Reading ALAƘAR ZUCI by Mai Dambu Chapter 27 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta dauka bakiWaya mutane dari da yan kai, daga nan ya tura musu yadda zasu raba mutane ranar interviews din. Sannan da kuma yadda zasu duba su. Sannan ya ce musu a tura musu sakon yau yadda zasu shirya akan lokaci. Haka ya tura musu yadda ya tsara, kowane su zai dauki ya 27 har da Jasminah. A ranar suka gama tsara kome. Yadda yake basu hit yasa Uncle Auta ya kira shi yana cewa. ""Kai don ubanka yaushe ka shigo?"" ""Ni kuma?"" Ya rena mishi hankali, sanin cewa bai gaya musu zai shigo ba, sai kuma ya saka a ransa cewa. ""Kawai ina zargin kamar ka shigo ne."" Murmushi yayi ya ce mishi. ""Na zata ka shigo ne!"" Murmushi yayi ya ce mishi. ""Ka cika zargi!"" Daga haka ya shashatar da"

"zancen, suka cigaba da abinda ya tara su. Domin daga karshe conference call suka yi."

"Kusan wunin ranar aikin da suka yi kenan, tunda aka kawo mishi abinci mai gadinsa ya amsa ya kawo"

"mishi, ya ci ya bar sauran. Can ya kara odar na dare. Kusan sallah yake d'aga shi a wurin bayan ya gama ya wuce ya tafi unguwa. Bai dauki mota ba, sai dai taxi d ya dauka haya, ya tafi kamfanin lokacin an tashi ya shiga dakyar suka bari ya shiga shima sai da ya bada cin hanci, bai nuna musu waye shi ba ya shiga yana kallon yadda ma'aikatan yake, daga nan ya wuce tsohon side, daga can ya hango office din MD Khamis ya bude asalima kamar akwai wani a cikinsa, haka yasa shi isa har kofar office din abinda ake zargi ya gani da idanunsa, daya daga cikin ma'aikatan ce take kuka, da rokon ya barta da mutuncinta sannan ya duba tana da ciki dakyar suka samu cikin kada wani abu ya same cikin rayuwarsu zata shiga"

"garari, amma Khamis ya shafawa idanunsa toka ya daka mata tsawa, tura office din yayi yana faWin."

"""Taso ki tafi!"" Ta cire hular kanshi na face cap din da ya saka ya ri™e. Kunya ne ya kama shi, ""thank you"

"sir!"" Murmushi yayi ya ce mata. ""Ki dauki maternity leave mana idan cikin yayi kwari sai ki dawo, yana da kyau hakan!"" Cikin wani irin girmama ta ce mishi. ""Zan dauka sir!"" Bata san waye shi ba, amma a yadda ya bata umarni, kuma Oga Khamis bai magana ba, haka ya tabbatar mata da shi wani ne, juyawa yayi ya rakata har bakin gate din, sannan ya nufi new side dinsu, ya gama kallon wurin da kyau, kafin ya wuce ya"

"fita. Koda ya isa gidan da abinci ya isa, ya haura parlourn sama ya baje."

"Next day ya kar shiryawa ya tafi ma'aikatan, ya samu suka bar shi ya shiga yasan Khamis ba zai tab'a"

"bada labarin ya dawo ba ko don a tambaye shi yaushe? A ina ya ganshi? Haka ya gama zaga kamfanin har ya hadu da masu sata a kamfanin, haka ya dawo gidan ya rubuta, kome zuwa uku yayiwa kamfanin. Khamis kuwa tattarawa yayi ya gudu Abuja, don yasan idan har suka sake ido hudu da shaidani Turaki"

tow sai dai ya bar kamfanin. Shi yasa ya gudu kafin su sake haduwa.

