An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
WATA KUSAN
RARAINE TIS 3
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
****** ****** ******
2
H
ayaniyar surutai da sallallamin da
Lake yi ne ya sa Goggo ta kasa
kunnuwanta, don fahimtar shin daga ina
ta ke jiyo surutan, wadanda suka hada
har da kara.
Tashi ta yi tsam ta fito daga
dakinta a bakin kofane suka ci karo da
Suwaiba da ta kwaso a guje zuwa dakin
Goggo. Suka dubi juna Goggon na
tambayarta Lafiya? Wai me ke faruwa
ne? Ta sa hannu ta share zufar fuskarta
da ke barazanar tona asirin rashin
gaskiyarta akan abin da ya faru tace,
wallahi muna daki ne da bakuwata kawai
muka ji shigowar Baban Baffa, kafin in
fito ne na ganshi ya fadi kasa warwas.
Ai Goggo bata bari ta karasa fadin
wata kalma ba ta garzaya dakin
Suwaiban da gudu har tana hardewa da
zaninta. Tana shiga ta ganshi a kasa
warwas babu motsi ba alamar motsi ko
numfashi a tare dashi. Ta gurfana
3
WATA KUSAN 3
Rahm
gabanshi ta dago kanshi tana ambaton
sunansa amma ko gezau ta tashi a rude ta
nufi hanyar fita gidan ta iske Jumona duke
yanata, wanki tace, masa, "Jume taho ka
taimakamin mai gidan ne ya fadi, mai
gadin su na jin haka shi ma a rude ya
rufawa Jume da Goggo baya zuwa dakin
Suwaiba, suka iske uban gidan naşu
tamkar yadda Goggon ta gaya musu su ma
sumbi sahun Goggo don tabbatar da shin
akwai rayuwarşa ko, babu, a dalilin rashin
motsi da yake yj don ko numfashi ba kowa
bane zai iya gane shin ya na yi ko ba ya yi.
Tabbatar da a raye yake ne yasa
Goggo ta sauke ajiyar numfaşhi tare da
rage koke-koke da salallallami da ta ke yi
ta umurci su Jume su kama shi zuwa mota
don tafiya da shi asibiti, Nan ne kuma aka
fara tunanin to- wa zaj tuka motar zuwa
asibiti? Dama a gidan daga, mai gidan sai
Muneeba ne suka iya mota Suwaiba bata
tsaya ta koya ba tafi gane idan zata
Anguwa a kaita.ors wdad
4
ど
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Jume ya dubi Goggo ya ce "Bari
mu sashi a mota in tuka ni ma ina dan
taba tuki idan na sami mota, tunda har
wani gari ina zuwa sun kama shi ne suka
ga hannunsa na hagu ya tafi yaraf ya fadi
Jume cikin firgici yace "Subhanallahi ai hannunsa na dama a karye yake". Goggo
ma ta sake rudewa tana fadin "Yau mun
shiga uku wannan wata irin faduwa ce
har da karaya, kuma ga rayuwarsa ma ba mu da tabbacin samunta.
Haka dai suka taitaye shi suka saka
a bayan mota Goggo ta zauna a gefensa
Jume ya shiga mazaunin Direba tare da
Suwaiba a gaban motar sai gursheken kuka takeyi har suka isa asibiti da ya
zama nan ne suke ganin likita.
Dakin taimakon gaggawa (Emergency Room) aka shige da shi,
manyan likotoci ne suka yi taron rubdugu akan ceto rayuwarsa wanda suka shafe
awani akansa suna bincike.
5
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Zama suka yi jigum-jigum a bakin
fakin da aka shige da shi. Goggo addu'o'i
take yi a bayyane akan Allah ya agajeta ya
tashi kafadar Muneebu, wanda take ganin
idan ta rasa shi a halin da take ciki a yanzu
ba karamin gibi ta samu a rayuwar ta ba
kasancewar shine bango abin jinginarta.
