Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 6
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels  BAR RAINA ALLURA, KARFE CE Na BENAXIR OMAR Misalin karfe takwas daidai yayi parking motarsa kirar benz E450 amazauninta, yafito a hankali sanye yake da kananun kaya, farar tshirt anrubuta,Love is life , sai kuma jeans,dakuma shade dinsa dayacire ya ajiye a motar kafin yafito, tafiya yake yana juya agogon rolex din dake hannunsa don yaga karfe nawa, har ya isa kofar yadanna kararawar, watace sanye da uniform fari wanda zai tabbatar ma dacewa mai aikice, tabude tare da rusunawa tanacewa welcome sir!, bai kulata ba balle ya amsa mata kai tsaye yashige falon zama yayi dirsham a kan kujeran yana maida numfashi adaidai lokacin yaji saukowa, yasan wacece donhaka yakara langwamewa tareda jiranta, tana saukowa fuskanta cire da annuri, dattijuwa ce, maabocin faraa da kamala, ga hasken fuska da kammani da dan nata wanda batare daka tambaya ba zakasan ita tahaifeshi komi nata tsak a fuskanshi, takaraso tareda cewa babana ka isone? Cikin shagwaba yace mumy wlh nagaji yunwa nakeji, tace yanzu zaakawomaka abincin ka tsaya kadan dafatan kayi sallah? Yace saidanayi a masallaci nakaraso, wasu ne sanye da uniform kamar wacce ta bude masa kofan da farko suka shigo rike da tire a hannunsu, kulolin abinci ne da plates, haka suka jera komi akan table din sannan suka juya,suka fice, mikewa yayi hajiyar tasa tana biye dashi har suka isa dinning din, budewa yafarayi daddaya, ferfesun kaza ne, sai kunun gyada, dakuma coconut fried spaggetti, duk kamshi yacika dakin, 2 BAR RAINA ALLURA KARFE CE Na Benaxir Omar Ya dauki serving spoon yafara zubawa , sannan yafaraci , yace hajiya ina rahma da ramlat? Tace yau sunada lectures har 6 inaga sai magrib kagansu, yadan yi shiru sannan yace ni wlh hajiya, dakin barsu sunzauna a hostel wannan to nd fro dasuke tayi, tace a a kam, inasu ina hostel? Kafini sanin halin kannen naka, baruwana donhaka ka hanzarta kaci kaje ka watsa ruwa, tafice tabarshi agun, wayarshi yadauka yakunna data dinsa, sannan yadale instagram, yanajin dadin abun ko bakomi yana ganin fuskokin mutane, hotunan abubuwa dakuma yadda duniya take ciki, yayi liking abunda yaga zai iya, sannan yasauka yakoma whatsapp, kwata kwata abincin baifi cokali uku yayi ba, anma duk hankalinsa nakan iphone6 golden colour, dayagama akalla yakai awa daya ahaka yamike yahaura sama dakinsa yanufa, dakin tsaf tsaf, daganan mutum zaigane cewa irin maza masu tsafta ne, don dakin kamshin turare take, ga sanyin ac. Na buga dakin, bandaki yashiga ya watsa ruwa, yafito ya shirya tsaf bayan turaruka daya fesa masu uban tsada ya kwashi wayoyinsa, guda biyu sannan yafito kasa yasauka yaje daidai gun keys set, yafara duba makullan motan, yana tunanin wanne zai hau, FE CE NA BENAXIR OMAR can dai yaga ta lexus yadauko sannan yakara hawa sama dakin mumy yanufa yabude dakin nata, kamshine yabugi hancinsa as normal kullum don shi yana ganin gadon mahaifiyarsa yayi, tanada son tsafta da kamshi, yace mumy barinje nadaukosu rahma , ta ce yoo gani kake kaman bazasu dawo bako? Kaikam kaida yarannan,ya sosa keya tareda cewa nikam dai