shigo dakin ta dubi Isah a
gadarance da nuna'isa ta ce "Wallahi
wulakancin da kake mani da nuna iyaka ya
isheka haka in ba wulakanci ba inzo duba
mijina sai ka rufemin kofa kace in tsaya a
waje sai kun gama, ko kafini kusanci da
shi ne a yanzu da har baka son in ganshi a
halin da yake ciki? In ma wankan za'a yi
masa ai mu ya kamata mu yi masa kai bai
dace kaga tsiraicinsa ba sai mu nan
balle.......???
Ke! Dakata don Allah ya isheki haka
wannan wace irin sakarcin magana ce
mara kan gado maganar da bata dace da
bakin mai hankali ba in ba sakarai ni dai
baki isa ki raba ni da dan uwa na ba in kina
takamarki raba 'yan uwa saboda haka ki
bini a hankali kawai.
"In kuma na ki fa? Na ce in kuma
naki fa? Ta sake maimaitawa ya gyada kai
yace "Zamu ci gaba da 'yar tsama da ke
kinsan sanni bani da mutunci ga duk
wanda bai rike mutuncin kansa ba tunda
54
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
girman danake baki a matsayin matar
yayana ke bakya gani duk da na girmeki
a shekaru to zan watsar da girmamawar
dama ance idan tsoho baiji kunyar hawa
jaki ba to shi kuma jakin ba zai ji kunyar
nana shi da kasa ba
Ta yi kwafa "Shi kenan muci gaba
da zubawa za'a gawanda zai fasa". Da
yake Muneeba na bayin cikin dakin bata
san wainar da suke toyawa ba, Goggo
kuma na gida shi yasa aka rasa mai shiga
tsakani ya tsawatar musu har suka yi
suka gama.
Karshen badakalar Muneeba ta fito
ta riska shine fa tayi ta basu hakuri tare
da nuna musu ishara akan abinda -ya
samu Mujeeb wanda ya ishi duk mai
hankali yasan mutum ba'a bakin komai
yake ba duk matsayinsa.
55
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
****** ****** *******
Alhaji Ayuba da mijin Inna Amina sun
hadu sun tattauna dangane da fita da
Mujeeb da za'a yi kasar waje sun tsayar da
matsaya akan za'a kaishi kasar (CAIRO)
wato (Egypt).
Sun tattauna da likitocin asibitin da
za'a kaishi har sun basu Appointment Date
din da zasu isa can za'ayi tafiyar ne da
Muneeba sai can akwai wani abokin mijin
Inna Amina zaune yake da iyalansa shi zai
jagorance su.
Ranar wata Laraba wadda kwanan
Mujeeb kusan Talatin kenan a halin da
yake ciki Muneebace ke tsaye a kansa
tana shafa masa rowan zamzam mai dauke
da addu'o'i kamar kullum yadda take
masa, cikin ikon Allah ta shafa masa a
fuska kawai sai ta ga idanunsa na motsi
alamum kamar yana son ya bude su.
Yayi motsi da idanun a hankali har
Allah ya taimakeshi ya bude su tangarau
56
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
amma shi sai yana ganin mutane dusudusu sai dai hakan baisa ya kasa gane fuskar Muneeba ba.
Ya tsura mata ido tamkar yana
karantar wani abu a fuskanta tata ko
kuma yana son ya gano wani abu murna
ta kama Muneeba ta daga hannuwa tana
yiwa Allah hamdala ta kwasa da sassarfa
tayi waje a harabar dakin Inda Goggo
suka shimfida tabarma suke zaune ita da
Suiwaba Isah kuma yaje siyo wata allura
da za'a amfani da ita.
