Reading ALAƘAR ZUCI by Mai Dambu Chapter 5 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dakina Hajiya ta"

kwana akan gadona da danta ni na kwana a dogon kujera.

"Washi gari na tashi na fara aikin abin karyawa, ga wani sanyi da yake ratsa ni haka na gama ina"

"atishawa. Bayan na gama na kai musu kowa dakinsa, sannan na kawowa Hajiya nata, na koma waje na karya sannan na hada ruwan wanka na shiga nayi, ina fitowa naji kamar zazzaSi zai rufe ni, haka na saka kaya na fito dakin Ya Hafiz, na ce mishi. ""Don Allah ka bani magani bani da lafiya ne!"" D'ago kai yayi yana kallon yadda nake takure wuri guda. Bai ce kome ba, ya ce min. ""Tow!"" Ya tashi ya dauko min har da wanda ya ke bani na sha, ya ce min. ""Ina son na fara ruin nawa business din Ina son kudi amma narasa inda xan samu ko zaki bani aron kudi ne?"" Shiru nayi ina kallonshi kafin na ce mishi.. ""Ai!"" ""Tashi idan kin yi nazarin abinda zaki bani nan kwana uku ina jiranki!"" Haka na fito ina mai barin dakinsa na koma dakina na kwanta, kwanciya nayi haka na fara barci sama sama, na ji an zuba min duka a bayana, bude idanu nayi ina kallon Hajiya ce. "" Kin tashi ko yaya anya ba shaye-shaye kika fara ba? Waye zai daura mana abincin rana yau har da tuwon dare zaki mana! "" Dakyar na mike kaina yana bala'in ciwo, na nufi waje na daura abincin rana, wurin karfe daya na gama nayi sallah na kwanta don ko abincin ban kalla ba, barci yayi gaba da ni wurin karfe hudu na ji an watsa min ruwan sanyi a firgice na tashi Hajiya ce ta saka Yusrah ta watsa min. "" Yawwa takwara gara haka, Uban waye zai mana abincin dare! Mau farar kafa kawai tunda Hafiz ya aure ki, tsiya yake binsa. "" Haka nayi sallah la'asar sannan na wuce na daura tuwon semovita miyar busashen kubewa, abin da na fara fahimta kayan firjina sun fara narkewa gidan ba wuta,"

"ina cikin wannan nazarin ya Hafiz yanzu da mai aikin wuta, ashe an saka abin invert dinmu bai jona ba ne, haka aka jona mana muka samu wuta, da nazo cin abinci mika min yakin daddawa Hajiya tayi tana faWin.. ""Gashi nan ki na ci da abinci, domin ke na daka na kawo miki . "" Amsa nayi nayi ta mata godiya yaushe na samu gatan da har Hajiya zata min kyauta, ai ko zan mutu ba zata ba ni abinta ba sai ma ta amshi nawa, haka na cigaba da abinda nake, kafin na zubo abinci na fara ci ta ce min. "" Idan ba zaki ci ba, bani abina. "" A hankali na ce mata."" Zanci kai! "" Na bude ledar na fara cin yajin ina barbadawa a cikin abinci. "" Dama sai da na kashe kudi kusan dubu biyar a hada yajin nan, yanzu gashi xan koma bani da sisi dan uwanki"

kuwa na mishi magana ya ce bai da shi....

*08130269641*

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*"

Ramlat Abdulrahman Manga

Mai_Dambu

SHIDA

"Haka kawai Hajiya ba zata min abu don kanta ba sai dai idan tana da bu™atar wani abu daga gare ni,"

"shiru nayi domin yanzu bani da kosisi iya dubu biyu ne a cikin account dina, idan na fada ba yarda zata yi"

"ba. Don haka nayi shiru haka na kyaleta tana ta rabtabo bayaninta ganin bance mata kome ba, sai ta fara"

