tunda an roki
Mujeeb ya barta ta je wankan gida yace
sam bai yarda ba ko dakinta na Dukku
ma yace bai yarda ba gara su zauna a
Gombe tunda ga Goggo nan in yaso a
samo wata cikin 'yan uwa da zata
zauna das u tana musu wanka.
Yanzun wa kike ganin a nan
Dukku zata je ta zauna da masu jegon
saboda kula da su wajen kwana da yi
wa Muneeban wanka nan dai zan tura
Laminde zata dinga sa musu ruwan
wanka da yin wasu yan ayyukan.
Innarsu Muneeba ta ce 'yanzu
Goggonsu Hinde ta taho ita zata zauna
a gurinsu zata dinga yi mata wanka da
yiwa jariran wanka kinga ita Laminden
sai ta dinga sa ruwan an gode Allah ya
kara zumunci" Ta ce Ameen Allah ya
raya mana su ya ba uwar su Lafiya.
Tun da Muneeba ta dawo gida
kullum gidan cika yake da jama'a yan
uwa da abokan arziki tamkar a ranar
53
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
ake yin taron suna sai aka samo wata
Kwararriyar mata ita ce ke yin girkin
gidan Suwaiba ta ce ba zata iya girki
mai yawa ba gara a nemo wadda zata
yi.
Muneeba tana jin dadin zaman
Goggo Hinde tare dasu saboda yadda
take kula dasu ita da jaririranta don
idan dare yayi cewa take Muneeba tayi
baccinta ta barta dasu ko kuka suke yi
bata tashinta don ta basu nono sai ta
kyaleta ta basu ruwan dumi da gulukos
ta goya daya ta saba daya tayi ta
jijjigasu har suyi bacci shi kanshi uban
'yan biyun kulawa ta musamman yake
nuna musu ita da 'ya'yan in har yana
gida to yana nan manne a dakin
baccinta tare dasu ko 'yan barka ne
suka zo ba ya fita sai dai akai musu
varan falo Goggo Hinde tun tana
korarsa tana masa tsiyar. wannan
binbini har taa hakura ta kyaleshi.
In kuwa ya shigo da daddare
bayan Sallar Issha to sai ta gaji idanta
ga Goman Dare ta wuce tace masa ya
54
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Gyaran da ta yi wa fuskar ta sai
ya maidata yarinya danya shakaf har sai
da Goggo Hinde ta tanka kai 'ya'yan
zamani sai a barkü yanzu danyen jegon
naki kika zauna kike irin wannan
kwalliyar don jawo wa kai jidali ko? Ni
nan uwarki sai da kika birgeni balle shi
wanda kika yi dominsa Wallahi ki kula
da kanki ki tausayawa yarannan don
mazan nan ba kunya gare su ba duk
hanyar lallaba sun santa iyakaci idan
kika biye masa kika sami ciki ke zai
bari da wahala babu ruwansa gara ma
ki sani ni kam na gaya maki.
Jikin Muneeba yayi sanyi tace
"Ni fa Wallatni Gaggo ba don shi nayi
kwalliyata ba, na dai riga na saba ne,
kuma ina nake binshi kinja gani dai shi
ke zuwa nan kuma akan idonki
'ya'yansa yake biyowa ni ba ruwana
don bana ma zuwa dakinsa".
Goggo Hinde ta murmusa tace In
ma 'ya'yansa yake biyowa ke ma ya
kusa ya biyoki in dai namiji ne ba yaga
67
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
kinyi garau ba kwadai ji da shi ni babu
ruwana.
Munceba ta fara kukan shagwaba
tana cewa "Ni dai babu ruwana gara ma
ki hana shi shigowa nan din 'ya'yanma
idan yana son ganinsu ga Karime nan ta
dinga kai masa su dakinsa kwalliyar ma
daga yau zan daina yi.
