Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 6
bainufi ko inaba sai gurin daya tsaya jiya, rahma tayi mamaki ramlat kam chatn take ko ajikinta, suna tsaye saigata tazo ta rsaya agefe, ashe kai gogan ka kara shaka, yadanna wani horn saidata juyo ba shiri bude motan yayi yafita dakarfi wanda itakanta sai data tsorata tafara jaa da baya. Sai yau taganshi a tsaye, namiji iya namiji anma duk hankalinta yatashi ayadda yadanno kanta tazata zaimata shegen dukane. Yana isowa gabanta ya tsaya cak, idonta arufe ne ko kiftawa tagagarayi saboda tsoron mezai biyoba, hasken fitilan gefen gydan ya haskata dam ya kare mata kallo for the very first time of his life daya mata kallon sama zuwa kasa, saikuma yaji yagagara matsifan dazaiyi din, ciro kudin yayi yamika mata, har lokacin idonta a rufe bataji yadaketa ba kuma bata budeba. Tadaisan mutum na gabanta. Rahma ce data fito tabiyo bayansa wanda itama a zatonta ko dukan zaiyi, tace ki karbi kudin, alokacin ta bude idonta a hankali, tamikaa hannu zata karbi kudin har da tsugunawanta alamun ladabi. Alokacin rahma tace yah sadiq ne yace akawo miki dafatan ba matsala? Tace babu nagode sosai Allah saka da alheri, tana fada tana share kwalla a idonta. Rahma ta matso gefe tace gobe inbai dawoba zanzo nabaki kinji? Tace to anty, rahma dariya yakamata wato yau dai tazama anty [5/25, 4:40 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Haidar juyawa yayi zaitafi alokacin rahma tace meye sunanki? Cikin sanyin murya tace KUHAYLA!, haidar dayake tafiya cak ya tsaya ya maimaita aransa KUHAYLA! Rahma tace you have a nyc name, sai nazo, tadan rungumota kuhayla sai godiya take, yana shigan motan yafara horn, rahma tajuya tashiga aikuwa kaman jira yake ya kara fusgan motan, yana tafiya harwani fushi yake, rahma dai abin nasa yabata tsoro , mutum ya gwadawa mutum tsana kiri kiri, suna isa suka fice suka barshi dama ramlat kam hotone bawai tayi wani abu bane, yana shiga bandakin yasake ruwa akanshi, maimaita sunan yake yi aransa for no reason, Kuhayla!, ji sunanma ko dadi babu. Yaja tsaki sannan yakashe yafito, kiran sadiq yayi tareda cewa wlh inbaka dawoba. Kasan yadda zakayi dawannan yarinyan, sadiq yace kayi hakuri dai don Allah flight din safe zanbiyo, hey wait kaje ne yaudin? Haidar yaja tsaki tareda cewa da zanzauna kannena suje sumaka bauta? U must b craxy. Nakaisu ne nadawo dasu [5/26, 8:12 PM] Adda bena: 6 BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Sadiq dai baice komi ba yakashe wayansa acewarsa kawai haidar na neman hanyan musgunawa baiwar Allahne, washegari da sassafe yataho bauchi donkar a maimaita masa irin najiya, yana isowa bayan magrib ya idar da sallah yayi wanka sannan yafto bai nufi ko inaba sai gydansu baiwar Allahnsa. Yasha kamshi da kyau, akalla yajira na mintuna ashirin kafin tafito, kasancewar tasan haidar ne mai zuwa kwana biyu batasan cewa yadawo ba, hakan yasa tazo daidai inda zata karbi kudin, yayi murmushi yabude mata kofan. Taji dadi sosai tabude tashigo tana murmushi ina wuni? Ya amsa da lafiya yakike kwana biyu? Tace hakane, sai yah haidar ne yake xuwa, ya gyada kai yau nazo hirane, inaso kimin tadi, tadanyi jum sannan tace wani labari kakeso?, yace inaso kigayamin labarinki wacece ke? Da komi naki, tayi shiru tayi mamaki sarai. Wato dai bazai fito direct yatambayi sunanta bane, ya gwammaci yayi indirect, hakan yasa ta yi murmushi sannan tace rayuwata bata cike da wani abu mai dadi dazaka sani, duk babu dadi , gwarama karkasani tun farko, yadan bata rai sannan yace , nidai ki gayamun da dadi ko ba dadi. I want to knw. Tayi dariya sannan tace toh barin fara baka, [5/26, 8:43 PM] Adda bena: 7 BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Sunana KUHAYLA USMAN, haifafiyar garin gombe ce. Mahaifina malami ne mai anguwa, mal usman yayi auren saurayi da budurwa da mahaifiyata inna lami, ita kadaice matarsa anan suka fara haifafa,suka haifi azeema, azeema ce yar fari saikuma ni ta biyu sai kannena maza guda uku,, kabir,abba, dakuma umar , muntaso cikin kulawa da tarbiya kasancewar babana babban malami kuma mai anguwa dukka suna ganin mutuncinsa, iyayena suna kokarin bamu dukkan abinda mukeso duk dacewa bawani wadata suke dadhi ba, ahaka wataran abbanmu yarasu, tuni dangin abba suka fara saka innanmu agaba. Don gydan damuke zaune ma yayan abba yaxo yace nashine bana abba ba, dakyar inna tasamu filin gadonta na mahaifiyarta a nan garin a wunti tace mudawo. Muna dawowa da watanni axeema tasamu mijin aure, akasamu dakyar aka daura auren. Ta tare. Toh shinefa kannena suka dawo nan makaranta, inna tana siyar da kosai don tasamu abinda zamunaci, nikuma sainake dinki , ahaka keken dinkin yabaci nasamu dakyar naroki wani yazo yagyramin tunda yatafi dashi baikara dawowaba,, shine azeema tace nazo gydanta nazauna akwai wan gydan babban mutum agefe sai ina masa wanke wanke ahaka ko zaa samu mutaimaka ma inna, inna bataso haka ba anma bayadda ta iya, azeema tabada hujjojinta [5/26, 9:11 PM] Adda bena: 8 BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Hakan yasa inna tayadda, aikuwa inafara aikin dan maigidan yafara nunamin so, ranan yarufeni adaki ina kuka, dakyar aka cetoni, shine matan gydan suka hadu sukamin duk acewarsu nice karuwan basuga laifin dansu ba. Hakan yasa azeema taji haushina don lokacin case akayi babba, azeema tayadda cewa karuwancin nake dana dawo gyda shine tace karna yadda nakoma gun inna donkar inna tassn meke faruwa zata san yadda zatayi, bayan sati biyu, dahaka kawai wata kawarta tazo tabata shawaran tana turani gud evening ba karamin taimako zansamu ba tunda Allah yabani kyau da diri. Hakan yasa azeema tabi shawaranya tamanta cewa daga ciki daya muka fito, toh Allah yataimakeni, kawata firdausi tana da aure harda yarta a gombe muka tashi da ita anma tana zama a bauchi, danaje gunta saitace ina zuwa kullum ina karba, ahaka tarinka bani idan kaje zaure saina zauna a lungun nayi bacci can tsakar dare sainatashi nashiga ciki saina bata kudin, abun mamaki mijinta baitaba tambaya ina nake ko ina nake xuwaba, ko yatambaya bansan ita meta fada mishiba, watarana naje gun firdausi natarar. Batanan sai mijinta. Natambayeshi ko tabar sako yace bata bariba anma nazauna najirata, ni bansaniba ashe kullum innazo muna wasa da dariya shi sona yake ni bansaniba kawai yafaramin surutu yanaso yadanneni, alamun kaman yasha wani abu hakan yasa nafita. Dasauri don nagudu yana jawo rigata, cak na tsaya don ganin firdausi nayi agabana, zagina tafarayi acewarta naci amanarta tanata kuka tana surutu, nikuma ina kokarin mata bayani anma taki yadda hakan yasa nafice nabar gydan , ina komawa gyda natarar da azeema a tsakar gyda bata amsa gaysuwa na ba, tamikomin hannunta alamun namiko mata kudin , nace mata yau bansamu ba, mikewa tayi tafara zagyna, tsinanniya laananniya, nayi shiru ina zubar da hawaye, inaso na mata bayani, jan tabaryar gefenta tayi tafara jibgamin ajiki, nayi kuka harna gode Allah, ranan banyi bacciba ta rinka uzuramin akan washegari na nemo kudi, inaso naje gurin inna anma ina tausayin inna da kannena, yaxama dole na nemi hanyan dazan taimaka mata inna har ciwon kafanta yasa bata iya tafiya, hakan yasa najure duk wulakancin yayata bantaba furtawa inna ko naje ba, washegari naje da asalin niyyan nemo kudin muka hadu dakai [5/27, 8:10 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Toh duk lokacin da kaban kudi na kanshiga zaurene na kwanta bacci can tsakar dare saina tashi na shiga ciki, dama duk wani aikin gyda ni nakewa axeema , narasa meyasa ta tsaneni nafi yadda ko dan cewa abba yafi sona akanta ne oho, mutanen anguwansu bata taba gwada musu cikinmu dayaba, cemusu take ni yar riko ce a gydansu shiyasa tadaukoni, hakan yabude wa mutanen anguwan bakin gayamata maganganu da bakin shawara akaina, kuma tsaf takebi, nidai bantaba furta komi ba asali ma ni kokarina don nataimaka wa innarmu nake zaune da ita, duk maganan da takeyi. Hawaye ne ke zuba a idonta, taarasa yadda zatayi ta tsayar da kukanta, sadiq hannunsa nakan stiyerin motan damka hannunsa yayi dakarfi yabuga motan zuciyansa namasa tururi, yarasa meyasa yakejin wani iri a game da ita, duk tausayinta ya cikasa, yadan gyra murya sannan yace kiyi hakuri komi na duniya mai karewa ne, yanzu inaso kimin alfarma, kikaini gurin inna ko, yaya azeeman zata yadda? Inyaso sai nasan yadda zanyi ki koma gun innan dazama, zamanki anan hatsarine, tayi shiru sannan tace bansaniba wlh, kuma zunzurutun kiyayyane yasa takemin haka, yayi shiru sannan yace kijeki yanzu zamusan yadda zamuyi kinji?,ta gyada kai tareda cewa Allah yakaimu, tabude kofan takarbi kudin tare da masa godiya, tafice, yakai akalla minti ashirin agun yagagara motsi sai daga baya yasamu dakyar yatuko motan gydansu haidar yanufa yayi horn [5/27, 9:55 PM] Adda bena: 0 BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Maigadi na budewa yashige dasauri don yasan suna da kallon ball yau kuma yayi latti yana shiga fridge yanufa yadauko coke sannan yazauna, hankalin haidar na kan tv baimasan yashigo ba saiganinshi yayi agabansa, nan suka gaysa suka cigaba da kallon, bayan sun gamane, sai haidar yace banganeba duk kacanja, kokuma kahadu da badluck ne a abujan?, sadiq yace inaafa wlh naje gun kuhayla ce taban labarinta wlh abun tausayi, duk dayasan wacce yake nufi sai yace wacece kuma kuhayla? Yace wanda ka tsana dinnan. Yaja tsaki can ta matse muku, change the topic please, , rahma ce tashigo tareda murmushi tana cewa yaya sadiq yaushe ka dawo? Yana dariya yace baruwana dake fa, dazu na dawo, tazauna agefensa tareda cewa ya kuhayla take? Yana murmushin jin dadi yace lafiyanta lao wlh yanzu nabaro gunta, raahma tace wlh yaa sadiq nikam inaso tazama kawata kahadamu, haidar ne ya danka mata harara saikace mayya daga ganin mutum sau daya kice kinaso haka akeyi? [5/27, 10:26 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Tadan tsume fuska kaidai yah haidar ka tsani yarinyan wlh tanada hankali. Ga alamu kuma tana cikin damuwa ayyadda yah sadiq yafadamin nikam kabarni nasamu ladan taimaka mata, yayi shiru dai baikulata ba, yana zaune sadiq yafara bata labarin rayuwan kuhayla, hawaye tafarayi, sadiq yayi dariya sannan yace kudai mata sarakunan tausayi, gogan naku yaki tashi yatafi ya baza kunne yanajin komi dasuka gama baidai ce uffan ba, saiyaji yakara jin haushinta for no reason, haryana mamaki dakanshi why ya tsani yarinyan, anma ko bakomi yanaso yaxauna yaji ana tadinta, itadai rahma kukanta tasha sannan tamike tafice daki, alokacin suka fice domin yarakashi yatafi suna fitowa har sadiq yashiga mota. Sannan yace abokina kamin alfarma inaso nafara neman kuhayla anma don Allah karage tsananta bana jin dadi ko kadan wlh, sannan duk lokacin dakaji tsanantan kadaure kana boyemin haidar yayi shiru haka kawai yaji gabansa yafadi saiyace toh bakomi, yashige gyda, washegari abin mamaki da yamma haidar yakira sadiq yace idan zakaje gun kuhayla kabiyo kadaukeni first, sadiq yaji mamaki anma yayi farinciki sosai, donhaka lokaci nayi yazo yadaukeshi suka tafi, suna isa yatarar harta fito don sundanyi latti, tazota tabude motan tashiga, dama tun ahanya haidar yace ya tsaya yakoma baya karya gwada yazo dashi, dake kuma motan tint ne hakan yasa cikin sanyin murya tagaysheshi suka fara magana. Magananta daddaya cikin sanyi. Muryanta da shagwaba , shidai haidar yana sauroro anma baice komi ba,anan sadiq yace mata yaushe zasuje gun innan? Ta ce duk randa kashirya yace bakomi , nan yafara cewa ke koyaushe cikin hijabi? Karki kuskura nasaki agaba fa. Zansiyo buhu nakawo miki, tayi dariya wanda shi haidar dake baya har ransa yaji dariyan tsantsan sanyin muryanta dayadda takeyi cikin jan aji, da shagwaba wanda halitta ne daban ita Allah yamata cikin ikon Allah sukayi tadinsu harsuka gama baice komi ba, tayi sallama tafice. Duk da cewa sadiq baiso hakaba yanaso ace ko da gaysawa suyi anma yaji dadin da haidar yazo kenan yana kokarin yaga yadena tsananta. Haka yaja suka fice, nima dai benaxir ina biye dasu, saidai akwai ayan tambaya, wani irin tsanane Haidar yakeyi? Yamasan meyakeyi kuwa? Toh dai kubiyoni don jin yadda abokannan zasu kare da baiwar Allah kuhayla [[5/28, 8:26 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Washegari ma haka ne yafaru domin kuwa haidar yaraka sadiq gydansu kuhayla yana zaune abaya, yana zaune sukayita hiransu yana saurarensu, yace sadiq dan mikomin wayanka, yana karba yaje duba hotuna, yabude bluetooth dinsa yafara turawa, hotunan kuhayla ne dama sadiq yace masa yadauketa hoto dayaje gunta hira da rana. Yatura yakashe bluetooth din nasa,sannan yaci gaba da sauraronsu,yadda kuhayla take bayani da magananta yasa duk yabi yana tausayinta, ashe yarinyan is soo innocent. Ko da zasu tafi bayan yadawo tagaba. Sadiq yace yakagani? Yanzu ka yadda cewa batada matsala? Haidar yaja tsuka oho dai, ni duk tadin ma baku iyaba, gobe bazanzoba baku iya komi ba , sadiq yace ayya baka ganin kokarin danakeyi don nasamu ne nataimaka takoma gydan mamanta tabar gydan wannan yartan, duk danasan bakasan komi akanta ba, haidar yace dama menasani kuwa?suna rabuwa haidar yanufi tredysys yamika musu wayan tareda cewa kumin printing hotonnan, 10copies anayi yakarba yawuce gyda ya watsa ruwa wayansa yadauko sannan yadanna wayansa, ana dauka yace kazo ina nemanka a gyda, falo yasauka yatarar da rahma tana cin abinci, yakuwa zauna yanajiran umasu masa abincinsa, aikuwa suna jerawa yaci a hanzarce a daidai lokacin maigadi yace ana sallama dashi fita yayi yasameshi wani saurayi matashi, yace ina wuni oga, haidar yace lafiya aiki nakeso amin,yace toh oga , yaciro hoton a aljihunsa sannan yamika masa, yace komi na rayuwanta nakeso kanemomin, a gwallaga take. Sukayi sallama yafice [5/28, 8:54 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Dakinsa yakoma kan gadonsa yahau, yarufe idonsa, zuciyarsa na masa turiri. Yarasa meyake damunsa idan yarufe idonsa itaa yake gani, muryanta na yawo a kwanyarsa, buga kansa yayi dakarfi akan gadon, yana rike kansa, salati yake yi, yarasa yazaiyi da rauwaryasa duk tsanan yarinya yamasa yawa, toh tarabu dashi mana, yawani jaa tsaki sannan yakara juyawa. A.c din dakin na aikinsa,ga kamshin turarensa duk yacike gun, yahadu saiwani irin jiri yakeji, tuni zazzabi tarufeshi, zuciyanshi natafasa, dakyar yadauki waya yakira rahma tashigo dassauri don yanayin dataji muryarsa, yah haidar meya sameka? Baice komi ba anma dai yana rike da kansa, tafita dassauri takira momy wacce take zaune a falo, tuni suka gangaro domin suka menene itada ramlat, hankalinsu yatashi ganin halin dayake ciki, domin abune mai wahala aga haidar ya kwanta ciwo, tuni momy tadanna waya takira family dr. Dinsu anma baya gari acewarsa yatafi wani program abuja hakan yasa suka fice kawai suka wuce reemee clinic, anan aka bashi gado, likitan yake sanar dasu migraine ne dakuma jininshi daya hau, momy hankalinta yatashi sosai, sai surutai take, haidar mekuma yafaru jininka tahau? Kaida damuwa baya zama aranka? Tajuya takalli rahma tareda cewa ke meyasameshi? Tayi shiru tareda cewa momy wlh ba abunda yafaru , nasandai yadawo lfy, sukayi shiru gaba daya, itadai momy tagagara zama, bata kaunar ace haidar yakwanta ciwo. Kuma Allah yasa bamai yawan ciwon bane [5/28, 9:10 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Bayan likitan yagama bada maganunguna andaura masa drip,yace abarshi yayi bacci kar adameshi. Hakadai suka zauna har asuba bawacce ta runtsa, dasafe nema ramlat da rahma sukayi gyda akan zasuje sudawo sai ita momy ta tafi, sadiq ne ya iso asibitin a firgice don yaji labarin meya sami abokin nashi, anma har lokacin bai farkaba, sai wuraren 9. Anan suka kira likitan yazo yadubashi, har lokacin kan haidar na ciwo, kuma duk runtsawa kuhayla ce a idonsa, bayan sun gaysa da sadiq, sadiq yace kaikuma daga rakiyan hira sai ciwo? Haidar cikin sanyin murya yace meruwanka?,sadiq yace oho dai, zakaji dashi, suna haka momy tahado mishi abin karyawa. Memet yaki ci yadamu a sallameshi yakoma gyda anma likitan yaki yarda,sadiq yafice akan zaije yadawo, haidar dai ba yanda baayi yafadi meke damunsa ba yace shikam babu, momy tabata rai tace kasan sarai duk lokacin dakasamu migraine da kuma jininka yahau toh ba lafiya ba. Donhaka kagayamin tun wuri, anma haka haidar yakafe yace babu, hakadai suka rabu dashi, Can bayan magrib sai sukaji sallama rahma ce adakin momy da ramlat suntafi gyda, , haidar na zaune agefen gado sadiq yashigo bayansa kuma kuhayla ce sanye da babban hijabi kaman kullum, sukayi sallama suka shigo, muryanta ne yadoki kunnensa dasauri yadago yakalleta, kirjinsa na bugawa tazauna agefe rahma ce ta rungumota tareda cewa kawas dina, yah sadiq yaki kaini gurinki tana murmushi kanta akasa, tace zaikawoki insha Allah, mikewa tayi tazo gefen haidar kamshi yaji yadoki hancinsa lumshe idonsa yayi, sannan yayi shiru yayinda zazzakar muryarta tadoshi kunnensa tana maicewa yajikinka yaya haidar? Bai amsaba. Don shi bayama duniyan gurin, takara maimaitawa alokacin rahmace tace dasauki rabu dashi haka yake bayason magana tunda ya kwanta, itadai kuhayla shiru tayi tasan tsabar tsananta dayayine yasa bai amsaba, toh yazatayi? Itakuma burinta taga yana magana kokuma taga yasake ransa, anma idan tana wuri shiru yakeyi, sadiq baiji dadiba hakan yasa ya lumshe idonsa tareda cewa mutafi inkingama, rahma tace haba yah sadiq dawuri haka? Yace inaso namayar da itane saboda kar dare yayi. Rahma tamike da niyyan rakasu, dazasu tafi tajuyo tace sai anjima yayah ta ajiye ledan drinks data shigo dashi ahannunta, baice komi ba dama she didnt expect him to say something, suna ficewa yadafa goshinshi kanshi ne yayi wani irin sarewa yaji kaman ansamar guduma5/30, 10:31 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Koda suka fice rahma tabi sawunsu inda tarakasu har jikin motan, tareda yiwa kuhayla alkawarin zataxo, suna rabuwa takoma asibitin, hannuna akan goshinsa yarike,tace