acewarsa bai
taba ganin macen da ciki ya wahalar
irinta ba.
Mujecb ya shigo dakinta cikin
shirin bacci a wani dare kasancewar
tunda cikinta ya shiga wata tara gurinta
ya koma kacokan da kwana da
suwaiban ta soma tawaye sai yayi mata
matashiya da cewa ai dole ne a ramawa
26
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
kura aniyarta tunda ita ma duk
haihuwarta da tayi guda biyu da watan
haihuwa ya tsaya dakin ta yake
komawa da kwana. Da ya gayawa
Goggo take ta goyi bayan hakan ita ma
acewarta ai dama kyan cin tuwon
kishiya ramako.
Hakan ya bakanta ran Suwaiba
na yadda kiri da muzu Goggo ta ke so
ta maida Muneeba wata yar gaban
goshenta kawai don zata haifo yan biyu
dadin abin dai kafin ayi daran akayi
kwandi ita ta fara haihuwa har biyu
kafin Muneebar na mijin ma itace ta
fara balle ayi, mata wani kan kajere
haka ta dubi tsabar idon Goggo ta gaya
mata.
Mujeeb ya zauna a gaban
Muneeba cike da tausayinta karara a
fuskarsa ya cc“Sannu da kokari ya
jikin na ki? Ta lumshe idanu, jiki
Alhamdulillah bacci nake son in shiga
ciki inyi amma tun dazu na kasa tashi
kafafuna sun rike. ya ce to ba sai ki
kirani a waya ba bako na yi ina can
27
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
waje hankali na gurinki". Ya mikar da
ita tsaye a hankali ya riketa suka shiga
dakin baccinta sai da ya tabbatar ta
kwanta sannan ya je ya kullo kofofinta
ya dawo ya zauna gefen gadon yayi
mata magana kin yi bacci ne? ta ce ido
na biyu a yan kwanakin nan ban cika
samun bacci ba ya ce wata shawara
nayi tunda kinki yarda in fita da ke
wata Kasa ki haihu a can to ko asibitin
zan kaiki ki zauna can ana kulawa dake
har ki haihu don ni ka mina tsoron kada
ki haihu a gida ko nakudar tazo miki
cikin dare mu rasa yadda za mu yi da
ke".
da Ta tashi zaune ta jingina
Allon gado, sannan ta ce, Gara dai ka
barmi a gida kai kanka zaka fi samun
natsuwa idan ina gidan kuma a yadda
suka ce a asibiti da zarar naji ciwo ko
yaya ne muyi gaggawar zuwa asibit ka
yi hakuri kawai Insha Allahu babu wata
matsala da za'a samu zan haihu lafiya.
Shi kenan tunda kince haka zamu
ci gaba da addu'a Allah ya saukeki
28
A
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
lafiya ba ta sami bacci ba sai da yayi ta
mammatsa mata jikinta da kafafunta
sannan ta samu yin bacci. Da asuba sun
shiga ba yi zata yi alwala tun a gurin
fitsari taji wani abu na mata zugi da
radadi a gabanta sai ta gaya masa yasa
cocila ya haska sai yaga ashe wani dan
kurji ne ya fito mata a bakin gaban دو nata.
Ya gaya mata abin da ya gani
amma yace dole da safe suje asibiti don
kada a sami matsalar sun sami ganin
likita tayi wa likita bayanin matsalarta
Allah yasa mace ce likitar shi yasa ba ta
dar da lokacin da ta umurceta taje
gado ta kwanta zata duba ta sai da
likitar ta taimaka mata wajen hawa
gadon don kuwa kasata tayi.
ji
Likita ta duba kurjin ta ga yadda
yayi daga bisani ta rubuta mata
magunguna da zasu siya ta sha don ya
noke in kuma bai noke ba to zaiyi ruwa
sai suzo a yanka shi a cire kwayar. Tun
a mota Muneeba ke addu'ar Allah ya sa
ma ya noke din kada yayi ruwa ace
29
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
za'a yanka ta kila kafin ya warke zata
haihu in kuwa haihuwa tazo ga yanka a
guri ai ba karamar azaba zata sha ba.
