ya so ya tsunduma
kansa a harkar neman mata tamkar
yadda yaga wasu abokansa masu tashen
naira irinsa nayi sun aje mata iri iri a
81
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Žařia
waje duk wadda šuka yi marari ita suke
dauka zuwa hotel su hole abinsu shi
kam yana Kyamar hakan kasancewar
irin wadannan matan sukan zama
angulu ne kazar kowa, shi kam ko ba
komai yana tsoron haduwar shi da
Allah, sannan ga cututtukan da
mazinata ke dauka masu hallakarwa in
ma mutum baya tsoron Allah ai yaji
tsoron daukar cuta.
A kwance ya sami Suwaiba tana
(Game) a wayarta sannu da zuwa kawai
tayi masa sai taci gaba da yin (Game)
dinta yace "Ina Waleeda ne? ta ce,
"Gata can a daki tana bacci", ya ce, Ok
to dauko ta ki goya ta zamuje anguwa
ne yanzu". Ta bar game din tana
kallonsa ta ce, "Anguwa? Za mu yi nisa
ne in canza kaya? Ya ce, A'a bar
kayan jikin ki sai dai kisa Hijab kawai
bana son dan gyalen nan da kike sawa
Ya fita zuwa dakinsa bai dade ba
ya dawo ya ce ta fito ta dauko 'yarta
suka fito taje tayi sallama da Goggo ta
leka dakin Muneeba ta shaida mata za
82
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
su fiţa da baban Waleeda kuma tayi
hakan ne don ta nunawa Muneeba
itama fa miji na fita da ita ba wai sai ita
ba"
Tana barin dakin wani
azabąbben kishi ya taso ya lullube
zuciyar Muneeba har taa ayyana a ranta
cewa shine ya turo Suwaiba tayi mata
sallama don ta san sun shirya da
matsąrsa in ma tana tunanin sun yi fada
ne"
Suna isa asibitin ya barta a inda
ake jira kafin a aga likita shi kuma ya
shiga ya sami likita da ya je gurinsa a
wani (Private) asibiti yayi masa
bayanin abinda yake so ayi mata wato
Gwajin (H.I.V).
A ka'ida kafin ayi maka gwajin
ko kafin a baka sakamakon gwajin sai
likita ya zaunar dakai yayi maka wasi
nasihohi akan yin hakuri ga duk abinda
sakamako gwajinka ya bayar ka dauki
abin a matsayin Kaddarar rayuwa.
Yadda likitan ya zauna yana yi
mata bayani tare da nasihohi ne hakan
83
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
ya ganar da ita abinda mijinta ya kawo
ta ayi mata wato gwajin cutar kanjamau
tunda yana tunanin tan dauke da cutar
dalili kenan da ya kaurace mata har na
shekara daya da watanni.
Likitan nasiha na gama yi mata
har sai ya dauko sirinji tare da wata
igiya yana kokarin daure mata hannu
don ya debi jinin nata. Ta dakatar da
likitan, "Tsaya likita nagane gwajin da
zaka yi mini a bayaninka ka nuna idan
za'a yiwa mutum irin wannan gwajin
sai da amincewarsa to ni ba da
amincewata za'ayi mini ba ban ma san
me ya kawoni asibiti ayi mini ba,
saboda haka ka gaya masa ban amince
ba, saboda haka ban yardaba, ba na so,
idan ya dawo ka ce masa na tafi gida".
Ta mike tsaye ta goya waleeda likitan
na mata wasu bayanan don ta tsava har
mijinta ya dawo amma ina ko tsayawa
ba tayi wajen sauraronsa ba ta fice
daga Ofishinsa. 'Bata fito da ko kwabo
ba hakan ne yasa ta dauki mota tayiwa
direban bayanin sai ya kaita gida zata
84
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
shiga ta kawo masa kudinsa. Mujeeb na
dawowa Ofishin likitan yaga babu
Suwaiba, kafin nan ya tambaye shi ya
soma yi masa bayanin yadda suka yi da
ita har ta a tafi gida.
