An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
WATA KUSAN
RAHMATU HASSAN ZARIA
(Mrs. AbdultahtS. Polo)
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
*** *** **** ****
Mummunan tashin hankali nan yayi
tsananin firgita zuciyar Mujceb, shi ne
har yayi sanadiyyar da ransa yayi
balaguro na wucin gadi kafin daga
bisani ya dawo gareshi cikin dakiku
kadan.
Ya bude idanunsa a
hankali yana kallon Muneeba sannan ya
sake rufewa. Hannu Muneeba tasa a
gefen gadonta ta dauko gorar ruwa Faro
da takesha duk dare sai ta shanye
babbar gora, Allah yasa shi ba ya sa
yawan fitsari kamar sauran.
Ta zuba a hannunta ta shafawa
Mujeeb a fuskarsa, ya bude idanunsa da
suka canza launi ya sauke ajiyar zuciya
tare da tsira mata idanu.
"Munceba abin da kika gaya min
shin gaske ne ko kuwa mafarki nayi?
Ta ce, "ba mafarki bane gaske ne cikin
jikina babu shi tun bayan da nayi
mugun mafarkin dana baka labara, ya
sauke wata nannauyan ajiyar zuciya ya
lalubo wayarsa da ke aje gefen gado
3
ب
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
yana tunanin shin wa ya kamata ya kira
don neman taimako a wannan
rikitaccen lokaci? Dr. Aminullah? Kai
wannan matsalar ta wuce da sanin
Aminullah. To wa zai kira? Sai ya tuna
da wani Malami da suka je gurinsa
akan matsalar matar wani dan ofis.
dinsu da aljanu suka hanasu zaman
lafiya a aurensu, kuma cikin ikon Allah
an dace yanzun suna zaunensu lafiya
har ta haihu da kuwa ko batan wata ba
ta taba yi ba.,
Yana da nambar malamin din sai
ya shiga laluben sunansa yayi sa'ar
ganin sunan Malam Abubakar ya latsa
ya. kira shi tayi ringim ba'a dauka ba
yayi kira har wajen sau goma sannan
Malam Abubakar ya dauka suka gaisa
sai ya ke gaya masa matsalar data faru
da matarsa a talatainin daren nan.
Ya ce "Ka kwantar da hankalinka
Insha Allahu babu matsala yanzu ina
matar ta ka? Ya ce, "Ga ta nan zauna
kan gado Wallahi Malam baka ga
girman cikin amma yanzun babu shi,
4
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
sai cikin yayi kamar jaka wadda ba
komai a ciki.
Ya ce "Aikin Jinnu ne ka barni
da su duk wanda aka turo yayi wannan
zaluncin yau zaiga zalunci akansa
kwatantamin gidan inzo yanzun nan
sannan kada ka barta ta sauka bisa
gadon nan har sai nazo"
Ya kwatanta masa gidan. A
daren Malam ya iso ya kira nambar
Mujeeb yace gashi a kofar gidan ya fita
yaje ya sa mai gadinsu ya bude gate din
ghidan Malam ya shigo da motarsa.
Malam na shiga dakin baccin
Muneeba sai ta soma wani irin gunjin
kuka tana tirje-tirje akan gadon yasa
hannu a aljihunsa ya fito da wata leda
mai bakin mai aciki, ai sai kunjinta ya
karu sosai tana nunowa Malam Hannu
"Don girnan Allah kada ka samin
wannan abin don kashe ni zaiyi idan ka
sa min ka yi hakuri"
Mujeeb tun daga nan ya fara
tsorata Malam ya matsa zaisa mata a
hanci Mujeeb cike da tsoro yayi
5
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
magana a hankali, "Malam yi hakuri
kada kasa mata tace abin zai kasheta".
