Reading ALAƘAR ZUCI by Mai Dambu Chapter 21 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ikonsa da buwayarsa kasancewar Uwa tana tare da da shi, yan uwansa kuwa masu hadin kai ne, sai gashi cikin buqatar mai kowa da kome ya bunkasa ya isa inda ba a zata ba, yanzu haka yana iya dinkawa ango kayan fitar biki, don bikin da aka yi kwanan nan dan gwamna Bauchi state, shi yayi ta kula da shiga da fitar angwayen, ba karamin kudi ya samu ba. Dama yana taru wurin Aunty Hindatu, ai kuwa ganin haka ya samu kudi aka kara mishi ya sake habbaka kayan auren, da sadakinsa da kome na shi, yana nan a hannu yanzu sun zo"

ne a gayawa Baban Bauchi shirinsa. Shine ya gayyaci yan uwansa.

"Bayan sallah isha, suka hadu a parlourn Baban, suka gaisa aka yi yan hira sama-sama, kafin Umar ya"

"kawo zancen da ya haWa su. Daidai shigowar Hafiz da ya koma gefen Baban Bauchi ya zauna kamar zai koma cikinsa tsabar munafunci, ran Tahir ya b'aci. Shiru baban Bauchi yayi kafin ya ce musu. ""Tow Allah ya nuna mana, amma naso da zaku amince da Firdausi, domin naga ai yarinyar itama."" ""Abba Yarinyar da yake so ba jiya suka hadu ba, ba yau ba akala sun kai shekaru hudu suna tare, don tun tana makaranta suka hadu, yanzu kuma sai a kawo wani batu Firdausin da."" ""Tunda kun shirya mishi yadda zai me yasa zaka kawo min batun amincewata."" Yadiko da take bakin kofa ta ce mishi. "" Ai kasan kuwa yadda ka hana Sani zaman shagonka wallahi ba ka da hurumin bashi abinda baya so, Lubnah ma da ya ta kwashe a hannun Hafiz kai ku tashi idan yaso kada ya bashi kwandala yarona ya yi duk wani abinda ya dace wa"

"kansa ko ni da na haife shi bai jira ni ba, haka kuwa ba wanda zai mishi dole!"""

"Wani irin rikici aka shiga tukawa aka kuncewa, kafin kuma aka kyale kowa yayi yadda ya so, Baban"

"Jama'are ya zo da wasu maza , wanda suke dangin Yadiko aka je nimawa Sani auren Halisah, yarinyar danginta yan Tilde ne, don haka suka tafi aka nima mishi aurenta, ganin yadda suka fito daga babban zuri'a kuma yaro yana da abin yi sannan shima Uban yarinyar ya shirya tsaf, kawai aka karbi sadaki da"

yanke rana. Wannan lamarin yayiwa kowa dad'i domin domin kuwa dangi kowa ya fara shiri.

"An saka ranar bikin wata uku masu zuwa, a cikin wata ukun gidan da Abban ya bashi wanda yake"

"kusa da gidan Ya Umar, aka fara gyarawa ana cire tsohon tsarin gidan, aka fara yin gyaran na zamani. Cikin kasa da wata guda da sati biyu aka gama gyaran gidan."

"Ashobe kuwa a shagon Aminu da Zubairu, Innah ta cire aka kai dinki na su Lubnah domin Mama ta ce"

dole ta zo.

***

Lubnah.

"Bikin sani zai zo lokacin mun gama jarabawa, sai dai har zuwa lokacin gabana yana faduwa da maganar"

