Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 8
da mai yi miki irin gatan da nake maki? Sai tayi saurin canza hirar tasu, "Ka ga yadda yaran nan yau naga sun kara girma da wayau tamkar sun yi watanni kaga yadda suke wangale baki suna dariya idan ana musu wasa, babu wanda zaice 'yan biyu aka haifo su" ya ce "Nima girmansu da wayonsu yana bani sha'awashi yasa ma naga ya dace yau 110 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria Munceba ta soma sharer kwalla tace don girman Allah Goggo ki dan dara kwanaki nidai inason zamanki a gidan nan sanna ga yaran nan ya zanyi da dawaniyar itama Laminde yau zata tafi. Goggo tace, "Amma ai Innarki Amina tace zata kawo miki wata mata da zata dinga yi muku aikin gida ga kuma yarinyar nan Karime itama tana da kokari har ta iya goyon yaran nan to me kuma ni zan zaune inyi miki. "To ki bari har Inna Amina ta kawo matar sai ki tafi shima Yaya Mujeeb dana gaya maşa kince gobe za ki tafi cewa yayi wai me zaki yi a Dukkun da kika kosa ki koma shi inda zaki yarda da kinyi zamanki a nan tare da Goggo in yaso ki dauko autarki ya canza mata makranta don ya san tunaninki akanta yake don kin baro ta a Dukku". Goggo Hinde tayi murmushi tace "Su can yaran ne bama zasu yarda ba sannan zamana da Goggonku ba zai yiwu ba kinsan halina na fadar gaskiya 107 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria komai dacin ta idan na zauna a gidan tsiya zamu dinga yi da Goggonku saboda abubuwan dake faruwa a gidan akwai gyara zanso kuma ayi gyaran to tan an zamu bata da ita shi yasa ma gara mu zauna nesa-nesa koda yake yanzu naga ta soma gyarawa har tana iya yiwa Suwaiba fada idan tayi ba daidai ba sabanin da can komai Suwaiban tayi daidai ne bata laifi a gurinta kedai ki tsayawa Allah ki ci gaba da addu'ah yadda mijinki ke sonki Allah ya karkato miki da zuciyarsa gareki kada ki yarda kiyi masa rikon sakainar kasha kici gaba da kyautata masa irin yadda naga kina yi masa tabbaas hakan ne yake dada kara masa kaunarki a zuciyarsa har suke ganin asiri ake masa alhalin ga inda ake masa asirin nan ta kuma sani amma har vau ta kasa yin wani hubbasa don ceto danta daga sharrinsu ita dinma gashi nan bata tsira a gurinsu ba irin yadda yarinyar nan ke mata fitsara da wani ne da yanzu duniya taji su ta debo ruwan 108 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria ki amshi girkinki kamar yadda na gaya miki jiya tunda yaranki sun yi kwariu kuma kina da masu kula miki dasu ba zasu hana ki kula da mijinki ba". Tayi saurin cewa, Ina ganin bari mu yi sallama don hirar taka na da tsawo kana ta cinye kudin wayarka idan ka dawo gida sai muyi maganar yace "Ina ruwanki da kudin danake kararwa a waya inada isasshen credit din da zamu iya kwana muna magana saboda haka kin dai ji umurnin na yau zaki amshi girkin don na gaji da rikon sakainar kashin da ake yi min sannan bana son cin girkin mai aiki ki tabbata abincin da hannunki ya dafa zanci tace "Sha kuruminka abokin rayuwa yau girkina zaka ci don ni ko kwanan cin tuwonka bazan yarda wata ta wanke maka idan bani ba hakan shi ne samun lada ga duk wata matar aure a gidan mijinta to balle har in bari mai aiki ta girka abinci kaci idan nayi hakan na rage wa kaina kima da daraja da dumbin ladan da zan samu a gurin 111 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria Allah saboda haka ruwa kaďai na amince kasha a Ofis nayi shirin tarbaka da cima mai kyau ya kyakkyale da dariya yace "Banda cima mai kyau sai kuma meye mai kyau da zaki tanadar min kinsan na cancanki ki tarbeni fiye da