Ran Mujeeb ya baci sosai, ya yi
sallama da likitan ya fito ya figi
motarsa ya biyo ta gidan a dakin
baccinta ya sameta zaune a bakin gado
ya watsa mata harara, "daga yau sai yau
Wallahi kada ki kara zuwa kice mini na
tauye miki hakkinki bana biya maki
bukatarki ta aure, tunda kinki yarda ayi
miki gwajin nan don ba zai yiwu naji da
kunnena irin badalar da kika je kuka yi
da bokanki ba sannan inci gaba da
mu'amala dake ba tare da na tabbatar
da lafiyarki ba.
Wallahi tausayin Waleeda ne
kawai yasa zan iya cigaba da zama da
ke ba wani abu ba, in baya'ga haka da
tun da na warke cutar da kika yi min
sanadinta da na sallameki saboda haka
kiyi ta zama a haka har sai ranar da
kika amince aka yi miki gwaji Allah ma
85
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
ya taimake ni naje an yi min gwajin
baki lakaba mini cutar komai, ke ma sai
kiyi ta addu'ar kada Allah ya kaddaro
cuta a kanki zabi ya rage gareki nikam
babu wani hakkinki a kaina har sai
ranar da na tabbatar da lafiyarki". Yana
gama bayaninsa ya fice a dakin nata
kuka mai Karfi Suwaiba ta saki saboda
wannan hali na tsaka mai wuya da ta
shiga kwarai tana cikin tsananin
bukatar mijin nata don kuwa ita ba
mazinaciya bace balle taje ta nemi
maza a waje neman duniya ne ya kaita
sallamawa boka kanta kuma a lokacin
ta sami biyan bukata saidai tasirin abin
baiyi tsawon lokaci ba gashi yanzun
tashiga halin rashin madafa, ita kam
tana tsananin tsoron gwajin da za'a yi
mata kada ace tana dauke da cuta tunda
kwarai ta sani bokaye nan fasikainc
kuma yawancinsu suna tattare da
cututtuka, ita kam a lokacin idanunta
sun rufe biyan bukata kawai take nema
shi yasa ta ba da kanta gashi yanzun
lamarinta duk ya jagule ta rasa mafita.
86
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Tayi kuka mai isarta daga karshe
dole ta hakura don har ta yi ta gama ta
kasa yardawar zuciyarta zata je ayi
mata gwajin ta yarda zata iya hakurin
zama a gidan haka nan, tunda hakan ne
rufin asirinta don ta san idan ya tabbata
tana da cuta to ba zai cigaba da zama da
ita ba yanzu ko tana zauna babu abinda
ta rasa babu abinda baya yi mata kuma
babu wanda yasan meke tsakaninsu har
yanzu ta san bai gayawa kowa ba,
saboda zurfin cikin da yake dashi,
kuma shi mutum ne mai rike sirrinsa
yana barin dakin Suwaiba kai tsaye
nasa dakin ya cuyce ya maida kofa ya
rufe ya euce dakin baccinsa ya ruvbe
kayan jikinsa ya wuce bayi ya sakarwa
kansa ruwan shawa mai sanyi duk da
irin sanyin da ake yi amma shi zafi ya
ke ji saboda yanayin da ya tsinci kansa
a cikin sannan ya rashin tudun dafawa.
Ya kwace a kalla mintuna talatin ruwan
sanyi na kwarara a jikinsa sannan zne
fa ya sami yar natsuwa ya goge jikinsa
da tawul ya saka jallabiya sannan ya
87
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
fito daga bayin ba'afi mintuna biyar ba
wani irin zazzafan zazzabi ya rufesa ya
lallaba ya haye gado ya lalubo bargo ya
shige ciki yana rawar sanyi dare yayi
nisa amma shi idanunsa biyu yana cikin
halin matsananciyar zazzabi wanda ya
galabaitar da shi matuka tabbas ya san
yana bukatar taimako a irin halin da ya
ke ciki tunda ba zai iya tashi ba balle ya
nemi magani a dakin ya sha.
