mai tsanani
saukin abin ma bata haihu ba don da ta
haihu son da zai yi mata sai ya fi haka.
Ita kuma Muneeban ga ladabin tsiya
da iya kanainaye miji da soyayya ji take
tamkar ta hadiye shi saboda so sai kace ita
kadai aka halittowa shi shi ya sa za ta iya
yin ko wani irin abu ne komai muninsa
don ta farraka wannan soyayyar.
Mutum na biyu da za ta bada
sunansa wa boka shine Isah kai wannan
yaro yana shiga mata hanci a kudundune
ya tsaneta itama ta tsane shi, abu daya ke
sa tana raga masa don yana son Waleeda
amma in bayan wannan wallahi za ta iya
sawa ayi masa danyar aika-aika amma duk
da haka zata sa boka ta saita mata shi kota
sa kiyayyarsa a zuciyar yayan nasa ta
108
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
yadda ma zai koreshi a gidan sai taga ta
karyar zumunci tunda abin na takamar
'yan uwantaka ake nuna mata.
Ita kam Goggo ko da baki za su
gama da ita to amma itama dole akwai
Iblis (Boka) sunanta duk da irin
muhimmiyar rawa da ta taka har ta
tabbatar Mujeeb ya aureta sam bata son
irin ladabin da yake wa Goggon ko da
yake abin ya ragu sosai ta dalilin wani
aiki da ta sa aka yi mata. Har ta raka Hajiyarta ta tafi ta dawo daki tana ci gaba
da sake-sake.
109
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
****** ****** *******.
T
Ranar wata Asabar da hantsi misalin
goma na safiya Dr. Aminullah ya zo duba
jikin Mujeeb jiki kam yanzu
Alhamdulillah sai godiyar Allah don har
yana iya mota hannuwan sa da kafafunsa a
dalilin tsayuwa da muneeba ta yi wajen
shafa masa man zaitun mai addu'o'i a ciki
kuma tana bashi yana sha gashi ma har ya
fara magana kadan-kadan. Muneeba kaďai
ya iske zaune a gefen da Mujeeb ke
kwance tana aikin mutstsika masa man
zaitun din a kafafunsa da jikinsa.
Bayan ya yi sallama ya shigo suka
gaisa da Muneeba ya cigaba da yaba mata
akan wannan irin kokari da take yi
"Wallahi kina burgeni abisa irin wannan
jajircewa da kika yi akan kula da jinyar
mijinki in dai Aljanna ake nema a dugadugan miji to muna miki kyakkyawan zato
kin sameta kin gama saboda Kalmar farko
da mijinki ya fara magana da ita a bakinsa
110
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
da ya fara magana ita ce sanya miki
albarka gaskiya kinyi babbar nasara a
rayuwarki ina fatan zaki dore akan
aikinki na alheri.
Mujeeb sai murmushi ya ke yi ya ji
ana yabon Muneeba, ita ma murmushin
take yi tare da amsa addu'ar da aka yi
mata da Ameen Ameen Dakta kaima
Allah ya baka ladan wannan dawainiya
da ka yi da shi Allah kada ya
gajishsheka".
Ya fiddo abin awonsa ya auna
lafiyar Mujeeb din yanayin jininsa da
dumin jikinsa ya tabbatar komai nasa
normal yake sannan ya dubi Muneeba ya
ce "Ina Isah yake" Та сеe, "yana
makaranta suna da Tes ne amma zuwa
azahar zai dawo".
Ok dama keken zama nazo da ita
zamu fara saka shi a ciki ana yawo dashi
a falo zuwa harabar gidan, nan bana son
yana yawan kwanciyar nan ina son a
dinga fita da shi yana shan rana kafin ta
111
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
yi zafi don tana da muhimmanci ga
lafiyarsa.
Muneeba ta fadada fara'arta 'Sannu
da kokari likita mun gode Allah ya saka da
alkhairi wannan dawainiya ta yi yawa
wallahi Allah ya bar zumunci'.
Da kansa ya fita ya dauko keken a
bayan motarsa ya dawo ya iske Muneeba
har ta kira Goggo dama tana bayi ne itama
Goggon godiya da shi albarka ta dinga yi
masa ya dauko Mujeeb cak daga kwance
ya saka shi a keken sannan ya soma tura
shi yana zagaye falon da shi da yake falon
babba ne sosai.
Mujeeb sai murmushi yake yi yana
ta motsi da bakinsa alamun yana magana.