Tun da ta fara shan magunguna
sai kurjin ya soma nokewa amma duk
da haka yana mata zogi tamkar yana
duran ruwa data gayawa Mujeeb sai
yace ta bari ta shanye magungunan in
bai daina zugin. ba sai su koma asibitin
har ta a shanye maganin zugin bai daina
ba sai suka sake komawa asibitin wani
maganin aka sake bata.
Cikin dare ranar wata laraba ne
ta fara nakuda amma ciwon ba sosai ya
ke mata ba shi yasa take ganin tamkar
ciwon bana nakuda bane ciwon bai yi
mata tsanani ba sai bayan da ta idar da
Sallah Subahi. Wani abun mamaki da ta
gani lokacin da ta shiga bayi shine
marurun da ke gabanta yayi wani irin
girma tamkar an hura balam-balam ya
rufe duka gabanta don tayi kokarin ta
nemi wata kafa a gaban nata taji babu.
Tun a bayin ta kwalawa Mujeeb
kira a guje ya shigo bayin kuma a
30
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
tsorace yana ganin yadda marurun yayi
sai abin ya tsorata shi da sauri ya fita
yaje ya gayawa Goggo suka dawo tare
itama taga wannan abun al'ajabi tayi
salati tana cewa 'Wannan ai babbar
matsala ce saboda yadda take nakudar
nan idan haihuwar tazo to fa babu kofar
da 'ya'yan nan zasu fito marurun ya
rufe ko ina ruf".
Mujeeb ya sake tsorata ya ce
"goggo taimaka mata sai muje asibiti
kawai" ya soma harhado kayan da ta
shirya don zuwa haihuwa Goggo ta
dube shit a ce"Kira suwaiba don bata
sani ba sai mu tafi asibitin da kai ita sai
ta zauna a gida", shi sai a lokacin ne ma
ya tuna bai gayawa Suwaiban ba.
Yadda tazo ta iske irin yanayin matsalar
da akace Munceban ta samu sai ta nuna
damuwarta a zahirance amma a can
cikin zuciyarta murna ta dinga ganin
hakarsu zata cimma ruwa.
Suna tafiya asibiti Suwaiba ta
koma daki tana rawa tana juyi ta dauko
wayarta ta kira layin Hajiyarta cikin
31
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
murna tace "Hajiya yau dai burinmu zai
cika akan tsinanniyar matar nan gata
can tana nakuda sun tafi asibiti "To da
suka tafi asibitin me ya faru? Abin da
boka yace mu zura ido mu sha kallo ya
faru din ne? Hajiyarta ce ta tari
numfashin Suwaiba ta ce "Ai kuwa ya
faru kurji na nan ya fito ya rufe gabanta
babu inda 'ya'yan za su fito kinga sai
dais u mutu a ciki.
In kuma aka yi mata aiki aka ciro
'ya'yan aida sauran rina a kaba. "Au
kin manta boka ya ce muddin aka yi
mata aiki ko aka yanka kurjin jini ne
zai tsinke mata yayi ta zuba har ta a
mutu 'ya'yan ne kawai zasu rayu? Ta
се.
"ban manta ba amma don ta
mutu ai an kashe macijine ba'a sara
kansa ba ke da muke son ita da 'ya'yan
duk su mutu a huta shine har zaki yi
murna don ita ta mutu 'ya'ya na nan da
ransu.
Suwaiba tayi ajiyar zuciya to
yanzu me ya abin yi Hajiya ta ce Abin
32
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zarja
yi kawai ki san yadda zaki yi ki ba
mijinki shawarar kada a yadda a yanka
kurjin nan kice kin taba ganin wata ta yi
irin shi da zata haihu ana yankawa jinni
yayi ta zuba har ta mutu, kinga idan ya
bi shawararki shikenan ita da 'ya'yan
sai buzunsu mun rabu da alakakai.
