Reading KIDA A RUWA BOOK2 COMPLETE BY BILLYN ABDUL Chapter 3 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

“Zak… kana nufin kaci karo da mutanen da kowa yaji tsoron ɗaga su?”.
     Wani ƙaramin murmushi mai zafi, mai ɗaci ya bayyana a gefen labban Dada. “Ni ba wanda nake tsoro, Imran. Amma gaskiya… ita ce abin da suka hana ni gani tsawon shekaru uku. Ni kaina kuma na yarda da hasashen General, ta irin hanyar da suke kai, kawai zamu bi mu gano su, mu kuma yaƙe su” ya ɗanyi shiru na sakan biyu. Sai kuma ya cigaba da faɗin, “Yau na baka wannan rubutun. Ka tafi da shi. Kada ka bari kowa ya gani a yanzu har Janar. Dan kai kaɗai nake son kayi waɗan nan binciken”
      Idanu kawai Imran ya kafeshi da su ya ma kasa magana. Wato idan Zak.. ɗinsa na wani abu a wasu lokutan yakan ga tamkar mai aljanu ko mai gani har hanji da yara kan faɗa. Kai har ɗan duba ma zai iya kiransa, amma yasan duk ba haka bane, tsabar kaifin basira ne kawai da iya sanin kan duniya da mutanen cikinta da ALLAH ya bashi.
    Shi ko Dada ganin kallon da Imran ɗin ke masa, sai kawai ya jingina da kujera a hankali ya lumshe idanunsa. A haka ya ce, “Ban san miya baka mamaki ba ka tsaya kana kallona bayan lokacin ka ƙayyadadde ne. Idan rana ta yi zaka gane me yasa naga mutuwa ta fi wannan shari’ar sauƙi.”
    Imran ya kasa magana yanzun ma, a haka har lokaci ya ƙare, masu tsaronsa suka buga ƙofa. Miƙewa kawai Dada yayi zai bar gurin, sai kuma ya tsaya ya kalle shi for the last time yasan kafin a sake ganin juna sai bayan shekaru. Dada ya lumshe ido tare da furta masa a hankali kamar sirrin da baya buƙatar iska ta ɗauka zuwa gaba a tsakanin su.
      “Ka zama hasken da nake bukata a waje. Ka cigaba da zama UBA kuma nagartaccen MIJI a cikin GIDA”. Daga haka yay gaba batare da ko waiwayen Imran ba. Shi ko Imran ya kasa motsi sai kai-kawo furucin ƙarshe na Zak-Shadow ɗin ke masa amsa kuwwa a cikin kai, dan magana ce a dunƙule ya bashi kuma mai ƙarfi.....