Muneeba ta matsa ta kara kunnenta a
bakinsa ta ji yana cewa "Nagode Dakta na
gode na gode kalman da yayi ta
maimaitawa kenan.
Muneeba ta gayawa Dakta abin da
ya ke ta fadi Dakta yayi murmushi yana
dubansa ya ce, babu komai yadda nake
112
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
tausaya maka wannan matsalar data
sameka wallahi zan iya yin komai don
ganin lafiyarka ta dawo kamar da ka
dawo cikakken mutum kamar kowa".
Tun daga wannan rana sai ya
kasance Muneeba da wuri take zuwa don
ta fito dashi harabar gidan ya sha hantsi
nan zasu zauna suyi ta hirarsu duk da
maganar tasa bata fitowa bata fitowa
sosai kuma a sarke take ba kowa ke iya
ganewa ba yawanci sai ita Muneebance
ke ganewa. Wannan abu na ciwa
Suwaiba tuwo a kwarya shi yasa ma ko
sau daya bata taba dauko shi ta fito dashi
ba. In har ba Isah ko Muneeba ne suka
fito dashi ba, in kuma ba sa nan to ranar a
daki zai wuni a kwance don ba ya iya
hawa shi kaďai sai an taimaka masa.
Ranar wata Juma'a gidan shiru
babu kowa Goggo ta je sallar Juma'a ita
da Isah Suwaiba kuma na dakinta tana
bacci sai Muneeba ce kadai a dakin
Mujeeb hakan ya sa ta gungurashi zuwa
113
WATA KUSAN 3
Rahmatu Hassan Zaria
bayin dakin baccinsa a zaune akan kekensa
tayi masa wanka dama tunda aka kawo
keken akai take masa wanka.
Tana gama masa suka fito ta zo ta
goge masa jikinsa ta shafa masa
mayukansa masu kamshi ta saka masa
kaya ta fesa masa turare shi dai yana ta
binta da kallo yana murmushi.
Ya riko hannunta ya yi magana
"Zan kwanta". Ta yi sauri ta matsa da shi
gurin kwanciyarsa ta kamashi ta kwantar
da shi ya yi mata ishara da hannunsa cewa
ta zo ta zauna kusa da shi ta yi kamar
yadda ya umurceta sai ya sa hannun mai
lafiya ya ja ta zuwa kirjinsa ya kwantar da
ita har sai ta dinga jin bugun zuciyarsa ke
yi cikin kunnenta ya dinga sauke ajiyar
zuciyar irin ta yaron da aka lallasa aka
bashi wani abu da yake so har yayi kuka
kafin a bashi abin.
Itama sai taji wata irin natsuwa da ta
manta rabon da ta ji irinta a tare da mijin
nata idan ta yi alamun za ta tashi sai ta ji
114
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
ya hanata da hannunsa dole ta hakura ta
kyale shi tunda ta lura hakan yake so
hakan ya haifar masa da natsuwa a
zuciyarsa.
Ta yi masa magana a kunne "Ka yi
hakuri ka san gidan nan bamu kadai
bane, sannan kuma Goggo sun kusa
dawowa daga masallaci kada su shigo su
ganmu a haka ido da kunya".
Rufe bakinta ke da wuya sai ganin
shigowar Suwaiba suka yi tsulum a falon
wannan dama dabi'arta ne babu sallama
a cewar ta ita da dakin mijinta babu
wanda ya isa ya yi mata dokar sai ta yi
sallama, sannan za ta shiga, ta manta
cewar dokar Allah ce yin sallama a guri
kafin ka shiga.
Wani uban ashariya da ta zunduma
shi ya firgita Muneeba har jikinta ya
dauki tsima "Kan uba can dama jarabar
da ke kawo ki gidan nan kullum kenan
kina like masa ana cin amana ta ni ga
hoto an ajiye ina ganinsa a mara lafiya
115
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
ashe garau yake tunda har ya iya
lunkumeki a jikinsa.
Lallai yau za'a yi tsiya a gidan
wallahi bari Goggo ta dawo ta zo ta ga
shedancin da ake yi a gidan nan tana
ruwan tijarar ne Goggo suka dawo ta
maimaitawa Goggon abin da ta zo ta gani
yake faruwa har sai da ta kara gishiri tana
kukan munafunci.
