da Goggo ne ke gabansa
suna kokarin ya ci abinci amma fafur yaki
karba suka shiga falon ita da Mustafa suka
gaisa da Goggo, Suwaiba bata amsa
gaisuwar ba sai wani cin magani ta ke yi
har sai da Muneeba tayi mata tata
gaisuwar ta daban sannan ta amsa da kyar.
Shi kam Mujeeb bin Muneeba yake
yi da kallo tamkar ranar ya soma ganinta
hakan ya kular da zuciyar Suwaiba ta
tsuguna gaban katifar da yake zaune an
jingina shi da bango itama idanu ta kura
masa tamkar yadda yayi mata kuri da nasa
idanun tayi magana, "Ya jikin naka? Duk
da ta san ko an gaishe shi ba iya amsa ya
ke yi ba amma ya san yana jinta kuma
akwai alamun amsawar da yake yi mata
idan ta gaishe shi lumshe mata idanunsa
yayi sannan ya sake budesu a fuskarta tare
da bayyanuwar wani kallo na soyayya
wanda ita kadai tasan sirrin kan dake cikin
kallon a duk lokacin da yayi mata.
L
82
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Ta sake tambayarsa "An ce min
kwana biyu kaki cin abinci me yasa? Ka
yi hakuri ka dinga cin abinci saboda shi
abinci yana karawa mara lafiya kuzari
tare da sake gina masa garkuwar jikinsa
da ta soma rugujewa a yayin da yake
cikin halin rashin lafiya uwa uba ma ita.
kanta lafiyar da ake nema ta samu ga
mara lafiya tana samuwa ne idan mara
lafiya na cin abinci kaji ko abokin. ???
Bata iya karasa sunan da take kiransa dashi ba, kasancewar Goggo na
gurin kuma dama daga ita sai shi takeе
kiransa da abokin rayuwa yanzu ma da
ace tayi subul da bakan fadan sunan to la
shakka wani shahararren gori Suwaiba
zata yi mata, gara da Allah ya taimaketa
bata gama ambatar sunan ba tayi birki.
Abincin dayaki ci ta dauko ta debo
cokali daya na shinkafa da miya ta kai
bakinsa sai ta ga ya girgiza kai alamun ba zai ciba tace "Ba zaka ci ba to me kake
83
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
so? Ya sake lumshe idanunsa take ta gano
manufarsa ta mike ta isa inda kayan Ti
suke ta debi garin Kostad na gwangwani ta
je kicin din ta ta dama masa tazo tasa
Madara da suga kadan sannan ta soma
bashi sai gashi ya saki ciki yana shan
Kostad din nan har sai da ya kusa shanye
kofi daya.
Suwaiba dake zaune nan da nan ta
kullu ta kai iya wuya da ganin wannan
abin al'ajabi abinka ga mara hakuri sai da
ta bara ta hau sababi 'Kwarai lallai kam na
dage na yi maka abinci na musamman
harda hadin Salad a ciki amma kaki ci sai
na wadda ba'a gidanka take ba tana yi
maka harka shanye to wallahi da sake ba
zai yiwu ba kina dai gani da idonki Goggo
sannan idan naki zama kusa da shi ayi ta
min surutu ni dama ai irin wannan
kisisinar nake gudu".
Muneeba itama bata kyaleta ba ta
bata amsa cikin lumana ba hayaniya irin
nata "Ayya kiyi hakuri kinsan mara lafiya
84
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
baya son abu mai karfi shi yasa da naga
ya nuna baya son shimkafar na dama
masa kuma ko bana gidansa ai hakki
nane in kula da lafiyar tunda har yanzu
miji na ne idan kinyi hakuri ma ni ba
zama na zo yi ba anjima zan tafi in barki
da shi kiyi hakuri ni tamkar bakuwace a
gidan nan.
Tsaki Suwaiban ta ja ta na
kunkuni ni ina ruwana inma zama kika
zo yi tunda dama can ba ni na kore ki ba,
wannan kuma tsakaninki da mijin ne shi
ya san me kika kunsa masa ya kore ki.
Murmushi kawai Muneeba tayi
bata sake kula Suwaiba ba don ta san
idan taci gaba da kula ta to`za su yi tanki
in tanka ne hakan kuma bai dace ba.