Laminde ta ce, "Ki kyaleta kawai
ta yi kwalliyarta Hajiya Hinde tunda
gidan nan wa kika ga tana masa
kwalliya inba ita ba, mazan nan na
zamani gara da hakan yadda yake ganin
mata iri-iri a gurin aiki ko cikin gari
gara idan ya dawo gida shima ya sami
nasa abin kallon ya ji dadi shi jego ai
bazai sa ka zauna ba kwalliya ba. Kina
dai gani da ya dawo gidan nan sai yazo
ya ganta ita 'ya'yan han sannan ya ke
samun natsuwa in da basa kwalliya
suna birgeshi yaushe ma zai damu dasu,
nan fa idan yazo ya makale sai kin kore
shi yake tafiya hakan inace kulawa ce?
Ki barta kawai taja hankalin mijinta
gareta?.
68
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
kuma nayi daga zuwa na an watso min
wannan uwar hararar mai makon ki tare
ni da murna"..
Ta juya suńa fuskantar juna
sannan tace Ai Wallahi kin kyauta
yanzu tsakaninki da Allah yau nme ya
kamata kizo? Jiya fa mukayi zaki zo
don ma kada in dameki shine har da
kashe waya, ba komai zan rama".
Murja ta riko hannuwan ta ta ce,
Afuwan aminiyata Wallahi laifin
yayanki ne tunda ya ga na matsu in taho
jiyan sai ya hana ya fake da cewa
Innarsu ba lafiya ('Yarsa) in bari ta
kara samin sauki zuwa yau zazzabi ne a
kawai kin dai san halin mazan nan da
kulafuci gay a can waje sai da ya biyo
ni
Muneeba ta kai mata duka lallai
yarinya yayan nawa kike cewa haka.
zan kuwa gaya masa". "Gaya masa din
ai ba zai iya ragewa ba dọn ni din ba ta
wasa bace suka yi dariya., Murja ta
tashi ta shige cikin dawayen Munecba
57
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
dake cike da gidan sukaci gaba da
gudanar da abubuwan da ya dace.
Ranar Suna yaran an canza musu
suna Hassan ya ci sunan Bilal Hussaini
kuma Hilal sunaye ne masu kyau na
sahabban Annabi Muhammadu (SAW)
kowa ya san Bilal Babban Bawan
Annabi ne kuma mai kiran Sallah'a
masallacin ka'aba shi kuma Hilal wani
sahabi ne cikin Sahabban Manzon
Allah. Mujeeb ne yake yi wa su Goggo
wannan bayanin.
Suna kam ya kayatar fiye da
tunanin mai tunani don musamman
Mujeeb ya ba da odar yin abinci nau'i
goma sha biyar a wani hotel sune suka
kawo abincin a motar din tare da
ma'aikatansu, su suka dinga rabawa
abincin ga jama'a babu nuna bambanci
duk abin da kake so shi ake kawo maka
tun daga abincin zamani har dana
gargajiya irinsu dambu, fate, danwake,
birabisko da sauransu. Hatta fura da
nono sai da aka zuba shi cikin wasu
robobi a damensu ake rabawa dasu
58
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
kunun gyada dana gero da na shinkafa
abubuwa masu sanyi kuwa basu da
iyaka na kanti da na yin hannu kayan
Sobeniyos kuwa wata babbar jaka ce
tamkar tirabilin bag jakar yin tafiya mai
dauke da hotunan 'yan biyu an shade
cikinta da tarkace a kalla kala goma sha
biyu duk masu dauke da hotunan yaran
haka ake ba kowa babu wani bambanci
duk itace dai jakar mai kaya a ciki ake
ba kowa.
