Reading ALAƘAR ZUCI by Mai Dambu Chapter 12 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kusan kashe shi!"" Mama da take bakin kofar basu san ta fito ba ta ce mishi. ""Me yayi da za a kashe shi? Shi bai yiwa lubnah kome ba, nice a matsayina na uwa na kashe Lubnah na sha ganin damuwa a cikin idanunta amma na rufe nawa idanun bana son na karanta. Balle har na samu damar cewa tayi"

"hakuri da ace na karanta ai da yau yarinyar nan bata nakasa har haka ba taya zan yi da Lubnah?"""

"Cikin kuka take magana, sanin cewa itama tana da laifi amma lokaci guda ta tsaya sai Yaran suka"

zagaye ta suna bata baki. Dakyar Mama tayi shiru.

"Shigowa suka yi dakin, suka same ni kwance nayi rigingine, ina kallon sama ni kaina bana ce ga dalilin"

"haka ba, amma na tsinci kaina da son kwanciya haka karar bude kofar yasa na rufe idanuna. ""Auta!"" Juyawa nayi ina kallonta. ""Tashi ki ci abinci!"" Duk yadda nake ji a zuciyata bana son ganin Mama tana damuwa balle yau ganin hawaye na zuba mata yasa na mike zaune. Abincin ta kawo min ta zauna a gefena tana mai diba ta bani a baki. Kallon cokalin nayi kafin na bude a hankali na amsa, hawaye na zuba mata tana bani ina ci, a hankali na kai hannuna saman fuskarta na goge mata. Murmushi tayi nima na mai da mata, na cigaba da amsa tana kuka har na kauda kaina domin idanuna yana cika da kwalla. Ruwa Aunty Innah ta bani na sha ina son Magana amma ban san me zance ba, a hankali na ce musu. ""Amma ba zan koma gidan Ya Hafiz ba ko?"" Ya Tahir ya matso gefena ya riko hannuna ya ce min. ""Waye ya ce zaki koma gidan Hafiz?"" Girgixa kai nayi matse hannuna yayi ya ce min. ""Ki kwantar da hankalinki, babu inda zaki in sha Allah. Daga gidana babu wani wurin da zaki kin ji zaki zauna a gidana ko?"" Gyada kai nayi"

"ya ce min. ""Kada ki kara tuna wani can da bai da amfani a rayuwarki da namu kin ji!"""

Gyada kai nayi suka gaya min kowa ya shirya domin na zauna a gidanshi. Amma firstly lafiyata suke

"bukata domin sai da ita zan rayu. Tun daga ranar aka daura ni akan magani, idan Aunty Innah ta taso zata zo ta zauna tana kara tisa min karatun Alqur'ani da azkar. Haka yasa kullum ina cikin Alwala koda kuwa bani da tsarki ne, zuciyata ta samu nutswa. A cikin sati biyar da nayi a cikin babban asibitin Bauchi,"

duk wnada ya ganni sai ya san na samu nutswa sama da can baya.

*

Hafiz

"Ya gigice domin har Karimah sai da ya koreta, kamar zai yi hauka sannan kullum yana hanyar wurin"

"Baban Bauchi, tare da rokon ya saka baki Lubnah ta dawo amma baban Bauchi ya ce yana kan ™o™arin ta dawo ya jira a sallamota, domin har ga Allah tausayi Hafiz yake ji, yadda ya gigice har Jama'are ya je gaban Baba Malam yana kuka wiiwii da yake shima Baba Malam ya Wan ji haushin abin da Hafiz yayi"

amma da yake zuciyarsa muguwa ce sai gashi ya kira Baban Bauchi...

*08130269641*

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*"

Ramlat Abdulrahman Manga

Mai_Dambu

*Littafin nan na kudi ne akan 1500*

"*1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105"

ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 04 67 67my Nita*

Domin tura shaida wannan number. +234 703 513 3148 ko wannan 08130269641

Posting Arewapen da Telegram

SHA SHIDA

"Da yake zuciyarsu ta cika da zalinci da mugunta, yadda yake shiga ba nan yake fita ba shi damuwarsa a"

"maida Lubnah dakin Hafiz haka ne zai saka Hafiz ya samu nutsuwa, sai dai shi Baban Bauchi ya tabbatar mishi da cewa case Win bayana hannunsa yana hannun Baban Jama'are, wato mahaifin Hafiz, haka ya saka Hafiz a gaba har gaban mahaifinsa. Bayan sun zauna ba tare da dogon magana ba, ya ce ga abinda"

zai yi kuma Umarni ya bada ba ba kome ba. Shiru Baban Jama'are yayi tare da kallon Mahaifinsa. Sannan

"ya kalli Hafiz da yayi wani zuru-zuru. Ya ce mishi. ""Baba ka tambaye tsakaninsa da Allah Lubabatu ta"

"zalince? Idan ya ce eh yau ba sai gobe ba zata koma dakinsa idan kuma ya kasa ba ni amsar tambayoyin da zan mishi har abada ya rasa ta kenan."""

"A matu™ar razane Hafiz yake kallon Mahaifinsa, ya kuma kalli Baba Malam, kamar ya ce. "" Don Allah"

"Baba Malam, ja saka baki wallahi abubuwan ba sauki."" Gyara zama Baban Jama'are yayi ya ce mishi. """

"Wallahi warabbul ka'aba idan har ka tabbatar sau daya Lubabatu ta cutar da kai tow yau zata koma dakinka! "" Wasu irin zufa ke karyo mishi yana sharewa suna kara karyowa."

"""Ka bawa Lubabatu maganin hana daukar ciki ko baka bata ba?"" Baban Jama'are ya watsa mishi"

"tambayar, kamar yayi kuka ya rike hannun Baba Malam. Yana me gyad'a. "" Da bakinka zaka gaya min?"" "" Na bata"" Hafiz ya fada yana shashekar kuka."

"Murmushi Baban Jama'are yayi yana kallon danshi, cikin wani irin yanayi na Tausayi me zagaye da"

"bakin ciki. Ya ce mishi. ""Ka bata kwayar yan shaye-shaye ko baka bata ba?"" Cikin wani irin kuka ya ce mishi. ""Na bata?"" Cizon lips dinsa Baban Jama'are yayi yana jin idanunsa na cika da kwalla.. ""ka sayar"

"mata da gidanta ko baka sayar ba?"" Kanshi a sunkuye ya ce mishi. ""Na sayar Baba!"""

"""Waye ya shiga tsakaninta da danginta?"" Cikin wani irin gigita ya kalli Babansa ya ce mishi. ""Baba ka gaya"

"min ba zan same ta ba har abada, wallahi yanzu na tuba ina son Lubnah kamar yadda ta so ni a baya. Don Allah kada ka raba ni ita."""

"Zuciyar Baban Jama'are yayi laushi amma abinda ya saka Hafiz saduda na karamin al'amari bane. ""Na"

"san halinka na san waye kai. Da ka girmama kanka da yau an wayi gari duniya ta girmama ka. Shi girmama ana nimansa ne tun daga yarinta Yaro ya yi abinda Manya suke yi sai ka ga girma ya shige shi. Da yau ka mu'amala Lubnah da adalci ina ga da yanxu kuna da Yara uku zuwa hudu, amma haka ka kashe ta kana ta kwashe duk abinda ta mallaka bayan ta tsaya maka, tayiwa Uwarka, tayi maka, tayiwa Yaranka, tayiwa yan uwanka, wacce irin son zuciya ce haka? Me tayi maka da zafi haka? Na zata kaf duniya idan akwai wanda zaka bawa kariya Lubnah ce, iyayenta suka maka riga da wando suka dauki yarsu mafi soyuwa suka baka, a lokacin akwai wani bawan Allah da ya zo yana sonta da gaskiya yarinyar nan ta juya baya ta ce bata son shi sai kai, yau an wayi gari ka gama lalata mata rayuwa, yau yarinya da bata wuce shekaru ashirin da shida tana zuwa da bakwai tana can tana fama da jinyar bakin cikin da kayi ta cusa mata, Hafiz ni na haife ka amma ni ma ban tsira daga kaidinka ba, me yasa sai Lubnah? Me tayi da zafi ka mata haka? "" Hawaye ne yayi ta zubo mishi yana faWin n. "" Don Allah ka yi hakuri ka rufa min asiri,"

"Lubabatu ita ce rayuwata, ita ce arzikina. Baba don Allah ka yafe min ka bani lubnah a karo na biyu."""

