su haidar
sushigo , zaema tasan sadiq zai iya shigowa
anma tasan haidar ko zaa kasheshi bazai
yadda ba, saitace bari agwada kiransu
atunaninta in haidar bazaizo ba toh shima
sadiq kawai ya tsaya
[5/31, 8:04 PM] Adda bena: BAR RAINA
ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Tana
fita taga basama tare, kowa na mota, haidar
tanufa tabude motan sannan tace mamanta
nason kushiga kugaysa, yazaayi. Ba musu
yace toh, tayi jum tasan its unlike him,
amma tace fito muje. Ta isa gun sadiq
shima tagayamishi shima yayi mamaki anma
yaji dadin hakan, suka shige atare, har falo
akamasa iso suka rusuna suka gayda inna,
itadai inna idonta nakan haidar aduk
tunaninta shine sadiq din tamusu godiya
sosai. Har abun yabasu mamaki, bayam
sungama suka fito anyi anyi dasu susha
wani abu sukaki sadiq ne ma yadauki zobon
haidar kam ko kallo bai isheshiba,suna
fitowa kowa yanufi motansa, haidar nashiga
yayi dialing cikin fada yace meyasa baku sa
fridge babba ba? Wannan fridge din kaman
zaa ajiye ruwa kadai? Ku tabbata kunje kun
canja banason rashin hankali, yakashe
wayan, , aciki kuwa zaema sukace zasu tafi
har waje onna tarokosu tanata godiya suka
shige mota suka tafi, Kuhayla nashiga gyda
tace inna meya faru? Tace kwantar da
hankalinki nabaki labari, Watan dayafita
farkon sa ne ina zaune sai umar yashigo
yacemin ana sallama dani awaje. Namusu
iso wasu mazane subiyu, sukacemin anbasu
contract din gyran gyda yadawo sabo, nace
waye sunce yace kar afadi sunanshi, suka
tattaremu sukace nafadi inda zanje nazauna
ko na sati uku ne, sunyi alkawari a sati uku
zasu gama, naje gydan lami, nayi nayi da
bayin Allahn nan sufadamin sunki, kuma
sukace karna sanarwa kowa nadai gayawa
mijin lami yace nabisu ahaka , anma
najadashi dasu sunyi magana. Kuma tunda
sukayi magana dashi sunce sunhadashi da
ogansu wanda yasa ayi aikin bayan sunyi
magana mijin lami yace nazauna ayi
aikinnan, shima shiyayi gyran wutan gydan,
kinsan aikinsa kenan, a sati uku suka gyra
nan tsaf duk abinda kikasani namu sundauke
suncanja da sabo, tashi mujr kiga dakin,
suna tafiya suna gani. Gyda tsaf tsaf dakuna
biyu da falo daya sai kicin da tsakar gyda an
zagaye gydan, [5/31, 8:14 PM] Adda bena:
BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA
BENAXIR OMAR Suna gama gyra suka dawo
damu nasamu sun ajiye duk wadannan
kayan abincin, kuhayla tabude baki tareda
cewa inna anya ba yan kungiyan shan jini
bane? Tace toh ai nima na tsorata anma
kinga mijin lami yace na kwantar da
hankalina alherine. Yasan wannene anma
yace kar afadi sunanshi, nayi iya tunanina
narasa waye. Kuhayla tace inna anya ba
sadiq bane? Inna tace yasan gydannanne?
Tace toh ai matsalan kenan baisan nanba,
toh waye? Suka gama tunaninsu basu kawo
kowa aransuba nimadai benaxir omar ina
gefe ina jimamin meyasa haidar zaiyi haka,?
Kuma yaboye? Nifa wannan bawan Allah
alamarinshi nada rikitarwa, komadai waye
sukam sunsa albarka, ranan kuhayla batayi
bacci mai kyauba sai sallah take tana
godewa Allah, yanzu basu da damuwa,
innarta tace kullum dasafe sai anshigo musu
da biredi dakuma dubu biyar suce inji
ogansu yace ayi cefane ko washegari da
akakawo kuhayla ta tike dan aikan tace
saiyafadamata yace shikam saidai yamutu
anma bazai fadaba dole ta hakura tabarshi,
wunin ranan haka tazauna jugum, hatta
kayan sawa an ajiye musu, kuma abun
mamaki da ita da kannenta dakuma innan
iya kansu aka siyo kaya aka ajiye, koma
waye yanashan adduan Alheri , inna tace
tunda yanzu angama aikin ai sai afadawa
azeema tazo tagani ko? Kuhayla tace ae
hakan zaiyi, zanje nafada mata kokuma inna
kibari itaama tazo tagani zaifi armashi
yabata mamaki, innan tabari ahaka, daredare
da sadiq yazo tayimasa bayanin komi
shikanshi yaji mamaki yace mata bashi bane,
toh kodai abokin abbanku ne? Tace anya?