yahyah yajikinka? Ko inkira likitan ne? Ya girgiza kai a a kibarshi, tadai zauna anma hankalinta duk nakansa,ahaka sukaji anyi sallama aka bude kofan, rahma dasauri tamike tayi gun dasauri tana cewa anty zaemah,tarungumeta kaf kaf kaman bazata saketa ba. Zaemah tayi murmushi tareda cewa sakeni nikam karki nakasani, tayi kan haidar wanda tunda yaji muryanta yayi lamo kaman yayi bacci. Tazauna agefensa sannan tace baby nasan idonka biyu kabude kawai mugaysa yanzu zantafi, rahma ta kwashe da dariya tareda cewa kedai har yanzu baki canja ba, zaemah tace yoh toh gaskiya ne kina abu kaman bakisan waye haidar ba. Ido daya yabude sannan yakara juyawa, aikuwa tariko kunnensa ba shiri yamike, arayuwa inzaka cucesa toh kataba mishi kunne, yaja tsaki ke wlh tlh kincika takuri. Rayuwarki da matsi. Tace ohodai naji mike oya, gayamin yanzunnan, gun aiki ko mace, yace kaman mefa? Tace gun aiki ko mace i mean aciki aina aka takuloka, ka kwanta ciwo? Kadaisan cewa sarai baka kwanciya haka banza siddam ko? Yace ni ba abunda yasamen, rahma ce tayanke maganan tareda cewa saidai ingurin aiki anma har yau baida budurwa, tace kiyi shiru bakisan wannan ba, yanzu haka macece ya tsaya girman kai da zurfin ciki bazai fadaba, rahma dariya tayi tareda ficewa tabasu guri, tasansu yanzu haka tadi zasuyi karta hanasu sakewa [5/30, 10:39 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Tana fita tace oya gayamin rahman batanan, yabata rai tareda cewa ke da Allah kirabu dani joh, nace miki ba komi, tace intayi tsami ill be the first to knw. Yace yaushe kika dawo? Tace jiya daredare. I had a though time wlh. But nadawo hutu nida komawa sai bayan sallah, bana dani zaayi azumi, Wacece zaemah? Zaemah ahmed tare suka taso da haidar, duk jida kanshi dawani rayuwansa toh banda zaemah, idan zaa tambayi waye haidar? Hatta momy bazata bada bayanin da zaemah zata bayarba, kawarshi ce sosai saidai yagirmeta, suna gama secondry school a command day, aka turata sudan karatu, tana karanta medicine. Toh shine fa har shi haidar yafita yagama yadawo batagama ba, karatun sudan da dadewa, duk wani sirrin haidar zaemah tasani, macece fara doguwa ga gashi asalin bafulatana ce, ga kunya anma kusancinta da haidar yasa tasake dashi sosai, tanada farinjini gakuma saukin kai da faraa, macece mai son tsabta da kwaliyya yana daya daga cikin dalilan dayasa haidar yake mutunta fiye dasayran mata, tafiyanta baisa sunrage shakuwansu ba, saidai of recent da karatu yamata zafi kasancewar tana shekaranta na kashe yasa basu samun time din dazasu gana, saudayawa haidar yakanje sudan domin ita, kowa yasansu tare, kuma abun mamaki abun nasu ba soyayya ba, don shikanshi haidar yasan saurayinta kuma suna shiri sosai, zaemah macece mai wayo da basira, tanada mugun hangen nesa da karanta mutane. Shell definately be a good dr. Ko dama tayi niyyan yimasa surprise ne tazo gari, daga baya aka sanar da ita yana asibiti hakan yasa tadaure karta kirashi don kawai yaganta a asibiti, zaemah ahmed kenan [5/30, 10:50 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Suna zaune ana tadin yaushe rabo. Har likitan yazo anma tsuf haidar yace yanaso a sallemeshi. Ana maganan saigasu momy sundawo anan tayi mamakin ganin zaemah tace adaren nan kika kinkimo kikazo? Tace momy ai ansan nan zanzo, yace dama kinsan tadawone ? Momy tace tunjiya tadawo tashigo gyda ta samen ai, yace aida kincemata na mutu, likitan ne yayi dariya don shi duk atunaninsa ma zaemah budurwar haidar ce. Suka yimagana anan aka sallameshi gabadaya suka dunguma gyda, sai sha daya zaemah tashiga gydansu, shima