Goggo ta tsorata da yadda ta ganta
a sukwane ta soma tambayarta "Lafiya"
me ya faru Goggo zo kuga ikon Allah
Yaya Mujeeb ya bude idanunsa har yana
motsi da baki kamar zaiyi magana. Ai
Goggo tamkar zata kifa haka ta táso da
saurinta Suwaiba ta rufa mata baya suka
shiga daki kewaye gadon sukayi suna
godiya ga Allah ya kurawa Goggo idanu
kyar ta soma kiran sunansa yayi alamun
kamar yana amsa mata amma sam baka
57
e
ir
a
a
u
a
a
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
jin me yake cewa sai dai bakinsa dake
motsi.
Ya soma alamun zai daga hannunsa
mai Karaya Goggo tace Muneeba yi sauri
ki kira Likita". Likirta tare da wasu Nosis
guda biyu suka shigo dakin suka umurci
dasu Goggo su basu wuri zasu duba shi
kowa ya fita ka barsu.
A waje Isah ya dawo ya gansu suka
shaida masa abin murnar da ya same su
shi ma daga hannu sama yayi yana wa
Allah Godiya daya nuna musu wannan
rana.
Ya tambayi Muneeba yayi magana
ne? Ta ce, Bai yi magana ba amma yanata
motsa bakin alamun yana son zaiyi
magana ai Insha Allahu sauki ya fara
samuwa kenan addu'o'i takobin mumini ce
Isah ya dubi Muneeba muna mika
godiyarmu ga ALLAH mara iyaka sannan
kuma mika godiyarmu gareki saboda
jajircewarki da tsayawarki a kansa da
addu'o'i babu dare ba rana wallahi ina
58
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
alfahari da samunki a matsayin 'yar uwa kuma mata ta gari Jaruma abar so ga Yayana Allah ya kara maki karfin guiwa ki kara tsayuwa akan al'ummuran mijinki tsakani da Allah, muna nan tare dake Insha Allahu".
Likitan da mukarrabansa sun dauki lokaci suna duba shi daga bisani suka fito tare da yi masu umurnin su koma dakin su zauna tare dashi ya sami komawa bacci amma bazai dade ba zai sake farkawa kada suyi nesa dashi sun kewaye gadon nasa suna kallon ko daga yadda yake sauke numfashi sun tabbatar lafiya ta soma samuwa sabanin da ba baka iya gane ko yana numfashi ko ba yayi sai kayi tsananin lura zaka gane hakan.
Bai wuce mintuna ashirin ba ya sake bude idanunsa ya dinga binsu da kallo daya bayan daya daya kali Muneeba sai kawai suka ga ya kura mata idanu hawaye na ambaliya a kuncinsa ya
59
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
dade cikin yanayin zubda hawaye wanda
basa raba daya biyu hawayen nadamar
abubuwan daya dinga yi mata ne a gidansa
da jingineta da yayi a gaban iyayenta.
Itama sharer kwallar ta shiga yi
idanunsa na kaiwa fuskar Suwaiba sai suka
ga yayi sauri ya rintse idanunsa bai sake
budewa ba sai dai hawaye da yake
gangarowa ta gefen idanun sa.
Dukansu mamaki ne ya kamasu na
yadda Mujeeb baya son kallon fuskar
SUWAIBA hakan ne nuni da wata ayar
tambaya a tsakanin al'amarin nasu wanda
babu wanda yasan amsar hakan sai su biyu
sai Allah da ya halicce su.
Wannan al'amari ya daurewa kowa
dake gurin kai na yadda da zarar Mujeeb
ya bude idanunsa sunayin arba da fuskar
Suwaiba sai ya rufe idanunsa ga dukkan
alamu ma kila da yana iya sarrada
harshensa da yayi umurni kada ya sake
ganinta kusa dashi.
60
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaría
Idan yayi ido hudu da Goggo ma
hawaye yake yi Muneeba ma hawaye
amma Suwaiba rufe idanu kai wannan
abu da ban al'ajabi Muneeba tayi masa
addu'o'i kamar kullum tana tofa masa
data gama kuma ta lura har ya sake
komawa bacci sai ta koma gefensa ta
zauna ta dauki wayarta tana ta kiran yan
uwa da abokan arziki tana shaida musu
cigaban da aka samu lafiyar Mujeeb hatta
Ogansa sai data kirashi ta layinsa da ke
wayar Mujeeb din ta gaya masa tunda
wayar na hannun Isah.
