mata
rafar kud sababbi dal 'yan dubu rafa
biyu yace, "Ga wannnan dubu dari biyu
ki fara rikewa ko ince ki fara dasu, idan
naga kin yi serious akan kasuwancin sai
in kara miki wasu.
Ta amshi kudin ta rungumje shi
tana murna táre Da vi masa Godiva
yace, "Muneeba ma zan bata amma ba
yau ba don hakan shine adalci. Mota
kuma zan saya mukun tare in yaso sai
ta kayautar da waccan tsohuwar.
161
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Ba haka Suwaiban ta so ba ta so
ne ya saya mata ita kadai in yaso
Muneeba ta ci gaba da hawa tsohuwar
tata, ba ta san har yanzu soyayyar
Muneeba na nan zaune dirshan a
zuciyarsa ba.
Da rana Muneeba na kicin dinta
tana hada abinci me gidan sai waleeda
ta shigo dauke da ledar nan ta leshin da
ta aika wa Suwaiban, ta zo tana mika
wa Muneeba.
Ta amsa tana cewa,"Hala antinki
bata kusa ne kika dauko kayan nan, kin
ganki da barna."
Ta duba cikin ledar lesunar 'ne
guda biyu sai rafar kudl dauri biyu
wadanda Mujeeb ya ba Suwaiban da
safe.
Ita da Kanta ta ba waleeda ta ce
maza ki kaiwa mama tavi haka ne don
Muneeba ta ga kudin da leshin ta san
cewa ita ma yanzu miji ya dawo
hannunta, ba ta san Munneba ta riga ta
ganin leshin ba, kudin 'ne dai ta yi
mamakinsa don ta san tabbas daga
162
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
J
gurin Mujeeb suka fito don ga kamshin
turarensa nan manne a jikin kudin,
sannan ga sunan bankin da yakc ajiya
nan rubuce a jikin takardar da ta yi rafin
din kudin, kenan shin ya ba Suwaiba
kudin.
Ita kanta Suwaiba ta san kudin
da kayan ba za su salwanta ba saboda
Muneeba mutum ce sak ta kwarai shi
yasa har ta iya ba waleeda ledar ita
kuwa ta tabbata da hannunta kayan
Muneeba da kudinnan suka zo to ruwa
da iska ba zata maido su ba cewa zata
yi bata gani ba kuma dole a hakura a
hakan.
Muneeba ta bar abin da take yi ta
riko hannun Waleedda daya hannun ta
riko ledar kayan tayi sallama ta shiga
dakin suwaiba, dama suwaiban na tsaye
ta window tana leken waleeda tun
shigowarta har fitowarsu, da ta ga zasu
shigo shine tayi saurin komawa bisa
kujera ta zauna ta ci gaba da kallon da
ta kunna.
163
WATA KUSAN 4
Rahmatu Hassan Zaria
Muneeba ta mika mata ledar nan
tace, "Hala ba kya kusa ne Waleeda ta
fita da ledar nan? Ta rike ledar tare da
sauke ajiyar zuciya tace, "Kai kai lallai
yarinyar nan sai na buge ki, ina can na
shiga bayi bisa gado ta dauko ta kuma
har da kudI masu yawa a ciki, tabdijam
ai da kin fita dasu wani ya kwace da
دو
babanki dole ya sake bani wasu.'
Munceba ta suri Walceda tana
murmushi tace, "Sai dai kam ya sake
baki wasu, amma ba zaki dukar mana
ita ba, ko ni ina baki nawa sai inci
girma nan gaba a bani.
Munceba ta fadI hakanne don
Suwaiban ta san ba ita kadai aka ba
kayan ba in ma ta yi hakan ne don bata
haushi to ba ta isa ba taga hushinta ba.
Suka fice da walecdar suka barta
cikin zurtin tunnai, "Lallai namiji ashe
munafiki ne ashe dukkan su ta saya
musu kudinnan kila ya bata shi da yace
ba yau zai bata ba, lallai sai ta canza
wata salon takun sabuwar kisisina a
gidan nan in ba haka ba matar nan sai
164
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
dai tayi ta bata haushi a madadin ita ta
bata.
