Reading KIDA A RUWA BOOK2 COMPLETE BY BILLYN ABDUL Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

KIDA A RUWA

Book 2

1

.........2016

        Shekaru uku da wasu watanni kenan da kama Zak-Shadow. Abubuwa da yawa sun faru marasa daɗi harma da masu daɗin ta wani fannin. Sai dai rinjayen marasa daɗin ya danne masu daɗin ta yanda har idanu basa ganinsu. Misalta kalar tashin hankalin da su Mammah suka shiga a wancan lokacin ɓata baki ne. Babu irin shigi da ficin da Imran baiyi ba amma ko damar ganin Zak-Shadow an hana musu har na tsawon watanni. Daga baya shima Imran ɗin suka kama shi.
      A farko manyan sojoji da yawa sun tsaya akan case ɗin da son ganin abubuwa sun dai-daita Zak-Shadow da Imran sun fito, sai dai daga baya sai suka fara janye jikinsu baya aka bar General Yusuf kawai da gwagwarmaya. Dan har cikin ransa ƙauna ɗaya tak yake ma Zak-Shadow da Imran. Faɗi tashin COAS yasa aka fara shirin miƙa case ɗin kotu, a lokacin Zak-Shadow nada watanni tara a rufe, kuma har lokacin ba'a taɓa barin kowa ya gansa ba sai masu tsaronsa sai shi COAS ɗin kawai.
       Kasancewar al'amarin shiri ne na musamman da kowa ya rasa bakin zarensa a zaman farko na kotun aka yanke hukunci. Sun yanke ma Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi hukunci zaman gidan yari na shekara ashirin da biyar, shi kuma Imran Abbas shekara biyar. Ya rabbi wannan al'amari ba zuri'ar Mammah da gidan su Imran kawai ya girgiza ba, ƙasa gaba ɗaya ce ta girgiza, dan a take matasa masu kishin ƙasa da wasu kungiyoyi suka fara zanga-zangar lumana akan basu amince da hukuncin da aka yankema Zak-Shadow da Imran ba. Wannan zanga-zanga taso kawo hargitsi daga baya, hargitsin kuma ba kowa ne ya haddasa shi ba sai ƙungiyar duhu da suka fuskanci ana neman warware musu nasararsu. An saka matakan tsaro masu tsauri daya tilasta matasan komawa gida aka koma ka-ce-na-ce a media kawai, tare da addu'ar neman ɗauki ga UBANGIJI, Sai gargaɗi ga ƴan siyasa akan ALLAH ya kaimu zaɓe na gaba, dan duk mai hankali ya kalli abinda ya farun da idon basira yasan lallai hukuncin nan na siyasa ne kawai...

      A ɓangaren Mammah ba'a magana. A wannan karon duk dauriyarta da iya danne abu sai da ta kwanta jiyya, kusan watanta biyu kafin ALLAH ya bata lafiya, sai dai ciwon hawan jini ya riga yayi tasiri a gareta. Hakama ƙannensa da sukafi kowa ɗaga hankalinsu, sai da takai har su Ma'aruff suka ce sun fasa aurensu da ake gaf da yi, amma Mammah tace bata yarda ba bata amince ba. Dan haka tana samun lafiya aka hau shirye-shiryen bikinsu, dama gininsu tun kafin a kama Imran ya dawo da shi anan cikin gidan, bayan an kama shi kuma Uncle Nasiru ya tsaya akai aka cigaba bisa shawarar Mammah. Satin Mammah ɗaya da baro asibiti, da yay daidai da sati biyu ciff da yankema su Dada hukunci akai bikin Ma'aruff da Ja'afar, sai dai bikin baiyi wani armashi ba, dan aure kawai aka ɗaura amare suka tare. Idan ka cire yara irinsu Nimrah dake shagalinsu kowa ƙarfin hali kawai yake, har dai akai aka tashi lafiya...