mumy sainadawo, ficewa yayi yatafi garage yabude lexus din yashiga fara ce sol, gashi yasha wasu kananun kaya fari dakuma bakin wando, yana shiga yakunna a c din motan sannan yafito horn yayi wa maigadin suka bude masa kofan sannan yafice, atbu yanufa yana isa gate din makarantan yadau wayansa yakira rahma, cikin karamin muryarta tace yayah ina wuni? Yace kuna ina? Tace muna slt. Yace ganinan zuwa batareda ya sauraresu ba yakashe wayan, slt yanufa sannan yaja yayi parking, bai daga waya yakira yace ya isoba, baikuma kashe motanba, rahma da ramlat dake zaune suna jiran lecturern ance bazaizo ba, ramlat tace kitashi muje waje kinsan yanzu mayb yayah yazoshi kuma kinsan akidanshi bazai taba kiranki yace ya isoba, kuma bazai taba tafiya ba, anma ke kinsan abunda zaiyi as result is beta tun farko mufita ko zamu ganshi, suka mike tsum tsum suka fito aikuwa suka ganshi rahma ce tabude gaban motan tashiga ramlat kuma tashige baya, rahma tadanyi yakee sannan tace yayah yaushe ka iso? Yace dazu , tayi shiru. Tohfa rayuwan kenan, kullum yanaso yaga suna gefensa anma dazaran sunzo saikuma zaman kurame, zaman kudaje sukeyi, Nasan zaku damu kusan wayeshi wannan guy din, inata bada labari anma bakuma san sunanshi ba ko? Toh sunanshi HAIDAR AMINU HAIDAR,*Kubiyoni donjin labari wanene shi? Sannan suwaye wannan yanmatan? FE CE NA BENAXIR OMAR Haidar aminu haidar Da ne danfari agurin alh.aminu haidar dakuma haj.hauwa wacce aka fi sani da hajiya fulani, shikadai ne namiji sai kannensa biyu mata ramla yar shekara 22 tana karanta chemical engineering a atbu ajinta biyar, yayinda rahma yar shekara 19 tana aji biyu tana karantan architrcture. Rahma da haidar suna balain shiri halinsu daya, sunkuma shaku, saidai gaba daya suna tsoron yayan nasu don mutum ne wanda baaganin faraarsa da garaje. Idan anga yayi murmushi toh hajiya fulani ce agefensa donko a gaban mahaifinsa baya murmushi. Kullum fuskansa ba yabo ba fallasa,suna zaune ne a kaftareren gydan da alh.aminu ya gina musu a g.r.a gydan sama ne. Babban gyda wanda yakamata a ajiye mata hudu, saidai inaa alh.aminu bayada burin auren mata biyu, donhaka haj.fulani itakadai take zaune a gydan ba kishiya, yaran suntaso cikin tarbiya. Da kudi da shagbwa, saidai akwai ladabi wana gaba dakuma hankali da nutsuwa , alh.aminu bayada son jamaa hakan yasa hatta matarsa bata kawo masa mutane. Balle azo kan yaran dama asali shi haidar bayada wata wacce yake kulawa 5 BAR RAINA KARFE ALLURA CE NA BENAXIR OMAR Kannenshi biyu sunzame mishi hasken idaniya, domin inhar zasu fita toh rahma ce agaba, gasu farare tas irin shuwa arab dinnan, kana ganinahi da rahama kamar yayi kaki ya ajiyeta, ramla kuma dibin ta dabanne, saidai itama akwai kyau tubarkallah , ga gashi da tsayi wanda shikanshi farin ciki yakeji imhar yafita dasu, donma Allah yasa bamai tara tarkacen abokai bane, abokinsa daya sadiq , sadiq yakada yaraya akan haidar yahadashi da kanwarsa daya anma inaa, haidar yaki, bakuma don wani hali na sadiq dinbane, shikawai yasan bayaso abata wa kanwarsa rai, idan aka bata toh tabbas kowaye zaasamu matsala dashi shiyasa tun farko baya so hakan tashafi abokantakarsu. Inmuka