***

"Yau kwanaki hudu kenan da aka ce mu je interviews, Ya Ado ya kira Mama ya gaya mata har da su Aunty"

"Hindatu, aka yi ta murna a Bauchi Mama kan har da sadaka tayi, domin gani take kamar na amshi kaddarata ne, amma har yau na kasa nutsuwa zuciyata tana wani irin tsalle a duk lokacin da na tuna da Ya Hafiz yana nan sai na ji bakiWaya kome ya rikice min, Ya Ado ya haWa ni da Dr Dijah Bala, ta min yan tambayoyi na bata amsa, ta ce mishi yayi hakuri abin yana barin mutum ne a hankali, amma da zaran wani abu da ya shafi past dina ya dawo tow zai cigaba da hunt Wina, Haka Aunty Nuratu Kafaya ta gaya masa, kusan sati aka saka a zuwa interview din, haka yasa Ya Ado ne ya kai ni kasuwa muka sayi kayan da zanyi amfani da shi, kuma yana da yakinin Allah zai bani sa'a, ranar ashirin da watan June aka saka"

zamu.

"Yau sha bakwai ina kwance da yamma a parlour kasance Asabar ne, Rufa'i ya shigo da sallama, tashi"

"nayi na zauna ina kallonshi yayi dariya yana faWin.. ""Manya Lubnah ki amince na kawo dubu goma a daura mana aure, ni bani da matsala xan amince ki ta juya ni kamar masa."" Murmushi nayi na ce mishi. ""Kai dan Yaro da kai ne zan amince na aure amma ka mugun rena min hankali."" ""Samun kyakkyawar saurayi irina sai an cika form, Gara na miki talla kafin mata su kwace miki ni."" Haushi ya kama ni na kalle shi na yi kwafa, Aunty Zakiyah ta fito tana mana dariya sai zoyalat suke karshe na biye musu aka wuce wurin, haka ya zauna har Ya ado ya dawo ya amshi abinda ya zo amsa ya koma, ranar Lahadi kuwa jin wani irin tsoro ya kama ni nake, ban taba zuwa irin wuri haka ba, nayi su goge karamin fashion hijab din da zan daura akan kayan, sai takalmana da na kara goge shi, sannan na koma na zauna ina ta azkar, domin zuciyata ta gama razana, lokacin da na ga kamfanin da Ya ado ya nuna min, da kuma aikinsu, sannan ya gaya min wani abu.."" kada ki rena kanki, idan kika yi haka ma'aikata zasu yi bullied dinki,"

"please ki tsaya akanki kada ki bada fuskar da za a wulakanta mana ke, ki yarda da kanki."""

"Daga haka na ji a raina zan yi kome don na wanke Ya ado, ruwan sama aka fara kamar da bakin"

"™warya, bayan na ci abinci na kwanta sannan na kara nazarin takardun da zan tafi da su, kafin na hada kome a wani jaka. Washi gari tun asuba Ya Ado ya buga min kofar dakin ya bani wayarshi. Addu'a mama take min kamar ta aro kafa ta biyo wayar, tayi min Addu'ar nasara da sa'a tare da dace, haka na amsa da Amin, bayan mun gama wayar na shiga wanka na hada da Alwala, sannan na yi sallah na shirya tsaf, karfe bakwai saura muka bar gidan tare da Ya Ado da Aunty Zakiyah, ita ta sauka a can asibiti ni kuma Ya"

Ado ya kawo ni inda ma'aikatan take.

Ikorodu Local Government.

"Anan kamfanin yake, kafin mu wuce ya ce min.. ""idan kika fito daga kamfanin idan kin samu abin hawa"