haka? Tace me kake ci na baka na zuba? Ka kwantar da hankalinka duk abinda kake so yau ka riga ka samu yayi dariya nishadi "Kin tabbata abinda kike fada haka yake har zuciyanki ba shigo-shigo ba zurfi kike yi mini ba? Don kada kisa in sakankance inyo kyakkyawar damara ki barni cikin tagayyara. Tace "Haba haba ya za'a yi inci gaba da barin ka kana ta watan gaririya kamar wani mara gata alhalin kana da gatanka kai dai sai ka iso gida kawai sai ta kashe wayar don tasan in ba hakan tayi ba to zasu dauki dogon lokaci suna wannan hirar don an soso inda yake masa kaikayi kamar yadda ta fada hakan ce ta kasance don kuwa da kanta ta shiga kicin dinta na ban garenta 112 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria tunda kowa tana da kicin dinta sai kuma na tsakar gida da suke girkin sha'ani kona Sallah to anan matar da dauko musu tun haihuwar Munceban take musu girki. Muneeba ta zauna ta shirya masa abinci iri-iren da ta san yana so da abubuwan sha masu dan Karen dadi. Tun safe dama ya shaida mata ba zai dawo ba yau sai yamma ko bayan Magrib saboda yana da ayyuka sosai a sabon ofis dinsa sannan zzasuyi mitin, sai ta ganshi kawai. Hakanne ya bata damar da tayi duk ayyukanta a saukadae duk inda tabi Goggo Hinde na binta da kallo cikin sha'awa don al'amuran Muneeba na birgeta in dai wajen kula da miji ne da hidimarsa sam bata da na biyu". Lallai ta yarda ilimin bokó da na addini yana da muhimmanci ga rayuwar dan Adam don duk abinda mace mai ilimi za ta yi sai kaga yana da bambanci dana mara ilimi nesa ba kusa ba idan ta zauna tana hada alk'amuran 113 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria Muneeba dana Suwaiba sai taga Muneebar tayi fintiunkau ta zarta Suwaiba iya komai nesa ba kusa ba, in ma banda Kadarar aure data 'ya'ya kwata kwata Suwaiba ba tsaran auren Mujeeb bace a yadda yake dan kwallisa dan gayu mai ilimi ga abin hannu da daukaka Allah ya bashi ina shi ina auren irin Suwaiba da ko Sakandire bata tsaya ta gama ba. Bama wannan ne matsalar ba sai kaga yadda take tafiyar da al'amuranta a gidan aurenta babu wata natsuwa ko birgewa sai kishin irin na Jahilan mata na yawon gidan bokaye da malaman tsubbu, dole ne al'amuran Muneeba su birgeka idan ka zo gidansu komai cikin tsari da bin dokokin Allah bayan ta fita wanka ta isa kan sallaya ta gabatar da Sallah Magriba tana zaune tana lazimi ne Mujeeb ya shigo dakin rungume da Hilal a kafadarsa yaron nata tsala ihu. Ya iso ya dora mata shi bisa cinyarta yace "Ashe ma kin idar da Sallar baki ji yana ta ihu kuka bane? Ta 114 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria amshi yaron tana cewa banji kukansa ba daga ina ka amsko shi? Can na ganshi goyc bayan Karime a tsakar gida tana sintiri dashi naga su Goggo duk 99 Sallah suke suma". Ta soma kokarin bashi Nono amma sam yaki amsa a tunaninta kio zuciya yayi don b a bashi nono a kan lokaci ba yake kuka amma ina duk wata dabarar tayi amma yaron yaki kama Nono. Mujeeb dake gefensu yace "Wai ko dai baya da lafiya ne? ta ce, to ni kam ban sani ba”. Goggo Hinde ce ta shigo dakin tana tambayarsu "Wai ya akayi ne kika kyale yaro yanma kuka kina jinshi bazaki bashi Nono ba? Ta mikawa Goggon shi tana cewa "Wallahi na bashi yaki amsa kila dai wani abu ke damunsa". Goggo ta soma bincikan yaron ta taba kunnensa taji bai nuna alamun kunnenna masa ciwo ba sai ta hura masa cikin kunne sai ya lafa da kukan tana dainawa sai yaci gaba ta dubi WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria iyayen nasa da sukayi cirko eirko suna kallonta