Reading KIDA A RUWA BOOK2 COMPLETE BY BILLYN ABDUL Chapter 21 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

   A motar tsakiya da Daddy Imran ya ƙarɓi tuƙin Dada ne a gefensa. A baya Mammah da ƴan gatanta Ruky da Nimrah sun sakata a tsakkiya. A binda zai baka mamaki kamar basu ba bakin surutun nan ya mutu murus. Dan har Daddy Imran ya kasa haƙuri sai da yay magana..
          “Mammah wai yau bakunan kafi autanki sun mutu ne? Na jisu tsitt kamar basa a motar nan”.
     Murmurshi Mammah tayi da ɗan kallon Nimrah da Ruƙayyan da suka lafe a jikinta. Dan gara ma Ruky wayar Mu'azz ce a hannunta tana kallon hotunan da sukai a airport ɗin. Nimrah kam idanunta a rufe suke da alama tayi zurfi a tunani. Ba kuma tunanin kowa bane face na wannan baƙo nasu da Uncle Ammar ya faɗa musu shine Dadan da suke ji ana faɗa tun tasowarsu. Duk da fuskarsa ta canja daga waccan fuskar data gani a video. Waccan fuskar da babu gashin saje sam, sai dai kuma sajen ne kawai ya bambanta ta da wannan fuskar ta yanzu da itama babu yawan murmushi, babu sakewa, babu filin kai wargi. Sai tsabar kwarjini, kamala, hasken ibada, kamewa da tarin cikar haiba irin ta masu tantsar riƙe girma. Tabbas a wannan gaɓar ta shiga ruɗani mai tsanani akan wannan fuskar da zuciyarta ta kasa yankema hukuncin daya dace. Jitai hotunan bidiyon na son dawowa. Sautin muryoyin da ke zargi na so sake yi mata amsa kuwwa.....
     Tunaninta ne ya katse saboda girgizatan da Mammah tayi. “Nimrah mi kike tunani haka?”.
    Mammah ta faɗa tana kafeta da idanu. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta saki tana girgizama Mammah kai da faɗin, “Mammah ba komai”.
        “Karya take yi wlhy Mammah, gaba ɗaya yanzu haka ta koma, haka kawai sai kiga ta shiga tunani bare ma idan muna ɗaki mu kaɗai, a gaban ku ne batayi”. Ruky ce mai maganar tana hararar Nimrah. Itama ramawa tayi, sai dai batace komai ba. Sai Daddy Imran ne ya ce, “Nima dai naso lura da haka, duk tayi sanyi babu kuzari. Daughter mike faruwa? Ko baki da lafiya ne?”.
      Idanun Nimrah suka ɗan ciki da hawaye, muryarta na ɗan shigewa ciki ta ce, “ALLAH ba komai Daddy sharri take mun. Kuma lafiyata ƙalau” sai ga hawaye sharr. Mammah da taji hankalinta ya tashi ta kamota jikinta, dan ita kanta a tsakanin nan tana lura da Nimrah ta ɗan rage kauɗi, sai take tunanin ko exam ɗin da suka fara ce a makaranta. Itama dai Ruky idonta har ya tara ƙwalla. Ta riƙo hannun Nimrah cikin nata tana faɗin, “Dan nace haka kike kuka, to kiyi haƙuri bazan ƙara ba”.
       Cikin ɗan tura baki Nimrah dake kwance jikin Mammah ta ce, “Nifa ba dan kinyi magana bane ba, kawai kaina ke ciwo”.