   (((★)))(((★)))(((★)))
         ★ 2021..... ★

       Duk wanda yasan gidan a shekarun baya takwas da suka shuɗe yanzu idan ya zo ba lallai ya gane ba. Domin kuwa gidan nan da Mammah da yaranta tara mai sassa biyu kacal a yanzu ya zama mai sassa da yawa sakamakon iyalanta da suka ƙara yawa. Kamar yanda Dada ya barma Imran wasiyyar dawo da ginin su Ma'aruff a cikin gida a wacan lokacin hakan ta tabbata, duk da kuwa shima Imran ɗin dole ya bar ragamar a hannun Uncle Nasiru sakamakon prison ɗin daya shiga na shekara uku.
     Duk da suna cikin ɗacin yanayi Uncle Nasiru yayi abinda ya dace harda kuɗin aljihunsa. Anyi bikin Ma'aruff da Ja'afar da amarensu Shariffa da Lailah, sai dai bikin baiyi armashi ba sakamon jarabawar da wannan ahali suke ciki a wancan lokaci na rasa jigon gidan da suke ma kallon Uba bawai yaya kawai ba. Amare sun tare a gidan Mammah kowace da ɓangarenta, kuma Alhamdullah dukansu masu tarbiyya ne da suka fito daga gidan tarbiyya. Dan kuwa akwai abubuwa da yawan gaske da suka bambanta su da surukar gidan ta farko Nabeeha. Mammah mace ce mai sauƙin kai da sanin haƙƙin ɗan adam, tana da zafi idan kace zaka kawo mata wargi, dan in har kaji muryarta a sama lallai an kaita maƙura ne. Duk wanda yazo jikinta ya zama ɗa na halak da zata haɗe da nata ƴaƴan ya riƙe babu bambanci a ciki, wannan yasa biyayya da nutsuwar Aunty Shariffa da Aunty Lailah ya basu fiye da abinda suke zato da farin ciki a gidan aurensu. Dan kuwa suna matuƙar kiyaye al'amarin Mammah a matsayinta na uwa, hakama ƙannen su Ma'aruff sun maida su ƴan uwansu na jini ba dangin miji ba, sai hakan ya bada masalaha da shaƙuwa mai ƙayatarwa da birgewa a wannan gidan, idan ka cire rashin Dada dake zagaye da zukatansu dan suna jin hakan a ransu a kowacce rana tamkar sabo. Babu ranar banza da zata zo ya wuce ba'ai hirar Dada ba, za kuma ka samu hatta su Ma'aruff dake magidanta kuma manya yanzu a gidan sai sunyi kuka suma. Mammah ce kawai jaruma mai danne komai a gabansu sai dai idan tana ita kaɗai ta share hawaye.
      Shekarar su Lailah ɗaya a gidan duk suka haihu, kuma Alhamdullah haihuwar tasu babu wani nisa tsakani. Dukan su yara maza suka samu, kuma yaran sunan Dada da Imran aka saka musu wato Haysam da Imran. Sai dai ana musu alkunya da Abees da Aheel. A shekarar da Imran ya fito bayan ya gana da Dada sau biyu sannan suna cika shekara uku-uku da aure suka sake haihuwa, sai dai wannan karon Shariffa mace ta samu, ita kuma Lailah Namiji. Bayan haihuwar tasu ne kuma Imran ya sake tada saban aikin gyaran gidan na su Mammah. Dan kuwa gaba ɗaya aka rushe sashen Mammah dana su Zak-Shadow tunda Nabeeha ba zama take ba sai jefi-jefi take zuwa gidan, shima ɗaukar wani abu ne ke kawota,  wani lokacin ma sai tazo ta fita su Mammah basu sani ba. A wannan karon ne akama gidan gyara fiye dana baya, dan komai da fasalinsa an canja, hatta Ammar da Bilal an musu nasu ɓangaren. Sai ya zama anyi sashe huɗu ta can baya, an fitar da gate ta wancan Street ɗin, ta cikin gida akwai katanga tsakanin ɓangaren su Ja'afar ɗin dana su Mammah da Dada da suma suke su biyu. Tsarin ya bada kamar gida biyu. Dada da Mammah a sashe ɗaya, su Ma'aruff su huɗu a sashe ɗaya sai dai kowa da part ɗinsa, akwai katanga tsakaninsu amma akwai ƙofar da zaka iya shigowa sashen su Mammah basai ka zagaya ta wajen gate ba. Wannan gyara shine ya sake sauya gidan Mammah daga mai sashe biyu na talaka mai ƙaramin ƙarfi zuwa na masu rufin asiri da wadatar zuci a yanzu, ga irinmu ma talakawa kai tsaye zamu kirashi ana masu kuɗi.....

))))(((()))))((((

      A ɓangaren Imran yanzu haka dai shekarunsa biyar kenan da ganawa da Dada dake cika shekaru 8 a prison, kamar yanda Dada ɗin yay hasashe ya faɗa kuwa ba'a sake bashi damar ganinsa ba. Babu irin shiga da fitar da baiyi ba amma sun hana masa damar sake ganinsa. Dan haka Janar ya zauna ya lallashesa akan yayi haƙuri komai yana da lokacin sa.
     Badan hankalin Imran ya samu kwanciya ba ya haƙura. Sai dai ya maida hankali akan binciken dukkan abubuwan da Dada ɗin ya bashi. Sannan yaje ya ɗauki saƙon daya ce ya ajiye masa. Inda saƙon ya fahimtar da shi abinda Dada ya shirya. Dole ya ajiye batun damuwarsa da kewarsa a gefe ya maida hankali akan aiki yanda ya kamata....

      Burin Janar ya cika na shigewa cikin siyasa tsundum da sha'anin ƴan siyasa. Cikin nasara ya lashe kujerar da aka tsaida shi a takarar ɗan majalisan tarayya. A yanzu haka yayi ɗan majalisa shekara huɗu kenan. A kuma yanzu haka ana shirin sake buga tambarin sabon zaɓe, babban shirinsa kuma shine fitowa takarar shugaban ƙasa. A gefe kuwa Imran ya sake samun girma zuwa Colonel saboda kwantar da kai da yayi shima bisa shawarwarin General ɗin dana Dada.....