Kafin wani lokaci 'yan uwa da
abokan arziki na kusa sun fara isowa
asibitin don taya murnar wannan cigaba
da aka samu Alhaji Ayuba shine na
farkon isowa asibitin tare da wasu
abokan Mujeeb din.
Fuskokinsu cike da murna a
lokacin da suka yiwa gadonsa zobe suna
yi masa sannu tare da addu'o'i shi kuma
yana bin kowannensu da idanu tamkar
61
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
yana amsa sannu da suka masa ne. likita ya
sake shigowa ya duba shi sannan suka fita
tare da Alhaji Ayuba zuwa Offis.
Likitan ne ya soma masa bayani
"Kaga cigaban da aka samu na samuwar
Lafiyar Mujeeb ko Alhaji"?
Ya gyada kai "kwarai na gani likita
kuna nayi murna sosai muna yiwa Allah
godiya tare da Addu'ar Allah yasa lafiyar
ta dore mu dinga ganin ci gaban lafiyar
tasa kullum.
Ya amsa Ameen shi ya sa ai da ku
ka zomin da maganar zaku fita dashi na
baku hakuri daku dan saurara ku bamu
lokaci tunda muma muna iya bakin
kokarinmu bisa ga tamu kwarewar munasa
ran da izinin Allah zai sami lafiya anan
din ba tare da kunyi wahalar kaishi wata
Kasa ba.
Wallahi Alhaji can din ma idan kuka
je zaku iske kwararrun likioci duk 'yan Najeriya ne irinmu abin da zasu masa acan
muma irinsa zamu yi masa bambancin
62
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaría
daya ne sun fimu ingantattun kayan aiki
a kwarewa suka fimu ba, muma da
gwamnatinmu zata wadata manya
asibitoci da kayan aiki a inganta mana
albashi da alawusoshinmu wallahi da
babu wanda takaici zaisa ya tsallake
kasarsa ya tafi yana hidimantawa a wata
kasa da arziki a garin wasu ai gara a
garinku mukam muna nan zamu ci gaba
da taimakawa al'ummar kasarmu da ita
kasar kanta mu baje kolin basirar da
Allah ya azurta kwakwalmu dashi muna
fatan mu samu sakayya ranar gobe
kiyama.
Alhaji Ayuba ya numfasa tabbas
zancen Dr. Aminulalah gaskiya ne
shikam har yaji bashi da sauran burin kai
kansa ko iyalansa ko wani nasa asibitin
ketare gara ya nemi ko wane asibitin ne
in dai a fadin Najeriya yake tunda ko
Zaria akaje (A.B.U.T.H. Shika) akwai
zakakuran likitoci masu gani har uwar
daka ga babban asibitin koyarwa na
1
1
63
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Malam Aminu Kano ga Babban Asibitin
Ibadan inma kashine yayi gardama ga
asibitin Kashi na Dala a Kano to me ya.
rage!.
Ya dubi likitan yace "Gaskiya na
gamsu da bayaninka likita don wallahi
bayaninka ya warware min kullin damarar
da nayi ta fita da yaron nan kasar waje ka
ruguza komai dana tsara saboda haka
zamu barshi a gurinku muna rokon Allah
ya taimaka muku ya baku sa'ar shawo kan
matsalar ciwon yaron nan Allah ya bashi
Lafiya likita ya amsa da "Ameen Alhaji
haka muke so a dinga karfafa mana guiwa
hakan na kara mana karsashi ba a nuna
mana kasarmu ba alhali muna iya bakin
kokarinmu akan duk wani majinyaci da
za'a kawo mana cikin kwanaki bakwai da
samun saukin Mujeeb likita yayi umurni
da a fara bashi abinci amma mai ruwaruwa kamar ti ko kunun ko koko amma
mara kauri.