Ta gogge masa bakinsa da (Tissue)
ta dauki mafici ta shiga yi masa fifita duk
da ga fanka na kadawa. Hakan da
Muneeba ta yi ya sake tinjirar da zuciyar
Suwaiba a ganinta Muneeba na nuna
mata ta fita iya kula da miji kenan ta kale
85
1
a
a
a
a
n
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
su ta watsar sannan ta tashi ta buga uban
tsaki ta juya zata fita Goggo tace "Wai
Suwaiba me ke damunki ne yanzu mijin
naki kike yi wa tsaki don rashin sanin
darajarsa lallai kin kyauta.
"In ma shi na yi wa tsaki Goggo ai
na yi daidai tunda a gabanki ya nuna ni
bani da muhimmanci a gare baki tayani
nuna masa yayi daidai ba basai nice yanzu
zakuce nayi masa ba daidai ba tunda shi
naki ne ni kuma ba taki ba ce ai wallahi
zanga yadda za a yi tusa ta hura wuta.
Ta juya Fuuw! Ta fice har tana
gwabje Mustafa da suka shigo tare da Isah.
Isan ya ja tsaki ya ce Lafiyarki Malama kin
bangaje mutum ba ko sannu kin wuce? Tа
kalleshi shekeke tace "Tunda ba kai na
gwabza ba sai ka kama bakinka ka barshi
yayi magana".
Ai wallahi ke ma kinsan dani kika
gwabza haka da kinga Karyar wulakancin
ki na gidan nan". Shi dai Mustafa ko ta
kansu bai bi ba ya shige dakin dama tun
86
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaría
zuwahsu da Muneeba suka fita da Isah
shi yasa ma badakalar da akayi tsakanin
Muneeba da Suwaiba basa nan.
Yana shigowa Goggo ke
tambayarsa kai da waye kake hayaniya?
Yayi kwafa yace "Ni da yarki ne mara
mutunci da bata san darajar na gaba da
ita ba, yaya Mustafa fa ta gwabje inace
wan mijinta-ne amma ta yi wucewarta ko
ta kalleshi balle ta yi masa sannu ita ga
wulakantatta don takamarta ta sami
daurin gindi" ya sake yin kwafa ya ja
uban tsaki.
Goggo ta numfasa ka kyaleta nima
din ai bata raga min ba balle wani tunda
rashin arziki ta zaba sai mu zuba mata
idanu kada ka dinga biye mata kuna
sa'insa ka kyaleta ka fuskanci kuła da
lafiyar dan uwanka shine a gabanka..
Har aka yi kiram Sallar Magriba
Muneeba na gurin minjinta don sai da ta
tabbatar ya ci abinci da ta yi masa da
kanta faten dankali wanda ya ji hanta
87
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zarja
sosai shi ta yi masa ya ci ya koshi sannan
hankalinta ya kwanta.
Ana kuwa kiran Magriba ta mike
tana duban Mustafa tace "Yaya Mustafa ka
tashi mu wuce kai da za ka wuce Dukku ga
shi har dare ya yi maka mu je ka aje ni sai
ka wuce tunda ban fito da mota ba.
Ganin duk sun mike har Muneeba ta
saka Hijabi ta rataya 'yar Jakarta sai gani
su ka yi hawaye ya tsinkewa Mujeeb
dukansu sun san dalilin Muneeba za ta tafi
ta barshi ne yake hawaye.
Tana ganin haka sai ta yi saurin
barin gurin ta nufi kofa za ta fita muryar
Mustafa ce ta tsayar da ita "Muneeba kada
ki fita dawo ki gani ta juya tana duban
Mustafa ya yi mata nuni da Mujeeb ta
dube shi ta ce "Na ganshi Yaya Mustafa
amma ka san dole in tafi gida tunda dare
ya yi sannan ni ba anan zan kwana ba,
hakuri zai yi gobe zan dawo”.
Ta dawo ta gurfana gaban Mujecь
din ta soma lallashinsa "Kayi hakuri Yaya
88
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Ya ce "Dole ke zan fara tambaya
tunda ke ce a gidan ita ba zuwa take ba
iyakacinta asibiti har sai da aka kawo shi
gida sannan ta zo gidan nan kinga kuwa
bani da Hujjan tambayarta saboda haka
idan kin san kudin nan na gurinki ki bada
don shima kudin ba nashi bane kudi na
Ofis dinsu ne a ranar ya shigo da su a
Jaka a ranar ciwo ya same shi shi ya sa
ma daga Ofis suka nemi bayanin kudin
tunda sun tabbatar gida yazo da kudin.