gangaro kanshi haidar wani irin namiji ne mai farin jinin yanmata, indai zai wulga ko yashiga taro sai ansamu wacce zata biyoshi, mata masu ji dakansu kuma, yayan masu kudi da yaran sarakuna, idonshi kadai ya isa yatafi da imanin kowacce mace, don cikin kwayan idonsa blue ne wanda hakan na wuyan samu agun mutane, saikuma manyan ido, yana da dimple ga gashun saje yasauko yarufo gefen fuskanshi, dogo ne yanada faffadan kirji, wanda hakan zai tabbatar ma dacewa baiyi wasa da lafiyar sa ba, bayason rana ko kadan. Hakan yasa yakanyi wuya aganshi da rana, sannan duk maitan shi da abu indai aranane yakan hakura. Duk da nafada bari dai nakara maimaitawa tsafta ni benaxira irin wannan tsaftanshi tana ban mamaki. Namiji mai uban kyankyami, ga son kamshi, bayason kazanta, acikin garin bauchin akwai anguwoyin dabaya zuwa, ko hanya bayabi saboda yanayin anguwan. Balle kuma yaga mace kazama akan hanya jiyakeyi kaman yayi amai, abunda bai taka kara yakarya ba, sai aji haidar yatoshe hanshi. Yanada raina tsaftar mace. Duk tsaftarki kankanim wari yana bugan hancinsa zai juya bakuma zaki gara ganinsa ba. Social ntwkn nayau da gobe yasa yasamu kawaye dayawa anma bakowacce yake kulawa ba, duk dacewa saidai a chatn anma banda haduwam fuska, baicika zama ba akasar balle ma atakurashi, wannan shine HAIDAR AMINU HAIDAR CE NA BENAXIR OMAR Ahankali yake tukasu harya isa gyda, horn dayayi ne yasa masu gadin suka bude a hanzarce. Yaduru cikin gydan daidai inda yadauki motan yaje ya ajiye sannan suka tsaya yabude kofansa sannan suka bude, don aladansa ne, idan har zai kaiki guri idan kun isa dole kijira yafara bude kofa duk saurinki kina budewa zaice kim rainashi yazaayi yakaiki guri kuma kifice kibarshi ko bazai fita ba, zai bude kofansa saike kibude naki kafin yamayar danashi yarufe, ganin yabude nashi yasa suma suka bude nasu, suka fito ramla Allah Allah take taganta adakinta don wlh tagaji ga yunwa gakuma ana so afara kiran sallan magrib, masallaci yafice yayinda sukuma suka shige ciki. Sama suka haura kowacce da dakinta acikinsu, rahma colourn dakinta komi pink yayinda ramla purple dakinsu tsaf wanda zaace budurwa nai tashe daji dakanta tasamu, komi a kimtse, watsa ruwa sukayi, yayinda masu abinci suka fara zarya zarya don shirya musu abinda zasuci, dama a maakaitan gydan tsabar tsince tsince irnna haidar da kyankyami yace shi bazaici abincin masu aiki ba, zuwa akayi akanemo musulmai wanda sukayi cathering skul subiyu, akayi training dinsu kan yadda zasu tsaftace komi kafin ya yadda yafara cin abincinsu, komi nashi dabanne BENAXIR OMAR Rahma ce tafara saukowa kafin ramlat kan dinning suka nufa, abincin suka bubbude suka fara diba, ganda ramla tadiba taja gefe, yayinda rahma tadauko fruit salad tafarasha, rahma tace ni nace sudena samin pineapple banaso sunki. Ramla tace yooh toh inbanda abunki yazaamiki fruit salad ba pineapple ai dadin bazai cika ba, nan dai rahma taringa surutai, dama ita shes too picky akan abinci, kamar yadda haidar yake shima, shigowa yayi tare da sallama yanufi kan kujera yazauna sannan yakunna tv, ball yafara kalla, arayuwansa shi dan arsenal ne. Yana balain son arsenal, komi nasu ya