"masifa ni dai har ta gama bance mata uffan ba, domin nasan kara mata haushi zan yi, haka ta bar dakina zuwa dakin Karimah wacce suke can da Ya Hafiz, suna cin gas meat, shigar Hajiya dakin ta ga sun baje suna ta fama wadaka da abin arziki ga Country Yorghurt a gefensu, zama tayi tana hadiye yawu. ""Yanzu Hafiz haka zamu yi da kai, ka zauna kana cin abin arziki ban da ni. "" Hade rai yayi yana faWin. "" Hajiya matsalata dake baki da hakuri so nake na gama na kira ki! "" Shiru tayi tana kallonshi sannan ya tura mata wani karamin kulli gabanta. Haka ta bude tana tab'e baki alamar ta rena ba haka ta so ba, ta cinye amma"

"maganar gaskiya bai ishe ta ba, amma ba yadda ta iya ta nad'e kwadayinta tayi musu sai da safe."

"Ina kwance a dogon kujera ta shigo ta kwanta a gadon, bamu jima da fara barci ba invert dinmu ya"

"dauke gashi ba maganin sauro, abin ba dad'i haka muka kwana a kuntacce, domin ban saba da irin wannan rayuwar ba, tun tasowata. Haka muka kwana a can dakinsu Ya Hafiz basu yi irin kwanan da muka yi ba, abin sai ya hadu min goma da ashirin, domin dakin wani irin zafi kamar gidan burodi ya Wauka, zarewa ne ban yi ba amma har kusan lokacin da nake tashi sallah dare ban iya rintsawa ba, gashi Ya Hafiz bai bani maganin da yake bani ba, abin sai ya min yawa. Bayan sallah asuba na fito na daura musu abin karyawa da ruwan wanka, na shirya Yusrah sannan nayiwa Yasir wanka na basu abinci, nan Yasir yayi ta kuka har sai da Uban ya fito yana faWin. ""Ke dai azzaluma mace, uban me yayi miki!"" Nasan ba yinsa ba ne, ina da yakinin zai dame na, zai dainaim. Abinda yake yi ya dawo mu shirya kamar baya. ""Ba magana miki ba!"" Shiru nayi sai da ya zaburo kamar zai dake ni nace mishi. ""Ban san me yake damunsa ba"" na fada mishi ina kallon Yaro na yake ta zufa. Karban yaron yayi ya Wan jijiga shi daidai fitowar Hajiya da Karamcy, amai ya fara yi, kuma ai laifina ne tunda na hango ya koshi amma yaki ya daina cin abincin ni kuma na kasa daina bashi wai kada yayi kuka. Sai da ya amayar da abincin da yaci sannan ya sauke ajiyar zuciya. Cikin jin haushi Karimah ta bangaje ni, na taka aman Yaron na zame nayi zaman yan bori. ""Muguwa mai bakar zuciya, ke baki haifa ba. Amma kina son ki kashe min, idan kin yi zuciya ki haifi naki mana. "" "" Gata mata dai ba zuciyar haifa sai na kashi."" Inji Hajiya, ni dai kamar wata sokuwa sai na yi kasake ina kallonsu, ko ya tuna wani abu ne ya fara faWa, da cewa baya son abinda suke yi. "" Luluna tashi da gangan ba zaki cutar da su ba."" Ai kuwa na fara gyad'a kai ina kokarin mishi bayani, haka ya dakatar dani da abinda zan faWa. Haka na tashi na koma daki na sauya kayana, na gyara inda"

"Yasir yayi amai na wanke, da yake gidan akwai rijiya."

