Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 6
da zafin nama yace rahma tashi muyafi jos sadiq yayi accident ankaishi gun, salati tafarayi tamike dawuro. Wayanshi yaciro yakira antyn sadiq wato [6/4, 6:52 PM] Adda bena: 4⃣6⃣BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Step mothernshi nafisat don yasan mamanshi nada hawan jini kar hankalinta yatashi, yamata bayani salati itama tayi tareda cewa gasunan zuwa, ramlat tashigo kenan taga rahma na kuka dama momy taje aiki, kawai shiga motan sukayi bawanda yayi tunanin kuhayla sai jos. Rahma kam kuka take wiwi, tana ambaton sunan Allah, ya Allah katashi kafadun yaah sadiq ya Allah kataimaka yah Allah, haidar dake tukin duk yaji jikinshi yayi sanyi bashiri yace cikin tsawa kimana shiru da Allah mutuwa akacemiki yayi ne kome? Tafiya suke anma gani take kaman baa sauri shikanshi haidar din gani yake kaman bazasu isaba, cikin minti 30 suka shiga jos asibitin suka wuce , inda aka gwada musu inda yake , emergency, suka tsaya cirko cirko mutumin daya kawoshi yamusu bayanin abunda yafaru sannan yamisu kwatancen inda hatsarin yakasance yakuma mika musu wallet din, rahma kam alwala tayi tazota fara sallah, adaidai lokacin su nafisa suka karaso, bata gayawa momyn sadiq ba tadai kawota ne kawai, momy naganewa tafadi agurin dama tace tun safe takejin wani iri, itama agun aka bata gado, likitan nafitowa yace yana neman dan uwansa kasancewar haidar shine namiji agun, yajashi suka shiga ciki yace kayi hakuri, duk iya kokarinmu mu ceceshi yasamu mummunan buguwa, which caused instant dead, Allah yajikanshi kuyi hakuri, tunda haidar yake baitaba fuskantar tashin hankalin dayake ba, tsayawa yayi cirkum can sai ya isa kan sadiq yana cewa haba abokina mutuwa? Noo a a bangayamaka abunda nake boye maka ba? Abokina kamutu da hakkinka akaina? Innalilahi wainna ilaihi rajiun rahma ce tashigo dakin salati sai maimaitawa take nafisa ma takarba, basai duk suka rudeba, rahma kam agun tafadi,(nima benaxir inadaga gefe ina kukan, shikenan munrasa sadiq innalilahi)f likitan ne yajasu haidar waje, sannan nurses suka dauke rahma aka bata gado suma tayi dama, hajiya kuwa bawanda ma yaje gunta don duk cikinsu kowa nacikin tashin hankali balle asan mezaace mata tabi tadamu akaita taga danta, gashi duk jikinsa ya kwarzane jini ya babbatashi, kuhayla ce takira rahma, cikin kuka rahma tadauka tareda cewa munrasashi , kuhayla yah sadiq yarasu, [6/5, 9:41 PM] Adda bena: 4 7 BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Kuhayla abun yazomata da mamaki donhaka saitace wani yah sadiq fa, yanzu muka gama waya dashi, jin rahma na kuka yasa gabanta ya tsinke yafadi, wayan tasake hannunta duk yafara bari tajuya tana kallon inna idonta duk yacika da hawaye, sannan tace inna kitaimaka min, yah sadiq ne babu! Yatafi fa, inna mikewa tayi tana salati sannan tace ke banson haukan banza, kigayamin gaskiya meke faruwa, waya mutu? Wani sadiq din, ta durkusa hannunta na kai kuka take sosai, tayi iya kokarinta taga tadaure don karta yi kuka tana tuni da hanin yiwa mamaci kuka, wayance takara kara tadauka alokacin rahma tace gamunan dawowa da gawansa, nana, zatazo tadaukeki kuje gydansu kafin muzo, hijabinta tadauko tarike hannu tagagara zama gani take kaman wasane, yah sadiq din? Ya ilaihi, cikin minti sha biyar saiga nana tana zuwa takira wayan kuhayla tana dauka tamata kwatancen gydan, data iso motan kawai tashiga ba nanan bace take tuki sai alokacin talura da ita kanwar sadiq ce, itama tana gsu daga gombe ta karaso, bawanda yayi magana sai kukan dasuka rinkayi a motan, harsuka