64
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Muneeba jikinta har rawa yake yi
jin wannan umurni na likita ta fiddo
kayan Tin dake lode cikin Loka, Isah ya
tsiyayo ruwa a Filas ta hada masa Ti mai
kauri ta aje a gefe don ya huce sannan
tace Isah ya dauko Roba da ruwa a buta
tasa makilin a burush wani Nos ya
taimaka musu suka tada shi suka jingina
shi jikin allon gadon.
Muneeba ta sa Burosh a hankali ta
goge masa bakinsa da kyar ta samu ta
tura Burosh din tsakiyar harshensa ta
wanke shi sai ba uhm ba uhum yana dai
ta binta da kallo har ta yi ta gama.
Isah dake fifita Tin ya miko mata
ta dan kurba don ta ji yanayin zafinsa
Isah ya yi dan Murmushi ya сe "Kai
Aunty ai ba zan bari ya kona mai baki
ba" Itama murmushi ta yi tace, "Ai na ga
ka kosa a bashi ne ba ka san na fi ka
kosawa ba fiye da wata guda mutum bai
sa komai a bakinsa ba sai dai Karin ruwa
in banda sun ce akwai abinci a karin
65
e
i
e
a
n
E
1
Π
Π
D
a
a
WATA KUSAN 3
Rahmatu Hassan Zaria
ruwan ai da mutum ya mutu kai ai ciwo bai
yi ba Allah ya rabamu da ciwo.
Ta soma bashi kadan kadan yana
sha har sai da ta ga yana kin karba sannan
ta aje kofin ta amshi (Tissue) da Isah ya
gutsiro ta goge masa baki
Nan fa ya soma sana'arsa ta zubda
hawaye Muneeba ta girgiza masa kai tace
"Don Girman Allah Yayana ka daina
yawan zubda hawaye nan kada damuwar
dake saka hawaye ta sake jefa zuciyarka
cikin wani halin. In har kana ganin wani
laifi kayi min da ke saka zubda hawaye
idan ka dubeni to ni baka yi min komai b
in ma kana ganin ka yi mani to wallahi ni
tuni na yafe maka ban kullaceka da komai
ba in kuma ni ce na yi maka laifin to ka yi
min afuwa ka ya fe min.
Alamun murmushi ne ta gani ya
bayyana a fuskarsa ya dan lumshe
idanunsa ya bude su tar akan nata hakan da
ya yi sai da ta ji wani sabon sonsa ya
malalu a zuciyarta ta dinga tunano rayuwar
66
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
aurensu ta baya musamman zaman
amarcinsu. a Dukku yadda ya dinga
riritata da nuna mata so da kauna duk da
ba ita bace zabinsa amma ya yi marhabin
da shigowarta rayuwarsa da zamansu na
Gombe kafin zuwan Suwaiba wadda ta
rikirkita komai ta damawa
kwakwalwarsa lissafin har aka kai
matsayar da ya dinga hantara da
kyamarta har dai ya kare ya nuna baya
sha'awar cigaba da zama da ita.
Hakika da anbi ta ra'ayinsa da
yanzu ya guntule igiyar aurensa dake
kanta tunda biris din da yayi da ita a
gaban iyaye ba waiwaiye alamu na su
neme shi ya bata takardan kuma da an
neme shin daya aikata hakan, shi ya sa
hakuri ke da ranarsa in ka ga hakuri bai
yi wa mutum rana ba to kadan ya yi bai
da yawa ba.
Tun daga wannan lokacin sai
Mujeeb ya dinga samun sauki daga Allah
tare da kulawa ta Musamman. daga
67
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
matarsa Muneeba sannan ga Isah shi ma
yana nan tsaye in baya nan to ya je
makaranta Suwaiba kam sai ta rage zuwa
saboda yadda ya nuna sam baya son ganin
fuskarta har gara in tana rike da Waleeda
to zai yi kallon Waleeda amma ita sam ba
zai yadda su yi ido hudu ba.