Ita kam Suwaiba babu baka sai kuka
ne babu abin da ta ke yi sai sharban Kuka
tare da tunanin makomarta a dalilin
Garanbaramar da ta yi na fallasar sirrin
rayuwarta wanda har Mujeeb din ya ji da
kunnuwansa kuma tabbas abinda ya ji
shine sanadiyyar wannan mummunar
al'amari da ya same shi ita kam bata
saduda ba dole cikin satin nan ta saci jiki
ta sulale zuwa gurin Boka don ta yi masa
bayanin katobarar da bakinta ya yi har
kunnuwan mijinta ya ji sirrin da aka ce
idan ta bari ya ji to ta yi kuka da kanta ga
dukkan irin bainda zai same ta, shi ya sa
tun ma kafin abin ya risketa ko akwai abin
da zai iya yi mata a mantar da
6
MI NIHCU C
Rahmatu Hassan Zaria
kwakwalwar Mujeeb abin da ya ji in ma hakan ba zai yiwu ba to zata iya yin
gammo ta dauki dakon zunubin sa wa a
dauki rayuwarsa in har hakan zai zamo
mafita ga halin ha'u'la'in da zai sami
rayuwarta, tunda hausawa ma cewa suka yi amfanin Zunubi romo to ta gwammace
ta sharbi romon zunubinta da tushe tunda
kwabarta ta riga ta yi ruwa.
Goggo ta kaikaita ta dubi Jume dake tsaye a gefensu wanda ke cike da
tsananin damuwa tamkar yayansa na jinniske cikin ha'u'la'in data samu uban gidansa haka yake ji a ransa, kasancewar Mujeeb mutum ne sak mai kyautatawa na kasa da shi tare da tausayawa al'amuran
da suka sami wanda baya da shi
musamman ma su da ke karkashinsa ko
yaya ya gankaa wani yanayi ya dinga
tambayarka kenan akwai matsala ne ko
baka da lafiya ne idan kace lafiyarka
kalau to nan take zai jika maka aljihunka
don yasan matsalar Talakan Najeriya
7
WATA KUSAN 3
Rahmatu Hassan Zaria
bata wuce bushewar aljihunsa ruwa shike
nan za ka nemi damuwarsa ka rasa kuma
duk abin da zai basu ba wai cikin
albashinsu bane a'a ihsani ne kawai irin
nasa uwargidansa Muneeba ma haka take
mai yayyafin alkhairi, shi ya sa kullum
suke ciki da bakin cikin rashinta a gidan,
amma suna nan ba dare ba rana sun dage
da addu'ar Allah ya maidota gidan.
Sabanin amarya Suwaiba mai
Kankanan tsiya, sam bata iya alheri ba,
komai kankantan canji idan ta aike su sai
ta amshe abinta gata da yawan aike don sai
ya jera kwana biyu zuwa uku tana aikensa
Dukku, daga kudin mota ba za ta iya kara
masa kwandala ba don ya sha ruwa a
hanya ba shi ya sa a dole yake zuwa
Dukkun albarkacin uban gidansa.
Ta cewa Jume "Jume ka taho da
waya ne? ya laluba aljihun wandonsa ya
fiddo wayar yace "Eh gata nan a Aljihuna
wani za'a kira miki? "Eh Isah nake son
8
„WATA KUSAN 3
イ
1 Rahmatu Hassan Zaria
idan kana da numbarshi ka kira min shi
ka bani in yi masa Magana,
Nan da nan ya laluba Numbat Isah
ya kira shi bugu daya biyu ana üku ya
dauka sai ya mikawa Goggon ya ce, Ga
ya nan ya daıki wayar Goggo ta kara
wayar a kunneta ta amsa sallamar da Isan
ke yi ta kara da cewa "Isah ba Jume bane
Goggonku ce, so nake duk abin da ake yi
ka barshi ka taho gombe yanzu ka same
mu a asibitin da muke ganin likita gamu
nan yayanku ne ba lafiya.