Muneeba. da 'ya'yanta kaya masu
asalin kyau da tsada suka dinga sawa
dama ta bada shaddoji da atamfofi
masu tsada da Maman Dijah kawarta
zasuje Dubai da Mijinta aka dinko mata
su rantsattsun dinkuna masu tsada aka
yo mata tun kafin ta haihu shine bata sa
ba ta bari sai da ta haihu.,
Ai kuwa ranar suna ta sha kallo
da tsegunguna musamman gurin dangin
Suwaiba wata Kawar Hajiya Harira da
ke aure a Yola take cewa Suwaiba "ke
sakarya wannan kishiyar taki tasha
gabanki gurin Miji dubi fa suturun
59
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
alfarmar da take sakawa tana fiddawa
leshina masu tsada akalla kowanne
daya ya tasamma dubu saba'in jibi
shaddojinta suma gezna ne masu tsada
atamfofi ina lura sufofi ne Exclusive sai
Super Sheraton da Aura ko Holland
banga ta saba ga dinkunanta duk irin
wadanda ake yowa daga Dubai ne ke
kina nan kina fama da atamfar Ingila.
Shin wai ke kina ina da har zai
kashe mata wannan dukiyar ke bai yi
miki ba? Lallai Suwaiba ke sakarya ce
dubi gwal din wuyanta a kalla yayi
dubu dari biyar, dubi wuyanki kina
fama da dan kunnin SAUDI du kina
naki 'Yan Dubai din.
Suwaiba tayi tsuru-tsuru don
kuwa nata sunci kasuwa kudaden na
gidan bokaye, wannan fan Saudia ma
na Hajiyarta ne ta ara mata, gashi
tsinannun bokaye sun cinye mata kudi
sunci moriyar jikinta babu wata nasara,
ko da na sararma ba'a dadewa tasirin
abin yake karyewa ita kam ta gama
yawo don bata yi tunanin kayan jikin
60
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Muneeba masu tsada har haka bane,
kwarai ta yarda masu tsadane da adadin
kudadensu da kawar Hajiyarta ta fada
tunda mijin ta mai hali ne itama surutu
masu tsada ta ke sa wa.
Ta dubi Hajiyar Yola (Yadda
suke kiran kanwar Hajiya Harira
kenan) ta ce, "Wallahi Hajiya bani da
wata fawa yanzu a gidan nan matarnar
ita ce a gabansa, balle yanzu da ta haifo
masa 'yan biyun nan Wallahi tamkar ya
hadiye su yake ji ita da 'ya'yan har fa
Ofis yake kin zuwa yana can yana
kallon 'ya'yan tamkar ba'a taба yi
masa haihuwa ba sai fa ya wuni a dakin
ba ma na sanin yana gidan sai idan naga
motarsa idan dare ne can yake bacci har
sai Goggonsa dake zama dasu tace ya je
ya kwanta zasu rufe kofa sannan zai bar
dakin in dai asiri ne suka yi masu
Wallahi ya ratsa jikinsa sosai yayi tasiri
kafin in shawo kansa zan sha wahala.
Ta soma matsar kwalla Hajiyar
Yola ta ce "Ke kwantar da hankalinki
idan an kwana biyu ki riko kudi kizo ki
61
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
sameni a Yola zan kaiki inda za'a share
maki hawaye, ita din banza Wallahi sai
ta raina kanta sai sun zamo tamkar
kasha ita da 'ya'yanta a cikin gidan nan
mu za a yi wa haka du kina Yaya
Harira take ake yi miki wnanan cin
kashin a tsakarka? Ai mu duk zuri'armu
ba sa boranci dole ne ki zama mowa a
gidan nan lallai Yaya Harira ta yi sanyi
ruwa ya doki Babban Zakara.
Suwaiba tace Wallahi tayi iya
kokarinta da nice ke fada aji ana
damawa a gidan nan tsautsayi ne ya
afko ya karya asirin da mukayi tunda
har korar ta yayi a gidan nan ta kusa
shekara a gidansu sanadin kwanciyarsa
a asibiti ne ta dawo shine fa al'amura
suka chanza sam yanzu asiri ba ya
kama su ita da shi.,
Hajiyar Yola tayi Kwafa tacс,
Karyarsu tasha karya zamu kai sunansu
inda za'a karya lagonsu sai mun cire
Imani akan aikin da za'a yi musu ke dai
ki yi kodari kizo Yola ki same ni”.