Suwaiba da hanzarinta tayi
saurin kiran Mujeeb a waya tana
tambayarsa wai Muneeba ta haihu ne ya
ce "Ba ta haihu ba marurun da ya futo
mata yayi girma har ya toshe kofar da
'ya'yan zasu fito yanzu haka ana
tunanin aiki za'a yi mata.
"Aiki? Gaskiya kada ka yarda ayi
mata aiki don ni na taba ganin wata
kanwar kawata irin haka ne ya sameta
da ta zo haihuwa sai aka yi mata aiki
daga ita har 'yar cikin nata mutuwa
sukayi wai ashe ba'a sawa marurun
wuka abin kamar iska ne ka ga abin
akwai tsoro gara dai a jira kila a sami
kafar da 'ya'yan za su fito.
Jin kalaman Suwaiba sai Mujeeb
ya tsorata shi dama sai da yayi tunani
33
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
ko dai aikin jinnu ne tunda babu irin
badda bamin da ba sa yi shi kam da ya
rasa Muneeba gara ya rasa 'ya'yan
tunanin kiran Malam Abubakar yazo
ransa ya lalubo wayarsa a aljihu ya kira
layin Malam din bayan sun gaisa yake
shaida masa matsalar data sami
Muneeba.
Malam Abubajar ya ce "Yanzu
haka tana ina ne? ya ce mun kaita
asibiti sun mace idan ba ta haihu ba
nan da awa daya zasu yi mata C.S. sm
yasa nace bari in gaya maka ko da ani
taimakon da zaka yi mana ni kam bana
son son su yanka ta".
Malam ya numfasa akwai abinda
zan taimaka dashi Insha Allahu kuma
za'a dace in dai ba'a sami miskila ba
wajen debo abin akwai wani ganye
vana fitowa ne a tsakanin duwatsu
kuma ya kan fito ne daga sha biyun
rana zuwa daya na rana sai ya noke ya
koma sai kuma gobe zai sake fitowa shi
zaka je ka debo Insha Allahu idan aka
murjeshi ruwan za'a shafa mata akan
34
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
marurun zai fashe da kansa ba sai an
yanka ba kuma zata haihu lafiya ba sai
an yi mata wani aiki ba.
Mujeeb ya ce "Yanzu Malam a
ina za'a debo ganyen na san kila ka
taba debowa? Ya ce "wane asibiti kuke
sai inzo in sameka muje kafin sha biyun
tayi anfi son ya fito a idanunmu Mujeeb
ya gaya masa asibitin sannan ya fito
harabar asibitin yana tsimayin jiransa
ganin har sha daya saura a lokacin
Malam din na zuwa suka tafi a motarsa
can bayan gari suka je wajen wani
dutse suka zauna a daidai inda suke
tsammanin ganyen zai fito cikin ikon
Allah sha biyun na yi da minti daya
ganyen ya fara yin tsiro yana fitowa
Malam ya taba Mujeeb ya nuna masa
Mujeeb yayi tsiru-tsiru yana kallon
ikon Allah har ganyen yayi fala-fala
kore shar sannan Malam yace yasa
hannu ya tsinka Mujeeb yayi Bismillah
yasa hannu ya tsinka, sannan suka tashi
a gaggauce suka bar gurin suka koma
asibiti Mujeeb yayiwa Goggo bayanin
35
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
ganyen tare da shaida mata yadda zata
yi har ta a je ta shafawa marurun inda
Allah ya taimakesu har da kawar
Munceba cikin masu amsar haihuwar ta
wato Sister Hadiza ita Goggo taba
ganyen tayi bayanin komai cikin ikon
Allah Sisiter hadiza na m ruza ganyen
ta shafa ruwan a kan marurun sai ga shi
ya fashe ruwan da ke cikin duk ya
tsiyaye gurin sai ya koma tamkar babu
wani kurji har an sami hanyar da zata
haihu lafiya.