isa sannan suka shige gydan, gydan acike tam mutane sunfara zaman makoki [6/5, 9:57 PM] Adda bena: 4 8 BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMARY Acan jos kuma, hajiya tadamu anuna mata sadiq, rahma tana zaune agefen gadon da aka bata duk tana tunani tarasa meyake damunta, takara dauka takira kuhayla sannan tace kun isa? Muma gamunan zuwa, tana kashewa tamike dakyar abun duniya duk yadameta salati take tayi aranta, hajiya nazaune tasameta alokacin haydar da nafisa sungama magana da dr. Yayi sighn yayi komi anbada gawan, sannan akasa a motan gawan da haidar yakarbo, alokacin rahma taja hajiya suka fice sukayi mota, acewarta an canjawa sadiq asibiti lokacin datake bacci,dahaka sukaja ta tashiga mota sai addua takeyi duk jikinta yayi sanyi, taji ajikinta wani abu yafaru da dan nata, rahma ta jingina ta, dama motarsu daya,nafisa kuma suna baya, har suka isa bauchi hajiya dai batace komi ba, tana saurarone itakam taga ikon Allah, tana zaune motoccin suka shiga gyda motocci uku biyu nasu daya na gawa, tana bude kofan taga motan bayantan na gawa, gagara tsayuwa tayi, don dama basu bari taga moton ba, rahma ta tallafota, alokacin duk mutanen dake gurin sautin kukansu yakaru, (kunsan abunku da gydan rasuwa, taron mata), hajiya karshe daukanta akayi aka shiga da ita ciki, ruwa aka watsa mata don tsuma tayi anan tafara salati, salatinnan saiyi take. Yayinda kuhayla kukan yaci karfinta duk kokarinta nakartayi kuka tagagara, hannunta tasa abaki tacija dakarfi , gyda dai babu mai rarrashin kuja, tashin hankalin da rahma tashiga ko kuhayla bata shiga ba, Allah sarki baiwar Allah tayi nadaman rashin gayawa sadiq tana sonsa, tafi shekara uku tana kiwon sonsa, tana jira yafurta mata anma sadiq bai furtaba [6/5, 10:09 PM] Adda bena: 4 9 BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Karshema sai gani tayi yafara neman kuhayla anma haka tadaure ranta, tacije don kar yagane, bata taba gwadawa kuhayla ba, duk tana kyautatawa kuhayla saboda sadiq yaji dadi, tayimishi sadaukar so, anma Allah baiyi ranan da zata furta ba, kuhayla kuwa dama can ba sonsa take sosaiba, anma sun shaku, akwai wani girma da daraja na musamman da sadiq yakedashi agunta bazata taba mantawa ba, haidar kuwa on the other hand duk gani yake he is at fault. Yana ganin he owe sadiq an apology, yaso yafadamishi abunda yayi, ji yayi yakara tsanan kuhayla, duk rashin gaskiyansa gani yake ita tasashi ya aikata abunda yayi, yanzu sadiq yabar mishi duniyan, Ahakadai kullum ake zaman makoki inna ma taje sau uku sannan tahakura kuhayla sai dare suke tafiya dasu rahama, duk tabi ta lallace gwara ita akan rahma wacce abinci mai kyau bataciba tunda sadiq yarasu rayuwanta yadawo jagwal batajin dadi ko kadan, duk wannan lokacin har anfara lectures anma duk basu zuwa Ananne rahma tace kuhayla to ki samu ko note nawata kina snapping hoto kina karantawa tunda bakida time din rubutu, ko ta whatsapp ne. Kuhayla tace taf ai anan akeyinta duk wayoyin nan bawanda na iya dannawa, nadai iya amsa kira nima nakira, msg ma dakyar nakoya, bayannan sai sa caji saidai zanxo nazauna ki koyamin, dahaka suka rabu [6/8, 6:31 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Bayan sadaqan bakwai shine hajiyan sadiq tace suyi hakuri dazuwa hakannan, sufara zuwa makaranta, aranan zaemah ta diro garin, dama haidar yace kar agayamata rasuwan tunda tana exams, kuma alokacin duk takashe wayanta, balle tahau whatsapp din zamani taga rasuwan, kuma kaman hadin baki bawanda yayi azancin kiranta yamata taaziya. Randa tadawo tashigo gyda kenan bayan tayi wanka