biyu baiga irin
wannan ba. Ya yi saurin amsar tiren
hannunta sannan ga lafiyayyen abinci
gaskiya kin kyauta gara ki dage ki rike
gidanki da mijinki ke kika fi sanin me
yake so menene baya so?.
Ta zauna daf da mijinta tare da
fadin 'Ya jikin naka ina can ina hada
maka abincin ne dana gama na yi wanka
na yi Sallah shi yasa na dade". ta dubi
Isah 'Ka kawo masa ruwa yayi alwala
ne? ya ce, Eh har Sallah ma ya yi abinci
kawai ya rage zai ci ni bari in fita gurin
budurwata tunda yau kin dawo ke za ki
135
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
kwana dashi". Ta Harare shi Lallai Isah
baka da Kunya a gabanmu kake fadar zaka
gurin budurwa to sai ka dawo ka gaisheta".
Yayi dariya yana sosa keya, ya
wuce ya tafi Muneeba ta janyo tiren ta
soma zubawa Mujeeb abinci shi kam yayi
sakato tamkar wani sakarai yana ta aikin
kallonta har sai da ta dago suka hada ido
suka yi wa juna murmushi. Ta dinga bashi
abincin yana ci tana bashi lemu yana sha
sai ganin Suwaiba suka yi a gabansu tana
huci ta dubi Muneeba shekeke ta се "То
tunda kin dawo dakin mijinki yau sai a san
abinyi raba kwana za'a yi yau yana can
gobe yana can ko ayi kwana bibbiyu don
ba zai yiwu kullum kina leke da shi ba
tunda ba ke kadai bace matarsa ehe!.
Muneeba ba ta ce Uffan ba Illa ma
ta cigaba da ba mijinta abinci a baki yana
ci Suwaiba ta sake kulewa ta ce "Kinafa ji
na ina magana in kuma tare zamu dinga
kwana da shi dukanmu sai in ji.
136
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Sai da Muneeba ta gama bashi
abinci ya sha ruwa sannan tayi magana
"Duk yadda kika ga dama ki yi, amma ni
kam yau da gobe zan kwana da mijina in
kula da shi jibi da gata naki ne, in kinga
zaki daukeshi zuwa dakinki ko ki biyo
shi duk daya".
Jin Muneeba ta maida kwanan
bibbiyu yadda suke yi sai ta ja Uban tsaki
kawai ta fice.
A kwana biyun da Muneeba tayi
tare da Mujeeb har wata kiba yayi ya
sake murmurewa kasancewar duk dare a
kirjinta yake kwana kuma duk wani abu
da yake so tana yi masa sai dai ta lura ba
ya da wani kuzari irin na sauran maza
kila sai yaga likita ko ya na da matsala ne
ta wannan fanni ba su sani ba.
Washe gari ta nemi shawarar likita
akan tana son ya fara gwada tafiya tunda
ta ga ya dafa bango ya mike Dakta
Aminulla ya ce ta jira shi gashi nan zuwa
zai nuna mata yadda za su yi.
137
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Ba'a fi mintuna talatun ba sai ga Dr.
Aminun da Sandunan koyon tafiya guda
biyu Muneeba bana ganinsa ta hau
murmushi tana cewa Sannu likita da
dawaniya kullum baka gajiya daga
maganar za'a fara koyon tafiya shine har
ka taho da gudunmuwar kafa.
Yayi murmushi ai gara ayi koyon
tare da madogari don kada a sami matsala
ya zo ya fadi idan yana bin bango gara
idan da wannan sandar ba zai fadi ba Insha
Allah Allahu za ta zamo masa abin
dogarewa shi yasa na zo masa da ita.
Likita ya mikar da shi tsaye ya bashi
sandunan ya amsa ya dogara ya soma
takawa a hankali. Muneeba ta yi saurin
zuwa ta tsaya a bayansa likiya ya yi dan
Murmushi ya ce "Kai Madam kina son
abokin nan nawa da yawa kin dauka zai
fadi ne kika taro bayansa itama
murmusawa ta yi cikin jin kunya ta ce
"wallahi gani nayi kamar jikinsa na rawa
shi yasa na zo bayansa kada ya fadi.
138
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Jikinsa kam dagaske rawan yake
yi amma Dakta ya hana Muneeba ta rike
shi ya ce ta barshi ya yi tafiyar da kansa.