Malam yace "Ba ita zai kashe ba
wani takadiri ne, ai wannan ba
muryarta bane kyaleni da shi koma kayi
zamanka Mujeeb ya kasa zama duk sai
ya firgice, ya tsaya tsuru yana kallon
ikon Allah. Malam ya tsaya a gabanta a
gefen gadon ita kuma taci gaba da
gunjin kuka tare da fadin "Ka yi hakuri
Malam Wallahi yanzun zan tafi”. “Aini
bance ka tafi ba, ba kai azzalumi bane
mata da cikinta har ya kusa isa haihuwa
don zalunci ka zo ka sace mata shi to
nima zan gwada maka zalunci ta yadda
gobe ba zaka kara tunkaro inda take
ba”. Ya kai maganin hancinta ta soma
yinkurin tana ihu tamkar zata shede
saboda azaba, aljanin ya ce "Wallahi na
rantse maka tafiya zanyi ni dama turo
ni akayi inzo in dauke abinda ke cikin
in salwantar dashi kuma har yanka aka
yi min na sha jini shi yasa nima zan
saka musu da abin alherin da suka yi
6
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
min na cika musu umurnin da suka
bani.
Malam ya ce, "ni ban tambayeka
me aka yi maka ba, bama na son ji
wanda ya turo ka kayi wannan danyen
aikin, ina son yadda ka dauke abin da
ke cikin nan yanzu-yanzun ka maidoshi
tun kafin in gana maka matsananciyar
azaba, sannan in kaika kurkuku in
kulleka tunda kai azzalumi ne ba ka da
imani ko kai ba Musulmi ba ne? ya
amsa "Ni musulmi ne? Amma shi ne
aka hada kai da kai za'a zalunce ta? To
yi gaggawar maida abin da ka dauka ko
in kaddamar da żalunci akanka, ka
sanni sarai nima azzalumin kaina ne in
ma banyi maka da kaina ba zan iya turo
'yan uwanka ka sansu wadanda suka
fika iya zalunci su lallasa maka azaba.
Ya ce Eh duk na san haka yi
hakuri zan maida yanzu". Ta soma juyi
bisa gadon ta sa hannu a cikinta tana
murzawa tamkar zata kwaso yan
hanjinta. Mujeeb ya yi sauri zai taro ta
7
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
don a tunaninsa fadowa za ta yi daga
gadon.
Malam Abubakar ya dakatar
dashi da hannu ya koma ya zauna akan
kujerar gaban madubi Mujeeb yaga
abin al'ajabi don dai bai Ankara ba sai
gani yayi cikin Muneeba yana tasowa a
hankali a hankali, bai gushe ba sai
ganin cikin ya yi ya dawo yadda yake ta
koma ta kwanta rigingine tana wani irin
aje numfashi.
Malam yayi magana,"In ka
tabbatar ka maida to fice ta bakin ta
kada in kara ganinka in ba haka ba
kaima ka san sauran.
Takwas Mujeeb yaga tayi a
kwance tamkar mara rai ganin
numfashinta da ke sauke shi ne zai baka
tabbacin tana da rai Mujeeb ya mike ya
iso gaban gadon daidai inda take ya
dubi Malam yace "Sannu da kokari
Malam Allah ya biyaka da gidan
Aljanna nagode da wannan taimako
naka yanzu shikenan sun maido cikin
ba za su sake dauke shi ba". Ya ce
8
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
"Insha Allahu babu abin da zasu sake yi
mata sai dai wani ikon Allah akwai
magunguna da zan bata ta dinga amfani
dasu da addu'o'i wadanda zasu zamo
mata garkuwa tsakaninta da sharrinsu
sannan akwai sharuďdan da zan shaida
mata ta kiyaye akansu to tabbas idan ta
kiyaye suma shaifanun za su kiyaycta.
Yanzu ka barta tayi barci iya yinta har
sai ta tashi zan yi addu'a a ruwa saika
rufe idonta tashi ka bata tasha ta shafa a
fuskarta da jikinta ko ina har cikinta
idan ruwan ya bushe a jikin ta sannan
tayi wanka taci gaba da amfani da
sauran magungunan Insha Allahu kome
zai daidaita kuma Allah ne ya
taimakeka ka kira ni a lokacin da abun
ya faru da ace an dauki lokaci to da
wuya cikin ya dawo don suna dauka za
suje su hallakar da shi ko su watsashi a
teku. Mujeeb ya sauke ajiyar zuciya
tunda Allah ya taimakeshi misalin karfe
hudu da rabi na Subahi Malam
Abubakar ya baro gidan su Mujeeb
9
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
lokacin ana ta kiraye-kirayen Sallah na
farko.