tace cikinsa ke ciwo yau hala bai yi kashi bane. Muneeba tace "Ai kuwa baiyi ba ina jin ko jiyama baiyi ba Goggo ta duba cikin nasa har ya dan Kumbura ta kwalawa Karime kira da take waje tace ta kawo mata toka, tana kawo wata diba ta shafa a cikin yaron sannan aka bashi (Grae Water) yana sha sai ya soma sakin kasha cikin Pampers sai yayi shiru ya daina kuka Goggo Hinde kasha ne da baiyi ba kwana biyu yasashi ciwon ciki sai ki dinga lura idan suna kukan daya wuce misali in kunnc ne kina tabawa zakiji sun sun tsanyara ihu in kuma ciki ne da kin hura kunnensa zakiji sun daina kukan sai ki kiyaye" Ta mika ma Muneeba yaron tace ki shiga ki wanke masa kashin". Ta amshe shit a shiga bayinta ta wanke masa sanna ta fito ta canza masa kaya ya dauke shi suka fice zuwa dakin Goggo. Bayan Sallar Isha'i tana zaune gaban Madubi tana gyara daurin 115 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria dankwalin da ta ke tsarawa kanta ne Mujecb ya yi sallama ya shigo Dakin baccin nata rungume yake da Hifal din yana bacci bisa kafadarsa ta dube su ta cikin madubi ba tare data juyo ba ta ce wai ina kuka shige ne tun dazu". Ya kwantar da yaron a dan gadonsa yasa bargo ya lullubeshi sannan yace dakin Goggo na barshi na wuce yin Sallar Issha'i dana dawo ne na iske har yayi barci a bayan Goggo. Tace kai kai yau Goggo ce da goyo lallai jika wahal da kaka ita da ke fama da kanta ya zo ya rankwafa a bayanta kansa ya kwantar bisa kafadarta suna kallon juna ta jikin madubi yace wannan irin kashe gayu da baza kamshi da kike yi ai sai kisa in yi tabargaza gaban Goggo Hinde ki dan sassauta min don Wallahi kin tsuma ni da yawa". Ta yi murmushi tana kallonsa tа madubi tace a hakan ne zan sassauta maka kana bibiyata? Ai Goggon cewa tayi in tattala mata danta inyi maka duk kulawa irin wadda ta dace macen 117 MATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria kwarai ta yi wa mijinta na sunna to ni kuwa sassaucin me zan yi maka ai sai dai in dada susutaka cikin Rauna. Ya saki dariya cike da nishadin jin kalamanta yace da gaske Goggo Hinden ce ta ce ki kula da ni ki tattala mata danta? Aini daukata gargadi take miki tare da jan kunni a kan kula da yan 'ya yayanki da basu yi kwari ba, a she hudubar tattalina take miki ban sani ba gaskiya Allah ya yi mata tukwici da gidan Aljannah, ke kuma Allah ya baki juriyar kula da ni sakamakon hakan mu kasance a aljanna kina jan ragamar tanba na can". Ta amsa da amen en abokin rayuwa nagode da wannan addu'ah ya mike tare da dagota suke mike a tare tana tallafe a gefen kafadarta yace "Yunwa fa nake ji sosai ki zo ki bani abinci". Hancinsa na cikin wuyanta yana shaker kamshinta yake maganar "na riga na shirya komai bisa teburin ein abinei falonka muje ina zuwa". Ya fice ya nufi dakin nasa ita kuma ta kara gyara fuskarta ta sake fesa 118 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria wasu irin turaruka masu sanyin kamshi da. ke kashe jikin wanda ke cikin nishadi ta fesa a wuya da bayan kunnuwänta sannan ta dauko na baki ta fesa ta yi sauri ta kunna bona ta saka gawayin kanti yana kamawa ta dauko hadin da Goggo Hinde ta bata da take yin tsugunno dashi tun farkon da ta haihu kwanson citta mai 'ya'ya ne auduga sai a daka a cakuda da turare mai kamshi sai a ringa tsugunawa ana turara gaba da shi yana hade mace ta koma fiye ma da da, to yau ma shi tayi don bata son idan mijinta ya dawo gareta ya ji ba yadda take ba hakan na haifar da Baraka tsakanin ma'aurata da yawa matsalar da ake samu kenan ga matan da suke haihu rashin gyara. alhali