"Kinga uwar bari ne yanzu? Ai
134
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
na dauka kina da juriyar da zaki iya
zama haka nan tunda kina samun komai
na jin dadin rayuwa? Kije zan neme ki duk lokacin dana shirya?
Ta marairaice "Ni dai yau zaka
kaini don Wallahi na gaji da juriyata ta
kare ni ba dutse bace ni mutum ce
kamar kowa ina bukatar samun
natsuwa kamar yadda kake samu
kanada madafa.
Ok laifi na kike gani ko naki?
Dama ni ba zan damu ba tunda ina da
inda zan kai bukata ta, ke dinma da
kinso ai zaki iya zuwa gurin abokin
masha'ar na ki don kila baki tuba-ba".
Ta soma matsar kwalla munafunci don
girman Allah kabar tuna mini wannan
mummunan al'amarin Wallahi nayi
dana sani ya fi cikin Kwando kuma
Wallahi tallahi bantaba ba kowa kaina
ba in ba wannan kaddarar ta auko kaina
ba saboda wata biyan budatar duniya
amma nayi nadama ba zan sake aikata
hakan ba ina rokonka ka yafe mini na
tuba zan hakura da matsayi na na rashin
135
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
so na da baka yi zanyi ta addu'a har
Allah ya karkato da zuciyarka gareni
kamar yadda zuciyarka ta karkata ga
Muneeba tana maganar tana hawayen
munafurci yazo ya dafa kafadarta ya
shiga lallashinta abinka ga mata da miji
al'amarinsu sai Allah nan da nan ta
karyar masa da zuciya yaji tausayinta
dama hakan take so ta faru"
Kiyi hakuri ki bar kukan na san
ba halinki bane bin maza tunda zan iya
bada shaidar na aureki a cikakkar mace
amma bansan rudin duniyar da ya
kwashe ki har idanunki suka makance
kika ba Boka kanki ba in kinyi haka ne
don in soki fiye da kowa kin zalunci
kanki don ni bance miki bana sonki ba,
sannan ina kamanta adalci a tsakaninku
da yar uwarki wani lokaci ma ita ce ya
kamata tayi korafi akan irin fifikon da
Goggo kesa ina nuna miki fiye da ita
amma duk baki gani ba shin wane irin
so kike son in nuna miki bayan wadda
nake nuna miki ke da 'ya'yanki.
136
a
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Ajiyar zuciya ta shiga yi "Ni bance ka so ni fiye da kowa ba, ina dai
son ka dinga yin adalci ne a tsakaninmu akan komai ka sakani cikin duk wasu
al'amuranka kamar ita, kayarda dani
tamkar yadda na ga kana ammanna da
komai na ta nayi maka alkwari zan
دو canza duk wasu dabiu da baka so".
Yaja numfashi ya sauke sannan yace
"Kayya Suwaiba kinfa riga kin 6ata
rawarki da tsalle kina ganin da gaske
kike kuma kinyi alkwarin zaki watsar
da makamanki za ki rungumi gaskiya
da samar da zaman lafiya da zaman
amana a gidan nan?
Ta gyada kai nayi maka alkawari
in har ba zaka sake juya min baya ba don ina tsananin sonka in kishinka sosai
inhar baka mayarmin da martanin
soyayyata to komai zaí iya faruwa ina fatan ka canza kamar yadda nima nayi
maka alkawarin canzawa.
Ya ce"Duk abinda ya faru
laifinki amma mu manta da abinda ya
faru mu fuskanci abinda ke gabanmu ki
137
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
tabbata kin rike amanata dake hannunki
ki tsaremin kanki bana son na sake
kamaki da yiwa aurenmu kwamacala ki
ji tsoron Allah ki ji tsoron duniya in ba
haka ba to zan dauki mataki da ba zai
yi miki dadl ba saboda haka sai ki
kiyaye tayi masa alkawurra masu dama
amma duk na bogi ne saboda ita da
kanta a zuciyarta tana tunanin anya
kuwa zata iya kyale bin bokaye don
anan ta ganin sai da taimakon su take
samun wasu nasarori a gidan aurenta.