"zuwa Bauchi. Domin gani nake kamar duk wani abu zai kara faruwa, haka na sake raina na cigaba da abinda yake gabana. Duk da na dan sauka kaWan, amma kuma ni kaina sai nake ga kamar da sauran yanayin domin jikina yana min nauyi, wani lokaci haka zan ta fama da haki, sau biyu ina zuwa ganin likita da Dijah Bala take hada ni da su, na farko ya ce kitse ne ya taru a zuciyata, na biyu kuma yace wai a cikina sai abin ya saka ni rud'ani, na shiga cikin wani irin tashin hankalin mara misaltuwa nayi shiga, na rasa me ke min dad'i. Ban gaya Ya Ado ba, don yana gayawa Mama zata iya cewa ayi aikin yaushe aka cire min karin mahaifa yanzu kuma wani aikin ni na koma kamar wata kazar mayu, ga shi na daina ganin Baby sai kaina yayi zafi,, ranar wata Alhamis na tafi wurin Dr Dijah Bala. Ta kalle ni a hankali, tana faWin.. ""Ni na ga kamar kina cikin damuwa?"" Jinjina kai nayi a hankali ina wasa da yatsun hannunta. "" Me yake damunki? "" Gyara zama nayi na rasa yadda xan yi magana domin har yau bani da kwarin gwiwa yin dogon magana a gaban jama'a, duk da tana kokarin nuna maka kai ma mutum ne kana da damar fadar abinda yake ranka. Matse hannuna nayi ina motsa bakina nace mata. ""Nan da wata biyu za muje Bauchi bikin Yayana!"" Murmushi tayi tana kallon yadda na matse hannuna da ™arfi. Na kasa fada mata abinda nake son fada, gogewa da tayi da masu irin laluranmu yasa ta matso da kujeran kusa da ni ta rike hannuna da kyau, ""ina tsoron kada Abba ya ce ki koma gidan Hafiz ko?"" Hawayen da nake dannewa ne suka shiga wasan tsare akan fuskana. Cikin shashekar kuka na ce mata.""ba iya shi ba ina tsoron abinda mutane zasu ce ne."" Nan ma nayi shiru ina kallon gefe, jinjina kai take a hankali ta ce min. ""Mutane sun daina maganar kina da kiba ne?"" Da sauri na d'ago kai ina girgiza mata. ""Ashe kuwa tunda basu daina ba, akan me zaki yi kuka? A yanzu Mama da su Barista suna tare da ke, tare da su Innah da Hindatu. Kina jin zasu bari a mai dake gidansa ne? Kada ki manta har yau baki yarda da kanki ba ne. "" Kallonta nake, "" har yau baki yarda kina da goyon bayansu ba ne, baki sani ba ko?"" Hawaye ne ya zubo min, gyara zama tayi tana juyawa akan kujeranta ta cigaba da cewa. "" Me yasa Ahmad ta daina zuwa?"" Shiru nayi ina kallonta na zata ko don an mishi magana ne, girgiza kai tayi tana kallona kamar tasan abinda yake raina ta ce min. "" Kina tsammanin Barista ya hana shi zuwa? A'a ni na gaya mishi ya rabu da ke, a halin yanzu ba namiji kike bukata ba, kanki kike bukatar you need tow love yourself."" Cigaba da kallonta nake, ta mike tana mai isa gaban frij ta dauko min ruwa ta ajiye min tana faWin. ""Har yau baki san yadda zaki kwanci kanki ba, har yau baki san yadda zaki yi fada don kanki ba, yaushe kike tsammanin zaki iya zaman aure bayan nasan wacece matar Ahmad, ya zo nan ya gaya min kin ki kula shi nace mishi ai ke yanzu baya ga kanki bakya bukatar ™arin wani a rayuwarki. Sannan idan ya nace ya aure ki rayuwarki ta baya zaki koma, me yasa muna janyo ki present zamu mai daki past dinki? Daga lokacin da kika fara sanin ciwonki, a lokacin zaki fara tantance waye yake kallonki da idanun basira waye yake kallonki domin biyar bukatar kanshi, ni na gaya mishi ba zai iya gina soyayyarshi yadda ya dace a tare da ke ba domin zuciyarki a rufe yake. A"

"duk lokacin da irin wannan abin ya faru ana bawa masu irin matsalarki lokaci ne, don haka kina da lokaci"

"ki cigaba da kula da kanki da lafiyarki. Sai me kuma?"" Shan ruwa nayi kafin na gaya mata yadda muka yi"

"da likitoci biyu. Murmushi tayi tana faWin, "" na gaya miki dole ki shiga ajin motsa jiki, kina cin abubuwan da na hana ki ci, har yau baki ware abinda zaki ci don lafiyarki ba, da kin kula da haka da tuni wata"

"Lubnah ake magana ba wannan ba."""