Dr. Aminullah ma ya yi tsayuwar
daka akan ciwon Mujeeb din babu dare
babu rana sannan ko yana hutun aiki ne ya
kan zo ya duba shi har a hutun karshen
mako haka nan ya dada karfafawa
Muneeba gwiwa akan cigaba da yi wa
Mujeebun addu'o'i da ta ke yi tare da
shafa masa zaitun a gabobinsa tanbayi tana
mummurza gabobin saboda su farfado su
koma aiki yadda ya kamata kuma ana
ganin nasara tunda har ya fara motsi da
'yan yatsunsa na kafar da bata aiki.
An yi nasarar gyaran aka yi wa
Mujeeb na karayar hannunsa an kwance
Filasta hannun ya yi daidai yanzu matsalar
da za'a fuskanta itace ta ganin sashen
68
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
jikinsa ya soma aiki wanda ana sa ran
hakan ta faru a kowane lokaci tunda har
yatsunsa sun soma motsi sai Babbar
matsala ta rashin maganarsa, amma ko
me aka fada yana ji tangarau.
Goggo ta bada shawarar tunda
hannunsa ya warke kuma har an sayi
keke an gungura shi a ciki ana fita da shi
yana shan iska to kamata ya yi a
maidashi gida aje a cigaba da yin
maganin gargajiya tafiya da maganarma
Insha Allahu zai yi su tunda har kafar na
motsawa bakin ma yana motsa shi
alamun yana son ya yi magana Allah ne
bai bashi ikon yi ba.
Wannan shawara ta yi tasiri a
gurin su Alhaji Ayuba da baffaninsa na
Dukku hakan ne yasa suka gayawa Dr.
Aminullah kudirinsu da farko bai bada
goyon baya Ba amma a karshe-karshe dai
ya amince musu ya basu sallama tare da
basu sharuddan da za'a dinga bi wajen
kula da shi da bashi magungunansa akan
69
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
lokaci tare da an tabbatar ana kawo shi
(Clinic) don ganin likita.
Kafin su wuce gida Isah ne ya fara
tafiya suka hadu da Jume da mai gadi
Malam Bilya suka gyara dakinsa suka
share suka goge duk wata kura kasancewar
ba'a bude dakin shi yasa kura ta sami
muhallin zama.
Goggo ce ta ba Isah umurnin yin
hakan tunda nan dakin nasa za'a kai shi
Isah ya yi tsaye a dakin baccin Mujeeb din
a gaban durowar gefen gadonsa yana cike
da ta'ajibin rashin ganin makudan kudin
daya adana wa Mujeebun tun ranar da
ciwo ya sameshi Goggo tace ya rufe dakin
ya aje makullin a hannunsa to shine daya
shiga dakin don ya fidda abubuwan cikin
Firij din Mujeebun ya ga kudaďen a jakar
Ofis dinsa shine ya kwashesu ya zuba a
durowar ya rufe ya cire makullin sai gashi
yanzu yaga babu makullin a jikin durowar
yana dubawa ya ganta a bude babu kudin
babu dalilinsu.
70
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Tabbas ko kaffara ba zai yi ba
Suwaiba ce ta bincika ta kwashe kudin
nan in banda shi babu wanda ke shiga
dakin, shi kadai ke da makullin dakin
kila itama tana da safaya ne bai sani ba.
Haka ya koma asibitin cikin
al'ajabi wannan al'amari ko Goggo bai
gayawa ba don ya san tun a asibitin za ta
iya fasa maganar dama tun a ranar ya
gayawa Goggo maganar kudin sai ta ce
ya aje su kawai kada ayi amfani da su
tunda ba'a sani nashi ne ko ba nashi
bane.
Amma fa Isah ya sha alwashin zai
binciki Suwaiban in har ya tabbatar ita ta
dauka to dolenta ta dawo da su don ba
hakkinta bane, in ma banda rashin
tausayi mutum na kwance cikin halin
haula'i sai ki bi dukiyarsa ki dauke babu
ko tausayi.