Shima a nasa 6angaren yayi mata
alkwarin canza yanayin zamantakewar
su tare da yin adalci a tsakaninta da
Muneeba bayan Sallar Magriba ne yayi
kiranta a waya yace ta shirya gashi nan
dawowa daga masallaci za su je asibitin
da saurinta ta tashi ta shirya Walceda ta
shirva kanta ta zauna jiransa yayi
sallama ya shiga dakin nata a falon ya
sameta tana sanyawa Waleeda rigar
sanyi yarinyar sai Ihu take yi ya isa ya
dauki yarinyar yana tambayarta me
mamana tayi miki kikasa min ita kuka?
138
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Tace "Wai rigar sanyi zansa mata shine
bata so sai dai a kyale da 'yar karamnar riga ga da nomoniya"
Ya amshi rigar yana Karasasa
mata tare da tambayarta "Wa ye ya
doke ki? Ta nuna Suwaiba "Anti ce ta
doke ni takI goyoni, ya dorata a bayan
Suwaiban yana cewa "Oya dauko zani
ki goyata ko nima in rama mata
dukanta in rama maki?.
Ya tambayi Waleedar ta gyada
kai ya kai hannu ya dan bugi bayan
Suwaibar yace "Na rama miki yi shiru
ki kyale Anti ba. zan goya ta ba".
Suwaiba ta sauko da Walecdar daga
bayanta ta dora a bayan Mujeeb din
tana cewa "Sauko min a baya na shi sai
ya goya ki tunda nima yace ba zai kara
goya ni bа".
Ya manne yarinvar a bayansa
yace "Oya sa hijjabi kizo mu tafi bari in
kaita gurin mamanta ta zauna gurin
kanninta har mu je mu dawo". Taso
a'a sai kuma ta tuna da yakin zamba da
zata soma a gidan sai ta fasa ta kyale
139
ta
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
shi yana rungume da Waleedar yar
kimanin shekaru uku ya shiga dakin
Muneeba ya sike ta gabansu Hilal da ke
zaune suna koyon zama cikin
kekunansu tana basu (Prisocream).
Ya aje Waleedar yabi yaran yana
sumbatarsu yace "Suna kuwa shan
abinnan sosai kuwa? Naga sunfi son
Madara? Ta soma ba Waleeda da ta
wangame mata baki wai itama zata sha
sannan tace "Suna sha sosai saidai sunfi
shan madarar don tafi yi musu kama da
Nono shima wannan din zasu saba.
Bilal ya soma miko masa hannu
yana zillo don ya daukeshi ya ciro shi
daga keken ya daga shi sama yana
masa wasa sannan ya maida shi cikin
keken ya dubi Muneeba yace "Ga yarki
nan ta zauna guren kannenta za mu je
asibii da Suwaiba". Tace Subhanalallhi
bata da lafiya ne ban sani ba" yace
"Lafiyarta kalau gwajin nan za mu je
mu yi yau ta ga dama bari ba shegiya
bace tana da ubanta Munceba tace sai
kun dawo Allah ya tsare ya jishshemu
140
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
alkhairi yayi dabara ya fice don kada
yaran su ganshi sun yi saboda da shi
sosai indai ya shigo zai fita muddin
suka ga fitarsa sai sun yi kuka.
An yi wa Suwaiba gwajin H.I.V
sakamako ya fito nan take bata dauke
da cutar (NAGETIVE) suka gani a jikin
sakamakon nata ".
A gaban likita tayi tsallen murna
ta rungume Mujeeb tana murna likitan
shi ma taya ta murna yake yi Mujeeb
ma yayi murna da ganin sakamako
amma zuciyarsa ta kasa natsuwa sai da
ya sake kaita wasu asibitoci har guda
biyu bayan wannan aka sake yin mata
wani gwajin duka sakamako iri daya ne bata dauke da cutar.