"Ciwon da kaina yake yasa na gyara kwanciyar da nayi a dogon kujera. "" Lulu yunwa nake ji. "" Inji"

"Yusrah. ""Na kai muku abincinku wurin mamanki! "" Wani irin ihu yarinyar ta fasa sai da naji kamar ™wa™walwar kaina zai yo waje, wani irin tartsatsi kawai nake ji a cikin kaina, wanda ya tilasta min na dafe kaina, zufa na karyo min. Sai na rasa me yake damuna ga wani irin sound nake ji yana kara a kaina, ji nayi kamar duniyar tana juya min, a hankali na shiga ambaton Allah tare da komawa jikin kujerar na kwanta ina min zuciyata tana wani irin bugawa mai karfi, shigowa Hajiya da Karimah ganin yadda nake ta haki da zufa sai suka ka ja hannun yarinyar suka fita da ita. Ni kuwa suka bar ni cikin wannan yanayin. Karshe har dare ina kwance a wurin, ya shigo suna ta hidimarsu babu wanda ya gaya mishi ga halin da nake ciki, sai da gama abinda ya mishi kafin ya ce musu. ""Yau mugun halin ya motsa taki fitowa!"" Babu wacce ta amsa mishi, haka yasa shi mikewa ya leka dakin dubu babu haske, torch din wayarshi ya kunna"

"ya ga halin da nake ciki, ""Innalillahi wainnalihir rajoun, Hajiya Karimah me ya same ta?"" Ya tambaye su,"

"take suka taso dukkansu suna faWin. ""Tow me zamu sani tunda ita dai bata fitowa cikin mutane."" Da"

"sauri ya ciro wayar shi ya kira Abokinsa da yake amsar magani a wurinsa, ™arshe dai zuwa yayi ya dauko abokin domin tun a can ya mishi bayani, shi kuma ya tawo da kayan aiki. Sai da ya fara gwada hawan jini ya ga yadda ya tashi. ""Amma kace matar nan matarka ce?"" ""Eh kai!"" ""Gaskiya akwai wani abu!"" Haka ya cigaba da aikinsa sai da ya saka min ruwa da allurai, sannan ya rubuta mishi magani a sayo min, a lalace dai sai da aka kashe kusan dubu ashirin da biyar, ai kuwa ran shi ya b'aci domin baya kaunar abinda zai"

saka ya kashe kudin da ba zasu dawo mishi ba.

"Hajiya ta kwana a dakin, amma itama barcinta tayi son ranta."

Karimah.

"""Ni dai ban ga amfanin rike yarinyar nan da kake yi ba tunda ba sonta kake ba, idan har ba sonta kake ba"

"ka sake ta ta tafi mana."" A wani hargitsetsan yanayi ya kalleta, kafin ya ce mata. ""Bana kaunar Lubnah ko"

"kaWan, amma ba zan sake ta ba. Ita din tsanin arzikina ce sai da na aureta na fahimci ashe arziki a jininsu ne, don haka kada ki kara min wannan maganar."""

"A fusace ta mike tana faWin. "" Gaskiya ba zai yiwu ba, taya zan cigaba da zama da ita bayan duk"

"al™awarin da ka yi min bai cika ba. "" Zuba mata idanun yayi yana kallon yadda take masifa kamar zata"

"rufe shi da duka. "" Na gaya miki ba zan sake ta ba na gaya miki na kara gaya miki, ina rike da ita ne domin ita din makami ce. """

""" Lallai fa wallahi ba zan zauna da ita ba! "" Ta fada tana ™o™arin mikewa ya janyonta jikinshi yana faWin."

""" Ki yi hakuri ita din ta rufa min asiri dayawa, a yanzu da muke tare ina cikin rufin asirinta ne. "" Ya fada yana kallonta. Haka ta hakura amma ita ko zata tafi tsirara sai ta saka shi ya sake ta. Sai tayi sanadin da zata bar gidan in sha Allah. Wannan shine kudirin Karimah gidanta ne gidan Yaranta ne dole ta sakata ta"

wahala yadda ranta yake so.