In kuma kina ganin su zo su yi
bincike da kansu to zan basu izini tunda
ni kam na san basa gurina ko sun yi
bincike ba za su kama ni da laifin taba
musu dukiya ba.
Za su gwada yatsu ne a durowar da
aka dauki kudin kuma dole su gano
yatsun wanda ya bude durowar indai
yana gidan saboda haka tun kafin su
tozarta ki a idon duniya gara ki dauko
kayansu ki basu.
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Abinka ga dakikiya ai nan da nan ta
tsorata da jin kalaman da ya shirya. Kudi
kam tabbas ita ta dauka ta kirga su Dari
biyu da hamsin ne har ta gayawa Hajiyarta
sun yanke shawarar yanda za su yi da
kudin sai gashi an yanka ta tashi balli ya
huje idan tana son tsira da mutuncinta dole
ta fito da kudin nan.
To amma abin da kunya ace yadda
suke tsama da Isah shine ya kamata DumuDumu da halin bera, dole ta yi wa abinda
tayi ma abinda tayi kwaskwarima ya zamo
ba halin bera ba.
Sai ta ce "Eh kudin kam na gansu
suna nan cikin dakin na boye su babu
abinda zanyi dasu illa idan ka hanani kudin
hidimarmu ni da waleeda in dauka in yi
tunda kudi na miji na ne, amma yanzu
kasancewar ka ce ba na shi bane zan maida
inda na dauka.
Isah ya yi murmushi ganin ta zurma
tarkon da ya dana mata ya juya ya fita a
dakin yana fita ta dauki wayarta ta kira
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Ya ce "Dole ke zan fara tambaya
tunda ke ce a gidan ita ba zuwa take ba
iyakacinta asibiti har sai da aka kawo shi
gida sannan ta zo gidan nan kinga kuwa
bani da Hujjan tambayarta saboda haka
idan kin san kudin nan na gurinki ki bada
don shima kudin ba nashi bane kudi na
Ofis dinsu ne a ranar ya shigo da su a
Jaka a ranar ciwo ya same shi shi ya sa
ma daga Ofis suka nemi bayanin kudin
tunda sun tabbatar gida yazo da kudin.
In kuma kina ganin su zo su yi bincike da kansu to zan basu izini tunda
ni kam na san basa gurina ko sun yi
bincike ba za su kama ni da laifin taba
musu dukiya ba.
Za su gwada yatsu ne a durowar da
aka dauki kudin kuma dole su gano
yatsun wanda ya bude durowar indai
yana gidan saboda haka tun kafin su
tozarta ki a idon duniya gara ki dauko
kayansu ki basu.
91
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Abinka ga dakikiya ai nan da nan ta
tsorata da jin kalaman da ya shirya. Kudi
kam tabbas ita ta dauka ta kirga su Dari
biyu da hamsin ne har ta gayawa Hajiyarta
sun yanke shawarar yanda za su yi da
kudin sai gashi an yanka ta tashi balli ya
huje idan tana son tsira da mutuncinta dole
ta fito da kudin nan.
To amma abin da kunya ace yadda
suke tsama da Isah shine ya kamata DumuDumu da halin bera, dole ta yi wa abinda
tayi ma abinda tayi kwaskwarima ya zamo
ba halin bera ba.
Sai ta ce "Eh kudin kam na gansu
suna nan cikin dakin na boye su babu
abinda zanyi dasu illa idan ka hanani kudin
hidimarmu ni da waleeda in dauka in yi
tunda kudi na miji na ne, amma yanzu
kasancewar ka ce ba na shi bane zan maida
inda na dauka.
Isah ya yi murmushi ganin ta zurma
tarkon da ya dana mata ya juya ya fita a
dakin yana fita ta dauki wayarta ta kira
92
WATA KUSAN З Rahmatu Hassan Zaria
hajiyarta ta shaida mata abin da ya faru.
Hajiyar ta hauta da sababi tana fadin
amma dai ke shashashace in banda ke
shashasha ce ya za'a yi duk tuhumar da
zai yi miki ki nuna kudin nan ke kika
dauka alhali kin riga kin san abinda za
mu yi da kudin aiki ne babba a gabanmu
tunda da kanki kike shaida min kina
ganin asirin da muka masa na kyamar
matarsa Muneeba ya sake shi.