Tamkar jira haihuwar take yi
kurjin nan ya fashe sai nakudar ta taso
gadan-gadan ba a fi mintuna talatin ba
Muneeba ta sauka lafiya ta haifo
kyawawan yaranta maza guda biyu
kuma babu wani jinkiri tsakanin
haihuwarta su don cibiyarsu ma a hade
ta ke sune (Identical Twins) masu
tsananin kama da juna.
Tana kwance bayan ta haihu tana
kallon Nosis suna ta aikin gogewa
yaran jiki ita kuma har an gama yi mata
duk abubuwan da ya dace amma sun ce
36
WATA KUSAN 4 Rähmatu Hassan Zaria
sai an yi mata dinki don ta sami karuwa
da yawa. Ta so tace musu bata son
dinki. saboda irin wahalar datasha
amma sai ta tuna a littafin DON
MA'AURATA data karanta an nuna
muhimmancin yin dinki ga matar da ta
karu a lokacin haihuwa don in ba'ayi
ba mace zata iya samun matsala da
mijinta yayin da ya dawo gareta bayan
tayi arba'in don zaiji ta ba daidai ba shi
yasa gara ka tsaya a dinke karuwar da
kayi daga nan kuma sai ka kara da
gyara na musamman.
Su gogon dake waje tare da Inna
Amina da su Khairee da suka zo daga
baya duk hankalinsu a tashe yake don
basu sake ganbin wata cikin Nosis din
da ke karbar haihuwar Muneeba wata ta
fito ba balle su san me ake ciki ta haihu
ne ko ba ta haihu ba.
Sister Hadiza ce ta fito ta nufu su
duk suka tsura mata idanu ganin tana
cike da fara'a yasa suma suka tarbe ta
da fara'a suna tambayarta "Munji shiru
ta haihu ne? Ta fadada fara'arta
37
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
"Barkanmu da arziki Goggo ta sauka
lafiya kun samu mazaje Goggo ta
Hassan Mama kuma mun baki
Hussaini.
Hamdala su goggo suka dinga yi
babu ma irin Inna Amina tafi kowa
murna su Khairee kuwa wani irin uban
ihu suka saka na murna Inna Amina ta
dube su ta ce "Kai kuna da hankali
kuwa? Dubi yanda kukasa hankulan
mutane ya dawo kanmu haka ake
murna in banda shashanci.
Sisiter Hadiza ta ce "Ai abin ne
abin murna mama ni yanzu ina baban
'yan biyu inyi masa albishir don na san
zan sami babban goro? Inna Amina ta
ce "Yanzu yaje yin Sallah a masallaci
Wallahi-Wallahi maza ki bishi ki amshi
Babban Goro nima ga nawa goron
albishir din" Inna Amina ta balle fosta
din hannunta ta zaro 'yan 'dari biyar
biyar sababbi dal ko kirgawa bata yi ba
ta mikawa Sister Hadiza ita ta ce.
Haba Mama Wallahi ba zan amsa
ba, ko shi ma da ika ji nace haka ai ba
38
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
masar zan yi ba ni Muneeba ai ta wucе
kawa a gurina yar uwa tace. Dole Inna
Amina ta maida kudinta jaka tan a
hararar Khausar data miko mata hannu
cikin tsokana tan ace, Mama miko
mana tukucin tunda bataso ba'a maida
hannun kyauta baya.
Sister Hadiza tana shirye-shiryen
barin gurin sai ga Mujeeb ya karaso
duk sai sukayi shiru suka kyaleta ta fara
sanar masa da haihuwar ta tare shi da
Congratulation kawata ta sauka lafiya
an sami (Identical Twins) masu kama
da kai.
Hannuwa Mujeeb ya daga sama
"Alhamdulillah" Masha Allah ina
godiya mara iyaka gare ka ya Allah da
ka azurtani da wadannan 'ya'ya Allah
ka albarkaci rayuwarsu ka ba
mahaifiyarsu lafiya".