"Washi gari na tashi da sauyi ba laifi, a haka na fita na daura abin karyawa. Sannan na hada wanke wanke"

"nayi, na share gidan ga jirin da yake ta dibana ina hutawa, fitowa yayi ya ga ina wanke taliyar da na dafa. ""Ina Hajiya ke daya kike wannan aikin ko da yake ai kin saba ne sannu ya jikinki?"" ""Da sauki sosai!"" Shiru nayi ma cigaba da aikin abin karyawan. ""Hmmm jiya ba karamin kudi na kashe ba domin rantowa nayi ko zan samu na mai dawa mai shi?"" Shiru nayi ina jin wani irin yanayi yana yawo a raina, itama jinyar sai dai nayiwa kaina. ""Ya Hafiz bani da kudi, idan na samu zan biya ka."" Hade rai yayi cikin nuna bai san wannan zancen ba. ""Ki kira Hindatu ta baki kuWi ko na tafi da wayarki ko zoben hannunki na je na sayar!"" Wayata kan ba zan iya bashi ba, amma zobe zan bashi domin ina jin kunyar na kira Aunty Hindatu na ce ina son"

"kuWi. Haka na cire zoben gwal din na mika mishi, Allah sarki wani tafiyar Aunty Innah umara da Mijinta ta"

"kawo min,. Ina son shi domin sunana ne a jikin hatimin zoben wato Lulu. ""Haka zan tafi da shi salon a ce"

"satowa nayi?"" Shiga dakin nayi na dauko recipted dinsa, na kawo na mika mishi wani irin kallo yake min yana kallon takardan. ""Kayi hakuri kayi hakuri, don Allah ka yi hakuri, ba zan kara ba. Kayi hakuri "" amsa yayi ya ce min. ""Ki kawo min abin karyawa dakin Karimah!"" ""Tow na gode in sha Allah zan kawo maka!"" Na wuce kitchen din na hada abin karyawan na kai mishi, sannan ya ce min. ""Su yaran mu ne zamu musu wanka?"" Jikina ya Wauki rawa na ce mishi.. ""don Allah Mamarsu tayi musu wallahi."" Wata Uwar ashar ya lailayo ya maka min, wanda ya janyo min shiga dakin da sauri, ganin yadda take kusan tsirara a kwance yasa ni juyawa na ce musu. ""Bari na hada ruwan!"" Haka na hada musu ruwan nazo na dauke su, ihun da Yusra take tana wani zakewa yasa ni muka zube domin kaina ya fara sarawa ai kuwa ta fasa ihu suka fito, ganin yadda muka zube na tashi da kyar ina faWin. ""Zamewa nayi!"" ""Ba dole ki zame ba, kina nan kamar buhun gawayi, ni kan kada ki kashe min Yarana!"" Inji Karimah haka na fara mata wanka yarinyar nan tana ihu da yakushin fuskana tana kuka da dukana, babu wanda ya mata tsawa. A haka ta saka min yatsa a cikin idanuna, hawaye ya zubo min, na wanke ta na kaita wurin iyayen nan ma suka sani na shiryata."

"Na fito da Yasir shima haka ya gama zamaninsa, sannan na koma daki na sami Hajiya tana ta shirin tafiya. ""Tow ni dai zan tafi yau ba zan iya kara zama a garin nan ba!"" Ta fada tana fito da kayanta waje."

"BakiWaya nima haka na biyo ta, koda danta ya fito suka fita, ta ce min. ""Ina binki bashi dubu biyar idan kin samu ki tura min kada ki bashi ya turo min tijani zai turo miki number account din da zaki tura min."" ""Tow Hajiya in sha Allah!"" Na fada haka suka tafi na shiga kitchen na hada abin karyawan da zan ci na koma dakin ina kallon roban karin ruwan, can wurin karfe goma sai ga Ya Hafiz da mutumin da ya saka min ruwan, haka ya gama duba ni sannan ya kara min wani ruwan, a ledar da Ya Hafiz yazo da shi maltina ce da fruit, ya ajiye min yana ta min sannu. Yadda ya damu sai da abokinsa ya ce mishi. ""In sha Allah idan ta bi sharaWin da zan gindaya mata ba zata kara shiga wannan yanayin ba, sannan ta cigaba da shan magani. Domin hawan jini mugun ciwo ne!"" Gyada mishi kai yayi sannan yayi ta damuwa da halin da nake ciki, har shi mutumin ya gama aikin da yake ya fita. Ya kalle ni yana faWin. ""Me yake damunki haka da zamu daurawa kanki damuwa har hawan jini ya kama ki?"" Ni dai ban ce kome ba, domin ba ni da abinda zan fada. Bayan ya gama surutunsa ya tafi nima ma samu barci, wurin karfe biyu saura na farka lokacin ruwan ya kare na cire na sannan na wuce nayi alola na gabatar da sallah, na bude friji dina na dauki zabuwa guda biyu na kai kitchen na zuba musu ruwa da na saka a kitchen din don ba zan iya"