"""Ba zan iya ba kayi hakuri, kaf duniya ni nake da iko da Adamu da Hindatu idan nace su dawo da ita"

"zasu dawo da ita amma itama ina son ta shaki iskar yanci, ta san itama mace ce kuma mutum mai yanci, idan na ji labarin ka kuma d'ago maganar nan wallahi akan mahaifiyarka zan sauke shi. Kai na shiga tsakaninku da Lubnah har abada babu aure a tsakanin sai zumunci shima idan ta gadama idan na ji"

"labarin wani abu ya faru sai ka gani a kwayar cin tuwonka!"""

"""Yanzu ni ban isa ba! Yaron nan yayi nadama!"" Inji baba Malam!,"

"""Kayi hakuri Baba kai ikonka akanmu ne, Yaranmu kuwa ka barmu, akansu da ace tun farko ka amshi"

"uzrin yarinyar nan da yau maganar bata dawo hannunmu ba, Baba ita gaskiya daya ce, don Allah ka bar yaran nan su dauki path din da kowa ya mishi duk wnada ya zalincin wani Allah ya bi masa hakkinsa."" Rikicewa Hafiz yayi yana kuka yana rokon a bashi dama Waya. Babanshi kuwa ya ce ai yayi watsi da"

damarshi tun fil azal yanzu ya cigaba da hakuri kawai.

"Wannan abin ya d'aga mishi haka, haka ya dawo wurin Hajiyarsu yayi ta kuka yana tambayarta me yasa"

"tayi masa haka, me yasa ta shiga rayuwarshi da farko ya zata zai iya handle din matsalar sai ya fahimci ina kome ya lalace mishi, bai taSa kawowa yana son Lubnah ba sai yanzu da ya rasata, haka yasa ya sha alwashin matukar bai same ta ba, har abada babu me samunta itama Hajiya ta kara tabbatarwa matukar basu dawo mishi da ita sai dai ta kare rayuwarta babu aure. Yadda suke kulla sharri matukar Lubnah bata dawo gare shi ba, abinda zasu mata sai ta zama abin tausayi. Wannan masifar da suke kulawa ya tsaya a tsakaninsu sannan itama Hajiyar zata je har Bauchi ta roke su idan suka ka ki kuwa sai dai su san"

"yadda zasu da Lubnah. Wanann shi ne tsarin da suka yi, bayan sun manta da akwai Allah."

**

Lubnah

"Rayuwa kamar littafi ne, yau idan wannan shafin ya bude maka gobe wani zai kara budewa, haka"

"rayuwata ta shiga cikin jerin littattafan da ban san lokacin da na mallake su ba, kwanakina arba'in aka sallame ni, zuwa gidan Ya Tahir. Wanda shi ya fara nuna sha'awarsa akan na zauna a wurinsa. Aka gyara"

min dakina ba abinda ba a zuba min ba.

"Tunda na dawo na samu nutsuwar zuciya da ruhi, shi yake bani magani ya kuma tsaya a kaina sai na ci"

"abinci na sha maganin. Safe da yamma da rana kuma Matarshi tana bani. A hankali nutsuwa da kwanciyar hankali ya fara dawowa a rayuwata. Tseren da muka fara da kaddara ya dawo abu mafi sau™in isowa. Mama gidan Ya Umar ta koma abinta, da suka mata maganar ta koma gidan Abba ta ce bata san da zancen ba, sosai Mama ta dauki wuta domin tafi kowa daukar zafi shi kanshi Abba sai da ta kai ta kawo yana shakkar mata magana, haka ya tafi har Jama'are yana samu Alhaji Ahmed Galadima babban wansu Mama ya roke shi ya saka baki Mama ya dawo, murmushi Yayi ya ce mishi ka zauna da ita tsawon shekaru arba'in ka san wacece ita ka je kai da kanka zata dawo! "" Ba haka Abba ya so, Alhaji Ahmed Galadima ya tirsassa Mama ta koma sai gashi shima ya ce ya lallabata, kai karshe sai gashi ya kira Ya Ado tare da rokon shi da Yan uwansa su saka baki Uwarsu ta dawo dakinta. Ya ce mishi zasu mata magana in"

sha Allah.

Ai kuwa Ya Ado yana yiwa Mama magana ta ce ita fa ba inda zata koma ba sai dai yayi duk abinda zai

"yi, dukkanmu muka yi ta bata hakuri kafin ta amince ta koma amma shima Abba sai da yaji a jikinsa. Tsofaffin nan suna son junansu amma bakiWaya sun koma kamar wasu kananan Yara sai wani jayayya"

suke. Haka muka cigaba da rayuwar a hankali ina ™o™arin zama mutum daga layin mahaukata zuwa jinsin

mutane masu lafiya da cikakken hankali.

"Sai da wata biyu kafin na fara jinin hailata domin shima daukewa yayi saboda tashin hankali, a wannan"

"watan na fara kirga kwananki Iddana, da yake kwanaki biyar nake ina gamawa, na gayawa Aunty Hindatu da Aunty Innah, suka sani. Don sun ce idan yazo na gaya musu. Kamar da wasa na daina tunanin wani can Ya Hafiz, na daina tunanin kowa ni yanxu ai mazan tsoro suke ba ni, ba iya maza ba duk abinda za ayi tashin hankali da fada a kai take sai naji kamar zan mutu da tashin hankali. Shi yasa bana shiga ko hayaniyar Yaran Ya Tahir, suna fara zan gudu daki bana son tashin hankali ko yanayi sai naji kamar wani"

abu yana yawo a kaina. Haka yasa Uwar tana jin sun fara zata fara fada da kokarin kiran Babansu.

"Wata hudu da mutuwar aure duk da ban gama idar ba, ranar na samu bakuntar Ruma Rabi'u Mai shanu"

"ta zo min, Nafisa Sadi Gital, Hafsat Faruq Babaji, dukkansu Uku kowacce da Yaranta nayi mamakin da suka ji labarin ina gidan Ya Tahir.. ""ladies a ina kuka ji ina nan gidan?"" ""Jalilah Kamil Jama'are ta gaya mana!"" Lashe bakina nayi, sai kallon tausayi suke min. Yadda nake zaune kowa yasan yadda bana son kallon tausayi domin sai na fara jin wani irin tashin hankali. ""Ku daina min kallon tausayi, ina da condition da mentally ill idan aka cigaba yanayin yana birkita min ™wa™walwa Please."" Yadda nayi maganar sai na ga suna kuka. Which mean sun san da haka, haka suka rungume ni tare sha faWin. ""Lulu in sha Allah zaki yi farin ciki, Ubangiji ya kawo lokacin farin cikin ne."" Murmushi nayi ina shafa bayansu nace musu. ""Alhamdulillahi Ubangiji ya bamu hakurin akan rayuwa."" Daga nan jefi-jefi ina shiga hiran wani kuma nayi shiru nayi ta kallonsu kowacce take gaya min Yaranta da sauran nasarar da suka samu a lokacin suka bani shawarar idan na gama Idda na fara aiki, wani aiki zan yi? Ni da hayaniya yake d'aga min hankali, tow kadai nace musu anan suka wuce sai dare suka tafi bayan sun kawo min kayan alkhairi kala kala. Haka na yi ta shafa rayuwata a hankali har na gama iddana ina kuma ganin likita a kai a kai. A"

lokacin likitan shima yana jin dadin ganin yadda nake rayuwa cikin aminci da nutsuwa.

"Ranar da Ya Hafiz ya ji labarin na gama Idda, sai da ya kwanta a gadon Asibiti. Yayi ta surutu Matarshi ce"

"aka raba shi da ita har da fisge-fisge, abin da ba dadin ji domin sai gashi kamar mai cutar farfadiya haka yake wasu abubuwan."

Da na ji labarin na tausaya mishi amma idan na tuna yadda yaso kashe ni sai naji shi ba abin tausayi ba

"ne da ya samu wuri kashe ni zai yi da kwanaki na, gara da Allah ya yakin ce min shi da an barni da halina tabbas da na mutu."

"Kwatsam ina zaune Aunty Innah ta nima min aikin koyarwa, wai ko dai rage min zaman da nake na"

"kadaici, matata kuwa da Ya Hafiz ya rike sun karba aka sayar aka sauya min wata yar karama mai kyau, haka na fara zuwa aiki da ita. Bana shiga rayuwar kowa bana iya d'ago kai kalli mutum, asalima maza tsoro suke bani domin kallon Ya Hafiz nake su. Malamai mata ma sama-sama muke gaisawa."

"Haka na cigaba da aikina yaran bani da matsala da su, musamman da suke ™anana. Ina koya musu"

"math, yadda na samu nutsuwa a yar wannan lokacin yasa hatta Yaran sun san bana son tashin hankali. Bana son magana bana son hayaniya. Sai Allah ya bani sa'a akansu yadda ko tari basu min nima da na fahimci sun fahimci halina, sai nake saya musu yar choco-choco ina bawa masu ™o™arin cikinsu, ina son Yara ina son ganinsu cikin farin ciki da walwala. Haka yasa yaran idan na shiga ajin sai su yi shiru kafin su mike su gaishe ni, sai na musu alama da da hannu suke zama na cigaba da musu karatu, kasancewar makarantar private ne sai Allah ya taimaka duk ranar Alhamis ina fita da su, PE physical education,"

saboda Yarar juma'a manya ke fita.

"Yau da ya kasance Alhamis na isa Makarantar da wuri, nayi parking sannan na wuce staff office nayi sign"

"sannan na nufi hanyar aji sai ga daya daga cikin malaman makaranta ya ce min. ""Mrs Jama'are kina headmistress tana kiranki!"" ""Ok na gode!"" Na juya na wuce office din, ina shiga da sallama idanuna ya"

fad'a cikin na......

*08130269641*

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*"

Ramlat Abdulrahman Manga

Mai_Dambu

*Littafin nan na kudi ne akan 1500*

"*1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105"

ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 04 67 67my Nita*

Domin tura shaida wannan number. +234 703 513 3148 ko wannan 08130269641

Posting Arewapen da Telegram

*Last Free pages*

SHA BAKWAI

"Wani irin faduwa gabana yayi wnada ya saka ni ji kamar na juya da gudu, me ya kawo Ya Hafiz inda nake"