Daga asibiti na karshe sun fito
zasu taho gida, sai dabarar yadda za ta yi ta cusawa Munceba Haushi a wannan
fita tasu tamkar yadda take jin zafi idan suka fita ta zo mata ta dube shi ta ce
Don Allah mu dan biya gidan kawata
Aima'u bata da lafiya tun rannan ta
kirani yayi magana ba tare da ya dubeta
141
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
ba Dare fa yayi za ki ce mu je gidan
mutane dubi agogo yayi mata nuni da
agogon motarsa ta duba ta ga tara saura
minti takwas tace ai dare bai yi ba
tunda goma bata yi ba don Allah ka yi
hakuri mu je tunda akan hanya ne ya ce
יי
"Shi kenan sai mu je tunda kin matsa.
A harabar gidan ta barshi ta shiga
ta tura masa mijin Aina'un don suyi
hira duk cikin shirinta nason su dade
wanda shi sam bai dago wannan shirin
nata ba.
Suna can sun kule a dakin
Aina'un suna kullawa da kitsawa ta
yadda Suwaiba za ta zargo zuciyar
mijin nata a wannan karon ta hanyar
Kissa da kisisina ba wai sai ta hanyar
boka ba ko malai ba.
Aina'un ta kara da cewa "Ke
sakarya yanzun an daina yayin zuwa
gurin teacher don basa wani tasiri kiyi
mai gaba daya ne ki tsaftace shegiyar in
zaki sha giya ki sha ta dubu ki yi tatil
sannan ki ki kanainaye shi da kisisina
na iri iri sai kifi samun kansa amma
142
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
yaushe ne za ki tsaya gurin ticocin
zaure ai gara kiyi mai gaba daya
haihuwa da 'ya'yan hanji sukayi shewa
suka tafa suwaiba tace shi ya sa kike
burgeni kin hana ko wace shegiya
shigowa gidanki ta gidan da kika samu
ma kin yi waje road da ita ta gudu ta
bar ladanta 'ya'yan har yanzu suna can
makarantar kwana?.
Ta yatsina baki tace dukansu
suna can don ba zan iya jidali ba sai
hutu suke zuwa, shima hutun can kauye
nake kada su gurin kakarsu a cewarsu
wai can ya fi dadin zama munafukai ai
ba zà su iya zama gidan nan ba don aiki
kadai ya ishesu hana masu aiki yin
komai na ke yi su suke yi shi ya sa
wuya ke korarsu su tafi can karata su
bare min daga ni sai mijina da `ya'yana
na biyui, wadda ta vave ma tana can
nasa ya mayar mata don ba zan iya rainon dan kowani mata ba na ma gaya
masa.
Suwaiba tayi shewa tace, "haka
nake son ki tawa kina birgeni kuma
143
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
dole ya yarda ya maida ta? Ta kara
yatsina baki saboda dabi'arta ce yin
hakan tace, ba dolen shi bani umurni,
kawai nake bashi tamkar uwa da danta
da na ce haka za a yi iyakarshi yace to
gimbiyata.
Suka saki shewa suka tafa
Aina'un taci gaba da cewa, "shima ya
san sauran idan ya ki bin umurni na
fuska kadai zan hade sai ki ga ya soma
rawar jiki yana lalllashi na, ai ni namiji
dan in ja akalarsa ba wata tsiya bace ina
da wanda ya tsaya min."
Suwaiba tace, "shi yasa ai nace
mu biyo don na san baza ki rasa
shawaran da zaki bani ba, sannan idan
'yan sinadaran da ake birkita
kwakwalwan Alhaji a bani yau nima na
birkita nawa mijin, ni ban san irin shi
ba duk kyan maganin mata idan nayi
amfani da shi bana gane ko yayi ko bai
yi ba don ba zai nuna ba sai yayi mirsisi
na rasa gane gabansa."
