sai nan gaba amma da bincike
za'a yi akan wannan abin da ya faru na san
tana da hannu dumu dumu kana bin da ya
same shi Allah kadai ya san me ya ji ta na
26
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Kafin su tafi sai da ta tsaya akansa
tayi masa addu'o'i ta tofa masa sannan
suka tafi da suka koma gida a tsaye a
tsakiyar falo suka iske Inna Amina tana
ganinsu ta sauke ajiyar zuciyar tace,
Haba Muneeba kunje kunyi dare ina nan
hankali na a tashe tunda kin san Idi ya
tafi babu mai zuwa dauko ku ai da sai ku
dawo da wuri ya mai jikin?.
Ta sabule hijjabin kanta tana cewa
Jiki sai godiyar Allah amma gaskiya
yana jin jiki don baima san wanda ke
kansa ba balle shi ma ya san a inda yake
bashi da Maraba da matacce illa ta
hanyar numfashi wanda sai ka yi
tsananin lura ne zaka gane yana
numfashin.
Inna Amina cikin tashin hankali ta
ce? Wane irin ciwo ke damunsa.
"A dakin matarsa abin ya same shi
a cewarta wai ita ma faduwarsa ta ji ta
fito kinga dai ya sami karaya a hannun
hagu, gefen damansa kuma baya aiki ya
25
WATA KLUSAN Rahmatu Hassan Zaria
sami (Stroke) sai Zuciyarsa da ita ma ta
sami matsala a cewar likitan wani abu ne
ya firgita zuciyar tasa Allah ma ya sa bata
gefen hagun ya sami mutuwar rabin jikin
ba da shi kenan zai iya kamowa da
matsanancin ciwon zuciya in ma ya zo da
karar da kwana bugawa kawai zata yi sai
dai aga gawar mutum a rasa meye sanadin
mutuwarsa.
Inna ta dau salati ta dire tana nanata
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un
Allahumma ajurni fi musibati wa aklifni
hairan minha wannan wane irin iftila'i ne
ya fadawa rayuwar yaron nan? Allah ka
kawo masa agajinka ka bashi lafiya ka
tashi kafadarsa.
Wannan Suwaiban ta zame wa
mutane jafa'i su kam ko za su gane
makircinta sai n gaba amma da bincike
za'a yi akan wannan abin da ya faru na san
tana da hannu dumu dumu kana bin da ya
same shi Allah kadai ya san me ya ji ta na
26
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
addu'o'in da kike masa don na lura idan
kina kusa da shi kina tofa masa addu'o'i
har alamu yake tamkar zai bude ido
kinga kuwa kusancinki da shi ai yana da
amfani data matsa ta fara yi masa addu'ar
Suwaiba ke barin gurin don ta san'da ita
Isah ke yada maganganunsa tunda dama
basu cika shiri ba akan Muneeba.
An kwashe sati guda cur da kawo
Mujeeb asibitin amma babu wani sauyi
daga yadda aka kawo shi a hakan ne yan
uwa na Dukku suka yanke shawarar ko
za'a hada da amso masa rubutu ne sai dai
kuma babu yanda zai sha rubutun tunda
babu abin da yake sha sai karin ruwa
shine aka dukufa da addu'o'i aka sa
Malamai na yin sauka duk kwana uku
kuma ana yin sadakoki duk don Allah ya
saukar da warakar sa Akan ciwon na
Mujeeb.
Muneeba ma ta shirya don zuwa
Dukku dubo Innarsu da Mustafa yace ya
baro tana zazzabi da Mura, sannan tana
29
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
son ganin ainihin Malamin Islamiyarsu na
Dukkun don ya bata wasu muhimman
addu'o'i na samun waraka daga tsananin
cuta da za ta cigaba da yiwa Mujinta.
Tunda ta isa gidansu ta ga jikin
Innar da sauki sai hankalinta ya kwanta ta
hau gyaran dakin Innan ta share ko ta
goge ko ina yayi fes sai ga Murja ta shigo
ta tsaya tana kallonta cike da mamaki ta ce
Bakin Gombe saukar yaushe ina can babu
wanda yace kunzo? Ta ce ban wani dade
da isowa ba na zo duba jikin Inna ne "yaya
Mustafa yace tana fama da mura.
Ta ce jiki kam yau Alhamdulillah ya
na ki mai jikin? Ta rausayar da kai gefe
cike da damuwa tace Jiki sai godiyar Allah
amma yadda kika ganshi wallahi har yau
haka yake al'amarin ya fara bani tsoro
amma dai muna nan muna masa addu'a
Allah ya kawo mana agaji ni kaina yanzu
na fi bada amanna a tafi (Cairo) din tunda
kasa ce ta Musulmai na tabbatar
maganinsu har da addu'o'I suke hadawa
30
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
sannan ga kwarewa Insha Allahu muna
saran za'a dace".
C
"To Allah yasa a dace amma
gaskiya ciwon nasa akwai ban tsoro
mutum a kwance ba rai ba alamar rai,
lallai idan baka mutu ba Allah bai gama
nuna maka ikonsa ba”.
Muneeba taso kwana a Dukku
amma yanayin data baro Mujeeb ya sa ta
ji ba za ta iya kwana ba innarsu ce ma ta
dan karfafa mata komawa a ranar tunda
ta baro majinyaci.
Tana rike da hannun diyar Murjan
suka fito daga gidansu suna tafiya da
kafa ba'a mota ba zuwa tsohuwar
islamiyyar da ta yi don ganawa da
malaminsu da yake ba lokacin Islamiyar
bane a zaune ta ganshi a bakin wani aji
yana nazarin wani littafi na addini taya
masa sallama ya dago idanu yana
dubanta tare da amsa sallamarta sannan
yace A'ah Hajiya Muneeba saukar
yaushe a garin namu? Dazun na zo, na
31
2
1
WATA KUSAN 3 Rahimatu Hassan Zaria
taho duba innarmu ne bata jin dadi yace
"Assha! Assha!! Allah ya bata lafiya ya me
gidan naki da jiki ance baya lafiya kamar
yana asibiti kwance ko?.
Ta gyada kai, "Eh yana can kwance
matsalar tashi ce ma tasa nace bari in zo
gurinka kafin in koma anjima wallahi
Malam yana jin jiki don baima san a ina
yake ba yadda aka kaishi har yanzun haka
yake a kwance magashiyan muma muna
masa addu'ar ba dare ba rana yanzu so
nake ka taimakamin da wasu addu'o'i da
zan dinga yi masa na wanda ke kwance
cikin mawuyacin hali". Malam Dauda ya
jinjina kai “Subhanallahi ashe ciwon nasa
ya yi tsanani haka? Ta сe "Eh" Malam ya
sami karaya a hannunsa na hagu sannan
gefensa na dama bai aiki ga zuciyarsa
itama sunce ta sami matsala abin dai sai
addu'a.
Malam Dauda ya shiga jajantawa
Muneeba wannan abu da ya same ta
sannan ya kara da cewa Akwai addu'o'i
32
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
nagartattatu da zan baki daga Manzon
Allah (SAW) suka zo ingantattatu ne ki je ki yi ta masa Insha Allahu za'a sami
waraka"
Ya bude wata jaka dake gefen sa
ya fito da littafin rubutu da biro ya rubuta
mata addu'o'in sannan ya yi mata karin bayanin yadda zata yi kuma za ki iya karanta masa Fatiha kafa Bakwai a ruwa
ko zamzam ki bashi ya sha in ba zai iya
sha ba sai ki dinga karantawa kina tofa
masa sannan ga wani sirri na wadanda
suka sami mutuwar rabin jiki ki sami
man zaitun asalin mai kyau na gwangwani idan kika buďe sai ki karanta Bismillah kafa dari (100x) sai fatiha kafa Bakwai ki tofa a man zaitun din ki girgiza sai ki dinga shafa masa a inda baya aikin zama ki iya shafa masa a duka jikin Insha Allahu ga6bansa za su yi aiki
su koma tamkar basu taba samun matsala ba.
33
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Wannan sirri kasidin ne an gwada an
ga nasara don ko da tafiya ce mutum ba ya
yi to zai mike yayi tafiya da izinin Allah.
Muneeba ta yi masa godiya mai tarin yawa
ta bude Jakarta ta ciro 'yan dubu dubu
guda biyar ta mikawa Malam Dauda "Ga
wannan Malam a sayawa yara Biskit a ce
ina gaishe su ya girgiza kai A'a Hajiya
Muneeba kada muyi haka dake ni ba zan
karbi ko sisin kiba abin da nayi miki na yi
ne domin Allah.
Ta сe Haba malam wallahi ba don
abinda ka yi mini bane, kaima ka sani ko
baka yi mini komai ba akwai ihsani a
tsakaninmu nima na baka ne domin Allah
kuma ina rokonka don girman Allah ka
amsa yara za ka saiwa wani abu".
Jin ta hada shi da girman Allah yasa
ya amshi kudin tare da yi mata godiya
itama tayi masa godiya suka yi ban kwana.
A hanyarsu ta dawowa ne ta ji ana
mata sallama a bayanta tun kafin ta waiga
34
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
ta fara tunanin a inda ta san me wannan
murya da ke mata sallama.
Ta waiga don ganin ko waye,
tsayawa ta yi kawai tana masa kallon na
manta inda na san fuskarka ya dan gyara
tsayuwarsa fuskarsa cike da murmushis
ya ce, "Malama Muneeba ba dai har kin
manta fuskata ba don na ga kina mata
kallon mantuwa?.
Eh na so in san fuskarka amma na
manta inda na sanka, ka yi hakuri ka san
dai ni matar aure ce bai dace ka tare ni a
titi kana min magana ba".
"Haba Muneeba na fa sami labarin
auren ya mutu tuntuni ba dai kyason
sauraro na ne ni Badaru dan gidan Mai
Gari na san kila baki gane ni nidin bane,
wallahi saboda sonki na kasa zama da
matar da aka aura min na sake ta duk
wannan susucewar da na yi domin ki ne
ki yi hakuri Muneeba ki tausayamin
wallahi ni masoyinki ne na hakika. Ta
soma tafiya tare da yi masa kashedi "Don
35
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Girman Allah ka daina bina, wallahi
aurena bai mutu ba karya ake maka gara
ma tun wuri ka je ku sasanta da matarka ku
maida aurenku", ya sake rufa mata baya
cikin magiya wai ta saurareshi yana da
batutuwa masu muhimmanci.
Sassarfa ta soma yi tamkar za su
tashi sama ita da diyar Mustafa ganin
hankulan mutane ya soma dawowa kansu
yasa ta yi saurin aukawa gidan iyayen wata
kawarta babu shirin yin haka.
Allah yasa babu kowa a tsakar gidan
hakan ne ya bata damar daidaita yanayinta
sannan tayi sallamata shiga dakin suka
gaisa ta tambaya ta jikin Mujeebu ta ce
"Jiki mun gode Allah nima nazo duba Inna
ne bata ji dadi ba anjima zan koma: Ayya
ki gaishe ta zanzo in duba ta".
Muneeba ta fito ta suri buta shiga
kewaye ta wanko fuskarta sannan ta fito
sai da ta tabbatar kila yanzu ya hakura ya
tafi sannan ne ta yi niyyar barin gidan.
36
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
A zaune ta dan labe tana lekensa ta
hujin kyauren gidan ta tabbatar bata
hange shi ba sannan ta fito suka tafi can a
kofar gidansu ta hange shi zaune abin ya dada bata haushi da mamaki shin wannan
wane irin mutum ne, ko ma tace jahili
tunda ta gaya masa aurenta na nan a
kanta bai mutu ba to me yake so tayi
masa? Koko so yake taci amanar
aurenta?
Tamke fuskarta tayi tamau tayi
fuskar shanu tana jinshi yana kwarara
mata wani mahaukacin kira irin na
mafarauta ta shige gida ta barshi nan tana
shiga dakin Innarsu kuka ta saka saboda
bakin ciki wannan abu da ke faruwa da
ita na kiranta bazawara da jama'a ke yi alhalin tana da aurenta.
Hankalin innarsu ya tashi tana tambayarta me ya faru kin fita lafiyar
Allah kin dawo da kuka? Tasa gefen hijjabinta ta goge hawayen da ke sauka a
kuncinta "Ni wallahi Inna na gaji da
37
i
1
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
yadda jama'a ke min kallon Bazawara
alhalin da aure na kullum na fita sai an
kawo mini harin zawarci kawai don ana
ganin ina zaune a gida, na yadda zanyi
abin ya fara isa ta ina neman mafita".
Inna ta tashi zaune ta ce, "Ki
kwantar da hankalinki wannan matsalar ta
aurenku Insha allahu zata zo karshe tunda
muna nan muna adduah kullum muna
kaiwa Allah kukanmu kuma muna bashi
zabi in cigaba da zaman aurenku alheri ne
to Allah ya daidaita ku koma da zamanku
idan babu alheri to Allah ya yi muku zabi
na alheri, mu dai yanzu fatanmu Allah ya
bashi lafiya a sannan ne za'a san abinyi ke
yanzu abin da zaki sa a gabanki shine
jinyar mijinki kuma kiyi tsakaninki da
Allah kada ki duba komai kuma babu
ruwanki da hantarar kowa tunda ba domin
wani kike yi ba sai domin Allah.
Abu na karshe shine ki ci gaba da
rikon amanar aurenki kada kiga don
mijinki ya jingine aurenku kema ki jingine
38
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
auren shaidan ya shammaci zuciyarki
kici amanar aureki duk da dai na san kin a
tarbiyantu da irin tarbiyyar da muka baki i
ki cigaba da yin hakuri da juriya akan a
dukkan abinda zai riski rayuwanki 2
kyakkyawa ko mummuna Allah yayi..
miki albarka ya baki abinda miki albarka i
ya baki abinda kike nema duniya da i
lahira.
1
Dadin wannan addu'a ta Innar ta,
sai ya mantar da ita kuncin da ya
mamaye zuciyarta ta saki ranta ta tashi ta
cigaba da shirinta na komawa Gombe
Muneeba na isa Gimbe ba ta zarce gida
ba, kai tsaye asibiti ta wuce don duba
yadda jikin Mujeeb ya kasance a yinin
ranar yadda ta tafi ta barshi haka ta dawo
ta same shi Suwaiba ce ke zaune a
gefensa tana ba diyarta Nono da kyar ta
amsa sallamar Muneeba da yake dakin
babu kowa sai ita.
Muneeban ce ta fara gaishe ta tare
da tambayar yadda mai jiki ya wuni yau
39
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
ta mika hannu zata dauki Waleeda
Suwaiban ta manne yarinyar da jikinta tace
Barta kawai Nono take sha ai waleeda ba
irin Baffa ba ce.
Muneeba tayi shiru tana luguiguita
maganar Suwaiba waleeda ba irin Baffa
bace to me hakan ke nufi? Watsar da
wannan kokwanton Da zuciyarta ke yi ta yi
ta fuskanci abin da ke gabanta, ta matsa
daidai fuskar Mujeeb ta soma karanto
addu'o'i da Malam Dauda ya bata, tana
tofa masa.
Isah ne yayi sallama ya turo kofar
dakin yana yin arba da Muneeba ya
yalwata fara'ar da ke fuskarsa ya nufeta
yana cewa Anti na ashe kin dawo dama
ina ta sauri in je in dawo don bana son
tafiya in barshi in ba ke bace a gurin ko
Goggo saboda ina tsoron kada a sake jefa
shi cikin wani mawuyacin halin fiye da
wannan da yake ciki.
Suwaiba ta fuskanci da ita Isah yake
yi wannan harbin Iskan a dalilin tunda
40
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
akace mujeeb a dakinta ya fadi shi kenan
kowa ya dau alhakin abinda ya same shi
aka dora mata sannan gashi likita yace lallai wani abu kunnuwansa suka ji na tashin hankali shine musababbabin
faduwarsa tunda gashi abin ya shafi lafiyar zuciyarsa to ita kam ta gaji fitittike masu zata yi ta yakice zargin da
suke mata.
Ta kalle shi a kaikace tana yatsina
tace, "Wannan fa gugar zanan da kake
mini ya isa haka, Isah, gara tun wuri ka
nemi wadda ta ke neman nakasa maka
dan uwa ba niba da yake zaune da ni
tunda bai kore ni ba a gidansa ba balle
inje in yi asirin da zan nakasa shi ko in
hana shi zama da kowa sai ni wannan
zargin naka ka ciccibe shi ka dora can ya dace ba a kaina ba ehe!.
Muneeba ta gano sarai ita Suwaiba
ke nufi tayi asirin da ya nakasa Mujeeb,
sai bata nuna mata damuwanta ba tunda
tasan inda me son Mujeeb a duniyar nan
41
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
bayan ita ce in aka cire Goggo kowa ya
san haka duniya ma ta tabbatar da haka.
Hakuri ta shiga basu ita Isah haba don
Allah muna da mai jinya kamar wannan ai
bai kamata ku tsaya kuna tanki in tanka ba
abin da ke gabanmu shine yi masa addu'a
ba muzo kansa muna sa'insa ba, don
gurman Allah kuyi hakuri.
Ta tsaida idanunta a kan Isa tana
tambayarsa 'yau Goggo ba ta zo ba ne?
"Eh yau bata zo ba itama jikin ne ya dan
motsa mata tace bata jin dadi sai gobe".
Washe gari Muneeba da wuri tayo
sammakon zuwa asibitin a dalilin wani
mummunan mafarki da ta yi da Mujeeb
din wasu mata masu bakaken Kaya sun
rufe fuskarsu suka zo suka same shi a
asibitin shi kaďai a dakin Isa ya fita suka
sa filo suka danne fuskar shi ya yi ta mutsu
mutsu sai gata ta shigo dakin ta gansu
shine suka kyaleshi a dalilin ta kwala ihu
suka banke ta suka fita da gudu bata gane
ko suwaye ba tana dubawa ta ga bai mutu
42
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zari
ba amma ya sha tsananin wahala kila ca bata shigo a lokacin da sun kashe shi shine fa da ta farka hankalinta ya gaza kwanciya tayo sammakon zuwa asibitie
dan ta ganshi ta tabatar abinda ta gani 1. mafarki bai same shi ba. i
Tana Isah ta fito da rowai
Zamzam din da ta zo da shi ta zuba a koa
tayi addu'o'i ta tofa a ciki sannan t
dunga diba a hannu ta tana shafa masa
fuskarsa zuwa jikinsa Isah ma yana tayı
ta.
Aka yi sallama aka shigo dakii
suka amsa sallamar Ogan Mujeeb din n
na Ofis tare da ‘yan rakiyarsa wasu daga
cikin abokan aikin Mujeeb din Muneeba
ta gaishe su cikin gimamawa kasancewa:
ta riga ta san Ogan da wasu mutum biyu.
Wannan shine zuwan Ogan nasa
na uku duba shi ya dubi Muneeb yana
tambayarta Madam wane cigaba ake
samu ne? ni naga har yau kamar babu
wani canji? Ta dubi Mujeeb din
43
WATA KUSAN 3
Rahmatu Hassan Zaria
"Gaskiya babu wani canji amma muna nan
muna addu'a Insha Allah muna sa ran
ganin canji.
Ya matsa sosai ya kura wa Mujeeb
din idanu tamkar yana wani nazari a kansa
Addu'ar da muke masa ma tana da
muhimmanci amma duk da hakan ina
ganin zan fitar dashi wani asibiti a Jamus
suna da kwarewa akan irin wannan ciwon
nasa ina ganin daga yau zan fara magana
da wani abokina a can Jamus din zamu
shirya yadda tafiyar zata kasance ina
ganin za'a yi muku Passport da Biza ke da
shi zaku tafi sai shi abokin nawa ya
jagoranci komai a can ko kuwa kuna da
wata shawarar.
Muneeba ta dan sunkuyar da kanta
cike da girmamawa ta ce, "Eh to akwai
wani mijin innarmu anan Gombe da yake
sunyi magana da yayanmu cewa zasu fita
dashi wano asibiti a (Cairo) har ma an fara
shirye shiryen to amma sai Goggo ta ce
ayi hakuri abarshi anan din muga abinda
44
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
da ingantattun kayan aiki sabanin namu
na kasar akwai da yawa wadanda aka kaisu masu matsala irin tashi da kafarsu
suke dawowa tangarau sabanin yadda
suke tafiya magashiyan to shima muna
fatan ya dawo da kafafunsa Insha Allah.
Gaba daya dakin suka amsa Allah
ya sa, Allah ya sa, Goggo tayi magana to Alhaji mun gode Allah ya saka da alheri
sai dai wani hanzari ba gudu ba mu bamu
da makudan kudin da za'a fitar don
kaishi wata kasa in ma akwai su to shine
mai Su, to shi kuma ga yanda Allah yayi
dashi balle ya fiddo su a kaishi wata kasa
kaga yanzu idan aka ce sai an kai ai za'a
shiga wani hali gara dai a barshi anan din.
Alhaji Ayuba yayi murmushi
'Babu komai Goggo nine zan dauki
uyin tofiyar da komai da za'a yi ku
ddane zaku biyo bayansa da shi.
Ai Mu zan iya kashe ko nawa ne a
kansa saboda yaro ne haziki mai
47
a
i
a
e
1.
i
i
a
Ο
1,
a
e
a
a
n
e
ג
2
i
C
i
WATA KUSAN 3
Rahmatu Hassan Zaria
kwakwalwa ga jarumtaka akan aikinsa
sannan ga ladabi da biyayya ya sami
tarbiyayya kyakkyawa daga gare ku nima
shuyasraokanta masa da abinda yayi
mani kuma zanyi haka ne domin neman
Lada a gurin Allah.
Goggo ia cigaba da sanya ma Alhaji
Ayuba albarka tare da godiya akan irin
dawaniyar da yake da aljihunsa akan
wannan ciwo na Mujeeb babu gazawa ga
sintiri da nyake yi shi da iyalansa.
Da za su tafi ya dauko rafar yan dari
biyar-biyar na dubu Hamsin ya mikawa
Muneeba ya ce, ga wannan ku rike ko da
zasu nemi wani abu "uneeba tasa hannu
biyu ta amsa tare da yi masa godiya
Goggo ma godiyar take masa "Haba Alhaji
baka gajiya da dawaniya ko da yaushe ka
zo sai ka yi hidima to Allah ya shi albarka
Allah ya baka masu yi maka kaima ya
amsa da Ameen! Ameen.
Suna fita Muneeba ta mikawa
Goggo kudin nan Goggo tace "Me zan
48
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
da ingantattun kayan aiki sabanin namu
na kasar akwai da yawa wadanda aka kaisu masu matsala irin tashi da kafarsu suke dawowa tangarau sabanin yadda suke tafiya magashiyan to shima muna fatan ya dawo da kafafunsa Insha Allah. Gaba daya dakin suka amsa Allah ya sa, Allah ya sa, Goggo tayi magana to Alhaji mun gode Allah ya saka da alheri sai dai wani hanzari ba gudu ba mu bamu da makudan kudin da za'a fitar don kaishi wata kasa in ma akwai su to shine mai Su, to shi kuma ga yanda Allah yayi dashi balle ya fiddo su a kaishi wata Kasa kaga yanzu idan aka ce sai an kai ai za'a shiga wani hali gara dai a barshi anan din.
Alhaji Ayuba yayi murmushi "Babu komai Goggo nine zan dauki nauyin tafiyar da komai da za'a yi ku
naku addu'ane zaku biyo bayansa da shi.
Ai Mujeebu zan iya kashe ko nawa ne a
kansa saboda yaro ne haziki mai
47
3
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
kwakwalwa ga jarumtaka akan aikinsa
sannan ga ladabi da biyayya ya sami
tarbiyayya kyakkyawa daga gare ku nima
shi yasa zan sakanta masa da abinda yayi
mani kuma zanyi haka ne domin neman
Lada a gurin Allah.
Goggo ta cigaba da sanya ma Alhaji
Ayuba albarka tare da godiya akan irin
dawaniyar da yake da aljihunsa akan
wannan ciwo na Mujeeb babu gazawa ga
sintiri da nyake yi shi da iyalansa.
Da za su tafi ya dauko rafar yan dari
biyar-biyar na dubu Hamsin ya mikawa
Muneeba ya ce, ga wannan ku rike ko da
zasu nemi wani abu "Muneeba tasa hannu
biyu ta amsa tare da yi masa godiya
Goggo ma godiyar take masa "Haba Alhaji
baka gajiya da dawaniya ko da yaushe ka
zo sai ka yi hidima to Allah ya shi albarka
Allah ya baka masu yi maka kaima ya
erise da Ameen! Ameen.
Suna fita Muneeba ta mikawa
Goggo kudin nan Goggo tace "Me zan
48
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
amsa in yi da su? Ki rikesu a hannunki
duk abin da aka nema sai ayi da su".
a Ran Suwaiba bai so a bar kudin
hannun Muneeba ba saboda a ganinta ba
ita.ya dace a dinga barwa komai ba, ita Suwaiban ce tafi cancanta tunda
Muneeba ba'a gidansa take ba zuwa
jinya take ta koma.
Tun daga lokacin ta dinga cika
tana botsara ganin haka yasa Isah da
Muneeba suka fita sabgar ta suka
fuskanci kula da majinyacisu don ranar
wuni suka yi shafa masa Zamzam mai
Addu'a da man Zaitun suna dan
mutstsuka masa jikin a hankali
Da wuri Suwaiba ta hada Inata
inata tace zata tafi gida a lokacin ne take
cewa Goggo wai abata wani abu cikin
kudin da aka bayar zata sayawa Waleeda
Pampers da magungunanta na mura ita
ma za ta je asibiti ganin likita.
Goggo ta ce "TO ai ga Isah nan shi
za ki tambaya shine me baki duk abun
49
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
da kike bukata ni kudi ai basa hannuna" Ta
juya ta harari keyar Isa da ke tsaye gaban
gadon Mujeebun, sai da ta gama hararar
bayansa sannan ta yi magana "Ina da
bukatar kudin da zanyi wa Waleeda
Hidima nima zani ganin likita shima sai da
ya ja lokaci kafin ya tanka mata ki kawo
list din abubuwan da za'a sayanma
Walidan kema idan kinje asibitin ki kawo
takardar maganin ni zan sayo don ba zai
yiwu inyi ta diban kudi ina baki kina
hidima ba, dubu goma na baki rannan ai
basu isah sun kare ba ba zai yiwu in yi ta
kadawa kogi bula da tunda asara ne yin
hakan.