To yanzu idan kika bada kudin
kina da wasu kudin ne koko kina da
hanyar samun wasu kudin da zamu je
gurin boka ne?.
Kinfa san aikin da za'a yi masa
yanzun sai ya fi na baya wahala tunda na
lura Tufka muke yi ana mana warwara
wannan karon so nake yi ayi mai
dungurungum ko dai ya saketa saki uku
mu yar da kwallon mangwaro mu huta da
kuda ko kuma duk idan haka ta gagare
shi mu sa yadda za mu da shi tunda dai
93
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
ko yanzu kasuwa ta tashi dan koli yaci
riba.
Suwaiba ta marairaice to yanzu
Hajiya ya kike ganin zan yi tunda har na
nuna masa kudin na nan a dakin Mujeeb
din na boye su? "Ai komawa za ki yi ki
gaya masa ke fa kin duba inda kika ajesu
baki gansu ba in ma tuhumar zai yi sai ya
tuhumi kowa dake gidan har kuwa da
uwarsa tunda ai ba ke kadai bace a gidan
ko kuwa ke kadai ke shiga dakinsa.
Inma banda ke sokuwa ce har zai zo
yayi miki burgar 'yan Ofis dinsu Mujeebu
za su zo bincike akan dubu dari biyu da
hamsin me akayi akai dubu dari biyu da
hamsin a irin kudin da Mujecbu ya tara.
Saboda haka ki natsu ki san abinda
kike yi in kuma ba haka ba wallahi ke kika
sani muddin kika kuskura kudin nan suka
subuce a hannunki don na gaji da daukar
kadarata in je saidawa don neman miki
biyan bukata alhalin ke kin kasa aje
94
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
kadarar komai tamkar ba mai kudi ki ke
aure ba.
Kina dai kallon tsinanniyar
yarinyar nan babu abin duniyar da bata
tara ba amma ke kina zaune ita ba aiki
take ba balle a ce albashi take dauka ki
tabbatar yau kin gaya masa abin dana
tsara miki gobe ina nan zuwa zan yi wa
hanci tufka kada ya kuskura ya kara
lakaba miki sata don ban haifi barauniya
ba in kuma ba haka ba to kotu ce za ta
rabani da shi tunda uwarsa na kalo ya
wulakanci iri iri amma ta kasa tsawatar
masa". Koda Suwaiba ta gayawa Isah
zancen ta duba kudin bata gansu ba
murmushi ya yi ya ce, baki gansu ba? Ai
kuwa dole ki gansu tunda ba kafa ce da
su ba balle su gudu daga inda kika aje su.
Saboda haka tun wani bai ji zancen nan
ba gara ki fito da kudin nan tunda ke da
bakinki ki ka ce kin adana su.
Inma wani ne ya zuga ki ya ce
kada ki bayar to zai kaiki ya baro ina
95
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
jiranki zuwa yamma idan na ji shiru ba
bayani zan dauki mummunan mataki
wanda ba zai yi maki kyau ba. Ya juya ya
fice a dakin ya barta duk wannan
badakalar da suke tafkawa Goggo bata
sani ba har saida Hajiya Harira ta zo.
Sanyin fuska karara Goggo ta gani a
fuskar Hajiya Harira, ko ga yanayin yadda
suka gaisa. A tunanin Goggo kila daga can
Dukku ne wani ya bato mata ranta.
Batatambayi Hajiya Harira komai ba
har sai da suka kebe a dakin Goggon
bayan sunyi Sallah suna zaune suna cin
abinci sannan ne take tambayarta "Ni Haj.
Harira na ganki ne wata iri yau halan wani
ya tabo ki ne?
Ta gyara zamanta tare da zubar da
Kashin kazar da take ci cikin wata roba
sannan tace "Ni a Dukku babu wanda ya
batamin rai anan gidan ne aka batamin rai
shine ma musababbin zuwa na don ba zan
yarda ba gara in biyo ba'asi.
96
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Goggo ta ware idanu, "Anan
gidan? Wane ne shi kuwa wannan amma
bani da masaniya ko? Ta yatsina fuska
"Ta yiwu kila kina da masaniya tunda
dan autan ki ne ya aikata abin. Ni kam na
rasa wannan irin kiyayya da Isa ke wa
Suwaiba tamkar wadda ta kashe masa
gyatuma sam ba ya kaunarta, yanzu har
ta kaima ya lakaba mata sharrin don
kiyayya.