mallaka, agogo, tshirt, dawasu car statue, da akafita break yamike yadau waya tareda cewa sadiq kana ina? Sadiq din yace ina hanya barin karaso, dama a kaida tare suke kallon ball, baadawo daga break dinbama sadiq yashigo suka zauna ayayinda masu hidiman abinci suka fara zarya zarya don serving dinsu dinner, suna tadi sunaci har aka gama kallon ball suka mike, ficeewa sukayi sukabar gydan, haidar ne mai tuki, ahankali yake tuki harya sukayi hanyan aroma, dama normally gurin akwai yan good evening, yanmata karuwai wanda sukecin kwalliya su tsaya abakin titi duk namijin dake raayi sai yazo ya tsaya ya kwashesu, sunsaba wucewa kullum shidai haidar Allah wadai yake dasu, gashi kyankyami suke bashi, kuma kaman dole kullum sai yazo yawuce inhar zai sauke sadiq,yauma sundanno har zasu wace sai sukaga kaman fada akeyi ma, yanmatan su ukune sunsa kananun kaya, toh biyu saisuka sa daya agaba da duka BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Sadiq dake ta gefen yaja glass dinsa yana kallonsu, harsuka wuce, yace nikam toh aneman kudinsunma akanme zasuyi fada? Haidar ko kulashi baiyiba donshi haushi suka bashi kaman yamusu duka, sunwuce har sun isa gate, sai sadiq yafara salati namanta wayana wlh dan Allah kazo muce in dauka, haidar yace kaifa matsalana dakai kenan kacika mantuwa wlh, nikam oya zoka ja motan, sadiq yafara lankwasa murya a a don Allah kayi hakuri muje aboki na,haidar ce ai baka isaba, fita yayi yazaga yaja yabude yace oya fito kaje kaja nagaji, donhaka sadiq yayi murmushin tareda futowa yashiga yaja motan fuuu suka fice, haka suka kara wuce gurin yanmatannan anma kaman abun tsananta yayi domin wannan karon sunyaga mata riga taja gefe tana kuka, shidai sadiq duk shiyake lura yayinda gogan naku shikuma ko ajikinsa, suka je yashiga yadauko wayan sannan yafito, suka kara dawowa ahanyan dawowa ne yafara rage gudu, haidar yace mekuma kamanta? Sadiq yace ba mantuwa bane inaso naga yarinyannan ne kaman tana cikin wani hali, haidar yaja tsaki akwai mutanen dayakamata kataimakawa dayawa ba karuwa ba okay? Shidai sadiq bai saurareshi ba, ya tsaya da motan tasa daidai inda ta tsuguna, ta sunkuyar dakanta akasa, tajanye inda aka yage domin tarufe tsiraicinta, hasken wutan yarage tareda horn anma bata dago ba, hakan yasa ya dalleta da haske, shidau haidar naganin ikon Allah, ahankali tadago fuskanta, duk da bata ganin suwaye tamike tareda ja baya don taga sun tsaya, a tsammaninta kar kuma su zata zata tafi ne itama A BENAXIR OMAR Wadannan yanmatan dasuka mata dukan ne sukazo dagudu suna tsaye tareda buga glass din alamun gasu sun iso, sadiq yasauke glass din sannan yace kumin magana da wancan,dayar wata baka wanda tunda haidar yadaga ido yaganta yajuya bai kara juyawa ba, asali toshe hancinsa yayi don wani wari yakeji da babu kanta, tadan yamutsa fuska sannam tace ai ita wancan ba aikim take ba, mune kadai muka rage, sadiq yace ae ki kirata, tadanja gefe tajeta, bayan mintuna kadan sai ga wancan din tazota ahankali, duk jikinta bari yake, sadiq din yabude kofan motan, alokacin haidar ji yayi kaman yafita yarikoshi yafara masa duka, anma yasan sadiq da laushin zuciya da son