Isah ya hau fadin "Innalillahi
wa inna ilahirin rajiun Goggo me ya
sami yayan? Ta ce "Ka bar bata lokaci ka
taho kawai? Jikin Isah babu inda baya
rawa da ya ji wannan abin tashin hankali
da ya same su Mintunabasu gaza hamsin
da biyar ba suka sada shi da Gombe.
Ba'a jima da zuwan Isah ba aka
gunguro Mujeeb akan gadon daukar
mara Lafiya zuwa wani daki na
musamman. A lokacin ne Baffa Adamu
9
WATA KUSAN E Bohmute Ne
suka tso daga Dukku kasancewar da Isah
zai taho ya biya ya gaya musu shi yasa
basu yi Kasa a gwiwa bu su ma suka tahu
har da Mustala yayan Muncta.
Cabe. dayansu 'yan wwan snka
hewaye gedon da Mujeeb ke kwance sny
kallon sarautar Allah tart da yi iasa
addu'a samun sauki likitah Re ya nemi son
ganin wani cikin su Baffa sai Baffa Adaty
ya unmrci Mastafa da cewar "Mustafa jekn
ga likitan a madadinmu tunda kaine ke jin
Turanci sai Meji bayanin wannan wane
trin ciwo ne ya sami yaron nam gushi
tamkut matacce bi rat be slaniir rai".
Mustafa ya iske likitan a Ofis, a nan
ne ya soma yi masa bayani Gaskiya dan
nwanku yana cikin mawuyacin hali domin
faduwar da ya yi ya huifar masu da
manyan matsaloli guda úku na furko akwał
(Stroke) da ya sare shi gefen sa na dama
baya aiki gabadaya, sannan zuciyarsa ta sami tabwwa sakamakon wani abu da ya firgita shi wanda ku ne kuku san ho meys
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
ya firgitashin ya sashi ya fadi har ya sami
mutuwar barin jiki, sannan matsala ta
uku da ya samu itace karaya da ya yi a
tsintsiyar hannunsa na hagu kaga kenar
hannuwansa duka biyun sun sami
matsala amma Insha Allah zai sami
lafiya don mun yi masa duk abin da ya
dace mun gyara masa karayar an yi mata
filasta muna fatan mu yi nasara a dukkar
taimakon da muka bashi a cikinj yardar
Allah.
Mustafa zuciyarsa a dagule da jir
iftila'in da ya sami dan uwansa ya y
naunauyan ajiyar zuciya ya ce "Allah ya
sa likita amma don Allah a hasashenku
na manyan likotoci kana ganin dar
uwana zai warke ya dawo normal mutum
irin yadda ya ke da can tamkar kowa
Likitan ya gyara zaman glas din da ko
idanunsa sannan ya soma Magana, El
muna da tabbacin akan haka Insh
Allahu tunda mu Musulmai ne muna yir
İya iyawarmu ne akan larurar mara
11
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
lafiyarmu sai mu barwa Allah sauran
lamarin shi, shi kadai ya san yadda zai yi
da bawansa idan munga nasara to daga
gare shi ne, idan mun ga akasin haka nan
ma daga gare shi ne.
Ya dan yi wani rubutu a Fayel din
da ke gabansa sannan ya tsaida idanunsa
akan Mustafa, "Abin da na ke son yanzu
muna so ku kula da shi sosai, ya kasance
ko da yaushe akwai mutum a kusa da shi
saboda zai iya yiwuwa idan zai farfado ya
motsa jikinsa to sai a rike shi tunda ya na
da karaya a hannunsa mai lafiya kada ya
lalata aikin da muka yi masa.
Zai kuma iya yiwuwa idan ya
farfado idanu kawai zai bude abin da bama
fata kenan saboda haka sai kuje kuyi ta
addu'a ALLAH ya bashi lafiya. Mustafa
ya aje ajiyar rai yana kada kai damuwa ce
fal a ransa yayi wa Likitan godiya ya bar
ofis din.
Ya yi wa Su Baffa bayanin komai da
likita ya gaya masa, anan ne Baffa
12
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Adamu ya tsare Goggo da idanuwansa
cikin tuhuma yace 'kin dai ji bayanin
likita ya yi ? to ina son sanin abin da
yaron nan ya ji har ya firgitashi yayi irin
wannan faduwar tunda abin a gida ya
same shi?.
Goggo ta share kwallar dake
shatato mata a kunci, zuciyarta cike
tsananin damuwa tare da dora zargin
komai akan Suwaiba tace, Wallahi ni
ban san me ya ji ba tunda abin a dakin
matarsa ya same shi, nima ita tazo ta
kirani, ita ya kamata a tambaya.
Baffa ya ce "Mu bamu da ikon da
za mu titsiye matarsa mu tuhumeta tunda
ke da muke da iko a kanki baki sani ba
sai mu bar maganar, mu barwa Allah
al'amarin mu yi masa addu'ar samun
lafiya koma me ya ji ya firgita shi idan
Allah ya ba shi lafiya ai za mu sąni ba
ma sai mun bata lokacin mu ba wajen
bincike bа.
13
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Suwaiba dake rakube a gefen su duk
tana jin abin da aka fada jikinta ya yi
la'asar ita kam addu'a take kada Ailah ma
ya tada kafadarsa ya sa daga wannan
baccin zai yi tazarce ne don kuwa tasan
samun lafiyar sa na cikin tonon asirinta
sannan kuma karyewar asirin da ta yi masa
tunda boka ya gargadeta da cewa kada ta
kuskura mijinta ya ji sirrin dake tsakanin ta
da shi, gashi kaikayin baki ya sa ta yi
baranbaramar da ya ji komai har hakan ya
yi sanadin shigarsa halin ha'u'la'i.
Ita kam za ta yi gum da bakin ta ne a
kada a raya babu wandá zai ji wannan
ta'asar da ta aikata da boka, tunda ta san
Goggo sam ba za ta yarda a ci amanar
auren danta ba ta hanyar yin fasadi da
boka, duk iya biye biyen malamanta da
bokaye, ita ma Hajiyarta ba za ta goya
mata bayan yin zina da Boka ba, bar su
dai da binne binne da yanke yanke ko zuba
asiri a abinci, amma ba za su yarda da
14
WATA KUSAN 3 Rabmatu Hassan Zaria
aikata wannan babban Fasadin ba da
igiyar aurenta da komai.
Tana matsar Kwallan munafunci ta
dan langabar da kai ta ce, ni kam Baffa
wallahi ban.san cikin firgicin da ya dawo
gida ba ila dai ina daki ina sa wa
Walceda kaya na ji faduwarsa a falo ni
wallahi ban ma san ya shigo ba, ko ma
me ya firgita. zuciyarsa ina ganin daga
waje ne".
Baffa ya jinjina kai, "Ko ma
mencne mu kam mun bar wa Allak
lamarin mmu yanzun fatanmu ALLAH ya
tashi kafndarsa ya bashi lafiya don
wahnan ciwo nase akwai tararrabi".
Mustafa kam tunda ya ji bayanin
Likita da kunnuwansa na cewa kada a
bari ya farfado ba kowa a gurinsa shi ya
sa ya yi saurin barin gurin su Cogge ya
koma dakin de Mujeeb din yake duk Isah
na can ya daifi son shima yana kusa.
Ya ja kujera ya zauna daf da fukar
Mujeeb din, ya Rura masa idanu yana SON
15
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
ya gano ta inda numfashin Mujech fin ke
fita, wanda duk iya kwakkwafi da
kurilarka, ba za ka iya tantance ta inda
numfashi ke fita bah.
Don dai likitoci sun tabbatar, musu
yana da raine; gaskiya da ba zai yarda
Mujeeb na da rai ba. Ya kaj hannunsa yana
shafar bannun Mujeeb din zuwa Kafarsa
wadda likita ya ce basa aiki ya kai ganinsa
ga daya hannun wanda yake nade, eikin
Alasta shima a karye ya ke,yn, girgiza kai
Aikin jin tausayin halin da rayuwar,Mujeeb
di ke ciki bai san lokacin da hawayg ya
ziraro, a kuncinsa ba.
Ya lalibo wayarsa a aljihu ya kira
Layin Muneeba wadda yake kyautata zaton
bata,san me ke faruwa ba tunda bata
Dukku tana nan Gomben.
Bugu Daya, biyu sai ta dauka tana
salamu Alaikum Baban Inna"
banda yn ji ta fara da wannan bark wancin
na kiransa, Baban Inna ya san bata san
komai ba dangane da abinda yasami
16
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
mijinta (Sunan Innarsu aka sakawa diyarsu shine ta lakaba masa Baban Inna)
don yace baya son a kira 'yar da Inna Shine take tsokanarsa da Baban Inna idan
tana jin barkwanci).
Yau bai biye ma barkwancinta ba saboda yana cikin tashin hankali "Kina
ina ne yanzu". Ta amsa ina gida yanzu na dawo daga kasuwa a gajiye ina kishingide ina hutawa"
"Ok, to ki tashi yanzu ki shirya ki
zo nan asibitin da kuke amfani da shi
muna nan tare da su Baffa, Mujeeb ba Lafiya yana cikin mawuyacin hali, me ya
same shi? Ka tabbatar yana raye? Ya ce,
yana raye ke dai ki zo ki same mu.
Gaba daya jikin Muneeba ya yi sanyi tana daga zaune ta kasa tashi sai jujjuya ciwon na Mujeeb takeyi a ranta, shin wane irin ciwo ne ya same shi? A
iya saninta da shi ba shi da wani na gama gari ko na kullum kullum to ko wane irin
ciwo ne ya same shi? Oho!.
17
Ta sami Mama Amina na a daki ta
yi mata bayarin wayar da. Mustafa ya yi
mata, ta kKara da cewa "Ni yanzu da ya
kirani me zan je in yi a asibitin tunda su
suna can sannan ga Guggo ga matarsa, ne
iyakaci kawai in je in gaishe shi in dawo".
Mama ta girgiza kai "yaro Man
Kaza to in ma kinje kince zaki yi jinyarsa,
ko Mustafa yace kizo kiyi jinyarsa da
wanda zai hana ki ne ko yayi miki shamaki
da shi ina ce har yanzu a matsayin mijinki
ya ke to bana son sakarci maza ki shirya ku
tafi da Hibba ku dubo shi, muma gobe za
mu je mu duba shi Allah ya bashi lafiya.
Muneeba ranta bai so zuwa ba a
dalilin irin wulakancin da tozarci da
Mujeeb din da Guggo da Suwaiba suka
dinga yi mata kafin barinta gidan tana ta
hakuri da su, har dai ta kare da bakinsa
yace kada ta dawo gidansa sai ya nemeta
neman da bai yi mata kenan ba ya jingina
aurensu babu ko waiwaiya to ita kam don
meye zata waiwaiye shi don ba shi da
18
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
lafiya ita ma fa tayi ciwo kuma an gaya
masa kila ko don bata kwanta a gadon
asibitin bane yasa bai zo gaisheta ba?.
Nuku - Nukun ta dinga. yi har kusan magariba hakan ne ya tunzura
zuciyar Mama Amina ta zọ ta rufeta da fada, Haba Muneeba ban sanki da zuciyar rikon dan uwanki Musulmi irin
haka ba, dan uwan naki ma na jinni kuma
Mijin aurenki ki juya wa duk abin da ya
faru baya, kije ki duba shi domin Allah
kuma domin zumunci in ba za ki je don
auratayya da ke tsakaninku ba ciwo ai ya kori komai kuma tunda kika ga har
Mustafa ya kira ki ai abin ba karami
bane. Oya maza sa Hijjabi ku wuce tun
dazu idi keta jiranku. Ba tare da tayi
Magana ba ta suri Hijjabi ta zira sai
wayarta da ta dauka tayiwa Mama
Sallama suka tafi.