      Sannu Mammah da Ruky suka shiga jera mata. Daddy Imran kam ya saki murmushi da faɗin, “Mammah kina fama.”
       Duk abinda suke Dada na jinsu. Amma ko motsawa daga yanda yake zaune bayansa kwance jikin kujera ya lumshe idanunsa baiyi ba. Zama ka rantse barci yake a hakan...
     Dai-dai nan jerarrun motocin dake tafe da tawagar jami'an tsaro suka iso cikin anguwar. Tsakiyar KOBI STREET. Dai-dai gate ɗin gidan zuri'ar Abdul-rasheed Shehu Isa Kobi da yasa mutane fara farga da abinda ke faruwa. Dan kuwa duk da akwai jami'an tsaro a tare da su hakan bai hana wasu biyosu ba tun daga airport dan samun labari duk da su ɗin ba ƴan jarida bane, amma ganin Imran da yaso fargar da masu wayo yasa suka tsargu shiyyasa suka biyo su dan tabbatarwa, da alama kuma zasu samu abinda suke so ɗin musamman ganin inda motocin suke ƙoƙarin shiga.
       Maigadi kansa ya girgiza da abinda ya gani, balle su Malam Buba dan su Mammah basu fita da driver ko ɗaya ba daga gida duk su Ammar ne suka ja motocin sanda zasu fita. Yanzu kam wasu motocin ma sai sojojin nan ne suka dawo da su dan har suka iso gida hawaye wasun su sun kasa tsayawa. Sai da gaba ɗaya motocin suka gama shigowa kafin kowa ya fara ƙoƙarin fita.
Su maigadi dai sunyi tsuru-tsuru suna kallon ikon ALLAH. Kusan motar su Mammah ce ƙarshen buɗewa, Nimrah da Ruky suka fara fita, kafin itama Mammah ta fito hankalinta duk akan Nimrah datai mata wani kalar tausayi. Riƙota tai tana kai hannu a goshinta,
        “Ciwon kan ne?”.
   Nimrah ta ɗan girgiza kai tana Kama hannun Ruky da itama ta zagayo inda suke cike da damuwar yanayin twiny ɗinta. Dai-dai nan aka buɗe ƙofor ɓangaren da Dada yake, a nutse ya fara sauke ƙafafunsa dake sanye cikin baƙin takalmi Boot mai ɗan tsaho. Kafin bayyanar baƙin wandonsa zuwa shafaffen cikinsa dake kwance cikin bakar t-shirt ɗin jikinsa kasancewar yayi zanzaro ne. Daga maigadi har Driver suka ɗan zuba masa ido daga can inda suke tsaye tamkar an basu aikin yin hakan ne. Har sai da ya kammala tsayawa cak akan ƙafafunsa sannan suka ɗaga idanun nasu a hankali zuwa kan fuskarsa dake sakaye cikin norse mask da p-cap.
       Shi kam da bai san sunayi ba, sai ma a bazata juyayyun idanunsa suka sauka akan Nimrah da Mammah kema magana ƙasa-ƙasa tana tattaɓa mata kai, anyi sa'a itama ta ɗago nata zata harari Mu'azz daya ƙaraso wajen yana tsokanarta wai tana ma Mammah shagwaɓa, ai ko sai idanun Dada cikin natan. cikin sauri ta janye dan har tsakkiyar ƙwalwa taji kaifinsu da tasirinsu ya riski tsakiyar zuciyarta.
     Shi kam baima nuna yasan mi akai ba ya maida idanun nasa ga kallon gidan cike da mazewa.......