Cikin matan nasa ya rasa wacce
zai kira cikinsu kjasancewar kowa tana
da laifin da ta yi masa kuma sune'suka
yi sanadin shigarsa cikin wannan halin
saukowa yayi a hankali ya rarrafa ya isa
inda ma'ajiyar magungunansa suke ya
nemo Panadol ya debi ruwa yasha guda
biyu sannan ya koma ya kwanta bai
sami yin barci ba a wannan daren har
sai bayan da yayi Sallar subahi shinc
bacci yayi awon gaba da şhi har tara
saura tayi bai tashi ba, hankalin
Muneeba na kansa a tunaninta ko yau
ma ya shigo ya wuce Ofis bai nemeta
ba, sai ta ji ashe ma bai shigo ba don
88
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
taji Goggo Hinde na tambayar Laminde
"Hala Mujeeb har ya wuce gurin aiki
muna can bayi? Laminde tace "Anya?
Gaskiya bai shigo ba kila dai bai fita ba
ko kuma ya fita din amma dai bai shigo
ba
Muneeba ta tashi ta je ta leka ta
window dakin baccinta don gani ko
motarsa na nan ko ba ta nan hakan ne
zai tabbatar mata da ya fita ko. yana
nan. Ganin motar ta yi a inda aka saba
aje ta har ma jume ya wanke ta ya
gogeta jiran mai ita kawai ake ya fito ya
shiga.
Ta fito daga dakin baccinta tana
shaidawa su Goggo Hinde, Goggo ina
jin fa bai fita ba donga motarsa can har
jume ya wanke bari in dubo shi ko
lafiya".
Tana murda kofar falonsa taji a
kofar a kulle da makulli tayi
kwankwasawa shiru bai bude ba, sai ta
dawo ta dauki wayarta ta kira wayarsa
nan ma bai dauka ba sai abin ya fara
tsoratata shin me ke faruwa ne? cikin
89
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
bacci yaji ana kwankwasa kofarsa ya
taso da kyar yaje ya bude kofar bai
tsaya ya duba ko waye a kofar ba kawai.
ya juya yaje ya shiage cikin bargo ya
kwanta.
Muneeba ta biyo bayansa tazo ta
zauna a bakin gadonsa tana tambayarsa,
"Lafiya yau ba ka tafi Ofis ba? Munji
shiru ne har yanzu ba ka fito ba shi yasa
nace bari in dubo ka don naga motarka
a waje har Jume ya wanke”.
Lamo yayi cikin bargo bai bata
amsa ba. Hannu ta kai tana taba jikinsa
sai taji jikin da zafi, ta yi saurin hayewa
gadon ta yaye bargon da 'ya lulluba tana
cewa "yanzu ba ka da lafiya shine baka
sanar da kowa ba in ma ni ba zaka
sanar da ni ba ai ka gayawa Suwaiba
tunda ita bata yi maka laifin komai ba
ni ce kake fushi dan". Ya dan kalleta
sannan ya lumshe idanunsa yace "Gani
na yi ciwo na zai dami kowa ba shi
yasa ban sanar da kowa ba, don bana
bukatar taimakon kowa kuma ba na son
kowa kusa dani".
90
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Ya maida idanunsa ya rufe ta
tsaya shiru tana kallonsa hakika abinda
ta yi masa sam ba ta kyauta ba to
yanzun me ya kamata tayi masa don ya
sauko daga wannan dokin fushin da ya
hau.
Wani tunani da ya zo zuciyarta
shine lallai kila sun sami sabani da
Suwaiba ne don in ba haka ba babu
yadda za'a yi ya shiga takura irin haka
don tasan halin Suwaiba ba idan ta
nemi biyan bukatar kudi-baiyi mata ba
ta nan ta ke gasa shi bata san wannan
karon matsalarsu ta wuce tunaninta ba.