"Wannan ai zalinci ne ni ina zaune
da shi bai bani nawa hakkin ba wata da
watanni ina ta hakuri shine ke zan sameki
yana baki naki hakkin to wallahi sai dai a
raba kwana ki dawo dakinki ki zauna a
dinga gungurashi ana kaishi dakin wadda
take da girki ko kuma mu dinga biyo shi
dakinsa in kuma ba haka ba wallahi zan
tashi hankalin kowa a gidan nan don ba
zan yarda da cin kashi ba”.
Goggo ta hau bata hakuri "Ki yi
hakuri ai ban san haka ce ke faruwa ba
wannan ai rashin kunya ne don an san bana
gidan shine za'a zo a tilasta shi yin abinda
116
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
baiyi niyayya ba yana fama da kansa in
abinda ki ke muradi kenan ai sai ki dawo
dakinki. Muneeba kuka ta saka tana
karyata wannan sharri da Suwaiba ta yi
mata Isah kuwa hasala yayi yace "Haba
Goggo haba Goggo wannan maganar
bata dace ta fito daga bakinki ba yanzu
ke har za ki yadda da karya da sharri irin
na Suwaiba in ma hakan ta faru ai mijin
ta ne ita me ya sa ba za ta zo ta zauna
kusa da shi ba in har son gaskiya take
masa wallahi Muneeba ba ta da rashin
kunyar da za ta iya yarda hakan ta faru alhalin ta san gidan nan ba su kadai bane.
Gaskiya Goggo idan kika yarda da
maganar nan baki yi wa Muneeba adalci
ba a irin yadda ta tsayu tsayin daka akan
kula da lafiyar danki wadda kike so din
gata nan bata tsinana masa komai ba sa
mummunan halin da take bullo da shi
kala-kala.
117
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Mujeeb ma hawaye yake yana
karkadawa Goggo hannu a nufinsa nuna
mata ya ke Karya Suwaiba ke yi Muneeba
ta soma hada duk wani abu da ta san nata
ne a dakin Isah ya tari gabanta yana cewa
"Aunty Muneeba wai me ki ke shirin yi
kenan ba fa za ki tafi ba akan wannan 'yar
maganar to meye ma abin damuwa ina ce
mijin ki ne ai gara ya nuna mata ke ya fi so
tunda har ya kasa hakuri da al'amarinki
dama duk abinda ya faru baya ba yin kansa
bane, ina ganin yanzu alkadari ne ya karye
don girman Allah ki yi hakuri ki manta da
wannan shirmen in ni ne ma wallahi a
gabanta zan yi abinda na ke so sai dai ta
mutu.
Muneeba ta rataya jakarta ta dubi
Isah ta ce "Ka yi hakuri Isah dole in tafi ba
zaka gane irin radadin da ke zuciyata bane
kwarai na san Mujeeb miji na nane kuma
don in yi jinyarsa in sami lada gurin
Ubangiji na ya sa nake zuwa gidan nan ba
don wani abu ba amma tunda an fara yi
118
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
min bita da kulli to gara in dan ba gidan
iska idan aka kwana biyu na dawo.
Haba Aunty wallahi dama haka
ake so zuwanki ne bata so ke kuma don
girman Allah kada ki yi fushi ki tafi ki
bar ladanki tunda ba don ita ki ke yi ba
domin Allah ki ke yi abinda take
kwakwazon an yi mata dinma in har an
yi ma ai shine daidai tunda hakan zai
samar masa da natsuwa kuma natsuwarsa
tana cikin nasarar samun lafiyarsa.
Duk yadda Isa ya so ya tsayar da
tafiyarsa Muneeba bai sami nasara ba
don har rantsuwa ta yi masa cewa sai ta
tafi tunda har zancen Suwaiba ya yi tasiri
a zuciyar ta ke tana ta kurawa danta yana
yin abinda bai yi niyya ba kenan a
cewarsu ita jarababbace wannan kalma
ita tafi komai kona mata zuciya.
Shi ma Mujeebun kukansa ya
tsananta har da shessheka, saboda ya yi
ta magana babu mai jinsa Isah ne ma ya
kai. kunnensa bakin ya ji yana masa
119
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
umurnin kada ya bari Muneeba ta tafi ya
bata hakuri. Shi kuma ya yi-ya yi ta ki
hakura itama Suwaiban bata fasa fadar
maganganu ba wa wadanda suka dada
tunzura hakurin Muneeba ganin Goggo
tana jinta bata iya tsawatar mata
kasancewar tana shakkar kada Suwaiban ta
gayawa uwarta Hajiya Harira.