     Kasancewar ba wani taro akai sosai ba gidan shiru babu hayaniya, su Gwaggo Khadijah ne dama kawai sai wasu tsiraru daga mutanen Kano suka zo. Tun bayan sallar isha'i aka maida amare sashensu, dan tunda aka kawosu anan sashen Mammah aka ajiye su sai yau da biki ya tashi. Ganin har ƙarfe goma babu Ma'aruff babu Ja'afar Mammah tai kiran Bilal tana tambayarsa su.
        Amsa ya bata da, “Mammah gasu nan fa a ɗakinsu. Da alama kuma basu da niyyar tafiya sashensu. Wanka ma da ƙyar na samu sukayi suka canja kaya”.
         Murmurshi Mammah tayi tana ɗan girgiza kai cikin danne damuwa, “Kaga basu wayar”.
    Da to ya amsa mata, yana nufar ɗakin su Yaya Ma'aruff ɗin dake jikin nasu shi da Ammar. Sai da yay knocking ƙofar suka bashi izinin shiga sannan ya shiga da sallama. Mammah dake saurarensa tace, “Saka wayar a amsa kuwwa”.
      Sakawar yay kamar yanda ta bashi umarni, ya sanar mata ya saka. Kai tsaye ta furta, “Ma'aruff! Ja'afar!”.
      A tare suka amsa mata, dan suna zaune ne a bakin gado su duka, “Yanzu kuna ganin abinda kuke shirin yi dai-dai ne kenan?. Karku manta yanzu suna da hakki a kanku, ɗaya kuka tauye sai ALLAH ya tambaye ku. Abinda kukeyi bashi zai dawo da Imran da Muhammad cikinmu ba, miyasa bazamu karɓi ƙaddara muyi haƙuri bane. Addu'a itace maganin komai. Dan haka ina baku umarnin tashi ku wuce Bilal da Ammar su raka ku sai da safe...”
        Ma'aruff da idonsa ya kaɗe murya a cinkushe ya ce, “Amma Mammah.....”
     “Bana son jin komai, ku tashi ku wuce kawai. Bilal kaje kai da Ammar ku rakasu.”
     “To Mammah”.
Bilal ya amsa yana share hawayen da suka cika masa ido. Dan Ja'afar ma kuka yake. Haka shima Ma'aruff ɗin gefe ya kauda kansa ya share nashi. Babu abinda ke cizon zukatansu sai tuna yanda suka shirya wannan ranar da ɗokin zuwanta tare da Dadansu da Yaya Imran, amma sai gashi yau anyi komai babu su, kuma suna raye, suna a gari ɗaya amma ƙaddara tai musu shamaki. Ba yanda suka iya dole sukabi umarnin Mammah, dama sunyi wanka, suka shirya cikin kayan barci iri ɗaya dan basa wani buƙatar wasu kaya saɓanin waɗan nan.
     Ammar da gaba ɗaya baida isashiyar lafiya tunda aka yanke hukuncin nan nasu Dada da ƙyar ya iya binsu saboda umarnin Mammah. Ma'aruff shine babba, shi suka fara takawa har falon sashensa daya ƙawatu da kayan more rayuwa, babu abinda ke tashi sai ƙamshin sabbin kaya dana turare da sabon fenti. A ƙofar bedroom ɗin da yake da tabbacin Lailah na ciki yay knocking, bai jira amsarta ba ya buɗe kaɗan ya leƙa. Hangota can a kan katafaren gadon da aka saka mata ya sashi ɗan sauke numfashi, kafin ya buɗe ƙofar gaba ɗaya yana sallama. Bai damu data amsa ba, ya juyo yana kallon su Ja'afar da ke tsaye.
    Nuni yay musu su shigo, dan haka suma duk sukai sallama ya amsa sannan suka shiga. A bakin gadon ya zauna kusa da ita, su kuma suka zauna a sofa ɗin ɗakin su duka. Duk da sun girmeta, matsayin ƙanwa take ma a garesu, dan uwa ɗaya uba ɗaya take da Imran, itace autarsu ma. Amma a tare matsayin matar Yayansu a yau suka fara gaisheta.
     Da sauri ta girgiza kanta tana share hawaye batare data buɗe fuskarta ba. Dan itama dai irin ciwon dake zuciyarsu shine a tata zuciyar. Cikin rawar murya ta gaishesu batare da ta amsa gaisuwar da su sukai mata ba. Dan kai tsaye ta ce, “Yaya ina yininku”.
    Amsa mata sukai da kulawa, kafin Ja'afar yay mata gajeruwar nasiha da addu'a. Shima Bilal yay mata a taƙaice. Ammar dai kasa cewa komai yayi sai addu'a da fatan zaman lafiya. Cikin abinda bai fi mintuna goma ba suka kammala suka fito zuwa sashen Ja'afar...