Yanayin yanda ta riski halin da
Mujeeb ke ciki abun ya firgitata ya bata
tsoro har sai da ta zubar da hawayen
19
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
tausayawa a gareshi. Ta iske su Baffa duk
sun koma Dukku sai Mustafa ne ke zaune
tare dashi a dakin a lokacin Goggo ta fita
yin sallar Magariba.
Muneeba ta dubi yayanta Mustafa
zuciyarta a tsinke da al'amarin tace "wai
yaya Mustafa wannan wane irin ciwo ne ya
same shi ga dai mutum a kwance tamkar
matacce amma wai yana da rai ya dade
yana ciwo ne? ya girgiza kai "A Yadda
Goggo ke gaya mini da na zo lafiyarsa
kalau don ko ciwon kai bai wayi gari dashi
ba har ranar illa lokacin da ya dawo gida
ne abin ya same shi a dakin Matarsa, ita
kam bata san me ya faru ba, Suwaiban ce
ta garzayo take gaya mata gashi can ya
fadi a falonta, wai ita ma bata san ya shigo
ba sai dai faduwarsa ta ji".
Muneeba tayi tsam da ranta cikin
nazari sannan tayi Magana, "A binciken
likitoci da suka duba shi me suka bincika
da ya kawo masa faduwar da ya yi sannan
me ye alakar hakan da abin da ya shafi
20
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
a
zuciyarsa "Eh to likita ya kira ni yayi
min bayani cewar ya sami. (Stroke)
bangarensa na dama baya aiki sannan ga karaya a hannunsa na dama kinga kenan
dama da hagunsa sun sami matsala sai
zuciyarsa ta sami tabuwa lafiyarta a
dalilin wani abu da ya tsoratar da żuciyar
tasa, wanda shine muke ta bincike don
mu gano me ya ya yi har yaba shi tsoro haka. Goggo kam ta dora zarginta akan
Suwaiba tunda a dakinta abin ya faru a
cewar ta lallai wani abin ya ji suna fada
ita da bakuwar da ta yi, amma ita
suwaiban ta musanta hakan`shi yasa na
roki Goggo da ta bar maganar tunda babu
tabbas kada rayuka su baci, mu dai muyi
ta addu'ar Allah ya bashi lafiya samun
lafiyarsa ya fiye mana komai
Tunani
Muneebа
Mujeeb
ne
na lallai
zaiji
ya darsu
duk
a
wani
zuciyar
abu da
mummuna daga bakin dSuwaibato bazai ras
Goggonsa a ciki ba,
S
21
alaka da
kasancewar duk
WATA KUSAN 3
Rahmatu Hassan Zaria
wani fadi tashinsu da biye-biyensu tare
sukeyi da uwarta da Goggon da ita
Suwaiban ko ma dai meye su suka sani ita
kam kankararta a kunne har ta manta da
matsalolinsu, kawai matsalarta yanzu
ciwon mijin nata, duk da dai bata da
tabbacin zata koma gidansa tunda har
baffaninsu sun fara maganar za'a nemo shi
don ya bata takardanta zaman nata a gaban
iyaye ya isa haka gashi nan ya janyo mata
sintirin mazaje gani suke auren nata ya
mutu ne ko ta gayawa masu biyo ta ko
aikowa cewa da aurenta karyatawa suke yi
shine fa dalilin da yasa Baffansu yayi ta
bambancin fada yace lallai dole a san
abinyi idan auren yake ta koma gidansa in
baya yi ya bata takardanta don ga masu so
nan fal a gari, ba zai yiwu ya jingine ta ba
kamar tsohuwar riga.
Shigowar Goggo dakin ne ya katse
mata tunaninta suka risina a gaban Goggon
ita da 'yar rakiyarta Hibba suka gaisheta
tare da tambayarta ya mai jiki da sakin
22
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
fuskarta da komai ta amshi bakuntar tasu har tana karawa da cewa "Kinga yadda Allah yai ikon sa kan mijinki ko? Larura farat daya ta same shi bamu san Musabbabin ba sai shi sai Allah, sai kuma matarşa da abin ya faru a dakinta,
ta yi gum da bakinta ta ki fadar gaskiyar
me ya faru Allah dai ya bashi lafiya zai fadi koma mene ne da bakinsa".