62
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Ba su sake firgita da al'amarin ba
sai da aka debo jakunkunan Sobeniyos
guda dari aka kawowa Suwaiba akace
gashi nan ta rabawa jama'arta da suka
zo har ma da wadanda basu sami damar
zuwa bad a suka bude jaka daya suka
ga irin kayayyakin da ke ciki sai da
Hajiyan Yola ta zunbduma ashar "Kan
jakar Uban nan lallai Suwaiba sai kin
mide tsaye akan matar nan don ta yi
miki fintinkau akwai babbar tazara a
tsakaninku ta sami mijinku irin yadda
ake so, ko tana aiki ne?.
Ta girgiza kai fuskarta cike da
damuwa ta cc, "ba ta fara aiki ba ta dai
gama Karatunta duk wannan hidimar
shi yayi tunda yanzu yana samun kudi
sosai fiye da da, kin san sun fara
kasuwanci a Kasashen waje shi da
abokinsa, sannan ga aiki yana yi, baya
da matsalar kudi a rayuwarsa nice dai
ya daina yi wa hidima, amma Waleeda
babu abinda baya mata don ita ma
akwati guda yayi mata na kayan sawa
da haihuwar nan, ni kuma ya bani
63
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
zannuwa gudaa biyar duka masu tsada
ne ban amso su gurin dinki ba kudin
daya bani na dinki na kashe bani da
wasu shi yasa ban amso ba".
Hajiya ta ce "Ai wannan duk bai
yi min ba dole sai na sa an yi maki
gyaran bawul a gidan nan sai an
sabunta kinyi tasirin gaske a zuciyarsa
in kuwa bah aka ba kin dinga zama mi
ara koma baya kenan".
Taron suna an yi lafiya an tashi
lafiya ba yadda 'yan tsegumi da
hassada suka so ba duk wanda yazo
taron sunan nan sai da ya koma gida
cike da farin ciki kuma dauke da kayan
arziki niki-Niki.
Jarirai biyu Bilal da Hilal kuma
suna cikin koshín lafiya su da
mahaifiyarsu Mujeeb kam harya shige
sabon Ofis dinsa a matsayinsa na
shugaban ma'aikatansu Karin girman
da ya samu ya samo asali daga irin
jajircewan da kwazo da tsayawa
gaskiya da Mujeeb din yayi akan
girmama duk wani na gaba dashi ko da
64
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Gyaran da ta yi wa fuskar ta sai
ya maidata yarinya danya shakaf har sai
da Goggo Hinde ta tanka kai 'ya'yan
zamani sai a barku yanzu danyen jegon naki kika żauna kike irin wannan
kwalliyar don jawo wa kai jidali ko? Ni
nan uwarki sai da kika birgeni balle shi
wanda kika yi dominsa Wallahi ki kula
da kanki ki tausayawa yarannan don
mazan nan ba kunya gare su ba duk
hanyar lallaba sun santa iyakaci idan
kika biye masa kika sami ciki ke zai
bari da wahala babu ruwansa gara ma
ki sani ni kam na gaya maki.
Jikin Muneeba yayi sanyi tace
"Ni fa Wallahi Goggo ba don shi nayi
kwalliyata ba, na dai riga na saba ne,
kuma ina nake binshi kinja gani dai shi
ke zuwa nan kuma akan idonki
'ya'yansa yake biyowa ni ba ruwana
don bana ma zuwa dakinsa"
Goggo Hinde ta murmusa tace In
ma 'ya'yansa yake biyowa ke ma ya
kusa ya biyoki in dai namiji ne ba yaga
67
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
kinyi garau ba kwadai ji da shi ni babu
ruwana.
Muneeba ta fara kukan shagwaba
tana cewa "Ni dai babu ruwana gara ma
ki hana shi shigowa nan din 'ya'yanma
idan yana son ganinsu ga Karime nan ta
dinga kai masa su dakinsa kwalliyar ma
daga yau zan daina yi.