Mudai munsa ido zamu gani ko wayene,
muna mishi adduan alheri, Allah yabuda
masa, yasaka da alheri. Suka gama hiransu
sannan tafice, tana fita haidar dake gydan
baya yafito yashiga gaba yaja dogon
numfashi, sadiq yace kana tunanin waye?
Haidar yace ta ina zansani? Batada
admireres ne?,sadiq yaja tsaki wani admirer
kuma, gaskiya wannan abu baiyiba, kowaye
its lyk ansiye zuciyanta fa, just luk at d way
shes talkn, soo happy nd free, haidar yace
toh ai saikayi godiya wa kowaye, yace akan
me? Zanbincika nagani ai, muga waye
yakeso ya tarwatsamin tunanin ta, inason
kuhayla sosai fa [5/31, 8:26 PM] Adda bena:
BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA
BENAXIR OMAR Dahaka suka isa gyda,
shidai haidar yanajinshi baice komiba, suna
isa yatarar da zaemah abakin kofa, sadiq na
ajiyeshi yakoma, yace meye kinwani tsaya
anan kaman wanda nayi laifi, tace laifin kayi
ai, zo nan muyi magana, suka zauna ta ciro
documents din gabanta ta ajiye agabanshi,
dasauri yadauke meye haka? Akan me
zakimin bincike adaki? Tace saikayi ai,aina
kika samu extra key? Tace dawannan
tambayan daka amsamin nawane?, wannan
yarinyan itace sadiq yake nema. D gal u soo
much hate nd will soo much love. Harara
yabata mai lafiya tareda cewa ke wlh kincika
kwakule kwakule why would i love dat village
gal? Tace ahap zamu gani ai, yanzu tell me
d truth kai kayi wannan renovation din ko?
Kanshi yadafa. Idan akwai mayyan mace toh
tabiyo bayan zaemah yarinyan so smart, duk
hanyan wayonshi tsaf take tikeshi. Yace
ohkay naji naji mekikeson sani?tace first of
all mekayi akanta? Yace babu fa. Kawai
nasa anmin underground bincike ne akanta,
den i renovated d house daz ol i did. Sai
admsn danace asama mata a atbu, zaemah
tayi murmushi sannan tace kamanta
budurwar abokinka ne? Yace toh aibasonta.
Nakeba, i hate yarinyan. Wlh shi yaroken i
should show some kia atleast. Daz y i tried
to help, tace toh meyasa kaboye masa ai
samiu gayamishi ko, ya zaro ido nooo don
Allah karkimim haka. Don Allah it should be
a secret a tsakaninmu wlh tlh bazai ji
dadiba, ta ce hmm kaidai bakada gaskiya, i
have to advise you, be very careful hes your
frnd, dnt ruin ur frndship
[6/2, 7:03 PM] Adda bena: 3⃣4⃣BAR
RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR
OMAR Shiru yayi ya gagara furta komi, sai
can yadaure yace wlh bahaka bane karkiga
bakina. Ba sonta nakeba fa. Am just tryn my
best ne but tunda kinyi magana bazan
karaba, itadai tajishi ne ahaka aanma bata
yarda ba, don canja tadi ma yayi inhar ana
maganan kuhayla aguri toh gabansa fadi
yakeyi, Kuhayla na daki taji sallama mai aika
yakawo aika, tamike suka gaysa takarbi
biredin dakuma dubu biyar din, saitaga
yamika mata wani kwali da leda sai
envelope, takarba tace nagode wannan
nawaye? Dan aikan yace nakine, oganmu
yace ki karanta wasikan dake ciki, yana
tafiya tanemi gu akan kujeran tazauna
sannan ta ajiye ledan tabude kwalin, tana
budewa taga letter yafado, tabude takaranta
kamar haka Hi Dont panic, ive charge d
phone already, on it and we shall talk,
Mr.right Tayi shiru tana tunani, tunda take
sadiq baitaba mata wasika ba, shiru tayi
tana tunani ahankali taciro wayan, galaxy 6