rabi da kwatan ni'imar mace yana zubewa a vavin haihuwa sannan mutum ya fito ta jikin mace ai dole guri ya bude idan aka kula da gyara gurin sai ya koma daidai babu matsala tana gamawa tayi saurin zuwa gurin mijinta a lokacin su Goggo na falo suna ta kallo 119 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria a tauraron dan Adam har ya zuba abincin ya soma 'ei ta same shi ta ja kujera daf da shi ta zauna tana cewa "yi hakuri harka Kosa ka zuba abincin" ta dauko kofuna ta zuba masa lemun 'ya'yan itatuwan data hada da kanta daya kofin kuma ruwa ta zuba masa ta aje gabansa. Ya kai loman abincin bakinsa ya lumshe idanu saboda dadin dandanon abincin ya ce, "Dandano girkinki ya kara dadi fiye da kowane lokaci meye sirrin? Ita ma idanu ta lumshe masa tare da yin walainiya da idanunta sannan tace babu wani sirri illa Karin experience dana dada samu gurin yan tsofafaffi nan da nake tare dasu kadai san Goggonmu. Hinde kawai iya girki sannan ga Laminde gwana ce gurin iya girki tamkar karatun allonta akan koyon girki tayi shi ya sa na amfana sosai a dan zaman da nayi dasu gashi har miji na yana yaba mini ya jinjina kai, kai Alhamdulillah da wadannan dattijan 120 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria alhairi Allah yasa alkhairan da zan iske tare dake su zarta dadin wannan girkin. Shiru tayi masa yayi masa nuni da zai sha ruwa don ya kasa ci gaba da magana illa taunar abinsa kawai yake yi ta dauki tambulan din ta zuba ruwa ta kai ruwan bakinsa ya sha sannan ta aje yace ya kukayi da Laminde kin gaya mata na ce tabar tafiyarta sai gobe tace eh na gaya mata tace Allah ya kaimu. Ya ce Akwai sayayya dana yi mata suna Boot din motata na manta ban ce Jume ya kwaso ba gobe sai ki duba ki gani yayi Muneeba ta fadada murmushi tace Wallahi ko ban gani ba nasan kayan sunyi tunda na san halin mijina idan ya tashi yin alkhairi ba Kananan kudade yake kashewa ba balle ga tsohuwar da ta kula masa da 'ya'ya ta gyata masa mata Allah ya saka da mafificin alkhairi. ilYa ce "yanzun kudi kamar nawa kika ga ya kamata a bata tunda kinga ganin gida za ta je? Tace ka bata duk abinda ka ga ya dace matar tana da 121 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria alkhairai da yawa tana kaunata nima ina Kaunarta Wallahi naso mama ta bar min ita amma sai hakuri ta bani wai ita ma zata iya rabuwa da Laminden ba yace sai ki yi ta addu'ah Allah yasa wadda za'a kawo miki kiji dadin zama da ita fiye da Laminden ta ce Allah tunda babu yadda Allah ba zai iya kawowa mutum mafita ba". Suna yan hirarrakinsu har suka gama cin abincin sannan yace ta hada masa ruwan wanka lokacin da zai shiga wankanne tace Bari inje in duba yarannan kada su tashi ka san kuma babu wanda zai iya biyo ni nan". Tana shiga kuwa ta iske Bilal ya tashi Laminde na faman lallashinsa ta mikawa Munceba shi tana cewa Rigima yake ji Rila dan uwansa yake tayawa yau na bashi madara amma bai hakura bah.. Ta amshe shi tana cewa "Lallai yaro sham madara ai ya zama dole in baso kuke ku tsotseni ta ba ta shige dakin baccinta ta zauna bakin gado ta 122 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria soma bashi nono idanunta na kan Hilal da har yanzu yake baccinsa Lakadan ta san in ba ciwon cikin ne ya sake matsa masa ba to sai asuba zai farka yaran ke baccin da wuya ne su farka cikin dare shan Nono amma Subahi nayi duk zasu farka idan suka sha sai kuma zuwa takwas na safe idan za'a yi musu wanka. Har bacci ya soma dibarta daga zaunen da take Bilal Nono sai ta tashi ta je ta kwantar da shi a nasa gadon