Reading ALAƘAR ZUCI by Mai Dambu Chapter 33 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kowa shi yaushe zai zama dan iska irin Mijinta, idan da shi ne Mijinta, zai ga yadda zata kula kowa domin a banza zai ta sare kan mutane ne, tsaki yayi ya cigaba da tafiya. Har inda aka yi zaman muka isa sannan muka fita inda aka ajiye kayan, na shiga ina rubuta abubuwan da Taj yake gaya min, har muka gama na juya kenan kawai muka ci karo da shi, kamar xan fadi ya riko hannuna, ya tsayar da ni. Ya harare ni cikin masifa ya ce min. ""Idan Mijinki baya kishinki, ke ba zaki iya kishin kanki ba ne? Kin zauna sai wangale hakora kike da wani? Ki sani ba zaki janyo min masifa a kamfanina ba, idan aurenki aurenki idan kuma kule-kule ne sai ki bar min aikin na gaya miki, kuma xan gayawa SAN yasan abinda kike aikatawa."" Irin kallon da nake mishi na tausayi ne, domin bakiWaya masifarshi ta rufe mishi idanun kawai fada yake kamar zai dake ni, wani abu da yake bani mamaki shi fa idan yana masifar ma baka tab'a jin tashin muryan sai dai ayi ta maganar cikin wuya da baki, irin kada a ji yana fada, tattara kayan nayi na rab'a gefenshi na wuce, kafin na isa wurin motar"

"na shiga Taj na min magana na ki kula shi, shima da yazo ya zauna a motar muka bar bankin muna hanya"

"amma naki kula Taj, ganin haka yasa shi cewa Taj. ""Ka kai mu Chinese dish."" ""Ok sir!"" Bayan mun dauki"

"hanya naji muryan Airah. ""Turaki ni ban ga wani aikin da sakatariyarka take ba, maganar tafiya kuwa sai na yi replace dinta."" Duk muna jinta, ni sai na fi kowa murna cikin farin ciki na ce mata.. ""Alhamdulillahi Ubangiji ya kai ku lafiya ya dawo daku lafiya, kai Masha Allah."" Ganin yadda na nuna farin cikina tare da musu addu'a, ya cika da mamaki yana ta taSa table tap amma zuciyarshi kamar ta dirko daga kirjinsa, har sai da ya kai hannu ya danne kirjin, ko da muka iso shagon ita da Taj ya tura shagon. Tunda na ji ya ce ita da ita da Taj su je su fita su amso na fahimci zai hau masifa ne, dauko airpies na saka s kunnena na kunna wayata. ""Cire!"" Ya fada a fusace, na cire daga kunnen na juya ina kallon titi raina yana b'aci, ""tafiya da ke xan yi idan kin so ki ajiye aiki yau!"" Daga haka ya cigaba da aikinsa. Haka suka dawo muka bar shagon, koda muka iso office mika min abincin Taj yayi na ce mishi. ""Ina azumi!"" ""Yau wacce rana kenan?"" Banza nayi mishi ban kara kula shi ba. Har aka tashi na wuce gida, ina isowa gida abin mamaki na same shi har ya rigani zuwa gidan, na samu suna magana da Ya Ado. Wuce su nayi na tafi cikin gidan. Ban san tafiyarshi ba, sai ganin Ya Ado nayi ya zauna yana kallona. ""Kuna da tafiya ne a kamfaninku?"" ""Eh amma ni nace ba zan samu zuwa ba, saboda."" ""Zaki je, abu daya nake so dake ki kama kanki, sannan ki rike mutuncinki. Kada ki manta Allah yana ganinki, kada ganin bamu nan yasa ki fada wani irin yanayi, ki sani Allah yana kallonki."" Idanuna ne suka cika da kwalla, haka yayi ta min nasiha duk da ni na nuna bana son zuwa amma ya ado ya ce na je, haka na cigaba da jin wannan abin haushin, ranar juma'a ba wani zama muka yi ba, aka tashi yau kan shi da kasan yazo kamfanin don haka da aka tashi, na fito zan je Garej ya tsaya tare da cewa. ""Shigo!"" Kamar ba zan shiga ba, sai kuma na shiga na ja belt na daura, muka cigaba da tafiya. Wannan dan renin hankalin ba abinda ya ce min, har muka isa gida na cire belt din xan fita ya ce min. ""Are you angry?"" Share nayi na bar shi a wajen ai tun da naje ya ga yadda fuskata take masifar haWe, haka yasa shi fahimtar raina a b'ace yake, wai kuma don renin hankali yana tambayata wai ina jin"

haushi ne?