Aina'u tace, Kyale shi Wallahi
karyan miskilanci yake yi yau zan baki
144
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
wanda zai yi ta kwara miki ihu kuma
sai ya manne miki tamkar cingom, kece
da shi yau ko?
Tace, "Eh, nice amma babu
tabbas din ko zai yi wani motsi don
miskilancin na kansa sai yayi ra'ayi."
Aina'u taja dogon tsaki au ke
kuma sai ki kyaleshi, baki san dabarar
da zaki yiu ya afka ba? To bari kiji ni
ko bani ke da girki ba idan ina jin tsiya
ko ina da muradinsa na san yadda zan
masa ya fado tarko na kawo kunne ki
ji,"
Ta yi mata rada a kunne suka
kece da dariya suka yi shewa suka tafa,
suwaiba ta ce na gode miki tawa kin
bani liked ai matar nan ta higa uku har
,, ita ta shigo tarko na.
Aina'un ta tashi ta zuge zif din
wata jaka ta dauko wata 'yar karamar
kwalba tamkar ta mai ta nuna ma
suwaiba tana mata karin bayani, kinga
wannan maganin daga China muka
bada sako aka taho mana da shi naira
dubu hansin kenan duk kwalba, dan
145
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
kadan zaki lakuta ki manna ba zance
miki komai ba ina jiran wayarki don ni
ranar dana fara amfani dashi kin ga
wannan." Ta dauko makullin mota dake
aje bisa kan madubi tace, "makullin
motar da ya bani kenan da safen,
waccan tawan yace in hada ko inyi
kyauta da ita bayan wasu kyaututtuka
da suka biyo baya.
Humm! Ai ni yanzu bana sanyi
da wadannan abubuwan don suna biya
min bukatu sannan ga boka Duna ya
tsaya min, ki zo in kaiki."
Tace, "ki sha kuruminki zan zo
mu je kudi ni da bani da shi, amma
yanzu idan ya zo hannnuna na san zan
sami kudi don ba kananan kudade
mutumin ke samu ba yanzu ni ina
zaune cikin rashi."
Ta dibar mata maganin cikin
wata 'yar kwalba. Mijin Aina'un yayi
sallama ya shigo yana cewa, "yace ki
fito ku tafi dare nayi ga garin da sanyi."
Ta mike tana gyara hijabinta suka biyo
146
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
bayan Alhajin Aina'u na sake yi mata
rada a kunne har suka fito.
Anan ne Mujceb ya gaida
Aina'un da jiki ta amsa tamkar ciwon
take yi da gaske, sannan suka yi
sallama suka wuce.
Ta dan marairaice masa tace,
"Don Allah baban waleeda ka tsaya ka
saya mana ice cream." Ya dan dubeta
yace, "kin fa san dare yayi za ki sa
muna tsaye-tsaye ki bari gobe na siyo
miki."
Ta kara narke murya."kayi
hakuri ina ce a kan hanya ne? bai ce
komai ba sai gani tayi ya tsaya Mr.
Biggs, ya shiga ya siyo ya zuba ledojin
a sit din baya Ana zuwa wata kwana
kuma ta sake kashe murya."Baban
Waleda don Allah ga gasassun kaji,
Wallahi yunwa nake ji ban ci komai
sabo da zullumin zuwa asibiti nan."
Ya dan Harare ta, "wai ke wane
irin kwadayi ke damun ki tamkar wata
mai ciki, kince ice cream an siya yanzu
147
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
kince kaza ai ko me yaron ciki sai
haka.
Tayi dan murmushi, " Ni dai
ayi hakuri a siya mana ciki kam ai ka
san na dade ban bi hanyarsa ba, amma
kwanan nan zamu hadu insha Allahu."
Girgiza kai kawai yayi lokacin da
yake yin fakin din motarsa. Ya fita yaje
ya siyo kajin suma suma ya bude sit din
baya ya aje ledojin sannan ya ja motar
suka tafi.