ta lullubeshi sannan ta canza kayan jikinta zuwa wata lallausar rigar bacci wadda iyakacinta rabin cinyarta sai ta daura zani a saman rigar kira ya shigo wayarta tana dubawa ta ga Mujeeb ne ke kiran tana dauka taji yace idan kin gama kula da yaran nima kizo ki kula da tawa larurar ina jiranki tayi saurin cewa kayi hakuri Wallahi nauyinsu Goggo Hinde nake ji sai in tsallakesu inzo gurinka in kwana? Me na yi kenan? Ya marairace "Bance kwana za ki yi ba, idan kika sallameni zaki iya 123 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria tafiya, zanyi ta hakurin rashinki kusa da ni har su Goiggon su tafi don zamansu na da amfani a garemu. Tace "sai yadda ta yiwu amma kada ka sa ran zuwana". Zai sake yin magana sai tayi saurin tsinke wayar tasu har ta a kwanta sai Goggo ah Goggo ashe ba ki yi bacci ba? Та се 'banyi bacci ba yanzu na idar da shafa'i da wutiri ki tashi ki tafi can gurin mijinki ki taya shi kwana kibar yaran nan gurina tun da basa farkawa koma sun farka suna da abincinsu sai su sha don ni bana son a sanadina a tauyewa wani hakkinsa. Muneeba ta dubi Goggo Hinde cike da mamaki tace, "Goggo ni me zan je in yi masa daga yin arba'in dina ina ce sai yaran nan sunyi kwari koda zan nemi inda yake? Goggo ta ce, "Wannan tsarin ki ne ko ko haka addini yace? Ina ce addini cewa ya yi da jinni ya dauke miki idan mijinki yazo da bukatarsa ki biya masa? Yaron nan sai sintiri yake miki tamkar zai yi miki 124 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria a Sujada ya ke bibiyarki don ma ganin idanunmu ne ya sa yake rage sintiri dakinnan sannan ki ce wani sai 'ya'yanki sun yi kwari wannan ba hujja bace al'adace da bata yi daidai da tsarin musulunci ba. Kin ganni nan ba tsohuwar kawai bace dole in dora ki akan hanyar da ta dace ko ko so kike yi a sake sake kwace miki shi saboda sakacin ki? Dole ki dage wajen kulawa da bukatocin mijinki kuma ki dage da addu'a wadannan sune makaman da zaki rike sosai in ba haka ba kina zaune sake da baki za a sake raba ki da mijinki tunda na lura shi me son a kula da shi ne. Tashi maza ki tafi ki kula da shi wa ma zai san kinje in banda shirmanki tunda ba kya son a sani ta soma nuku - nuku tana cewa ni fa Goggo tsoron ciki nake yi ina tausayin yaran nan shi fa ko a jikinsa dama 'ya'yan ya ke nema ba zai damu ba". Tace eh dama su maza ai ba sa damuwa to amma kema ba za ki zauna haka babu yan dabaru ina ruwan 125 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria lemon tsaminnan dana tace na baki a kwalba?. Ta ce "ga ya can na ajiye, ta ce "To ki tafi da shi kuna gama abin da za ku yi sai ki sha rabin dan karamin Insha Allahu duk abinda ya shiga mahaifarki za ki fitar da shi ko da cikin ne sannan irin wannan halayyar taki ta kan jefa mazaje ga zuwa neman matan waje alhalin mutum na da matarsa ta ki biya masa bukata saboda tsoron ciki ba ki san duk ki gama tsoron ba dare daya Allah kan yi bature ba. Muneeba duk sai ta ji kunya ta kamata amma ita Goggo sai bayani take mata ko a jikinta don Goggo Hinde irin matannan ne wayayyu duk da a karkara take tana sakewa dasu tamkar wasu jikokinta, sannan tana ba su shawarwarin da suka dace musamman akan mazajensu balle Mujeeb yadda ta ke ji da shi tamkar ita ta tsuguna ta haife shi saboda zumuncinta saßanin sirikar Muneeba Goggo Rahin. 