da ba ya iya boyewa ko a gaban
waye ya ke.
Su kuma Suwaiba ita da Hajiya
Harira suna ta kulle-kullensu na ganin yadda za ai su salwantar da cikin
Muneeba sun yi ta zaga gidajen bokaye
da Malaman tsibbu suna narka masu kudi
amma duk a banza ba su cimma nasara
ba, balle da Suwaiba ta sami labarin
hoton da akayi ance da namiji ne sai suka
sake bazama gidajen bokayen don ganin
kota halin yaya ta haifo abin da ke
cikinta a mace tun lokacin haihuwarta bai
yi ba.
Ranar wata Asabar yana gida baije
aiki ba kasancewar ranar hutu ce sai sha
dayan safe ya tashi daga bacci ya shiga
dakin Goggo suka gaisa yake tambayarta
Muneeban ta ce ita bata ji motsinta ba
tun safe da ta zo suka gaisa.
Ya nufi dakin Muneeba bai isketa
a falonta ba ya zarce dfakin baccinta a can
ya same ta zaune a tsakiyar gado ta
191
WATA KUSAN З Rahmatu Hassan Zaria
mimmike kafafunta da suka kumbura
suntum.
Ya hau gadon yana tambayarta
"Lafiya yau baki fito ba, jikin ne? Ya kai
hannu yana lallatsa kafafun nata". Ta се
"Wallahi su ne gashi nan yau sun dame ni
da ciwo da kyar nake tafiya", ba' an baki
magani a asibiti ba da kika je"? Sun bani
ina shafawa amma abin sai addu'ah.
Ya shafo cikin nata, dad yayi
zungurere ya ce, Gaskiya Muneeba girman cikin nan ya bani mamaki tun bai isa watan
haihuwa ba gashi nan da kyar kike yin
komai bari in Kira Dr. Aminullah in masa
bayanin kafar nan ko akwai wani magani
da za'a gaya mana mu siya.
Ya kira wayar Dakta yayibmasa
bayani sai yace zai zo anjima ya kawo
mata wasu magunguna Mujeeb da kansa
ya shigo kicin dinta ya hado mata abin
karyawa ta karya sannan ya hada mata
ruwan wanka da kansa ya kaita bayi yayi
mata wankan ya shafa mata mai ya sa mata
192
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
१
kaya sannan yace ta dawo falo ta zauna
kada ta kwanta.
Da Karime ta zo ita ya sa ta gyara
dakunan ta wanke bayi ta sa turarukan
wuta, ita kuma ya ce koda ta yi aikin
komai ta zauna ta huta.
Bokan da su Suwaiba suka je
gurinsa ya tabbatar musu lallai idan ta
saki kudi to zai yi mata aiki na ban
mamaki don zai tura wani iblishin. aljani
ne ya bi dare ya sace dan da ke cikin
Muneeba sai dai ta farka ta ga babu cikin
kuma ya tafi kenan har abada.
Murna ta kama su saboda jin
wannan aiki mai sauki sai dai boka ya
bayyana musu dole za a yi wa aljanin da
zai yi aikin yanka ne na bijimin sa wanda
a kalla ya kai dubu dari biyu shi kuma
kudin aikinsa dubu dari, kenan zasu
kawo dubu dari uku.
Sun dawo gida cike da tunanin
hanyar da za su samo wadannan kudade
cikin 'yan kwanaki yunda dama aikin ba
193
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
1
2
C
C
a
k
2
h
n
y
d
s)
b.
a yi sai ciki ya shiga wata bakwai, kuma
gashi yanzu ne a lissafinsu ya shiga wata
bakwai idan ya wuce bakwai ba a yin
aikin.
Babban gwal din Suwaiba wanda ta
siyo da suka je aikin Hajji shi suka kai
kasuwa suka sayar dubu dari biyu da 'yan
daruruwa. Ana neman cikon dubu dari.
Haka nan Hajiya Harira ta saka filinta a
kasuwa aka siye shi a wulakance Dubu
Dari da Ashirin abinda ta siya Dubu Dari
Biyu tunda abin na gaggawa ne.
Sun hada kudin Dubu Dari Uku
suka kaiwa Boka ya ce su je su jirayi abin
da zai faru cikin kwana bakwai da za su
Zo.
Har akayi kwana biyar babu wani
abu daya sami Muneeba lafiyarta samul
m ranar Litinin ta je Asibiti Awo a can ne
ai suka sake bata hoto saboda mamakin da
watannin cikin ya basu, wai ciki wata
bakwai amma girmansa ya wuce misali
194
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
2
nauyinsa ma ya zarce tunanin tamkar na
mai wata tara.
Wannan karon 'ya'ya biyu aka
gani a hoton wai ashe dayan ya kwanta
akan dan uwansa ne sun dunkule suke
bada mutum daya, yanzun kuwa ga su
nan su biyu hoton.
Tun a asibiti Muneeba ta Kira
Mujeeb tana gaya masa Murna ya hau yi
ya ce "Yanzu kina ina ne". Ta ce Gani
nan a asibiti ni da Karime Jume na
jiranmu zai maida mu gida ya ce Kice
masa ya tafi gida gani nan zuwa da kaina
zanzo in dauko ki, ya tafi da karimen".