Suna daf da kwanar da za ta
kaisu gida ne ya dube ta yace, "Ga mai
soya kifin ruwa can shima za'a tsaya a
siya ne? ta san tsokanarta yake yi shi
yasa tace,
"A'a na gode da wanda aka saya
mu je gida kawai da dai ciki gareni ka
san dole sai an tsaya an siya.
Ba su isa gida ba sai goma da
kusan rabi. Suna fitowa daga motar ya
amshi ledoji hudu biyun yace ta wuce
masa da su dakin ta gashi nan zuwa..
Can ya sami Muneeba a dakin
baccinta tana zaune bisa abin Sallah da
148
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
hisnul muslim a hannunta tana
karantawa.
Ya aje ledojin da ya shigo da su
yana cewa, "kin gammu sai yanzu ko?
Wallahi asibiti uku muka je, na farko
sunce bata da ciwon, amma ban sami
natsuwa ba sai da muka sake zuwa
wasu asibitocin kinga result din.
Ya fiddo takardar daga aljihunsa
ya mika mata ta amsa ta duba sannan ta
maida masa tana cewa, "Ai an gode
Allah da sakamakon ya kasance haka,
Allah ya kara tsarewa", Yace,
"Amecen".
Ya dubi su Hilal dake bacci bisa
gadonta Waleeda na can bayan su yace,
"yarannan duk sun yi bacci har
Walecda? Tace
"Tuni suka yi bacci dare ai yayi, Bilal ne ma yau bai yi da wuri ba,
Waleedan kam tun tara saura ta bingire tunda ta cika cikinta da riso".
Ya yi dariya "yarinya da kwadayi
sam yanzu ba ta cin abinci sai abincin
yara taci zamaninta za ta ci na su.'
149
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hạssan Zaria
Ya nuna mata ledar da ya
aje, "Ga ice cream nan da gasassar
kaza, daga zuwa aibiti mun bige da
siyan kayan kwadayi har da cakulet a
ciki."
Ta dau ledar tana dubawa, "An
gode Allah ya amfana yace, " Akwai
wani abu ne zan je in kwanta baссі
nake ji gashi ko Sallar isha'I banyi ba"
Tace, "Babu komai Allah ya tashe mu
lafiya." Har ya juya zai fita sai tace
"Waleeda nan zata kwana mu rufe kofa
ko? Ya juyo yace Wallahi na manta da
ita ki barta ta kwana nan tunda tayi
bacci".
Bai jira abinda zata ce ba ya juya
ya tafi yana kara yi mata sai da safe
kishi kummalon mata nan da nan ya
taso ya lullube zuciyar Muneeba take ta
soma karanto addu'ar yaye kishi. a
zuciya don ba taso yayi tasiri a
zuciyarta duk da zallar zúmudi da
murna da tagani karara a shimfide a
fuskar Mujeebu wanda ta rasa gane
cikin abu biyu wanne ne ya saka shi
150
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
cikin murna tsallake siradin da
Suwaiban tayi ko murnar yau zai
kasance tare da matar tasa bayan shafe
kusan shekaru biyu rabon da wata
mu'amular auratayya ta hadasu ta dade
zaune tana yan tunane-tunane da, 'yan
canke cankenta daga karshe dai ta
watsar da komai ta tashi ta je don ta
rufo kofar falonta dake bude. idanunta
karaf akan Suwaiba dake tafiya zuwa
dakin Mujeeb tana sanye da wata 'yar
yaloluwar riga da bata boye sirrin
komai a jikinta ba, iyakacin rigar
guiwarta kuma ga dukkan alamu
rigarce kadai ke jikinta Allah ya sa ba
su ga juna ba bayan Suwaiban kawai ta
hanga da cewa za ta yi Muneeba
lekensu tazo yi jikinta a salube ta rufo
kofar ta zo ta zauna a bakin gado tayi
shiru yau kam tsakanin Suwaiba da
Mujeeb sai Allah an dade ba'a hadu ba
banufe ya ga Koko shi ya sa ma yace ta
bar Waleeda ta kwana gurinta wato don
kada ma ta kawo musu cikas sauri tayi
ta fatattaki wannan tunanin daga
151
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
zuciyarta don in ba ta yake shi ba sai ya
nemi dagula mata tunani ya hana ta
bacci mai dadi tayi addu'o'i ta tofawa
yaran dukansu ta ja bargo ta shige
sannan ta latse fitila mai haske itama ta
karanto nata addu'ar ta tofa miyan ya
dawo jikinta sannan ta soma baccinta
mai dadi.