"Ranar asabar, ina tsaka da barci domin duk jikina a gajiye nake tun daren jiya Aunty Zakiyah ta ce"

"zata shiga asibiti. Wurin karfe goma, mai aikin ta ce nazo ina da baki, saukowa nayi shine da su Ilham. Cike da mamaki yaran suka taso da gudu na sauko nima na rungume su. ""Aunty Lulu!"" ""Na'am yau kunne!"" Zama nayi nace mishi. ""Ina kwana?"" Hankalinsa yana kan wayarshi sai latsawa yake, kamar bai ji ni ba, sai da na sake gaishe shi ya amsa, kitchen na nufa na shiga aikin gaggawa domin Yaran gidanmu sun tafi Islamiyya. Babu wani abin karyawa don dumamen tuwo suka ci, doya na fere na turara musu, tare da miyar sauce din kwai, sai kunun tsamiya da na dama musu na shiga fito da shi, na hada bakiWaya a gabansu, yaran na zuba musu. Sannan na koma na matse fruit nayi musu juice da shi na fito na zuba musu. Abin ya bani mamaki yadda yake cikin abincin kamar bashi ba. Komawa sama nayi, wanka da brush nayi na shirya cikin riga da zani na atamfa, na karya dan daurin dan kwali, Ban san me ya ke fisgana ba, amma na samu kaina da shafe jikina da humra mai kamshi, sannan ka fito na samu ya gama yana fama da wayarshi ne, lokacin da na iso parlourn kura min idanu yayi, sai da na kama shi yana kallona ya wayance kamar bai yi kome ba, na wuce kitchen na zauna a can na karya sannan na fito yaran suka gama cin nasu na tattara na kai kitchen. Sai Santi suke. ""Aunty Lulu zaki raka mu, muje birthday party na yar class dinmu, kuma ance anan son two parent su zo ne, kin san Mom ba zata amince ba,"

"shine muka zo da Uncle ko zaki bi mu. Please!"" Yadda suka yi maganar kamar nayi kuka, domin na"

"fahimci ba wai zuwan kansu ba ne ba mamaki shi ya shirya musu haka. ""Bari ka kira Mijina na gaya"

"mishi!"" Na tsinci kaina da fadar haka, bai d'ago ya kalle ni ba har na haura sama na gama abinda zan yi ja fito sanye da wata laffaya akan kayan jikina. Na fito a hankali nake takawa, yadda na iso yaran suka yi ta"

"murna, haka muka fita satar kallona yake sau biyu ina kama shi, amma sai wani haWe rai yake.."

"A wurin Birthday din hidima sosai aka yi, mu kanmu iyayen yaran sai da suka saka mana wani gasa."

"Kusan a tare muka ci gasar, karon farko da naji wata irin soyayyar Yara ya kama ni, domin saboda Yaran nan sai da nayi kawaye Iyayen Yara, dayawa a wurin dauka suka yi ni Matarshi, ce kasancewar an san shi sai ya zamana idanun mutane akanmu, a kyautar da ya bada har da dollar guda ashirin, sai gift da yaran suka bada. A waje haka mutumin nan yana da mutunci, rashin mutuncinsa a office suke. Haka muka gama bikin muka dawo suka ajiye ni a gida, fitowa yayi daga motar yana dan matsa hannunsa, ni duk a tunani na crwa zai yi na gode. ""Idan kika shiga ki yi wanka domin turarenki."" Kambu, banza nayi da shi na wuce humran nawa ne zan yi wanka akan shi wanda idan ba kazo kusa da Ni Rufe bakina nayi wata"

"irin kunya ta kama ni, kenan turaren ya. Da gudu na shige parlourn tare da haurawa sama, yayi gaskiya Innalillahi wainnalihir rajoun, wanka nayi tare da tsarkake jikina. Duk kunya ya kama ni, haka nayi ta juyi har lokacin cin abinci yayi, ina cin abincin kawai sai naji gabana yana faduwa, sakamakon tuno maganarshi, gaskiya tafiya Japan ba zai yiwu ba, don ma azumi ya kusa. Haka nayi ta cakalar abincin har Ya ado yace min.."" idan ba zaki ci ba ai ba a miki dole ba! "" Mikewa nayi na dawo parlourn da Yorghurt ina sha a hankali, ni fa yanzu na lura wannan aikin ya kara ramar da ni, domin yan dukiyar fulanina basu"

zama a cikin yar bra da nake sakawa.