**** ***** ****
Suwaiba kam ta sami kan miji irin
yadda ta ke so yana yi mata sai dai duk
abin da zai bata gurin bokaye take
kaiwa da sayen magungunan mata suke
karewa, bata jin kyashin kashe ko nawa
ne ta saya kuma ta fi gane ta sayi
wanda za ta tura a gabanta, a ganinta ya
fi yi mata aiki cikin gaggawa.
Don ko kudin da ya bata ta fara
yin jari, bata yi ba dubu dari ta ba
Aina'u aka kawo mata dan china
kwalba biyu.
Munecba idanu ta kawo ta zuba
musu shi da Suwaiban, farin cikin ta
daya yadda bai juya mata baya ba ita da
'ya'yanta yana sonsu fiye da komai,
yana mata hidima ita da su dan basu
rasa komai ba, illa ita da take hadiyar
abubuwan da yake yi mata duk ranar da
aka ce Suwaiba ce da girki to ya din
rawar jiki kenan yana nan da Suwaiban
165
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
C
sam baya son ya ga ta bata rai yanzu sai
ya susuce yayi ta lallashinta ita kuma
tana dada botsare masa.
Babbar matsalarma yadda sam ba
ya nuna mata zumudin kasancewa da
ita, wani lokacin ma sai yayi fiye da
sati biyu bai yi auratayya da ita ba
alhalin tana kallonsa yadda yake rawar
jiki da Suwaiba har dawowa yake da
rana idan abin ya ciyo shi.
Duk ta kawo idanunta zuba masa
bata taba yi masa korafi ba, hatta ita
Suwaiban ta rasa yadda aka yi
Muneeban bata nuna jin zafinta, ko a
jikinta sabgar gabanta kawai take yi.
Maganar fara aikinta dama
Mujeeb yace sai ta yaye su Hilal to
Allah cikin ikonsa tun kafin su shekara
suka fara tafiya shi yasa suna cika
shekara ya yaye su.
A lokacin ne takardar daukanta
aiki ta fito, aka dauke ta aiki ta fara
zuwa sai tana barinsu Bilal gurin Baba
Hajjo fita aikin da take yi ne yake rage
166
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
mata radadin wasu abubuwa da ke
faruwa a gidan nasu.
Ko ba komai tana samun natsuwa
bisa 'ga irin tsananin kauna da Mujeeb
ke nunawa yaranta ta yadda ko gida ya
dawo ba ya iya shiga dakinsa in ba ya
gansu ba, har hakan na kunada zuciyar
Suwaiba wani lokacin sannan gashi
Kiri-kiri Waleeda ta gujeta ta koma dakin muneeba saboda su Hilal don ko
bacci tayi idan ta farka ta ganta a dakin
Suwaiba ta dinga ihu kenan ko mai dare
sai an kaita dakin Muneeba.
A wannan lokacin ne za'ayi bikin
Isah, ya kamala karatunsa na digiri har
Mujeeb ya sama masa aiki a nan
Gombe, kasancewar matar da zai aura
iyayenta 'yar asalin Dukku ne su ma
aiki ne ya kawo su Gombe kuma
Dukku za'a daura auren suyi shagalin
biki a can sannnan a kawo amarya
Gombe gidan da Mujeeb ya saya musu,
shi yasa Mujeeb ya saya musu, shi yasa
Mujceb yace aje can Dukku bikin idan
167
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
aka kawo amarya sai a dawo a karasa
bikin a Gombe.
Ranar alhamis Suwaiba suka
wuce Dukku ita da yaran duka tare da
mai girkinsu da karime da kuma Baba
Hajjo, ita kuma Muneeba zata biyo su
washe gari ranar Jumna'a idan ta tashi
daga aiki tare da Mujeeb za su taho don
shima sai Juma'ar zai tafi.