"Sai na ji kamar nayi knocking heart dina tare da bude kofar ta ce min farka Lulu. "" Yes dole ki fara motsa"

"jikinki, ki biya kuWi a unguwarku ai akwai inda ake motsa jikin, sai ki fara ina son na ganki nan da wata biyu."" Kallonta nake ta yi cike da mamaki. "" Kina nufin. Idan nayi zan samu lafiyar jikina? Amma kuma ai kunya nake ji wurin za ayi ta kallona."" Na fada kaina a sunkuye. "" Kina jin kunya ko? Kada a miki dariya, bari na haWa ki da wani yaron da na sani sunan Wasim!"" Gyada kai nayi ina wasa da yatsuna, har ta kira Yaron ta gaya mishi, ashe a unguwar yake ta bani number wayarshi. Sannan na mata sallama na dawo gida, bayan na yiwa Ya Ado bayani ya ce gobe zai tafi har wurin da kanshi ya ga yadda Gym din yake, haka muka kwana ina ta addu'a Allah yasa kada na samu matsala da kowa Allah yasa na kasance jaruma wacce zata iya daukar duk wata matsala, wurin karfe tara na gama shirin zuwa makaranta Ya Ado ya kira ni ya ce min. ""Ki je zasu baki wasu tips and abincin da zaki ci, sai ki amsa idan kin dawo muje a saya ko?"" ""In sha Allah zan amsa kafin na tafi."" Na fada ina shiryawa, bayan na gama na fito na nufi titin unguwar"

"da kafa, na je shagon babba ne na gaske....."

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 32"

"A hankali nake tafiya ina kallon mutanen da suke wurin karti ne majiya karfi, sai yan mata yan gayu masu"

"kyau da su, sai na ji na muzanta, gasu gwanin ban sha'awa yadda suke wani yauki zaka fahimci yan gayu ne da basu son tara kitse, wannan yanyin ya dauke kin dan kwarin gwiwa da nake da ita, a hankali na isa ciki tare da tura kofar sai aka bude ta ciki. ""Lubnah ko?"" Gyada kai nayi ina mai kallon cikin wurin yadda kowa yake rayuwarsa. Wasu suna motsa jiki wasu kuma suna hira can gefe da aka saka wani abu kamar labule mata ne a zaune suna yogo. A hankali nake bin wanda ya min magana, wani office ya bude mana, wata kyakkyawar bakar mace cikin shigar kamala da mutunci zata iya kaiwa arba'in amma yadda take kula da jikinta ba zaka Wauka ta kai arba'in ba, da murmushi ta kalle ni. ""Lulu!"" Ya kira sunana, sai na ji na samu nutsuwa da ita, na gaida da ita murmushi tayi ta ce min. ""Adam ya ce min wai auta zai kawo?"" Sai na rasa a ina na santa, kurban tea dinta tayi tana mai ajiye min wani kofi a gabana. ""Baki sani ba don tun kina yar yarinya muka bar Bauchi!"" Zama nayi ina gyad'a mata kai. ""Sunana Nuratu Abdulfatahi kin tuna gidansu Kafaya?"" Sosa kai na fara ina kallon kasa na tuna gidan har yau ana kiran gidan da sunan. ""Nice Kafaya."" Sai na ji kamar an yantani daga wani yanayi na musamman, muryanta na ji a kaina tana tura min cup of tea din. "" Lokacin da Dr Dijah Bala tayiwa Wasim magana ban san cewa ke ce ba, da nace kawai ki zo, sha kada ya huce "" dauka nayi na kurba ba sugar sai kamshin kayan kamshi, da lemon tsami. Da kamshin ganyen tsamiya. "" Tea din ganyen tsamiya ne, yana taimakawa. "" Ta fada tana murmushi, haka na sha sannan ta cigaba da cewa."" Adam yazo wai biya miki, kawai aka turo min shi OMG kin san rabona da Bauchi shekaru ashirin kenan fa yau ga sai dan Bauchi kuma Wan unguwarmu, dan abokin Babana."" Murmushi tayi kafin ta sha tea din nima rashin sabo yasa na sha kaWan..""Bayan rasuwar Babanmu muka dawo nan, Mamanmu ta cigaba da kula da mu har na samu miji nayi aure"

kasancewarmu Yarbawa da aka haifa a cikin arewa sai muka taso da dabi'ar yan arewa bamu manta da

"yarenmu ba."" Shiru tayi tana kallon yadda nake kallon tea din. "" Kada ki damu zaki saba da shi."" Ta fada"