"aiki? Me ya kawo shi? Abinda zuciyata take ta tambayata kenan jikina yana rawa a hankali. ""Shigo mana Malama Lubnah!"" Ya fada yana murmushi, wani irin kuka ne yaso min, na shigo ina gaida headmistress, ""Auta kin tashi lafiya!"" Kasa nayi da kaina ina faWin. ""Alhamdulillahi Aunty Barakah."" ""Masha Allah, ga sabin dalibai ne aka kawo miki sai kuma Malam Hafiz yace yana son yasan Malamar domin dai fada mata yadda zata kula da Yaran "" ""tow!"" Na fada muryana yana rawa. ""Yawwa Madam na gode, ga Yaran Aliyu Hafiz Aliyu Jama'are, Asiyah Hafiz Aliyu Jama'are ."" ""A'a tsaya ba sai kai ne Ex dinta!"" Inji Headmistress, murmushi yayi irin wanda ya saba yaudarar mutane da shi, ya ce mata. ""Madam ba wani Ex raba mu Dole suka yi amma nasan Luluna tana sona!"" ""Aunty Barakah zan tafi Class idan ya gama ya kaai yaran!"" Na aro jarumta nayi waje kafin ta samu damar sake wani Magana, ina tafiya amma bani da nutsuwa duk wnada ta ganni musamman yadda nake kallon office din Aunty Barakah zaka fahimci a tsorace nake, haka na isa ajin yaran suka gaishe ni na amsa tare da zama ina sauke numfashi, daya daga cikin Yaran da suke me suna Munir ya kawo min ruwa da gudu, ya mika min. Murmushi nayi na nuna mishi nawa, murmushi yayi na ce mishi. ""Je ka zauna na gode!"" Komawa yayi ya zauna na fara kiran sunansu, ina cikin kiran Ya Hafiz ya iso class din, tare da Yaransa ni dai ban d'ago kai na kalle shi ba, haka na cigaba da aikina ina kiran sunan Yaran. Yadda yazo ya min rumfa a kaina ya janyo min wani irin tashin hankali da tsoro uwa Uba jikina wani irin rawa yake. ""Luluna, nayi kewarki ina bukatarki sosai ina jin kewar kome naki, ina jin kewar can ™asarki me jekewa jabga!"" Wani irin mikewa nayi jikina yana wani irin rawa. Na fara ja da baya, yana takowa har sai da ya kure ni a bangon. "" Ki dawo ko kuma na saka miki abinda zai saka ki dawo dole!"" Yadda yayi magana yasa ni durkusawa a wurin tare da toshe kunnena. A tsorace hawaye na zuba min ashe ina murna na rabu da shi ashe zai dawo innalillahi wainnalihir rajoun, Ya Allah me nayi da zafi haka, fita yayi ya bar Yaran suna ta min dariya, ni dai ban kula ba bayan fitarsu na ji kaina yana amsawa da dariyarsu, daurewa nayi na fara koyarwa a lokacin Yaron nan ya fara kuka, wato Yasir, kuka irin me d'aga hankali sai ji nayi kaina kamar zai fita shi dai a kai shi Yusrah. Ranar Yaron nan da ya saka ni a gaba da kuka, sai da naji kamar zan yi hauka. Haka ya Hafiz yake zuwa yayi ta min rashin mutunci, idan ta kama kamar dai rufe ni da duka a gaban jama'a, da yake gaya musu ya mayar da ni, yan uwana suka zuga ni, a hankali sai damuwar da na rabu da ita ya fara dawowa, na kasa fadawa kowa domin ya tabbatar min duk ranar da aka kira shi aka mishi magana wallahi zai dauke ni a nime ni a rasa"

"wannan yasa Ya Hafiz ya sake dawowa Rayuwata, kamar zan yi hauka rashin mutunci sai wanda ya karu."

A hankali na fara kin zuwa aikin sai dai na kwanta idan kuma zan fita zan tafi wurin Aunty Hindatu ko

"aunty Innah, idan suka tambaye ni me yasa ban tafi aiki na sai naki basu amsar tambayoyinsu. Ranar dai Headmistress ta kira Aunty Innah tace kusan sati biyu ban zo makaranta ba, Aunty Innah tayi ta fada ta kira Ya Ado ta gaya mishi, kai tsaye ya ce mata. ""Lubnah ba zata ki zuwa makarantar ba, akwai wani abu"

"da yake faruwa. Ta je zan tura Sani ya bi bayanta ya kuma yi min bincike idan da wani abu ya gaya min."""