Wani katafaren gida Mujeeb ya
gina musu a Dukku mai dauke da
bangarori manya guda uku nasa daya
na Muneeba daya na Suwaiba sai na
Goggo a can karshen gidan hade da na
saukar baki.
Baba hajjo da karime suka bude
bangaren Munecba suka shiga tare da
su Waleeda.
Ba su zauna ba suka shiga gyaran
gurin har sai da suka ga komai yayi tsaf
sannan suka kunna turarukan wuta ko
ina ya dauke kamshi kamar yadda suka
ga tana yi.
Washe Gari Munccba suka iso
tare da Mujeeb amma kowa a motarsa,
168
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
ita a sabuwar Peugeot 307 shi kuma a
tasa Mercedece C350.
Ta Suwaiba na gida an rufe da
tamfol don har yanzu ta kasa maida
hankali ta koya.
Da yake a satin aka saya musu
motar ba kowa ya sani ba shi yasa 'yan
uwa na ganinta da motar suka soma
taya ta murna har wata cikin dangin su
Mujeeb tace, "Ai Wallahi ilimin zamani
na dadi kuma da naga mai ilmi ya
bambanta da wanda bai yi ba, yanzu
dubi daga fara aikinki har kin sayi mota
inda baki yi iliminba ai sai dai ki kalla
gurin masu ilimi." Muneeba tayi saurin
cewa, bani na saya ba maigidan ne ya
saya mana Suwaiba tata na gida don
bata gama kwarewa bad a itama kunga
tata.
Matar tacc, "oh, kinga ikon Allah
albarkacin kaza har kadangare kan sha
ruwan kasko ke ai kin dade da hawa
mota Allah dai yasa 'ya'yanmu a
danshin ki komai naki acan-acan masha
Allah."
169
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Nan fa Suwaiba ta kullu iya
wuya dama abin ke hana ta shiga cikin
dangin Mujeeb kenan sun dinga yaba
mata maganganu kenan sun fi kaunar
Muneeba saboda saye su da abubuwan
alkhairi da take musu, ita kuma ta sha
alwashin in har sai ta basu abin alkhairi
za su so ta ba tunda mijinta na sonta
babu ruwanta da su.
Duk wani abu na hidimar bikin
nan a hannun Muneeba Mujeeb ya
damka shi, don hatta lefe ita ya ba kudl
yace ta hado masa, da ta nemi rakiyar
Suwaiba don su je kasuwar tare sai
cewa tayi tana da abin da zata yi taje
kawai.
Makullan bangarena na nan
Dukkun duk suna hannunta, anan ne
suka aje abubuwan da za'a bukata na
hidimar bikin, sannan Munceba ma can
ta tare kacokam sabo da Jama'arsu duk
nan gurinta su ke makil.
Takaici bai gama kashe zuciyar
Suwaiba ba, sai da tag a irin suturun da
Muneeba ta dinga sakawa tana fita,
170
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
C
hatta Waleeda sai da Muneeba ta dinka
mata kaya masu tsada kala shida,
lesuna biyu atamfa super guda biyu sai
shaddoji gezna da aka yi musu anko ita
da su Hilal, har da 'yan hulunan dube
aka saya musu yaran sunyi kyau tamkar
ka sure su kagudu don kyaun da suka yi
cikin malum-malum din da aka yi
musu.
Ita kuma Waleeda stone work
aka yi mata a shaddojinta da lesunan, iri daya ne da na Muneeba.
Suwaiba ta ji takaici kwarai don
shawarar su ya nema cewa su zo ya
kaisu shago su zabi duk irin kayan da
ske so sai ita Suwaiban tace a ba kowa
kudinsa ya sayi abun da ya ke so da
yaki yarda sai Muneeba tace yayi
Hakuri ya ba kowa kudin sai su sayi
zabin a ransu ke so.
Dubu dari-dari ya basu yaba
yaron kowa naira dubu ashirin ashirin
na waleeeda ma Muneeba ya ba yace ta
saya mata kaya masu kyau don ta iya
zaben kaya.