Duk da ba zata iya masa abinda yake
so ba amma bari ta yi 'yan dabarunta
don ta saka shi cikin natsuwa.
Hakan kuwa tayi don bata bar
dakin nasa ba sai da ta ga ya sami
natsuwa yaje yayi wanka ya dawo ta
hada masa Ti ya sha, ya sha magani
sannan tace masa zata je ta duba su
Bilal kila zasu nemi Nono. Ya rikota
lokacin da zata fita yace, A kalla kinyi
awa daya da zuwa dakin nan yanzun
91
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
idan kika koma me zaki gaya musu ya
rike ki har tsawon lokaci haka? Kin dai
san Goggo Hinde ta zuba idanu
kanmu.
a
Tayi murmushi tace ka barni
dasu ni na san irin tsarin da zanyi musu
bari inje". Tana shiga dakin sukabita da
idanu, Goggo Hinde tace, Lafiya kika je
kika dade yara suna ta neman nono?
Hala baya lafiya ne?.
Ta ce zazzabi ne yake yi wait un
jiya amma bai fada ba shine na tsaya
nasa masa ruwan sanyi a jikin yanzun
haka har ya fara sauka". Gaba daya
suka hada baki wajen fadin
"Subhanallahi" Laminde tace, "Shi
Alhaji kamár yaro zai rufe kansa a daki
cikin ciwo na ina ita matarsa da ba zata
tsaya gurin saba sai ke mai jego?.
Goggo Hinde ta tabe baki "Ba ma sai in
ta san yana ciwon ba me wannan ta sani
na kula da miji in banda tsinannan
kishin banza ki ba yaran nono ki koma
ki kula da lafiyar mijinki in har ita ba
zata kula dashi ba jego ai ba zai hanaki
92
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
kula da lafiya mijinki ba Muneeba ta
zauna ta shayar da yaran Nono ta mika
su gurín su Goggo Hinde suka goye su
sannan ta nufi dakin Goggo tab shaida
mata Mujecb ba ya da lafiya ta isa
dakin Suwaiba ta gaya mata, budar
bakinta sai cewa tayi "Ba ya da lafiya
shine ni bani da matsayin da zai gaya
mini sai dai ya aiko a bgaya min, lallai
ma mutumin nan to Allah ya sawwake
idan kin koma ki gaishe shi Muneeba
tace, Haba Maman Waleeda wannan
wace irin magana ce nima fa ba gaya
min yayi baya da lafiya ba, nice na ga
shiru har kusan taran safe banga ya fito
ba sannan ga motarsa a waje shine na je
na duba ko lafiya sai na iske yana
kwance baida lafiya tun jiya kuma idan
zancen gaskiya ne aike ya kamata ace kin sanar damu halin da yake ciki tunda
kece a tare dashi ko da yaushe don
Allah ki yi hakuri ki daure ki dinga
kulawa da al'amuransa don kada mu yi
sake ya fada wani halin da bai dace
ba"
93
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Nasiha ce Muneeba ta yi mata a
fakaice saboda lura da tayi da halin da
mijin nasu ke ciki in ba'a saa aka ci ba
Allah ya taimakesu tsoron Allah ya
mamaye zuciyarsa yana iya kai kansa
inda bai dace ba a dal,ilin rashin
kulawar da yake samu.
Allah ya sanbi tana son bashi tata
gudunmuwar to amma tana jin nayin su
Goggo Hinde kada su ga tana binshi su
gano zakewarta ga al'amuran mijin
nata alhalin tasan yana bukatar a kula
da shi don ta riga ta saba masa duk
rintsi zata kasance da shi in ita ke da
kwana gurinsa.