kowani aiki na ja ruwa a rijiya ba.

"Sannan na wuce ban daki nayi tsarki na dauro Alola nazo na gabatar da sallah azhar, tea na hada na"

"sha kafin na sha magani na fito waje aiki. Sosai na mai da hankali kan aikina, buga gidan aka yi na mike na je na bude makotanmu ne, na bude suka shigo suna ta fara'a. ""Sannun da zuwa, sannu mu shiga daga cikin."" ""A"" a waje ma ya isa wannan zafin ai kuna shan fama musamman wacce take wannan dakin zata fi kowa shan zafi ita da jin sauki sai ko damina ko hunturu."" Murmushi nayi bayan ma shiga daki na dauko musu kafet na shimfida musu. Sannan na shiga na dauko musu pure water na ajiye musu ina kara gaishe su. Sun amsa sannan na ce musu ."" Bari na kira muku abokiyar zamana! "" Na tashi na buga kofar Karimah dakyar ta fito tana wani hade rai, suka gaisa sama sama, sannan ta koma wata yar yarinya ce ta bani sha'awa, na dauke tana ina faWin. ""Ina Mamanta!"" Murmushi Mamar tayi tana faWin. ""Sunanta Suleimin"" gashi yarinyar tasha wanka an gyarata. ""Allah sarki sunana Lubabatu amma ana kirana da Lubnah!"" Fitowar Yusrah ta ce min.. ""Lulu zan sha tea!"" ""Tow ina zuwa!"" Na shiga dakin da kananun"

"kofina uku na hada har da na yarinyar na fito waje na mika musu itama yarinyar na mika mata. ""Har da"

"dawainiyya!"" Murmushi nayi ina kallon yarinyar, don ta shiga raina duk inda zan ga Yaro kamar na dauke"

"shi nake ji, haka muka yi ta hira ina leka kitchen din, dab Magariba suka min sallama, sannan suka min bayanin gidansu ne a bayan na mu, ita babbar cikinsu sunan ta Maman Abidah ta aurar da ita ma, sai yan mata biyu Na'ilah da Na'ima, sai ta gefenta ita kuma Maman Boy da alamu ita kamar yare ce, Yaronta daya Boy tana sayar da kayan miya da sauransu, sai Maman Suleimin, sai wata kamar Amarya ta ce min. ""Ni amarya ce! Akwai Maman Salim da Maman Yaya basu gama aiki bane amma zasu shigo gobe!"" Na"

"musu godiya na rako su waje, suka tafi. Na dawo na karasa aikina tare da jollop din macaroni."

Wurin karfe bakwai ya shigo shi da likitan ya kara duba ni ya saka min ruwan karshe sannan ya bani

"shawara yadda xan kula da kaina, sannan ya tafi Ya Hafiz ya ajiye min leda bag din da ya kawo min, ya shiga buWewa, yana faWin. ""Gashi nan ki ci, amma ki sani kudin wannan abin da nake miki shima dai rantowa nayi!"" Gyada kai nayi nace mishi. ""Na gode!"" ""Ba fa batun godiya biya zaki yi ai kin sani biya zaki"

"yi a tow!"" Daga nan ya mike ya bar dakin."