taci abinci takira haidar yashigo gyda suna hira alokacin take tambayansa inasu sadiq da kuhayla, shiru taga yayi,sannan yace sadiq fa Allah yamasa rasuwa yau sadaqan bakwai, ji tayi abun yazo mata daga sama, antaba fadan rasuwa haka? Taja tsaki kai naga alama so kake sadiq yamutu don kasamu ka samu kuhayla ko? Kabi ka munafunce bawan Allah kayi kib kib dakai, toh gwara ma kasa aranka sadiq nanan wanda yafi karfi shizai kwashi kuhayla, ganin tanata magana baice uffan ba, yasa tadan tsagaita tareda cewa meye kawani shiru? Hawaye taga sunzubo a idonsa, a duniya idan akwai abinda ke daga mata hankali shine taga haidar acikin damuwa, tace lafiya meya faru? Namaka wani abunne? Alokacin taga ummanta zata wuce, tareda cewa ke tunda kin dawo ai saikije kimisu taaziya, taso muje, haidar zo ka kaimu, yamike baice komi ba, saitace umma wakuma yarasu? Sai tayi gim tace yayan naki bai cemiki sadiq yarasu bane? Rike kirjinta tayi dakarfi don ji tayi ya soketa, tadan dafa bango tahau salati innalilahi wainnailaihi rajiun, yah sadiq? Saikuma kalmomin data furta mintoti kadan da suka wuce suka fara dawo mata, gabanta ya tsinke yafadi dam, sai ta dan zauna, umma kawai tawuve motan alokacin yashiga yakunna ganin zasu tafi su barta yasa tayi sauri tamike tashige motan [6/8, 7:02 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Tana zaune anma tarasa meke mata dadi, idonta duk kafewa yayi, dama asalinta bamai kuka dawuribane, zuciyanta ne yafara mata zafi salati tafarayi a hankali, hannunta na gamke suna tafiya ummanta talura da halin data shiga saitace, nifa karki faramin wannan mazarin naki, kiyi hakuri muje mudawo, anma inaa zaemah bata sauraro hankalinta duk baya gurin, suna karasawa mutane daidai ne alokacin anwatse umma tafita tashige gydan zaemah tana zaune bata fitaba batace komi ba, haidar shikanshi hankalinshi atashe yake kalmomin da zaemah tafada mishi duk suna dawo mishi akanshi, “”naga alama so kakeyi sadiq yamutu don kasamu kuhayla, kabi ka munafunce bawan Allah kayi kib kib dakai, toh gwara ma kasa aranka sadiq nanan wanda yafi karfi shizai kwashi kuhayla,””” maganan sai yawo take masa yarasa yazaiyi, rike kansa yayi gefen kansa tana mummunan sarawa, dakyar yabude walleta dinshi yadauko wasu kwaya guda biyu yasha da ruwan faro dake gefensa sannan yadan rusuna, har lokacin maganan namasa yawo, zaemah tassmu ta daidaita hankakinta tafito daga motan simi simi tanufi cikin gydan, tana shiga ta tarar dasu umman da hajiyan sadiq suna zaune hajiyan sadiq sanye da hijabi tarike carbi a hannunta, [6/8, 7:14 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Jikin hajiya ta je tajingine hawaye zafafa suka zubo mata, tace hajiya sadiq yatafi, dama hajiya kaman jira tske tuni dan hawayen dake makale suka fito ringim a fuskanta, itama tafara kukan, ainan da nan kuka yadawo sabo, zaeman nayi, hajiya nayi,umma nayi ga sauran dangi suma suka farayi, babu mai rarrashin wani, bayan sungama kukan ne, hajiya taja zaemah suka shiga daki hajiya tace zaemah jikina yana bani sadiq yasan zai hadu da kaddara, don dazai tafi yazo yasamen yace “hajiya zantafi kuma nabada amanan kuhayla agurin haidar da zaemah, nasan haidar yaki karbane saboda dalilansa, anma ga wannan wasikan kibawa zaemah idan tadawo” hajiya ta share guntun hawayen dake fuskanta sannan tace wlh zaemah harnake cemasa yaushe yasam dawowanki? Bagwara yatura miki ta wayaba? Tunda kuna abun zamanin nan whatsapp, anma yace shi nabarshi ahaka kawai nabaki, babu wanda yabude donhaka gashi ahannunki kije gyda kinutsu ki karanta, idan tayi kama da wasiya kizo