Muneeban na barin gidan Isah ya
dubi Goggo yace "Shi ke nan Goggo mai
yi miki jinyar danki tsakani da Allah ta tafi
ni kuma kin san ba zama na ke yi ba
saboda makaranta, saboda haka ta barki da
Suwaiba wallahi ko kaffara ba zan yi ba ba
za ta kula da jinyarsa kamar Muneeba ba
kina gani kwana biyu ma bata zo gurinsa
ba ya kauracewa abinci yanzu kuwa sai
abin da Allah ya yi.
Shi ma daukar littafinsa ya yi ya fice
ya bar musu dakin Muneeba na isa gida
Inna Amina ta lura da yanayin fuskar shine
fa ta biyo ta daki ta isketa kwance akan
gadonta tana tsiyayar hawaye ta zauna a
120
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
gefen gadon tana cewa Lafiya kike kuka
jikin nasa ne ya tashi"? Ta girgiza kai, to
mene ne? Gaya min don kin jefa zuciyata
cikin damuwa ta kwashe duk abinda ya
faru ta gayawa Inna Amina ta kara da
cewa "Na hakura da zuwa jinyar tasa duk
randa Allah ya sa ya warke idan yana da
muradin cigaba da zama da ni ya zo ya
neme ni, amma na gaji da wulakancin
matarsa ta yi min Goggo ta yi min,
wallahi da a ce ina biyewa halin matarsa
da kullum sai an ji mu amma yau ta kaini
makura don wallahi na tsani abinda ban
yi ba ace na yi,.
Inna Amina ta yi dan murmushi ta
ce "Ke don Allah share hawayenki in ma
ya kwanta da ke ba mijinki bane, in ita ta
gaza da al'amuransa ke ma sai ki gaza
wannan ai ba zai yiwu ba.
Wallahi mama babu abinda ya faru
tsakaninmu kawai ta shigo ta ganni
kwance a saman kirjinsa ne kuma wallahi
ina zaune kusa da shi ne ya matsa min sai
121
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
na sa kaina a kirjinsa, da na ki ma shi da
kansa ya kamo ni ya kwantar da ni shi ne
fa abinda ta gani", Inna Amina ta kamota
ta tasar da ita zaune tana share mata
hawaye "Yaro dai yaro ne in banda abinki
Muneeba ai abinda yake so ya fi haka a
gurinki tunda kullum fa kece a kusa da shi
sannan ki duba tsawon watannin da yayi
yana jinya idan aka haďasu da watannin da
kika yi a gida ma ai kun haura shekara
rabonki da shi to meye in kin nuna
mararinku akan juna, kawai kishi ne ke
damun zuciyar Muneeba saboda haka ba
zaki daina zuwa ba karewa ma dakin zaki
ko, ai ba sakinki yayi ba, in ya so idan ya
warke ya ga baya son zamanki sai ya baki
takardanki.
Muneeba ta ce Ni gobe ma Dukku
zan tafi garin nan ya fita raina sai na
kwana biyu zan dawo "B a zan hana ki
tafiya ba amma ki kwantar da hankalinki
wannan ba wani abin damuwa ba ne da zai
sa ki dami zuciyarki tun bayan dawowarta
122
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Isah ke 'ta kiranta a waya tana tsinke
kiran nashi daga bisani ma sai ta Daina
taba wayar har ya hakura.
Ashe ba hakura ya yi ba sai gashi a
daren ya zo sake bata hakuri mujeeb ne
ya matsa masa yazo ta ce masa ita ta
hakura gobe ma tana nan zuwa a tunanin
Isah da gaske za ta zo bai san ta kifeshi
bai bai ne ita gobe ma kauyen su ta nufa.