"Haka nayi ta juya maganar, nan har barci ya dauke ni,"

"Washi gari lahadi, sakon da na gani ya turo min ya ce min. *Daren yau zamu tafi please kada ki hada"

"kayanki d wannan perfume din yana da karfi bana sonshi* kambu mutumin nan ya rena min hankali, buga kofar da Ya ado yayi na ce mishi. ""Na'am!"" ""Dazu oganki yake gaya min tafiyarku karfe shida na yamma!"" ""Tow!"" Haka na shiga hada kayana bakiWaya dogayen ruguna ne, humran nan barinsa nayi na dauki body spray sai roll on na hammata, saukowa kasa nayi na samu Aunty Zakiyah na ce mata. ""Wai Aunty Zakiyah humran nan meye amfaninsa ne?"" Dariya tayi tana faWin. ""Kin saka ne?"" ""Eh kai yana da dad'i."" ""Sannu ko, tow na masu miji ne ranar ina ta son hanaki Wauka, amma saboda Maman Amal ta cinye ki da baki kika Wauka."" Kasa kasa ta ce min. ""Na masu maza ne. Idan kika saka namiji haukacewa zai yi akanki "" Da gudu na haura sama ban yarda na ji karshen bayaninta ba, na je na dauka na boye idan"

aka samu Mama ko Aunty Hindatu suka zo zan basu su su raba fa Aunty Innah. Allah sarki shi yasa duk

ya shiga damuwa.

"Har dare ina kwance kawai nazarin yadda zan ganshi ne, karfe biyar da rabi Ya ado ya saka muka fito,"

na saka kayana a cikin motar dukkan yan gidan suka rako ni.

"Yana cikin mota shi da Ubaid da Uncle Auta, kallonshi Uncle Auta yayi ya ce mishi. ""Bilal zaka tafi da Yar"

"mutane kuma kace matar aure ce, please and please ka taya ta kare kimar aurenta, don Allah kada ka sake wani abu ya tab'a kimar aurenta Please."""

"""Wai wace ce ita da ya damu kansa da ita ne?............"

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 56"

"Shiru Uncle Auta yayi, suka fito domin raka Turaki har cikin airport Win, ganin yadda take rungume"

"Yayanta yasa shi jin wani irin abu. Šauke kai yayi har suka gama alamar rarrashinta yake ita kuwa sai wani kukan shagwaba take, haushi ya kama shi kamar ya ce ya fasa kowa ya kama gabansa. Anan dai suka daure har suka gaisa da Uncle Auta da Ya Ado, Ubaid ma sama sama suka gaisa da juna. Wurin"

bakwai da wani abu jirginsu ya tashi.

"Kallon Uncle Auta Ubaid yayi yana faWin. ""Kana ta ja min tai wacece ita?"" ""Lubnarsa yarinyar da ya so ya"

"Bauchi. A yanzu Allah ya haWa su a wuri guda amma ita kamar bata san shi ne wanda ya sota a Bauchi ba."" ""A'a renin hankali dai ni dama tun ganinta na ji bana sonta, haushi take bani kawai bata dace da shi ba shine yake haukarshi akanta, gaskiya ba zan tab'a barin ta kara saka mu, rasa shi ba domin babu"

"alkhairi a tarayyarsu."""

"""Ba ruwanka da ita idan har kaso son alakarku tayi tsawo kada ka shiga tsakaninsa da ita ka ga yadda"

"yake jin kishin nan tas zai iya yanke hukunci rabuwa da kai, a yanzu haka bai san bata da aure ba. baffa ya nuna mishi tana da aure kada ya ce zai yi wani abu na daban. Don Allah kada ka yi wani abu da zai lalata alakarku!"" Jin shi Ubaid yake amma yasan tabbas tazo sake yaudarar dan uwansa ne kafin tayi"

"haka tabbas ya shiga tsakaninsu har abada."""

"Zance wannan ce karo na farko da nayo tafiya da wani ba muharramina ba, duk sai na takura. Wani"

"abinda na fahimta inda muka zauna VIP ne. Tunda muka shiga wurina daban wurinsa daban, amma sau biyu ina kama shi dumu dumu yana kallona, na dauke kai ban kara kallon inda yake ba, har muka isa dubai da rana. Mun bar can dare ya shiga mun shiga dubai da rana, anan muka yi sallah asuba da na duhur, kafin muka dawo airport Win ya zo min da abinci, na amsa ina kallon kasa. Har muka shiga jirgi"

ban ci abincin ba.