171
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Nan ma Suwaiba ta ce ita sam a
bata kudin 'yarta don ta gaji, mulkin
mallaka ake mata kyauta da dan
kishiya.
Muneeba ta mika mata kudin,
yace kuma idan an sayo a kawo masa
na kowa ya gani don ba ya son
karabitin kaya.
Muneeba bata bi ta kanta da taje
kasuwa duk sayayyar da tayi wasu Bilal
tare da waleedan tayi musu bata yi
la'akari da cewa suwaiba ta amshe
kudin sayayyar waleedan ba.
Sai gashi ita suwaiba bata
sayawa Kanta komai ba ball ma
waleedar, tsofafin kaya ta saka haka
waleedan ma dake bangaren Muneeba
tsoffin kaya ta bada tace a saka mata
wai basu sami dinki ba sai telan ya
kawo alhali ta. kai kudaden nasu
sayayyar wajen bokaye.
Sai kawai ta ga Waleeda cikiin
sababbin kaya kuma tsadaddu, duk sai
ta tsargi kanta ta ji ta muzanta har ta ma
kasa hada ido da ko sahu da Muneeba,
172
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
don sai ta zamo tamkar yar aikin
gidan, don 'yan aikin ma sun fita shiga
mai kyau, Muneeba din kuma kala
bibbiyu tayi masu karimen da baba
hajjo da mai girkinsu na cin biki.
Hatta su jume da baba mai gadi
sai da saya musu shaddoji guda bibbiyu
ta basu, tare da kudin dinki shi dai
Mujeeb sai yaji suna gaya masa tare da
yi masa godiya, anan ne ya fahimci
alkahairin da tayi musu.
Suwaiba saboda haushi da bakin
ciki bata bari yamma tayi su bi ayarin
da za'yi na tafiya da amarya ba, sai ta
bi motare da za'a fara wucewa da su
baba hajjo da yara tare da ladiyo, suka
wuce Gombe domin yin girkin da za'a
tarbi jama'a.
Tu da suka koma gida suwaiba
bata sake lekowa waje ba, balle ta baki,
har aka kawo amrya bata fito an tafi da
ita ba saboda tsananin haushin
Muneeba da ta ke ji.
Da su muneeba suka iso ne ta
shigo dakin nata tace ta fito za su je
173
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
gida amarya sai tace su tafi kawai bata
jin dadi. muneeba tace Allah ya
sauwake ta debi jama'a a motarta suka
tafi.
****** ******* ******
Shekar su bilal daya da rabi a lokacinn
muneeba tana dauke da ciki wata biyu
wannan karon tsananin laulayin da
cikin yzo mata dashi ne ya fallasa ta
kowa ya san tana da ciki har Suwaiban
ta san cikin.
Hnkalin suwaiba ya tashi Matuka
ganin har yanzun a wani labarin ciki a
tattare da ita, ballle yadda taga hankalin
Mujeeb gaba daya ya karkata wajen
kula da lafiyar Munceba bashi da wani
sukuni sai tattalin ta.
Wannan karon ma sun sake
fantsama gidan bokaye don su so suke
ko ta halin yaya muneeba ta bar gidan
nan wutsiya zage kuma ko da mutuwa
ce zata zama sanadin sanadiyar barinta
gidan suna maraba ita da hajiyarta.
174
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Suwaiba ta isa gidan kawarta
Aina'u a wata yammaci, sun kule suna
ta neman matsalolin gidan mijinta anan
suwaiba ke tamabayarta ayauawa ina tabilet din nan da kika ce zaki bani
masu kara girman nono don kin san
tunda na yaye waleeda nawa sun koma
kamr kokuma duk sun tamushe dama
knsan básu da girama, ita ko tsinnanniyar har yanga take tana dada
karakada masa su, can yake lalacewa
gurin kallon su tunda ta lura yana
sonsu.