"zasu kawo ki can inda mutane suka tsaya sunan wurin Garaj kenan, daga nan zaki samu mota zuwa gida kin ji ko?"" Gyada mishi kai nayi ya dunkule hannunshi yace Goodluck! Murmushi nayi ya kawo ni har kofar kamfanin ya ajiye ni, ya fito zuwa bayan motar ya mika min lema da rigar ruwa nace mishi. "" Ya Ado wannan ma ya isa."" Ciro dubu goma yayi ya ce min. "" Ki rike wannan! "" Murmushi nayi na ce mishi. "" Allah ya kara budi. "" Har ya juya zai tafi ya dawo ya Wan janyo ni jikinshi.."" ki kula kada ki bari a rena min ke kin ji ko? "" Gyada kai nayi, yayi murmushi sannan ya wuce ya shiga motarshi sai da ya tafi na shiga kamfanin, ana ta taruwa, ina shiga na ga matasa ire-irena, ina zuwa wurin na musu sallama babu wanda ya amsa min, kame kaina nayi na koma gefe, domin daga dukkan alamu duk masu zuwa interview ne, har wurin karfe takwas motocin alfarma suka fara shigowa kamfani, gabana ne ya fadi sosai, haka wasu fararen mutane suka fito, ni dai ban tab'a ganin irinsu ba, haka suke fitowa tare da tafiya cikin kamfanin kamar zasu tashi sama, kowa ka gani sanye yake da coat irin na aikin nan black kusan shigar mu ce da su, wurin karfe goma saura wata mota ta shigo kamfanin wanda yayi daidai da fara kiran sunayen mutane, Yara ne guda biyu suka fito, daya tana cin abu a cikin kwali, tana ta zaga wurin. Kiran wasu mutanen aka yi a lokacin na lura bamu wuce ashirin da wani abu ba, haka muka cigaba da zama, har karfe sha biyu ba rana sai ga wata mota ta shigo, a lokacin Yaran nan sun zo kusa da ni suna wasa, masu kula da Yaran"

"suna ta tare tare da su, ban san ya aka yi ba sai ganin daya daga cikin yara biyun ta tsaya........"

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 44"

"Cak idanunta kawai yake motsawa, a daidai lokacin da aka kira sunana kenan, yadda yarinyar ta tsaya"

"zaka zata ko wasa take tana kallon mutane amma ni nasan ba haka ba ne, saboda ya tab'a faruwa da Yasir ya saka abu a bakinsa sai da na rungume shi ta baya na matse mishi cikinsa abin ya fado da amai. Da gudu nayi watsi da takarduna, na nufi yarinyar da kowa ya kama gabanshi tana niman faduwa, na rungume ta ta baya na shiga matse cikinta tare da buga bayan da kaina sau biyu nayi mata na ukun sai ga amai da kwallon abin ya fado, zubewa muka yi dukkan mu, domin ta suma ne, da sauri na kara gyara mata kwanciya a jikina masu kula da su, suka shiga ihu, ""ban ruwa!"" Ka fada musu, mika min suka yi na"

"kunsa a bakina na watsa mata sau uku sai gashi ta fara ajiyar zuciya. Nima ajiyar zuciyar nake saukewa,"

"na tashi duk kayana yayi kura, ashe labarin abinda ya faru har an isar ciki, tallafo yarinyar nayi na zauna"