Suwaiban ma ta gano inda
kalaman Muneeba suka dosa sai taс,
"Ni fa ban iya wannan shisshigin gurin
miji ba haka kurum bai neme ni ba in yi
ta masa sintiri har ma ya kare ya
wulakantani shine abinda ba zan dauka
ba Muneeba ta sassauta murya "Haba
dai ya wulakanta ki yanzun don mace
ta je inda mijinta yake sai ace tayi
shishshigi? Hakkinsa dake kanki zaki
94
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
sauke babu maganar kin yi masa
shisshigi kulka da cinsa da shansa da
gyara muhallinsa da biya masa
larurarsa ta aure duk yana wuyanki
mata biyu gare shi bai kai mata ace har
ya shiga halin da yake ciki ba in ni ina
jego ke me ya sameki da zaki barshi
cikin larura?.
Don girman Allah kiyi hakuri
koma laifin me yayi miki ki bashi
kulawar da ta dace a matsayinsa da
mijinki don kada rashin hakan yasa yaje
ya tsinduma kansa cikin hallaka sannan
abin mu zai zo ya dama daga baya”.
Suwaiba ta dubi Muncebas sosai
tace, "Oh gaya miki yayi bana sauke hakkinsa da ke kaina? To bari kiji in
gaya miki ni ban shiga hakkinsa ba
shine ya tauye mini nawa hakkin kuma
sai Allah ya sakamin don yanzun kusan
shakara biyu kenan rabon da ya bani
nawa hakkin tun kwanciyarsa ciwo har
ya warke ga shi nan ke har kin sami
ciki kin haihu ni ina zaune kamar ya aje
hoto sai dai ya kale ni in zancen
95
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
gaskiya ne aini aka cuta shekara biyu
sai kace an sassakani da ice".
Zancen ya girgiza Muneeba ya
kuma jefa ta cikin mamaki sai ta shiga
ba Suwaiban hakuri don bata yi
tsammanin al'amarin har haka bane,
"Kiyi hakuri don girman Allah Wallahi
ni bai taba gaya mini komai game da ke
ba wannan ba halinsa bane ke ma kin
sani baya hrar wata irin wannan da
wata, wannan al'amariun naku sirri ne
don Allah kada ki sake fadawa wani
dolensa ya gyara in dai yana tsoron
haduwarsa da Allah kiyi hakuri laifin
da na dora a kanki ashe shi ya janyowa
kansa shiga wani hali ki daure kije ki
duba jikinsa isha Allahu zai gyara".
Jikin Muneeba a sanyaye ta baro
dakin a zaune ta sami Mujeeb da
(Laptop) a gabansa yana 'yan danne
danne ta zauna a gefensa tace, Ah jiki
yayi sauki har an hau internet wane
labaran duniyar ka samo mana?.
Hankalinsa na kan Lato din yace
"Labaran Lahira na samo matso ki ga
96
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
wa'azin dana karantawa jikina ya mutu
Rwarai tunatarwa ce akan lahira da irin
bala'o'in dake tattare a filin kiyama ita
ma jikin nata har yayi la'asar tun kafin
ta duba tunatarwar ta matso jikinsa
sosai ta jingina da kafadarsa tana
karanta tunatarwa kafin ta yi masa
maganar dake cin ranta.
"Abokin rayuwa wata magana
nake so muyi ina son ka fahimceni
kuma kada kace na yi maka shishshigi
so nake kayi gyara don an sami baraka
kuma daga gurinka 6arakar take shin
don girman Allah Allah me Suwaiba
tayi maka har ka dauki mummunan
mataki akanta wanda zai iya jefa
rayuwarta da taka cikin matsaya?.
Ka fa yi hakuri kada kace nayi
maka shisshigi so nake kai da kana ka
yi gyara". Ya soma kada kai kafin ya
dube ta yace. Gaya miki tayi mun sami
sabani ni da ita, ko ko hasashe ne kika
yi? tace, ba hasashe na ke ba zuwa nayi
na gaya mata baka da latiya da shine ta
ji haushin wai baka gaya mata ba, ni
97
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
kuma sai na dora laifin a kanta na
yadda bata kulawa da kai don ya
kamata ace itace zata fara sabin baka da
lafiya bawai ni în gaya mata ba wannan
laifin dana dora mata shi yayi sanadin
da ta gaya min matsalar dake
tsakaninku, abin ya bani matukar
mamaki wai ka kaurace mata kusan
shekara biyu kenan tun kwanciyarka
ciwo, in har haka ne ka zalunceta ashe
ma bata da laifin komai akan halin daka
shiga.