Mujeeb ya dawo zai wuce dakin
Muneeba yaga Goggo tsaye A bakin
dakinta tana ganirtsa tace "Lafiya tun
dazun nake ta jin ana bude gate duk na
tsorata ya ce, Mumeeba ce ba lafiya
amma yanzų ta sami sauki.
Ta ware idanu, "Ba dai nakuda
ba? cikin ai bai isa haihuwa ba sai dai
in bakwaini zata Haifa ko? Ya ce "Ba
nakuda ba te, mu je ki ganta har ta a
sammi sauki bacci ma take "Suka nufi
dakin Muneeba tata tambayar shi, Ina
ka je da talatainin daren nan?
"Wanda ya duba ta ne dana
kirashi a waya yazo yanzu shi na raka
ya tafi dalili kenan da kika yi ta jin ana
bude gate, suna shiga suka iske har
vanzun baçein take yi a rigingine
ciknta yayi wani irin tsini tamnkar yau
abin da ke cikin zai fito duniya.
Goggo ta ce, Me yasa kake bari
tana irin wannan kwanciyar a rigingine
alhalin dukanku na gaya muku yin
10
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
hakan nasa idan aka haifo yaro cibiya ta
nannade shi karshenta ma in ba wanda
ya iya cireta ta shake yaro ya mutu,
tashe ta ta gyara".
Ya đau bargo yana rufa mata
saboda ganin yadda ta takure yatsunta
shi a ganinsa sanyi take ji. Ya soma ba Goggo labarin abin da ya faru tun daga
mafarkin da Munceba ta yi da yadda ta
farka a firgice taga cikin ta wayam
babu shi da zuwan Malam Abubakar da
irin artabun da aka yi da aljanin da ya
ce turoshi aka yi ya sace cikin da yadda
aka yi cikin ya dawo.
Goggo ta hau sallallami tana tafa
hannu. "Eh kwarai kam wannan ture
ne, lallai ni za a sace wa jikoki a ciki
tun kafin su zo duniya to Wallahi koma
waye zan dauki mummunan mataki a
kansa don sai nayi ramuwar gayya.
Mujeeb ya ce, "Ki yi hakuri
Goggo ki kyale koma waye Allah zai yi
maganinsa don girman Allah Goggo ki
daina yarda ana cinye kudinki a iska
duk makaryata. ne masu amsar kudi
11
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
suce za su yi maka abinda bai yi maka
ba, a irin haka har sai a shammace ki a
kaiki inda zała halaka rayuwar jininki
ba ki sani ba.
Gara kawai duk abin da ya
sameki ki tashi cikin dare ki hana
idonki bacci ki gayawa Allah to
Wallahi zai duba matsalarki. Ta sauke
numfashi "Humm" Ai na dawo daga
rakiyar mayaudara nima na yi amanna
da tsayawa gaban Ubangiji cikin
talatainin dare saboda wani waʼazi da
nake sauraro a gidan rediyo. Allah dai
ya fisshemu kunyar duniya da ta
Lahira.
Mujeeb ya amsa da amen guri
suka nema shi da Goggo suka zauna ita
a bakin gadon shi a kan kujerar gaban
madubi suka tsurawa, Muneeban idanu
da ke kwance abinta lakadan tana sauke
numfashi a hankali idan kaga yadda
suka tsura mata idanu zaka ďauka
Kidayar numfashin da take suke yi har
aka soma kiran Sallah da za a yi Sallah
ba ta farka ba Goggo ta dubi Mujeeb ta
12
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
ce. "tashi ka je ka yi haramar tafiya
masallaci kada ka rasa jam'i idan ka
dawo sai inje in yi tawa Sallar".
