sa a kama mutumin nan
a nuna masa iyakarsa. A'ah ummi baa yi haka ba, ki dan
bari zan ja kunnanshi, wai a ina yake? Dady ka san ko abin
da ya yi min, mari fa Dady, ko ma menene a dai yi hakuri
ummi. Haj. Kaltum ta katse shi a'a Alhaji a na me zai bugar
nin yarinya a kyale shi? ai ya kamata a nunamishi
kuskurensa. Ya yi murmushi, Kaltum ke nan ke kam wani
sa'in kikan mance da shekarunki har ma ki kam biye wa
diyar taki, ai babba da tsinkaye a ka san shi.
Hajiya hakurin dai za a yi. Cewar Aunty Na'ima.
Wani banzan kallo ta watso nata, me dauke da sakon ke fa
ba komai ba ce sannan ta ce, "Ina jin dai a maganar nan dai
ba a sako da ke ba ko?" cewar Hajiyan. Kai ta daga mata,
to dan haka sai ki iya bakinki. Daga hakan ba ta kuma cewa
komai ba ta ja bakinta ta rufe domin dai wannan abu ba
bakon abu ba ne a gurinta, yara san babu tarbiyya sai abin
14
da suke so suke yi, ka fadi gaskiya a ga zafinka. To da kyar dai Alhajin ya iya shawo kanta. Misalin karfe hudu na yammaci Tahir El-Hussein
ya iso cikin motarsa Hammer Jeep, kamar ko yaushe ya
neme ta a layinta ya sheda mata isowarsa, ta san da zuwan nashi dan haka tuni ta gama kintsawa cikinleshin kasar Esphania (Spanish Lace) me matukar tsada ta yi kyau ainun ita kanta ta san hakan ba al'adarta ba ce sa ka mayafi don haka sai ta yafo shi a gefen kafadunta irin dai na 'yan
matan zamani, ta bi ilahirin jikinta ta feshe da (palona
picas). Sai kuma ta ja ta tsaya cak, sakamakon tunano karyar da za ta yi mishi ba zai yiwu ta bayyana mishi abin
da ya hana ta zuwa Birthday Party ba.
Saboda sanin zafin da yake da shi da kuma dan
banzan kishi, kila ma abin ya juye kanta ba ta mancewa
daga yamımacin jiyan har zuwa dare yana ta kiranta a waya
amıma kuma sam ta ki dauka, saboda 6acin ran da take ciki,
sam ba ta son bacin ranshi wanda muddin ya sani dole ne
ma ta harzuko shi har ma ya shiga cikin damuwa ita dai kam tana son Tahir dinta so mara iyaka.
Kwankwasa gilashin motar ta yi sannan ta ja ta
tsaya domin ba ka iya hango na cikin motar saboda duhun gilashin. Kare mata kallo ya yi sama da kasa ta ko ina Heedayanshi ta hadu tana da kyau mai ban mamaki kai a
tunaninshi ta zarce kowace mace a iya ganinshi. Ya bude murfin motar yana mai murmushi bayan da ya miko hahnunsa, harararsa ta yi gami da ba shi hanya ya fito fuskarshi dauke da annuri, suka jera zuwa Kayataccen lambun gidan (Garden) kamar yadda suka saba zama a
15
cikinsa, a duk lokacin da ya zo gurinta ya dube ta yana mai
kashe mata zuciya.
Heedaya kin sani cikin damuwa completely daren
jiya, nakasa bacci na yi kiran wayarki kin ki fagawa why?
Why Heedaya?" kin sani cikin damuwa Halisa kawarki da
shi kansa failsa din wallahi sam lamarin be yi kyau ba, kin
sani cikin damuwa kwarai da gaske.
Ta dafe kai Tahir kai min afuwa na san ban kyauta
ba amma akwai uzurin da ya hana ni zuw?. Menene shi
kuwa? Ashe akwai abinda ya fi ni muhimmanci a gurinki?
Ba haka ba ne Tahir. Haka ne mana na gode kawai daman
dai kin yi niyyar gwada min iyakata ne. haba Tahir me ya
sa kake fadar haka dan Allah ka bari kada ka sani
cikindamuwa please... Tahir don't hurry.
Ya harare ta cikin sigar so muddun kina so na
hakura sai kin min wani abu guda, menene? Ta fada da
sauri. Yauwa to zo ki ga da sauri ta kufce na ki wayon ta
fada tana dariya. Ya dada tamke fuska shi ke nan je ki
kawai ba tun yau ba na riga na soma fahimtar matsayina a
wurinki, ya mike da niyyar tashi, dakatar da shi ta yi, Kа
fahimce ni tahir ba haka ba ne.
Ta dan harare shi dole man ka ce hakan bayan da ka
sanı yin abin da ba na ra'ayi., Heedaya... ya ambata hakan
cikinwani irin salo ya ci gaba kin san ina kaunarki ina yi
miki wani irin so da ni kaina ban san adadinsa ba so why?
Dan na gawda kaunata a gare ki za ki dinga ganin laifina?
Ina sonki Heedaya son da baki ba zai iya fafarsa ba, kin
kasance tauraruwa a cikin dubban taurari kowace mace ba a
gabana take ba komai kyawunta komai matsayinta, ni dai
na sani na kuma sheda Heedaya na kadai nake so.
16
Da irin wafannan zantuttuka ya kashe mata jiki har
ma ta kasa katabus, ko dayake a yawancin lokuta ta kan
kasa bijirewa umarninsa saboda tsananin kaunar da take
mishi.
***** ***** *****
idaya Sa'ad Mohd, 'ya ce gurin Ambassador