"tana murmushi, ""Na auri wani dan uwana kuma kabilata, sai dai zamanmu bai yi dad'i ba haka muka rabu da dakyar shima ba ni ce na nime saki ba, mun haifi yara biyu da shi, kamar yadda kike gabana haka nima na kasancewa. "" Sunkuyar da kai tayi ina ganin yadda take dauke kwallar da yake zuba mata, haka na rabu da shi na cigaba da rayuwa, sai Allah ya haWa ni da wani dan kasar ghana yazo nan yana kasuwanci ya koma, wani abu da ya faru shine yadda aka yi ta cin zarafina da kibar da nake da shi."" Ta kalle ni yadda nake kokarin toshe bakina, saboda kukan da yazo min. ""A lokacin kaf narasa wani wanda zai dafa min ga tsohon mijina da yake yawan d'aga min hankali, haka Mr Anwar wanda ya kasance bako a cikin mu, shi ne mutum na farko da ya fara kallona a matsayin mutum mai daraja, duk da an san cewa mijina shi ya sake ni don kanshi amma sai da aka yi ta hango gazawata da nuna min halayyata ce bai da kyau domin tunda ya sake ni bani da hali mai kyau ne, haka na cigaba da taimakon Mr Anwar ya gaya min cewa dole na rayu domin har na fara fama da ciwon damuwa, a irin haka na rasa Yarona karami a wani ruwan saman saboda ya je wurin Babansa, a hanya dawowa ya fada cikin lambatu, sai da na ji ina ma da nice na mutu, sai mace da take tare da ni, Mahaifiyata ta kaWai ta fahimci yadda nake rayuwa, hatta yan uwana sai da suka na tsani kaina na ji bana kaunar kaina. Wannan yayiwa tsohon Mijina dad'i"

"bani da zabi dole ya cigaba da abinda yaso. """

"Turo kofar aka yi wata matashiyar budurwa ta shigo tana faWin. "" Momma! Daddy yana ta kiranki fa!"""

"Daukar wayar tayi tana faWin.."" Tuba nake Sarkin da yake mulkar zuciyar Kafaya!"" Ban san me ya faru ba sai ga tana dariya tana faWin."" Idan ka sake na kama ka zaka sha wuya! "" Fita yarinyar tayi tana faWin."" Momma baku girma ke da Daddy;"" ta jima kafin ta katse wayar ta ce min. "" Sorry Mijina haka yake baya iya minti talatin bai ji muryana ba."" Murmushi tayi sannan ta daura da cewa. "" A lokacin na rasa kowa dai Mr Anwar shi ya tallafe ni da shawara da yadda zan tsaya domin har rasa aikina nayi, shi da kanshi ya bude min shagon saloon na fara Allah ya saka albarka a shekara daya na samu damar komawa makaranta, shi ya kara bani shawarar na rage jikina, ina cikin haka sai ya bijiro min da soyayyarshi, duk yadda naso kauce mishi haka ya shiga duk inda xan ji maganar mutane, yayi min hidima da ba xan iya tsallake bu™atarshi ba, a lokacin na tsaya da kafata da taimakon shi na san wacece ni, bai taSa nima na da wani fasikanci ba, sai dai gina ni da yayi da soyayyarshi wanda ya saka na fahimci kaina na fahimci ashe nima mace ce, tunda ni na bukaci mu yi aure idan har da gaske yake, bayan wannan yarinyar da take waje, Nasiba, sai Abdullahi da Hafsa, da na haifa da shi. Sannan shi ya kara tsaya min har na bude nan ina aiki da ma'aikatan gidajen kurkuku na jahar nan, a can na hango Mijina Babansu Nasiba, kinsan me yasa na baki labarin nan?"" Girgiza kai nayi, ina share kwalla murmushi tayi ta ce min."" Saboda ki gane kafin ki zo nima ban gina nan domin niman kudi ba, sai da labarina ya gina min nan, asalin nan Labarina ne ya gina min shi ™addarata tana da nasaba anan, a duk lokacin da aka kawo sabuwar daliba abu daya nake tambayar me ya kawo ta me yasa ta zo? Idan tana da past dinta Mai duhu sai na daura mata nawa labarin ta gane nima ban gina nan ba sai da nawa labarin, akwai mata victim irina da irinki, anan muke bude zuciyarmu, ki saki jikinki Adam ya gaya min kome ya kuma bukaci mu taimaka miki, idan har da gaske sauya kanki ke kanwata ce dole na baki special class domin bana son na hada ki da kome, na tuna lokacin da Babanmu ya rasu har kudin da aka biya na motar da zaa dawo damu Alhajinku ya biya mana hatta abincin da zamu ci na tsawon wata shida, kafin mu bar tsohon unguwarmu Alhajinku yana mana aika duk bayan wata shida, kayan abinci da sutura daga baya fitinar dangin Babanmu yasa muka bar"

"unguwar, daga muka rasa taimakonsa. Yau ga Lulu da na tafi na barta tana Yar shekara shida a gabana!"""