Ta dubi Karime ta ce "Ki je ki
cewa Jume ku wuce gida ga Yaya
Mujeeb nan zai zo ya daukeni ina jin
wani guri za mu je, ki dafa min Indomi
da dafaffan kwai yunwa na ke ji sosai".
Ba su dade da tafiya ba Mujeeb ya
zo asibitin sai da ya biya wani kudin aka
sake yin hoton wai so yake ya gani da
idonsa, ya kuwa ga 'ya'yan su biyu
195
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
kwance cikin koshin lafiya tun a asibiti ya
kira ya gayawa Goggo an sake yi wa
Muneeba hoto anga 'ya'ya biyu ai
Suwaiba na jin haka ta ji tamkar za ta mutu
don bakin ciki.
Tunda suka dawo gida cikin
Muneeba ke ta murda mata da ciwo
'ya'yan cikin nata sai watsalniya suke yi
sun hana ta sakat zama dirsham Mujeeb ya
yi yana kallon wannan iko na Allah mutum
cikin mutum yana mata sannu saboda
rintse idanun da take yi yace "ina ganin
yamutsa cikin da akayi yau shi yasa kike
jin ciwo.
"Ta ce ni dama duk ranar da na je
awo sai na yi wannan ciwon cikin amma
na yau yafi na kullum kafin dare ciwon ya
lafa mata har ta yi wanka ta ci abinci sai
dai kadan-kadan ciwon ke mata.
Tare da Karime suke kwana amma
yau sai Mujeeb ya ce Karimen ta je gida
shi zai kwana da ita in har girkinta ne to
can take zuwa dakinsa ta kwana in ba
196
스
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria |Σ
girkinta bane shine Karime ke zuwa ta
taya ta kwana. Yau ma ba girkinta bane
amma yace sam ba zai yiwu su kwana da
Karime ba tunda bata da lafiya shi zai
kwana da ita don baisan me dare zai
haifar ba.
Cikin dare Muneeba tayi wani
mugun mafarki wai wani mutum ya
biyota da wuka suna ta fafata gudu a
dokar daji ba gida gaba ba gida baya har
sai da tazo gabar wani kogin a rami ya ke
sai ta fasa fadawa kawai ta tsaya.
Mutumin ya iso ya kamata tana ihu
tana rokonsa ya kwantar da ita tana gani
ya sa wuka ya fede cikinya ta kwaso
'ya'yan cikin guda uku ne ba ma biyu ba
tana ji tana gani ya tashi sama da su tana
kallonsa har ya bace a sararin samaniya
ita kuma ta kasa tashi sai ihu take tana
neman dauki.
Haka ta farka a firgice tana salati
tare da fadin Innalillahi wa'inna ilaihir
Rajiun Allahumma Ajumi fi musibati wa
197
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
akhlufni khairan minha sai taji cikinta
wayan ba ciki ba alamarsa ta kai hannunta
a firgice ta shafo cikin sai ta ji babu shi
wayam.
A firgice ta tashi Mujeeb dake
kwance a gefenta tana nuna masa cikinta
ganin babu cikin ya sa ya tashi shima a
firgice yana tambayarta. "Kin haihu ne
baki tashe ni ba? Ta girgiza kai ya ce,
Bangane a'a ba to ina cikin jikinki? Tana
kuka ta labarta masa irin mugayen
mafarkin da tayi ai bata Ankara ba sai
ganinsa ta yi ya tafi luuw yana sambatun
fadin Innalilahi Wa'inna Ilaihir Rajiun.
DOLE IN DAKATA ANAN DON NIMA
KANIN SUMA NAYI TARE DA YIN TASBIHI GA
ALLAH.
KU BIYONI A LITTAFI NA HUDU WANDA
SUKA FITO TARE DA NA UKU
3
TAKU
RAHMAN ZARIA
080-6889-5555, 080-2843-4948
198
*
*
LITTAFAN MARUBÜCIYAR
SANIN HALI 1,2,3
HUJJATA 1,2,3
MENE AIBUNA?
ALKAWARIN DA CIWO 1,3
NA YI BIYAYYA 1,2
WA YA CUCE NI? 1,3
BAYAN WUYA 1,2
SAIHAМ 1,2
* MU YI HATTARA 1,2
*
AUREN MANUFA 1,2
SIRRIN GIRKE-GIRKE 1,2
MIJIN ARO 1,2
ILLAR KUSANCI 1,2,
DON MAʼAURAТA
WATA KUSAN 1,2
MUHAMMAD SANI BOOKSHOP
CHARANCI ROAD KASUWAR BARG
080332684404,07089897389
AL-MUSTAFA BOOKSHOR
BAKIN RIMI GIDAN JUMA S/GARI ZARIA
08026570893, 08130616029
ABUBAKAR ABUB
RABLL WUSE BOOKSHОВ
Wuse market zone 1 Abuja.
08030777669, 08091331166
No Ag 1 Anguwar rimi
market Kaduna
08023607345
HNARS BOOKSH
Behind Kofar Doka Central Motor Park, Zana
08028341964.
el
Layi Na Hudu Bayan Masallacin Abacha
A.A. Rimi Market, Kano
Inside Club 69 Garejin Hayi-Hayl
Sheik Abubakar Gumi CentralI Markat Kaduna. 07066708030,08029645801
Desia
ZAZZAU VENTURES
General Printing & Publishing 08028401199, 08035336868
Block A 36 Inner Idear T/wada Zaria.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels