ba za ka daina
ba? Ya ce ya za ayi in daina ni ma ai irin
naki zan yi sai muna mu biyu zan dinga
gaya miki sunan. In kuma kika dame ni in
dinga fadan gaban kowa.
162
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Ta juya zata fita ta na masa sai da
safe yayi magana cikin tsokana 'Ba zaki
tsaya in gama ki gasa min jikin bane ita
fa tace ta yafe maki har da kwanan". "In
baka sam gatse ba aini na sani yunwa dai
ba zan iya barinka da ita ba amma ma
gasa jiki ka yi abinka ka kwanta tunda ka
iya, saida safe".
Kafin yayi magana har ta fice ta
bar masa falon ya ja namansa da fura ya
ci ya sha yayi hani'an sannan ya je ya yi
wanka yayi kwanciyarsa.
163
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
**** **** ******
Sun isa kasar Egypt lami lafiya, sun sauka
a masaukin da abokin maigidan mujeeb
wato Alh. Ayuba ya tanadar musu wani
hotel.
Washe Gari shi mutumin ne da
kansa ya zo ya dauki Mujeeb a masukinsu
ya kaishi asibitin da zai ga likita.
Duk ya gayawa likita matsalar dake
damunsa, yadda hannun sa ke masa zugi
da nauyin da yake masa sannan matsalar ta
rashin samun kuzari a matsayinsa na da
namiji. Sai dai ba ko da yaushe bane yake
jin rashin kuzari ke dawo masa lokaci
zuwa lokaci. Ya kara da cewa,
"yadda abin ke mai in har zan dade
jikina bai rabi jikin mace ba to babu yadda
za'a yi inji sha'awar komai sannan ko jikin
namu ya hadu ba lallai bane inji wata
יי sha'awa sai dai in abin ya zo min"
Tunb daga ranar likita ya dora shi
akan shan magani, hannunsa kuma aka
164
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
saka shi cikin wata na'ura aka gyara
masa kashin sa da bai daidaitu ba, sannan
suka bashi ranakun da zai dinga zuwa
ana masa gashin hannun.
Yabawa da asibitin yasa Mijeeb
suna kwance a wani dare yake shawartar
Muneeba akan matsalarta.
"Muneeba ina ganin ya kamata gobe
muje asibitin nan da ke, mu kai musu
kukan matsalarki ko Allah zai sa a dace".
Ta yi dan jim sannan tace, Ni
kam na hakura da zuwa duk wani asibiti
in dai akan matsalar haihuwa ce tun da
babu irin maganin da ba mu yi ba na
asibitin da na gargajiya, ina ganin gara
mu hakura kada muyi ta ma Allah
shishshigi akan abin da ya tsara kila bani
da rabon haihuwa ne a duniya."
Nan da nan hawaye ya ciko a
idanunta. Mujeeb ya lura da hakan, sai ya
jata jikinsa ya rungume yana lallashinta,
ki yi hakuri mu je goben ai ba a san inda
za a dace ba tunda shi magani gwadawa
165
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
ne inda ma sunan shi ya samo asali kenan
inji bahaushe wai bari ma gwada ma gani,
kuma Atlah shi ya saukar da larura kuma
yace a nema ni magani don babu cutar da
bata da magani sai mutuwa da tsufa. Da
wannan shawarar suka kwanta ba
amma ita a ganinta da ya kyale ta kada ya
yi asarar kudinsa tunda ko a asibiti sunce
bata da matsalar komai lokaci kawai zasu
jira, to me zai sa su wahalar da kansu da ba
za su jira lokaci da Allah ya tanadar mata
ba.
Shi ba gashi nan ba da na sa lokaci
ya yi Allah ya kaddare shi da kara aure
kuma har ya sami haihuwar.
Washe gari da wuri suka shirya suka
tafi asibitin, ita bangaren likitar mata aka
kaita, wadda likitar ma mace ce 'yar kasar
Pakistan kuma musulma ce, shi yasa
Muneeba ta saki jiki ta dunga zayyane
mata matsalolinta.
166
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Anyi mata duk wasu gwaje-gwaje
masu matukar muhimmanci, sannan aka
ce su dawo gobe.
Shi ma Mujeeb din an yi masa
nasa gwaje-gwaje tunda sai da suka
nemi ganin mijinta, amma ta shaida musu
shi ba ya da matsala yana haihuwa itace
mai matsala.
Likitar ta kwantar mata da hankali
cewa ta yiwu ita ma bata da wata matsala
kila jinkiri ne kawai daga Allah lokaci na
yi zata ganta dauke da ciki, har ta bata
shawarar ta je ta ci gaba da addu'a don
addu'a na maganin matsalolin rayuwa,
bawai sai magani ba.
A washe gari da suka koma
sakamakon gwajin da aka yi wa
Muneeba ya nuna bata da matsalar rashin
haihuwa, komai nata lafiya yake, amma
zasu dora ta akan shan magunguna
saboda su karawa kwayoyin haihuwarta
karfi ta yadda zasu kyankyasar da
167
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
halittar mutum ba tare da ana yin asararsu
ba a yayin saduwar aure.
Kuma sun bata shawarar ta yawaita
Mu'amularta da Mijinta a yayin da take
shan magani, zai iya yiwuwa ta sami ciki
amma fa idan Allah ya kaddara.
A masaukinsu zama tayi tana ta
tunanin hanyar da zata sanar da Mujeeb
abin da likitarta ta bata shawara na yawan
mu'amular aure yayin shan maganinta,
gashi ya sami rauni ta wannan bangaren
yanzu yaya kenan.
Ashe faduwa ce tazo daidai da zama
shi kuma nasa magunguna masu karfi ne,
ta yadda har sun fara tasiri a jikinsa dama
likitan ya gaya masa da zarar sun fara aiki
to zai dawo daidai dinsa koma yafi da
samun karfi da kuzari.
A wannan daren ya ga tabbacin abin
da likitansa yace, don ya kasa sarrafa
kansa har sai da ya tabbatarwa da matarsa
hakan sakamakon kyakkyawar mu'amular
da suka gudanar a tsawon daren ranar.
168
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Har. sai da ya dinga bata hakuri
ganin lafiyar da ya samu har tana
barazanar yi masa yawa, koda yake
hausawa sunce komai yana ginsar mutum
amma banda lafiya.
Amma fa kafin wannan ranar sai
da yasa likita a boye ba tare da sanin
Muneeba ba yayi masa gwajin (H.I.V)
sabo da zuciyarsa ta kasa natsuwa da
nagartar lafiyarsa.
Bai sami natsuwa ba har sai da aka
tabbatar masa lafiyarsa kalau Jininsa
baya dauke da ko wace irin cuta sannan
ne fa hankalinsa ya kwanta kuma Ya
tabbatar ma Muneeba cewa lafiyarta
kalau,' Suwaiba ce kawai yake Kokwan
to akan tata lafiyar kila a tsawon shekara
gudan da yayi yana jin ya ta sake zuwa ta
aikata wata masha'ar tunda bokaye sune
abokan mu'amularta su kuma basu da
aiki sai na fasikanci da duk wata
la'ananniyar da ta kai kanta gurinsu da
169
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
sunan neman biyan bukata, za su yi miki
aiki sannan za su miki aika-aika.
Wata guda su Muneeba suka kwashe
a birninm Egypt, sun yi kyau har sun gaji
don idan ka gansu zaka dauka sababbin
amare ne da suka zo yawon amarci saboda
yanayin da suka tsinci kansu na shauki
soyayyar junan su, kansu ji suke yi tamkar
yanzu ne suka yi aure saboda nishadi da
suke ciki koda yaushe.
In ba asibiti za su je ba to basa fita
ko'ina suna nan gida manne da juna, sai
gab da zasu dawo ne ma suke fita shaguna
don sayen kayayyakin da za su yi tsaraba.
Ranar laraba da daddare suka sauka
gida Nigeria sun tarar da kowa lafiya, sai
dan abin da ba za'a rasa ba na matsalolin
cikin gidan Mujeeb na irin rashin kunyar
da Suwaiba kewa Goggo, don ma isa na
tsakanin zaman nasu kila da wata rana sai
ta mari Goggo.
Θ
170
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Σ
3
१
Tsananin gajiya yasa Muneeba ko
ina na jikinta ciwo yake mata har ta kasa
tabuka komai a washe gari sai aikin
bacci.
Mujeeb ya shigo fakinta shima
sanye yake cikin riga da wando masu
tsananin taushi na bacci, ya same ta tayi
dai dai a tsakiyar gadonta tana bacci ga
sanyin A.C da ya ratsa dakin.
Ya kalli agogon dake aje gefen
gadonta yaga sha Biyu da kwata na safe,
a tunanin sa ma ko karyawa bata yi ba.
Ya zauna a gefen gadon ya soma
bubbugata a hankali, ta bude idanunta da
suka yi jawur ta dube shi sannan tayi
kokari ta tashi zaune tana cewa," Wallahi
ko ina a jikina ciwo yake yi, har yanzu a
gajiya ta ki saki na yadda kasan an yi
mini dukan tsiya haka nake jin jikina ya
yi min nauyi.
Yace,"Ai kwanciyar ba za ta
magance miki wannan gajiyar ba, ki
daure ki tashi ki yi wanka da ruwa mai
171
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
zafi, ki ci abinci don na san baki karya ba
zaki ji dama-dama."
Ta yi mika tare da yin salati, sannan
ta sauko ta wuce bayi tayi wanka da ruwa
mai zafi sannan ta fito ta same shi a zaune
inda ta barshi.
Ya dube ta yace," Me zaki yi mana
mu karya da shi nima fa har yanzu ban
karya ba." Baka karya ba? Ina Suwaiban?"
yace, "Na tambayeta tace bata yi dani ba,
sun cinye abunsu."
Muneeba ta tsura masa ido sannan
tace "Wai don Allah laifin me kake yi wa
matar nan take butsare maka, ya kamata ka
gyara"
Ya murmusa, "To yaya muneeba
za'a gyara insha Allahu." Tayi Dariya "au
abin ma na zolaya ne? babu batun zolaya,
ni wane laifi kike ganin zanyi mata? Kin fa
san halin yarinyar nan ba sai anyi mata
laifi ba take wulakancin ta ba. ke laifin ki
ke mata take miki abin da take miki? Don
Allah ni zura riga kawai ki shiga kicin ki
172
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
sama min abinda zanci, cikina ya riga ya
horu da cin abu mai dadi bana son
Jagwalgwalo, garama ta daina bani zan
fi son haka" Muneeba tace, ka gani ko ai
daman a san da taka matsalar wallahi
gara ka gyara don nima na kusa daina
baka abincin ranar girkin ta".
Ya yi dariya," Haba yarinya ai
baki isa ba da kinga yadda ake kuka da
birgima a dakin nan har sai kin bani".
Ta dauko doguwar riga mai gyale
ta saka ta murza 'yar hoda, ta yafa gyalen
sannan ta dube shi, "Don Allah ka koma
falonka idan na gama zan kawo maka".
Ya kura mata idanu, "wai kinga farin da
kika kara kuwa? Kin kara wani irin kyau
jikinki ya yi lukui-lukui tamkar bayan
tarwada, gaskiya kasar Egypt ta amshe
ki, kina kuwa kallon madubi? Ta girgiza
kai, "Bana kalla, ni dai tashi ka tafi zan
kawo maka".
Yace, "Au korata dai ki ke yi to
bari in tafi, idan baki yi sauri ba zan
173
لم
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
dawo" hakika ita kanta Muneeba ta ji
sauye-sauye a jikinta, kasancewar bata jin
ciwon komai sai ta alakanta yanayin
sauyin jikin nata da gajiyar tafiyar da suka
yi, amma tana kokwanto akan hakan a
dalilin yau kwana goma kenan da bata ga
al'adar ta ba, sai dai ta kasa gasgata abin
da zuciyarta ke saka mata.
Ta dauko wayarta ta kira lambar
wata kawarta nos ce da ke aiki a asibiti
sister Hadiza tace," sister kina gida ne ko
asibiti ina son ganinki" tace, "Gani nan
yanzu zan fita zuwa asibiti lafiya ko?"
Tace, "lafiya kalau so nake kiyi mini
gwajin fitsari". Tana jin saukar ajiyar
zuciyar Hadiza sannan tace, "Gani nan
biyowa gida in yi miki Allah yasa muga
alheri kai na yi murna." Tace, "Ni fa ban
tabbatar bane ina dai zato ne." Tace, "Ai
wannan kyakkyawan zato ne, gani nan
zuwa yanzu-yanzu".
Mintuna kalilan suka kawo sister
Hadiza gidan, gwajin farko na fitsarin ya
174
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
nuna ciki, Muneeba tace ita fa bata yarda
ba, ta sake yi mata wani shima dai ya
nuna akwai ciki. Murna ta baibaye sister
Hadiza ta dube ta tana rike da abin
gwajin tace, " wallahi shima wannan
cikin ya nuna, meye naki na kokwanto to
abu ya nuna kansa baro-baro abu ne fa
ake nema ido rufe sai gashi Allah ya
kawo, ba sai mu godewa Allah ba mu
addu'ar Allah ya raba ku lafiya”.
Muneeba hannuwa biyyu ta daga
sama tana yi wa Allah godiya. Hadiza ta
dubeta tace, "Gaskiya wannan albishir
din ni zan yi wa mai gidan ko a bani
babban goro mai tsoka".
Muneeba tace, "ki yi hakuri
Hadiza ba yanzu za'a gaya masa ba kin
dai san komai dangane da zaman gidan
nan, bana son a san ina da cikin nan, don
idan aka san ina dashi tun bai kwari ba
komai zai iya faruwa, shi kuma yanzu
idan aka gaya masa na san ba zai iya yin
shiru ba saboda murna kowa sai ya ji."
175
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Hadiza tace, "Gaskiya kuma da
wannan don wannan wai an tura tsohon
banza biko". Yanzu gaya min irin
matsalolin da kike fuskanta a jikinki don
insan irin magungunan da zan kawo miki"
Muneeba ta yi mata bayani nauyin
jiki da kasala sai yawan bacci, sai yawan
cin abinci sau ba adadi, in ta ji yunwa ma
bata ci sai ta fara ganin dusu-dusu jiri na
dibarta, amma sam bata wani ciwo in
banda wadannan.
Hadiza ta hado mata magunguna da
zata dinga sha wadanda zasu rage mata
nauyin jiki da kasala, amma cin abinci
wannan ya zama dole saboda dan dake
cikinta ya sami koshin lafiya.
Cikin har ya shiga watanni biyu da
'yan kwanaki Mujeeb bai sani ba, sai dai
yana yawan mata korafi akan yawan
baccin da take yi wanda sam bata gajiya,
da yawan cin abincita gashi nan ta yi kiba
ta yi wani irin fari mai ban sha'awa.
176
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Abin fa ya soma ba Mujeeb
mamaki, rannan suna hira miyau ya
dinga cika mata baki yana shaketa. Ta je
ta zubar ta dawo ya dubeta yace, "ke ni fa
bangane wannan miyan ba shin wata cuta
ce ta same ki ta zubar da miyau ban sani
ba?" Tace, "To nima dai haka na tsinci
kaina kila ciwon ne".
Ya suri. makullin motarsa yace,
"Tashi mu je mu ga likita, wannan ai
babbar cuta ce a ce mutum ya kasa
(controlling) miyau a bakinsa" Asibiti
suka nufa yai wa likita bayanin
matsalarta, likitan ya kara yi mata wasu
tambayoyi daga bisani ya bata wata
kwalba yace ta shiga bayi ta yi fitsari ta
kawo masa.
Yana gwada fitsarinta ya dubi
Mujeeb yace, "Ina taya ka murna madam
na da shigar ciki wata biyu". Wasu
hawaye ne masu sanyi suka ziraro daga
idanun Mujeeb, ya mike yana Hamdala
ga Allah sannan yace, "Likita da gaske
177
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
ka tabbatar cikin ne don kada in sa rai ga
abinda ba zan samu ba? "Likita ya yi
murmushi yace, "Tabbas abin da gwajin
fitsarinta ya nuna min kenan, amma idan
kana tababa bari in yi mata (scarning) sai
kaga zahiri”.
Tare suka shiga dakin yin hoton, su
uku, likita ya yi mata hoton ya ga tabbacin
cikin sannan ya nuna masa shi ma ya gani.
Tun a dakin a gaban likita Mujeeb ya
rungume Muneeba yana murna tare da
godiya ga Allah.
Tun a asibitin ya kira wayar Goggo
ya shaida mata, ya kira mutanen Dukku ya
dinga shaida musu kowa aka gaya masa sai
yayi murnar wannan abin farin cikin.
A mota take shaida masa gwajin
sister Hadiza ta yi mata har ya nuna tana
da ciki. Ya dubeta ta baki bude yace,
"shine tun a lokacin baki gaya mini ba?
Oh, dama kin riga kin sani shine kika boye
mini? To me hakan ke nufi kenan?
178
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Ta raunana murya saboda ganin ya ji zafin rashin gaya masa din tace, "yi hakuri ka maida wukar, wallahi ni ina ta
kokwanto ne sai ina ganin kamar ba
gaske bane shi yasa na yi gum da baki
na, amma kayi hakuri tunda ya tabbata
yanzu a yafe min".
Ya murmusa tare da shafo cikin
nata yace, “Ai ni yanzu babu wani laifin
da za ki yi min in ji zafinsa saboda
wannan abin farin cikin da kika dasa
mini a zuciya wace irin kyauta kike so in
baki a duniyar nan, gaya min ko me ye
indai bai fi karfi na ba zan baki".
Ta ruko hannunsa da har yanzu
yake bisa ruwan cikinta tana shafar
hannu nasa tace, "Babban abin da nake
so yanzu a gurinka shine addu'arka gare
ni Allah ya bamu lafiya ni da abin ke ciki
na, ya sauke ni Lafiya idan ka dinga yi
mini komai a duniya".
Yace " wannan ya zama dole a
gare ni, dama addu'a kullum ina yi miki
179
1
1
1
1
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
a duk salloli naki fadi wani abun". Tace, ni
kam babu wani abu da nake so tunda duk
wani abu da mace ke so a gurin miji na ji
dadin rayuwa babu wanda ban samu ba sai
soyayya da kulawa duka na samu, to me
kuma zan nema sai dai godiya Ga Allah
kawai".
Yace, "zan ci gaba da nuna miki so
da kulawa zanyi miki gata zan sangarta ki
zan ririta ki, ke da abun da zaki Haifa
tamkar kwai a kan fa"
Haka ya yi ta gaya mata kalamai
dadadan zuciya har suka iso gida, A
harabar tsakar gidan suka iske Goggo ta
tare su da murna tana tambayan su,
"Mujeeb da gaske ne abun da ka gayamun
Muneeba na da ciki? Ya ce wallahi Goggo
da gaske ne nama ga Hoton da akai mata a
asibiti cikin watansa Biyu da kwanaki. Ya
dauko hoton Scarning din daga aljihunsa
ya mika ma Goggo ta amsa tana cewa to ni
me zan gane a hoton ba boko na iya ba,
Allah mun gode maka kaine abin godiya ta
180
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
juya ga Muneeba, sannu kinji Muneeba
Allah ya raba ku lafiya sai ki dage da cin
abinci ki kula sosai da lafiyarki".
Ita dai Muneeba sunkuyar da kai
tayi saboda kunya bata iya cewa komai
ba. Suna shiga daki Muneeba alwala ta yi
nafila ta yi godiya ga Allah da ya bata
wannan kyauta na ciki sannan tai addu'ar
Allah ya raba su lafiya”.
Shi ma Mujeeb a nasa dakin Sallan
nafila ya yi don nuna Godiyarsa ga Allah
da ya bashi wannan kyauta da ya dade
shekara da shekaru yake nema sai yanzu
da suka fid da tsammani sai gashi Allah
ya basu.
Suwaiba tunda Goggo ta gaya
mata maganar cikin Muneeba ta shige
daki, saboda wani kugin firgici da cikinta
ya dauka, har sai da ta zaga bayi saboda
rudewa da ta yi.
Ta dauko wayanta na kuka w'iiw'ii ta kira Hajiyarta ta shaida mata abun
bakin cikin da ya same ta.
181
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Haj. Harira ta dunga nanatawa,
"Muneeban da ciki? Ciki dai ciki dai anya
kinji da kyau ita din aka ce? Cikin rashin
kuka, tace ita din fa akace Goggo take
gaya mun, a lokacin suna asibiti ya kira
Goggo yake shaida mata, yanzu haka gasu
can sun dawo sai murna Goggo take yi
tamkar ba'a taba haifar mata jika ba".
Haj. Harira ta kurma ashar, kan
Ubancen Rahin din ce ke murna dan
Muneeba na da ciki lallai dole gobe ki zo
muje mu ga boka dole a zubar mana da
cikin nan dan ba zai yiwu ba ta haihu a
gidan nan dan a gidan nan da 'ya daya tilo
har yau shiru ba wani bayani".
Suwaiba ta ja tsaki, "Ai yau zamu yi
ta da shi a gidan nan, ni fa zaune kawai
nake a hoto ce min yayi bashi da lafiya,
tun kwanciyar jinyarsa na ke zaune haka
har ya warke sukai tafiya suka dawo,
yanzu zai gaya mun in a ruwa Muneeba ta
sha cikin ko kuma a yi wacce za a yi”.
3
오
182
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaría
Haj. Ta yi saurin kwabarta. "Akul
kikai masa tijaran da zai sake ki, ki bi
komai a hankali, in kika tada kayar baya
ya sake ki ay ba muci riba, ki barni da su
kowa sai ya kwashi kashinsa a hannu".
A daren ranar ta same shi a
falonsa, yana zaune da remot a hannu
yana lallatsa tashoshi yana ganin ta ya
san ba lafiya tunda ya san ba Girkin ta
bane koda yake ita babu ruwanta duk
lokacin da take da bukatan kanta zata
shigo dakinsa kuma sai ta ga dama take
sallama.
Ta zo.kansa ta tsaya kerere ta tsaya
ya na dubanta yace "Ke! Lafiyarki kalau
za ki zo kaina ki tsaya min kerere ko
ladabi tamkar sa'ar ki ko wani kanin ki?
Ta yi ya tsine, "magana nake san
yi da kai ba zama na zo yi ba. Ay nima
bace wa na yi ki zauna ba, ki matsa daga
gefe sai ki mun magana amma ba zai
yiwu ki tsaya mun akai ba".
183
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Ta ja gefe tana 'yan girgije girgijen
kafada ta soma magana dama zuwa na yi
in san matsayi na tunda ance mun
Muneeba nada ciki alhali kace baka da
lafiya kila a ruwa tasha, in kuma ba a ruwa
ta sha ba kenan ni ake zalinta an danne
mun hakkina idan nai magana ka ce bani
da hakuri ni wannan ya dama ai gashi ita
da be dama ba har ta yi ciki saboda haka
ba zan yarda ba dole ka bani Hakkina
kamar yarda kake bata ni ma ai matarka ce.
"ya yi dan murmushi sai daga can jira nake
Allah ya kawo irin wannan rana to bari ki
ji in gaya miki abin da kika san na sani
shiru kawai na yi miki, bara nayi miki
matashiya.
Ranar da na fadi a dakinki dawowa
na yi in dauki wasu takardu a dakinki da
na ajiye shine na tsinkayi maganar da kike
yi da kawarki tun farkon hiran takì inajin
irin naman da kikasa a gabanki wanda har
kikai mun miya da shi alhanin kun yi
1
3
184
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
fasikancin ku da boka kin hada janabarsa
da tawa.
Abin da kika nema lokacin kin
samu tunda kin mallakeni iya yanda kike
so, kinsa na wulakanta matata ina ci mata
zarafi har sai da na koreta a gidan.
Kin dauki alhakin mu ni da ita, dan
rashin kunya ni ban yi miki Allah ya isa
ba kullum za ki dubi tsaban idona ki ce
wai baki yafemin ba danne miki hakkin
ki da na ke yi ba.
Bari kiji in gaya miki ni ba zan
kara yarda na hada jikina da naki ba
saboda tsananin kyamarki da nake yi ga
tunani (H.I.V) dan ban aminta da
lafiyarki ba, ban sani ba ko bayan
kwanciya na rashin lafiya kin koma ki na
aikata masha'arki ba, ni ko a Egypt na sa
an auna jinina an tabbatar banda cutan
komai an tabbatar lafiyarki kalau kila in
cigaba da zama dake amma ba tabbas dan
Al'amarin yana bani tsoro, saboda haka
gobe ki shirya mu je asibiti dan bokayen
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
nan da kuke zuwa kuke basu kanku duk
suna dauke da cutan kanjamau.
Ni kam na gode ma Allah da be
Kaddara kin lika mun ba in ma kin je kin
kwaso. Saboda haka dole gobe mu je
asibiti ki san matsayinki.
Kuka ka shirban Suwaiba take yi
tunda ta ji ya ambaci cutan H.I.V dan bata
san tana jin tsoron cutar ba sai da ya bata
matashiya. Duk wata tsiwa da ta dauko
damaran kwance masa sai gashi ta tattara
abinta ta wuce sumui sumui tana kuka.
Muneeba dake dakin baccin sa tana
jin su, daskarewa ta yi a kwance cikin
dakin dan ita kanta Suwaiba ba ta san
Muneeba na dakin ba dama ta zo yin tijara
ne bata dauka za'a ai mata wannan
bankada ba sai gashi allura ta tono garma.
Mujeeb ya shiga ya sami Muneeba a
gefen gadonsu ta zuba uban tagumi ya kai
hannu ya sauke tagumin da tayi, yace
meye abun tagumi? Na san duk kinji
maganganun mu da suwaiba, wallahi ban
Σ
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
yi niyyar in tona maganar nan wani ya ji
ba, amma sai gashi yau ta kaini makura
har kinji, sai godewa Allah kaikayin abin
da ta yi miki ya koma kanta dama haka
bokanta ya gayamata, wallahi irin
kiyayarki da na dinga ji a lokacin irin ta
yanzu. nake ji a kanta ke fiye ma da
wadda na yi miki.
Gobe zan kaita asibiti ayi mata
gwaji, in Allah ya taimake ta bata
jijjibowa kanta cuta ba to ta yi babbar
sa'a, hakan kuma ba shi zai sa in ci gaba
da zama da natsuwa da ita ba zan dinga
jin zarginta a zuciyata".
Muneeba tace, "indai ance bata da
wata cuta gara ka hakura kaci gaba da
zama da ita, tunda uwar 'ya'yan kace
kuma akan san da take maka ta je ta
aikata wannan danyen aikin".
"sam wannan ba hujja bace, ke din
Baki fita sona ba, amma me ya sa ke baki
taba tunanin kwatanta wannan sabon ba
sai ita da yake jahila ce".
187
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Tace, "To ai ka san kowa da irin
nasa tunanin, ka yi hakuri ka mata afuwa
ta yiwu yi mata afuwar ya sa ba za ta sake
ba.
Fita falo ya yi ya bar Muneeba tana
ci gaba da nazarin wannan al'amari mai
ban mamaki da daure kai.
Washe gari babu yadda Mujeeb bai
yi da suwaiba ta zo su je asibiti ba, amma
fafur tace ba za ta je ba, ya kyale ta kawai,
ita tsoron da take ji kada a auna jininta ace
tana dauke da cutar kanjamau, shi yasa ta
ga gara ta hakura taci gaba da zama haka
agidan ko ba zai mata komai ba rufin
asirinta kenan tunda ba zai kore ta ba.
Ya dubeta yace, " in kuwa ba zaki
ba to kada ki "kara cewa na danne miki
hakkinki, don kuwa ba zan kusance ki a
wannan matsayin kila wa kalan da kike
ciki ba.
Inma kina tsoron kada ace kina da
cutarne, to na yi miki alkawarin ko da ance
kina da shi wallahi ba zan gayawa kowa
188
스
2
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
ba, zan kuma iya barinki ki cigaba da
zama a gidan nan sai dai kin san babu
wata mu'amular aure da zata gitta
tsakaninmu”.
Ta share kwallar dake malala a
kuncinta tace, "Gara dai ka barni a cikin
rashin sanin dana ke ciki, da in je inji
abin da zai hana rayuwa ta kwanciyar
hankali, ka barni kawai”.
Dole haka ya tafi ya kyale ta,
kenan ya sami maslaha ta wannan
bangaren bata da damar da zata sake yi
masa korafin ana danne hakkinta, tunda
it ta zabi ta zauna haka don rufuwar
asirinta, inma ta ga ba zata iya zama ba,
shi kam a shirye yake da ya bata
takardanta idan ta nemi hakan, sai ya
amshi waleeda ya damkawa Muneeba
don ba zai so ta rayu a hannun Suwaiba
da Haj. Harira ba ko dan kada tarbiyyarta
ta gurbace irin tasu.
189
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
飲飲飲 **** ******
Cikin Muneeba yana ta bunkasa cikin
lafiva da kanciyan hankali, harma ta fara
zuwa awon saboda yanayin girman da
cikın ya vi. Kowa a zuri'arsu fatan alheri
da sauka lafiya ya ke yi mata tare da
addu'ar Allah ya sauketa lafiya.
A bangaren Mujeeb kuma tsananin
kulawarsa yake nuna mata tare da tsabar
zumudinsa tamkar ba'a taba yi masa
haihuwa ba duk wani da ya san za a bukata
na jariri sun saye shi kuma komai bibbiyu
ya saya, idan Muneeba ta tambaye shi
dalilın iyan abu biyu da yake yi sai ya ce
shi a yadda ya ke ganin girman cikin kila
ba da daya ke cikin ba, duk da cewa an yi
mata hoto a asibiti ance da daya ne na miji
amma shi sam ya bai yarda da hoton ba.
Ita kam Muneeba sai dai ta yi masa
murmushi idan yana dokinsa, duk da ita
ma tana dokin amma na ta ba irin nasa
190
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
bane