"Haka yasa bakiWaya yayi ta duba ni ko naci abincin, ni kuwa naki cin abincin. Haka muka isa kasar"

"Japan da dare anan mukumukun sanyi, abin bai kara bani mamaki ba sai da na ga garin na kara godewa Allah da ya hankad'o ni nazo na ga sabon duniya, mun sauka a Tokyo anan aka yi taron na tsawon kwanaki uku, daga ni har shi bamu haduwa da juna sai zamu tafi taron, idan muka dawo kowa ya shige dakinsa, zai matu™ar wahala ka ga mutum ya leko, a cikin sati daya zuwa kwana goma sau biyu muka zauna a wuri guda. Sai ana jibi zamu dawo ya buga min kofa, ba bude kallona yayi daga sama zuwa kasa ya ce min. ""Ins jiranki!"" Komawa cikin nayi na gyara jikina, sannan na fito sanye da doguwar riga sai katon coat na sanyi da na daura, sannan muka fita yawo. A ranar yawo kan munyi shi, sannan ya ja ni zuwa wurin part na abokansa, a lokacin da suka hadu aka yi ta hira, amma hankalinsa rabi yana kaina, ban san me aka mika min a kwalba ba, dawowa kusa da ni yayi a hankali ya sa hannu a ture ruwan, kallonshi nayi domin ruwan har wani hayaki yake, kallonshi abokan suka yi ya kalli wata daga cikin abokansa mata ya ce mata. ""Tinah kaita ta wanke jikinta."" Muna tashi suka fara mishi magana. ""Me yasa zaka zubar da liquor din da muka ba ta?"" Murmushi yayi ya mike tare da Waukar jakarta. ""Ita muslmace kamar ni, kamar yadda Allah ya haramta haka nima hakkina ne na kare mutuncinta, sannan kuma ai baku gaya min zaku bata wani abu ta sha ba, da ta sha kuwa sai ka hadiye kwalbar!"" Iya nan naji ya mika min jakar muka bar wurin. A hankali muke tafiya daga ni har shi jikinmu a mace yake, na rasa me zance me shi, shima kuma bai min magana ba har muka isa masaukinmu. Sai da na bude kofar na shiga ya wuce abinsa. Washi gari da sassafe ya tashe ni muka je sayayya. Muna gamawa aka wuce da shi airport kafin gobe sun gama kome, da la'asar na dan fito daga hotel din ina tsaye a waje na hango Airah da shi suna magana, yaushe ta zo? Abin ya bani mamaki ganin na hango su yasa ta karaso. Cikin yanga da jan hankali ta ce min. ""Duk iya kwanakin da kika yi da shi bai isa ba sai kin biyo shi?"" Ban fahimci me take nufi ba, don haka kallo daya na mata na dauke kai. Na cigaba da kallon garin sai da ta hauro inda nake zata tab'a ni na rike hannunta. ""Kul kada na ji kada na gani, ni ba sa'ar yinli ba ne don haka ba zaki saka hannunki a jikina ba."" Na ture hannunta, ""karuwa me bin namijin da bai damu da ita ba."" Wannan maganar ya min ciwo, murmushi nayi nace mata. ""Ke ya kamata na kira haka tunda zuwan da kika ce kina so ya nuna baya yin zuwanki sai ni. Yana da kyau na kira ki da Uwar karuwai ni wancan abin ko a kafa aka daura kin shi bana yinsa."" Na wuce abina, ita ta damu da namiji har take faWa akanshi, amma ni da na sha wuta a hannun da namiji har wani abin burgewa ce da su da zan damu kaina. Mtseew, na ja tsaki. Ashe ina barin wurin kai ™arata tayi wurinsa, ban san ya suka kare ba. Da asuba muka hadu da ita a nan airport. Ni ban shiga harkanta ba, kuma ban wani damu da ita ba. Ban san me ya gaya mata ba"

"amma tabbas naga ta shiga hankalinta, amma tana harara ta idan muka hada ido ba mistake."