       °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°     
       
     ★Gaba ɗaya tambayoyin zuciya sun gagara ƙarewa a zukatan su Maigadi dama jami'an sojan da aka bari gidan, dan suma dai har yanzu basu san wanene ba balle abinda ke faruwa. Sai dai duk sun sha jinin jikinsu. Amma a ɓangaren mutane biyu da suka san Dada tun a baya sun shaida tabbas shi ne ba saƙo ba ba kuma mafarki ba duk da yaƙi buɗe fuska. Dan haka suka kasance a firgice fiye da sauran. Saboda ɗimuwa ce ta gaske ta samesu da ruɗani na bazata. Tambayar kawunansu kawai suke ta yaya hakan zata kasance? Dan tabbas wanda akace an fitar a prison kwanaki biyar kacal da suka shuɗe ba zaiyi kama da hakan ba sam a idanun mai kallo. Yafi kama da jarumin dake rayuwa a ni'imtaccen muhalli da kwanciyar hankali da nutsuwar rayuwa. Da alama ana raina musu hankali ne ko wani abu daban gaskiya......

<<%>><<%>><<%>>
       
     Gab da magriba Daddy Imran ya bar gidan. Su Aunty Ummi kam har akai isha'i suna nan abinsu suna hidima da Dada. Dan abubuwan da aka shirya masa harma ya rasa mizai ci a ciki.
       Abin zai baka mamaki yanda gidan ya nutsu babu hayaniya duk da yaran dake cike da shi. Amma kowa ya nutsu waje guda alamar wargi ma waje yake samu. Duk da kuwa baƙon idon daya saka su nutsuwar ko harara baima kowa ba. Hasalima cike da so da ƙauna ya dinga rungumesu lokacin da ake gabatar masa da kowa da sunayensu. Dan Mammah bata rage kowa ba hatta ƴaƴan Uncle Tasi'u ya masa bayanin su a taƙaice, sai dai komai baice akan su ba. Ga shi macen ta mugu-mugun jin mutuwa akansa. Dan a cewarta bata taɓa ganin namijin daya daki zuciyarta a kallon farko irin Dadan ba, wanda ita kanta ta tabbatar ko cikakken kallo ɗaya bai mata ba. Lokacin da akai masa rakiya ɗakinsa da aka zubama kaya jiya jitai tamkar tayi tsuntsuwa ta bishi, sai dai babu dama...

      Duk wannan bidirin da ake babu Nimrah a falon, dan tunda suka shigo tai wucewarta ɗakinsu. Kayan jikinta da gaba ɗaya ƙamshin turaren Dada ya gauraye ta cire, jin ƙamshin yaƙi barin har jikinta dole tai wanka kafin al'awalar la'adar. Koda ta fito tai sallar sai ta haye gado ta kwanta dan wani ma ɗan zazzaɓi take ji. Lokacin da za'aci abinci bayan dawowar mazan sallar la'asar Mammah taga babu ita ta fara jajenta. Dan haka ta aika a duba mata ita. Nusaiba da tazo kiranta ta sameta kwance, sai tai tunanin barci take, dan haka ta koma tace tana barci. Mammah datai tunanin ko ciwon kan ne tace a barta tayi barcin...
Nimrah da sarai tana jin sanda Nusaiba ta shigo tun tana juye-jiye da tunane-tunane har barcin gaskiya ya ɗauketa, daga nan kuma zazzaɓin na gaske ya rufeta. Gab da magriba Mammah ta shigo ɗakin da kanta, anan taji jikin nata da zafi. Babu ɓata lokaci ta saka Biebah ta haɗo mata abinci da magani, tashinta Mammah tayi, da ƙyar kuwa ta yarda taci abincin kaɗan tasha maganin, sai ga amai. Aman ne ya sata galabaita dole aka kira doctor ya dubata. Tunda ya dubata yay mata allura ta sake komawa barci shine bata farka ba sai kusan tara saura.
       Lokacin su Aunty Mommy da Mammah ta kora gida akan dole duk suka shigo suka sake dubata suka wuce. Sai kuma gobe idan ALLAH ya kaimu, dan Mammah ta tabbatar weekend ɗin nan kaf a gidan zasu yi shi. Yo sukai yawo mara dalili ma balle wannan mai dalili ya samu. Ruky na ɗakin Nimrah ta farka, cike da farin ciki tai kanta, dan tun da Nimrah tai amai aka kira doctor itama ta koma kalar tausayi, abokiyar rayuwa ba lafiya ba nutsuwa. Ita ta shiga hidima da ita sai kuma ga Biebah ta samesu, dan ta baro ɗakinta ne tana mitar takura mata da zaman Hanoon yayi, yarinyar ta cika iyayi da feleƙe, ko jiya dauriya kawai tayi da ƴar kunyar baƙunta ga Hanoon ɗin, amma harga ALLAH yau ji take bazata iya ba. Itama ganin Nimrah ta farka sai ta sakin batun Hanoon ta nufesu da farin ciki tana mata sannu..........✍️