"Murmushi nayi ta ce min.."" zaku school ko?"" "" Karfe bakwai muke tashi idan kin taso sai ki zo ki amshi"

"tips dinki! "" Godiya na mata sannan na bar office din, sau yawa mukan yi alkhairi ba tare da mun san zai dawo ko ya tafi ga mizaninmu, duk da abinda Abba yayi amma yau alkhairinsa da rokon marayu ya saka na samu nima wata alkhairin da shi ya aikata. Murmushi nayi duk da laifinsa yau naji ina sonshi ina kewarsa. Don haka da na shiga motar da zai kai ni makaranta, na fito da wayata ina kallon wayar number shi ne don ko na rasa number kowa bana iya manta number shi da Yadiko da Mama, haka nayi ta kallon wayar. Har muka isa makaranta na biya kudin na fara tafiya, sai da na shiga makarantar sannan na samu wuri na zauna. Da yake karfe daya zamu shiga class na kira Number Abba, haka wayar yayi ta ringing bai dauka ba, na sake kiran bai dauka ba, sai a karo na uku ya Wauka. ""Waye ke kira haka?"" Haka yayi ta magana na kasa magana sai hawayen da yake zuba min haka ya gaji ya kashe shi wayar, kuka nayi ta a wurin na rasa abinda yake min dad'i, sake kiran Mama nayi tana dauka na ce mata.. ""Mama ina kewar Abba ina son ganin Abba Mama ina son Abbana, Mama ki koma wurin Abba ko don ni, Mama ina son Jin muryansa da farin ciki da annashuwa, amma na rasa Mama."" Abinda ba zai tab'a sauya our Afrika mother, wato da ta danna min wani Ash'ar tare da zabga min warning idan na kara kiranta akan Abba sai ta ci Ubana sai na tsinci kaina da yin shiru, ban kara magana ba, kai na ga jidali da lukutar masifa, tass ta wanke ni kafin kuma ta sauko tana rashina, daga haka nayi shiru bayan mun gama waya sai ga kiran Aunty Innah ina gamawa Aunty Hindatu ta kira ni, sai ga Ya Umar da Tahir, ban gama nutsuwa sai ga Ya Ado. Ina zaune a wurin ya kira ni na dauka ya tambaye ni ina aji ne? Nace a'a gani a lambun makaranta bari na fito, har a lokacin kuka nake a hankali na dauki jakata na fita yana tsaye ina isa wurinsa na goma gefen da yake tsaye na kifa kaina a gefen hannusa ina kuka. ""Kina kewar Abba ko?"" Jinjina kai nayi, kiranshi yayi bayan sun gama gaisawa ya ce mishi. ""Abba kai min wata alfarma daya?"" ""Ina jinka!"" ""Zaka yi magana da Lulu ne tana kewarka, gata nan."" Kafin ya kara magana ya manna min wayar a kunnena, sai dai kuma nayi danasanin kiran Abba da Ya Ado ya min, Abba ya kara watsa min bakin fentin da ba zan tab'a mantwa da shi ba, sau gani ina wani irin hakki zuciyata, ta kasa Waukar mugayen kalmomin Abba, tun ina jin shi a tsaye a har na jingina da motar na zame kasa, domin kafana sun kasa Waukar nauyina, zuciyata ta gagara daukar maganar da Abba yake gaya min, wani irin nauyi na ji tare da bude bakina ina niman numfashi, fisge wayar Ya Ado yayi ya saka a kunnenshi ya ce mishi. ""In sha Allah ba zan kara kiranka akan Lubnah ba, ba zan kara ce maka ga ta ba, Abba idan ka yi sanadin mutuwar Lubnah Allah ba zai barka ba!"" Kashe wayar yayi ya d'ago ni tare da saka ni a motar domin har an fara taruwa, ruwa wani dan ajin mu ya mika mishi yana faWin. ""Bata tana bukatar ruwa!"" Amsa yayi ya bude min ya kafa min na shanye, sannan aka kira class rep dinmu aka gaya mishi halin da nake ciki ya ce a je da ni gidan, da taimakon Allah na samu nutswa, daga haka na rufe idanuna, a hanya Ya Ado ya kira Mama ya gaya mata, halin da na shiga amma bai san me Abba ya gaya min ba, ai kuwa Mama kamar ta dirko ta wayar fada take yi kamar zata aro baki ta kara. Kuma tayi alkawarin sai ta kunyata Abba shima kamar yadda ya min a"

gaban Jama'a domin ranta yayi mugun b'aci.....