Laminde ta ce, "Ki kyaleta kawai
ta yi kwalliyarta Hajiya Hinde tunda
gidan nan wa kika ga tana masa
kwalliya inba ita ba, mazan nan na
zamani gara da hakan yadda yake ganin
mata iri-iri a gurin aiki ko cikin gari
gara idan ya dawo gida shima ya sami
nasa abin kallon ya ji dadi shi jego ai
bazai sa ka zauna ba kwalliya ba. Kina
dai gani da ya dawo gidan nan sai yazo
ya ganta ita 'ya'yan nan sannan ya ke
samun natsuwa in da basa kwalliya
suna birgeshi yaushe ma zai damu dasu,
nan fa idan yazo ya makale sai kin kore
shi yake tafiya hakan inace kulawa ce?
Ki barta kawai taja hankalin mijinta
gareta?.
68
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Goggo Hinde tace Ai na barta
tunda kin bata goyon baya Allah ya
Kara so da kauna. Basu dade da gama
zancen ba sai ga dan Halas dın yayi
sallama ya shigo dakin ya gaidasu
Goggo sannan yasa hannu ya dauki
Bilal dake hannun Laminde ya
rungume a kafadarsa yana cewa
"Goggo yaran nan naga sunyi kiba
sosai nonon ya amshe su kenan? Tace
"Eh Nononta na da kjyau, amma dole
za'a hada musu da madara don wannan
Karamin yana da tsotso fiye da dan
uwansa kaga ma ya fi shi kiba ruwan
nono ba ya isarsu yace "Ok to zan
tambayi abokina likita inji wace
madarar ya kamata a fara basu sai a
siyo musu.
Yana maganar amma idanúnsa
na kan Munecba wadda ke ba Hilal
Nono don tun ana masa shafa yake
neman nono shi ne ana gama sa masa
kaya Goggo ta bata shi tace ta bashi
Nono.
69
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Ya rankwafa yana liken fuskar
Hilal din ganin haka ya sa Laminde tayi
saurin barin dakin Goggo Hinde ma sai
ta suri bahon da ta gama yiwa Hilal
wanka ta fice a dakin hakan ne ya bashi
damar kai baki ya sumbaci yaron
sannan ya dawoi ya sumbaci kirjin
Muneeban ta dago idanu tana harararsa
cikin sigar soyayya ta ce, Ka fara ko?
Ya kyalkyale da dariya "ban ma fara ba
zan dai fara kinga irin kyan da kika yi
yau kuwa? Gaskiya jegon nan ya amshi
jikinki fatarki tayi luf-luf tayi kyau ni fa
na kosa 'yan tsofafaffin nan su barni da
ke don Goggo Hinde tasa ido sosai a
kaina".
Ta ture hannuwansa dake jikinta
ta ce, "Au korarsu ma kake yi? Su
kuwa suna nan sun dage suna gyara
maka mata da 'ya'ya to zan gayawa
musu gara tun wuri sai su fara hada
komatsansu.
Yayi saurin cewa "Don Allah
rufa min asiri da Goggo Hinden ai ni
ban san gyara min ke ta ke yi ba shi
70
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
yasa na ke sonta wallahi ta san duk
wasu hanyoyi da za ta yi wa jininta yaji
dadi a duniya ki tambayar min ita in ma
ana budatar kudi don siyan kayan
gyaran naki zan bayar don bana son inji
kin canza min.
Ta sake dubansa "Aika fini kusa
da Goggon Hinden gata can a waje sai
ka je ka tambayeta don ba zan iya isar
da wannan aiken naka ba ya ce "Kin
san zan iya kuma ce mata zan yi in jiki
kince in bata kudade akwai abubuwan
da za ta siya na gyaran da take maki.