54


.......Afalo kam su Kulu ne ke faman tsaftacesa, dan harsu Ja'afar Mammah ta kora sashensu. Tace kowa yaje ya huta a barma gobe kuma idan ALLAH ya kaimu. Kodan su Lailah dake fama da kansu, musamman ma Shariffa data tsufa da yawa. Badan sun so ba suka wuce, dan Dadan ma tuni yana ɗakinsa dan ya samu ya huta da wannan hayaniyar.
      Tamkar ba dare ba su Kulu suka gama gyaran ko'ina suka saka ƙamshi. Sai falon ya ƙara zama cikin nutsuwa.  Shayin Mammah na ƙa'ida Kulu ta ɗauka takai mata ɗaki, ta sameta zaune tana karatun Alkur'ani, dan haka ta ajiye sannan tai mata sallama dan zasu wuce suma su kwanta yau sun sha aiki, dan ma su Aunty Mimi basu barsu su kaɗai ba sun tayasu. Kai kawai Mammah ta ɗaga mata, ta cigaba da karatunta. Itama sai ta fice tana jin ƙaunar wannan baiwa har ƙasan zuciyarta. Duk da basu san miya faru da Dada ba, yanda ƴan gidan basa gajiya da hirarsa sun san yau suna cikin matsanancin farin ciki da dawowar tasa. Dan ko su yau da ganinsu na farko da shi sun tabbatar lallai shine zakin gidan, sannan garkuwa mai ɗaukar matsayin uba... 

     ✨✨✨✨✨✨✨

    Tunda ya shigo ɗakin da komai na cikinsa ya tabbatar sabo ne ya tsaya shiru yana kallon komai daki-daki. An shirya komai fiye da yanda yake buƙata. Ga ƙamshi mai ƙarama zuciya butsuwa na tashi. A hankali ya kai zaune cikin sofar ɗakin, cikin yanayin zamansa na ƙasaita da girma ya kwantar da kansa tare da lumshe idanunsa dake nuna matuƙar gajiya. A karo na farko tunanin da yaketa dannewa ya shiga dawo masa cikin kai. Yaga kowa daga zuri'arsa harma da wanda aka haifa baya nan amma babu Nabeeha. Ina ta shiga? Tunda yabar gidan ne itama bata nan? Ko tayi tafiya ne tunda babu wanda yasan da dawowar sa. Maimakon samun waɗan nan amsoshin sabuwar hoton fuska ya gitta masa a brain, ba kowa bace sai Nimrah. Yarinyar da ya bari tana shekara bakwai… yanzu ta zama mace, cikin tsabta, nutsuwa, da wani yanayi mai ban mamaki. Damuwar da ya karanta a tattare da ita tazo masa a tsakkiyar tunani, sai kuma sanda yake magana da Imran Bilal ya shigo da wani, wanin da yaji sun kira doctor wai zai dubata bata da lafiya. Baiyi magana ba a lokacin sai Imran ma ya tashi yabi Bilal ɗin, yana gurin kuma har Imran ɗin ya dawo, shi kuma bai tambayi abinda ya faru ba, Imran ɗin kuma yaƙi faɗa masa komai suka cigaba da maganarsu. Ji yake acan wani sashe na zuciyarsa kamar ya kamata yasan mike damunta. Koba komai ita ɗin AMANARSA ce ai...
      Idanunsa ya buɗe tare da ture tunane-tunanen ya miƙe. Kai tsaye ƙofar da yake tsammanin ta bathroom ce ya nufa, dan gwara yaje yay wanka ko zai samu nutsuwa daga waɗan nan shirmen tunanin nasa...

       Ƙarfe goma dai-dai ya kammala kimtsawa cikin kaya marasa nauyi daga akwatin kayan da sukazo da shi daga Germany. Ya saka turare kaɗan. Maimakon kwanciya sai ya nufi hanyar fita, dan yaji hira da Mammah kawai yake buƙatar yi. Bai san suwaye da waye a upstairs ɗin ba. Bai kuma yi tunanin leƙa kowane ɗaki ba ya sauka ƙasa. Tunkan ya gama sauka a stairscase ɗin ya fahimci babu kowa a falon. Dan hatta fitilu sa ma an kashe. Ƙaramin murmushi iya lips ya kufce masa, dan yasan aikin Mammah ne wannan, in ba haka ba yaran nan zasu iya kwana suna hira basu gaji ba balle tunawa da gidajen auren su. 
          