"da ita a kujeran da na tashi. ""Sannu daga yau kada ki kara cin abu a tsaye, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce yana daga kyauwun dan uwanku ya ci abu cikin nutsuwa, haka zai kiyayye daga sharrin shaidan da sauran abokan halitta, idan zaki ci abu ki daina zuwa gaban jama'a kin ji, ki samu can gefe guda ki ci, mutane ba kowa bane normal wani yana da evil eyes, evil tongue, da bad mouth. Kada ki sake tsaya a gaban mutane kin ji."" Gyada min kai tayi na mike tare da kallon masu kula da su. ""Iyayen Yaran nan sun yarda da ku, suka baku amanarsu, sannan sun amince da nagartakun suka bar Yaransu a wurinku, ku kula da aikinku kowacce addini da kabila ta yarda da gaskiya da rikon amana, please ku taya su kula da Yaransu. Allah ya bamu sa'a."" Lokacin da na juya na ga bakiWaya mutanen da suka fito sun koma ciki abinsu, ajiyar zuciya na sauke na tattara takarduna, sannan na nufi ciki don sai yanzu na tuna da an kira ni fa, ina shiga cikin hall din naga wasu daga cikin staff din sai kallona suke irin kallon wulakancin nan, kofofi uku ne, kuma dukkansu an rubuta interview, wurin matan na isa na ce musu. "" Don Allah a wacce kofa aka kira sunana? "" Ina ga wannan ba wani abu ba ne da na fada da zafi, amma daya daga cikin matar ta ce min. "" Kin ajiye mu ne mu ji ko an kira sunanki?"" Kalaman Ya ado ya dawo min na kada na bari a wulakanta ni, kuma kada na wulakanta kowa, murmushi nayi nace mata. "" Sorry! "" Daga nan na wuce na zauna har wurin karfe biyu bakiWaya suka fito mazan suka tafi sallah wasu daga cikin wadanda suka zo interviews din suma sun fito, haka nima na fita nayi sallah, ashe sun rigani dawowa, ina zuwa kuma suka fito wai ashe an yi ta kiran sunana, bana nan. Sai nayi kamar na kunyata Ya Ado ne, haka na tattara kayana wani mutum ya ce min. ""Mrs Jama'are!"" Wani irin kwallar farin ciki ne ya cika min idanu, na juya ya ce min.."" ana kiranki! "" Gyada kai nayi na bi bayansa, wani hadadden office ne, muka bi stair aka kai ni, kusan tattaunawa ake suke suna faWin "" a cikin mutane dari da wani abu bakiWaya mutane sha bakwai ne suka tsallake!"" ""Sha takwas dai Uncle Auta, sha takwai kamar ya?"" Shigowar da nayi yasa suka zuba min idanu, murmushi Macen cikinsu tayi duk da bata kai su shekaru ba, amma da alamar suna ji da ita ga Yaranta s gefe, d'aga min hannu daya wacce na taimaka yayi na mata murmushi. ""Mom ita ce ta ceto rayuwata!"" Mikewa uwar tayi ta mika min hannu. ""Na gode da abinda kika yi, yau kamfani tana alfahari da ke da kuma irin wannan ceto ran da kika yi, min gode."" Gyada kai nayi ban iya amsawa ba. ""Me yasa kika yi missing interview din?"" Wani can na gefenta ya tambaye ni, cikin girmamawa na ce mishi. ""Na farko na tsaya ceton Rayuwarta ne, saboda yar adam ce kuma hakki ne a kaina na tsaya na taimaka mata, na biyu idan da na tafi na barta wani abu ya same ta har abada ba"

"zan yafewa kaina ba, koda ace ban samu aikin nan ba, ba laifi amma nayi sa'ar ceton Rayuwarta. """

""" Bayan nan an kara kiranki bakya nan ina kika je? "" Ya kara cilla mun tambayar. "" Ibada na tafi, koda"

"na dawo na samu an tashi, duk abinda ake nima a duniyar nan, anan zamu barshi, can ne dolenmu don na rasa wannan damar ba wani abu bane, babbar damar da zan rasa shine rasa sallah nan."""

""" Kina magana da kawazuci, me yasa kika ajiye son kika dauki kawazuci?"" Yar dariya nayi, yadda"

"suka kalle ni sai na rufe bakina, kaina a kasa kafin na ce mishi. "" Duk wata mace a duniyar nan idan har ta isa mace uwa ce, ko ta haifa ko kada ta haife ita din uwa ce, idan har da rayuwa ta bamu abinda muke so,"

"zan ji ciwon idan aka ce Y'ata ce a cikin wannan yanayin, akwai abinda dukiya baya iya siyansa a cikinsu"

"kuwa har da Yara, kawazuci ba iya mutane ke raye akanshi ba hatta dabbobi suna da ita. """

"Jinjina kai yayi ya kara da cewa. "" Yanzu idan kamfanin nan tana cikin wani irin yanayi kuma lokancin"

"sallah yayi zaki iya tsallakewa ki yi sallah!"" Kallon kasa nayi nace mishi. ""Ba mamaki wanda ya tsaya har kamfanin ya iso wannan matakin bata raye, yau ya tara amma baya nan balle ya ga yadda yake tafiya, an tambayi wani daha cikin magabata me tafi yin addu'a a kai game da Lokaci, ya ce Allah ya bashi aron numfashi ya kara ganin wata lokacin da zai ibada, kamfani bata kai ibadana muhimmanci ba, zan bawa kamfani lokacina amma banda ta ibada ta."" Daga haka suka yi shiru basu kara magana ba, Nima kuma ban ce uffan ba, ina tsaye a wurin karar shigar sakon da aka musu na d'ago kai ina kallonsu, daya babban cikinsu ya ce min. ""Mrs Jama'are, idan aka baki damar aiki da kamfanin nan me kike ganin zaki yi har ya kai ga nasara."" Jan iskar bakina nayi na ce mishi. "" Na karancin hadahadar kasuwanci a degree na farko, na kara yin master a tallace-tallace, idan har akwai abinda xan yi shine zan tsara yadda kamfanin nan zata fito idanun duniya. Zan mai da hankalina wurin daidaita kamfanin izuwa ga sauran takwarorinta na"

"duniya, sannan zan bawa aikina muhimmanci sama da kome da kowa na kamfanin. """

""" Mrs Jama'are idan kamfanin ta dauko karyewa, nasan kin san aikin kamfanin me kike ganin zaki mata"

"kada ta karye?"" Lashe bakina, na sauke ajiyar zuciya kafin na ce."" A matsayina na karamar ma'aikaciya kuma wacce take da ilmin tsara tallace tallace, shine zan fara duba yadda zan janyo hankalin masu zuba hannun jari, daga gida zuwa kasashen ketare, aanan kuma zan yi ™o™arin rufe duk wata kofa da zata janyo min karyewa a cikin kuwa shine zan zubar da ma'aikata, ba zan debi sabbin ma'aikata ba, tsofin zan kara basu horo sannan na kara inganta ilimin su yadda zasu fuskanci yanayin da ake ciki, za a rage wasu abubuwan da ake yiwa ma'aikata idan kamfani ta farfaWo sai a kara musu, wannan tsarin economic"

"ne ta kowacce kamfani da kuma manyan ma'aikatun duniya."""

""" Kina nufin a watsar da tsarin diban ma'aikata kenan? Idan haka ne kuwa har dake a cikin haka ya"

"miki?"" Gabana ne ya fadi shi kenan nayiwa kaina, sai nayi murmushi na ce mishi."" Haka ma ba laifi bane, kowacce kamfani tana kokarin ceto rayuwarta ne. Idan har aka duba masalahar kamfanin babu amfanin"

"diban ma'aikata, idan kuma kamfanin tana da bu™atar haka ai ba laifi bane. """

""" Mrs Jama'are ko dai zaki gare muradinki ne? "" Inji matar, murmushi nayi mata nace mata. "" Ko daya ni"

"ina da nawa ra'ayin ba wai aikin kamfani nake da buri ba, amma a tambayar da aka min dole na bada amsa."" Cidar d garin ya fara alamar za ayi ruwa yasa na kalli agogon hannuna. ""Shi kenan zaki iya tafiya!"""

"""Na gode!"" Na fita ai nasan ba wani batun daukar aiki, ya xan yi da Ya Ado?"

"Ruwan da aka fara yasa da na sauko kasa ba tsaya ina kallon waje kamar yadda kowa ya tsaya, matan"

nan sai gulma suke.