Ta riko hannuwansa da ta ture
tana bashi hakuri "Don girman Allah
kada ka je na san zaka iya kuma
Wallahi za ta iya yardan don yar
kwalliyar nan da na yi yanzu cewa tayi
ina neman janyowa kaina jidali, ba
kunya garc ku ba ku mazan zamanin
nan ya kame baki ya ce to fa! Yanzun
daina yimin kwalliyar zakiyi? Ta cе
"Haka ta ce nima na fara jin tsoro
kwada kiran sallaar Magriba da aka yi
shi ya dakatar dashi abin da yake son
71
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
fada bayinmta ya shiga ya yo alwala
sannan ya fito ya wuce masallaci tun da
ya dawo Sallar issha'i bai shigo dakin
Muneeba ba yana can nasa dakin yana
cike wasu takardu da yazo das u, amma
rabin hankalinsa na kan Muneeba
surorinta na ta yi wa fuskarsa shawagi
kyan da tayi na ta dada dayatuwa a
fuskar tasa ya tsaida abinda yake ya
dauko wayarsa ya kira Ikayinta tana
dauka sai yace "Ki sawa yaran nan
kayan sanyi sosai yanzun zan zo mu je
asibitinsu Dr. Aminullah za'a duba su
don a san madarar da ya dace a soma
basu".
Ta ce, "Garin akwai sanyi me zai
sa ba zaka bari sai gobe ba yaran nan fa
basu da kwari, ya ce ba zan bari sai
gobe ba yanzu nake so kiyi sauri kada
ki batamin lokaci ganinan zuwa"
Babu yanda ta iya dolente ta
tashi tá đauko kayan sanyi masu kauri
sosai ta mikawa Laminde dake rike da
Bilal tana bashi ruwa tace "Asa masa
kayan sanyin nan wai asibiti za mu je a
72
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
daren nan "Laminde tace "asibiti wani
ne ba lafiya? ta ce "kowa lafiya za'a
kaiwa likita sune wai ya duba su yaga
wace irinb madara ya kamata a fara ba
su".
Та се "Gara kam a fara ba su
madarar don mijin nan na Hajiya Hinde
sai da madara". Goggo Hinde kuwa
fada ta dinga yi wai don meye za a fita
da yara da daren nan alhali lokaci ne na
sanyi don kawai a kwaso musu sanyi.
Ita dai Muneeba tana jinta ta san tunda
yayi niyyar fitar tasu to ruwa da iska
babu mai hana wannan fitar ko da kuwa
Goggoce.
Tana sakawa Hilal Safa ne ya
shigo dakin cikin sallama kallo daya
tayi masa ta kawar da kanta, saboda irin
kyan da yayi mata cikin wasu sabbin
Kananan kaya wando da riga shirt long
slip sai ya kawo bakar jaket ta sanyi ya dora bisa shet din saboda sanyi sai ya
koma dan saurayi abinsa.
Ita ma sai ta dauko katuwar rigar
sanyi ta saka sannan ta saka dogon
73
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
hijjabi ya dauki Bilal ya rungume shi
ya rufe shi da babban bargo ya salami
su Goggo Hinde ya fita.
Ita ma tan ade Hilal a nasa
bargon ta rungume shi tana cewa su
Goggo sai sun dawo Goggo Hinde ta
dubeta tace "Kai wannan zamani
yanzun sai goyo dai ya zama tsohon
yayi sam ba kwa son goya ‘ya'yansu ji
dumin jikinku alhalin hakan na kara
dankon soyayya tsakanin iyaye da
'ya'yansu ta ce "Gani na yi mota zamu
shiga shi yasa ban goya shi ba, amma ai
na rumgume shi a kirjina zai ji dumi
goggo.
Taja tsaki "Ni wuce ku tafi ku
bani guri, yara kun sangarce da kuya
kawai, ku an yi ta goyonku amma ku
kiri da muzu ba zaku dinga goya naku
'ya yan ba.mu zamaninmu har da goyo
kwana mukeyi.
Munceba dai ta wuce ta bi bayan
mijinta tabar goggo Hinde na ta korafi.