(Kuna ganin mu bar Mama tayiwa Baban Bauchi tijara a bainar nasi? Yes or no

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 33"

"Gida Ya ado ya kawo ni na kwanta, duk da bana jin barci amma na zaSi nayi lumo. Ina jin kamar na ni ba,"

"taya mahaifin da ya haife ni zai tsane ni ya kira ni da karuwa? Abba ya kira ni da karuwa! Naki zaman aure na biyewa Adamu ya yanka min tikitin karuwanci a lagos, tow in sha Allah idan n kwaso kwanjamau sai dai na kare ni daya na domin suma guduna zasu yi. Bude idanuna nayi tar ina kallon hannuna. Wani irin sarawa kaina yayi kamar an hada karfe da karfe a hankali na ji abu yana zubewa daga hancina, ban kula ba sai da na ga zubar yayi yawa na tashi zaune ashe jini ne, yadda kaina yayi wani irin nauyi haka na koma na kwanta tare da lumshe idanuna, bana son karawa Ya Ado wani damuwar a hankali nayi ta ambaton Allah har na samu sauki na tashi zuwa ban daki na sakarwa kaina ruwan sanyi, can kuwa jinin ya tsaya, na jima a ban dakin na fito na sauya kaya. Na sauko kasa ba kowa sai mai aiki haka na zauna a"

parlourn har lokacin sallah yayi na wuce nayi sallah na kwanta barci ya dauke ni.

***

"Mama kuwa da suka gama waya, tashi tayi gaban wardrobe dinta, kayanta tayi ta sauko da shi, ta ciro"

"wabujejen wando mai matu™ar girma kamar palazzo, ta saka ta dauko wani babban hijab dinta ta saka, sannan ta fito zuwa bangaren Umar ta bugawa matar gidan kofa da sauri aka bude tana ganin Mama ta ce mata. ""Mama ke ce? Fita zaki yi? Lafiya dai?"" ""Central zan je!"" ""Lafiya dai ko? Ai da an gayawa Baban Nawwara ya miki ba sai kin je."" ""Yanzu xan dawo"" ta juya ta fita yadda zuciyarta take tafasa idan ba tsinkawa Abba rigar mutunci tayi a idanun duniya ba, ba zata tab'a jin dadi ba. Don haka ta nufi waje,"

"tana fita matar Umar tana kiranshi, sai aka yi rashin dace ya shiga sallah, baya kusa da wayar ma."

"Mama kuwa tana fita ta samu me keke napap, ta ce ya kaita Central ya fada mata kudin bata damu ba,"

"ta ce su je. Kawai yadda zata yiwa Abba rashin mutunci kawai take hasashe. Duk da gudun da me Napep din yake amma Mama gani take kamar ba tafiya yake ba, kamar ta rufe shi da duka haka take ji, haka ya sauke wasu mata a unguwar Jaki, sannan ya fito ta masallacin Shehi dahiru Usman Bauchi, ya iso daidai office din Yan sanda na Central ya tsaya ta fita ta biya shi kuWinsa,. Sannan ta tsallaka cikin Central, sai da tayi tafiya sosai kafin ta isa layinsnu Baban Bauchi, an taru a kofar shagon ana cin abincin da ake kawowa kasuwa kullum daga gidan domin saukakawa Yaran shagon kashe kudin abincin. ""Usman Jama'are nazo wurinka ne?"" Da mamaki kowa ya juya yana kallon Mama. Wacce ta hade rai sosai kamar ba ita tayi maganar ba. Da kamar ba zai kulata ba sai can ya ce mata. ""Ki je gida zan zo!"" ""Ba isa ba! Ka gaya min yaushe ka ci maita da kake son kashe min Y'a? Mai Lubabatu tayi maka da zafi har haka?"" Shiru yayi kai dan kanzagi ya taso yana faWin. "" Mama kasuwa ne nan don Allah ki yi!..."" Tass Mama ta wanke shi da mari, ta kara wanke shi da mari sai da yayi baya kamar zai fadi, Baban Bauchi ya ce mata. "" Wacce irin hauka yake damunki? "" "" Irin wanda kake dauke shi! Irin wanda yake kanka, irin wanda ya saka ka yi fatali da zancen Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, kowa Ni shugaba mai kiwo ne, kuma za

Please Login or Register in order to submit comment