       Ƙofofi huɗu na corridor ɗin daya tabbatar bedroom ɗin Mammah na cikinsu ya zubama ido, bai san wanne ne ɗakin ba, amma yana ƙyautata zaton na farko ne. Duk da haka sai da yay kusan sakan biyu kafin yay knocking ƙofar.
     Daga ciki Mammah dake ƙoƙarin rufe Alkur'ani ta juya tana kallon ƙofar, sai kuma ta furta, “Waye? Shigo”.
        “Uhhmm”.
   Ya faɗa cikin maƙoshi tare da   murza handle ɗin ƙofar. Cikin takunsa na nutsuwa da ƙasaita ya tura ƙofar ya shiga da sallama mai cike da girmamawa.. A jiyar zuciya mai nauyi Mammah ta sauke da jin muryarsa, kafin fuskarta ta washe da murmushi mai sanyi tana mai zuba masa raunanan idannunta. Sai da ya kai zaune kusa da ita, sannan ya furta, “My Sweet Mammah”.
         Murmurshi Mammah ya ƙara ƙawatuwa, jin komai take tamkar a mafarkin data saba. Cike da jin nutsuwar zuciya na tuna zahiri ne ba mafarki ba ta furta, “Na zata yanzu kamayi nisa a barci Muhammad”.
       “Mammah na kasa barcin ne, shiyyasa na taho kawai muyi hirarmu mu more, hira ta zahiri ba wadda nake gani a mafarkina ba. Ina yaran naki? Naji gidan shiru tun 10”.
          “Duk na kora kowa makwanci, su kuma iyayen dabar gida, dan in aka biye musu nan zasuce zasu kwana ma”.
      Ya ɗan murmusa. “Har yanzu basu canja hali ba kenan?”.
        “Cabjawar tasu ɗin nan ai babu rana, ƙila to in kun fara aurar da ƴaƴa.”
     Yanzun ma murmushin ya sake yi. Itama Mammah shayin data zuba masa ta ajiye gabansa tana nata murmushin. Daga haka suka cigaba da hira cike da shauƙi da kewa. Gaba ɗaya hirar ta ta'allaƙa ne akan abubuwan da suka faru a lokacin da baya nan. Musamman gyaran gidan nan, albarkar kasuwancin su daya sake haɓaka, auren su Ma'aruff da akasha kicimmili, da yanzu su Bilal da suka dage akan sai randa ya dawo zasuyi nasu. Ganin bai tambayi ina Nabeeha ba ita ta ɗakko masa batunta akan zuwa da safe zata kira Hajiya Hasiba ta sanar musu tunda basu san da dawowar tasa ba.
     Shiru yay kamar bazai ce komai ba akan batun, sai zuwa can har ma ta ɗakko wani sai kuma ya furta,
          “Ba gidan take zaune ba kenan?”.
     Mammah ta ɗanyi murmushi da girgiza kai. “Yanzu dai ya kamata ta dawo ɗin, tunda gaka sai ka bata haƙuri akan laifin da take gani ka mata, in sha ALLAHU a satin nan za'a zuba kaya a sashen naku.”
         Yanzu ma maimakon amsa batun zai bada haƙurin ko zuba kaya a sashen nasu sai kawai cayay, “Zan huta anan sashen dai tukunna Mammah. Yaran can uku kuma kukace yaran Uncle waye?...”