   A sashen Ja'afar ɗin ma dai shine yay musu jagora har bedroom ɗin Shariffat. Itama dai komai na funichars ɗinta irin na Lailah ne, kala ce kowa wadda yake so aka saka masa. Ga ƙanshin turare na tashi kamar dai sashen Lailah ɗin. Ita kam a kwance suka sameta, sai da Ja'afar ɗin yay sallama sannan ta tashi zaune, fuskarta na lulluɓe itama cikin lifaya. Suna zama ta fara gaishesu. Suka amsa mata da kulawa. Yanzu kam Bilal ne yay mata nasiha ita, Ammar yay addu'a. Anan ma basu wuce mintun goman ba sukai musu sallama suka fito...

       Kamar haɗin baki su Ja'afar na fita a sashen Ma'aruff Lailah ta saki kukan da take riƙewa. Haka ma su Bilal na fita Shariffat ta fashe da kuka. Dan su dukansu auren nan tamkar fami ya zama ga damuwar family's ɗin nan nasu guda uku. Sai dai babu yanda aka iya da ƙaddara. Ma'aruff ya haɗiye abu mai nauyi daya tsaya masa a maƙoshi, tare da matsawa kusa da Lailah ya jawota jikinsa a karo na farko a rayuwarsu ya rungumeta. Sai kawai ta sake sakar masa kukan da yafi na farko. Murmurshi yayi mai ciwo. Kafin ya fara magana cikin ɗacin murya sai dai tana fita da sanyin sauti mai tafiya da lallashi...
         “Yau rana ce ta farin ciki da ɗunbin tarihi a garemu, rana ce da iyayenmu sukaci buri a kanta damu kammu. Sai dai gata ta cika babu waɗanda mukema kallon iyaye na biyu a tare damu. Lailaty ƙaddara batai mana adalci ba, miyasa zata ɓoye mana su a lokacin da mukafi buƙatar su...?”

      “Saboda makirci da zaluncin azzalumai ne Yaya Man. Kuma bazamu yafe musu ba..”
     “Tabbas bazamu yafe musu ba Lailaty, za kuma mu cigaba da gayama UBANGIJI kukanmu da kai ƙararsu gareshi. Dan sun cutar damu.” hawayen da yake riƙewa suka shiga gangarowa suna sauka akan kafaɗarta. Da sauri ta ɗago tana kallonsa a karo na farko, sai ya kauda kai gefe yana murmurshi. “Bafa kuka nake ba, abu ne ya faɗa min a idona”.
       Hannunta mai ɗauke da lallen da daƙyar suka yarda akai musu ita da Shariffa takai saman kyakkyawar fuskarsa mai kama data Ja'afar matuƙa, dan kamanninsu na saka mutane da yawa yarda su Twins ne. Fuskar ta maido saitin tata dan tabbatar da abinda ta gani, sai dai suna haɗa idon ya ɗaga mata gira kaɗan, cikin son kauda mata zargin dama yanayin nasu ya matsar da fuskar sosai gab da tata. Ƙoƙarin komawa baya tayi yay saurin riƙota ya hana hakan, nan ma tai ƙoƙarin kife kanta a kafaɗar tasa ya sake hanawa ta hanyar riƙo fuskar da duka hannayensa biyu, a bazata taji lips ɗinsa kan nata. Sai kawai jikinta ya kama rawa ta daburce, dan abunda batai zato ko tsammani bane daga garesa. Tun tana mutsu-mutsu harta nutsu dan tuni ya mannata da fuskar gadon dole ta sallama.
     Sai da ya tabbatar ya tabbatar mata da wannan ranar da sun zama ɗaya ta hanyar sumbatarta yanda ya dace kafin ya haƙura. Gaba ɗaya kunya ta sanyata naɗewa a jikinsa tama kasa tashi. Shi ko murmushi kawai yake yana shafa bayanta. Yo banda ALLAH ya rage ma aya zaƙi ai wannan ranar tanadin da sukai mata shi da Ja'afar ɗinsa ba'a magana. Amma ina ƙaddara tace musu bata yarda ba, sai dai kawai ayi wani abun dan sauke haƙƙi da rahamar UBANGIJI mai sassauta zukatan bayi da ikonsa..........✍️