kifadamin asamu acika masa burinsa, zaemah sai kukka yakaru ido shar shar tagagara yin shiru, yanzu duk saitaji zuciyanta ya karaya, gabanta yayi mummunan fadi, tarike envelope din ahannunta tafice daga dakin, awaje tasamu har ummanta tashige mota donhaka taje tashiga suka wuce, haidar na ajiyesu yawuce bai kula zaemah ba dan har lokacin magananta suna masa ciwo itama bata damuba duk ta kagu taga ta isa gyda don tabude wannan takardan [6/8, 7:41 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Tana isa tashige dakinta tarufo kofan daki ta durkusa agaban italian bed din da mahaifinta yazuba mata a dankareren dakin kamar bazatayi aureba, taga full scaf ne saida gabanta yafadi wannan menene takunsa?tana budewa tafara karantawa kamar haka “Salamu alaikum zaemah Dafatan kina lafiya? Kindawo lafiya? Zakiyi mamakin meyasa nace hajiya tabari saikin dawo ban turamiki tun kina canba, toh kinsan karatun shekara dayane, anma gani nake kaman shekara goma, zaemah kimin alfarma wanda babu dan adam din dazaimin saike, zaemah nasan haidar nason kuhayla, yana boyemin ne saboda kar raina yabaci, sannan yana boyemin ne don kar abokantakanmu ya lalace, anma zaemah kinsan wani abu? Kinmanta tun muna yara idan aka siyo mana abu haidar yakan tsani abun ? Saidaga baya yafaraso? Kintuna lokacin da akace haidar yakarbi jaka blue da umma tasiyo mana? Ya tsani jakan har kuka saidayayi? Daga baya yazo yana balain son jakan? Kintuna lokacin dakuka hadu dashi? A islamiya? Ya tsaneki? Bayason wani abu yahadaki dashi? Anma daga baya fa? Har iyaye sunfara zumunci a tsakaninsu saboda kaunar da shakuwar dakukayi, toh zaemah banmanta ba, haidar tunda mukaje nadauki kuhayla nadauketa da niyyan idan na ajiyeta bazan kara komawa ba, anma yadda ya tsaneta yasani kokonto nayi tunanin zaicigaba da tsananta duk randa yaganta har yazo yafara sonta, toh kuma ahalin danaganta nasan idan bamu nemi hanya ba lallacewa zatayi, sanadin haidar yasa nadauki nauyin kowani rana nake zuwa nake kulawa da ita nabata abun bukata don kartashiga halin da yayarta takeson sakata BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Nayita kulawa da ita ina janyo haidar anma yana kara gwadamin tsananta , baitaba tsanar ya mace kamar yadda ya tsani kuhayla ba, hakan yabani tabbacin zaisota har kololuwar rayuwarsa, duk abinda nayiwa kuhayla bantaba sonta ba, nadai shaku da ita, nayi hakanne don nasamu haidar yacanja, toh alhamdulilah kafin nabar garin, naga yafara taimakawa, baiyi tunanin nasan cewa shi yagyra musu gyda ba, kuma bangwada mishi ba, nayi hanyoyi na duk banganeba anma wataarana nashigo dakinsa naga files dakomi harda hotunan kuhayla hakan yatabbatar min dacewa lallai kuhayla tafara shiga ransa as expected. Banyi niyyan kara masters ba, anma nayi hakkanne don natafi nabashi guri domin yashaku da ita, naje don nabashi amana amma yaki karba dama nasan bazai karba ba domin yana tsoron kar nagane yana sonta, anma nakiraki nabaki , donhaka natafi ne don nasamu su sasanta kansu kafin nadawo, inyaso sai na bayyana gaskiya, inaso kitaimaka kihadasu su sasanta kansu, inason kuhayla da haidar domin kuhayla macece iya mace, haidar kuma ayadda yakeda zaben mace itace zatayi maganinsa, ni from day 1 rahma nakeso anma haidar yahana, yagwadamin wataran zan iya bata mata rai, zai shafi abokantakanmu baiyadda zan iya kula da rAhma ba, kum nasan rahma ma tana sona, donhaka kisamu plx kimin hanya kisamata ido karwani yazo ya kwacemin ita, i love her loads of bunch, to the moon and back , donhaka zaemah my trusted fund, kitaimaka, kicika min alkawarina, natafi