Reading ALAƘAR ZUCI by Mai Dambu Chapter 24 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce ba zasu yi aikin da shi ba, shi kuwa ya rubuta musu cewa duk wanda ya bar tsohon ma'aikatan ya bari kenan share dinsa za a rike bakiWaya Saboda an same su da laifi dama. Jin zasu yi biyu babu yasa suka hakura. Hauka suke da zasu asara. An raba abubuwan sanarwar daukar ma'aikata"

ta ko ina babu kama hannun Yaro.

***

Lubnah

"Gym kaWai nake zuwa, bana zuwa ko ina sai zaman ya fara gundura na. Ina zaune a parlourn ni da Ummu"

"da Princess ina daura lalle a yatsuna, shekaranjiya ya Ado ya dawo daga Bauchi akan jikin Abba, ya je dole ya ganshi kusan cutar saukar jini da tagayyara da mutum, haka yasa shi ya je har yana ganin ko za akawo shi nan lagos ne, sun dai ajiye maganar idan jikin yaki dole lagos za a kawo shi. Shine Mama da"

"aka yi ta rokon arziki ta dawo dakinta, ki tayi sai da na saka baki na rarrashe ta, ta amince ta dawo. Duk"

da haka ana d'ago maganata zata takawa kowa burki ita fa mama na lura ta zama yar kunar bakin wake

yanzu abu kaWan zata tashi boom.

"Da zai dawo ta haWa mishi tsara har da madarar kuka da yake na gaya mata ina ciwon mara kwanaki,"

"shine ta ce idan aka samu me zuwa zata bani madaran kuka. Kullum da safe ina shan cokali daya na hada ruwan dumi, ba lallai sai da na dumin ba, saboda yana wanke mara da maganin sanyi. Sai lalle da nake so saboda yatsuna, sai magarya, nomi ridi mai gishiri da yaji da mai, gyada mai gishiri, aya da suga na yara ne, ni dai kayan cina har da garin karago, haka dai aka turo min da acca da kome na irin namu masu"

gyaran jiki.

"Aunty Zakiyah da safe madarar kukan ta haWa min da fruit ta min shaka da shi, sai yar yau da tayi da"