126 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria A kunyacc Munceba ta dauki 'yan abubuwan da zata bukata tayi mata sai da safe ta wuce dakin mijinta wanda tana kallon kiraye-kirayensa a wayarta da ta sakata silent kin dauka ta yi ne don ta san tatsuniyar gizo ba ta wuce koki. A bude ta iske kofar falon nasa tana shiga sai ta maida makulli ta rufe yana zaune yana kallo a tauraron dan Adam idanunsa na kanta tana zuwą ta zauna a gefensa ya dubeta yana murmushi yace, ya aka yi kika fito ke da ke jin kunyar su Goggo Hinde? Ta ce Hmmm Ai Goggo Hinde ta gama farke min laya, samu na ta yi a daki tace maza na tashi na je na tayaka kwana har wa'azi fa ta dinga yi min ka ji dadin wannan Kauna da Goggo Hinde ke nuna maka ņi ko tausayi na da na 'yan 'ya'yan nan bata yi sai ma 'yan dabaru da ta koya min, tunda taga tsoron ciki nake yi ta nuna masa lemun tsamin nan tayi masa bayanin yadda Goggo Hinden tace ta yi amfani da shi 127 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria ya kyakkyale da dariya yace Allah sarki uwata wadda ta fi ta kowa, Allah ya saka mata da aljannar Firdausi shi yasa nima nake kaunarta kema ai ta taimaka miki baki da wata fargaba sai mu sha shagalinmu babu wani dar dar tunda an bamu dama kawai sai mu dama kin san Bahaushe yace babbar dama maganin nadama се". Rimot ya sa ya latse T.V. din ya dubeta ya ce "Mu je mu kwanta dama wannan kallon na rage dare nake yi akan dole don na kasa bacci sannan ba na ma gane me ake yi a tibin kallon kawai nake". Wata irin rayuwa suka gudanar a wannan dare wadda tana daya daga cikin ranakun tarihi a rayuwar aurensu wadda Mujeeb ya fi jin farin ciki a wannan darc saboda wani irin baccin nishadl da ya yi haka ya yi ta yi wa Muneeba addu'ar sa albarka tare da godiya wadda har ta a dinga. ba ta mamaki sai kace tayi masa kyautar aljannah. 128 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria A nan dakinsa tayi wanka ta saka wata doguwar rigarta dake dakinyana fita masallaci Sallar subahi ita ma ta yi hanzarin barin dakin zuwa nata dakin ajiyar zuciya tayi lokacin da ta isa dakinta ta iske su Goggo Hinde ko tashi basuyi ba 'ya'yan ta ma nata baccinsu ta tashi Goggo Hinde don su yi Sallar Subahi itama ta shimfida darduma ta tada Sallah tana zaune tana lazimi ne Hilal ya fara tashi taje ta dauko shi ta na cewa "Goggo sun farka halan sun sha madara? Ta girgiza kai "ya'Yan albarka ai babu wanda ya motsa cikinsu a tunanina ma Hilal zai tashi saboda ciwon cikinsa kuma shi ya riga yin bacci sai gashi basu tashi ba sai yanzu". Ta soma bashi Nono yana sha tana laziminta don a kalla tana son tayi ta lazimin na akalla awa daya bayan yin Sallar Subahi idan ka gama sai ka tashi kayi nafila raka'a biyu za'a kankare maká zunubansa ta riga ta saba kuma ko yanzu data haihu 'ya'ya ba zasu hana ta ba. 129 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria Daga masallaci Mujeeb nan dakinta ya shigo suka gaisa dasu Goggo Hinde da Laminde a lokacin ya tuna da kayayyakin da ya siyo da zai ba Laminde sai ya koma harabar gidan ya bude but din motarsa ya kwaso kayan ya wuce dakinsa ya kira wayar Muneeba yace "ki zo ki amshi kayan nan na Laminde ta mike ta isa dakin nasa ya nuna mata kayan. Turamen zannuwa ne guda hudu masu kyau sai sinkin sabulai da mayuka shafawa da su jakunkuna Omo sai shadda yadi Goma a Ledarta. Ta na gama duba kayan tace "kaya kam sun yi Allah ya kara budi an gode Allah ya saka da alheri ya dauko kudi 'yan dubu dubu guda ashirin ya mida mata yace ki hada mata da wannan ta kara don yinwasu hidindimum kin san yanayin zuwa ganin gida" Nan ma wata godiyar ta shiga yi masa ta kwashi kayan ta je ta kaiwa Goggo Hinde ta gani ta yi godiya tare 130 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria da sa albarka. Ita kam Laminde