Ka sai dai rashin sauke, wannan
hakkin yana kawo babbar matsala ga
ma'aurata raini zai iya shiga tsakaninku
da rashin daraja juna, in ma laifi tayi
maka shekara biyu ai yayi yawa a
matsayin Punishment, in ma horarwa za
kayi mata ba'a so ya wuce na watanni
hudu.
Rufe Lato din dake gabansa yayi
sannan ya juyo ya fuskanci Muneeba
don yaji dadin yi mata bayanin dake
bakinsa". Yanzu ita da kanta ta iya yi
miki wannan bayanin don bata da
98
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
kunya? Wato duk yadda naso in rufe sirrin dake tsakaninmu sai ta sa na bankada shi kenan don in ban hakan
nayi ba ke dinnan ba zaki yarda cewa
bani ke danne hakkI ba tunda ta tsara
miki nata bayanin kuma kinyi amman
da bayananta dari bisa dari to bari kiji
abinda banso kowa ya sani ba wanda
shine ya zanío shamaki a tsakani na da
ita"
Ya warwarewa Muneeba hirar da
ya/ riski Suwaiba nayi da bakuwarta
Larai ranar daya fadi da abinda
kunnuwansa sukaji har abin ya firgita
shi wai shi Mujeeb matarsa taje tayi fasikanci da wulakantaccen mutum irin
boka, sannan ta hada janabarsa da ta bokan duk hakan baiyi mata ba sai da ta
ciyar dashi naman daya kwana a
gabanta wannan alamari va bashi
tsoro, ya firgita -da shalanín mata irin
marasa tsoron Allah shi yasa da ya
warke daga ciwo da ta zamo sanadinsa
ya Kaurace mata sam yaji Kyamar
kuşantarta yake yi harzya kafa mata
99
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
sharadin sai ya kaita an gwada jininta
in har bata da wata cuta to zai iya yin
hakurin ci gaba da zama da ita
albarkacin diyarta Waleeda ita kuma
taki yarda suje asibitin da yayi hikima
ma ya kaita gudowa tayi shi kuma
Wallahi ya sha alwashin ba zai taба iya
hada makwanci da ita ba har sai ya
tabbatar da ingancin lafiyarta in kuma
bah aka ba to sai dai tayi ta zama hoto a
gidansa shi bai zalunce taba itace ta
zakunci kanta.
Shiru Muneeba tayi tana aikin
sauke numfashi kawai cikin tsananin
mamaki da tsoron kila dukansu ma sun
kamo da cutar tunda ai an gauraye da
juna tun kafin ta bar gidansa tayi
magana a tsorace "mu din yanzu ka
tabbata mun tsallake siradin da kake
ganin ita tana kai? Ko kai kana da
tabbacin taka lafiyar?.
Ya gyada kai kwarai ina da
tabbacin lafiyata Kalau bani da wata
cuta don nasa an gwada jinni na a
zuwan da mukayi Egypt sai dana
100
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
tabbatar da hakan sannan naci gaba da
mu'amalata dake zaki iya tuna hakan ta
faru".
Ta ce to me yasa ni bakasa an yi
mini ba ka barni cikin duhu alhalin ina
gidan nan lokacin da abin ya faru tunda
shine masomin juya mini baya daka yi?
Ya ce "Ke ma an yi maki gwajin a
Egypt lokacin da suka yi miki gwajegwaje an kuma bani sakamakonki
lafiya kaulau kike abinda yasa ban gaya
miki ba don kada in tada miki hankali
ko ki dameni da son sanin dalilin da zai
sa ayi miki gwajin alhalin banason
kowa yasan abinda Suwaiban tayi mini.