"Haka ta kira ni ta ce na shirya na tafi, kuka ne ya zo min tsoro da fargaba ya cika ni, domin kullum sai"

"kira ni da barazanar sai ya dauke ni ko ya kashe ni kowa ya rasa, tunda naki na zo makarantar. Haka yasa na shirya ina kuka na tafi, ina isa wurin parking na fita daga motar sai gashi, yadda ya juyar da ni yayi ta kifa min mari, Malamai maza suka zo ya daka musu tsawa tare da kwatar key motar ya bude zai saka ni, Ya Sani ya rufe shi da duka, wani irin dambe suka kama yi, na shiga motar na rufe kaina ina kerma. Dole Headmistress ta kira Aunty Innah tare da gaya mata abinda yake faruwa, ita kuma ta kira Ya Umar daga muda lawan suka nufo makaranta lokacin an samu an raba fadar da kyar, Ya Sani yana faWin. ""Kai uban"

"waye ya tsaya maka a Bauchi shege bagidaje, ka kuma taba Lubabatu sai na karya maka hannu."""

"""Wallahi idan ina raye Lubnah ba zata tab'a samun peace of mind ba, matu™ar ina numfashi, sai dai ta"

"ga wasu mazan da idanu, amma wallahi babu namijin da ya isa samunta, gara ta kare rayuwarta a matsayin karuwa!"" Zuwan Ya Umar da Yan sanda yasa aka kama ya Hafiz ni kuwa Aunty Hindatu tana zuwa a hankali na saka kafa na fito, wani duhu ne ya lullube min ganina, a wurin na zube sumammiya."

"Daga nan ban kara sanin me ya faru ba, sai bayan wani lokaci, na farka na ga Yadiko tana zaune suna"

"hira. ""Yar iska munafuka ta koma wurin Uwarta ban isa ba, ni ina nan ina tausayin Jalilah ashe ita ta gaya masa har inda Lubnah take, kai hatta number Lubnah munafuka ita ta bashi, nayi mamakin ashe duk abinda yayi ta faruwa tana sane da ita Hafiz yake hada baki a cutar da ita me Lubnah tayi mata? Ai Sani ya so zane ta, na ce ya kyale ta ta ji Allah zai mata sakayya mene ne a cikin duniyar wanda Lubnah bata gani ba, Allah yasa haka ne mafi alkhairi, zaman Bauchi ya kare itama Lubnan ta bar Bauchi hala wani arzikin ne yake nimanta!"" Inji Yadiko tana fada kallon yadda na tashi a hankali, ina kuma zan tafi? Na gaji na gaji da rayuwar da nake ji nake kamar rayuwata tafi bu™atar mutuwa da wannan rayuwar, na rasa yadda zan yi da kome baya min dadi, sai da nayi alwala na fito na gabatar da sallah azhar da asar, ina idarwa Yadiko ta tura min abinci, kallon abincin nake ina kallonshi kamar naga sabon abu, haka nayi ta kallon abincin. ""Ci abinci Auta!"" Haka na dauki cokalin na dibi jollop din macaroni na kai bakina, ina ci hawaye na zuba min. ""Ba zan hana ki kuka ba, domin lokacin da kika so fahimce ki mun kasa fahimtar ki, yanzu kuwa da muka fahimce ki ba zamu hana ki kuka ba."" Haka yasa na dan ture abincin na cigaba da kukana, shigowar Ya Tahir yana waya. "" Yawwa gata ta farka bari na bata. "" Mika min wayar yayi, na dauka ina shashekar kuka. "" Lulu"" "" bana son sunan nan"" na fada a sanyayye. "" Lily fa! "" Sauke kukan nayi a hankali na ce mishi"" Ya Ado!"" "" Na saka Innah su hada miki kayanki, in sha Allah zan miki booking flight nan da yan kwanaki, am sorry bana nan amma nasan Attahiru da Umar da Sani sun yi duk abinda zan yi, Lily i promise you in sha Allah daga lokacin da kika dawo wurina ba zaa ki sake samun wani threat daga wani ko ayi bullied dinki ba zan tab'a bari ba. Zan zame miki Abba zan zame miki Mama zan zame miki kowa naki, ba zaki kara kuka ba. "" Sai ga hawaye wannan nabin wannan, sharewa nake. "" Ba zai kuma sanin inda kike ba, kai ko takowa ba zai kara ba, in sha Allah ba zaki kara kuka ba. Lily na gaya miki in sha Allah. "" Kukan da

Please Login or Register in order to submit comment