✷✷>><<✷✷>><<✷✷
★SCHOOL★

          “Yau sai naga waye ubanku a cikin ƙasar nan, ƴan iskan yara kawai kamar wasu ƴan daba ku kama min yarinya da duka, koni dana haifeta da ubanta bamu taɓa dukanta haka ba. To wlhy idan kuna taɓa wasu ku zauna lafiya yanzu kun taɓoma kanku kuwa, dan har prison sai na saka ubanku yayi bama ku ba.......”
      “Ranki ya daɗe dan ALLAH kiyi haƙuri, mahaifinsu bashi da laifin komai sune sukai miki ba daidai ba. Wlhy mu kammu yaran nan sun kai mana wuya a makarantar nan, kawai dai babu yanda muka iya ne.....”
      “Oh babu ma yanda kuka iya? Wato tsoronsu ma kuke ji saboda uban su ne shugaban ƙasa, yara na irin wannan ta'addacin amma kuke iya barinsu a cikin makarantar ku harda faɗin babu yanda kuka iya.....”
      Kasa cewa komai principal yayi, sai ma haƙuri daya cigaba da bama hamshaƙiyar matar da kallo ɗaya zakai mata kasan matar babban mutum ce a ƙasar. Dai-dai nan akai knocking ƙofar ofishin, principal ya bada izinin shigowa. Wani matashin saurayi ne da alamu suka nuna shima ma'aikaci ne a makarantar, yay sallama ya shigo sannan ɗalibai biyu dake bayansa riƙe da wata matsakaiciyar budurwa da bata wuce 15years ba suma suka shigo. Zaram matar ta miƙe tai kansu, jikinta har rawa yake ta kamo hannun yarinyar da suka riƙo kanta naɗe da ƙaton bandeji, fuskata kuwa da ganin yanda tai suɓu-suɓu kasan tasha maruka da kuka ta kuma ci bugu, dan idanun jazur suke suma luhu-luhu. Jikinta yarinyar ta faɗa, yayinda ita kuma ta ɗauki dogon salati ta dire tana mai ɗago yarinyar a jikinta.........✍️

Wannan aiki nasan sai Zakanya da vice ɗinta Damisa🤣.


_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*


*_ASSALAMU ALAIKUM MUTANE NA MASU ALBARKA_*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*


*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*


*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*


*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*


*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*


*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*

_(2k)_

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.


_(1,500 CFA)_
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_AREWAPEN (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull



*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


7


.......Cikin matuƙar bala'i da ihu matar ta ce, “Babbar bala'i kai, wlhy bazan yarda ba, dolene ma yaran nan suje police station dan sai nayi shari'a da su.....”
     Da sauri matashin malamin nan ya katseta da faɗin, “A'a ranki ya daɗe kada ai haka. Mudai bari a zauna dasu aji miya haɗasu, duk da nasan Naja'atu da Ruƙayya fitinannun yara ne amma basa faɗa sai da dalili...”
         “Oh yanzu na fahimta, to kodai kaine ka sakasu su aikata ma saboda kana nemansu? Dan ba abin mamaki bane idan muka dubi yanda malamai suka koma fasiƙanci da ɗalibansu a makarantu”.
      “Innalillahi wa'ina ilaihiraji'un, Hajiya wane irin magana ce wannan? Dan na faɗi abinda yake gaskiya kuma sai ki aibantani da yaran da suke tamkar ƴaƴanki. Amma dai.....”
       “Teacher Khalil ya isa haka. Ka fahimta kawai ranta ne ya ɓaci. Yanzu dai ka kira gidan su yaran sannan azo min da su nan yanzu nan”.
     Sosai ran wanda aka kira da Teacher Khalil yake a ɓace da zancen matar, sai dai bai sake cewa komai ba ransa na ƙuna ya shiga neman layin wanda yasan Yaya ne gasu Ruƙayya, amma fin kira goma bai shiga ba. Ganin ba samu zaiba principal yace ya sake kiran wata number mana, canja kiran yay zuwa ɗayar number da yake da ita, cikin sa'a kuwa ta shiga. Koda aka ɗaga cikin nutsuwarsa yay bayanin daya dace, a ƙarshe ya sanar da ana buƙatar ganin wani nasu babba daga haka ya ajiye wayar ya fita a office ɗin....