bayan godiya da shi albarka har da 'yar kwallarta. Da ya shigo ma da safe godiyar suka yi ta masa tare dasa albarka shi ma godiya ya dinga yi wa Laminden na yanayin dawainiyarta misalin sha daya na safe Direban ya dauki laminde tare da Sha Tara na arziki don Muneeba ma bata barta ba sai da ta kara mata wasu turamen zannuwa da sabulai har da kudi. Muneeba ta rakata gidan Inna Ameena suka dan yi yini sannan Direba ya je ya maida su gida daren wannan ranar kam Goggo Hinde bata ma yi wa Muneeba wani Tambihi ba ita da kanta tayi mata sai da safe ta tafi gurin mijinta tabar mata yaran. Kafin kwana goman da Goggo Hinde ta kara har Inna Amina ta samowa Munecba mai tayata kyla da yan biyunta duk daga Karime sai dai ba zata iya dawaniya kula da yara biyu ba shi yasa aka dauko matar ita Karime sai ta dinga yiwa Muneeba Shara da 'yan goge-goge sai 131 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria wanke kayan su Bilal din in bata komai kuma tana taya Baba Hajjo (Sunan matar) rainon su Bilal. Munceba na jin dadin zama da Baba Hajjo ba nan take kwana ba tana zuwa ne tun bakwan safe sai ta tafi da yama kuma direba ke maida gida macece mai sanin ya kamata ga ba ta shiga sabgar daba tata ba abinda ya kawo shi kawai take yi shi yasa Muneeba ke jin dadin zama da ita. ***** **** ****** Duk wani lungu da sako da Suwaiba da Hajiyarta zasu bi don shawo kan matsalarta da mijin ta abin ya gagare su sun yi yawon gidan Malaman tsubbu sun bi bokaye sune har wani kungurmin daji bisa tsauni gurin wani boka amma babu nasara saboda Muneeba kam ba ta yin bacci tana dagewa da tsayuwan dare kuma tana matsawa Mujeeb din su raya daren tare da yin ibadar Allah. 132 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria Suwaiba ta kwancewa Hajiyarta matsalar da take fuskanta da mijinta na kaurace mata da ya yi da Hajiyar taso jin Musababbin wannan wulakancin sai ba tayi shayin komai ba ta zayyane mata irin badalar da boka ya aikata da ita a zuwan da sukayi gurin Boka mai Bukka ba tare da sun san me ya faru ba. Hajira Harira ta ja uban tsaki "To me ye abin boye min don kin aikata dan wannan abin ni ko mutum da ransa yace na kwantar na yanke da wuka-zan iya in dai bukatata zata biya ina ganin ki tanadi kudi sosai muje Yola gurin Hajiya Badawiyya ta kaimu gurin nata bokan kin dai ga yadda take damawa miji da kishiyoyi sai yadda tayi dasu binta suke tamkar rakumi da akala kо bawa da uban gidansa kema haka nakeso inga kina wannan damawar don yanzun mijinku kudi yake samu ba Kananan kudade ba tunda har suke kokarin bude kamfanin hadin guiwa shi da abokin kasuwancinsa. 133 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria Ke kina zaune sake da baki sai dai aga abin arziki gurin kishiyarki sai kace ke ba matarsa bace ai dole ya gane bayi da wata dabara muddin yana aurenki amma fa kiyi kokari ki same shi kice kin yarda a je ayi gwajin don ina ga baki da wata cutar komai da kina da ita da yanzu ta bayyana shekaru fa ya fi uku ki je kuyi kawai yaki ai dan zamba ne sannan shi zaman aure ba zai taba yiwuwa haka ba ita kuma mallakar miji da kika gani sai in ana tarayya ne ake samu a mallakeshi ta hanyar dan dabaru in ba haka ba yaushe ne kunyi nesa da juna zaki sami kansa". Wannan Karfin guiwa da Hajira Harira ta bata shi ya dada karfafa mata guiwa a wani yammaci bayan ya dawo Ofis ta je ta same shi tayi masa sannu da zuwa, sannan tace dama zuwa nayi don muje asibiti ayi mini gwajin da kace don ni na gaji da zama haka kamar hotó. Sai da yaja lokacikafin yayi-mata magana

Chapter 5 of 8