Aina'u ta mike ta bude wadrob
dinta ta dauko tabilet tanacewa, "Aini
autarki nake gani da har kuka zauna da
mace mai dauara zani ta hannun dama
ta fiki da wasu abu wanda kod Allah be
wadata ki dasu ba zaki iya siya a
kasuwa, in farin ne kawai mai in
nonuwan ne akwai kwayoyi har da ne shafawa, in ma kwankwason ne tafi ki
da su to ai duk akwai magungunan da
bature ya kawo masu kara musu girma.
175
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Don Allah dube ni? Da can haka
nake? Ta yi juyi tana girgiza jikinta.
Suwaiba ta girgiza kai ta ce, "Ba haka
kike ba da ke siririya ce ba wata shef
din arziki."
Ta yatsina baki, "Ai dana lura da
cewa mijin mai gane-ganene kuma na
san abubuwa dake jikin mace, shi yasa
na tashi tsaye ban zauna ba na tashi na
siyo sinadaran kara jiki da kuma gyara
su da kuma kara su to ba gashi na dawo
irin macen da yake soba, ai mazan nan
idan kika zauna sai wata ta zaune miki
su.
Kafin suwaiba ta bar gidan sai da
ta bata magunguna na kara nono tare da
maganinta da ta zo karba na China dan
matsi tun ma a gidan Aina'u ta fara
hadiyar na nonon.
Tun daga ranar Suwaiba ta fara
shan maganin sai fa nonuwa suka yi
bula-bula gunin ban sha'awa har sai da
Mujeeb yayi mata magana yake cewa
ko ciki gareta tace bata da komai.
176
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassań Zaria
Muneeba kanta sai da ta dinga
mamakin canzawar jikin na suwaiba ta
cika fam ta yi bul-bul nonuwa sun cika
kirji, kowa ya ganta sai ta bashi
sha'awa, sai muneeba ta dauko ciki
gareta ita ma har take wa Mujeeb tsíyar
ita da suwaiba kila lokaci daya za su
haihu zasu yi masa rubdugu kowa na
jego ya kada baki yace,"To meye idan
kuka haihu lokaci daya? lyaka idan
naga ba zan iya hakuri ba inyo amarya
ku ku je ku ji da jegon ku ni kuma naje
naci amarci dan ma ba zan aje ta gida
daya da ku ba, gida daban zan saya
mata. Munceba tayi shewa ta ce, "Aini
dai zaka birgeni biyu ya kamata ka auro
rana daya kaga biyu na jego biyu na cin
amarci, ka leka nan ka leka canmu har
hutu za mu dauka muei girma mu bar
maka su duk ranar ga gishiri va sallace
akan kaza sai ka neme miu, mu huma
sai mun gasa masa gyada a tafin hannu
idan ka dawo."
Dariya sosai yayi sannan yace,"yi hakuri uwargida sarautan mata
177
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
bata ma da ciki balle tun yanzun ku fara
tunanin yadda za su gasa min gyada a
tafin hannu."
Wata matsala da Suwaiban ta
soma fuskanta shine wani ruwa mai
yaukin da ya ke fito mata ta gabanta
wanda kuma yake da wari da kuma
doyi wanda sam bata iya zama sai tayi
kunzugu da audugar mata in ba haka ba
to duk inda ta zauna sai ya jike, gashi
ruwan na da dan Karen wari duk sai
gurin yayi ta wari.
Idan kuma suka yi tarayya da
Mujeeb gurin azabar zafi yake mata
tamkar zata mutu, haka take ji daurewa
kawai take yi, sannan yana mata
korafin warin da yaji gabanta keyi a
duk lokacin da ya kusance ta.
Sai tana nuna masa ita sam bata
jin warin alhalin ita kanta abin na
damunta har yana son ya fi kartinta.