Wata irin murna da bai taba ji b
a rayuwarsa ita yaji a yau don ko
lokacin da aka Haifa Baffa baije irin
wannan Murnar ba a ganinsa dila don
Muneeba ta dade ta haihu dashi bane
39
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
yasa yake wannan murnar ko kuma
dalilin irin son da yake mata ne".
Ya dubi Hadiza yace, Sannu da
Kokari Hadiza mun gode kwarai da irin
kulawa da gudunmmuwar da kika ba
Kawarki Wallahi na` fidda raid a samun
rayuwarta ita da 'ya'yan da ke cikinta
yanzu a masallaci kuka na dinga yi da
hawaye ina gayawa Allah matsalarta
tare da rokonsa ya kawo mata dauki ya
raba ta da cikin nan lafiya har mutanen
da ke cikin masallacin suka yi ta kallo
na. da kuzar na baro masallaci saboda
zuciya ta da sami yakinin tabba Sallah
ya amshi addu'ar ta ashe gaske ne sai
gashi kun tare ni da wannan daddadan
labarin lallai Allah abin godiya ne
kuma abin dogaro ne".
Ya zura hannu a aljihun rigarsa
ya fiddo kudade da bai san yawan su ba
'yan dubu dubu ya mikawa sister
Hadiza yace "Ga tukuicin wannan
daddadan albishir da kika yi min.
Ta hade hannuwanta guri guda
tana girgiza kai Haba Haba gaskiya ba
40
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
zan amsa ba ai ka wuce nan kabar
kudinka, ya bata rai ai kema kin wuce
nan kuma kinfi karfin kudin nan a
gurina wannan na yi maki ne don in
nuna irin jin dadi na da nuna godiya ta
ga Allah da wannan arziki da yayi mini
ke din nan kin cancanci in yi miki
komai kece kika fara sanin Muneeba na
da ciki sannan yau ke ce kika fara sanar
da ni ta haihu kinga kuwa ai kin wuce
kyautar wadannan kudi don girman
Allah ki amsa kada mu yi haka dake".
Jin ya hada ta da girman Allah
yasa ta amsa tare da yi masa godiya tare
suka karasa gurinsu Goggo nan fa suka
shiga yi wa Juna barka, Inna Amina ta
dubi Sister Hadiza tace idan an gyara
yaran don Allah akawo mana su mu
gansu "Ta ce Eh ai za mu kawo su na
barsu ana gyara su në ita kuma don
Allah idan an fito da ita ku barta ta yi
bacci ta huta sosai saboda data sha
wahala da yawa "Ai dole mu hana
kowa shiga gurinta su dai yara shigansu
41
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zària
ita kam dole a'barta ta huta gajiyar da ta
sha".
Inji goggo Mujceb na can zaune
bisa wata kujera yana ta sanar da 'yan
uwa da abokan arziki haihuwar da aka
yi masa Suwaiba kam daya gaya mata
Kiris ya rage ta zabga kururuwa sai
Allah ya taimaketa ta kashe wayar
sannan ta zabga ihu tana cewa yau na
shiga uku na lalace! Muneeba ta hangi
'yan biyu? Wallahi sai na yi ajalin
'ya'yan nan tunda ita ta gagareni ita
dimma ba zan kyaleta ba sai na ga
bayanta. Tana kokarin kiran Hajiyarta
ta shaida mata wannan Mummunan
labarai (Acewarta) sai kiran Mujeeb ya
sake shigowa wayarta ta ja uban tsaki
sannan ta dauka yace, Baki ji abinda na
gaya maki ba Munceba ta hangi 'yan
biyu maza ki gayawa Waleeda da ta
sami kanni yanzu ma zan turo Direba
na Ofis ya dauko ku sai ku shirya kafin
ya niso.
Cikc da bakin ciki ta yi magana
"Kada ka turo shi yanzu girki nake ban
42
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
gama ba idan na gama zamu taho da
Rabe Direba yana nan ya dawo yace
'Ok to don Allah ki haďo duk
abubuwan da suka dace maijegon sai ki
yo mata kunun gyada da farfesu saboda
ta sami ruwan Nono.