Washe gari kuwa ta kama hanyar
Dukku ta isa da wuri innarsa na ta
mamakin ganinta da ta yi da akwatin
kaya kuma ta ce sai ta kwana biyu zata
koma inna ta ce kwana biyun Malam
Bahaushe ko kwana biyun gaske". Ta ce
kwana biyun Malam Bahaushe", shi
kuma majinyacin kin daina kula dashi
kenan kin bar ladan ko? Ta ce inna na
dinga zama da shi kenan ga goggo
sannan ga matarsa Isah ma yana nan tare
da shi indai ba makaranta ya je ba”.,
Ta ce "Na san duk suna nan amma
wannan ai ba Hujja bace da za ta sa ke ki
123
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
taho ki bar wa wasu ladanki kin, kuwa san
ladan wanda ya yi jinyar wani balle ma
ladar jinyar miji ga matarsa? Zan dai fi
yarda idan kika ce min wani abu ne ya faru
kika ki zuwa amma ba haka kurum ba"
Da kyar ta gayawa Innan abinda ya
faru sai gani tayi Innan ta girgiza kai ta ce
"Allah ya kyauta amma wannan aiba abin
jin zafi bane balle har ya sa ki yi fushin da
zaki bar miliyoyin ladanki da bama kisan
iya adadinsu ba shike nan ki zauna duk
ranar da zuciyarki ta lafa sai ki koma.
Kwana daya biyu Isah bai ga
Muneeba ba gashi kuma jikin Mujeeb yayi
tsananin tashi ta yadda komai ma sai an yi
masa don ko kekensa ba'a dora shi ya
daina cin abinci ko wanka ya ki yarda a yi
masa yana kwance kawai sai aikin tsiyayar
hawaye.
Hankalin kowa a gidan ya tashi
musamman Isah da Goggo wadanda suke
ganin ta leko ta koma ga samuwar
lafiyarsa Isah da ya je gidan Inna Amina
124
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
ita ke shaida masa Muneeba ta tafi
Dukku ya zo ya shaidawa Mujeeb shine
fa yace maza a lokacin yaje Dukku su
taho tare.
A Dukkun sun yi ta tafka
Muhawara da ita tace sam ba zata koma
Gombe a lokacin ba ya tafi za ta zo shine
yaje ya shaidawa Baffa Adamu abinda
kenan. Baffan ya jinjina kai ya ce ita
Rahin din ce ta turo ka ka tafi da
Muneeban don ta yi jinyar danta? Lallai
duniya da abin mamaki take shin tamanta
lokacin da ya ce ta zauna sai ya neme ta
na kirata a matsayinta na mahaifiyarsa na
ce ta lallashe shi ya zo ya dauki yar
uwarsa ta ce ita babu ruwanta a kyaleshi
me. daki shi ya san inda yake masa
Yoyo? In ta manta ka je ka ce na ce ka
tuna mata ko kuma ni da kaina zan tuna
mata.
Ai dama zuru na yi mata don ko
zaman jinyar da Muneeban ta je ta yi
kyalewa kawai na yi sabo da tausayin
125
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
halin da yake ciki amma ba don zumunci
ba.
Ka tashi ka je ka shaidawa mata
Muneeba ba zata dawo ba har sai ranar da
ita da kanta ta tako gidan nan ta bamu
hakuri akan irin cin kashin da suka yi wa
yarinyar nan in kuma ba haka ba to ta je ta
yi jinyar danta ai ita ta haifi abinta ba wani
ya haifar mata shi ba kamar yadda take
fada.
Isah ya raunana murya "Baffa don
girman Allah kayi hakuri ni kaina na san
Goggo bata kyauta muku ba amma ku yi
hakuri ku duba makomar rayuwar Yaya
Mujeeb wallahi a halin yanzu rayuwarsa
tana cikin hatsari sosai ta kai fagen ma sai
dai a kwantar dashi sai dai a tayar da shi
abhinci sam baya ci duk dalilin rashin
Muneeba a kusa dashi”.
Baffa Adamu ya ce "To dama ai
mutum yana da ranarsa kuma ba'a sanin
yana da rana sai bayan baya guri ko idan
ya mutu tunda yanzu ta san akwai ranar da
126
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
muneeban za ta yi mata to ni ban hana
Muneeba kowa ba jinyar mijinta ba
amma da sharadin sai ta rahin din ta zo
nan da kafafunta ta bamu hakuri kuma ni
da kaina zan dawo da ita ka tashi ka je ka
shaida mata sakona don mun gaji da cin
kashi a tsakar ka da akewa yarinyar nan
da me za ta ji da rashin haihuwa da Allah
bai bata ba suke mata gori ko kuma da
kwarzabarsu ita da abokiyar zamanta".,
Isah haka ya taso gwiwa a salube
ya yi sallama da Baffa Adamu ya dau hanyar Gombe wannan sako na Yayanta
bai risinar da zuciyar Goggon ba sai ma tayi mirsisi da sharadin daya gindaya
mata na cewa sai ta zo da kanta ta ba su
hakuri sannan Muneeba zata dawo a
cewarta ai idan ta yi haka ta zubar da
girmanta ace ita da kanta za ta je ta ba
Muneeba hakuri to ita meye nata tunda
ba įta ta kore ta ba.