Yanzu kuwa lokaci yayi da zan gaya
miki tunda har ta a iya budar baki ta
fadl cewa na tauye mata hakkInta
alhalin nine tayi mini cutarwa da ba
kowane namiji za'a yi masa ya iya
hakurin cigaba da zama da irin wannan
macen ba.
Saboda haka, ki kyaleta duk
lokacin da ta shirya cigaba da zaman
aure dani to dole ta yarda muje ayi mata
101
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
gwajin, in kuma bata shirya ba to tayi ta
zama haka na riga na bata zabidole
Muneeba ta bar al'amarin a haka, dón
kuwa ta san mijinsu yayi nan mijin
kokari kuma yayi matukar hakuri a irin
wannan badakalar da aka yi tafka masa
wadda har ya iya juriya bai saki
suwaiban ba.
Al'amarin ya kada hantarta sosai
na irin shige-shigen da Suwaiba ke yi
ita da uwarta har abin na nema ya sa su
kauce hanyar Allah sun ma riga sun
kauce tunda abin har da bada kai ga
boka da ba miji naman da ya kwana
cikin gaba alhalin ance duk macen da ta
wanke gaba taba miji ko ta bashi wani
abu da ya fito daga gabanta kafin
mutuwarta sai tayi ta tsigar gashin
gaban nata har sai yayi jinni kuma a
gaban mutane har hakan sai yayi
ajalinta.
To don Allah ko wannan kadai
ma ai ya isa abin tozarci ga mace, balle
kuma idan anje gaban Allah me macen
data aikata irin wannan halin zata cewa
102
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
mahaliccinta? Don girman Allah mu
tsare imaninmu muji tsoron Allah mu
tsarkake zukatarmu mu yi yaki tamu
kada mu yarda mu biye mata ta kaimu
ga aikata sabo irin na Suwaiba ko
makamancin akan ki mallakje miji ko
kisa a wulakanta kishiya ko a koreta ki
zauna ke kadai da 'ya'yanki.
In kuma asirin baiyi tsawon
kwana ba wani sanadi yasa ya karye
irin yadda ya faru da Suwaiba sai abin
ya juya kanki kinga baki sami riba
yadda kike so ba, in ma asirin ya
dawwama iyakacin a nan duniya kin
gyara duniyarki tayi miki kyau kin 6ata
lahirarki wadda itace matabbata, inda
zaki rayu, rayuwa mai dadi ta har
Abadan abandon.
Wasu matan kuma gani suke ke
duk baladar da suka aikata a duniya ai
zasu tubane kafin su mutu, sun manta
ita mutuwa bagatatan take zuwa wa
mutum ba tare da yi shirya ba shi yasa
ake son kullum kayi shirin tafiya
kiyama kada kayi tunanin kaifa ba
103
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
yanzu ba alhalin a rana ita mutuwar
tana kawo maka ziyara sau saba'in
kuma kankanin sanadi zai iya saka
mutu sannan ko ba ciwo ma zaka iya
mutuwa saboda haka don girman Allah
mata mu gyara al'amüranmu
musamman masu kishiyoyi su sukafi
daukar gidan bokaye da malaman
tsubbu guraren kai kukan su sun manta
cewa idan matsala ta dameki kika daure
kika hana idanunki bacci kika gayawa
Allah zaiyi miki maganin ko wace irin
matsala ke gareki, amma fa idan kina
da tsarkin zuciya tare da yakini, a
zuciyarki don yawanci abinda yasa
Allah baya amsar addu'armu kenan
rashin tsarkin zuciya kullum burinka ka
cuci Musulmi dan uwanka sannan
rashin yakinin a zuciya sai ka dinga
ganin idan kayi addu'ar shin zama ta
amsu kuwa?.
To wannan rashin sa yakini a
zuciyar yanasa Allah yaki amsar
addu'arka saboda haka sai muyi gyara
akan al'amuranmu dogon nazarin da
104
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Muneeba ta zauna kenan tana yi a
zuciyarta.