"Sauran kwanakin da suka biyo baya, na ji sauki makotana sun shigo, bayan kwana biyu nima na"

"shiga musu muka gaisa sannan na dawo, nayi haka ne don fita hakkinsu, sannan a gefe guda Karimah tana d'aga min hankali rigimar yau daban na gobe daban, haka yasa kullum ya dawo sai ya ji kamar ya"

"rufe ni da duka, haka xan ta bashi hakuri."

"Kusan wata mun Waya a zango, Ya Hafiz bai tab'a cewa na kira gida na gaya musu mun tashi ba, sai da"

"ya ji a ransa. Ya kalle ni da zai tafi kasuwa ya ce min. ""Yau ina ga zaki yi baki me nene babu a gidan?"" Shiru nayi kafin na ce mishi. ""Kayan miya, shinkafa ma ya kare"" nayi ta mishi lissafin abinda babu, koda ya fita wurin karfe goma sai gashi da kayan abinci niki -niki, ya kawo dakina ya ajiye su kwalin madara da milo duk ya kawo dakina ya zuba, sannan ya sakar min murmushi. Tunda na ga haka na fahimci akwai wani abu a kasa, sai dai kamar kullum ina mishi fatan shirya sannan ina da yakinin zai daina abinda yake"

yi.

Haka na dawo dakina na kara kintsa dakin na fito na daura abincin rana. Ina waje wayata da babu

"chaji yayi kara na shiga dakin. Ya Umar na gani kamar nayi kuka na Wauka. ""Yanzu Lubnah kin kyauta baki gaya mana kun tashi ba? Har shi Hafiz din ya iya gaya mana?"" ˜asa magana nayi ina jin shi. Yayi ta fada sannan ya kashe wayar, Aunty Hindatu ta kira ni. ""Auta me ya faru?"" Murmushi nayi mata nace mata. ""Ba kome Aunty!"" ""Lubnah idan kika cigaba da shiru taya zamu taya ki wannan yakin, wannan ba hujja ba ne, Lubnah ki bude baki kiyi magana ki gaya min me ya faru?"" ""Ba kome!"" Na kara fada mata, ""Lubnah ina takardun gidan can?"" ""Don Allah kada ki tambaye ni, don Allah kada ki saka min magana! "" Na fada kamar zan yi kuka, murmushi tayi ta ce min. ""Shi kenan idan kina bukatar kudi zan turo miki da"

"dubu dari!"" Ban ce mata kome ba, ta kashe wayar. Zuwa yammacin ranar sai ga Aunty Innah ta shigo ita"

"da Aunty Jamilah matar Ya Umar, ganin gidan yasa duk suka yi shiru. Ni dai ban ce musu kome ba, shine"

"dai yayi ta fada yana faWin. ""Ai ban san me ye matsalar Lulu ba, ace bana gari domin Allah ya gani nayi tafiya kusan wata guda nayi tare da Karimah kuma na bar mata yaran jiya da muka dawo nake tambayarta ashe bata gaya muku, ai har nayiwa Baban Bauchi bayanin dalilin tashinmu, amma in sha Allah kafin nan da wata shida zamu koma wani hatsari ne ya faru amma an shawo kansa. "" ""Allah ya"

"kyauta ya kiyayye na gaba!"""

"""Amin Ya Allah, Luluna idan zasu tafi ki diba musu tsaraba nan, akwai wasu a dakin Karimah bari na"

"kawo sai ki hada musu."" Ya tashi ya fita, can sai gashi dauke da jaka cike da fruit, ya kawo musu da Naira dubu goma a ciki wai su yi kudin abin hawa, Aunty Innah ce ta kawo su a motarta, bayan fitarsa da ya ce musu bari ya tafi muda lawan akwai kayan da aka kawo zai je ya duba, ya fita Aunty Innah ta kalle ni yadda nayi shiru. ""Tunanin me kike yi?"" Ta ciro kuWin da yake cikin jakar ta ajiye min a gefena. ""Mu yan uwanki muna jiranki duk lokacin da kika shirya ba zamu kashe miki aurenki ba!"" Tana gama fadar haka suka mike tare da barin kayan ma bakiWaya basu dauka ba, domin tun kafin su fita Karimah ta fita da"

"Yaranta, aka bar ni a gidan ni daya tal."