Suwaiba lokacin da suka dawo
wanka ta yi sauri ta shiga don ta san
kaidar mijinsu ba'a kwanciya da shi
sai kin yi wanka kuma ya jiki kina
Kamshi tana Sallar Isha ya shigo ganin
tana Salah sai yace idan ta gama ta
sameshi dakinsa ya juya ya fita tana
idar da Sallah ta saka yar rigar baccinta
ba tare da tasa komai a jikinta ba, ta
shigo bayi ta manna maganin da Aina'u
ta bata, sannan ta fito ta feffesa turare ta
suri ledar data shigo da shi ta fita ta
rufe kofofinta ta nufi dakinsa.
Shima har yayi wanka yana
Sallah ta same shi hakan ne ya bata
dammar dauko filet ta juyc kajin nan ta
dauki robar Ice Cream guda daya tana
152
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
sha tana kallonsa har ya idar da Sallar
ta dauka filet din ta kawo gabansa ya
dubeta yace "Ba zan iya cin komai ba
bani Ice cream din matsowa tayi ta
debona hannunta ta kai bakinsa yayi
murmushi "Yau dai na ga so kike ki
shagwabani miko min wannan nasha na
hutassheki"
Ta turbune fuska "wai ni meyasa
komai na yi maka sai ka gwale ni ne
sam bana birgeka da Muneeba ce ai ba
zaka ki sha ba". Yace "Kinga matsalata
dake ko? Ke dai bakinki ya zama sai
kinyi korafi kin kawo zancen wata ki
daina irin wannan babu kyau”.
Sai dai ta fadi hakan ne ita ma
taga sakarcinta da take son 6ata
nishadinta da suke ciki tun yamma cin
yau hakan kuma zai iya bata al'amarin
da take fatan ya wakana tsakanin su
don kuwa tayiwa daren nan shiru sosai
ta langabe kai cikin kisisina "Shikenan
kayi hakuri ba zan sake sako sunan
kowa ba idan huna tare yi hakuri
kasha"
153
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Ta kai cokalin Ice Creamn din
bakinsa bai ki ba ya amsa yasha. A
haka tayi ta bashi har suka shanye
sauran ta je ta saka Firij dinsa ita kadai
ta ci kaza daya kadan ta rage saboda
yunwar da ta ce tana ji daga nan
al'amura suka fara canza salo shi kam
yace bacci sosai yake ji amma sakat din
da ta hana shi shi yasa ya sallama mata
suka raya daren cikin nishadi irin yadda
take mafarkin samu shi kam har
tausayinta ya dinga ji na rawar jikin
data dinga yi lallai ya yarda ta dade
cikin kewarsa da kyar ya iya tashi ya
tafi Sallar Subahi saboda taki barinsa
yayi bacci duk. cikin kisisinar data
shirya ne don tana son tasa shi ya
makara wajen zuwa Ofis don ta
Kunsawa Munceba kishi a zuciya ana
idar da Sallah ya kasa zama yayi karatu
a masallacin kamar yadda ya saba Allah
- Allah yake ya dawo ya iske Suwaiban
da wata sabuwar bukatarsa don kuwa
tayi rugu-rugu da tunaninsa a daren jiya
ta canza masa tamkar ba ita ba ko dakin
154
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Goggo da Muneeba bai shuga ba kamar
yadda ya saba idan ya dawo sallar
subahi yana yi.
Ta sake kanainayeshi ta nuna
masa tamkar baida kowa inba ita ba har
sai da ya zo yana tuhumar kansa yadda
ya kasa saurara mata abin tamkar tishin
karatu wani irin nannauyan bacci ne
yayi awon gaba da shi wanda ya kaishi
har kusan tara safe san nan ya farka a
gaggauce yayi wanka ya soma shirin
zuwa office a makare ya tashi Suwaiba
da ke shara baccin ta hankali kwance
yana tambayarta abin da zai yi
breakfast da shi tayi mika babu wani
salati idanunta na kallon agogon bangon dakin murna fal cikinta da
ganin lokaci sannan tace "Ni yanzun
me zan iya yi maka yadda nake a
gajiyen nan kaje gurin mamansu Bilal na san ba za ka rasa abin da zaka ci bа`.
Jin abinda tace sai ya soma shiri a
gurguje don ya shiga gurin Muneeba
yayi break sannan ya wuce Ofis
Muneeba ita kuma tana can tana fama
155
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
da Walceda dake rigima tana ta kiran
anti ko tace Baba tana neman Suwaiban
ita kuma babu halin ta je ta kaita dakin
Mujeeb din tunda har a lokaciun basu
fito ba kada su yi zuwan nata fassarar
lallashin yarinyar ta dinga yi har dai ta
hakura ta saki jiki tana wasa da 'yan
kunnenta Mujeeb ya shigo dakin nata
tare da sallama ta amsa masa amma
hankalinta na kan yaran dake wasa ta
soma gaishe shi ya amsa tare da cewa
"Yau nayi lattin zuwa Ofis ko zan sami
abin break fast?.
Mamaki abin ya bata na sakaci
irin na Suwaiba kin iya kwana gurin
miji ki kainainaye shi amma ba zaki iya
bashi abinda zaici ba ta kalle shi cike
da mamaki tace "Abin breakfast tace
akwai a kicin bari na kawo maka na
dauka ka tafi Ofis ko ina bayi lokacin
Yace "Ban tafi ba wani, bacci ne
tamkar na asara ya same ni tunda na
dawo Sallar Asubahi Allah yasa ya
zamc min alkhairi". Tace "Amcen ta
wuce kicin dinta ta kawo masa kunun
156
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
gyada da soyayyan dankali da kwai ta
barshi zaune gurin yara a falo ta shige
dakin baccinta ta kama gyaran durowar
kayan su Bilal hakan nan ta tsinci kanta
da yin wannan aikin da bata shirya ba
kasancewar bata son cigaba da zama
gurin Mujeeb saboda kishi da ta ji yana
yunkuro mata na ba gaira ba dalili
mutum da matarsa me za su fasa?
Har ya kammala karinsa bata fito
ba ya tashi ya shiga dakin ya sameta
yayi mata magana cike da kulawa 'Ni
zan wuce Ofis koda wani abu da kuke
so?
Ta girgiza. kai "Babu abinda
muke so Allah ya tsare ya bada sa'a ya
amsa "Ameen" ya kai hannu ya shafi
gefen fuskarta sannan ya juya har zai
tafi sai ya dawo yace "Abincin yaran
akwai saura da yawane tunda naga har
waleeda ma sha take yi'.