Ranar Munceba yini tayi tare da
mijinta tana jinyarsa tare da bashi
kulawa yadda ya kamata, ta so ta bar
Suwaiba ta zauna tare da shi sai taga
tana zuwa ta gaishe shi tayi tafiyarta
bata sake dawowa dakin nasa ba shi
yasa ita ta yi ta sintirin kula dashi.
Ita kanta Goggo Hinde sai da
al'amarin na Muneeba yayi ta bata
sha'awa na yadda taga ta hana kanta
sakat wajen kula da lafiya mijinta nata
har suka dinga hirar da Laminde cewar
Lallai in ba asiri ba wane namiji ne zai
sami mace mai kula da al'amuransa irin
Muneeba har ya iya juya mata baya
yace baya sonta?.
Shi dinma kulawar daya samu ne
ya sa ya dada narkewa ba wai don bai ji
sauki ba ya fi son yayi ta ganinta ne
kusa dashi don hakan na kara masa
samun natsuwa matuka.
105
WATA KUSAN 4
Rahmatu Hassan Zaria
****** ****** *****
Kwana arba'in kenan cif da haihuwar
Muneeba a wannan safiyar kamar
yadda yake a al'ada anyi su waina
fanke kosai harda su cincin da nakiya
anata rabawa na yin arba'in Goggoninta
nata guda biyu Goggonsu tan an gidan
da kanwarta Goggo Hinde sune suke ta
wannan hidimar da misalin biyun rana
goggo Hinde ce ke zaune a falon
Muneeba tana ta saka kayan sawanta da
jume ya wanke ya goge ya kawo a
Jakarta babba. Muneeba ta kara
dubanta a karo da dama sannan ta sake
yi mata magana wai don Allah
Goggonmu da gaske tafiya zaki yi
gobe".
Ta soma kokarin zage Zif din
Jakar tana cewa tafiya zan yi mana
Muneeba kwana nafa arba'in a gidan
nan can na bar gida sai yara da matar
yayanku ayyukan gida sunyi mata yawa
sannan ni ma aj na koma in kula da
nawa gidan ko".
106
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
dafa kanta kuma babu wanda ya isa ya
fada ki dage da addu'ar nemawa kanki
da mijinki da 'ya'yanki tsari kullum
kiyi addu'a ki tofa musu kiyi musu a
ruwan shansu Insha Allahu Allah zai
kareku.
Muneeba dai sai da tayi nasara
akan Goggo Hinde har ta a yarda zata
kara kwana goma sannan ta koma
Dukku. Tana ba Bilal Nono Mujeeb ya
kira wayarta yake tambayarta Madan
yau ko fa kira na baki yi ba tunda na
tafi Ofis? Tace yi hakuri abokin rayuwa
yau hidima tayi min yawa ne amma
Wallahi kana cikin zuciyata kasan yau
mukayi arba'in sannan ina nan ina fama
da Goggo Hinde tace Gobe-gobe zata
tafi Dukku yan zu dai na shawo kanta
tace zata kara kwana goma Wallahi na
riga na shagwabe komai yimin suke yi
sun sangartani kofa nono su Bilal zasu
sha idan ina Bacci ba za'a tashe ni ba
sai dai a karasu a nonon su sha ga
yanzun idan suka tafi dukkansu wa zai
yi min wannan gatan? Wallahi ko Pant
109
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
na cire goggo ke wanke min wannan
gatan aiba kowa zai min ba.
Ya ce ni dinnan idan kika barni
da ma zan nuna miki gatan da ya zarta
nasu, don ni har goyaki zan dinga yi
zan tarayyeki tamkar yadda naga kike
tarairayyar su Hilal da Bilal har ma
zanyi mii fiye da yadda kike musu ko
akwai me iya goya ki yanzu in bani ba?
Tayi dariya tana girgiza kai tamkar
yana ganinta,
"Wannan hirar tafi karfi na mu
canza wata", au kinsan zata fi karfinki
meye na gaya min su Goggo sun
shagwabaki alhalin ni na fi kowa iya
shagwabaki, ko