Muneeba ta yi saurin ratar numfashin gogon "Abin da kawai zamu yi tayi addu'a kenan samun lafiyarsa
koma meye sanadin ciwon nasa sai ayi hakuri a barwa Allah shi ai baya bacci. Goggo ta gyara abin Sallah dake gefe zata fara Sallah Muneeba tace "Inna
Amina tace a gaida mai jiki, ta so mu zo tare to baba baya nan kuma bata sami
wayarsa ba gobe suna nan zuwa
To Madalla ai babu komai yau da gobe duk daya ne a gurin Allah Allah ya kaimu goben".
23
WATA KUSAN 3 Rahmatu Haşsan Zaria
Muneebata dubi Mustafa yace Yaya
Mustafa ka je ka yi Sallah idan ka dawo ni
sai inje in yi kada ka rasa jam'i ya fita
zuwa masallacin dake Harabar asibitin da
Goggo ta idar sai ta ce suje suyo alwala
zata zauna kusa da shi.
Har tara na dare ta 'wuce Muneeba
na asibitin bata da alamar zata tafi,
Mustafa ya yi mata Magana Dare fa ya
soma ku zo ku tafi gida ga Isah nan tunda
ya dawo sai ya kaiku a motata idan ya
sauke Goggo sai ya saukeku ni za mu
kwana da shi".
Ran Muneeba a kumba ya ke ne
yadda za ta iya barin asibition nan alhalin
tana ganin yadda yanayin jikin mijinta
yake a kwance tamkar mutum-mutum a
tunaninta idan ta tafi da kyar zata dawo
gobe ta iske shi da sauran numfashi.
Ta san dole ta tafi tunda koda tana
gidansa ne zai yi wuya ta dinga kwana da
shi a asibitin tunda ga su Mustafa da Isah
nan ko Isah ma kaďai zai iya kwana da shi.
24
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
Kafin su tafi sai da ta tsaya akansa tayi masa addu'o''i ta tofa masa sannan suka tafi da suka koma gida a tsaye a
tsakiyar falo suka iske Inna Amina tana ganinsu ta sauke ajiyar zuciyar tace,
Haba Muneeba kunje kunyi dare ina nan hankali na a tashe tunda kin san Idi ya
tafi babu mai zuwa dauko ku ai da sai ku
dawo da wuri ya mai jikin?.
Ta sabule hijjabin kanta tana cewa
Jiki sai godiyar Allah amma gaskiya
yana jin jiki don baima san wanda ke
kansa ba balle shi ma ya san a inda yake
bashi da Maraba da matacce illa ta
hanyar numfashi wanda sai ka yi
tsananin lura ne zaka gane yana
numfashin.
Inna Amina cikin tashin hankali ta
ce? Wane irin ciwo ke damunsa.
"A dakin matarsa chin uo some shi
a cewara wai ta a ji ta
fito kinga dai ya sami karaya a hannun
hagu, gefen damansa kuma baya aiki ya
25
WATA KUSAN 3 Rahmatu Hassan Zaria
sami (Stroke) sai Zuciyarsa da ita ma ta
sami matsala a cewar likitan wani abu ne
ya firgita zuciyar tasa Allah ma ya sa bata
gefen hagun ya sami mutuwar rabin jikin
ba da shi kenan zai iya kamowa da
matsanancin ciwon zuciya in ma ya zo da
Karar da kwana bugawa kawai zata yi sai
dai aga gawar mutum a rasa meye sanadin
mutuwarsa".
Inna ta dau salati ta dire tana nanata
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un
Allahumma ajurni fi musibati wa aklifni
hairan minha wannan wane irin iftila'i ne
ya fadawa rayuwar yaron nan? Allah ka
kawo masa agajinka ka bashi lafiya ka
tashi kafadarsa.
Wannan Suwaiban ta zame wa
mutane jafa'i su kam ko za su gane
makircinta