"kunun gy'ada wanda ta zuba alkama a ciki, sai da na sha shaka kafin na taSa abincin, a cikin kayan Aunty Zakiyah na ga har da wani hadin daka da Mama ta turo mata, tunda na gana kunshe dariya na, ta zungure min goshi. ""Munafunci kawai surukata ta aiko mun da kayan gyaran aure ne, bana son saka idanu?"" Ban san me ya jefo tambayar kan harshe na ba nace mata. ""Idan nima na samu nutsuwa irin taki haka Uwar mijina zata min hidima?"" Juyawa tayi tana kallona cike da mamaki ta ce min. ""Kina da saurayin ne?"" Girgixa mata kai nayi da sauri ina rike bakina. ""Da gaske kina da interest akan aure?"" Ajiyar zuciya na sauke na ce mata. ""A'a ni fa kawai yazo bakina ne, bawai don ina da ra'ayin yin auren ba ne, sannan wa nake da shi?"" ""Doctor Ahmad!"" Kallonta nayi nace mata, ""don Allah mu bar maganar nan Allah ya gani bana son shi, kuma ban tab'a daukar shi a matsayin wanda zan zauna da shi ba, asalima yaya na dauke shi, don Allah kada wani ya ji ya dauka ko na ajiyewa wani ne!"" ""Lubnah zo ki bani document dinki ga wani opportunity ya samu Allah yasa a dace!"" Fitowa nayi na samu Ya Ado ya nutsu akan computer dinsa, ya d'ago kai yana faWin. ""Oya dauko min takardunki zan rubuta miku VC letter ana niman ma'aikata har da masu irin matakin karatunki."" Haurawa sama nayi da gudu na gaji da zaman gida kusan for good 3 yrs, a yanzu fa ina ina gudu ni kaina sai naga ina burge kaina, ba da kamar wata bukka ba, amma a yanzu jikina a tsantsame. Wargaza wardrobe dina nayi na kwaso takardun na sauko da gudu na kawo mishi, sannan na tsaya a bayanshi ina ganin yadda ake cike vc din. ""Wacce ma'aikata ce a ma'aikatan sufurin kudi ne?"" (Wato ministry of financial) "" Kamfanin KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY ne!"" Wani yatsina fuska nayi ina faWin. "" Wannan ba zai wani abun arziki ba idan ba zaman shan shayi ba! Amma ai kudi yana aikin gwamnati!"" "" Ki cigaba da jiran aikin gwamnati idan a kasan nan ne kafin ki samu aiki da takardarki, babbar Yarki ta gama jami'a har da yara uku gare ta. Sai dai ko idan kina son koyarwa?"" "" Haba Ya Ado, aikin gwamnati bai da wuya kai da kake lauya fa! "" Na fada ina tura baki. "" Ai suma organization ce ta bude firm Winsu, ba gwamnati ba sannan baki ga su ma da kansu suna shara'a da gwamnatin ba, kudin da suke samu ana bayansu daga kudin da clients dinsu suke biya ne idan za ayi Shari'a, so su ba gwamnati ba ne, su masu zaman kansu ne!"" Inji Aunty Zakiyah, ta kare Mijinta. ""Ikon Allah, a gidan nan ne zaka yi magana da mata miji ya shigar mata kayi da miji matar ta shigar mishi. Ke ba aikin gwamnati kike ba?"" Na tambaye ta ina tura baki. "" Nima da farko wata kungiya ce ta dauke ni aikin wucin gadi daga baya kuma sai asibitin suka ga ana bukatar gurbina. Idan kuma zaki yi aikin goge"

"goge da share share ai duk aikin gwamnati ne sai ki zo mu baki!"" Tura baki nayi Princess ta kwashe da"

"dariya wai. "" Aunty Lulu idan kika yi haka sai ki yi kama da Moana, ki ga yadda kika yi da face Winki, ko"

"Ummu?"""

"Kallon iyayen nayi da suke ta min dariya, ""Allah dai na gayawa Mama abinda kuke min!"" Wayar Ya Ado"

"ne yayi kara ya dauka yana magana a hankali, "" ok bari na shirya booking Allah ya kawo ku lafiya!"""

""" Lafiya Ya Ado!?? "" "" SAN lafiya? "" "" Daddy lafiya?"" Duk lokaci guda muka mishi tambayar. Katse kiran"

"yayi ya ce mana."" Jikin Abba yaki za a kawo shi nan ne."" Ya fada yana kallon laptop din, ai kuwa hankalina ya tashi take na nime walwalar da nake na rasa. "" Shi da waye zasu zo?"" Aunty Zakiyah ta jefa mishi tambayar. Tana kallona. ""Shi da Tahir da Mama ta yadiko zata zauna, matar Sani bata da lafiya tayi bari."" Ajiyar zuciya na sauke murmushi tayi ta ce min. ""Zai tab'a samun damar zuwa inda kike ba har abada!"" Hawaye ne ya cika min idanun. Na zauna jikina a mace, ""je ki motsa jikinki, yar lukuta."" Ba musu na wuce don tasan kuka zan yi, haka ya Ado ya ajiye aikin da yake ya koma nima musu jirgin Jos to lagos, bayan nan ya saka Aunty Zakiyah ta nima musu likita anan kuwa cikin ikon Allah wani abokin aikinta Dr Abraham Abati, shi ta samu ta gaya mishi ya ce mata ba damuwa Allah ka kawo su lafiya. Bayan sun gama waya sai ga kiran Aunty Hindatu ta ke ce mata.. ""Maman Abbana, zamu zo muma amma sai zuwa weekend ki gayawa Mijinki na kira yana busy."" ""Wayyo Allah Ubangiji ya kawo ku lafiya, don Allah a zo mana da doya."" "" Amma matar nan baki da kirki a jirgi zamu zo fa! "" "" Ku saka a mota ya rigaku zuwa."""