Haka ya yi ta zagaye falonsa a hankali a
hankali, amma fa yayi zufa kashirban
don har diga take yi daga fuskarsa ya
dubi Dakta ya yi magana can kasan
makoshi "Na gaji zan zauna kada na
fadi" jin haka ya sa Dakta ya kama shi ya
zaunar da shi a gefen kujera ta zaman
mutum biyu.
Gaskiya ka yi kokari yanzu
shikenan ba zaman keke tunda ka fara
tafiya kullum abin da za'a yi kenan
koyon tafiya sai ka gaji da za'a maidaka
keke ko a zaunar da kai a kushin.
Ranar da Suwaiba ta amshi girki
jarfa aka sha da ita wai lallai Muneeba ba
zata zauna gurin Mujeeb ba sai dai idan
ta gaishe shi ta fita ta bar dakin tunda ba
girkin ta bane.
Muneeba ta tashi tayi tafiyarta
daki Isah da ya dawo ya iske shi kadai a
139
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
dakin yana ta kici-kici hawa kekensa
amma ya kaga shi ba murya ba balle yа
Kwalawa wani kira.
Isah ya kama shi ya dora shi bisa
akan keken sannan ya nufi dakin Muneeba
yake ce mata ya aka bar Mujeeb shi kadai
daki gashi nan saura kiris ya fadi garin
hawa kekensa.
a
Muneeba ta gaya masa yadda suka
yi da Suwaiba da safe Isah ya ce wannan
ma sam ba zai yiwu ba ita ba zata zauna ta
kula da shi ba sannan ta ce ke ma kada ki
zauna to bata isa ba ai ba kwana kika ce
zaki yi da shi ba tunda ita abinda ke ranta
kenan ba kula da lafiyarsa ba.
Bari in je gurin Goggo sam ba zai
yiwu a barshi ba, shi da ke neman taimako
ya je ya sami Goggo da maganar sai ta
nuna gara a kyale Suwaiban in yaso duk
ranar girkinta Muneeban ta dinga fito da
shi harabar gidan zai ta zauna tare dashi.
Isah ya ce yanzu Goggo shi kenan duk
abinda matar nan keso shi za a yi mata a
140
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
dinga jin maganar ta tamkar ana tsoronta
tana juya mutane son ranta".
Ta ce Isah kaga bana son neman
fitina ka je ka yi abin da nace tunda na
lura yarinyar nan neman tashin hankali
take yi da kowa a gidan nan, Isah ya
koma dakin Mujeeb ya sako shi
kekensa ya fito da shi harabar gidan ya
je ya kira Muneeba ya ce ta zo inji yayan
na sa yana can harabar gidan.
a
A can ta same su da Isan shi yana
zaune a kekensa isan na zaune a kujerar
roba a gefensa ma wata kujerar ce anan Muneeba ta zauna suka shiga hira abinsu
don muryar Mujeebu ta soma fita.
Wannan abu ya bata ran Suwaiba,
saboda tana hangensu ta window dakin
baccinta ta yi kwafa ta fada a fili "Lallai
ma isan nan wato tunda na hana abi min
miji daki shine ya fito da shi waje don su
haďu to zan bullo masa ta bayan gida bai
sani ba kenan".
141
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Sabon salo ta fito dashi idan ita ke
girki sai ta kama kofar falon Mujeeb din ta
rufe shi a ciki in har bata dakin don kada
wani ya shiga sai da suka yi tsiya-tsiya ita
da Goggo akan ta ce sam ba zai yiwu ta
dinga rufe shi a daki ba Isah ma yayi mata
nasa tijarar sannan aka sami saukin
al'amuranta.
142
2
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
****** ***** *****
Jikin Mujeeb yayi sauki sosai don yanzu
ma ya rike sanda shi kadai yake tafiya
maganarsa ma tangarau take fitowa
hannun sa da ya karye ne kadai wani
lokacin yake yawan masa zogi ko yayi
masa nauyi.