anmafa zandawo soon so kisamu kicika alkawari kafin nadawo, Ur frnd truly sadiq Rike papern tayi tafara wani zazzafan kuka, kuka tayi sosai wanda tunda take a iya wayonta bata taba wannan kukan ba, tayi kuka sosai har kanta yafara ciwo, aranta tarike alkawari tare da cewa yah sadiq namaka alkawari insha Allah kuhayla zata auri haidar Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 13 3 days ago Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 12 3 days ago Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 11 1 week ago Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 13 3 days ago Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 12 3 days ago Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 11 1 week ago Share this on WhatsApp Share this on WhatsApp FE CE NA BENAXIR OMAR Insha Allah babu wanda zai nemeta bayan haidar. Duk taurin kan haidar zan san yadda kuhayla zata juyashi, ta dauki papern ta nannade tamayar cikin envelope tabude safe dinta sannan tasaka tamayar ta rufe, wanka tashiga ta kwarama kanta ruwan zafi taji dadin jikinta, wayanta tadauko tadanna numban kuhayla tana daukawa tayi sallama wacece? Zaemah ce kuna ina? Tace lahhh anty zaemah yi hakuri bansan ke bace,ina gyda tace ohk tom ganinan zuwa, tana kashewa tasako dogon rigan abaya ita yanzu saka atamfa nabata wahala duk kayanta yawanci abaya ne, tana sakawa tarufo fuskanta da bakin glass sannan tafito rike da jaksnta hermes birkins, tace umma barinje gurin kuhayla nadawo, tace toh kigayda innarta, kasancewar sunsaba agydan rasuwa, tana fitowa tashige mota anguwansu kuhayla tanufa, aikuwa tana isa tashige cikin gate din, maigadi yana rufowa yace hajiya sannu hannu tadaga masa tashige ciki kuhayla na falo tashigo dagudu ta rungumeta tareda cewa oyoyo anty, zaemah tace sakeni barni, bayan tsabar bakin hali ace sadiq yafadi yamutu acikin ku bawanda zai iya kirana yagayamin? Kuhayla tace lahh anty wlh tlh yaa haidar ne yace karkowa yafadamiki, yace kina karatu kar hankalinki ya karkata, tasan bakaramin taimakonta haidar yayiba don da anfadamata bazata karasa exams dinba zata dawo, donhaka tace Allah yajikanshi har lokacin kirjinta na bugawa, taana zaune kuhayla tayi shiru tace meye?,kekuma tsoron haidar din kikeji? Don kawai yace kar afada saiki yi shiru? Kuhayla tabude baki laaa wlh ina tsoronsa wannan mareni zaiyi inna masa rashin hankali shiyasa nake jan girmana, zaemah taja tsaki tsiya dai, ya makarantan? Tace lafiya kalao, sai yau muka fara zuwa, ni duk wahala ma wlh, donma rahama na taimakona, tace ae kam, yanzu ina inna? Tana ciki muje, sukaje ciki zaemah tagayda inna , inna tamata murnan gama makaranta dakuma zama cikakkiyar likita takuma kara mata taaziya nan ma dakyar tamike don zuciyanta yayi nauyi yanzu burinta taga andaura auren kuhayla da haidar inbahakaba dutsen datakeji yana mursusu azuciyanta bazai daina damunta ba, anantacewa inna kuhayla zata rakata kasuwa inna tace bakomi, tana fitowa saiga kuhayla tasanyo hijabo har kasa. Irin na malaman islamiyan nan, zaemah tace ina zuwa? Islamiya? Tace habawa anty kasuwa kikace narakaki fa, tace ahto naga kinsanyomin kayan islamiya ne, alhali ni kayan aiki zamuje siyowa, tabude booth dinta saiga wani hijabi fari mai kyau mai hannu tace zurma wannan don bazaki bini da wancan ba, tana sakawa tace toh suna shiga kwayan zaemah yafara kara takashe wayan kuhayla tace meyasa? Tace saboda filin yaki zamu shiga kuma kinsan duk wanda zaishiga filin yaki dole yasiyo kayan aiki, donhaka kasuwa muka nufa [6/9, 8:17 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Itadai