"""Ai kuwa kin kawo shawara me kyau bari na gayawa Raliyah a saka ta jos."""

"Ai kuwa kamar yadda ta fada a group aunty Munah ta ce musu. "" Ku tura mata dankalin turawa tunda"

"mun fi kusa zan saka a mota idan zan zo!"""

"Haka suka tsayar da magana, dakin da yake gefena na kara gyara musu, da inda Mama zata zauna a"

"kasa don tace Allah ya kashe ta ba zata kara yarda da yaudareta ta zauna a sama ba, A lokacin muka mai da hankali a gyaran gidan, washi gari Ya Ado da safe yake gaya min cewa. ""Na tura takardanki!"" ""Na gode!"" ""Naga kin fison aikin gwamnati ko?"" ""Eh mana ga fansho da garatuti, wannan fa idan haukarsu ta motsa zasu kore ka aiki!"" ""Daga nan sai mu ce miki korariya!"" Inji Aunty Zakiyah""Ai duk abinda kike min sai na gayawa Mama ita Waya ta damu da lamirina!"" "" Gaskiya kan yar lukuta autar mu, SAN baka lura da wani abu ba, su fa yan auta kiba ce da su."" Tura baki nayi nace mata. "" Maganarki ba zai yi aiki akan wannan kyakkyawar matashiyar ba!"" Na fada ina barin parlourn, ai sun san ba kibar sai dai idan suna son takura min sai su ce min yar lukuta. Shiga daki nayi na kalli kaina a madubi, wanda yake tsaye zalla. Ka juya ina kallon bayana, sannan na kalli gabana, ni dai kamar ba mace ba babu ya'yan gwaiba da za a gani ya ja hankalin kowa, wai tsaya me yasa nake tunanin jan hankalin wani ne? Na ga yan tsakanin nan sai batun wani ko aure, rintsa idanuna nayi sharrin makiya ko? Zasu sako ni a gaba, na kalli kaina a madubi na ce. "" Ke Lubnah ki nutsu, idan baki manta ba kin sha wuta a hannun Hafiz!!"" Daga haka na cigaba da shirmena a madubi, wayata ce tayi ™ara na Wauka. "" Ashe za a kawo Alhaji ba lafiya?"" "" Sorry Aunty Nuratu, mantawa nayi ban gaya miki ba, za a kawo shi gobe in sha Allah."" "" Allah ya kai mu, Allah ya bashi lafiya."" "" Amin Ya Allah!"" Ta lashe wayar kuma fa naje Gym din ni na ma manta da wani kawo Abba"

"sai da na dawo aka tashi zancen, kasancewar yau Laraba."

"Da dare muna parlourn Ya Ado ya ce min. "" Ke bani e-mail Winki don na lura yadda kika tsani aikin"

"nan ko an turo miki ba zaki fada ba!"" Lubabatushehuusmanjamare'a@gmail.com daga haka na cigaba da shan fruit dina. ""Shima password din sai na roke ki?"" Nifa aikin kamfanin nan sam bai min ba,"" ni wallahi aikin nan haushi yake bani! Lulu@19"" na fada ina hura hanci, "" don Allah dube ta yadda take hura hanci kamar wata sauro ke yanzu baki ji dad'i kin samu aiki a Lagos ba, kin zama big girl!"" Kalaman Abba ne ya"

dawo min........