"Bayan fitar ta ya juyo kujeran, yana ta rubuce-rubuce. ""Bro yarinyar tayi tana da kwarin gwiwa!"" Inji"

"Jasminah, ""Kuma da alamu zata yi abinda ya dace, shi dai bai ce kome ba, "" can dai Uncle Auta ya ce mishi. "" Sunan yarinyar kamar yaso na taSa jin sa a wani wuri?"" "" Usman Umar Jama'are, Baristan nan!"" Inji Ubaid, "" wow dole ta samu confidence, irin wannan ake bukata asalin kwarin gwiwa na gani a cikin kalmanta!"" Shi dai shiru yayi can Uncle Auta ya ce mishi. "" Ni kuwa yarinyar ta min, tana da nutswa da hankali!"" "" Oo Uncle Auta fell in love daga kallo daya."" Buga table din yayi ya ce musu."" Bata min ba ta cika surutu, mai surutu baya abinda ya dace!"" Daga haka ya bar office din yana mai riko hannun Yaran.."" Uncle BT amma tana da kirki, me yasa ba zaka dauke ta ba. Ina sonta."" "" Princess idan aka kawo ta kamfani ba zata yi aikin da ya dace ba zata yi ta hira da mutane ne."" "" Uncle BT yana da kirki Please!"" Dan durkusawa yayi yana kallon yarinyar da take murza idanunta. "" Uncle tana da kirki she is a good person!"" Taya zai gaya mata bata da kirki, bayan ta ceto rayuwarta. "" Princess kada ki damu da irinsu."" Idanunta ne suka cika da kwalla, har suka zubo mata ta ce mishi.""please!"" "" Ok ok bar kukan haka kin ji! "" Gyada kai tayi tana murmushi, haka suka fito sai lokacin ya hango tana fita daga kamfanin a hankali tana tafiya ruwa na zuba kaWan kaWan, bodyguard dinsa ne suka fito da lema suka saka mishi bayan ya dauki Yarinyar, suka bude motar ya sakata, ya daura mata belt sannan ya shiga suka tashi motar, a hankali"

suka bar kamfanin a bakin gate suka tsaya sakamakon wata motar da ta danno kai.

"A hankali nake tafiya har na samu wani abin hawa na gaya mishi inda zai ajiye ni, ya ce na shiga, sai dai"

"cikin ikon Allah motar taki tashi dole na sauka na cigaba da tafiya nayi tafiya sosai, kafin na nufi garej, kamar ance na d'ago kaina daga lemar na hango ya Hafiz ban san lokacin da na sake lemar na fara ja da baya ba, murmushi ya sake yana kallona, daidai sake wata irin ruwa mai karfin gaske shaaa, karafuna ne suka dauka rawa, na ji kamar cikina ya hautsine, wani irin abu na ji ya tsaya min a wuyana. Na fara ja da baya, yana bina ina ja da baya yana bina, ga titin ba motar da suke wucewa, hawaye ne ya fara zubo min. Karar horn na ji na kalli wurin, na hango motar kamfanin ce, wani irin kuka ne ya kwace min ganin yadda suka wuce. ""Ba fa mai taimakonki, kaf duniya babu sai ni, ni kaWai ne last hope dinki!"" Yadda yake tawowa ban san me ya tare ni ba, haka na zube yayi kaina zai damke ni, na kare kaina tare da fasa wata irin kara tare da kiran sunan Allah, na rufe idanuna hannuna biyu na saka ina mai kare kaina, wani irin"

"kara naji wanda ban san yadda akayi na bude idanuna ba, sai ganin............."

(Alhamdulillahi na gode sosai wannan wurin nasan sai an ji kamar a cije ni kuma duk wnada ya zagi

hafiz shi da kanshi)

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 45"

"Kamar yadda aka ce mata suna suka tara, haka ma Maza sun kashi gida daban daban, domin ni dai ban"

"tab'a ganin irin wannan mutumin ba, hannun da ya Hafiz ya kai zai damko ni ita aka murder a baya sai da tayi wata irin ™ara, kafin ni da shi mu farfaWo, bawan Allah nan ya kara sake mishi naushi. Sai na kasa fahimtar tsoron waye zan ji a tsakaninsu Hafiz ne ko wannan mutumin da sauri na kara kifa kaina kasa ina wani irin kuka, ji nayi an lullube ni da abu, an d'aga ni. Muryan mace na ji tana faWin.. ""Sannu muje mota, ai ke ma'aikaciyarmu ce, Sir ba zai bari wani abu ya same ma'aikancinsa ba."" Haka ta saka ni a"