         Mammah tasan sarai ya fahimci wa ake nufi tun a ɗazun, kawai yana son sake ji ne a bakinta. Murmurshi tayi da jinjina halin Muhammad ɗinta da bazai canja ba. Kai tsaye ta maimaita masa sunan Uncle Tasi'u ɗin, ta kuma ɗora da labarin duk yanda suka haɗu a Egypt har kicimillin da aka sha da ƙannensa a watannin baya da yasa Uncle Tasi'un haƙura ya koma kan aikinsa sai jiya kuma yazo da yaran. Ta lissafa masa sunansu. “Babban shine Dayyan, sunan mahaifinku ya saka masa, sai macen Hanoon, ƙaramin Afeef. Nasan halinka Muhammad, sannan nasan halin ƙannenka, in har baka amshi tuban Tasi'u ba suma zasu sake birkicewa ne. Nasan shi mai laifi ne a garemu, amma sanda ya aikata yaransa basu sani ba ma. Sannan shima daya aikata ɗin bai ragemu da komai ba da UBANGIJI ya ƙaddara zamu samu, sai ma ɗaukaka da sanadin hakan ya jawo mana. Tunda gamu a yau cikin rufin asirin ALLAH da yalwarsa da har shima yazo ya raɓemu da zuriarsa zai ci. Dan ALLAH da kaina ina roƙon komai ya wuce kaji”.
        Dada daya zubama Mammah idanu ya ɗan murmusa. Sosai yake jin wannan baiwar ALLAH a zuciyarsa, yana mata wata irin ƙaun mara misali, kyawawan halayyar nan tata ita ke sakashi yin sanyi a wasu lokutan koda ya ɗauki zafi damuwa ta mamayesa. Tabbas wanda ya samu mahaifiya irin Mmamansa ya more, dan uwa ɗaya ce tamkar da dubu. Flaks ɗin shayinta ya ɗauka ya ƙara kawai, batare daya sake cewa komai akan zancen ba. Itama bata sake cewar ba, sai ma ta ɗakko wani batun.
     Sun cigaba da hirarsu har sha ɗaya da wani abu, agogo ta kalla da faɗin ya kamata yaje ya kwanta. Sai ya kalla gadonta dake gyare tsaff yana murmurshi. “Anya Mammah ba gadonki zaki bani na kwana ba, maybe hakan yasa na sake yarda ba mafarki nake ba fa ina tare dake a yau ɗina.”
        Cikin ƴar dariya Mammah dake kallon gadon itama ta ce, “In dai gado ne gashi nan Muhammad kayi kwanciyarka akai”.
          “To Mammah ke fa?”.
     “Ga ɗaki nan ba kowa, dama ɗazu su Mimi sun saka a gyara musu shi na kora su.”
    “A'a Mammah kiyi kwanciyarki a ɗakin ki, zan koma sama na kwanta”.
      “Ai ni nace ka kwanta abinka ko. Bari ma kaga na duba Nimrah ko zazzaɓin nata ya sauka. Dan duk ciwon da kaga ya kwantar da Nimrah da Ruƙayya ba ƙarami bane ba.”
             A karo na farko kan al'amarinta ya furta, “Kina shagwaɓa su ne da yawa Mammah shiyyasa.”
      “Toba dole ba Muhammad, ku yanzu duk kun girma, idan nace wayyo kafin naga wani a cikinku na gansu su huɗun nan. Ga Biebah kam tunda ka dawo gida na tabbatar ta fara mana bankwana kuma.”
            “Ai gara ta tafi nata ɗakin itama haka nan Mammah. Yanzu fa kusan 26 take nema. Damma bata da girman jiki tunda har su Ruƙƙayya na neman taddota naga”.
       “Ruƙayya da Nimrah kam tubarkalla, dan nan da wata shekarar tsaff zasu danne uwar tasu kam. A hakama wai tattalin jiki suke basa son suyi ƙiba.”
      Guntun murmushi Dada yayi da ɗan taɓe baki. Itama Mammah data kammala haɗa duk abinda take buƙata tai masa sallama ta fice. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali. Sai kuma ya miƙe ya hau gadon da bismilah, wani irin sanyi na ratsa masa zuciya da ɓargon jiki. Shifa yanda yake jin kewar Mammah bai ƙi ace ma ya kwanta a kusa da ita ba ko zai samu sassauci....