Isah har kuka yayi shi da
Mujeebun suna rokon Goggo da ta je
127
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Dukku amma taki saima ta suri gyalenta ta
bar gidan.
Dr. Aminullah ne ya zo ya iske abin
dake faruwa Isah ya gaya masa yadda
rigimar ta samo asali Dakta ya kada baki
yace "Alhamdulillah aimu likitoci abinda
muke son ji kenan saboda muna tunanin
gaban nasa ma ba ya aiki a dalilin matsalar
da ya samu dama jira na ke ya warke in
akwai matsala sai a san abin yi, yanzu ko
ba abin da ya faru tsakaninsu muna
kyautata zaton yana nan garau.
Yanzu kana ganin idan muka saka
shi a mota muka je gurin Baffan naku ba
zai bashi ita ba tunda dama tun farko shi
suke son ya je?.
Isah ya ce "Eh to ban sani ba ko
Baffa zai yarda bari mu gwada mu gani".
Suka kama shi suka kaishi cikin
mota suka saka kekensa sannan suka dauki
hanyar Dukku basu iske kowa a kofar
gidan ba hakan ne yasa suka fito da keken
Mujeeb suka ciccibeshi daga mota suka
128
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
dora shi akai, sannan Isah ya gungura
keken suka shiga cikin gida.
Salallamin da matan gidan suka
hau yi saboda ganin Mujeeb yasa Baffa
Adamu fitowa daga turakarsa ya hau Isah
da fada "Haba Isah don me za ka dauko
yaron nan ka zo da shi yana cikin
mawuyacin hali irin wannan ai ni bashi
na ce ya zo ba ita Rahin din na ce sai ta
Zo
Dr. Aminullah ya risina yana gaida
Baffan sannan ya ce "Ni nace mu taho da
shi, ita gwaggo ta ki bada hadin kai tazo,
kayi hakuri Baba matsalarsa tana bukatar
a tausaya masa". Baffa ya matsa jikin
keken ya dafa kafadar Mujeeb ya ce
"Sannu Mujeebullah haka ciwon nan ya
maida kai? Allah yasa kaffara ce kayi
hakuri matarka zata dawo amma sai
Rahin ta zo dole saboda akwai
maganganun da zan yi da ita akan
matarka ni kuma bata isa in bita inda take
ba".
129
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Mujeeb ya soma sana'ar tasa ta
tsiyayar hawaye saboda ya san ko yayi
magana ba dole bane a jiyo sautin maganar
tasa duk matan gidan da yaran gidan sai
aka hau koke-koke ganin kukan da Mujeeb
ke yi ga shi ya zama abin tausayi mutum
lafiyayye kakkarfa mai kwarjini da cikar
halitta ga kudI, amma yau shine a na
kashe cikin keken guragu ana tura shi ya
rame ya kwantsame ya fiya hayyacinsa.
Kai duniya ina za ki da mu duk
wanda bai ji tsoron Allah ba wallahi ya yi
babban asara duniya da Lahira".
Baffa ne ya ke ta nanata wannan
Kalmar da hannunsa ya tura keken
Mujeeb ya shiga da shi turakarsa shi ma
sharar kwalla yake yi yace Isah ya shigo
da bakonsa.
Isah ya dubi Baffa yace, "Wannan
likitansu ne a can asibitin da ya kwanta to
shine yake zuwa gida koda yaushe yana
duba shi, ko wannan keken ma shi ya siya
ya kawo masa".
130
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Baffa ya sake mikawa likita hannu
suka yi musabaha yana cewa "Mun gode da dawainiyya Likiya Allah yayi albarka
ya shirya zuri'arka ya jikan magabata ya kara maka budi a al'amuranka.
Dr. Aminullah ya amsa da Ameen
Baba" tare da nuna jin dadinsa bisa ga
wannan addu'ar Baffa ta kanshi ya amshi
abinci yana ba Mujeeb yana lallashinsa
da cewa in dai ya ki ci ba zai bashi
matarsa ba, ai yana jin haka ya hau
hadiye tuwon laushin da aka bashi kafin
kace meye har ya cinye. Duk sai abin ya
basu mamaki.