dakyar momy ta hankadata, don zama sukayi a falo da ita da rahma da ramla dashi kanshi haidar din, saidai duk kokarinsa daya boye damuwansa zaemah tagane yana cikin damuwa. Tana isa gyda tabi lafiyan gado. Ahaka dai yafara samun sauki kullum suna tareda zaemah a gydansu ko gydansu zaeman, watarana sadiq yace yakamata taje taga budurwarshi tave toh badamuwa, suka shirya tsaf lokacin haidar yadawo yace inazuwa? Tace gwallaga gurin budurwan sadiq, ya harari rahma datake gefen motan tareda cewa munafuka kekika ingizata ko? rahma tace kai yayah wlh bani bane, zaema tace yooh toh meyene don munje? Kai inzakaje shiga mutafi, bashiri kaman jira yakeyi yace jirani nayi parking aikuwa yana parkin yazo tsum yaduru yashige, tanajan motan tanacewa yoh ni wacce yarinya sadiq ya kwakulo a gwallaga tundaga gra? Rahma tace anty zaemah wlh tahadu sosai fa. Saidai ustaziya ce, zaemah tave zamu gani ai, suka kirashi yace shikam yanagun saisun iso, rahma ce tamata kwatance harsuka isa. Haidar nan da nan ya tsume, zaemah ta kalleshi meye haka kaman ka ziyarci mutuwa? Rahma tace wlh haka yakeyi idan yazo nan, tace banganeba?raaahma tace wlh ya tsani yarinyan munrasa meta masa. Salati zaemah taja innalilah wainna ilaihi rajiun, rahma tace lafiya? Zaemah tadan matse tareda cewa babu muje, suka bude kofan alokacin sadiq shima yabude suka fito yauma kaman kullum tana sanye da hijabi, zaemah daga mota tana kallonta anma hankalinta inyayi dubu yatashi,, budurwar sadiq ce toh meke shirin faruwa?Allah yasa tunaninta karyazo daidai, anma indai haidar din datasanine. Inhar ya tsani abu toh zaizo ya so abun kamar ranshi zaifita, yadda idan baisamu abunba zaishiga tashin hankali, tadai daure tace sannu budurwarmu [5/31, 7:32 PM] Adda bena: 2 8 BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Kuhayla ta rusuna tareda gaysheta kasancewar tun kafin su karaso saadiq yamata bayanin wacece. Rahma tayo kanta tareda rungumanta oyoyo kawas, kunya sai yarufe kuhayla, haidar kam yadai bude kofan mota anma yaki fita yarasa yazaiyi sadiq ne yace bazaka fito ayi hirat dakai ba? Aikuwa kaman jira yakeyi sadiq yayi magana yahade rai tareda cewa kuyi daga can, yafito dawayansa duk abinda yakeyi akan idon kuhayla, abun yabata mata rai. Talura yanzu abunnasa yadawo iskanci donhaka itama saita share tacigaba da abunda takeyi , ashe gogan naku yayi hakanne donta gaysheshi saikuma yaga tadaga kai. Abunsai ya sosa masa zuciya ya tunzura, yaji yakara tsananta. Kanshi atake ta sara. Gefen kan yarike sannan yakoma yajingina kannshi ajikim kujeran motan, zaemah talura dahakan sai tace yanzu medaya zaayi ne? Sadiq yace ke bazaki ganeba, yajuya kan rahma tareda cewa nasamu jiya dakyar nashawo kanta tasamu yayanta tace zatakoma can gyda dazama, yayan taki yarda anma duk dahaka nace tashirya donhaka yanzu gydan nasu zamu wuce, kowa sai yashige mota kawai. Itadai kuhayla duk tsoro yacikata akan abunda sadiq yasata tayi kirikiri yace tacewa antynta zataje gun inna takoma can dazama. Data gwada mata dawani kudin, saita ce mata zata na fita kullum da wayo yadda takeyi anan, anan hankalin yar yatashi acewanta batada hankali kinaso kikashemin uwar tawane? Jakar yarinya ! Kizauna anan ba inda zakije, toh kasancewar dama tuntunu tana neman hanyar tafiyan batassmuba, kuma abunku da mutum kasaba takura mishi randa yasamu wuri bazai maka ta dadiba, aikuwa tuni kuhayla ta fita mata a giya, tace zankoma wajen uwata, kuma baki isa kihanani ba, idan kika nemi ki takurani zangayamata duk halin dakika jefani, sai mugani dani dake wazai fara kasheta [5/31, 7:43 PM] Adda