Ya shiga bayin Munceba yayi
alwalla ya nufi masallaci har ya dawo
Goggo na zaune ya ce "Goggo je kiyi
Sallah ki kwanmta zan zauna da ita har
ta a tashi”.
Goggo ta nufi dakinta shi kuma
yaci gaba da zaman tsammani ba ita ta
farka ba sai wajen bakwai na safe mika
tayi tana salati idanunta karaf suka kai
kan agogon da ke manne a bangon
dakin tana ganin lokaci tayi saurin
yunkurawa zata tashi tana cewa
"SubhannAllahi abokin rayuwa wannan
wane irin bacci nayi da har ban tashi
nayi Sallar subahi ba kai kuma baka
tashe ni ba? ta kare maganar tana
kallonsa ya cc, yi hakuri nasan kina da
larura shi yasa ban tashe ki ba Allah ma
ya san kina cikin larura ba zai kama ki
da laifi ba”.
Ta kai hannu ta shafi cikinta tace
"Ciki na ya dawo ko dama mafarki nayi
13
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
an sace min ciki? Ya ce "Ba mafarki
bane da gaske an sace amma cikin
hukuncin Allah an dawo da shi yi
Bismillah ki sha wannan addu'ar ki
shafa sauran duka a jikinki idan ruwan
ya bushe sai ki je ki yi wanka ki yi
Sallah".
Ta amsa ta sha ta yi duk yadda
ya gaya mata sannan ta dube shi ta ce
"Duk jikina wani irin ciwo yake min
cikin kuma ya kara nauyi tamkar an
Kara min da dutse sam, sam bana jin
dadi".". ya ce sannu ai yanayin jikin naki
sai dai hakuri tare da addu'ar Allah ya
rabaki da cikin nan lafiya.
Suna zaune cikin mintuna kalilan
jikinta ya bushc, ta tashi suka shiga
bayi tare ya hada ruwan, wanka da
kansa yayi mata wanka kamar yadda
suka saba kullum saboda yanayin
larurarta ga tsinin cikin sam ba ta Iya
dukawa ta wanke kafarta da wasu
sassan na jikinta don ko alwala zata yi
shi ya ke taimaka mata idan baya nan
14
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
ga Karime shi yasa in daya ba ya kusa
dole daya yana tsaye a gurinta.
Ta idar da Sallah tana lazimi ne
Goggo ta shigo suka gaisa take ce mata,
Ashe kin tashi Wallahi baccin naki ya
bani, tsoro". Ashe kin shigo ina bacci?
Mujeeb ya ce "Tun hudu da rabi na
darė muke nan tarc da ita Sallah ta tafi
yi.
Muneeba ta cika da mamaki "Ya
aka yi ni ban sani ba? Me ya faru dani
ne? Goggo ta ce, "Abin da ya faru da ke
ne ya kira wani Malam Abubakar cikin
dare aka yi ta artabu da aljanun da aka
turo suka sace abinda kc cikinki da
yake Allah ya fi su cikin ikonsa dolensu
suka dawo da cikin ni abin al'ajabi ya
bani ban taßa jin inda aka sace ciki ba,
na dai san ana sace jarirai.
Mamaki Muneeba ya Karu na jin
abubuwan da suka faru cikin daren
amma ita duk ba ta sani ba ta dübi
Mujeeb, Yanzun kenan ina da aljanu
yanzun?". Ya girgiza kai, sam baki da
su shi ma aljanin da ya sace cikin turo
15
1 WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
shi aka yi amma bai fadi wanda ya turo
shi ba don Malam yace kada ma ya
fada shi ba bukatarsa kenan ba. Ni kam
tunda sun dawo da cikin ai mun gode
Allah, Allah ya Kara tsare min ke da
abin da ke cikinki koma waye ya turo
din Insha Allahu zai ga Karshen sa".