Goggo ta dafe haba, "Isah ne da
yiwa Suwaiba Sharri ? lalli yaron nan
yana son ya zinguro sama da Kara, abin
da kuma ba zai yiwu ba kenan. Gaya
mini me Isah ya aikata?.
Hajiya Harira ta zauna ta warware
Goggo abinda ya faru ne 6acewar kudi a
dakin Mujeeb, tare da tuhumar da Isah ke
wa Suwaiba wai ita ta dauka tunda babu
wanda zai bude dakin ya shiga in ba ita
ba.
Goggo ta hangame baki cikin
kakabi da al'ajabi ta ce, "Wallahi Hajiya
97
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
bani da masaniyyar akan wannan al'amari
Isah sam bai gaya mini ba sannan ita ma
Suwaiban ai bata gaya mini ba, in da ta
gaya mini da tun kafin ma ta gaya maki
zan yi wa tufkar hanci.
In banda. Isah shashasha ne yaushe
ne zaka yiwa matar dan uwanka kuma
uwar 'ya'yansa irin wannan sharrin zai
kuwa ci kaniyarsa yau a gidan nan".
Suwaiba da ke gefe ce tayi tsulum ta
ce "Yaushe ne zan gaya miki tunda yanzu
ba kya ganin laifin 'ya'yanki jiyan nan a
gabanki nayi abinci har dake muka yi ta
lallashin Mujeeb ya ki cin abincin, alhalin
rabon sa da cin abinci tunda aka sallameshi
daga asibiti. Kiri da muzu ya ki ci amma
wannan kinibabbar (Muneeba take nufi) na
zuwa ta dama masa Kostad tsaf ya shanye
har girki tayi masa ya ci amma ni yaki cin
nawa wai dama saboda bata zo ba ne
kwana biyu yaki cin abinci har sai da ta zo
Goggo duk tana kallo bata tsawatar masa
98
WATA KUSAN 3
Rahmatu Hassan Zaria
ta nuna masa yayi ba daidai ba tunda ai
yana jin duk abinda ake cewa.
Ni yanzu a gidanan ai na shiga uku
bayan sharri ma wata ran Isah duka na
zai yi ana kallo ba za'a hana shi ba tunda
ya tsane ni Hajiya Harira ta hau girgiza
kai "Ai kuwa da yaga danyen aiki
muddin ya ware hannu ya buge ki zan
nuna masa ke 'yar gata ce "Tab dijam!
Dama haka ce ke faruwa a gidan kika
kame baki kika yi gum baki gaya mini ba
har sai yaron nan ya yayi maki lahani.
Goggo ta luguiguita murya ta shiga
ba aminiyar ta hakuri Haba Hajiya Harira
ke ma kin san idan ina nan da raina haka
ba zata taba faruwa ba kiyi hakuri bari in
kira Isan.
Ta mike ta leka waje ta kwalawa
Isah Kira, ya fito daga dakin Mujeeb ya
zo gurin kiran da goggon ke masa yana
ganin yanayin fuskokinsu Hajiya Harira
da 'yarta yayi saurin gano makasudin
wannan gangami.
99
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Goggo ta dubeshi ta ce, Isah 'Meke
faruwa ne a gidan nan tsakaninka da
Suwaiba har ban sani ba"?.
Ya ce "Abin da ya faru naga tsakani
na da ita shi yasa ban gaya miki ba, kuma
da ta dawo da kudin kamar yadda ta ce ita
ta adana babu wanda zai ji, tunda ko yanzu
ma ai bani na fasa maganar ba. Kudi kam
dole ta maidosu tunda ta ce ita ta dauka ta
adana ni sam ba zan yarda wai ta je dauko
su a inda ta aje bata gansu ba wannan
tatsuniya ce".
Goggo ta harzuka ta nuna Isah da
yatsa ta ce "Kul! Ka kiyayeni ni Isah
wannan wace irin magana ce za ka yi wa
yarinya sharri bata ji bata gani ba wai ma
wadanne kudi ne kake magana a kansu"
Tiryan - Tiryan ya zayyanewa
Goggo yadda ya ga kudin da inda ya adana
su har yazo bai gansu ba da tuhumar da
yayi mata da yadda ta amsa cewa eh ta
gansu amma ta sake musu ma'adani a
100
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
5
dakin Mujeeb amma daga baya take gaya
masa bata gansu ba.