Abu fa yayi tsanani har sai da ya
kwantar da ita don tafiya ma gagaranta
yake yi. Mujecb ya tsareta da
tambayoyi,"so nake ki gaya mun
178
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
gaskiya me kike sawa a gurin nan ne
yake wari ga kuraje duk sun fito a gurin
ya tsatstsage yayi ja." Ta soma indainda tana hawayen azaba tace, "ni fa
babu abin da nake sawa wannan ciwon
ne kawai." Ya bata rai". "shikenan
tunda ba za ki gaya mun ba in mun je
asibiti su za su gano me ke damunki
kuma zasu gaya mun, kuma zasu gano
ko meye musabbabin ciwon ni kam
bana raba dayan biyu ko ire-iren
magungunan da kike mannawa don ki
mallake nine sakamakon ya fara
bayyana a jikin ki, ko kuma bin
bokayen ki har kina basu tukwuicin
kanki gurin da ya zamto halaliya ga
mijin ki ne ya janyo miki wannan
bala'in, nayi nadama da danasanin sake
amince miki da na yi har na dawo ina
tarayya dake alhalin na san ba za ki iya
daina halinki ba,
Ya daga hannu yana rokon
Allah,"Ya Allah kasa wannan cuta da
ke gabanta bata goga mini ba, in kuma
ta goga mun ya Allah ina rokonka da
이
179
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
kasa ban goga mai baiwarka Muneeba
ba don bata san hawa ba balle sauka
akan wannan ciwon."
Haj. Harira da ta iso ta ga yadda
gaban 'yarta ya koma kuka ta saka
mujeeb yana bata hakuri "kiyi hakuri
Hajiya laifinta ne da ba ta jin magana
tunda na hana ta saye-sayen
magunguna nan gaya mata suna kawo
ciwon daji amma bata ji ba yanzu wa
gari ya waya?
Sannan Suwaiba har boka ta tabа
bashi kanta duk don ta mallake ni, gashi
nan bata yi nasara ba ta sayo wakanta
larurar da na sani.
Haj. Harira ta fitittike
tamkar batasan labarin ba ta cc "Don
kuma lalura ta same ta sai ka hada mata
har da sharri? Suwaiba ce zata je ta ba
boka kanta kai wane algungumin ne ya
gaya maka?
Ya nuna Suwaiba yace, "Babu
algungumin da ya gaya mini, gata nan
da bakinta ta fada har kunnuwa na suka
ji. ki tambaye ta gata nan, a dalilin
180
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
hakan da naji ne har na fadl na karye
aka kaini aibiti.
Suwaiban ta sunkuyar da kai
kasa yin magana Haj. Harira ta hauta da
sababin karya. "kin yi shiru kina ji ana
miki sharri da yaushe haka ta faru?"
Suwaiban ta kallí Hajiyar tata ce,
"Ni fa ki daina min fada alhalin kin san
komai, inma Ce keda Goggonsa ne
kuka kaini gurin bokan har ya yaudare
ni ya biya bukatarsa? Da baku kaini ba
zan je ne? ai duk zunubin da na samu
tare aka raba mana da ku don ku kuke
yi min jagora."
Bakin cikin yasa Mujeeb ya fice
ya bar musu dakin don ba zai iya jin
wannan irin ballake-ballake da suka yi
ba kuma wai duk da uwarsa a ciki.
Haj. Harira ta fita ta nufi' dakin
Goggo Rahin ta same ta a kwance ta
hau bala'I. "Au kenan kina kwance ne
yarinya na can na fama da bala'in
ciwon da har da ke aka yi sanadin da ya
same ta? Eh, lallai duniya ba gaskiya,
sannan ga dankin can ya ta sata gaba da
181
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
fada yanan cewa ai ya hanata wai yanzu
wa gari ya waya.
Goggo ta tashi zaune tana cewa,
"Au ni kike son inje in yi jinyarta? Ai
bani nasa ta zuwa tana sanye sanyen
magunguna a gabanta ba ta na
mannawa dan ta mallake min da ba,
saboda haka kece zaki je ki jinyarta don
ke kika haifi abarki."
Haj. Harira tayi shewa ta tafa
hannuwa tace, "A yau ne zaki ce haka?