"Mun iso Nigeria kai tsaye, da misalin karfe sha biyu saura na dare, kallona yayi ya ce min. ""Ko zaki"

"kwana a gidan Uncle Auta idan gari."" Ban barshi ya kai aya ba nace mishi. ""A'a bamu yi haka da kai ba, kawai kai ni gida!"" Na fada ina kallon gefe tsaki tayi haka muka kira Uncle Auta ya zo, ya dauke ni, ni da ita muna baya. Shi da Uncle Auta suna gaba, har kofar gidan Ya ado aka ajiye ni sai da ya buga gidan Ya gaisa da Ya Ado, sannan ya ce mishi. ""Ga amanar da ka bani!"" Murmushi yayi ya ce mishi. ""Na gode sosai da wannan abin da ka yi na yarda kai me amana ne!"" Ya ji dadi, ni kan dakin kasa na wuce ka kwanta, tunda nayi sallah asuba na koma na kwanta sai sha biyu na tashi da mugun mura na kwaso sanyin can, ai"

"muryata ta dishe, mura sosai da zazzaSi na kwanta."

"Ban sani ba ko Ya Ado ne ya gaya mishi, bayan isha sai gashi da kayan dubayya, ya zo duba ni. Kaya"

"niki-niki sai da abin ya dasawa Aunty Zakiyah ayar tambaya. Ganin haka yasa bayan tafiyar naki magana duk yadda taso nayi magana naki, sai ta zuba min idanu."

***

Bauchi

"Jikin Abba da sauki sai dai ya daina zuwa kasuwa, koda yake kasuwar ma yanzu suna ce domin shagonsa"

"ya mutu murus na atamfofi, sauran da yake ba a hannun Hafiz suke ba yasa kome yake tafiya normal, wani abu da Abba yayi shine raba hannunsa da yayi, shine kawai Allah bai bada ikon karya shi ba, amma shagon sai da aka rufe domin babu kome a cikin shagon kamar wacce aka yi mata yasa."

Ya nima da lafiyarsa da karfinsa amma yau an wayi gari kome ya kare shi. A haka shima Baba Malam

"ya kwanta rashin lafiya, sosai fa ya kwanta jinya. Duk da wannan yanayin da yake ciki sai da ya kai ya kawo yana fama da jinya amma yana sakawa a kira Abba ya tuna mishi lallai ko bayan ransa ne a tabbatar na koma gidan Hafiz, shi Abba ba lafiyar ce da shi ba, amma a haka ya tafi jama'are ya samu tashin hankalin da ya wuce tunanina domin Hafiz ya zo ya gaya musu karya da gaskiya, lokacin da suka dawo daga lagos, bai magana ba kuma Ya ado bai fadawa iyaye mazan abinda ya faru ba, Yadiko ce ta sani, ai kuwa rako su Baba Malam gida domin inda Baban Jama'are zai makale an rufe gidan da yake shirin rikewa Ya Umar ya ce an saka a kasuwa saboda zasu saka kaya a shago, wannan ya kara bawa Hafiz daman zuduma sharri son ransa. Wannan abin yayi bala'in d'agawa Abba hankali wanda ya haifar da saukar jininsa har ya nemi faduwa, don ma Allah ya so da Sani suka tafi.. haka suka yi ta kula da shi, wato cewa Hafiz yayi shi duk abinda zasu mishi zai karba amma su sani ba zai tab'a gudun Lubnah da take karuwanci a Lagos ba, haka yasa har Rufa'i sai da ya bada shaidar Lubnah karuwanci take har da hotonta suka nuna wanda take motsa jiki a cikin gidan. Wannan abin yayiwa kowa zafi Mama da bata da hakuri har Jama'are ta isa aka yi uwa ubanka, wannan abin ya tsaya mata a rai, tayi kuka har ta godewa Allah, Hafiz ya ki rabuwa da Lubnah duk inda ya zauna sai ya zage ya ce shi zai rufa mata asiri, koda ciwo zata kwaso zai zauna da ita a haka, wannan abin ya saka aka manta da itin cutar da yayiwa Lubnah aka"

"fara ganin ™o™arinsa da yadda ya ganta kuma zai zauna da ita, sharri kuwa ai dan aike ne."

"Haka Abba ya dawo Bauchi da ciwo hade da bakin ciki, Yadiko ta ce mishi. ""Alhaji ai baka ci ta kuka ba,"

"Maman Lubnah ce da kuka domin ita aka cuta kuma Allah sai ya saka mata, wannan zalinci har ina kuma kaima Hafiz bai barka ba."""

"Wannan abin ya taru ya mishi yawa, ga bakin ciki ga takaicin Hafiz."