A bayan motar ta iske ya kwantar da
Hilal ya lullube shi da bargonsa ganin
74
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
ta tsaya tana kallon yaron sau yace
"Shima kwantar da a bayan ki rufe su
zan kunne hitar mota ba zasu ji sanyi
ba.
Та се, "Ni na so ne in rikesu
duka a jikina don Goggo tace, in dinga
rungumesu suna shan dumin jikina
hakan na kara soyayya tsakanin uwa da
dfanta ya amshi yaron a hannunta ya
kwantar dashi kusa da dan uwansa
shima ya rufa masa bargon suka shiga
motar suka bar harabar gidan.
Sai da ya hau titi sannan yayi
mata magana "Ni kam yanzu na lura
son yaran nan yana neman ya ture
gwamnatin tawa soyayyar, in bayan
haka su kadai ne wadanda zasu sha
dumin jikinki ko ko ni ba'a gaya miki
ya kamata ki bani kulawa bane?
Shziru tayi masa ya kai hannu ya
damki nata hannun yace "wai ba kiji
abinda nace bane kika min shiru? Tа се
"to idan na ji me kake so ince maka? Ni
kadai ke gareka balle kace baka da
madafa?"
75
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Ya ce Ok haka ne fa bake kadai
ba ce har kin tuna mini shike nan
nagode da tunatarwa tun daga nan bai
sake cewa komai ba har suka isa asibiti
yayi wa Dr., Aminullah bayanin abinda
ya kawo su ya kira wata Nos yayi mata
bayani tare da gaya mata abinda sukeso
yace ta kaisu inda ya dace. Gurin likitan
yara ta kaisu aka duba yaran sannan aka
rubuta musu sunan madarar da za su
sayawa yaran.
Sun koma gurin Dr. Aminullah
suka yi masa sallama sannan suka bar
asibitin wani (Super Market) ya kaisu
anan ya sayawa yaran katon din
madarar ya sayawa Walceda Katan din
Cerelac da ta ke sha sai kayan kwalama
da ya saya musu da wasu abubuwan
bukatar ya kashe kudi sosai sannan
suka nufo gida.
A hanya sai da ya sake tsayawa
ya saya masu gasassun kaji suna isa
gida ya dauki Hilal ya rungume tare da
wasu ledojin ya ce mai gadinsu ya
kwaso sauran kayan ya biyo shi da su.
76
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Ya dubi Munceba ya ce, ki
sameni dakin a Hakan da yace ta san
neman jidali yake yi"
Suwaiba ta hanga ta labulen
windonta tana lekensu hakan ne yasa
kawai ta bi shi dakin nasa don ta san
Suwaiban ta ji umurnin da yayi mata na
cewa ta same shi a dakinsa kila shima
ya ganta tana lekensu ne yasa
Muneeban shigowa ya maida kofar
falon nasa ya rufe da makulli don ya
san halinta sarai zata iya biyo su don
taga me za su yi.
Kuma kullum yana gaya mata ta
ragewa kai daraja ne ka dinga bin
kwakkwafin sai ka ga me miji ke wa
kishiyarka alhalin ko kin gani ba ki isa
ki hana shi ba sai dai ki karawa
zuciyarki takaici ya hanata shigo musu
tsulum ba sallama amma tayi kunnen
Rashi taki dainawa shi yasa in dai yana
tare da Muneeba yake sawa dakin
makulli ya rufe ba wai don tsoron kada
ta ga me suke yi ba a'a baya son ta dinga katse masa abinda yake yine in
77
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
bayan hakla ta zo ta yi ta gani ita ce za
ta sha takaici.
Ya wuce kan doguwar kujera ya
kwantar da hilal ya isa gareta ya amshi
Bilal shi ma ya kwantar da shi sannan
ya dawo itama ya ja hannunta suka
zauna bisa (2sita) ya kwantar da kansa
a kafadarta yace. "Wai laifin me dakin
nan yayi miki rabonki da shigowa tun
ranar su Bilal a kalla sati biyu kin daina
zuwa gaishe ni sai dai ni in zo inda kike
meye hujja yajin da kika yi wa dakin
nan?.