Goggo, "Ni yanzu abin da nake so
da kai tunda har ta duba bata gansu ba to
abar maganar in dai har na isa da kai,
kada in sake jin tashin maganar nan".
"Yanzu Goggo shike nan ta ci
bulus? Wannan ai an daure mata gindin
gobe ta yi fiye da haka kenan.
Babu ruwanka in ma ta ci kudin ai
na mijinta ne, tana da hakki akan
dukiyarsa babu ruwanka, wuce ka bani
guri saura kuma inji maganar nan a wani
guri" ya wuce yana yan surutai na
takaicin wannan abu"Shikenan na
kyaleta garin banza ai a farau farau din
banza yake karewa.
Hajiya Harira ta kanne wa yarta
idanu suka dan yi murmushin cin nasara
magana ta mutu, an kashe wannan Bos
din. amma a zahiri sai ta ci gaba da
sababi, "Haba wannan zance ai ya
fusatani ya ban takaici kazafin sata! In
101
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
ma banda yaron nan ya mu Suwaiba aiba
ita kadai ba ce macen aure a gidan nan da
zai ce ita ta dauki kudin mijuinta 'yar
uwarshi ba gata nan me yasa ita bai
tuhumeta ba sai Suwaiba don ita ce
marainiya wayonsa.
Ke ma Hajiya Rahin na ga beken ki
da har za ki yi sake kina kallo Isah na ma
Suwaiba cin kashin mahaukaciya da bakya
masa birki matar fa yayansa ne duk da
yake ganin ya girmeta, saboda haka, ke da
kanki za ki ganar da shi kurensa kuma ya
san cewa tana da babban matsayi a gidan
nan inma ya manta ne".
Goggo dai sai ban hakuri take ta yi
wa aminiyarta har sai da ta sauko suka hau
hirar duniya cikin raha sannan hankalin ya
kwanta Suwaiba sun sami kaďaicewa ita da
mahafiyarta a can kuryar dakinta Suwaiba
ta dubi Hajiyarta ta сe "Kai amma fa
hikimarki ta manya ta yi amfani Hajiya,
cikin dan kankanin lokaci harshenki ya yi
kokarin kwato mana yancin mallakar dubu
102
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
S
dari biyu ni kam har na soma jimamin
yadda zan mayar masa da kudin ta leko
ta koma ashe ba za ta koma ba.
ta ja tsaki “An gaya miki ni Hajiya
ta wasa ce wai gwari ta bada magani an
sha an mutu ai ni nan da kika ganni kura
ce mai tsohon laifi na bara bai wuce ba
ga na bana ya zo, Rahin ta sanni sarai
bana shayin koma don zan iya fitowa
ince kin dauka din kuma ba za ki bayar
ba in sun isa kotu ta amsar musu, ita ai ta
san da kunya ma ace wannan maganar ta
fito yanzu abin da za'a yi tashi maza ki
dauko min kudin nan tunda kura ta lafa
babu sauran tashin tashina don na lura ke
sokuwa ce yaron nan zai iya zuwa ya
sake tsorata ki har ki fito da kudin nan ki
bashi alhalin kinsan aiki ne Jawur a
gabanmu dole ne mu sake sabon shiri
akan wannan gawa taki rami, ni da zai
mutu ma kowa ya huta don na san idan
ya warke to watan jin kunyarmu ya tsaya
kenan tunda ya riga ya ji hirar da kika
103
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
saki baki kina yi da kawarki alhalin kina
sane boka ya gargadeki.