_Alhamdullahi barkanmu da dawowa a littafi na biyu. Duk da dai na barku da jira, Amin afuwa uzuri ne yasa aka samu dogon hutun. Ina fatan kuna cikin ƙoshin lafiya kuma bakuyi fushi ba 😘. Kar ku damu faka-faka ne in dai naga kuna so kuma. Dan in babu kwarin gwiwa daga gareku rubutun bazaiyi gudu ba kamar yanda muke fata. Karna cikaku da surutu kumuje zuwa kawai dan book 2 ɗin nan hummmm ba'a mana, in sha ALLAHU sai ya tashi kanku fiye da yanda kuke tsammani, na tattaro muku tari-tarin abubuwa a cikinsa da sai kun karanta kawai zaku gane abinda nake nufi 😘😘😘💃._
KIDA A RUWA 2

2...
..........Da ƙyar ya lallaɓata ta tashi tayo alwala, shima yayi suka gabatar da salla tare da addu'oi masu tsaho da rabinsu duk akan Yaya Imran da Dada ta ƙare. Bayan sun kammala ya riƙe hannunta, murya a sanyaye ya ce, “Yanzu ya za'ayi kenan?, ango na shigowa da kaza ni da Twiny na mun shigo hannu rabbana. Ina fatan aminan juna zasu yafe mana, amma in sha ALLAHU zamu biya wannan bashin ranar da kuka haifo mana Haysam da Imran”.
         Murmurshi tayi tana mai sinne kanta saboda kunya. Shima sai ya sake murmusawa yana mai jawota jikinsa ya rungume gaba ɗaya yana sanya mata albarka. Cike da jin kunya tana naɗe a jikin nasa ta amsa da, “Amin na gode. In dai kaza ce mun yafe muku. Dan ko ma kun kawo bazamu ci ba”.
       “Oh baki kuka haɗa kenan?”.
   “A'a fa”.
“Faɗi gaskiya dai Lailaty, dan gara mu sani, musan yanda zamu tafiyar da rayuwar aminan juna kada wata ran a haɗe mana kai a tare”.
       Ƴar ƙaramar dariya tayi tana mai yunƙurawa zata bar jikinsa. Sai shima ya miƙe yana murmurshin da kamata ya ɗaga cak ya ƙarasa da ita zuwa gaban gadon. Zata janye ya hana hakan, sai ma ƙoƙarin warware lafaya ɗin jikinta da yake yi. Ba yanda ya iya kuma dole ta bashi dama yayi yanda yake so. Daga ƙarshe ya rikice mata dan rigace doguwa a ciki mai mannewa a jiki data fidda komai na halittar da UBANGIJI yayi mata masha ALLAH. Ita ko duk ta daburce saboda kunya, ƙoƙarin ganin ta ja lafayar ma ta fara dan rufe jikin nata. Amma ya hana hakan ta hanyar riƙe hannun nata yana shinshinar wuyanta dake fidda wani ƙamshi na musamman daga shiryayyun turarrukan SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387 na musamman da aka shirya musu, dan hatta kayan gyaran jikin da akai musu duk daga gare ta ne. Abinka da tuzurun ango ji yay komai ya ƙwace masa. Tuni ya manta da batun bazasu iya taɓa amaren nasu ba anan kusa kamar yanda suke ayyanawa a zukatansu. Su kansu su Lailah sun sakankance angunan nasu zasu barsu sai nan gaba kodan halin da ake ciki, amma sai ga saɓanin haka, dan jikin Ma'aruff har rawa yake ya ɗagata cak zuwa gadon bayan ya sake manne lips ɗinsu tamkar ɗazun.....