Sun baro asibiti sun dawo gida a
nan falonsa aka saka masa madaidaiciyar
71
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
katifa a nan ne zai zamo gurin jinyarsa,
saboda jama'a masu zuwa gaishe shi.
A ranar Muneeba yini ta yi
hidinmarsa har bayan Magriba sannan ta yi
sallama da su ta tafi tana lura da Majeebun
na tsiyayyar hawaye tun da ya ji za ta tafi
gida.
******* ******* ********
Tun ranar da aka salami Mujeeb daga
asibiti Muneeba ba ta sake zuwa gidan ba
har kwana biyu. Tana kiran Isah a waya ta
tambayeshi mai jiki ya yi mata korafi
rashin zuwan nata amma sai tana kawo
masa uzurori wadanda zuciyarsa taki
amanna da su su dai kawai ya kyaleta.
Wannan rashin zuwa na Muneeba ya
kawo cikas da koma baya ga lafiyar
Mujeeb da ake ganin an samu, tunda har ya
72
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
haifar masa da kin karban abinci idan
aka bashi nan da nan sai jikin na sa ya
rikice, zazzabi mai zafin gaske ya rufe
shi har yana wata irin jijjiga.
Kowa fa ya rude hankula suka
tashi Isah ya dubi Mustafa da ya zo a
ranar ya ce "Yaya Mustafa ko zamu kira
wayar Dr. Aminullah ne tunda ya bani
wayarsa yace in da wata matsala in kira
shi in gaya masa?
Ya ce "Eh mana yi maza ka kira
shi muna murna sauki yazo sai kuma
wata sabuwa ta bullo.
Bugu daya biyu Doktan ya dauka
suka gaisa da Isah tare da tambayar ya
jikin Mujeeb din ya ce, Wallahi Dakta
jikin nasa nema ya tashi shine nace bari
in kira ka ko da wai taimakon da za ka yi
mana in babu matsala.
"No babu wata matsala ai na ce
idan da matsala ka kirani. Ku saurareni
gani nan zuwa yanzu don yau ina Up ne
bana asibiti mintuna kalilan suka sa da
73
2
a
a
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Dr. Aminuklah da gidan Mujecb
kasancewar Anguwanni su na makwaftaka
da juna ya yi masa aunc-aune ya dan
dudduba shi sannan ya dubi Isah, "Me
kuka yi masa har ya shiga damuwa haka?"
Isah ya ce "Mu kam Dakta me za mu yi
masa? Ai mu duk wani abu da zai dorar da
lafiyarsa shi muke so kuma shi za mu yi
masa ka ganshi nan ya ki cin abinci tun
jiya sai dai zubda hawaye mun rasa gane
kansa".
Dakta ya dan yi shiru cikin nazari
sannan ya yi tambayi Isah "A tunanin me
kuke ganin ya dami zuciyarsa a yanzu,
don ya zama dole mu san ko mene ne don
mu magance shi ko mu hana faruwarsa
gareshi.
Mustafa ya yi karaf ya amshe Dakta
gaskiya matarsa ce da ke jinyarsa bai gani
ba kwana biyu tun ranar da aka dawo da
shi daga asibiti mu a zaton mu rashin
zuwanta gareshi shine musabbabin tashin
ciwon nasa har ya kauracewa cin abinci.
74
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Likita ya сe "A'a to ita meye
dalilinta na tsallake zuwa unguwar
kwana alhalin ta san tana da mara lafiya
wannan ai bai dace ba gashi ta jefa mijinta cikin cikin wani hali gaskiya ku
gaggauta kiranta a waya tayi maza-maza
ta dawo yau don kula da lafiyar mijinta lafiyarsa ai tafi mata komai.