Ta tunzura da kalamansa zuciyarta
ta kawo mata iya wuya kudi fa dole ka
bani tunda ba naka bane na miji na ne, dole
in amsa in yi wa yarsa hidima don ita kadai
ke gareshi a duniyar nan Inni an ce bani
kadai bace”.
Shima Isah ya maida mata martini,
Eh munji Waleeda kadai ke gare shi nima
50
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
nan ni kadai ke gare shi balle kuma
Goggo da ba shi da kamarta kuma zai
taba samun kamarta Waleeda kuwa muna
sa ran Aunty Muneeba za ta haife ire
irenta harma da mafiyanta Insha Allahu.
A nan ne Goggo ta tsawatar musu "Kai
Isah ya isa haka ka kyaleta dole ta ci
darajar yayanka ta juya gun Suwaiba
"Ke kuma ai banga laifin abinda yace ba,
ki rubuto duk abinda kuke bukata a sayo
muku tunda dai a gidan nan babu abinda
babu a Sito hatta da Ashana katan muke
da ita to me ake nema, sannan shi
Pampers din inace an sayamma manya
manya ko kyautarwa kika yi? Yanzu ma
ai ya kamata a rage yin wasu hidindimum
tunda mai bayarwan gashi nan a kwance
in kuma ba dan abin da ya tara ba za mu
taru mu cinye ba.
Jin Goggo ba ta goyi bayan a bata
kudi ba ya sa tai zumbura baki ta suri
Jakarta ta fice fauww daga dakin ko
sallama ba ta yi musu ba. Muneeba dai
51
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
T
ハ
na zaune gaban mijinta ta na kallon ikon
Allah Isah ya dubi Goggo kin gani ko
Goggo wallahi duk iskancin da yarinyar
nan ke yi don ta sami daurin gindi daga
gurinki ne, gashi nan ke ma bata barki ba
balle Yaya Mujeeb da ta mayar tamkar
sa'anta ni wallahi zan yi mata saiti ne
Goggo da kwafa kawai ta ke yi ta na
girgiza kai saboda takaici.
Washe gari Muneeba ke cewa Isah
Gaskiya yau zan yi wa Yaya Mujeeb
wanka da Tawul da Ruwa dubi fa yanzu
kwanansa kusan goma sau biyu suka goge
masa jiki ka je ka tambayo likitansa idan
babu matsala sai mu goge masa ni tsoro
ma nake ji kada bayansa ya sabule saboda
kwanciya.
"Ni ma na yi tunanin haka amma
bari zan tambayi likitan in akwai wani abu
da za'a dinga sa masa a bayan nasa saboda
kwanciyar". Isah yaje ya shaidawa likita
kudirinsa likitan ya basu izini tare da gaya
masu yanda za su yi masa, in kuma ba za
52
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
su iya ba ya sa Nosis maza su yi masa
Isah ya ce za su iya.
Ruwa mai dumi suka debo a hitar
bayin dakin Muneeba ta zuba detol da
rowan sabulun wanka a rowan ta umurci
Isah ya rufe kofar dakin sannan suka fara
goge masa jikin na sa amma suna yi da
taka tsan tsan saboda hannunsa mai
filasta.
Dukan kofa suka ji ana yi
Muneeba tace Isah ya je ya ji kowaye
amma kada ya bude yace a jirasu
Suwaiba ce ke bugun kofar ya ce ta jira
suna goge masa jiki yanzu za su gama,
yana jin wani uban tsaki da ta ja tare da fadin "Kan Uba ni ba matarsa bace da za
ka ce in jira a waje, lallai ma gayen nan wallahi ka rainani amma zan yi maganin
wulakancinka yana jin surutanta yayi
tamkar bai ji ta ba ya koma abinsa.
Sun gama gyara shi tsaf sannan
Isah ya je ya bude kofar amma sai baiga
suwaiban ba. Da 'yan Harare-harare
53
1
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Suwaiban ta