     ★Banbancin da aka samu tsakanin Ja'afar da Ma'aruff shine, shi da farko lallashin tashi gimbiyar Shariffa kawai yayi a farko. Ya mata nasiha akan muhimmancin haƙuri duk da shima nasihar kamar yana yinta ne harda kansa. Hannu yasa ya share mata hawayen da suka jiƙe fuskarta sannan ya kamata ya miƙar shima yana miƙewa. Kusancinsu ya sakata jin kunya sosai ta kasa daurewa ta duƙar da kanta tana kallon ƙafafunsu. Amma sai ya saka hannu ya ɗago fuskar tata ta hanyar kamo haɓarta. Cike da raɗa ya furta,
         “Sherry kalleni mana”.
    Kanta ta girgiza alamar a'a.
  Ya sake ƙanƙance murya da matsar da fuskar tasa gab da tata ya ce, “Why?”.
      “Ina jin kunya Yaya J”.
   Ta bashi amsa hawayen da take riƙewa na silalowa a saman kyakkyawar fuskarta”.
       A hankali ya haɗiye abinda ya tokare nasa maƙoshin, kafin ya sake matsota jikinsa da ƙyau ya rungumeta. Murya a shaƙe irin ta mai damuwa ya ce, “Kina son nima na miki kukan?”.
      Kanta ta girgiza masa alamar a'a tana jan shashsheka. Ya fara ɗan buga bayanta kaɗan-kaɗan alamar lallashi, sannan ya cigaba da faɗin, “Kiyi haƙuri, ko nace muyi haƙuri. Haka ALLAH ya tsara komai bamu isa canjawa ba. Ki ƙarfafa ni Sherry dan nima gab nake da faɗuwa. Ina jin tamkar bamuyima Dada da Yaya Imran adalci ba a wannan ranar. Kamar mun fifita buƙatarmu akan halin da suke ciki. Kwanaki goma sha huɗu kacal da yanke musu hukuncin zalunci da bamu da tabbacin kuɓutarsu an ɗaura mana aure. Miyasa su Mammah suka kasa fahimta ne?”.
      Kuka mai raɗaɗi Shariffat ta saki, dan kalamansa na fita tamkar yana karanta abinda ke cikin zuciyarta ne. Ita ƙanwar Aunty Hafsat ce, kuma cousin's suke da su Imran, hasalima a gidan su Imran aka riƙesu su biyar ciff sakamakon rasuwar mahaifinsu tun ita bata wuce shekara tara a duniya ba. Yanda su Ja'afar ke ɗaukar Imran Yayansu jininsu haka suma suke kallon Dada a garesu. Da ƙyar Ja'afar ya share nashi hawayen, ya fara lallashinta da daɗaɗan kalamai. Sannan ya kama hannunta zuwa bayi sukai alwala.