*08130269641*

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*"

Ramlat Abdulrahman Manga

Mai_Dambu

BAKWAI

"Zama nayi ina nazarin makomar rayuwata, me nayi na kuskure? Duk da ina son Ya Hafiz amma ban san"

"me yasa yake jin dadin daura min laifi ba, shi ya hana ni gayawa mutane, yanzu yazo yana faWin ni ce me yasa yake min haka ne? Me yasa tow? Dama soyayya tana zama kiyayya ne? Ina cikin wannan tunanin Baban Bauchi ya kira ni, wato Abbanmu yayi ta min fada yana faWin nayi haka ne don ba lalata zumuncin da yake tsakaninsa da Wan dan uwansa, wallahi ban isa ba. Haka ya gama fadar shi nace mishi yayi hakuri. A hankali kuka ya zo min can kuma na fara dariya kamar mahaukaciya, domin haka ne kawai zai saka ni"

jin dadi.

"Tunda na fahimci dariyata tafi kuka saka ni nishadi, na saka a raina na daina kuka akan Ya Hafiz, zan yi"

"dariya. Aunty Hindatu ta zo ita da Ya Sani suka ga gidan, babu wanda yayi magana har suka fita. A ranar Aunty Hindatu ta kira Ya Ado ta gaya masa. Murmushi yayi yana faWin. ""Hindatu dadina dake baki da hakuri, mutane biyar suke da iko akan wannan lamarin Baban Bauchi, Baban Jama'are, baba malam, sai ita Lubnah idan ta ce bata yi duk inda nake zan kwana a Bauchi, amma fa sai ita da kanta ta ji a ranta bata yi duk abinda zamu yi ba yadda muka iya."". ""Amma kasan ya sayar mata da gidanta na Tambari?"" ""Tow ya za ayi tsakanin mata da miji sai Allah idan ita ta bashi fa!"" ""Ado kasan sai Lulu bata da hankalin da zata bashi gida ya sayar ko? "" "" Tow waye ya sani kin ga idan tana bukatar wani abu ayi magana batun gida dama ai an saya mata ne domin su huta da Yawon gidan haya tunda ya sayar ya sayi wani."" "" Amma ai a getto area ne! "" "" Ba gashi ta zauna har na wata guda ba ta gaya miki ne?"" Shiru tayi ya cigaba da magana. "" Baba da Mama sune suka involved din rayuwar Lubnah, idan da zasu tsaya mata Lubna zata samu yanci amma fa sai taso idan bata so ba, kuwa koda su zasu shiga ba zata matukar bata bada hadin kai ba. Babu yadda zamu karshe sai dai shara'a tayi aiki kanmu haka magatakarda kin manta da dokar ce. "" "" Ba dokar na manta ba, na hango tashin hankali da bukatar taimako, bata bukatar kome amma kuma"

"idanunta yana kukan tsoron da niman taimako, wallahi Lulu da ka sani ba ita ba ce a gabanmu"""

"Dakyar ya shawo kanta Ya Sani ya ce mata, ""Ni dai na rasa me shegen Yaron nan yayiwa Abba ne da"

"baya kaunar laifinsa, ki ga yadda Lulu ta koma don Allah? Ko ni da nake zukar wiwi wallahi ban ga dalilin dariyar da take ba, ki ga yadda take abu kamar wacce take cikin tashin hankali."""

"Kwafa yayi suka cigaba da tafiya,"

***

"Ko Ya Hafiz ya ji abinda yake faruwa ne, yadda Yayuna suka fusata, sai gashi

Please Login or Register in order to submit comment