taimako, yana fita tana gefen windown haidar din aloacin ko kallonta baiyiba, atunaninsa zaiga irin wancan fuskan, saidai wannan baiji wariba, haryake cewa toh ko ita bata wari ne, sadiq ne yace meya sameki naga suketa daka kaman sunsami sakwara,? Abun yaso yabawa haidar dariya anma dai yadanne, batace komi ba, yakaracewa ko zaa kaiki gyda ne? Tadan gyada masa kai. Yace toh oya shiga muje nakaiki, yabude mata gydan baya, haidar ji yayi kaman yasa hannu akai ya tsala ihu, anma bayaso ya disga abokin nasa don motanshi ne, sai yashare kawai, yayi nadaman bashi tukin aidashine da ba wanda ya isa yasashi tsayawa sadiq ya zago yafara tukawa yace wani anguwa kike? Cikin rawar murya tace agydan yayata nake zaune a gwallaga saidai kar ka kaini, ka kaini ko wunti ne na kwana, yace meyasa? Cikin sheshkan kuka tace saboda zatamin duka tace miyasa bansamo kudi ba,, haidar saiyaji jikinsa yayi sanyi, daga ganinta saan rahma ce karamar yarinya ce. Saiya yi shiru sadiq yace muje nakaiki, sai nabaki kudin nawane? Tace arana dai kwana daya dubu biyu ne ko dubu uku, haidar wani tsaki yaja, wai ace karamar yarinya har zataje tabada kanta don kawai tasamu dubu biyu? Ashe sadiq shima abun yatabasa donhaka saiyace, yanzu kina nufin kullum kina zuwa nam don abaki dubu biyu, tazaro ido tareda girgiza kai cikin kuka tace wallahy bantaba kwana da kowaba, akwai wata kawata datayi aure idan antyna tace nasamo kudin sai kawartawa tace mijinta yabani, toh jiya mijin ne yace yanasona sai muka bata da kawar tawa, sanadin haka yau nafara zuwa nan, shiyasa danazo wadannan suka rinka cewa ban iyasa kayaba, sukeso suciremin don nadawo irinsu danaki shine suka hauni da duka, Allah ne yataimaken harkuka iso, sadiq shiru yayi barinma haidar da tunda tashiga motan bai tanka ba, kuma bai nuna alamun zai tankan ba, ita kanta rashin maganan nasa yasa ta tsargu hartake jin ko yanajin haushinta ne, sadiq ne yatsaya adaidai kasuwan. laushi fita yayi ya je yasiyo kayayaki yazo yabude kofan yaje shagon matan, tareda rokon subata guri domin tasamu. Tacanja, yadawo motan yazauna yana jiranta, yacewa haidar kayi hakuri abokina wlh yarinyan tayi karama ne sosai for all this stuff shiyasa kaga nadage, kuma daga gani kasan shes a novice, haidar yace bakomi. Hakan ya mugun bawa sadiq mamaki, anma dai yayi shiru tunda ansamu saa abokin nasa bai yi complain din dayake expecting ba, bude motan sukaji tashigo alokacin sadiq yajuya tareda cewa muje nakaiki? Ta gyda kai ae uncle, dariya ce ta kufcewa haidar wanda baiyi niyyan yiba, tare dacewa wato ma sadiq yadawo uncle, yadda yayi maganan har cikin ranta taji maganan, wato yasan yanada dadin murya daz y yake makalewa saboda kar anaji 1 0 BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Sadiq yadan hade rai tareda cewa haidar kaikuma watz funny? Haidar ya girgiza kai baice komiba, itakuma bata kara cewa komi ba, sadiq ne yace sunana abubakar sadiq, zaki iya kirana sadiq, tace toh yaya sadiq, yauwa gwara hakan injishi da fada domin shikanshi yaji wani iri datace masa uncle, gwallaga suka isa, tana nuna musu hanya dakyar suka ringa duruwa, tunda haidar yake baitaba zuwa gunba duk ginin gun yamasa