Mintina kaɗan Teacher Khalil ya dawo, sai da ya shigo sosai matasan ƴammata biyu suka bayyana. Ta gaba fara ce tas kuma ƙyaƙyawa, siririya daga ganin fuskata kasan zatai rashin ji. Wadda ke biye da ita ma da zasu iya zama kai ɗaya black beauty ce masha ALLAH, itama dai daga ganin fuskar nan kasan zatai tsiwa. Su duka sanye suke da uniform skirt peach color da farar riga long sleeve shirt, sunyi zanzaro da skirt ɗin, sai ɗan ƙaramin baby hijjaf fari shima da iyakarsa matashin ƙirjinsu da ake kiran kamar su da suna ƙwailoli. Daga ƙasa safa ce doguwa data zo har gwiwar ƙafa saboda skirt ɗin nasu kaɗan ya zartar gwiwar sai takalman sandal baƙaƙe na ƴan makarnta. Ga shi dai uniform ne ana saka shi badan ado ba, amma yayi musu matuƙar ƙyau da zaunawa a madaidaicin jikinsu ɗas kamar ka lashesu. Ga wani ƙamshin turare mai sanyin daɗi na fita a jikin nasu da gogaggun uniform ɗin su da suka sha karin guga kamar batun safe suka sakasu ba.
     A makarantar ba'a dukan ɗalibai sam, dan makaranta ce ta kuɗi kuma ta ƴaƴan manyan ƙasa. Duk wanda aka gani a school ɗin lallai ubansa yaci ya ƙoshi ne. Shiyyasa daga ƴaƴan masu mulki saina jami'an gwamnati dana manyan ƴan kasuwa. Dan makarantar ma ta baƙin haure ce ƴan ƙasar waje ba ƴan ƙasa ba. Rabi da kwatar malaman cikinta duk masu jajayen kunne ne, sauran tsiraru irinsu Teacher Khalil ne kawai ƴan ƙasa baƙaƙen fata, sai kuma shi kansa principal ɗin shima dai ɗan ƙasa ne.
      Da farko idanu principal ya zuba ƙyawawan ƴammatan biyu, yayinda matar nan ke zuba musu uwar harara kamar idannunta zasu zubo. Hakama ƴarta dake lafe a jikinta tun shigowar yammatan dake sa'ointa ta sake mannema uwarta tana harararsu. Suko sun wani tamke fuskoki suna cika suna batsewa. Haɗa ido baƙar tayi da yarinyar, tako watsa mata uwar harara da nunata da yatsu biyu alamar saita tsokale idon...
     Wani irin takaici ya sake mamaye zuciyar uwar, dan ta kasa gane ita zata tsokalewa ido ko ƴar tata tunda itama hararar take. Baki ta buɗe zatai magana principal ya katseta sakamakon ambaton sunan yaran da yayi.
       “Ruƙayya Imran Abbas”.
  A cinkushe farar tace, “Yes Sir!”.
Ya sake maida idonsa ga baƙar ya ce, “Naja'atu Muhammad”.
Itama cikin tura baki tace, “Yes Sir”.
      “Ku miyasa bakwa jin magana ne, yara kamar ibilis ne malamin ku kullum cikin kawo ƙararku ake. Yanzu ku duba yanda kuka fasa mata kai, inda abin yazo da ƙaddara fa...?”