Har a wannan lokacin bai koma
bakin aikin ba kasancewar jikinsa bai
gama koma masa daidai ba, kuma yana
son zuwa ganin Likita a (Egypt)
Ko da yaushe Mujeeb ya kalli
Suwaiba sai ya dinga jin kyankyaninta a
dalilin badakalar da yaji da kunnensa ta yi da boka har ta kai ga shima ya shiga
cikin kokwanto lafiyarsa kasancewar duk bokayen nan zandikan fasikai ne masu
dauke da cututtuka zamani iri iri, in
kuwa haka ne yana rokon Allah ya rufa
masa asiri bata je ya kwaso cuta ta lakaba
masa ba sannan shi kuma ya lakabawa Muneeba.
143
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Maganar ma ya fadawa wani
wannan laifi da tayi masa ma duk bai taso
ba don a ganinsa hakan tonon silili ne
garesu gara kawai ya barwa cikinsa zai
bari idan ya je Egypt a yi masa gwajin
jinni don a tabbatar da lafiyarsa.
Babban tashin hankalinsa na yadda
dole itama Muneeba sai an yi mata gwajin
don kuwa ya san itama ba za ta shallake
siradin da ya afka ba tunda duk sun
gauraye da juna sau ba adadi tun bayan
Suwaiban ta ba boka kanta, ya daga
hannuwansa biyu sama yana addu'a ya
Allah ina rokonka in har za ka jarabeni da
ciwo a rayuwa kada ka jarabci ni da
wannan cuta da jama'a ke Kyamarta ake
kyamar mai cutar ya Allah don alfarmar
son da kakewa Annabinka ka kawo mana
al'amura masu sauki a rayuwar mu ta
duniya da lahira". Ya yi Salatin Manzon
Rahama sannan ya shafa addu'ar ya cigaba
da yin istigfari ga Allah.
144
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
A bangaren Suwaiba kuma tunda
ta ga Mujeeb bai tunkare ta ko ya
tuhumeta da hirarta da Larai kawarta da
ya ba wadda jin hirar ne ya haddasa masa
larurar da ta same shi sai ta ayyana a
ranta lallai aikin da tace boka ya yi mata
na rufe masa baki kada ya tada maganar
shine ya yi tasiri a kansa tunda gashi ko a
fuska bai muna mata ba illa dai abu daya
da ke bata mamaki tunda ya warke ko
sau daya bai taba nemanta ba, kuma tana
binsa kwana dakinsa.
Babban takaicinma har da kanta ta
tallata masa kanta sai ya juya mata baya
yace shifa ta kyale shi bashi da lafiya ta
barshi ya sami isasshen lafiyar. Cikin
daren nan ta tashi ta saka masa kuka tana
surutai "In wani abu na yi maka ba sai ka
gaya mini ba da zaka dinga zaluntata a
kalla yanzu an sami shekara da wannan
larurar taka haka nan na daure ina hakuri
tunda ba dutse aka hallice ni ba, yanzu
kuma ka warke garau amma ka ce min
145
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
1
1
kai baka da isasshiyar lafiya alhalin
matarka babu abin da bakwa yi tun ma
kana jinya, sai ni ce da baka kauna za ka
ce min baka da lafiya wallahi na gaji ba
zan yarda ba hakuri na ya kai makura ya
Kare.
Ya tashi zaune yana mata kallon
mamaki ya ce "Wani ne ya gaya miki abin
da ke faruwa tsakaninmu da ita koko labe
kike mana da har kika san ina mata abinda
ke bana maki?.
Allah ya kyauta in yi muku laбе
gani na yi ita hankalinta a kwance kullum
cikin annashuwa take ta yi kiba ta yi kyau
abin ta ni kuwa ina cikin tashin hankali
alhalin in duniya da gaskiya ita ya kama ta
fini shiga damuwa ita da ta dade bata
gidan miji.
Mujeeb ya yi murmushi cike da
al'ajabin kalaman Suwaiba ya ce, "Sa rai
ga koshi ai shi yake kawo jin yunwa, ita
bata sa ranta ga wannan abin ba shi ya sa
bai dameta har ta kasa sukuni ba balle ta
146
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
shiga cikin garari kinga ke da ki ka
kallagawa kanki ai gaki nan kin lalace
kin hana kalanki sukuni har kina zargin
da ita ake harka ke ba a yi da ke.