       Koda Mammah ta fita sai da ta share guntayen hawaye tana murmurshi, kayan nata takai ɗakin kusa da natan sannan ya nufi ɗakin su Nimrah. Har sun kashe fitila alamar sun kwanta, dan haka ta haska da fitilar wayarta tana ƙarasawa. Ganin Biebah a ɗakin ya bata mamaki, sai dai batace komai ba ta tattaɓa jikin Nimrah dake barci, jin zazzaɓin ya sauka yasa ta sauke ajiyar zuciya. Addu'a ta sake musu su duka sannan ta fice. Koda ta koma ɗakin ba kwanciya tayi ba, alwala ma ta ɗauro ta kabbara salla....

      Kusan 12:30 Nimrah ta farka. Bayi ta shiga tayi fitsari, koda ta fito ta koma gadon sai ta kasa barci. Tunane-tunane marasa daɗi suka cika ƙwaƙwalwata. Tun tana turesu da fatan barci ya sake ɗaukarta harta fahimci bafa ɗaukar tata zaiyi ba. Ga kanta har ya fara mata ciwo. Bargon ta yaye tare da sakkowa a gadon ta saka bedroom slippers ɗinta ta fito a ɗakin gaba ɗaya. Gara ta koma ɗakin Mammah ƙila gurɓataccen tunanin nan nata ya barta karma zazzaɓin daya sauka mata ya sake dawowa. A hankali ta murɗa ƙofar ta shiga dan tasan Mammah ta kwanta yanzu, dan tana barcin wuri saboda tashi sallar dare da bata wuceta. Bata damu da ganin ɗakin da duhu ba, dan Mammah bata son kwana da haske koda na lamp ne, shiyyasa suma suka koya. Da lalube ta isa gadon, hankali kwance ta haye, jin mutum data san Mammah ce yasa ta matsa sosai ta shige jikinta tare da gyara bargo da ƙyau........✍️

        Yau fa akeyinta, ke madam Ninah ya da haka?🤣. Gaskiya Dada kana cikin alheri yau ɗin nan🤭, ga tsuntsu daga sama gasashe😂 koya kukace mutane na🥱😜.


55


...........“Baka ganin kayi gaggawa akan fitar da yaron nan kuwa Genaral? Kasan fa ita siyasa shegiyar aba ce a zahirinta da baɗinin ta.”
       Murmushi shugaban ƙasa yayi mai ƙayatarwa, cike da girmamawa irin wadda ake bama oga, duk da ba wani girmarsa yayi sosai ba, amma a siyasa ubangida zai kira shi.
“Ranka ya daɗe a zahiri wasu zasu iya kallon al'amarin a haka. Sai dai idan mukai dubi da gaskiya abinda ya dace ace nayi kenan akan Haysam. Duk wanda yasan shari'ar Haysam a shekara takwas data gabata ya san Shari'a ce ta gaba gaɗi akayi. Dan kuwa an ɓoye muhimman hujjoji da yawa shiyyasa shari'ar ta taƙaita aka rufesa. A yanzu kuma fito da shi zai taka rawar gani mai yawa dana tabbatar kowa zai ji daɗinta.”
        “Hakane, ni ka cire tani na fahimceka, kuma ina goyon bayanka akan duk abinda zaka yi. Sai dai lokaci yayi da zaka duba ƴan jam'iyya suma. Kayi baɗe-naɗen bada muƙamai a fara gudanar da mulki. Sannan shi Haysam ɗin wane shiri kake da shi a kansa? Dan bayan takardar afuwa baka sake cewa komai ba game da fitarsa a prison ɗin. Ya kamata kayi abinda ya dace kafin masu hannu a rufesa su suyi wani motsi. Dan na tabbatar ba zasu kwanta barci ba awannan gaɓar”.
        Ba saurare kawai ba, tasiri sosai maganganun ogan keyi a kwakwalwar Janar. Amma sai ya murmusa cike da dattako ya furta, “In sha ALLAHU duka za'a duba ayi kuma abinda ya dace. Sai dai ƴan jam'iyya zamu iya samun matsala da su akan batun 60-40 na muƙamai”.
         “Saboda mi?”.
     “Saboda gwamnatin mu ta zama ta kowa da kowa ce ba ƴan jam'iyya da suke ganin sunyi wahala dan jiran waɗan nan sakamakon ba. Idan ma har za'ai 60-40 ya kama ace itama jam'iyya tayi 30-30 ita da sauran al'ummar wajen jam'iyar. Hakan zai ƙara kimantamu a fahimci canjin mu daga na jiya zuwa yau. Bawai akoda yaushe ƴan ƙasa suyita ganin fuskokin da tun haihuwarsu sune ke mulkar su ba. Abar matasa da shaye-shayen

Please Login or Register in order to submit comment