Yanzu fa tunda ya ji aikin da aka yi
masa ya karye sai dai a sake sabo, kuma
sabon dole zai ja kudi za'a rufe bakinsa ne
ya kasa fadin abinda ya ji ko a mantar da
shi gabadaya sannan dole ki sake
mallakarshi, in yiwu mallakar ma ta fi ta
da kuma asa ya yi wa kaskar matarsa din
nan saki uku don kada mu barta ma
tsautsayi ya sa ta haihu a gidan nan ni ba
yanzu ma buri na ya yi ya warke in ganki
da wani cikin gara ko zai mutu ya zamana
kin sake haifo wani da namijin wannan
shine babban burina" uded
Suwaiba ta mike tana bincike cikin
durowar kayanta tana cewa "Aini Hajiya
ban taba ganin mara zuciya irin matar nan
ba miji ya wulakantata dake a gidan ku hảr
mutane na miki daukar bazawara wadda
aurenta ya mutu amma don rashin zuciya
sai ki zo ki tare a gindinsa wai da sunan
jinya, yanzu fa idan ya warke sai ta koma
104
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
こ
gida simi-simi ba ko kunya tunda ba shi
ya ce ta dawo ba".
Ba dole ta koma ba, aini na fi son
ma ayi mai gaba daya ne haihuwa da
'ya'yan hanji yayi waje rod da ita ta bar
miki gidanki daga ke sai 'ya'yanki itama
tsohuwar nan dole ki tubure masa ya
maidata Dukku don ba dole bane
zamanta tare da daku tana muku ido don
na lura yanzun ta soma canza halayya"
Suwaiba ta dauko kudin daga cikin
tsummokaran da ta yi boyon a cikinsu ta
mikawa Hajiyarta tana amsa ko duba su
bata yi ba ta danna su cikin Jakarta da
tazo da ita tana cewa "Ai kin gani abu
yayi kyau sai kiyi kokari cikin satin nan
ko karyar zuwa asibiti kiyi ki zo mu je
mu ga boka, ayi mana aiki cikin gaggawa
tun kåfin bakinsa ya bude ya tona maki
asiri mu sa a daure bakin nasa ko a dasa
masa mantuwar abin da ya faru a zuciyar
in kuwa ba haka ba muddin ya fallasa
aika-aikar da kika yi uwarsa ma kadai ba
105
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
zata lamunta ba duk da cewa tare muke
fadi tashi da ita amma ai bata san an aikata
wannan danyen aikin ba, nima din da
muka je tare daga baya kika gaya min duk
da dai kona sani ba zan hana ki ba, in ana
neman mafita koma ma yi ake in yaso ayi
istigfari daga baya tunda Allah da kansa ya
ce shi mai jin tuban bayinsa ne
(Wa'iyazubīllah kunji fa jama'a Allah ka
shirye mu baki daya Ameen)
Nima fa na taba haduwa da irin
wannan tsinannan bokan shege gasu basu
da tausayi idan mutum ya je hannunsu sai
sun galabaitar da kuzarinsa ke lokacin da
cikin Waleeda shi yasa kika fito bukkar
nan wujiga wujiga ni dama sai da zuciyata
ta gaya min kila fa bokan nan ya gwada
miki halin su na 'yan akuya don wallahi
bokayen nan duk haka suke da su da
Malaman Zaure masu tsubbu basu da aiki
sai turmushe matan mutane wai in dai kana
son biyan bukata cikin gaggawa to suma
dole ka biya musu bukatarsu.
106
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Tsinannu a haka suke kwasar
ciwon alakakai su likawa mutum bai sani
ba, saboda haka ki kiyaye duk inda za mu
je duk rintsi kada kazamin banza ya sake
yaudararki yana shanye romon jikinki
gara komai yawan kudi mu basu tunda
akwai su".
Suwaiba na jin hudubobin
mahaifiyarta kuma ta yi amanna da su
don ita kam yadda take ji ma a zuciyarta
in akwai abinda yafi wanda ta aikata a
baya ko shakka babu za ta yi in zata sake
mallakar zuciyar Mujeeb a tafin
hannunta.
Kai ita fa so take yi mulkin
mulaka'u a gidan mijinta fiyema da
wanda ake yamadidin Hajiyarta ta yi, in
son samunta ne ta raba Mujeeb da kowa
har mahaifiyarsa don a yadda take jin
tsananin sonsa a zuciyarta bata son ya
hada sonta da na kowa a fadin duniyar
nan bata son ya samma kowa in ba
'ya'yan da ta Haifa masa ba, shi yasa duk
107
i
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
rintsi duk wuya zata san hanyar da zata bi
ta raba shi da kowa koda zata rasa komai
nata ne mutum na farko da take kishi ta
tsana a duniya ita ce Muneeba Saboda a
zahirance ta san Mujeeb ya fi son muneeba
da ita shi ya sa ta tsaneta tsana