.......Adeel ibn Ubaidullah Qureshy. Cikakken balarabe ne ɗan asali gaba da baya. Jinin sarauta dan kuwa daula babba suke da ita a yankin larabawa. Sannan zuri'arsu zuri'a ce mai ɗunbin dukiya da kaso huɗu na arziƙin Dubai yana da alaƙa da shi. Adeel irin gagararrun yaran nan ne da giyar mulki data kuɗi ke ɗawainiya da su. Dan kuwa iya shegen da yake zubawa a cikin Dubai ba'a magana.
     Harkar business ce ta haɗashi da Hajiya Hasiba, a dalilin First Lady da suke aminta. Sunyi wani zaman meeting Hajiya Hasiba ta kasance kujerarta kusa data Adeel a meeting room ɗin, irin ta ajiye wayarta a table sai aka irin kirata ɗin nan, bata ɗaga ba kasancewar suna a halin meeting har kiran ya tsinke, dai-dai screen ɗin wayar na komawa yanda yake ƙyaƙyƙyawan hoton Nabeeha dake a fuskar wayar Hajiya Hasiba ya bayyana. Sai ko karaf a idon sa. Cak ya tsaya da bayanin da yake ya zubama wayar ido, abokan meeting ɗin nasa sukaji shiru duk sai suka ɗago suna kallonsa, cike da basarwa ya ɗauke idanunsa ya cigaba da jawabinsa, amma bini-bini idonsa nakan screen ɗin wayar Hajiya Hasiba har aka tashi.
      Hajiya Hasiba ta lura da kallon da Adeel kema wayarta, amma sai bata kawo komai a ranta ba har suka wuce. Mizai faru da daddare kawai sai ga Firt lady ta kirata wai Adeel nason magana da ita, idan ba damuwa kuma so yake su haɗu. Mamaki ya kama Hajiya Hasiba, ta tambayi ko lafiya? First Lady ta bata amsa da cewar wai akan wani hoto ne da ya gani a fuskar wayarta sanda suke meeting. Sosai Hajiya Hasiba ta zaro idanu tana dafe baki, kafin ta ce, “Kai ranki ya daɗe ɗiyarki ce fa Nabeeha, kin san dai tana da aure kin kuma san waye mijinta da fitinarsa”.
     Cikin nuna rashin damuwa First Lady tai murmurshi da faɗin, “Yo ALLAH na tuba sai me Hajiya Hasiba, aure nawa ne a wannan zamanin da shi gara babu. Ke dai kawai ai sha'ani. Mijinta kuwa girman kansa na banza ba ko sisi, kin san waye kuwa Adeel? Hummm na baki dama daga nan zuwa minti talatin ki bincika sai ki yanke hukunci. Ni dai na isar da saƙo yace zai turo mota a ɗaukeki a kaiki inda yake ”. Daga haka ta yanke wayarta.
     Shiru Hajiya Hasiba tai na tsawon lokaci, dan babu abinda ke zuwa mata a zuciya da brain sai fuskar Zak-Shadow. Amma dai ta daure ta fara binciken waye Adeel kamar yanda First Lady ta bata shawara. Tun a ambaton farko kanta ya nema bugawa, jin nasabar gidansu kawai, jin ɗan waye daga zuri'ar daya fito. Data bincika arziƙin zuri'ar tashi kawai bama shi wadda ya mallaka ba bata san ta rikito a kujera ba tsabar rawar jiki. Har lokacin da za'a ɗauketa yayi bata iya ta dawo a hayyacinta ba saboda matsanancin mamaki. Ai babu ɓata lokaci ta shirya a gurguje tabi ɗan aiken. Ai ko kanta da zuciyarta sun nema fashewa saboda inda aka kaita matsayin wajen hutawarsa. Wani mahaukacin azababben garden ne da in ka kirashi da suna aljannar duniya bakai ƙarya ba. Ga masu hidima zagaye da wajen da wasu mugayen masu tsaro ya subahanallah. Ita dai haka aka kaita har inda yake jiki na ɓari.
     Kallo ɗaya yay mata ya maida kansa ga laptop ɗin gabansa, a haka cike da isa ya nuna mata wajen zama. Sai ta dinga jin kamar ba Adeel ɗin juya bane da sukai zaman meeting, koda yake ko'a jiyan dama yanda yake magana da isa da ƙasaita kasan akwai girma da izza. Amma a yau ɗin ba'a magana. Ya share fin mintuna goma sannan ya gyara zamansa, babu wani tauna harshe ko girmamawa kai tsaye yana kallonta ya furta, “Yarinyar dana gani kan wayarki nake buƙata, ina fatan ba hotonki bane dan naga kuna kama sosai, tsufa kawai zaki nuna mata”.
     Kan Hajiya Hasiba a ƙasa tana murmurshi ta ce, “A'a bani bace. First born ɗina ce, sunanta Nabeeha”.
      “Nice...”
   Ya faɗa cike da iskanci yana ajiye kofin hannunsa. Sai da ya ƙara busar iska ya cigaba da faɗin, “Za'a iya kawo min ita a yau? Zan bada ko nawa ake buƙata, daga biliyan 1 zuwa sama”.