wani iri, har yake jinjinawa aransa lalle toh tundaga wannan kusurmin lungun take takawa bakin titi? Babu abinda yabashi mamaki saijin datayi cewa mu tsaya anan , mota baya shiga ta lungun, sadiq yayi parking yace zaki iya karasawa da kanki? Ta gyada kai tare dacewa ae, yaciro bandir din dari biyar yabata, ungo wannan kiboye, kullum kina cire dubu biyu kinabata, shikenan zata barki ko? Ta gyada kai tareda cewa anma idan ta bincikeni tagansu dayawa zata iya korana naje nanemo irinsu. Ya karba yaware dubu uku yabata, yace ungo wannan kibata, gobe zanxo saiki fito nabaki haka zamunayi har Allah yakawo hanya ko, karki kuskura ki saida mutuncinki kina ya mace [5/24, 9:56 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Ta gyada kai tareda cewa nagode, nagode. Allah saka da alheri, Allah kara budi, yajikan iyaye.bashiba hatta haidar yaji dadin adduan, duk da Allah Allah yake tafita don so yake tafice yanaso yayi magana, tana fita ya danka wa sadiq harara tareda cewa bangane kanaso ka makalewa yar mutane ba, daga ganin yarinya bakasan halinta ba zakafara biyeta?,you are so cheap, who knws ko yarinyan tazauna ta sheka maka karyane?, shidai sadiq gyra mota yayi yafice baice uffanba, gydansu ya tsaya tareda cewa abokina i believe bacci kakeji tuka kakoma, haidar tsaki yaja cike da takaicin yadda sadiq yabata masa lokaci yafita a motan yakoma gurin mazaunin mai tuki sannan yaja motan, ayadda yaja yatabbatarwa sadiq lalle ran abokinsan yabaci. Haka yashige gyda duk tunanin yarinyan yakeyi gashi ko sunanta baisaniba, Haidar nashiga gyda yabada mukullin wa maigadin tareda cewa gobe ka tabbata gobe anwanke motan nan don Allah, yace toh oga!, yana shiga toilet yawuce yasake wa kansa shower, saidai yadda yarinyan take magana yakeji akansa, haushinta duk yabi yacikasa, shikam jiyake kaman yahadata da ita da sadiq yayiwa duka, haka dai yakwanta ranan Washegari sadiq tuni yashirya domin yatuna alkawarin dayamata nacewa zaina zuwa don yabata kudi, yana xuwa daidai inda motan ta tsaya jiya yajirata, yakai minti ashirin kafin yaga tafito sanye da hijabi har kasa, zata wuce Allah yataimakeshi wutan gefen gydan dayayi prking ne ta haska dabazai ganetaba harta wuce, tuni yamata horn anma taki juyowa ita a tunaninta zataga motan jiya, fitowa yayi yasha gabanta ta mugun tsorata. Don dogo ne a zube yake, tsayinsu daya da haidar, zata yi magana yace muje kishiga kafin su ganki, nan ta tsuguna ina wuni ya sadiq, bai kalleta ba yawuce motan yabude mata tashige sannan shima yazaga yashiga tagefensa, yana shiga yaciro kudin yabata. Sannan yakaramata dubu daya gashi ko zaki bukata. Kinada waya? Tace bandashi, yace zansiya miki, ta zaro ido antyna zata kwace kabarshi kawai, yace toh shikenan, gobe in zaki zo ki tsaya anan innazo zaki ganni, harzata fita tace dawannan motan ko? Kar wasu dabanne, yace motata ba daya bace kowani mota zaki iya gani, kedai inkinzo kitsaya in nine zanfito, tace toh, harta fita taleko tareda cewa ina dayan yayan? Yau baizoba, yayi dariya yace waye haidar? Wannan halane ki kara ganinshi, baya shiga maganan mata, tajuya tareda cewa sai anjima, harta shiga lungun ta tuna har lokacin bai