"motar sannan ta koma ta dauko min lemana da tarkace na, a hankali na kalli inda Ya Hafiz yake kwance,"

"mutumin ya murde hannunsa. Sai zabga mishi naushi yake irin na b'acin ran nan, barin wurin muka yi, na"

"kifa kaina a kan cinyata, idanuna rufe. ""Wacece unguwa kike?"" A hankali na gaya musu ma cigaba da kuka."

---

"A can kuwa Garej Mr Turaki bai yi niyyar shiga al'amarin ba, tunawa da yadda aka yiwa Mrs Thomas yasa"

"shi kiran security na kamfanin kafin ya fita da sauri duk da kiyayyarshi da sanyi kuwa, amma ta gane ta ne da lemarta. Sannan Ilham ta kara ce mishi, ga wacce ta taimake ta. Haka yasa shi tsayar da motar, umarni ya bawa Tajudeen akan ya kira sauran security din domin ya tuna abinda ya faru da wancan matar haka yasa shi sauka ya samu Hafiz. Ba zai ce ya yake ji ba, domin abu ne me sauki da mutum zai"

"bada labarin yadda ya ji shi, wani babban al'amari ne da Allah kaWai yasan yadda abin ya™e."

Yadda ya dage da dukkan zuciyarshi yake kai mishi duka zaka rantse da Allah irin yasan Mafarin

"lamarin ne, amma ina shi zuciyarshi abinda ya bashi ita din mace ce me rauni kuma tana bukatar taimakon shi, fisge shi Ubaid yayi yana faWin. ""T meye haka? Me yayi maka? Haba da girmanka?"" Huci yake yana nunawa security Hafiz. ""Ku tabbatar kun hada shi da yan sanda."" Sannan ya juya ya bar wurin ranshi yana soya, ko ruwan da ake yi bai dame shi ba, tunda Ya shiga motar yake jin wani irin zafi. Har suka isa Mansion na Kumo bai magana ba, yana zaune shiru towel Jasminah ta lullube shi da shi tana faWin. ""Sanyi zai kama ka!"" Komawa gefensa Alhaji ELYakub yayi ya zauna yana press din hannunsa a hankali, alamar yana calming dinsa da ya huce wani irin zuciya ce me cike da kishi, dafe kanshi yayi ga hannunsa da ya ji ciwo yayi ja saboda naushin fuskar Hafiz kawai,"" Me ya faru da ita?"" Daddah ta tambaye su hankalinta a tashe, "" Fada yayi da wani!"" Uncle Auta ya fada yana kallonshi. "" Fada!!!"" Duk suka hada baki, domin abin da mamaki Daddah ta ce. ""Wai yaushe ma taso ne?"" ""Muma ganinsa muka yi dazun!"" Ubaid ya bata amsa, cike da mamaki Alhaji ELYakub yake kallonshi. "" Kuna nufin bai gaya muku zai shigo ba?"" Alhaji ELYakub ya tambaye su cike da mamaki, shigowa Alhaji Abbas kumo yayi yana faWin.."" Amma wannan wacce irin abin kunya ne Bilal ya aikata? Duk an dauki videon ana yaWawa a duniya. Baffa ya kamata ka yi wani abu, taya zai shirya interviews without our knewing, ba laifi sai ya je ya kama fada da yan iska idan wani abu ya same shi fa? Ya yake tunanin al'amarin zai kasance ga masu saka hannun jari."" Mikewa yayi bai karasa jin mai yake faWa ba yayi waje abinsa, "" Turaki! "" Ina tuni ya bar

Please Login or Register in order to submit comment