Sun gabatar da salla da addu'oin da suma a nasu ɓangaren mafi rinjaye suka tafi akan Imran da Dada. Shine ya fara miƙewa, ya je wadrobe ya ɗauka mata kayan barci ya dawo inda take. Kamata yay ya miƙar yana faɗin, “Kukan ya isa haka, canja kaya dare na ƙara yi, ga kaina na ciwo ina son na kwanta”.
     Hawayenta ta share, ta amshi kayan ta nufi hanyar bayi. Bai hanata ba ya kai zaune bakin gado. Da gaske kansa ciwo yake kamar zai faɗi, dan haka ya kai kwance kawai yana rage fitilar ɗakin. Fin mintuna goma sannan ta fito, idanunsa a lumshe dan motsinta kawai yake ji. Sai dai jin shiru babu alamar ta ƙaraso wajen gadon ya sashi buɗe idanun a hankali. A mamakinsa can ya hangota kan sofa ta kwanta. Ya ɗan murmusa da buɗe baki a hankali cikin murya mai taushi ya kira yi sunanta..
       “Sherry!”.
    Amsawa tai a ƙasan maƙoshi, sakamakon kuka daya disar mata da murya.
     “Mi kike yi anan?”.
  Tana faman cuɗa hannayenta a waje guda ta ce, “Zan kwanta ne”.
     “Kuma anan?”.
Kanta ta jinjina masa.
Sai ya ɗan girgiza kai yana wani murmushin. Cike da lallashi ya ce, “Toyi haƙuri ki dawo nan. In dai nine babu abinda zai faru barci kawai zamuyi. Zoma kimin addu'a kaina ciwo yake sosai”.
     Ciwon kai daya ambata ya sata tashi ba musu ta nufesa. Sai dai sai faman gyaran wuyan riga take duk da mai ƙwala ne bai kuma mata yawa ba. Hasalima kayan wando da riga ne sun mata burun-burun. Hannun daya miƙa mata alamar tazo ta side ɗin da yake ya sata nufar can. Zata zauna a side drawer ya riƙo hannunta dole ta zauna a bakin gadon kusa da shi har jikinsu na gogar na juna. A haka ya ɗaura hannunta saman goshinsa da sanyin sa ya sashi sakin ajiyar zuciya. Ita kuma ɗumin goshin ya ratsata. Baiyi magana ba itama batace komai ba ta fara masa addu'ar ciwon kai tana tofa masa da shafawa. Fin mintuna biyar ta kammala, tana masa sannu zata miƙe ya hanata, zatai magana ya ce, “Shiiii!” yana kamota gaba ɗayanta a haka ya hawo da ita gadon, maimakon ya barta ta kwanta a gefensa sai ya barta a jikinsa a haka yaja musu bargo dan akwai ɗan sanyi-sanyi.
     Ina ƙasa Shariffa ta shige ko zata huta da kunyarsa. Ga zuciyarta nata bugawar tsoron da har yana iya ji. Har cikin rai bata tunanin wani abu zai faru, a ganinta halin da suke ciki akan su Dada ai basu da lokacin wani abu kuma a yanzu. Amma mi a bazata taji saukar hancinsa akan wuyanta yana bin ƙamshin turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Da aka zazzage musu kala-kala a jikin. Ga wanda akai musu gyaran jiki. Ga kabasa da akai musu turaren kaya. Ga khumra kusan kala uku da aka basu suka shafa, gana man gashi, ga oils. Hatta ƙanshin sashen duk turaren wutar SHUWA INCENSE AND MORE ne. Al'amarin kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba, dan tana tunani kawai sai jin saukar lips ɗinsa tayi a cikin bakinta. Kafin tayi wani yunƙuri ya sake matseta yana yanda yaso. Da ƙyar ya iya raba lips ɗinsu yana faɗin, “Sherry wannan wane irin turare ne mai canja tunani da hana gangar jiki zama lafiya ya rabbi.”
      Bai ma bari ta bashi amsa ba ya sake ɗaukar wani sabon salon mai gigitarwa, ai duk yanda yaso control ɗin kansa da batun damuwa da barinta ba yanzu ba shima a nashi ɓangaren lissafin ya canja gaba ɗaya. Dan kuwa dai mai afkuwa ta afku ya bar Sherry ɗin tasa da kuka da magiyar neman ceto. Sai dai a wannan gaɓar babu mai jinta balle ya kawo taimakon, kamar yanda babu mai jin kukan aminiyarta Lailatyn ya Ma'aruff dake can itama tana amsar sakamakon nata ƙamshin turaren.

     Masu karatu sai ku gayama Maman Abdull kayanta sun haɗa yaƙin ƙasa da ƙasa. Tai maza ta kawo ɗaukin ruwan zafi inba haka ba mu tattaro mumu zuwa gidanta a bamu rabonmu. Koda yake nifa na riga na kama nawa rabon mutanena. Kuma ku garzaya ku amshi naku dan wlhy turarrukan nan ba ƙarya, ni shaida ce a kansu ƙwarai da gaske. Ba amare kawai ba har uwargida kina buƙatarsu kodan faranta ranki da ƙamshi, balle ma idan oga yaji shima fa zai iya rikiɗewa zuwa Yaya Ma'aruff da Yaya Ja'afar. SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Suna da turare wuta da khumra kaloli har uku: black humra, white humra, brown humra.

Akwai oil perfume da kullacham da genine da Turare kabasa kaloli uku shima. white, black, and brown. Akwai man kitso, da kayan gyaran jiki masu gyara fata da sanyata laushi da santsi kiyita glowing abinki hajjaju.
Kar ku bari a yi babu ku, tana aika kaya a duk inda kake har wajen Nigeria makwaftanmu. Ga arha ga mutunta customers abin sai wanda ya gani. SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Tabbaci ne na haƙiƙa daga ni Bilyn Abdull dan na gwada na tabbatar😘😘💃.

Washe gari sai ga angunan da aka kora tsitt kake ji, suna can suna aikin lallashi da sanya albarka. Dan kuwa suma dai sun isa duniya mai tsada da sai ɗan gata ɗan ƙwarai ke zuwanta har ya zame masa tarihi a ranar farko. Babu abinda zasuce da UBANGIJI sai godiya. Tare da addu'a da fatan ALLAH ya fito musu da su Dada anan kusa dan farin cikinsu ya

Please Login or Register in order to submit comment