To bári in gaya maki larurar da ta
sameni ta yi sanadiyar tafiya da lafiyar
kuzari na, in kinga za ki iya hakurin
zama da ni a haka har in samu lafiya to in
kuma kinga baki iyawa to hanya a bude
take gare ki. Saboda haka ki barni in yi
bacci in baki iya bacci tare dani to kama
gabanki don bani da kuzarin da zan iya
tsinana miki komai. Yana gama fadin
haka ya ja bargo ya rufe jikinsa ya hau
bacci ya kyaleta na zaune.
A haka aka cigaba da zama a gidan
kuma duka 6angarorin biyu baya iya
hasala komai ba wai don bashi da lafiyar
bane kamar yadda yace lafiyar tasa ba
isasshiya bace sannan bangaren Suwaiba
ba kyamarta ya ke ji ita kuma Muneeba
tausayinta yake ji kila. ya kwaso cuta
kada ya lakaba mata yanzu in har da can
147
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
bata dauka ba saboda haka dole sai ya
tantance lafiyarsa shi da su.
Shi da Muneeba ya ke ta yi musa
shirye-shiryen tafiyarsu Egypt wanda ko
ita Muneeban bata sani ba Passpot ma a
Jakarta ya dauka bata sani ba har aka gama
komai sannan ya gaya mata.
Ta zauna daf da shi a doguwar
kujerar falonsa sannan tace da gaske ka ke
yi da ni za'ayi tafiyar ya gyada mata kai
amma kana ganin ba za a sami matsala da
Suwaiba ganin tunda ka aureta baka taba
ko'ina da ita ba a gani na ita ya kamata ka
tafi da ita sai barin Waleeda in yaye ta
tunda na ga ta isa Yaye.
Ya sauke numfashi "Bada ita na
tsara tafiya taba saboda haka kadama ki
sake cewa in je da ita, in ba zaki min
rakiyar bane sai in tafi ni kadai kila ma
Allah ya tausaya min wata balarabiya ta
like min in aureta a can kinga sai ta yi
jinyata.
148
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Muneeba ta kankame shi tana
kukan shagwaba da 'yan tsalle-tsallenta
irin na yaran goye tace, Insha Allahu
Allah ba zai tausaya maka ta wannan
fannin ba kafata kafarka tunda na gano
ba neman lafiya zaka ba neman aure za
ka je gara in bika in kashe maka kasuwa.
Shi ma dada matseta ya yi a jikinsa
har sai da ya ji notinan jikinsan sun fara
kwancewa sannan ya yi saurin sakinta
don kada ta jika masa aiki shi kam
mamakinta yake ji na yadda bata taba yi
masa korafi irin na Suwaiba ba duk da
dadewar da suka yi rabonsu da juna
wanda akalla an kai kusan Shekara daya
da rabi kuma tsaf ya lura tana cikin
tsananin bukatarsa daurewa kawai take yi
a dalilin kunya irin ta matan Hausa
Fulani duk da duka bane suke da irin
wannan kunyar sabanin irinsu Suwaiba
wadda ta fito karara ta nuna masa
maitarta a fili na gazawar hakurinta.
149
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Tunda maganar tafiyarsu Egypt din
nan ya bayyana sai Suwaiba ta hau adawa
da al'amarin ta fito karara ta nuna
bijirewarta wai ita sam bata yarda da
wannan rashin adalcinda ake nuna mata ba
dole sai dai ayi tafiyar da ita. Rigima sosai
suka yi da shi har sai da ta kaisu gaban
Goggo.
Goggo ta hau sulhu a tsakanin su,
"Kai meye dalilinka da ba zaka je da ita
ba? Ya karkata yana duban Goggo kina
sane jinya zan je in yi a kasar nan, ko dole
ne in tafi da wadda ta san muhimanci na a
gareta kina kallo jinyar da na yi ta kusan
shekara daya yarinyar nan bata damu da
kula da al'amurana ba dai fi kula da in an
yi min abu ta tada kayar baya tayi haukan
kishi akan abun shi yasa ni kuma zan tafi
da wadda zata kula dani.
Goggo ta jinjina kai, "wannan kuma
kana da gaskiya, tunda ni ganau ce ba jiyau
ba, kuma na yi ta fama da ita tun a wancan
lokacin tayi kokari tana kulawa da kai
150
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
kamar yadda abokiyar zamanta ke yi
amma tayi biris da batuna yanzu ai ga
shinan wa gari ya waya ni ba zan hana
shi ba tunda laifin kine in kinga zaki
gyara don gaba to sai ki gyara'.