kuhayla shiru tayi tana jira taji wani kasuwa aka nufa da ita, central suka nufa. Tashiga da ita suka jido abaya dakuma inner wears, turaruka da takalmi itadai kuhayla kallo takeyi zaemah tagama diba, suka wuce shagari tabada dinkin na dinki sannan tace muje gyda, suna isa gyda bata fito da kayan ba tace mushiga suna shiga ta isa gun inna ta durkusa har kasa, tace inna nazo neman alfarma agunki inna tace mekenan yar nan? Tace inaso kuhayla ko sati biyu kibarta tayi aguna ko wata daya, inna inaso incika wani alkwari dana dauka wa yah sadiq kafin yarasu kitaimaka incika masa, ko zan samu nutsuwa, inna tayi shiru duk da bata tambayi menene ba tasan alkawarin ba karami bane donhaka tace toh badamuwa, ana don Allah zaemah ina tsoro kinga marainiya ce karki dandana mata dadin duniya tazo tasaka ranta akai, inaso kullum ta tuna daga inda tafito, zaemah tace wlh inna kuhayla bahaka takeba yarkice kinsanta donhaka kiyadda dani insha Allah babu abinda zaifaru kiyadda dani, tana ficewa tace wa inna tattaro kayan dakikasan suna da muhimmanci banda kayan sawa, kuhayla taje tadauka chargernta sannan tazo gun inna tare dacewa inna metace miki? Wlh inna bansaniba bani naroketa ba, inna tacec aiban tambayeki ba kawai kije kikuma kama kanki karki kuskura kimanta daga inda kika fito [6/9, 8:57 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR gydansu zaemah suka nufa kuhayla dai batace komi ba a motan, babu tunanin dabatayi ba amma zaemah taki furta mata komi balle tagane metake nufi tadaukota takawota nan, suna shiga makeken gydan zaemah takira masu aiki biyu suka tattare kayan data siyo tabude wani daki tace sushiga dashi, dakin ta ne ananma kuhayla tayita zare ido tana mamakin kayan dakin, sai wani plasma acan gefe da kujeru alamun babban dakine aka rabe gefe aka mayar mata dashi falo, kujerunta masu kyau sai can kuma wani table ne da kujera laptop ne akan gurin, suna shiga zaemah ta tattare komi kayan abayan tahau sama ta dauko wani babban akwati ssnnan ta sauke akasa tazuba kayan abayan sannan turaruka ta daura akan dressing mirror. Tajera takalmomin ma a shoe racker, sannan tace zauna kiji abinda zance Kuhayla tazauna agefen gadon dataji laushi sosai, tazauna dakyau sannan zaemah tafara dacewa “Na tambayo inna kizauna ananne, saboda wasu dalilai karki damu kisan dalili, but nadai gayamiki gona zakije toh tunda munsiyo kayan aiki saimufara aiki ko, ? Yanzu kullum zakina ganin aikin daga gobe zamu fara, nan dakin zamu zauna nidake, kisake ranki nagayawa umma zandaukoki kike kugaysa , kuhayla tafice don gayshe da umma. Yayinda zaemah tashiga bandaki tayi wanka sannan tazauna akan sallaya tayi sallah taroki Allah ya gafarcewa sadiq, tanayi hawaye na zuba a idonta, taroki Allah yabata saan cika alkawarin data dauka, dakuma cikawa sadiq burinshi, tana idarwa saiga iphone din kuhayla na kara tana dubawa taga rahama ce tadauka acan kuma rahma tace lafiya yau shiru? Gobe kishirya dawuri fa muwuce, zaemah tace tana gurina karki damu zanna kawota, rahaama tace awh anty yakike? Suka gaggaysa dai, rahama tace anty yah haidar fa inaga kaman ba lafiya ba, wlh yadawo duk kaman mai zazzabi ko zaki kirashi kiji, zaemah tace badamuwa karkidamu zankirashi, tana kashewa tayi tunani lalle kalmominta ne suka masa ciwo donhaka saita danna waya takirashi har wayan tagama ringing baidauka ba, donhaka saita share kawai Haidar kuwa yana kwance kansa ciwo yake sosai, yarasa ina zaisa kansa, yasha maganin anma kai kam har lokacin, yana ganin wayan zaemah yayi tunanin karya dauka taji muryanshi zata gane