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 38"

""" Idan karuwanci ne dubunki sun yi babu riba."" Hadiye yawun bakina nayi da yayi min kauri yanzu haka"

"Abba zai zo ba halin na je na ganshi ko na ji muryansa sai na ji lokaci guda tsoronsu ya kama ni daga shi har Ya Hafiz, wani irin masifaffen tsoronsu ya kama ni. ""Lubnah!"" Kallonsu nayi na mike a hankali zan wuce sama Ya Ado ya ce min. ""Kina tsoro ko?"" Tsayawa nayi ina mai da kwallar da ya cika min idanu ciki na ce mishi. ""A'a kawai im wondering yadda zamu zan ga Abba ne!"" ""Kada ki damu zaki ganshi."" Da sauri na koma sama, ranar dai saboda na saka tsoro da damuwa sai da nayi mafarkin, wai gashi nan Ya Hafiz zai tura shi a rami, amma na kasa zuwa cetonshi, karshe ina ji ina gani ya fada. Da wannan mummunar mafarkin na farka around 3am, ban daki na shiga nayi alwala na zo na gabatar da sallah Nafilla, ina zaune a wurin har aka kira sallah farko nayi raka'atu fijir, ina idarwa na cigaba da addu'a domin wannan lokacin yana da muhimmanci, karfe biyar da wani abu aka yi sallah asuba nima nayi, da na idar sai na ji na kasa fita motsa jiki, haka na kwanta saboda barcin da ya cika min idanu. Ban farka ba sai karfe daya na rana, ashe tun karfe goma su Mama suka iso, ganin kayanta nayi a kusa da ni ga kamshin turarenta na Touch me, da sauri na shiga ban daki nayi wanka na saka wata riga irin bubu din nan na sauko kasa, ba kowa a gidan, wayata na koma na dauko na shiga kitchen na hada abincin da zanci wanda ganye yafi yawa na zauna na fara ci a hankali, ina shan tea, a hankali ina kallon tv. Wayata na kunna, sannan na cigaba da kallon tv ina jin kamar wani abu yana damuna. Can na duba wayar na kira Mama. ""Mama shi ne ko ki tashe ni?!"" Murmushi tayi tana faWin, ""tow sannu ban tashe ki ba jinjiirata na ga kina barci ne kamar mage."" Murmushi nayi na ce mata. ""Kun iso lafiya ya Abba da jikin?"" Bana gabanta amma yadda ta amsa min kamar irin she does care ta ce min. ""Gashi can ana ta fama da shi."" ""Kamar ya?"" ""Tow ai yaki ya tsaya a duba shi dai fama ake yana tirjewa!"" Idanuna ne suka cika da kwalla. ""Allah sarki Abbana Ubangiji ya bashi lafiya."" ""Ke kashe wayar kada ki fara min kuka!"" Haka na kashe wayar ina jin wani iri a raina, karfe shida na yamma ta dawo gidan ita da Ya Ado don Aunty ta dawo da wuri tayi abinci ta kai, naso na"

bita ta ce min. Na zauna saboda Yara. Tana kaiwa bata jima ba sai gata nan.

"Tow dai gasu Mama ma sun dawo, Kallonsu nayi na tafi na rungume ta. ""Mama ya Abba da jikin?"" ""Da"

"sauki matsa min na je nayi isha,."" Ta fada tana wucewa haka na bi bayanta ina faWin. ""Mama zasu min dariya!"" ""Yo ba sai na musu rashin mutunci ba!"" Haka dai ta amsa min anan ta shiga ban daki tayi Alwala da wanka sannan ta fito ya sauya kaya na kawo mata abinci, tana idar da sallah ta fara cin abincin, ni kan gasashen kaza Ya Ado ya kawo mana, na fara ci ina kallonta. Tashi nayi tafi kitchen na hada Yorghurt fruit na dawo dakin ina sha. ""Yanzu haka rayuwarki zata koma ba abinci mai taimakawa sai irin wannan?"" ""Mama kibar da ba aso zan yi!"" Gyada kai tayi tana kallon yadda na ci kaWan na namar sauran"

"kuwa na barshi sai Yorghurt din na shanye, muka cigaba da hira.. ""Lubnah!"" Kallonta nayi don yadda ta"

"kira sunan yasa na fahimci maganar ba na wasa ba ne. ""Kin san yadda kome yake tafiya ko?"" Gyada kai"