Suwaiba ta zumburi baki ta ce "Ai
dama na san bayansu za ki goya tunda su
'ya'yanki ne kuma wallahi ban yafe ba
hakki na ake tauye min". Ta mike Fauu!
Zata fita Mujeeb ya damkota a fusace
yace "Uban wa kike cewa baki yafe ba
ko akwai sa'anki ne a nan? Banza mara
kunya mara tunani fice ki ba mutane guri
sakarya"
Ya hankadata har sai da ta kusa
faduwa Goggo ta haushi fa fada Mujeeb
meye haka kada ka ji mata ciwo mana su
mata in suna shirmen su ai ba a biye
musu tunda in mutum yace zai biye musu
sai ya zama irin su hakuri ake yi da
sha'aninsu.
151
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Tun daga ranar ya fita sabgar
Suwaiba ya maida hankali kan shiryeshiryen tafiyarsu.
Ranar Juma'a ana saukowa
Masallaci yayi sallama ya shigo gidan rike
da hularsa a hannu, Jume ne ke biye dashi
da wasu kaya a bayansa saukowarsu kenan
daga Sallar Juma'a Jumen ne yake tukashi
yanzu tunda ya warke ciwo.
A dakinsa suka iske Muneeba tana
'yan goge-goge tana ganin shigowarsu ta
aje abinda take yi ta nufo shi tana masa
sannu da dawowa ta kai hannu ta amshi
hular hannusa. Jume ya gaisheta ya aje
ledojin da ya shigo da su ya fita ta yi
saurin dauko ruwa me sanyi a Firij ta
tsiyaya a kofi sannan ta isa ta kafa masa a
bakinsa ya shanye duka yana dubanta yace.
Wallahi Muneeba kina sangarta ni a
hakan ne zan iya tafiya wani guri na
tsawon lokaci in barki? Kawai so kika yi ki
kwareni Allah ya taimake ni Goggo bata
152
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
bada goyon bayan in tafi da wata ba in
bake ba itama tana son in ririta mata
danta.
Ta murmusa "Ai dama abin da
kake so kenan a riritaka a dinga
shagwaba ka ga abincinka can bisa tebur
ko nan zan kawo maka don na ganka ne a
gajiye Tubus".
Ya ce "wallahi a gajiyan nake
kafin mu je masallaci Anguwan muka je
daga can na wuce gurin amsa bizarmu
tafiyar Insha Allah gata litini da yamma
kinga gobe sai ki je Dukku ki yi musu
sallama don jibi bana son ki fita ko ina
sai mu yi shirin kayanmu ko ya kika
gani?.
Ta fadada fara'arta yadda kace
haka za'a yi Allah ya nuna mana ranar"
Ta dauko kayan abincin ta aje masa bisa
kafet din tsakiyar dakin ta zuba masa
sannan ya sauko ya soma ci.
Ya dubi Ledojin da Jume ya aje ya
ce. Baki duba ledojin can ba akwai
153
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
danyen kifi an gyara ki fita da shi kada ya
bata min daki kiyi mana farfesu sai kaji
suma an gyara kiyi mana dambun naman
da za mu yi guzuri daya ledar kuma kayan
kwalama ne tunda ke da 'yar (Waleeda
yake nufi) baku san komai ba sai kwadayin
cin kayan zaki.
Ta bishi tana masa godiya ai kuwa
mun gode ni da 'ya ta bari in kai wannan
kicin ai ban san kayan karni bane muka
barshi a daki". Yace Shaf na manta kin san
fa ni idan ina kallonki komai mantawa
nake wai ina Waleedar ne na ji gidan
shiru? Ta ce, "Ta gama kiriniyarta da na
lura bacci take ji shine na kaita aka bata
nono ta yi bacci tun dazun".
Ya ce wai ba zaki je ki dawo da
Karime bane? Ta ce, 'Mun yi waya da
mamanta rannan mun tsaida matsaya cewa
zata dawo amma sai mun dawo daga
tafiyar nan don na tambayi Suwaiba
maganar dawowarta ta ce bata da
bukatarta za'a kawo mata wata daga
154
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Dukku kaga dawowarta yanzun baida amfani tunda ni kawai za ta yi wa Aiki.