edge ce golden colour, takunna anyiwa
wayan full charge anyi settings ga layi aciki,
tana duba numbers din taga abun mamaki,
numban innanta, saiwani number ansa
mr.right taduba numban mtn saitafara
dialing, can ta tuna hala ba kudi saita kashe
taduba account din dubu ashirin tagani saida
tadafa kirji tana salati [6/2, 7:15 PM] Adda
bena: 3⃣5⃣BAR RAINA ALLURA KARFE CE
NA BENAXIR OMAR Sannan tace cikin takaici
wlh mutuminnan inaga kudi ne yamasa waya
inbahaka ba awani dalili kawai zaisa dubu
ashirin awaya?, dialling numban tayi harta
kashe baa daukaba, saidata kira sau biyu
sannan sai yakirata. A zuciyanta tace oh
kafin yakira ma saiyaja aji, duk ta kagu
tasan wayene, tanaso tasan muryarshi
sannan idan sadiq ne tasan zata gane don
haka daya kira saita tuna ajin daya jamata
duk da batasan waye bane saitaki dauka
itama tana rike da wayan ahannu Can fannin
haidar kuwa dama a safiyar ranan yasiya
mtn double sim, yayi rechargn dinta sannan
yabada akai mata yarike dayan layim, don
yasan zata iya nunawa sadiq in yayi amfani
da numbanshi kuma baisan me zaije yadawo
ba, dayaga kiranta dadi yaji anma yaki
dauka da gangan acewarsa yanaso tagama
kira sai yakirata don kar kudin daya samata
yakare, aikuwa baiwar Allah itama dayafara
kira yags yakira har sau biyu taki dauka, sai
yayi shiru yasan dagangan ne donhaka
saiyayi shiru kawai yana jira yaga gudun
ruwanta, daya kira sau biyu bata dauka ba
itama saita fara kiran, shima saiyaki dauka,
nan tasaka ranta a inuwa. Wannan bawan
Allah yafita boris da rikici gashi duk ta kagu
taji muryanshi, tana dauka tayi sallama cikin
isa da mulki ya amsa sannan yace how are
you? Tayi gum lallema ba bahaushe bane?
Tace am fine, nd you? Bai amsa dinba sai
yafara magananshi kaman haka Check out
the envelope given to you. Go through
everything and do as it says, do not tell
anyone abt these, i mean ANYONE!!!, bai
saurari mezatace ba yakashe shiru tayi
tabbas wannan ba sadiq bane, koma waye
itakam jitayi gabanta nafadi, mugun
tsoronshi taji. Tabude komi ahankali
credentials dintane tayi mamakin yadda
akayi sukaje gun. Sai ga admsn na atbu
dakuma screening form da date dakomi,
bude ido tayi sosai. Tana so tayadda da
abunda tagani, tsalle tafarayi alokacin inna
tana cikin gyda tana tattare tattare saiga
kuhayla tayi kanta da gudu, inna nasamu
maakaranta, inna ta tunkudeta sannan tace
shine kikeso ki karyani? [6/2, 7:27 PM] Adda
bena: 3⃣6⃣BAR RAINA ALLURA KARFR CE
NA BENAXIR OMAR Yadda inna tayi
yatabbatar mata dacewa inna tasann da
maganar bata gayamata bane kawai. Tace
inna baki murna? Inna tazauna tariko
hannunta hawayen dasuke makale duk suka
zubo, tace mekikeso nace yar nan? Farin ciki
wataran bazai yiwu fuska tadaukeshi ba, ina
zaune Allah yaturomin bawan Allahn dazai
sharemin hawayena, inafatan Allah mishi
albarka yabiya mishi bukatunshi, kuhayla ma
hawayen ne ke zuba tashare idon innanta
sannan tace inna insha Allah bazan baki
kunya ba ,inna tayi murmushin karfin hali,
tana shigewa daki tahau kan gado zaune
take anma hankalinta duk ya tattara kan
bawan Allahn dabatasan wayeba, babbane?
Yarone? Farine? Baki ne? Guntu? Siriri?
Babu tunanin dabatayiba , dasauri taciro
wayan ta tana danna layin da zummar takira
shi saikuma taji switch off, txt msg tafarayi,
da hausa tayi anma data tuna yadda yamata
dasauri itama tagoge tassmu tahada mishi
da turanci don kar yace bakauyiya ce,
aikuwa ta tura tadauko files din tana dubawa
daddaya, abin mamaki arayuwanta tana son
zama architecture, kuma abun mamaki shi
tasamu akabata, wannan abun da daure kai
yake komi nata bawan Allahn nan yasani
yazatayi da rayuwanta, tazauna tayi kukan
farn cikinta sannan ta goge idonta, Haidar
yadawo daga duban wani fili dazai siya,
yazauna yadauko wayan dayasiya
musamman akan kuhayla kunnawa yayi da
niyyan yamata txt ko ta gani, sakonta ne
yashigo mishi yabude sannan yafara
karantawa All thanks to you, am having a
meaningful life now, Mss.left Shiru yayi yana
murmushi yarinyannan tana da wayo, wato
yamata short nd brief shine itama tamasa?,
hmn ashe kuwa zaayi wasan txt, yadanna
reply Good of you, Mr.right Yana turawa
yakashe wayan tana gani takira taji switch
off, bata masa replyn ba, saima shiri
datafarayi zataje gydan azeema
[6/3, 9:30 PM] Adda bena: BAR RAINA
ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Tana
isa gydan azeema ta tarar da ita a tsakar
gyda tana share tsakar gydan dayasha datti.
Ta rusuna ta gaysheta, ta amsa cikin faraa
tareda tambayan yakowa da kowa. Kuhayla
tace lfy lao, tana zama takawo mata ruwa
kaman abun arziki suna gaysawa suna tadi,
har kuhayla tace inna ce tace nazo na sanar
dake cewa munsamu sauyi a gyda kije kileka,
tayi shiru sannan tace nifa kicewa inna
bantara wani kudin dazan taimaka mataba,
nikaina ina fama dakainane yanzu, dubu
daya zan iyabayarwa kikai mata, kuhayla
tayi murmushi sannam tace zaifi kyau ai kije
dakanki tunda tanaso kije ko, itadai azeema
duk gani take kaman inna tana mata wayone
taje gyda ace tabada kudin wani abu, tace
toh kicemata zanzo, bashiri kuhayla ta
kimtsa tsaf tafice ta isa gyda tasanar da
inna abunda azeema tace, inna haushi taji
tareda cewa wannan yar bansan meye
matsalar ta ba, daga maganan nan shine
zatadau maganan kudi? Haka ai baidaceba,
ni wlh banason haka. Inna dai tayi mitanta
harta gama azeema kam hakuri tadage take
bata, hartasamu tayi shiru tace bazata kara
kulata ba inbatazo gydan taga meyake
faruwaba, bayan magrib tashirya tsaf tana
jiran sadiq yazo, yana isowa ya aika akirata
ta dauki wayanta ta ajiye don akunna musu
generator wanda yana daga cikin abunda
haidar ya ajiye musu a gydan, tadau turare
tafeshe jikinta tsaf tayo wa inna sallama
tana fitowa tashiga motan , suka gaysa
kanta a sunkuye yace kwana biyu ko
kinemeneni? Tayi dariya sannan tace
bangama marmarin sabon gyda bane, yayi
murmushi sannan yace haryau bakiga
wayeba? Tace ae, dahar zatace masa
yakawomin wayama saita tuna msg din
dasauri tayi shiru, tace ankawomin admsn fa
na atbu kuma architecture, wlh naji dadi
sosai, zuciyansa ne yaji ta buga dakarfi
wannan wani irn abune? Shikam yashiga
uku, shiru yayi sannan yace kinji dadi ko?
[6/3, 10:05 PM] Adda bena: BAR RAINA
ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Tayi
murmushin farin ciki sannan tace naji mana
sosai, yayi shiru sannn yace yayi kyau, ga
waya nakawomiki tunda yanzu kindawo nan
gurin inna bawanda zai takuraki, yamika
mata kwali, da sim card kaman karta karba
anma batada hujja donhaka takarba kanta a
sunkuye tareda cewa magode Allah kara
budi, baice komi ba yace zanzo ran monday
muje nakaiki kiyi komi suka danyi hira
sannan tashige gyda, tana shiga kawai dakin
inna tayi tanuna mata wayam, inna tayi shiru
sannan tace angode Allah yayi albarka
wacce wayace wannan kuma? Kuhayla
tabude kwalin, iphone 6 ce fara sol, saitaji
son wayan yashiga ranta, tace inna wlh
wannan wayan fa sabuwar fitowa ce naga
ana tallanta a tv agydan anty azeema,
wancan ma da aka kawo wannam samsung
din shima duk sabbin fitowa ne, inna ta
jinjina sanman tace toh Allah yabasu lada.
Tadauko chargern taje tajona sannan tadauki
dayan samsung din takunna txt msg tagani ,
Hi, Pray before sleeping Mr.right Shiru tayi,
lalle ma, da shi yake mata adduan, abunma
dariya yabata donhaka itama saitayi replyn
Hy Noted. Mss.left Takashe wayan, tamike
tabi lafiyan gado Ran monday karfe bakwai
sai ga dan aika da bread dakuma 25k yace
ance abawa kuhayla 20k saikuma wani jaka
kaman troley tabude tsaf tagani abaya ne
baki, yasha duwatsu masu tsada, sai jaka
kirar fendi wanda akalla zata kai dubu sittin
a kudinmu na nja, saikuma takalmi kirar
Alexander mcqueen dubu arbain ce ita, ga
turare JAR don baacire tag din ajiki ba $800
akudinmu na nja yatashi. Dubu casain, (abun
na karyane, lalle haidar dagaske yake ).duk
dacewa ita kuhaylan bata gane tsadansu ba ,
itadai sunmata kyau, tayi wanka tasha
powder a fuskanta tafito tsum, da ita yar
cas, abayan kaman angwadata aka dinka,
tana fitowa taga sadiq awaje tashiga motan
kamshinta duk ya gigita shi [6/3, 10:24 PM]
Adda bena: 9 BAR RAINA ALLURA KARFE
CE NA BENAXIR OMAR Suna isa gate din
atbu taji wani irin dadi, tunda take bata taba
tunanin zatazo makaranta ba, suna shiga
agurguje yaje akayi musu komi, kasancewar
sadiq din nada hanyansa, duk inda ta gifta
sai anjuyo ankalleta, haryafaraji kamam ya
boyeta, tayi balain kyau, suna tare sai ganin
haidar sukayi yafito a motarsa, wanda dama
yarigasu shiga makarantan, yana kallonsu
suka gama komi, tana ganinshi tajiya kanta,
yamika hannu wa sadiq suka gaysa, asace
yakalleta saidayaji wani mummunan kishi
dayaga wasu abaya suna kallonta, yarasa
yazaiyi sai cewa yayi kungama ne, kutafi
mana toh, sadiq yace ahn tare mukazo ne?
Kodai kazo gurin watane bakaso muganta?
Itadai kuhayla tanason gaysheshi tana
tsoron kar ya bounsa ta tasan halin shi,
gogan kuwa Allah Allah yake tamishi
magana, tadai daure kaman ta karanta
zuciyanshi sannan tace ina wuni, yadanyi
jum kaman bazai amsaba , sannan yace
lafiya ya makaranta, cikin sanyin murya tace
lafiya. Baikara cewa komi ba suma wucewa
sukayi,sadiq hanyan federal low cost da ita
yayi, tace mezamuyi kuma anan? Yace
zamuje siyan frozen chicken ne, tace ahah
ba akwai a kasuwa ba? Yace ke bari, bazaki
gane wannan bane, daban take kazan ga
zaki, gashi a saukake kawai siya zakiyi,
harda kifi fa nan rahma take damuna muzo
tasiya wai zatayi ferfesui, adaidai junction
din federal low cost suka tsaya, takaranta
sighn board din H&S aqua and poultry, ya
fita yaje yashige shagon, can gashi yafito da
ledodi a hannunsa, yashige dasu ya ajiye
abayan motan, sanna yashigo suka wuce,
suna isa gyda yace dauki leda biyu kika wa
inna kice tamuku kuji yatake. Gobe dasauri
zaku nemoni, dariya tayi tareda cewa kaidai
kawai gayamin santi kakeyi, yace wlh bazaki
ganebane saikin ci tukunna, sukayi sallama
tashige gyda, a kitchen tadirewa inna
taredacewa inna ga kaji wai. Inji sadiq ki
girka kici saikunnenki ya sinke. Inna tayi
dariya tareda cewa nikam zan iya gyra kaza
kuwa yanzu, kuhayla tabude ledam tace laaa
inna aibasai kin gyra ba agyre take tsaf ,
zokigani, taleka taganshi tsaf tsaf tace ahto
kawo wuka kawai na yanka muwanke ai anyi
mai wahalan, suka yanka sannan kuhayla
tawuce dontayi sallah, tana shiga daki taciro
wayanta cikin jakanta, tana budewa taga
msg tashigo Hy Frowning your face make
you look ugly Mr.right
[6/4, 5:37 PM] Adda bena: BAR RAINA
ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR
Tunani tafarayi, toh lallaima yau yaganta
kenan? Wayene? Haidar?,dassauri ta kawar
da tunaninta wannan dan rainin hankalin
bashi bane. Shidaa ya tsaneni ma kuma
inzaiyi ai sadiq zaifara sani, tayi iya
tunaninta tarasa waye donhaka ta ajiye
wayan tayi sallahn da ake binta, ko da inna
tayi ferfesun taje tazauna taci nayi nak, inna
kuwa bakinta yagagara shiru, acewanta
kuhayla zatana kawo mata don taji dadin
kazan, ko da sadiq yazo kuhayla tayita
mayar masa da yadda inna take yaba kazan,
yayi murmushi yace aina gayamuku dadinsa,
suna hira yakara jajjada mata yana sonsa,
daya tashi tafiya yace takirasu abba idan
tashiga tana shiga ta kado su, dama suna
fomwan da inna tasakasu tuntuni, suna
fitowa ya ciro akwatuna kanana biyu yabasu,
abba ne yakeja, kabir kuma yana turawa
daga kasa har suka shiga, suka kara fitowa,
yace sudawo suna dawowa bayan sunkai
yabasu envelope yace sushiga dashi, suna
shiga suka kaiwa kuhayla wacce inna tatike
da matsifa akan tamayar da kayan, tana
cewa wannan yadawo kwadayi da son
zuciya, yazaayi ki karba?, tace inna wlh
bansan abunda zaibayar ba kenan kiyi
hakuri, suna shigowa suka mika mata
envelope din, ta bude sai ga kudi suka zubo,
rafar dari biyar guda biyu saikuma letter.
Tadauki letan tafara karantawa Kawata!
Gashi kiyi hakuri kowa nakowa
gudumawarsa na sabon gyda nima ga nawa,
Rahma. Tace inna rahma cefa!, kanwar yaah
haidar wannan marar dariyan, inna tace
tohhh ai kin gode anma yayi yawa wlh,
kinemeta kimata godiya, tadauko iphone
dinta takira sadiq sannan tace masa yaturo
mata numban rahma, yace toh, tana
kashewa taga numban [6/4, 5:48 PM] Adda
bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA
BENAXIR OMAR Tadauka takira yana ringing
biyu tadauka, kuhayla tace. Rahma kuhayla
ce, rahma tace aw aw kawas yakike yagida
yasu inna? Tace lafiya lao, munga kaya
mungode sosaii sosai Allah kara budi yabar
zumunci, rahma tace bakomi kawata,
wannan ne numbanki ko? Zaanyi savn, har
zata kashe rahma tace yauwaaaaa naji yaah
haidar nacewa kin shiga atbu mesuka baki?
Tace architecture, tace wow daidai kenan
zamuna haduwa nasamu kawa, dama ramlat
tagama project, munxama mubiyu kuhayla
tace ae zamuyi registration upper week, suka
kashe wayan, taduba akwatin kayan sawane,
atamfofi masu kyau harda super aciki dasu
holland, da takalmuka da jaka, sai mayuka
da kayan kwaliya, atamfofin duk adinke,
kuhayla taji dadi sosai har ranta. Rayuwar
kuhayla haka tacigaba da gudana, sadiq a
sati yakanzo hira sau biyu, yana iya
kokarinsa ganin ya kyautata mata, yayinda
haidar kullum dasafe yana aika bread da
kuma 5k, saikuma daya lura timing yayi
yakara aikawa da kayan abinci duk kokarin
inna tagane waye takasa, anma mijin lami
kam yasanshi yakuma cemasa karya bari
kowa yasan shine, acewarsa ihsani yake,
ganin mijin lami yasan komi shiyasa inna
takwantar da hankalinta akan maganan, a
sati na biyun ne kuhayla taje sukayi
registration sannan suka fara lectures, sadiq
ne yake kaita harta gama registration,
saikuma admission dinshi yafito na masters
dinshi dazai karayi, a kasan u.s donhaka
tuni yafara shiri, yanzu hankalinshi yadan
kwanta ganin kuhayla bata cikin damuwa,
duk iya kokarinsa yagano waye ke taimaka
masa yakasa, da yaje yariko mai kawo musu
biredi gurin mijin lami aka kaishi, mijin lami
kuwa cemasa yayi wanine yakeso yasauke
nauyin daya dauka wa kansa tun abbansu
kuhayla na raye [6/4, 5:56 PM] Adda bena:
BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA
BENAXIR OMAR Don abinda haidar yace
yafada kenan sanin cewa dole watarana azo
gunshi tambaya, dawannan hankalin sadiq
ya kwanta, dazai tafi yadire mata kudi a
account, sannan yaje gurin haidar daredare
ana washegari zaibar kasa yace haidar don
Allah zan rokeka alfarma, don Allah haidar
nasan bakason kuhayla anma zan damka
maka amananta,haidar cikin sanyi rai da
rashin damuwa yace ban karba ba, sadiq
yayi mamaki sarai, har ranshi yaso yabaci
yace haba haidar tsanan dakake mata aisai
ka rangwanta tunda kana ganin idona, haidar
yace a a kam gaskiya bazan iyaba, kabawa
zaemah, tunda ita saura sati uku ne sugama,
last week ma tatafi zata dawo upper week,
ko farkon nxt month, sadiq yayi shiru sannan
yace bakomi ni zantafi sai anjima sarai
haidar yasan ran sadiq yabaci toh anma
yazaiyi?, ya isa yadauki alkawari yazo asami
matsala? Idan sadiq yagane yana mata
hidima ai zasu batane saiga kaman sonta
yake (uhm haidar fa baiyadda yanason
kuhayla bane kutayani jin wannan abun
haushin ni benaxir ), gwara yabarshi akan ya
tsaneta kar azo susami matsala daga baya,
BENAXIR OMAR Sadiq kuhayla yakira awaya
duk muryanshi a dishe tace meya faru kuma
dan wurina? Yayi shiru sannan yace zaemah
kitaimaka don Allah inaso nabada amanan
kuhayla agun haidar yaki yadda, kinsan ya
tsaneta, tace uhm ,sannan yace tunda zaki
dawo upper week bashikenan ba? Tace toh
kabarta zankira rahma zasuna dubata, duk
da bazatana fada mata matsalolinta ba
anma zanna magana dasu. Karka rike haidar
arai yanada dalilansa tunda kaji haka, sadiq
cikin dacin rai yace a a kam wlh
musgunamin yakesonyi, tun randa nafara
ganin yarinyannan kwata kwata ya tsaneta,
tayita bashi baki dakyar yahakura. Tana
kashe wayan tayi shiru tana tunani, lalle
haidar yayi dabara dayaki yadda, don da ya
yarda idan sadiq yazo yagane yana sonta
zaiga kaman don ya bashi amananta ne,
baisan cewa tun fil azil yafara sonta ba.
Tadai bar komi don tafara final exams dinta
dazata dawo complete medical dr.
Specialized in denistry, Yana gama wayan
gydansu kuhayla yanufa yashiga sukayi
sallama da inna, tayita mishi waazi duk
jikinsa yayi sanyi,sannan yafito kuhaylan
tabiyoshi abaya, tafito idonta a kasa duk ya
kumbura tasha kuka sosai, don bata kaunar
yayi nesa da ita, duk dacewa sonsan baiyi
wani tasiri ko nauyi akanta ba anma inda
sabo yasaba da ita , cikin muryarshi data
dishe yace Kuhayla inaso kisan wani abu a
rayuwa, bakomi kake so kake samuba,
hakuri zakiyi karatunnan na shekara daya ne
kacal zanyi nadawo, sannan bayan haka.
Inaso kisa akasan ranki, ina sonki, jini da
tsoka kasan ruhina duk ina kaunarki kuhayla,
kirike min amanar kanki. Ki kama min kanki,
ki adanamin kanki sannan ki kiyaye
minkanki, Allah na taredamu nasan na gina
soyayyata akan gaskiya da tsoron Allah,
karki bari mutanen atbu ko mazan atbu su
toshe miki basira sumiki wayo, ki kama
kanki kirike mutuncinki ko ina kema zaa
mutunta ki, akwai rahma akwai zaema,
akwai haidar duk. Zasu kula dake, kuka take
sosai, tarasa yazatayi da ranta, haka
yagama waazinsa, yace zantafi sai
watarana, tafito a motan duk tagagara
magana. Sai tanufo kofan gydan, haryaja
motan tashige ta tsaya a falo tanata kuka,
yakara dawowa kofar gydan yayi shiru yana
tunani ji yake kaman ya kwasheta yatafi da
ita, saidayagama tunaninsa yaja motan
yafice. Wayarsa yadauka sannan yace
zaemah munyi sallama don Allah ku kulamin
da ita. Karku bar wani abu ya cuceta,
zaemah kuhayla ruhita ce, nabaki amananta
duniya da lahira, zaemah shiru tayi dontafara
tsorata mutum yana wani magana magana
ko gani yake kaman zaa kwasheta agudu da
ita? Ko zaa aura mata wani,?
BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA
BENAXIR OMAR Haidar saidaya tabbata
sadiq na gyda sannan yaje wuraren sha
daya. Yace masa naxo muyi maganane,
sadiq dai bai nuna bacin rai ba yace inajinka,
sannan yace masa don Allah kayi hakuri,
tsoron dauka maka alkawarine nazo nagaza
cikawa Allah yatambayen, kayi hakuri don
Allah abokina zanyi iya kokarina, sannan
idan kana tunanin na tsani kuhayla wlh ban
tsaneta ba, saidai kawai banjina asake game
da ita. Shidai sadiq yanata saurarensa
haryagama, sannan yace bakomi wlh, yasu
momy nikam banzo na gaysheta ba yau,
bamuyi sallama ba, katayani mata don Allah
gobe zanwuce gombe nabi flight kafin
nawuce abuja, den saimu tafi, sukayi sallama
cikin nutsuwa irin tasu ta maza masu ji da
kansu, yafito yarakoshi sannan yawuce
yatafi, yana dawowa gyda yabi lafiyan gado,
Washegari da sassafe sadiq yayi hanyan
gombe yaje duk yayi sallama dasu sannan
yayi bookimg flight, but kasancewar
weathern very bad babu jirgin dazai tashi
alokacin, shikuma bayiso yayi misding flight
dinshi na 11 na dare zuwa u.s donhaka
kawai yakarbi mota don yawuce abuja, harya
wuce jos ahanyan titin, wanda wasu manyan
motocci ne agabansa, yana kokarin yaga
yawucesu,wayarsa ce tayi kara da kaman
bazai dauka ba harsai yawuce sai kawai,
yaga kuhayla ce bashiri yadauki wayan,
jiyayi tana kuka, hankalinsa tuni yatashi duk
yabi yarude sannan yace lafiya kuwa? Motan
data kwaso buhuhuna tayo kanshi yayi iya
kokarinsa yaga yakaucewa wannan trailern
saikuma ya fada kan hanyan wata trailern. Ji
kake kiiiiiiiiiiiiii Innalilahi wainnailaihi rajiun
shine salatin da mutane akasari dasuke cikin
motocinsu suka rinkayi, gaba daya motocin
dake baya duk sun cunkushe, fitowa akayi
akayi kan moton sadiq motonshi duk ta
ruguje ba ta ganuba, dakyar akasamu wasu
suka fito dashi anma duk jikinshi jina jina,
babu rai, innalilahi wainna ilahi rajiun,
wayarshi ma duk ta fashe, anrasa dame
zaayi amfani aganeshi, sai wallet wani ya
tsinto dakyar aka duba sai ga i.d card dinshi
na aiki a fcmb, saikuma atm dinshi dawasu
kudade mai uban yawa hoton kuhayla ne
agefe sai nawata mata wanda duk ya
tabbatar musu mamansa ce da matarsa, sai
card dasuka gani Aminu haidar & sons, nan
da nan suka dauki numban. Sai kira, Haidar
na zaune masu abincinshi sun jera masa
abincinsa , don karfe daya ce ya idar da.
Sallah yayi wayarsa tayi kara, baidauka ba
yaci gaba da cin abincinsa, ganin dayayi
wayan tanata ringin yasa yadauka tareda
sallama, sai mutumin yace don Allah anyi
hatsari ne anan, mukeso muji ko kasanshi,
wani mai matrix baka lambar gombe, a titin
abuja,haidar yace anya? Gaskiya banganeba,
yakashe wayan, yayi shiru yana tunanin
waye nashi a gombe ? Dazai tafi abj, yatuna
da sadiq anma yasan sadiq bayabin mota
sai flight, bai idda tunaninsa ba saiga rahma
tana waya takaraso takashe tareda cewa w
kuhayla ce duk tabi tadamu wai fa suna
waya da sadiq taji shiru yanzu wayar tasa
akashe kuma yace zaitafi abuja,
[6/4, 6:39 PM] Adda bena: 4⃣5⃣BAR
RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR
OMAR Haidar yace baki cemata in mutum
zaishiga jirgi kashe wayansa yake ba? Basu
karasa ba saiga ta takara kira haidar ne
yakarbi wayan tareda cewa ke anayamiki in
mutum zaishiga jirgi yana barin wayansa
akashe ne? Tace ba jirgi yabi ba fa, baisamu
flight ba wai ana ruwa a gombe shine yabi
da mota, har zaiyi magana saikuma yayi
shiru yace mekikace gombe? Tace ae karfe.
Sha daya yakiran yace yadau hanya da
mota, kashe wayan haidar yayi sannan
yakira wannan numban mutumin duk jikinshi
na bari rahma tanacewa meye yah yah? Yayi
shiru saida mutumin yadauka sannan yace
kuna ina don Allah danuwanane; mutumin
yace anko dashi jos asibiti duk da baa da
tabbacin yana raye, kaje juth zaka sameshi ,
cikin azama