"nayi ta cigaba da cewa. ""Yanzu na ji Adamu yana cewa zai nima miki aiki babu wani ne da yake nimanki?"" Wani irin tsoro ne ya lullube ni har nake ji kamar an lullube ni da danyen nama. "" Ko har yanzu tsoron yana nan!"" Bakina yana rawa na rufe shi, domin sai naji kamar xan yi amai ne, a hankali jikina ya Wauki wani irin rawa. Ai kuwa da sauri na shiga ban daki sai da nayi aman abincin da na ci, na dawo na kishingida bata kara min magana ba, ta yi shiru da zancen ranar a wurinta na kwana. Washi gari Yaran gidan da gulma wai. "" Aunty Lulu yau ta kwana a wuri Mamanta."" Sosa kai nayi na ce musu. ""Oh dai Mamana ce!"" Haka na raka su har inda school Winsu yake, daga can kuma zasu wuce islamiyya don an"

"sauya musu na yamma nan, idan suka dawo zamu yi karatun dare da su, har da home work."

"Bayan na karya su Mama suna ta shirin tafiya Asibiti, Mama take gaya min ai tun asuban fari Ya Ado"

"ya kaiwa Tahir abinci, ya dawo ya tafi aiki. Ina can ina baza kafasiti a wurin Uwata. Karfe goma Aunty Nuratu ta zo muka tafi asibitin da ita, daga waje na tsaya ina kallonshi da yake ta barci.. hawaye ne ya zubo min haka na koma na zauna ina kallon ina share hawayen da yake zubo min, fitowa suka yi a lokacin Ya Tahir ya iso yana min tsiya. ""Who is this fine lady? Daga wata kasar take anya ba daga Somalia ba ce!"" ""Ya Tahir zaka fara ko?"" ""No na ga wata hadaddiyar baby doll ce, mai kalar Somalias."" Murmushi nayi ya kai maganin sannan ya fito nan aka yi ta gaisawa da raha. ""Kafaya kin ga yarinyar nan ko a hanya na hadu da ita dai dai na juya nace kamar na santa!"" ""Allah ya ganar da kai Attahiru."" ""Mama da dai kin ce Dahiru zai fi gane yana tsokanata!"" ""Mama don Allah kada ki biye mata!""? Haka muka yi ta hira, wurin karfe biyu sai gashi ya je ya sayo abinci, ni nawa kusan rabi ganye sai fried rice da grilled fish, sai soda drink. Ya ajiye min yana faWin. ""Nasan ba zaki hada kifi da madara ba, shi yasa na amso miki soda!"" Da yake an kebe dakin mutum daya ne, kuma maganar gaskiya a can amenity muke akwai parlourn da family zasu zauna, kuma abin dad'i babu al'umma sosai a wurin haka yasa na sake naci abincin, wanda a lokacin ya lura da yadda nake cin ganye ya ce min. ""Ganye yafi kara lafiya kenan?"" ""Eh shi shinkafar akwai starch a cikinsa, shi kuma yana bin jini ne!"" Matsa lemon tsami nayi akan abincin da kuma kan kifin, ""shi kuma na meye?"" ""Yana narka da kitse da maiko!"" ""Sodar fa?"" ""Ita tana hana ciki cika ya kumbura, ruwan da na fara sha shi zai hana ni cin abincin kamar yadda baa so!"" Jinjina kai yake sai a lokacin Mama ta ce min. "" Tow idan kika auri talaka fa?"" Murmushi nayi nace mata, ""Alayawu, kafi Egu, tafasa, bawon kabeji. Lemo da gwaiba ba arasa su a gidan talaka, rama da yakuwa duk suna da amfani"

"zanci ai babu inda Allah baya kai mutum."""