Ya kada kai, Shike nan gara a
barta sai mun dawo din, yarinyar na da
hankali gata da aiki ta ce, "ga son yara
ga iya dawainiya dasu, yace Insha Allahu
nan da dan kankanin lokaci za ta yi dawainiya da naki dan ko 'yar". Ta yi
shiru, yace banji kince amen, ni fa bana
san wannan fillancin kawai duk inda kika
ji an yi mana wannan addu'ar ki amsa da
amen kika sani ko ki amsa a bakin
Mala'iku.
Murmushi kawai ta yi ta suri ledar
kajin nan ta fice a dakin tana jinsu yana
mata korafin ta yi ta dawo ta yi masa
tausa domin bacci zai yi.
Washe gari suna ta shirye shirye
tafiya Dukku don tare da Mujeeb din za
su tafi shi ne ta ce mana "Su Waleeda ba
za su Dukkun bane? Ya tabe baki Ai gaki
ga su nan idan za su je wa zai hana su"
155
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Muneeba ta shiga dakin Suwaiba ta
sameta a falon ta tana kallon film a Tibi ta
ce "Yaya Mujeeb yace, ki shirya za mu je
Dukku gaba dayanmu". Ta yi shiru tamkar
ba zata yi magana ba, sannan dai ta dubi
Muneeba a wulakance ta се "Duk zuwan
da nake yi ai ba wani ke sa ni ba nake saka
ranar da zan tafi ki gaya masa ba zani ba in
kuma za a yi mani dole ne to nada ganmo
ki daukar masa ni aka"
Muneeba ta cika da mamaki "Yi
hakuri babu zancen dole a wannan tafiyar
Allah ya huci zuciyarki sai mun dawo ta ja
dogon tsaki "Aikin Banza kawai,
kinibabbar mata da can ke kike kaini garin
namu idan idan zan je wato ga 'yar rakiyar
raka ku yi wa dangi sallama lallai sai na yi
maganin matar nan shiga hancinta yayi
yawa".
Muneeba ba ta iya gaya masa bakar
maganar da Suwaiba ta fada ba illa ta се
masa Suwaiban ta ce bata jin dadi su
gaida mutanen Dukkun. Murmushi kawai
156
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
yayi ya kaďa kai don ya san kwanan
zancen ya karanto hakan ne a fuskar
Muneeban duk da kokari da ya lura take
yi na saisaita yanayinta.
Babu inda ba su je ba a gidajenmu
'yan uwa har gidan Diddi sun je tana ta
yi wa Mujeeb tsiyar wai sai dai ya tafi da
ita ya bar Muneeba in kuwa ba haka ba
zata sake shi don zai tafi mata wata Kasa
da igigoyin aurenta akayi ta barkwanci
ana raha. Da za su tafi ta yi ta musu fatan
alheri na Allah ya kaisu lafiya ya dawo
da su lafiya yasa ayi nasara akan abinda
ake nema.
Sun je gidan Adda zuwa a gidan
Adda Fadima ne Muneeba tafi sakewa
saboda yadda suke dasawa anan ma taci
abincin rana a kwano daya ita da mijinta
Adda tana ta yi musu tsiyar wannan
soyayya tasu da basa jin kunyar nunawa
a gabanta don sun maida ta abokiyar
wasansu.
157
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Nan suka Sallaci azahar sannan suka
wuce gidan Goggo Hinde. Itama ta dinga
ina taka saka ina ta ka aje da su ta cika
gabansu da cima iri iri dolensu suka ci don
in ba haka ba sai sun sha fadanta akan ta
basu abu basu ci ba.
Ba su suka baro Dukku ba sai
yamma Likis haka suka shigo gida a gajiye
tubus Muneeba wanka da Salloli kawai ta
iya yi don ko abinci ba ta nema ba
kasancewar cikinta a cike ya ke ta ta zo ta
yi kwance dai dai a tsakiyar falonta tana
shan iskar A.C. tana kallon tauraron dan
Adam sanin ranar ba ita ke da miji ba balle
ta je ta mammatsa masa jikinsa kuma ta
san kwarai abin da yake bukata kenan a
lokacin saboda irin gajiyar da suka kwaso
a Dukku wajen yawon zaga dangi.