Goggo kam sai sauke ajiyar
zuciya take tana jinjina kai don tabbas
ta san babu wanda zai aikata wannan
aikin inba Hajiya Harira da 'yarta ba,
shi yasa take tsoron al'amuran Hajiya
Harira ta san ita dinma ba kyaleta zata
yi ba. kasancewar yanzun ta fara sakin
layinsu ta soma gano kura-kuranta na
irin kiyayyar da take nunawa 'yar
Kaninta da uwarta alhalin basu yi mata
komai ba balle danta da ake so wannan
cikin sai ya wanke rabi da kwanta cikin
kashi daya na irin kiyayyar da take wa
Muneeba. kilama idan aka haifo jikokin
nata kaunar su ta yi sanadin goge
raguwar kwantan kiyayyar na
Munecba.
16
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Kiran Mal. Abubakar ne ya shigo
wayar Mujeeb yayi saurin dauka tare da
yin sallama Malam ya amsa ya gaya
masa gashi nan a waje ya zo Mujceb ya
mike yana cewa Goggo "Ga Malam đin
nan bari na shigo da shi ya dubi
Muneeba da har a lokacin tana bisa
sallaya yace Maza ki sakaya Malam zai
shigo ya sake duba yanayin jikinki yana
fita ta mide ba tare da shafa maiba ta
dauko doguwar riga ta saka dama sune
kayanta koda yaushe kasancewar duk
kayanta basa shigarta sunyi mata kadan
sai ta karo doguyen riguna ta dinka
wasu don tafi sakewa a cikinsu.
A falo Malam ya zauna Goggo ta
fito suka gaisa tayi masa godiytar irin
gudunmmuwa da yazo cikin talatainin
dare ya bada ya ce "Haba babu komai
mun riga mun sabda irin wannan
taimakon tamkar likitoci muke idan aka
kawo mana za muyi gaggawar yin abin
da ya dace in kuma munga dacewar
muje har gida mu samu mai larura
muna zuwa don wasu matsalarşu ta
17
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
wuce gaban a iya dauko su sai dai
muje. Allah ya Kara mana lafiya ya
rabamu da sharrin mutum da aljan"
Duk suka amsa da "Ameen Ameen"
Tambayoyi sosai Malam yayi wa
Muneeba daga karshe ya bata
shawarwari kamar haka".
"Ina so ki sa a ranki wadannan
magunguna da zan baki ba su bane za
su warkar da ke, nima bani bane zan
warkar da ke Allah ne kadai zai
warkar da ke ya yi miki maganin
dukkan larurorinki amma tare da
taimakawa da shan magani saboda
Allah da kansa yace bai saukar da cuta
ba sai da ya saukar da maganinta. Kada
ki yarda ki yi shirka ga Allah sannan
kada ki yarda kokwanto ko shakku ko
zargi ya auri zuciyarku ki dinga zargin
ko wane ne yayi miki abu kaza shi yasa
abu kaza ya same ki, ki kaddara cewa
duk abin da ya same ki daga Allah ne
ba daga wani ba saboda babu wata
halitta da ta isa ta cutar da ke in ba
18
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Allah bane ya bata ikon yin hakan
kinga sai ki nemi waraka daga gurinsa.
Ki kasance mai tsarkin zuciya
kada ki yarda ki cuci wani daidai da
kwayar zarra in ma mutum ya cuceki to
ki barshi da wanda ya hallice shi in ma
kinsan tabbas shi ya cuce ki to ki yafe
masa tare da nema masa shiriya gurin
Allah. Abu na gaba ki kasance mai kula
da ibada kuma ki kyautata ibardarki ki
dinga yin azkar ko da yaushe ki dinga
yin itigfari a kalla sau saba'in a rana ko
dari kada ki kuskura ki kwanta sai kinyi
alwalla sannan idan za ki kwanta kiyi
addu'ar kwanciya bacci kuma ki daina
barin kanki a bude ki daina kwanciya
tsirara daga ke sai zani don zai iya
kwancewa ya barki baki sani ba, su
kuma shaidanu sun sami hanyar shiga
jikinki su cutar da ke.