tambayeta sunanta bafa! Lalle mutumin nan wani iri ne? [5/24, 10:12 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Sadiq kuwa jan motanshi yayi yafice, tundaga ranan kullum zaixo yabata kudi hardana kashewa baitaba tambayanta sunanta ba, sannan kullum inzata fito toh da hijabine, inzai wuce gydansu haidar saiyazo yabata kafin yatafi, ahaka har sati biyu, kuma kullum in haidar zaice daga ina? Toh zaice daga gun baiwar Allah, wataran kam ma, saiyace inagunta yanzu zandawo, ranan saida haidar yatikeshi tareda cewa banga maikagani ajikin yarinyannanba, kabi kanace. Yanmata nawane masu asali a garin bauchi ka gagara dubawa? Shidai sadiq baice uffan ba , daga bayane ma yace bazaka gane ladan danake samu bane, sunsha samun matsala akanta anma sadiq haka yake shanyewa tunda yake baiga yadda haidar ya tsani mace kamantaba, kiri kiri yake nunawa, watarana urgent meeting takama sadiq yabi flight sai abuja magrib nayi yatuna cewa lallai ashe yau ashe zai bawa baiwar Allah kudi, yarasa yazaiyi gashi tunda yake baitaba zuwa da kowa ba, balle yace aje akai, mutum dayane haidar kuma yasan ko sama da kasa zata hade bazai je ba , yarasa yazaiyi saiya fara tausayin yar baiwar Allah, yarasa yazaiyi da ransa, wayansa yadauka duk dayasan bamai yiwuwa bane yakira haidar. Haidar na dauka bayan sungaysa cikin tausayi yace abokina kataimakeni, haidar yace menene? Yace nasan bazakayiba anma badon halina ba don Allah nace maka, yacr inajinka, wannan baiwar Allahn ne nabarta, yau yakamata nakai mata kudinnan kuma kasan daddy yaturon urgent meeting abj, inbatakai kudin gydaba antynta zata iya sata awani hali, don Allah kacece tarbiyan ya mace, harya gama haidar baice uffan ba, saidaya gama sosai, sannan haidar yace kanemi wani, kafin yakashe wayan sadiq yace wlh tlh babu wanda yasan gun saikai, haidar yace nidin angayama zanganene?, sadiq yace kai zakafi ganewa da kwatance don Allah abokina, don darajan manzo SAW ba don halinaba, ganin yadda yaketa rokonsa yasa yace oya karka kashe wayanka harna isa, tsalle sadiq yayi don baizata haidar zai yadda ba. Da kwatance yakaishi har gurin inda yake parking sannan yace yajira zatazo yanzu, suna magana saigata da jibgegen hijab, saidai datazo ta tsaya agefe kamar yadda sukeyi sai ta tsaya idan sadiq yaga ta tsaya sai yabude motan yamata magana, toh kaikuma gogan haidar ashe ya shaka har ransa! Yazaayi ita dazaa taimakawa tazo ta tsaya kaman soja yacewa sadiq wlh zantafi inbanda iskanci tazo ta tsaya agaban motan nizan fita na sameta? Ko ba ita bane? Sadiq yace itane kabude kofan kamata magana, haidar yaja tsaki lalle kuwa ashe bazata taba karban kudin nanba, saidai na juya natafi, har ya kunna motan yayi horn dakarfi bashiri tazo tagun, yaciro kudin yamika mata, ta saba tashigo sugaysa donhaka shigowa da zatayi anma ganin yamika kudin ba magana yasa ta sha jinin jikinta tasa hannu takarba ganin ba sadiq bane, anma haidar ne for the second time takare masa kallo lallai guy din yahadu, tace cikin zakin muryanta ina wuni yaa haidar. Haushi yaji kaman yamata duka aina tasan sunansa? Tana karban kudin ya ja motarsa fuuuuuuii yafice yabarta a tsaye agun! [5/25, 3:49 