"""Yanzu bakya cin kome fa!"" "" Eh duk wani abu me starch bana sonshi, saboda akwai wata ™waya da"

"nayi tasha bude tsoka take sai mutum ya bude kamar an hura shi, har da shi a karin kibar jikina."" "" Allah ya kyauta!"" "" Amin Ya Allah! "" Daga haka muka cigaba da hira kar yamma sallah yake tashinmu, wurin karfe biyar sai ga Ya Ado da fruit da abincin dare, nan aka sake bude hira anan na ji sun ce ashe Rufa'i da su Aunty Hindatu da Aunty Innah zasu zo. Shi Ya Tahir zai koma, sai Ya Sani yazo. Idan Allah yana sonka da arziki sai ba ka ikon yiwa Yaranka hidima a kananun shekarunsu da zarar sun girma su biya wannan abin da ka yi musu. Wannan abinda ake kashewa babu kwandalar kowa Ya Ado ne yake a cikin aljuhunsa abu daya yace ba zai dauki nauyin kawo kowa ba. Su kuma da yake sun saka ransu zasu so suka ce ya huta, muna isowa gida na ga sakon River State ya iso doya ce manya manya. Kamar yadda nake zaton"

"akwai wani abu da yake faruwa yadda na ga Ya ado da Ya Tahir tattaunawa, ban sani ba amma ko Mama"

basu bari ta sani ba. Da muka dawo ina kwance a dogon kujerar parlourn ina kallon wani yoroba film da

"yake zuwana nima na zama jikar oduduwa, ina son film dinsu musamman irin na kauye na zamanin baya, yana nuna yadda suke kare martabarsu da kimar kabilarsu."

"""Lulu!"" Tashi nayi ina amsawa, ""kin san wannan kwayar?"" Kallonsa nayi kafin nace mishi. ""A ina ka"

"samu?"" Gabana yana faduwa, ""Kin san shi kenan?"" ""Eh!"" Na fada idanuna yana kawo ruwa, ba dai shima Abba ya fada irin matsalar da nake ciki ba ne. ""A ina kika san shi?"" ""A wurin Ya Hafiz!"" Daga haka ya maida aljuhunsa, ni kuwa na fashe da kuka, bai gaya min kome ba. Amma na ji a raina akwai wani abu. ""Ya Ado mai ke faruwa? Ka gaya min don Allah!"" ""Ba kome kawai bincike muke!"" Duk yadda naso yayi magana yaki, ""ki yi shiru kada Mama ta san me yake faruwa zan tafi Bauchi ranar Monday, idan na dawo"

"dan miki bayani!"" Haka ya Ado ya bar ni a dame."

"Kamar yadda ya ce kuwa haka ce ta faru, ranar Monday ya wuce Bauchi. Sai dai zuwan shi Bauchi bai"

"haifar da Wa mai ido ba, domin anyi wani irin tashin hankali ne akan maganin Baban Jama'are ya ce shi ya kaiwa Abba yayinda yan uwanmu bakiWaya aka zargi Ya Hafiz amma kiri-kiri mutumin nan ya wanke danshi, sannan suka ce ko da basu da arzikin Jirgin sama zasu zo su ga dan uwansa. Karshe haka Goggo Alti ta kashe case Win, amma don goyan bayan sun goyi bayan Hafiz har da cewa ai kafin suyi yunkurin kai Abba lagos waye yake kula da shi, Baba Malam tsohon munafuki har da cewa a gaya min na dawo dakina na daina yawon gantali da karuwanci. ""In sha Allah Ubangiji ya ™are Lubnah wannan fatar sai dai ka ganshi a cikin wasu jikokin da kafi so!"" Inji Yadiko, kai anyi gurmi Goggo Alti ce kawai bata yi magana ba, tace ita bata ga laifin Yaran Baban Bauchi ba, da gaskiyarsu, haka suka bar zancen washi gari shi da su Aunty Hindatu da Aunty Innah suka bar Bauchi har da Rufa'i aka tawo jos daga Jos suka hadu da Aunty Raliyah suka biyo jirgi, sai tsiya suke ta yiwa Rufa'i wai Allah ya kira shi lagos, amma yana da"

rabon zuwa lagos. Da yake shima akwai baki tuni ya kare kanshi.