Ina fatan duk kinji bayanai na
kuma za ki dinga kiyayewa? Ta ce "Na
ji na gode Insha Allahu zan kiyaye ya
bata magunguna yayi mata bayanin
yadda za ta yi amfani da su babu fashi
19
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
ko tsallake har sai sun Kare sun fita tare
da Mujeeb zai yi masa rakiya ya kawo
rafar dubu hamsin ya mikawa Malam
shi kuma ya ki amsa ya ce "Wadannan
kudi sunyi yawa ka rage sannan in
amsa ya ce "Ka yi hakuri Malam ba
zan iya ragewa ba, saboda ni abinda
kayi min ban isa in biya kaba sai dai
inyi maka addu'ah kai da zuri'arka
Wallahi kafi Karfin wannan kudin a
gurina ihsani ne kawai nayi maka,
Allah ne kadai zai biya ka.
Da kyar Malam ya amsa sukayi
sallama ya shiga motarsa ya tafi sun yi
cewa da wata matsalar ta taso to ayi
gaggawar sanar' da shi don rayuwarta
na cikin hatsari amma da izinin Allah
babu abin da zai faru.
Goggo da kanta ta shiga dakin
Suwaiba ta gava mata Munecba ba ta
da lafiya, amma ba ta gaya mata abin
da ya faru ba saboda sanin hali ya fi
sanin kama.
Da kyar ta iya shiga ta gaisheta
saboda sam ba ta kaunar kallon cikin
20
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
na Munceba sakamakon wani bakin
ciki da ke tokare kahon zuciyarta sai
taji tamkar ma tayi ta naushin cikin har
sai 'ya'yan da ke cikin sun mutu in ma
so samu ne har uwar ta mutu babu
ruwanta amma babu hali yin sata a
lahira azo duniya a siyar. Goggo da
kanta tayi waya Dukku ta shaida musu
Muneeba fa bata da lafiya amma bata
fadi matsalar da ta faru ba aikuwa
washe gari 'yan Dukku suka yo mota
guda suka zo gaisheta Innarta ma da
Murja har da babansu sunzo a motar
Mustafa tare da Mustafan.
Murja ta dubi Muneeba lokacin
su biyu ne a dakin ta ce "wai Muneeba
kin sake yin hoton cikin nan kuwa don
ni ban yarda da daya ne a cikin nan ba
in kuwa daya ne za'a ga shirgegen da?.
Munecba ta karasa shanve ruwan
zam-zam mai kumshe da addu'a da ta
tsiyaya a kofi duk Malam Abubakar ne
ya bata sannan tayi magana, jiyan nan
da naje awo aka sake yi min hoto ashe
dai 'yan biyu ne kamar yadda mutane
21
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
ke ta fadi, sunce daya ne ya kwanta
akan daya shi yasa idan anyi hoto ake
ganin guda daya wai a dunkule suke
guri guda"
Murja tayi ihun murna na ta ce,
Kai Alhamdulillah ina murna da jin
wannan labara wai ya Mujeeb yayi da
murna yadda naga yana dokin cikin nan
kamar ma ya fi ki zumudi kan samun
cikin nan? Ta ce kin san ina asibitin da
na yi masa waya na gaya masa abin da
scanning din ya nuna sai dai yazo ya
gani da idonsa don zumudi ni kam ai
nayi saranda na san ya fini zakewa don
a gaban kowa zancen cikin nan da
haihuwata yake yi ni ko ina zan iya".
Dan halas din kuwa tana rufe
baki yana śhigowa dakin kai tsaye
gabanta ya nufo bayan yayi sallama ya
jikin naki ko da yake kinga su Inna kin
murmure sai murna kike yi ko nema na
ba ki yi ba" ta yi dan murmushi ta ce
Wallahi kana raina yanbzu nake
tunanin in kira wayarka inji ko ka fita
ne.