***

Lagos

"Kwana uku a tsakanin wanda yayi daidai da Monday na koma aiki, yadda naga ana kallona yasa na dan"

"tsargu. Ashe gulma aka yi me zafi. Wanda Sarah ce ta iya bani labarin wai ai Airah ta ce mata a daki daya muka sauka sannan mun ta yawon dare da sheke ayarmu. Kallonta nayi tare da dariya na ce mata. ""Duk abinda aka fada a kaina da wanda na sani da wanda ban sani ba na yafe, idan kin gadama ki yarda idan"

"baki gadama ba ki watsar. Ni ban zo kamfanin nan don shirme ba, su da suka ga zasu iya Bismillah."""

"Haka lamarin ya cigaba da tafiya, ba dad'i ga gidan Jaridu da suka sako shi a gaba da kafe hotonshi a"

"magazine ana cewa yana sheke ayarsa da sakatariyarsa, kanwar wani babban lauya a nan lagos, har kamfanin ake zuwa leken asiri wannan yasa na ajiye aikin na tafi hutu don ma Allah yasa saura sati biyu a fara azumi. Kanshi ya dauki wuta haka yayi ta min masifa akan me zan dauki hutu bayan ba ni daya ba ce a cikin wannan tashin hankalin har dashi, kashe wayar nayi na tattara na bar lagos da goyan bayan Ya Ado na tafi rives wurin Aunty Munah hutu, a can na yi sati biyu, Ya ado da fari ya zata ko ina sonshi ne nake wannan abin ni kuwa ba wannan tunanin kawai na gaji da matsalar kamfaninsa ne, wata na biyu kenan a kamfanin amma kamar don ni aka bude kamfanin satin biyu cib Ya Ado yazo da kanshi wai na koma gida Mama tazo. Haka muka iso gidan cike da farin ciki, na ga Mama na ji dadi sosai. Kusan kwana muka yi a tare muna hira, washi muna karyawa ya jifo min tambayar da tasa na kusan kwarewa. ""Ance kina aiki da wani namiji wanda ake ganinku tare waye shi?"" ""Mama oga na ne na wurin aiki."" ""Sonki yake yi ne?"" ""Amma aiki ya haWa mu fa, babu wani maganar so ni yanzu babu aure a gabana."" Shiru tayi kafin"

"ta ce min. ""Babu aure a gabanki taya aka yi har wannan hotunan suka Bayyana a idanun duniya."""

"Ta watsa min hoton, wani irin razana nayi tare da rufe bakina. Zan yi magana ta dakatar da ni. ""Bana son"

"jin kome a bakinki. Ki ajiye aikin ki hada kayanki mu koma Bauchi.."""

**

"""Na gaya maka bata bukatarka, wannan gayen da ka daka a kanta wanan ranar shine Mijinta, har yau"

"yana nan bai rabu da ita ba, idan akwai abinda kake yi da ita tow ka daina ita din matar aure ce."" Inji Ubaid."

"Cike da mamaki yake kallon Ubaid cikin sanyin murya ya ce mishi. "" Zargina kake? "" Gaskiya na gaya"

"maka, ka rabu da ita."""

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 57"

"Murmushi Turaki yayi mishi tare da mikewa, ya nufe shi ture shi yayi har suka fito waje. ""Idan na kara"

"ganinka, a rayuwata ko a rayuwar lubnah, sai na kashe ka!"" Ya tura shi waje. ""Akan mace zaka rabu da ni? Akan mace zaka lalata alakarmu?"" ""Dama can Alakar ta lalace, ai dama can alakar babu ita, dama can"

"babu wata kauna ko soyayya da yake tsakaninmu, stop pretending like kana tare da ni bayan na san kai"

"da sauran yan gidan so kuke su kashe ni da goyan bayanka, idan ma Lubnah tana da aure zan cigaba da tafiya ba zan tsaya ba, idan bata da aure zan tsaya na ga me take bukata a rayuwata. Ba kai ba Mujitafa idan ya ce zai nunawa Lubnah yatsa sai na karya shi balle kai karan kade miya, fita kada na kara ganin munafikar fuskarka."" Cike da mamaki Ubaid yake kallon Turaki da ya kore shi. ""Korana kayi fa? Korana kayi Turaki?"" Murmushin takaici ya sake mishi tare da cewa, ""abinda yafi haka ma zan maka fita!"" Ya daka mishi tsawa. Girgiza kai yayi ya fita, duk fuskar da aka bibiya shine bai kyautata Alakarshi da turaki ba, ya san yayi kuskure amma duk lokacin da yayi da wani katobarar kara nisanta kanshi da Turaki yake"

ya rasa me yasa yake jin haushin Yarinyar.

***

"Tsare Mama nayi da idanu, na rasa abinda zan fada. Amma sai na

Please Login or Register in order to submit comment