..........“Sir kawai fa dan na taka ita Ruƙayya ɗin ne ban kula ba, kafin na bata haƙuri sai ta hankaɗe ni ta ƙwace wayata ta jefar a ƙasa ta fashe, ni kuma na zuba mata ruwa a jiki ƴan class suka yi dariya. Itafa Nimrah ɗin ma bata ajin ta fita, kawai tana shigowa ba tambayar ba'asi ta hau dukana itama Ruƙayyan na tayata, ni kuma naji wahala na cijesu kawai suka gwara kaina da bango wai aljanunsu ya tashi...”
        “Da dai kin fito kin faɗi gaskiya yarinya da yafi miki”. Cewar Ruƙayya tana hararta. Uwarta zatai magana principal yay saurin tarar numfashinta. Idanunsa akan su Ruƙayyan ya ce, “Ke haka akai?”.
      “Sir ta ɓoye asalin zancen”.
   “To miya faru?”.
“Yarinyar nan ƴar iska ce Sir, a bayan desk ɗinmu suke ita da ƴar iskar ƙawarta, kullum sai suna damunmu da kallon Film ɗin iskanci a waya, mun musu magana akan idan suna kallon rashin tarbiyyarsu a waya suna saka Bluetooth amma sun ƙi dainawa. Kawai yau suna kunnawa na juya na ƙwace wayar na fasa banza, shine tazo zata min hauka ni da Ninah muka sauke mata nata ƙaramin hau ɗin”.
     Rawa jikin yarinyar ya fara, ta fara rantsuwa ita sharri su Ruky sukai mata. Uwarta ma bala'i ta fara wai za'a ma ƴarta sharri bazata yarda ba. Kodai principal ya bari ƴan sanda su tafi dasu Nimrah ɗin ko kuwa tai ƙarar makarantar gaba ɗaya. Cikin takaici Ammar ya ce, “Hajjaju ya kike Abu kamar baƙya ganewa ne, shin anan akwai wai mai tsoron zuwa police station ɗin ne anan akace miki. Yaran nan sun faɗi abinda ya faru har sukai rikici da ƴarki, maimakon ma ki damu da abinda take aikatawa kina neman juye wa mutane shirme. To muma bazamu yarda ba, dan bazata ɓata mana tarbiyyar yara ba, banda ma rashin kula har yara na kallon banza da wofi a waya iyaye basu sani ba, kuma miye na zuwa da waya makaranta? Gasu nan ko waya basu da ita yaran nan kuma basu taɓa damuwa ba duk da sun kai ƴammatan daya dace ace an barsu da ita, idan anyi maganar ku daina bama yara waya ko ku dinga kula dasu idan kun basu musamman masu tashen sabuwar balaga irin su kuga kamar an raina ƙoƙarinku ne. Ba haka bane, a irin wannan gaɓar waɗan nan abubuwa suke kwaɗaituwa a zukatansu, dan haka muma bazamu yarda ba, yaranmu masu tarbiyya ne, bakuma za'a ɓata mana su anan ba, kuma yanda sukai mata sun min dai-dai....”
    Hayaniya sosai ta kaure a office ɗin tsakanin Hajiya da Ammar, sai da ƙyar aka fitar da Ammar itama Hajiyar principal yace taje zasuyi bincike akai. Dan haka an bama yaran suspension na sati ɗaya su duka ukun har sai an tabbatar da gaskiyar mai laifi. Suko ƴan sandan data kira suka sallamesu. Suma ƴan sandan sanin makarantar ta jiga-jigai ce basu ja da nisa ba suka wuce.
       Yaya Ma'aruff dake hararar su Nimrah ya ce, “Sai ku wuce muje masu kunnen ƙashi. Hankalinku ya kwanta ai ko. Banda ma fitina ku kuma haifeta da zaku hukuntata? Ba kusan hanyar kai report bane, jibeku da kawuna kamar kullun magani”.
     Babu wanda a cikinsu bai cika baki da iska ba. A haka suka fito suka shiga mota shima Yaya Ammar na zuba musu tashi hararar.....
   
      ★ Koda suka iso gida ko kallon inda suke su Yaya Ma'aruff basuyi ba suka shige ciki abinsu. Kallon juna Nimrah da Ruƙayya sukayi, cikin marairaicewa Ruky ta ce, “Wlhy yau akwai matsala Trouble Queen....”
    “Babba ma kuwa”.
Aka faɗa daga bayansu, a tare duk suka juya, Mu'azz ne daya zama matashin saurayi ɗan shekara goma sha takwas, dan kuwa ya kammala Secondary ɗinsa ma yana shirin shiga jami'a. Yanzu kam Nimrah ce tace, “Ya Mu'azz kaji tsoron ALLAH”.
         “Oh, to da tsoron ku nake ji. Ba kunce ku baƙwa jin magana ba. To Daddy ma na nan zuwa dan Uncle J ya kirashi shima”. Wani mugun ƙwalalo idanu waje sukayi a tare, shi ko ya kwashe da dariya yana barin wajen. Da sauri sukabi bayansa, amma yaƙi tsayawa har suka shigo falon. Cak kuwa suka tsaya, ganin kowa yana nan har su Aunty Lailah. Yaya Ja'afar ne

Please Login or Register in order to submit comment