Hum! Kawai ta fada sai ta kashe
wayar tare da yin wani matsiyacin tsaki
tana fadin "Ji wani kitifi har sai an
jaddadamin in kawo abubuwan da suka
dace "Ki yo mata kunun gyada da
farfesu saboda ta sami ruwan Nono" Ta
kwaikwayi muryarsa lokacin da ke bata
umurnin sannan tace in ban yi ba sai ayi
yaya dani? Kawai zan yi mata ne don in
ramawa kura aniyarta tunda ni kam tayi
dawaniya da ni a haihuwar Baffa da
Waleeda amma in ba haka ba shi ma ya
san in banga dama ba ba zan yi ba kafin
Sallar La'asar jama'a sun cika asibitin
nan Musamman mutanen Dukku
wadanda tamkar jira suke yi a fadi
haihuwar su taho irin su Murja da
Mustafa da su Adda fadima duk sun iso
asibitin a wannan lokacin ne aka fito da
43
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
jariran cikin wasu nagartattun kayan
sanyi ‘yan biyu waje kalar sararin
samaniya mai haske saiti ne tare da
abin daukarsu. Sister Hadiza ce da wata
Nos suna fitowa aka soma rige-rigen
amsarsu Sister Hadiza tana murmushi
tace kuyi hakuri gurin babansu zan fara
kaisu sai in dawo muku dasu".
Murja tace "Haba Sister yadda
muka kosa mu ga yaran nan shine zaku
yi mana kwalele 'ya'ya ai sai ya gaji da
ganinsu mu tafiya zamu yi mu bar shi
da su.
Ta ce Eh haka ne amma dai
yanzu kuyi mana hakuri mu fara kai
masa yanzu zamu dawo muku dasu
Mujeeb shi da Mustafa ne a
zaune a lokacin da suka kai masa
yanzun za mu dawo muku dasu"
Mujccb shi da Mustafa ne a zaunc a
lokacin da suka kai masa yaran sai bai
amshesu ba Mustafa ne ya amshi daya
sai ya nade saboda su Goggona
kallonsa ya ce "Ga su Goggo can su ya
kamata ku fara basu kada su nayi rashin
44
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
kunya ku maidasu can don Allah kada
muyi laifi. Yana maganar amma
idanunsa na kan fuskar yaron da
Mustafa ya amsa Godiya ga Allah
kawai yake yi a zuciyarsa saboda
azurtashi da yayi da wadannan
kyawawan yara masu tsananin kama da
shi don ba'a taba haifo (Photocopy)
dinsa ba irin wadannan yaran, sai ya ji
tsananin son su ya kara darsuwa a
zuciyarsa. Mustafa yayi wa yaron
hannunsa addu'a sannan ya tambayesu
"wannan wa ye na dauka? Don na ga
kamar tasu tayi yawa". Hadiza tace
wannan shi ne Hassan ga Hussaini nan
ka duba gaban rigarsa mun manna
sunansa don kada a shiga rudu
kamannin yaran akwai rikitarwa mu
kanmu da muka amshi haihuwarsu sun
so su rikita shi yasa muka mannawa
kowa sunansa". Ya mika mata Hassan
ya amshi Hussaini Shi ma ya yi masa
addu'a ya miko musu yace Don Allah
ku kaiwa su Goggo kallonmu suke yi
tayi kada mu yi laifi.
45
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Mujeeb yace "Don Allah Hadiza
zan iya ganin Muneeban don ni ita na
damu in ga halin da ta ke ciki ta сe Ok
zaka iya ganinta tunda na san ba zaka
dameta da surutu ba, su ma Matan ba
wai mun hanasu bane ba ma so aje a
tsaya a gurinta ne ana ta surutu muna so
ne ta sami isashshen bacci ta yadda za
ta huta sosai ku biyo ni in kaiku gurinta
sun kaiwa su Goggo yaransa, suka
shiga dakin da Muneeban take ita dasu
Mujeeb kowa ya amshi yaran nan sai ka
ji ya ambaci masha Allah saboda kyan
yaran gasu da girma tamkar ba 'yan
biyu ba. Nan da nan su Khausar suka
fara daukansu hotuna a tsadaddun
wayoyinsu (Iphone) suka saka hotunan
a cikin (Whatsapp) dinsu.