***

Hafiz

Ya razana yadda aka fahimci shi yake bawa Baban Bauchi magani tow meye dalilinsa? Amma haka suka

"bar zancen shi babban damuwarsa ya ga Lubnah in sha Allah duk ranar da ya ganta ko tana so ko bata so sai ya kwanta da ita, domin a yanzu da yake nan babu wata mace da take tare da shi, ko ya dauko maganar aure za a lalata mishi, ga Baban Jama'are da ya dawo Bauchi shima ya dawo shagon Wan uwansa, hmm wani abu da Yaran Baban Bauchi basu sani ba shine ana ta murkushe kudin shago domin kuwa na karamin barna Hafiz yake yi ba. Wanda haka da Baban Bauchi ya d'ago ne yayi sanadin da Hafiz"

ya fara dirka mishi magani.

(Wash hannuna )

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 39"

Ganin yadda lokaci guda asirinsa ya nime tonuwa ne Baban Jama'are ya saka shi a gaba da tambayar me

"ya faru, sanin cewa Babanshi yana tare da shi amma sai ya kasa faWa mishi gaskiya ya ce musu. ""Kawai don sun tsane ni ne, amma me nayi musu da zasu ji haushi bayan ni nake kula musu da mahaifinsu da suka yi watsa da shi, meye ban shi ba. Me kuma bana mishi kawai ban san me na musu suka tsane ni ba ne."" Wannan magana sai yayi tasiri a ran Uban Hafiz ya cigaba da cewa. ""Idan sun tsane ni saboda Lubnah har yau Lubnah matata ce tunda ba ni na sake ta, kuma ban amince da sakin ga har yanzu ina son Matata."" Yadda yake maganar a dame yasa Uban shima ya shiga damuwa, ya tafi dakin da Baba Malam yake ya gaya mishi, nan dai suka kara kulla wata munafuncin zasu zo lagos su ga halin da Abban"

yake ciki su gaya mishi abinda Yaransa suke zargin Hafiz da shi.

"Wannan kuwa ya yiwa Hafiz dad'i, wanda ya kai har cikin ransa yaso ya biyo su. Amma suka hana shi,"

"da yake sun san al'amarin na kudi ne, basu fara zuwa da batun kudin jirgi ba, can bypass suka nufa anan suka biya kudin mota dubu sha bakwai daga Bauchi to lagos, sannan suka dawo idan bar aka samu fasinjoji zasu tafi, a Hajiya da ta ji labarin abinda ya faru bata yi kasa a gwiwa ta kira Malaminta ta gaya masa. Abin da ya gaya ya, ba karamin dadi ya mata ba, ta kuma ta ji a ranta idan har Lubnah zata dawo rayuwar d'anta bata ki tayi kome a kai ba, wannan abin ya saka ta kara tura kuWi. Sai dai shima ai ya boye"

mata gaskiya ya barta da duhun zuciya.

Bayan haka ita kanta tasan yaudarar kanta take amma da yake ta sauka akan hanyar da ya dace kyaleta

kawai ta dace ayi ta ji a jikinta.

****

"Lokacin da su Aunty Hindatu suka iso sai da suka fara biyawa asibiti kayansu aka kawo, ina kan injin"

"motsa jiki nayi zufa shakaf kunnena ina sauraren karatun Alqur'ani, suka turo kofar. Zuba min idanun suka yi kasancewar na basu baya. A hankali Aunty Innah ta lallabo sai da ta zo kusa da ni na ji an tab'a ni, da sauri na juya ina ganinta ba fasa ihu, tare da rungume ta. Da sauri na koma wurin Aunty Munah da Aunty Raliyah, sai Aunty Hindatu da ita kan har da daukata. ""Auta kece haka kika koma fine lady haka ashe da gaske Tahir yake da yace mana, wallahi kuka ga auta

Please Login or Register in order to submit comment