Tace "Ina jin saura gwangwani
biyu cikin kwalin zuwa jibi za'a iya
siyo musu wani yace Ok zan aiko
direba da shi anjima ina son ki yi min
157
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
kunun alkama ya taho min da shi
tamkar zata ce masa meye aikin
Suwaiba fa da ba zata yi masa ba sai
dai ta fasa tace "Sai ya zo". Ya juya ya
fice ta bi bayansa da kallo tana girgiza
kai misalin daya da rabi na rana direban
Ofis dinsu ya iso har bakin falonta mai
gadinsu yayi şallama ya shaida mata an
aiko direba ta saka hijjabi ta fito suka
gaisa ya mika mata kwalin Prisocream
din yara tare da wata babbar leda yace;
"Ga shi nan inji yallabai yace ki kirashi
yanzun kafin in tafi". Ta amshi kayan ta
koma falonta ta dauki waya ta kirashi
yana dauka tace, Direbanka yace kace
in kira ka yace "Ki bashi kunun ya
kawo mini sannan ga wasu kaya nan ki
dauki kala biyu ki cirewa Goggo biyu
sai ki ba Suwaiba guda biyu mun fita da
abokina yawale ne zai yi wa matarsa
sayyaya ta haihu shine na ga kayan sun
bani sha'awa Allah ya sa sun yi miki.
Ta amsa sunyi kyau sosai Allah
ya kara budi mun gode". Suka yi
sallama kowa ya aje wayar ta dauki
158
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Filas din kunun ta saka cikin wani
basket tare da kofuna da cokula ta zo ta
duba lesunan ta cire nata kalolin da take
so ta cirewa Goggo don ba ta nan ta
zuba na Suwaiba a ledar gurin da aka yi
siyayyar ta ba direban tace ya je ya kai
wa Suwaiban.
Lokacin da ya kai mata yace inji
yallabai don haka Muneeba tace yaga
ya mata yana fita ta duba ledar tayi
tozali da rantsatssun lesuna 'yan dubu
arba'in arba’in, don haka taga kudinsu
manne jikin ledar kasancewar a Super
Market aka sayesu.
A tunaninta ita kadai ya siyama
tukuicin fadawa tarkon da ta dana masa
ya afka a daren jiya ta dauko wayarta ta
nemo Ainau ta soma labarta mata irin
wainar da suka toya a daren jiya ita da
mijin nata wanda sai da ya aje wani
miskilanci da jin kansa ya dinga kodata
abinda bai taba yi mata ba ta kara da
cewa kin san yanzu ina zaune sai ga
direbansa na Ofis ya aiko a kawo min
galla gallan lesuna yan dubu Arba'in
159
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Arba'in na san duk tukuicin abinda nayi
masa ne"
Aina'u ta kyakyale da dariya
tace "Me na gaya maki an gaya miki ni
ta wasa ce to kada ki kyale shi don so
nake ki kanainaye shi da sabon kisisina
ki tatso wasu kudade don ki bada
akawo maki naki kin daiga aikin
maganin sha yanzu magani yanzun ne
kada kiyi wasa da wannan dama da
kika samu ina jiranki gobe in sake jin
wani cigaban da za'a samu.
Cikin daren yau ma bayan sun
gama nishadantar da junansu sai ta
narke cikin jikinsa tana masa 'yan
koke-koke na kisisina, nan da nan
hankalinsa ya tashi saboda cikin daren
nan guda biyu jin al'amuran Suwaiba
yake kamar me........ya dan dago
fuskarta dake narke bisa kirjinsa yana
kallonta yace "Me kuma ya faru muna
cikin nishadi zaki tada min hankali? Ta
Kara marairaicewa "Ni kam gaskiya na
gaji da zama ba wata sana'a jari nake so
ka bani in fara sayan kaya ina saidawa
160
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
ko in bayar a sayarmini sannan nima
ina son in fara hawa mota kamar sauran
mata tunda dai Allah ya hore maka
bawai baka da hali bane".
Ya. sauke ajiyar zuciya
yace, "Wadannan 'yan bukatocin ne za
su saki-tada hankalinki? Ki bari zuwa
da safe zan san abin yi.
Tun bai bata kudaden ba ta shiga
yi masa godiya.
Da safe kamar yadda yace tana
zaune gefen gadonsa, shi kuma yana
saka kaya, yana gamawa ya mika