Suka dan yi jim sannan Isah yace
"Eh to gaskiya Likita sun dan sami
matsala ne tun kafin ya fara ciwo shi da
kansa yace ta zauna a acan gaban
iyayenmu sai ya nemeta to tana can dine
ciwo ya same shi bata ji haushin komai
ba ta zo ta yi ta jinyarsa shine yanzu da
aka dawo da shi gida ita ma ta koma can
gida inda take.
Dakta ya dafe kai yana kakabin
wannan al'amari 'yanzu babu yanda za'a
aje aba iyayenta hakuri su taimaka ta
dawo ta zauna dashi saboda dorewar
lafiyarsa? Kun dai ga yadda jikin nasa ya
koma. A gaskiya idan abin ya cigaba to
75
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
za'a koma yar gidan jiya gara tun abu baiyi
nisa ba asan abinyi in ta kama aje dani can
durin iyayenta nata ne sai mu je don in yi
musu bayani amma ai dole mai irin
wannan ciwon ya kasance da matarsa
kusa da shi, saboda wata kulawar da
lallashi sai ita.
a
Isa ya ce "Yana da wata matar gata
can a dakinta, amma bata da wani amfani
tunda ba za ta iya zama ta kula da shi ba,
Muneebar ce kadai dama me dawainiya da
shi kamansa ita ce tunda ita 'yar uwarsa ce
shi yasa tafi jin ciwon nasa a zuciyarta.
"Haba ba mamaki ai alaka jinni
daban take balle kuma an hada da
auratayya matarsa ashe su biyu ne to
gaskiya kam ku san yadda za'a yi ta dawo
gare shi don yana cikin hadari".
Mustafa ne ya hau motarsa ya nufi
gida Inna Amina wurin Muneeba. Dukansu
a falon gidan ya iske su har Muneeban aka
gaggaisa sannan ya kebe da Muneeban a
dakinta ya shaida mata halin da ake ciki da
76
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
S
bayanan da likita yayi musu da irin
gudunmuwar da ake son taje taba mijinta
tunda ya fi kusanci da ita fiye da kowa.
Halin da aka gaya mata ya shiga ya
soki Zuciyarta sai dai tana ganin ba zai
zamo dole ace sai ita zata je ta zauna da
shi ba alhali yana da wata matar, matar
da mahafiyarsa ga kaninsa aiko su sun isa
jinyarsa. Ita kam a wani matsayi za ta je
ta zauna a gidansa tunda bai ce ta dawo
gidansa ba duk da ba sakin ya yi ba.
Ta dubi Mustapha ta dan kauda
kanta gefe tace, Yaya Mustafa kayi
hakuri gaskiya ba zan iya komawa gidan
nan ba in zauna ba tunda bashi yanemi in
koma ma, ka da ya warke ya sake kora ta
gara dai in zauna gaban iyayena kamar
yadda ya bukata zaman da nayi dashi ma
a asiiti ai na yi kokari ida ka yi la'akari
da yadda ya wofintar da aurensa ya share
ni a babin rayuwarsa, ni din har ciwo na
kwanta na yi kuma an kirashi a waya an
gaya masa, ko sannu a waya baice mini
77
WATA KUSAN 3
Rahmatu Hassan Zaria
ba balle ya tako ya zo ya gaishe ni balle in
sa ran zai saya min magunguna, Su Mama
Amina ne ke ta dawaniya da ni har na
warke haba Yaya Mustafa in maye ya
manta ai uwar da ba zai yiwu ta manta ba.
Mustafa ya sauke numfashi "Mun
san haka Muneeba, amma kiyi hakuri ki
bar wani tone-tone idan ana sallah ai ba'a
magana, ki bar tuno abin daya faru a baya
ya wuce mu fuskanci abin da ke gabanmu
yanzu kowa ya san abinda kika yi kin yi ne
domin Allah kuma domin zumunci sannan
har yanzun a matsayin matarsa kike tunda
ba sakinki yayi ba babu wanda zai ce don
me kika koma dakinki ki yi hakuri ki
tausayawa dan uwanki wallahi likita yace
komai zai iya faruwa ga rayuwarsa a halin
da yakė ciki.