22
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
Ya ce Ina zan fita in barki'yau
Ofís ma dole suka daga min dafa ce
musu nayi ni da matata bamu da lafiya
dukansu ita da Murja dariya suka yi
Murja ta ce "Au ashe har kaima ba ka
da lafiya ai bamu sani ba" ya ce
"Gimbiya ta ba lafiya dole nima bani da
lafiyar kallo na kawai kuke a tsaye ni
tun yanzu ma har na fara mata nakuda,
dama Goggo tace daga wata bakwai ake
fara nakuda.
Wata dariyar suka sake yi masa
Murja ta ce, Shi kenan ke kin huta 'yar
gata har nakudar ma tayaki za a yi ina
Yaya na yazo ya dauki sabon darasi ya
sa hannu yana mammatsawa Muneeba
kafarta yana cewa "Na ga kafafdun
kamar sun dan sabe yau? Ta ce, nima
haka na lura har ciwon da suke yi ma
sun rage. Murja ta ce h Mujceb ashe
'yan biyu za mu samu? Ya washe baki,
"Wallahi kuwa har na riga kowa ganin
su a kwamfuta, duka maza ita da take
son mace gashi duka maza ne sai ki bari
wata shekarar kya haifo macen bayan
23
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
kin'haifo min Mazaje na. ta danyi masa
harará ta ce "Ai Insha Matan zan Haifa
tun das u ma asibitin a hasashen suka yi
babu tabbas tunda sun sha cewa na miji
a haifi mace ko suce mace a haifi
namiji mace ko suce mace a haifi
namiji ko suce 'yan biyu a haifi daya
ko suce daya a haifi 'yan biyu duk
karya suke idanb har kaga an haifi abin
da suka ce to dama can hakan Allah ya
kaddara za';a Haifa ni kam Insha
Allahu mataye zan haifo wata shekarar
na haifo maka mazajen. Ya ce bakinki
ya sari danyen kasha ai baki isa ba ki
dai fara haifo min nawa naki sais u biyo
baya in kuma ba haka ba inyi tar okon
Allah su zama 'yan hudu biyu mata
biyu maza kjin gas hi kenan rigima ta
Kare".
Munecba ta watsa masa idanu
tana shagwaba, Ni ni Wallahi yaya
Mujeeb kada kayi min wannan addu'ar
in azan kai 'ya'ya hudu Allah ma kada
ya amsa wannan addu'ar aid a shikenan
na zama Allah sarki biyun ma yanzu sai
24
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
zullumi nake yi naga masu goyon daya
ma suna wai waiu balle biyu bare kuma
hudu ai sai dai ka aje aiki muyi
rainonsu tare ya ce “Ai in dai zaki haifo
hudun sai in aje aikin don samun
'ya'yan ni ya fi min samun aikin tunda
gashi nan shekaru nawa ki ka kwashe
bamu samu ba sai yanzun gara kawai
kiyi uku uku ko hudu, hudu kiyi ki
gama.
Ta soma shagwaba, Ni dai
Wallahi bana son addu'ar nan taka
nasan halinka baka san wasa yanzun
kana iya hana idonka bacci kayi mini
wannan addu'ar. Murja dai tana jinsu
tana musu dariya har Mustafa ma ya
shigo falon aka ci gaba da hirar dashi,
har lokacin ya fiyarsu yayi suka tafi
tare da yi mata addu'a Alllah ya raba ta
lafiya da cikin jikinta.
25
WATA KUSAN 4 Rahmatu Hassan Zaria
**** **** ****
Tun da cikin Muneeba watan ya shiga
haihuwa sai wahalhalun ciwo suke
tsananta a gareta yau nan ke ciwo gobe
can har ta kai bata iya yin komai sai anyi mata don ko sujadar Sallah bata
iya dukawa daga zaunen da take Sallar
sai dai koma a zaunenta ke yi saboda
girma da tsinin da cikin yayi abin ya
euce tunanin duk wani mai tunano idan
ta zaune shima cikin zama ya ke a kasa
dirshan in kuwa a kwance take to shi
ma kwanciyar yake a gefe guda duk
mai imani da ya ganta a wannan halin
sai ya tausaya manta balle Mujeeb
wanda ya fi kowa tausaya mata ya
shiga tsananin damuwa