bena: 2 9 BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Ta tsorata da kalamun da kuhayla tajefeta dashi, nan ta tabbatar gwara ta lallabeta anma ina kuhayla tace ita gyda zata tafi, idan tabarta bazata fadawa inna komiba, inkuma tahanata zata tafi kuma zata fada komi, hakan yasa tabarta kawai badan tasoba, shikenan dan kudin datake samu yanzu duk babusu, a gabanta kuhayla tashirya tsaf ta ajiye kayanta tafara jiran sadiq, Ko da ya iso fitowa tayi kawai, alokacin data bashi labarin abinda yafaru ya jinjina mata. Acewarsa yancinta tanema domin yau idan yafadi yamutu wani hannu zata shiga?suka jeru tsaf ga motan sadiq gakuma motan zaemah suna tafuya ajere harsuka isa cikin wunti suna cikin tafiya har suka isa, kuhayla tace ya tsaya saikuma yaga tana kalle kalle, sadiq yace lafiya? Tace gabana ne yafadi, yah sadiq dafa gydan nan gydan kasane, dan karami haka, toh kagafa yanzu yadda yadawo? Babban gyda harda gate dan daidai? Anya inna basu tashiba? Sadiq yace rabonki dakizo tun yaushe? Tace gaskiya nakai kwana 41,, yace toh kisauka muji inda suka koma, tafito alokacin zaema da rahma ma suka fice tace musu nanne gydan anma inaga suntashi don da bahaka gydan yake ba, inaso nayi tambaya, saisuka tsaya jum haidar daga cikin mota yakare wa gydan kallo, aikin yayi kyau, yadanna wayansa yasa a kunne, sannan yace kunbasu takardan gydan? Daga dayan bangaren akace ae, sai yace meyasa kukayi painting brown? Nace muku kuyi blue that is her best colour, nan suka fara masa ban hakuri, yakashe wayan adaidai lokacin zaemah tabuga masa windown yabude tace bari mushiga ciki mutambaya, yace toh, cikin rashin damuwa da abunda zasuyi, suka shige saiga sadiq ya iso, cikin mamaki yace munshiga uku yanzu ina innanta suka koma? Haidar bai bashi amsa ba. Dama shima baisa ran zaabashi amsan ba [5/31, 7:55 PM] Adda bena: 3 0 BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Cankuma saiyakara jan tsaki, anma wlh kosu waye basu kyautaba dazaa rushewa su kuhayla gydansu ba, bayin Allahn dasuke nema wa kansu na ci, Can ciki kuma kuhayla wacce take tafiya a tsorace gabanta duk ya tsinke yafadi tanaso taji ina innarta takoma, Allah yasa ba gombe bane,suna duruwa suka buga gate din, ahankali maigadin yabude tareda cewa sannunku, kuhayla tace ina neman wandaa suka tashi ananne, yace anya? Wlh bansaniba, sai zaemah tace malam sannu don Allah masu gydan suna nan? Yace ae hajiya tana nan. Suka duru tareda cewa barisu ganta, kuhayla kam sai kallon gydan takeyi cikin mamaki, inba ikon Allah ba wazaice wannan gydan kasan zaidawo haka? Suna isa suka ga kofan abude ga takalmuka sukayi sallama suka shiga, bakowa a falon donhaka saisuka zauna a lallausan kujerun falon kamshi yake. Ga plasma inda yake kunne, wallpapern falon blue harda labulen ma, kuhayla duk da tana cikin hankali saidataji dadi arayuwanta tanason blue colour, sundade azaune kafin sukaji motsi kaninta tagani abba yashigo da gudu da abun wasa a hannunsa, tace laah abba ya iso kanta da gudu oyoyo adda! Suka rungume juna tace ina inna? Wani gyda kuka koma? Waye mai wannan gydan, abba yace nanne gydanmu ai, dazaayi gyra ne muka koma gydan anty lami, ana gamawa muka dawo. Bata bude baki tayi tambayan gaba ba saiga inna dagudu ta rungumeta. Mata kyakyawa da kyaun siffa, kamilar mace maabociyar faraa tashigo tana musu lale marhaban. Anan aka shigo musu da drink dakomi, suka gaysheta sannan kuhayla tace tadawo gunta yanzu, ta kuma mata bayanin kannen sadiq ne, inna tace ayya duk da batasan waye sadiq dinba tabar tambayan saisuntafi, anan inna tadage

Chapter 2 of 6