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Mamaki yacikata wannan wani irin mutum ne? Komawa tayi gyda, shikuwa gogan naku ya na tafiya haushinta duk yabi yacikesa, yama zaayine yakai mata abu sannan ta tsaya tana jira yafita yamata magana. Yana isa gyda yatarar da rahma na kallo a falo, zama yayi yana hushi daganan tasan lalle ranshi abace ne. Donhaka tamike taje ta yanko fruits. Takawo masa, kallonta yayi yaji sanyi aransa. Yanason kanwar tashi tana ganinshi cikin damuwa zata nemo hanyan. Sashi dariya, dama kowacce mace hakane anma yadda yakai kankanan bakinshi daya tuna da yadda baiwar Allahn sadiq tamishi saiyaji duk yakoshi, yarasa wani irin tsana yake mata, shi a matanma tsananta dabanne, ya tsani yaga namiji yana lallabin mace ko rarrashinta, mikewa yayi yanufi daki sannan. Yashiga wanka yamike yafara danne danne awayansa kamar yadda yasaba, Sadiq kuwa sai yayi regreting meyasa tun farko bai saya mata wayaba, duk da yataba so yabata taki amincewa, yau ga amfanin wayan, gashi bai samu daman dazaice haidar yabashi ita suyi magana ba, yasan haidar sarai yanzu zai iya gasa masa magana zaice akan me zaiba wa wata can wayarsa tarike? Inkuwa baaci saa ba, zai iya hakura dawayan akan tarike, donhaka sai kawai yashare yafara maidakai saboda yasamu yakammala washegari yakoma, kodan yasan haidar bazai kara masa alfarma ba. Washegari kuma sai baisamu yadawon ba tunda yamma yafara kiran haidar yana lallabi anma haidar yanuna baisan maganan ba asalima kashe wayansa yayi abunsa, balle yadameshi, can dai sadiq baida choice rahma yakira yasan itakadai ce zata iya lallabin haidar yaje. Donhaka yamata bayanin komi daga farko har karshe ta tausaya sosai takuma ce masa yamata kwatancen gun anma ya gwada mata bazata saniba, ta gwada masa ai tasan anguwan yamata dallah dallah zataje tun kafin dare yarufa, yace toh zai namata harta isa. Tamike tsaf tashirya cikin abayanta, wacce musamman daga dubai mumy tasiyo matasu, sunsha tsada dakyau ga daukan ido, ta kira dahiru direba takarbi mukullin matrix tashige, ahaka suna waya da sadiq harta isa kasancewar ta mai saurin fahimta, yace adaidai gun zaki tsaya inkinje dare dare, zata fito, sai rahman tace toh y not nashiga yanzu kawai? Yace ai matsalan nikaina agun nake tsayawa bansan gydansu yanata inabane [5/25, 4:03 PM] Adda bena: BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR Tace toh bakomi zankoma, zandawo anjiman, takoma gyda har lokacin. Haidar bayanan, tana idar da sallahn isha ta shirya tsaf, tayiwa mumy bayani dalla dalla mumy tace toh suje tare da ramlat , tunda tasan haidar sarai bazuwa zaiyiba, suka shiga motan harsunzo first gate saiga motanshi ta danno kai, suka yi wining glass din , yace ina zuwa? Rahma tace aika yanzu zamu dawo, yace zuwa ina adaren nan bazaku jiran nazo nakaiku ba?; tace saboda bazaka yadda bane ai , aikan yah sadiq ne. Yayi gim yace wani aika kuma? Tana fada mishi yana hada rai. Wato sadiq saidana. Cemasa karya fara anma yakijina ko? Kukoma gyda!,tace haba yaya nagayawa mumy fa. Ba dadi wlh, parking motanshi yayi yace koma baya, takoma baya yakarbi tukin baikara kulasu ba harya isa cikin gari

Chapter 1 of 6