Baffa da kansa ya kira wayar
Goggo da kyar ta iya dauka saboda a
duniya tana shakkar sababin yayan nata,
don ta san halinsa, ko gaisuwar bai amsa
ba ya ce "Wallahi Rahin ki kiyayi rudin
duniya tunda har ni zance ki zo ki ki
zuwa saboda ba kya ganin kowa da
gashi, to wallahi ki yi wa kanki karatun
ta natsu ga Mujeebu abokinsa likita ya
131
MATANUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
kawo shi bikon matarsa ni kuma na yi
rantsuwar ba za ta koma ba sai kinzo nan
gaba na da Kafarkı sannan za ta koma in
kuma kinki zuwa har shi ita sun bar maki
gıdan za su zauna anan gurina sai kici
uwar da zakı ci Gomben.
Ya kashe wayarsa ya barta da
saluba6ben jiki ko Suwaiba bata gayawa ta
shirya ta baro Dukku a motar haya zuwa
Gombe zama akayi na musamman anan
gidan su Baffa zaman da ya hada da duka
su Baffan da Babansu Muneeba da Innarsu
da ita kanta muneeban ga Mujeeb likita
Isah ne kawai ya fita.
Maganganu sosai aka yi akan
abubuwan da ke faruwa a gidan Mujeeb
din an bukaci Goggo ta fadi in akwai
wani abu da Muneeba ke mata na 6atanci
ta fada ayi wa hanci Tufka.
Sai ta kama kame-kame zance babu
na kamawa balle a yanke wani hukunci. A
karshe dai yayyin nata suka yi mata fada
sosai tare da nasiha akan muhimmancin
132
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
zumunci itama Muneeban sun yi mata
nasiha akan ta ci gaba da ba Goggo tata
girman a matsayin na uwar mijinta kuma
yar mahaifinta duk da yake sun san irin
girmamawar da take mata amma suna so
ta kara akan wadda take mata.
Shi ma Mujeeb sunyi masa tasa
nasihar tunda yana jinsu akan ya kamanta
adalci tsakanin matayen nasa daga karshe
aka rufe zaman da yi masa addu'ar Allah
ya bashi lafiya.
Baffa Adamu ya yi wa Muneeba
umurnin ta bi Mijin ta, ya ce idan sun isa
Gombe su biya su dauki Innarta Amina
ta rakata dakinta suka dingumo su hudu
suka taho gombe Isah da likita sune a
gaban motar Mujeeb da Muneeba a baya
hakan ne ya bashi damar da yayi kwance
a cinyar Muneeba 'yar hirarsu a hankali.
Likita yana tuki yana kallonsu ta
madubi yana murmushi saboda shi
sha'awar soyayyar su yake yi don shi bai
taba tunanin suna da wata matsala a
133
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
rayuwar aurensu ba bisa ga yadda yake
ganin kulawar da Muneeba ke bashi a
asibiti, ashe matsaloli ne cinkus a rayuwar
auren na su sai da ya shigo cikin rayuwar
ne ya ga hakan wanda yana fatan Allah ya
sa karshen matsalolinsu ya zo kenan.
Ganin su da Suwaiba ta yi a tare
sannan har da Inna amina kuima kai tsaye
Muneeba ta bude dakinta su Jume da
Maigadi suka hau aikin sharewa da gogegoge ya tabbatarwa Suwaiba bikon
Muneeba aka je wato don munafinci har da
Goggo da shi Mujeebun da bashi da lafiya
lallai dole ta dauki babban mataki tunda
Munmeeba ta dawo gidansu.
Komawarta daki ta yi babu wanda ta
yi wa sannu a cikinsu sai da Inna Amina
ta tabbatar an gyara ko'ina na dakin
Muneeba sannan ta kara yi musu nasiha
daga bisani ta tafi.
Muneeba ta shiga kicin dinta ta
shiryawa Mujeeb lafiyayyen abinci da abin
sha sannan ta zauna ta tsala kwaliya wadda
134
WATA KUSAN З Rahmatu Hassan Zaria
rabonta da yin irin tatun barinta gidan ko
turaruka ta fesa yayi kala goma sai
kamshi ya iya rikita kwakwalar mutum.
Ta dauki tiren da ta shirya kayan
abinci ta isa dakinsa, Isah na ganinta ya
hau murmushi yana fadin "Kai Auntyna
wannan kwalliya ai sai ki rikitamin
kwakwalwa yaya ko da yake idan yana
ganin irin wannan sai ya fi saurin
warkewa tunda ya kwana