meke damunsa, donhaka yaki dauka , haka kawai tunanin sadiq yadamesa , hawaye zafafa suka kwaro masa, indai yatuna sadiq sai gabanshi yafadi, saikuma yafara tunanin kuhalya, yakamata yashare yarinyan, saboda idan abokinsa na nan bazaiji dadin cewa yana tunanin masa budurwa ba, donhaka, mikewa yayi yadauro alwala yafara sallah yana rokon Allah kar kiyayyen dayakeyi yadawo so, don kar yaci amanan abokinsa, yana kuka yana share hawaye yana cewa Allah ya ceceshi yakuma ji kanshi, ji yayi ya tsani kansa, lallai aganinshi aure yaharamta tsakaninsa da kuhayla tunda ko sadiq na raye bazai taba aurenta ba, [6/9, 9:05 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Ya na idarwa yabi yakwanta dahaka bacci mai nauyi tadaukeshi Zaemah ce ta tashi kuhayla tashi kishiga wanka tunda kikayi asuba kin mike kin kwanta agurin, kuhayla tamike zaemah tamiko mata wani sabulu avon, tace kina wanka da wannan daga yau, tana shiga kafin tafito zaemah tafito mata da wani riga da sket na atamfa exclusive. Baki da. Launin ja sannan da gyale baki tadauko takalmi ja da jaka ja shima dukka na vincci , sai black dankunne, masu kyau da agogo azurfa mai kyau, kuhayla nafitowa tazaunar da ita agaban mirror tace shafa mai shima avon ne, tashafa powder sleek, tadauko red lips mac tabata tasa sannan tace ungo wannan janbakin sashi ajakanki a matsayinki na mace karki rabu da janbaki da turare, tabata kayan tasa da inner wears all red, sannan tabata turare oud sharqiya, sannan ta shafa body spray tace tsaya naganki da kyau, saidatayi grading dinta ta gyra mata gyalen tareda cewa kisa gyalen haka. Yafi aji anfi kuma ganin mutuncinki [6/9, 9:17 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Kuhayla tadanyi murmushi wanda kyanta duk ya bayyana, bata taba fitowa haka da gyale tayi daras da itaba sai ranan donhaka taji dadi sosai itakanta tasan tayi kyau, gashi zaemah tadaura mata dankwalin irin yanmatan zamani, yayi fanka takarshe. Zaemah hijabi tadauka sannan taja mukullin mota, muje ki karya kigayda umma muwuce, suka isa falo, anshirya dinning tsaf ummace akai tana cin abinci sannan suka gayaheta suka zauna suma, zaemah sai surutu take, umma nikam ina yaah yusuf (yayanta wanda suke uwa daya uba daya) umma tace kema kinsan yau kintashi dawuri baifito ba tukun suka karya da soyayyen dankali da kwai sai tea, zaemah tajawota suka fito inda suka shige motan fuuu tajasu sai atbu, alokacin rahma takirata tareda cewa kina ina? Kuhayla tace kofar skul of science. Toh nima ganinan zuwa takashe wayan. Suna isa gun kuhayla tasauka sannan tace kijira rahama tazo ku gaysa mana! Zaemah tace inbatayi sauriba tafiyata zanyi, kuhayla na tsaye rike da jakanta wanda ta tusa wayoyinta da bironta aciki, tana kallon zaema suna dan magana alokacin saiga wata benz tadanno, motan baki ne tasha tint, zaema tace ga rahaman can, kuhayla tace laaa yakikaganeta? Tayi murmushi kawai domin tasan haidar ne a motan yakawo rahma, rahma tafito tana tahowa itama kuhayla tafara isa gunta runguman juna sukayi rahma tace woow, u r lukn soo btfl, ohh emm gee kiganki? Kuhayla sai murmushi take dimple din fuskanta ya dada bayyana, zaemah kuwa hankalinta nakan motan tabbas tasan yatsaya kallon kuhayla ne donhaka itama saita tsaya kawai taga ikon Allah [6/9, 9:26 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR haidar kuwa yana daga zaune ya tsaya yana mamaki kuhayla ce haka? Ya ilaihi salam dubi yadda take haska gurin gaba daya? Yaah masha Allah! Sai maimaitawa yake duk tunaninsa baya gane meyakeyiba , doguwa ce , yar tarwada tana da dan haske dai, abunda yafi