Mallakar danki kuma sau nawa aka yi?
Ina ce ke da kanki kika fara ba da kudin
da aka kai gurin boka don a mallaki dan
naki? In yawon bin bokayen ne ai tare
ta ruga ni da ke ko kin manta ne in tuna
miki? Tunda wai kenan yanzu kin tuba
a cewarki?
To bari in tuna miki wani sirri da
Kila kin manta vana lullube a fatala na
kuma zan iya bankade shi dan naki ya
ji. Wai Mujeebu ne yake cewa Suwaiba
ta ba boka kanta don ta mallakeshi, to
zan gaya masa ba Kanta faru ba ba ita
kadai ta fara hakan a duniya ba kuma
182
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
3
ba a kanta za'a daina ba, wasu matan
sun dade da aikata wannan sabon kuma
sun mallaki miji tun kafin shi Mujeeb
din yazo duniya zan kuma iya bankada
masa yaji ko su waye don ya sassauta
ma 'yata a ganin da yake mata na
wadda ta aikata babban zunubi don ba
kanta farau ba, anyi da yawa a
bayanta.
Goggo ta mike tsaye ita ma suka
fuskanci juna sosai da Haj. Harira
sannan tace, "Au bankade-bankade ki
ka zo yi? To bari ki ji in gaya miki
Wallahi muddin wani labara na da ba
kowa a duniya ya sani sai ke ba idan ya
shiga kunnuwan dana sai na tozarta
mutuncinki Wallahi"
Haj.Harira tace. "Ai ni nan da
kika ganni bani da wani sauran mutunei
nawa da nake tattali. balie har invi
tattalin na wani, kece kike ganin kina
da mutunci har kike tsoron a bankade
shi, to bari ki ji Wallahi yau ba sai
danki yaji naki sirrin boyen don ya san
183
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassah Zaria
bani dadiyata bane kadai mu ke da abin
fada ba.
Ta kama hanyar fita a fakin, ita
kuma Goggon ta yo hanzarin biyo
bayanta, amma kafin ta kai gareta sai
jirin da ya mamaye idanunta 'ya kada
ita, ji kake tim a kasa.
Haj. Harira ta dawo da baya ta
rike ta tana sallallami, yayi daidai da
foitowar Mujceb daga falonsa, zai fita
zuwa Sallar la'asar.
Yana jin sallallamin Haj. Harira
a dakin Goggo sai ya shigo ya iske abin
da ke faruwa Goggon ce a kasa har
bakinta ya jirkice yana dalalar miyau.
Cak ya sure ta ya fita yasa ka ta a
mota ya kira Muneeba suka wuce
asibiti. Gado aka ba Goggon aka daura
mata karin ruwa.
Likita yayi masa bayanin ta sami
mutuwar barin jiki don, bakin ta ya
jirkice guri daya.
Hankalin Mujeeb ya tashi sosai
akan ciwon Coggo sannan ga Suwaiba
dole ita ma asibitin ya dauke ta ya kaita
184
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
asibit. Ana yi mata gwaje gwaje aka
gano ciwon daji ne ya kama gaban na ta
wato (cancer) a dalilin magungunan da
ta ke amfani da sun a matsi masu illa ne
ba ta sani ba.
Wata matsalar kuma nonuwan ta
sai suka fara ciwo, wasa gaske sai gasu
sun yi suntim har bata iya saka rigar
nono, suma ana yin gwaji aka gano
dajin ne ya kama su a dalilin kwayoyin
da ta dinga sha musu kara girman nono.
Goggo kam ta sami sauki har an
dawo da ita gida, amma bata iya tafiya
sai da sanda bakinta kuma bai dawo
dai-dai ba ya riga ya nakasa.
Nonon Suwaiba ya tsananta da
ciwo har ta kai ga ya huje yana zubar
da ruwa kuma duka biyun, kafin wani
lokaci har ya fara tsutsa dole aka yi
shawarar sai an vanke su in ba haka ba
zata iya rasa ranta.