Mujeeb ya dade kwance cikin gajiya
yana ta juyi ga wata uwar yunwa da ke
kwakular cikinsa amma shiru ba Suwaiba
babu dalilin ta duk da yana tsananin
kyamar cin girkinta a dalilin abin da ya ji
158
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
ta taba bashi ya ci bai sani ba, amma ko
dai fura ce ai idan ta bashi zai iya sha. Ya
yi ta kiran layinta da kyar ta daga ya ce,
"Wai baki san mun dawo ba ne da ba
ząki iya zuwa yi min sannu da dawowa
ba".
Ta yatsina fuska tamkar yana
ganinta ta ce "Au kun dawo? Ai ban sani
ba ko da yake ko na san kun dawo me
zanyi maka tunda baka cin abinci na ba
ka hada jiki da ni ban san dalili ba ai gara
nima inyi nesa da kai tunda kusancinmu
zai iya sa ni in sa rai ga abin da ba zan
samu ba.
Na yafe ka nemo matar so ta ciyar
da kai babu matsala kaga gobe sai ku
dora daga inda kuka tsaya yau tana
gama fadin haka ta kashe wayarta ya yi
shiru a kwance yana nazarin
maganganunta, daga bisani ya latso
wayar Muneeba tana daga kwance ta
amsa kiran nasa "Matar so ki taso ki zo
159
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
ki bani abinci kafin yunwa ta yimin
lahani.
Ta ce "Don girman Allah kada ka
Kara kirana da wannan sunan don yin
hakan zai haifar maka da husuma a cikin
gida ko ni ai bana kiranka da abokin
rayuwa sai in muna mu biyu",.
Ni ma ba ni na sa miki sunan ba
yanzu na kira kanwarki ta bani abinci
shine ta ce ba zata zo ba ta yafe maki ni
inje matar so ta bani, wai an yafe ni kamar
wani kaya'.
Ta ce, to In kinshinta yasa ta ce haka
kai kuma sai ka biye mata? Don Allah
tashi ka je ka lallaso ta ka san mace idan ta
butsare sai da lallashi.
Ya ja tsaki "Au kin goyi bayanta
kenan? Yanzu tsakani da Allah yadda na
kwaso gajiyar nan ai inso samu ne a cika
ruwa mai zafi a Baf a sakani a gargasa
mini jiki na sannan ayi min wanka idan na
fito kuma a shafe ni da man zafi a bani
abinci da dumi inci sannan a kwantar dani
160
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
ana min matsar jiki har in yi bacci amma
an barni nan bisa kafet ina, ta juyi cikin
yunwa da tsamin jiki tamkar mara
galihu"
To ni yanzu ya kakel so inyils Yı ua
dai ka san ba duty/nasbaneoindanawæ nemmok
duk wadannan abubuwadakaslissafduk
dare su nake maka ko kosookakesin stigaas
hurumin da banawasbal Ydrjesajiyar r 1sd
ki tausayamin ki zo ki baniabindazancimsb
wallahi ita ta ce ta yafe miki ke ki żo kiaret
ba ni.
Yanzu kai ba ka san gatse ba In ma
gatse ta yi ni ina ruwa na zan zauna da
yunwa ne alhalin duk kuna gidan. Kinga
don Allah damo min furar da muka zo da
ita ki dan gaso min irin gashin naman
nan mai romo romo da kike min"
Та се "Hum ai bakinka ne romoromon ya yi dariya 'ke ma ai bakinki da
romo-romon". Ta katse wayar tunda ta
lura ya koma fagen zolaya.
161
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Dolente ta ta shiga kicin Allah yasa
firizarta a kashe ta ke hakan yasa bata sha
wahala ba wajen ciro nama ta yanka shi
yadda take yi ta sa a farantin gashi tare da
su magi albasa da kayan ya ji ta gama hada
komai sannan ta soma gasawaub se
Ta koma ta dauko furar ta dama
masa da wadataocen Yougurt mai sanyi
har dayar ayaba kadan ta saka a wajen
damun furar ta juye a Jug ta dora a faranti
tare da kofi ta jira har sai da naman ya
gasu sannan ta dibar masa nasa ta zuba
sauran a wani filet din don ta kaiwa
Goggo.
Tana kai masa yayi saurin tashi daga
kwancen da yake yana cewa sannu matar
so Allah ya yi miki albarka ya kara min
sonki a zuciyata" Ta dan Harare shi ta ce
"Yanzu don girman Allah