burgeshi da ita shine manyan idanunta dakuma karamin bakinta wanda akwai wushiryanta aciki tana da kiran kalangu wanda hausawanmu kecewa coca cola shape, domin macece iya mace, ga sajen gefen fuskanta yazubo yadda shiyafi dagawa maza hankali yake janyosu gareta balle inmuka gangaro kan idanu, toh nidai benaxir barinyi shiru haka ta isa, shi baitafi ba shi ya tsaya, haka zalika itama zaemah taki tafiya sai addua taje aranta. Don motan tint ne bazata sami daman ganin wake cikiba anma tanada tabbacin ae lallai kallon kuhayla yake, sukuwa karasowa gun zaemah sukayi tasauke glass din motan suka gaysa sannan tamayar tarufe, suka shige dept dinsu, ahankali yaja motan zaema tabishi abay suk fita daga akuk dun, sannan ya mata sighnal ta tsaya, fitowa yayi sanye yake da farar tshirt da wando jeans yatoshe idonsa da glass donkar zaemah taganw halin dayake ciki bude masa motan tayi, yashiga sannan suka gaysa, anan tabashi hakurin kalmominta yagwada mata bakomi sannan yace kiyi hakuri, inaso infadamiki cewa bazan iya soyayya da kuhayla ba yanzu ta haramta agareni, donhaka ko zanmutu inaso kimin alkawarin cewa bazaki yarda na aureta ba,arazane tajuyo tana kallonshi [6/10, 9:02 PM] Adda bena: 6 1 BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Tace kaifa kanada problem, how on earth zaka fara wannan tunanin? Just try that mistake and youll die regretting it. Kanason yarinyan nan for God sake, its beta kaje kayi shawara da zuciyanka dax ol i can say for now, yadafa kanshi ke bazaki gane bane? Sadiq fa ita yaso. Kuma yayi niyyan aurenta akanme zanci amanansa? Tace yoohh toohh ai shine ma kare hakki, tunda kasan yana sonta kuma he was protecting her. Saika daure ka idda masa burinsa, marry her, show her care nd love, shine burin sadiq, kar kuhayla tayi kuka ko regreting wani abu, kadaiyi tunani bude kofan motan yayi sannan yafice yana tafiya yana goge fuskansa, don gumi yahada kanshi yayi zafi, shidai baida abunyi da kuhayla yanzu ko zai mutu yana sonta ne bazai auretaba, don tamkar cin amanan sadiq ne, Kuhayla a skul tashiga lectures anan tafita har karfe hudu sannan tajira rahma data gama nata tashirya tsaf ta fito tashige motan, rahma tace wlh ke ko mikomin wayanki, ke ko dan whatsapp din zamani bakiyi, da wani waya kikeson yi? Kuhayla tace samsung, ta bude purse dinta sai ta ciro card din 1500 guda biyu, ta loda mata, sannan tayi sake sakenta, tace gashi namiki subscription, barin fara miki downloadn, anan ta mata downloadn whatsapp , bbm, da instagram tabude mata tsaf tsaf, sannan ta gwada mata yadda akeyi, tayi inviting dinta, tasa mata pin din ramlat, haidar, dakuma na zaemah , saina nana, dakuma na. Yaa yusuf tace duk wannan yan kusane namiki adyn dinsu, saikuma mayb idan kinada frnds saiki kara, whatsapp kuma gasu numbobin dakike dasu, instagram zamu hadu nakarasa miki bayaninshi, takunna motan tafara tafiya sannan tace yakamata ki koyi mota ma wlh muna canje atukin, har gyda suka isa ta ajiyeta sannan tawuce Intakaita labari haidar don ya nisanta kanshi tattarawa yayi yatafi u.s don cigaba dawani kamfanin mahainfinsa, [6/10, 9:18 PM] Adda bena: 6 2 BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Yayi hakanne don ya nisanta kanshi daga kuhayla, zaemah tana hankalce dashi bata kara masa maganan kuhayla ba don kar ya rainata yaga kaman cusa masa ita ake, donko bbm dayayi accepting basu taba magana ba, ita tsoron mishi magana take shikuma girman kai, har whatsapp ma, ahaka wasa wasa acikin sati uku kan kuhayla yawaye duk wani shiga wacce ya mace zatayi taji da kanta toh

Chapter 4 of 6