Kwalla ce ta cika idanun Muneeba
ana tausayin mijinta, itama tana tausayin
kanta to amma dole ne ta dan dinga ja baya
tun kafin Goggo ko Suwaiba wani cikinsu
78
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
bayanan da likita yayi musu da irin gudunmuwar da ake son taje taba mijinta
tunda ya fi kusanci da ita fiye da kowa.
Halin da aka gaya mata ya shiga ya soki Zuciyarta sai dai tana ganin ba zai
zamo dole ace sai ita zata je ta zauna da shi ba alhali yana da wata matar, matar
da mahafiyarsa ga kaninsa aiko su sun isa jinyarsa. Ita kam a wani matsayi za ta je
ta zauna a gidansa tunda bai ce ta dawo gidansa ba duk da ba sakin ya yi ba.
Ta dubi Mustapha ta dan kauda
kanta gefe tace, Yaya Mustafa kayi
hakuri gaskiya ba zan iya komawa gidan
nan ba in zauna ba tunda bashi yanemi in
koma ma, ka da ya warke ya sake kora ta
gara dai in zauna gaban iyayena kamar yadda ya bukata zaman da nayi dashi ma
a asiiti ai na yi kokari ida ka yi la'akari
da yadda ya wofintar da aurensa ya share
ni a babin rayuwarsa, ni din har ciwo na kwanta na yi kuma an kirashi a waya an
gaya masa, ko sannu a waya baice mini
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
ba balle ya tako ya zo ya gaishe ni balle in
sa ran zai saya min magunguna, Su Mama
Amina ne ke ta dawaniya da ni har na
warke haba Yaya Mustafa in maye ya
manta ai uwar da ba zai yiwu ta manta ba.
Mustafa ya sauke numfashi "Mun
san haka Muneeba, amma kiyi hakuri ki
bar wani tone-tone idan ana sallah ai ba'a
magana, ki bar tuno abin daya faru a baya
ya wuce mu fuskanci abin da ke gabanmu
yanzu kowa ya san abinda kika yi kin yi ne
domin Allah kuma domin zumunci sannan
har yanzun a matsayin matarsa kike tunda
ba sakinki yayi ba babu wanda zai ce don
me kika koma dakinki ki yi hakuri ki
tausayawa dan uwanki wallahi likita yace
komai zai iya faruwa ga rayuwarsa a halin
da yake ciki.
Kwalla ce ta cika idanun Muneeba
tana tausayin mijinta, itama tana tausayin
kanta to amma dole ne ta dan dinga ja baya
tun kafin Goggo ko Suwaiba wani cikinsu
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
ba tun da ba ni ke da iko da ita ba masu
iko da itane suka bani amanar ta zauna a
hannuna sune iyayenku idan suka yauyauta koma wallahi ina murna da hakan
ai munfi kowa son ta koma dakin mijinta
ta zauna to amma dole a nuna musu
Muneeba ma ‘ya ce ba baiwa ba, muna
sonta tamkar yadda Goggon ke jin tana
son Suwaiba, ai tana gidan ake ta
wulakanta Muneeban bata tsawata ba
shine sai yanzu za'a ce ta dawo saboda
zata taimaki danta ai dama ko kare yana
da ranarsa balle dan Adam mai daraja.
Ka kyale Goggo taje ta samu 'yan
uwanta babu ruwanka". Mustafa yace ni
dama ba zuwa zanyi ba, ai ban isa in
tunkari su Baffa da wannan maganar
yadda suke cike da Goggon ko nan da
nazo bata san nazo bani ne dai da likita
muka ga dacewar ta zauna kusa dashi.
Inna Amina ta lallashi Muneeba
suka tafi tare da Mustafa sallamar kadai
Mujeeb ya ji ya wani saki ajiyar zuciya a
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
lokacin Suwaiba