Ta soma nokewa saboda
abubuwan da ya ke mata sannan ta ce,
"Yaushe ne zan yi ta biyo ka alhalin
kana zuwa ko da yaushe kana dai gani
'yan tsofaffin nan idonsu na kanmu ko
zuwa dakina ka yi basa jurar suji mu
shiru a daki idan ka daďe ma korarka
Goggo Hinde ke yi, ka yi hakuri kawai
har su tafi tsanani ai bai wuce su yi
arba'in biyu ba'sannan su tafi".
Ya watso mata idanu "wane irin
arba'in biyu? Kina hauka ne? lallai in
78
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
baki yi wani abu akan faruwar hakan ba
to zan nuna rashin hakuri na karara don
Wallahi na shiga halin takura". Та
kalleshi cike da mamaki "Ni fa kana
bani mamaki wai shin me yake amfanin
aje mata biyu a gida ina ce idan daya
nada larura mutum ba zai shiga matsala
ba tunda ga 'yar uwarta. Gaskiya idan
ma kace kana cikin takura kai ka so
hakan tunda babu wani shamaki a
tsakaninku in ma rigima kuke Wallahi
gara kaje ku shirya ni kam bani da abin
da zan yi maka"
Ya manneta sosai a jikinsa
sannan ya ce, "Kina da abin da zaki yi
mini, amma fa idan kika so in kuma
baki so ba sai in kyaleki tashi in raka
ku". Ya mike ransa a bace ya soma
kokarin daukar Hilal ganin ransa ya
baci sai hankalinta ya tashi don sam
bata son bacin ransa ko ya ya nc.
Tayi saurin isa gare shi ta
rungumo bayansa tana cewa "Ka san
dai jego nake `yi me kake so in yi
maka? "ya sha kunu sosai ya ce "babu
79
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
komai inma akjwai na hakura sake ni in
daukar miki yaron nan dare nayi kada
Goggo Hinde ta ga kin dade don na lura
ka'idojin sosai take kafa maki a kaina
gara ki dinga kiyayewa".
Kalamansa ya nuna ya ji haushi
sosai akan abinda ta yi masa, sai ta
shiga lallashinsa tana bashi hakuri
amma ya basar ya ce ya ji ya hakura su
je kawai ya rakata.
Ya dauki Hilal ita kuma ta biyo
shi da Bilal har dakinta ya kwantar da
yaron ya koma dakinsa ya debo ledojin
da suka dawo dasu da kwalin madarar
yaran yazo ya aje mata su Goggo Hinde
kawai yayi wa sai da safe ya fice
abinsa.
Shirin kwanciya kawai tayi, suka
kwanta ita da yaranta amma fa ta yi
bacci ne zuciyarna cike da tunanin halin
da mijin nata yake ciki shin ita wai
meye laifinta don ta ce jego take yi
kuma shi ina amfanin aje mata biyu in
har wata ba zata iya daukc masa
80
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
matsalarsa ba shine fa abin yin fushi
meye laifinta anan?
Washe gari tana dakin baccinta
tana jinshi a falo ya tsaya suka gaisa da
su Goggo Hinde ya duba yaransa
sannan yayi musu sallama ya ce ya
wuce ofis, su kansu sun yi mamaki da
bai nemi Muneeba ba kuma bai leka
dakin gurinta ba.
Wunin ranar sai abinda yayi mata
yayi ta damunta da kyar ta samu ta saki
ranta har ta manta da abin shima abin
ya yi ta damun zuciyarsa sai dai ya
yanke kansa shawarar yau dole ya kai
Suwaiba asibiti don a auna jininta a
tabbatar masa da lafiyarta ko ya sami
madafa don kuwa ba zai iya jure har
nan da kusan wata daya yana juriya ba
alhalin yana da wata matar.
In har ya tabbata suwaibar garau
take to zai lallaba da ita don babu yanda
zai yi shi kam ba