Mujceb na shiga ya iske
Muneeba kwance bisa gado daya dake
dakin idanunta a rufe ga alama bacci
take yi ya tsaya daidai kanta yana
yadda ta rame rana daya kacal dagani
ka san ba Karamar wahala ta sha wajen
haihuwar nan ba tausayinta ne karara
46
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
ya bayyana a fuskarsa har ta kaiga ya
kasa jurewa sai da ya risina ya sumbaci
fuskarta sannan ya kai hannu yana
shafar gashin kanta yana mai dashi
baya.
Sam bai ji kunyar Mustafa ba da
ke tsaye kusa da shi kila ma ya manta
da shi ne ta yi alamun zata bude idanu
sai kuma taci gaba da baccinta sun dan
jima a dakin sannan Mustafa ya shafa
cikinsa yace "kai ni fa hantsi yadubi
ludayi 'yar Gusau nake ji kaina ga ba
ma kajin yunwa murna ta kosar da kai".
Ya shafa nasa cikin shima yace
"Karka tunamin wai ance da mahaukaci
ashe ya daina duka ya ce har kun
tunamin Wallahi sam na manta da wata
yunwa amma yanzun tunda an haihu
lafiya na kuma ga matata tana lafiya to
Muje mu nemi wani gidan cin abinci
nan kusa muci don gaskiya ba zan iya
komawa gida ba sai na yi ido hudu da
matata":.
Ya yi murmushi yace in ma nan
zaka kwana babu mai hanaka ni dai mu
47
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
je mu ba ciki nasa hakkin. sun fita
gurin cin abinci su kuma su Inna Amina
suka dinga shigowa suna ganin
Muneeba suna fita saboda har a lokacin
bacci take yi ga dukkan alamu ma
allurar bacci akayi mata tun a gurin cin
abincin nan Mujeeb ya soma sadaka ya
siye kaf abincin da ke gurin cin abincin
yace a raba wa almajirai da gajiyayyu
da ma duk wanda ke da bukata.
Kafin su bar gurin har
ma'aikatan gurin sun soma raba abincin
Muneeba ba ta farka daga baccin da
take yi ba sai gab da Magriba a lokacin
Mujeeb ne ke dakin don kuwa ya kasa
ya tsare ba zai bar asibitin ba sai ta
farka, ya tsaya a gabanta yana mata
sannu da ya ga tana dodarin mikewa
sai ya kamat. Zaunar da ita yana ta
faman yi mata sannu ya tambaycta "Mc
zaki ci? Akwai kunu akwai Ti ga
farfesun can Suwaiba ta yo miki da
kunun gyada mama Amina tasa anyo
miki kunun alkama da farfesun kaza
wane zaki ci? Dama da wata irin
48
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
mahaukaciyar yunwa ta tashi sai tace
zan sha kunun alkamanm da farfesun
kajin amma ka bani ruwa zan wanke
baki na.
Yayi sauri yaje ya kawo mata
ruwa da burosh da makilin ta wanke
bakinta, sannan ya kira Inna Amina
tazo ta zuba kunun ta sa wadatacciyar
madara ta soma sha.
Inna Amina ta ce sannu da
kokari Allah ya kara miki lafiya, bari a
kawo yaran idan kin gama ki ba su
nono don tun dazun suke tsotson hannu
suna neman nono sai ruwan dumi da
glocouse kawai ake basu".