A ranar da likita ya fadı hakan
kwana suka yi kuka ita da Hajiyarta da
ke jinyarta don kuwa dakin da take
babu mai iya shiga sabo da wari, shi ma
185
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
gaban nata har yanzun warin yake yana
fidda ruwa.
Anyi nasarar yanke nonuwan
gaba daya, suna nan a asibitin ana yi
mata gashin gurin. Shi ma gabanta sai
ya fara fitar da tsutsa wasu irin farare.
Wannan al'amarin ya
girgiza Mujeeb, Haj. Harira kuwa
komawa tayi tamkar tababba in banda
sambatu ba ta aikin komai.
A wannna lokacin ne Muneeba ta
haifo 'yan biyunta mata masu matukar
kama da ita, ko da yake Mujeeb yace
sam bai yarda ba da shi yaran suke
kama, tunda ita ma Muneeban dashi
take kama.
Labarin haihuwar na shiga
kunnuwan Suwaiba da Hajiyarta sai
suka ji tamkar za su mutu sabo da bakin
ciki, sambatun Haj. Harira sai ya dada
karuwa har yada labarin haihuwar ya
zauna daran a bakinta kowa ta gani sai
ta gaya masa tana cewa kunji Muneeba
ta sake haihuwar 'yan biyu ko? Daga
fara haihuwar ta har ta wuce Suwaiba,
186
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
'ya'yanta hudu yanzu suwaiba ko
Kwaya daya dayar ma ta kwace ta rike
wannan ai zalunci ne don an ga ciwo ya
kama suwaibar."
Muneeba suna dawowa daga
asibitin su Bilal suka haye gadonta suka
kewaye jariran suna kokarin daukarsu.
Tana shigowa ta gansu tayi saurin
sauko dasu daga gadon, ai sai suka saka
ihu gaba dayan su, Mujeeb na jin
ihunsu ya shigo da sauri yana tambayar
abin da aka yi musu. Tace, "wai yaran
nan za su dauka ina zan barsu ko wuyar
da na sha ban manta ba."
Ya dauko su dukansu ya
rungume yana lallashinsu tare da cewa,
"kuyi hakuri wadannan yaran na momi
ne, ku bari zata sake haifowa Dadi nasa
irinku masu kama ada ku sai in baku ku
dauka kowa dava ko?"
Suka gyada kai a tare. Ya dan
dubi Munceban yace, "Na lura yaran
nan dukansu za ki dinga yi akan
'ya'yan nan, wato kinfi son sababbi
akan tsofaffi ko?" Tace, "Wannan
187
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
kuma ai kai ka raba, tun a haihuwarsu
Hilal din kace in fara haifo maka naka
sai in hifo nawa daga baya sai kuwa
gashi Allah ya bani nawan ba dole inyi
tattalinsu ba, kowa yaji da nasa"
Ya dubeta, "Au haka ne? to shike
nan kowa ya rike nasa za'a ga su waye
'yan gata." Tana Dariya tace, " Ai
kuwa za'a ga 'ya'yan gata, yanzu ma
kwashi naka 'ya'yan gatan ku tafi don
kada su sake mini laifi ace na daki
'ya'yan gatan Dadi."
Yana mikewa suka cangara ihu
suka makale shi suna fadin Dadi!
Dadi!! Dadi!!! Kowa ya daga hannu sai
a daukeshi. Ya dauke su ya fice yana
jin Muneeba na masa dariya tana cewa,
"Haba wa ai mutum zai sha wahalar
nasa `ya yan gatan indai su Hilal ne, sai
sun hanaka fita otis, ni dai 'var kallo
ce.
Yaran an canza musu suna
Hassana da Hameeda, Hussaina kuma
Haneefa taron suna kadan-kadan aka yi
shi sabo da majinyata da ke gidan ga
188
ا
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Goggo a kwance, ga suwaiba ita ma an
dawo da ita gida don an gama gasa
ramin ciwon ya kame, matsalar
tsutsotsin da ke fita a