Muneeba ta dan 6ata rai "Mama
tun yanzu za'a fara ba su nono inace sai
gobe? Mama ta harareta "Inji waya ce
maki sai gobe? Ai ana haihuwar yara da
an wanke su ake soma basu Nono kema
don kina bacci ne aka kyaleki to in ba'a
basu nono me za'a basu?.
Tace "Ruwan dumi mana mama
Amina tayi tsaki ta kyaleta tan agama
shan kunun ta zuba farfesun kajin a filet
49
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
ta mida mata ta ce "Gashi nan ki cinye
duka ki bani filet din, sannan a kawo su
su sha".
Та се "Mama duka wannan ai
yayi min yawa a rage? Ta ce ni ba zan
rage ba don banga yawan da yayi ba in
za ki dage ki dinga cin abinci sosai ki.
dage shayar da yara biyu bana rago
bane in ba haka ba ki kanjame saboda
tsotso".
Ba ta sake yin musu ba ta amshi
ferfesun ta cinye shi tas kasusuwa
kawai ta bari a filet din su Khairi suka
shigo da yaran suka dora mata su bisa
cinyarta suna tsokanarta "Bude nonon
ki basu" Ta Hararesu ta ce 'Idan na ki
fa? Mu gayawa Mama gata can waje ita
ta turo mu ko mu haďoki da babansu
kinga kuwa yadda yake son yaran nan
Wallahi kamar zai hadiyesu ya wani.
rungume su dukansu sai sumbatar
kumatunsu yake yi shine Mama ta ce
mu amso su Magariba ta gabato
amkawo su ki basu Nono.
50
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaría
Bude kawai ki basu kada mu tara
miki jama'a azo aga kukanki don
Wallahi tsotson farkon nan akwai zafi
ni kuka riris na dinga yi? Kausar ta
harari Khairi da tayi magana tace Ok to
zuga ta kina cewa da zafi Wallahi sai in
kira mata Goggo. Muneeba na jin haka
ta fiddo nonon tace to Antis dina a bani
ruwa in wanke nonon sai azo a
koyamin yadda zanyi musu.
Maganarta ta basu dariya khairi
ta shiga bayi cikin dakinta ta debo ruwa
a karamin baho ta kawo mata ta wanke
nonon sannan suka taimaka mata ta
soma ba yaran suna cafka a take ta ji
wani zafi tamkar zata kwala ihu ba ta
yi ihun ba illa rintse ido da tayi har
suka sha nonon ba'a salami Munceba
sai washe gari da ta haihu a ranar
Mujceb yayi barin kudi wajen vin
sadaka ga nakasassu da kyauta ga
jama'ar annabi mabukata da yan uwa
bar sai da Suwaiba ta tare shi da
maganar wannan irin barin kudl da
yake yi".
51
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
"wai baban Waleeda ba'a taba yi
maka haihuwa ba ne da kai ke ta barin
naira haka? Ko dai ni da na fara aje
maka kwanka a duniya a ranar banga
kayi wannan barin kudin bako su nawa
ba yayan so bane yanzu ne aka haifo
maka 'ya'yan so tunda matar so ce ta
haife su? Ya girgiza kai yana murmushi
yace Duk 'ya'yanda aka Haifa mini
babu wanda bana so kuma babu wanda
ba zan nuna masa so ba tunda jinni na
ne, amma kin san kyautar 'ya'ya biyu a
lokaci daya babbar kyautace kuma dole
ne in nuna wa Allah godiya ta. Shin
akwai aibu ne idan nayi sadaka don in
nunawa Allah godiya ta? kasa-kasa tayi
magana cikin kunkuni, ni bance da aibu
ba. amma gani nayi tu yanzu zaka fara
nuna bambanci tsakanin 'ya'yanka ya
cc "Eh kece dai kike ganin haka amma
ni ban gani don banga abin da nayi ba
korafi ne kawai zirin na ki da ba ya
karewa bai ci gaba da sauraronta ba ya
fice ya bar mata dakin.
52
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Inna Amina ta kira Innar su
Muneeba don su yi shawarar wadda
zata zauna da Munceba