Reading KIDA A RUWA BOOK2 COMPLETE BY BILLYN ABDUL Chapter 25 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma su Nimrah tambaya.
      “Yanzu ina farin cikin kwana biyu kun nutsu ashe lumbu-lumbu kuka min. Yau kuma mi kuka aikata?”.
       “Hummm! Ɗan tsohon shugaban ƙasa suka sumar Mammah”.
    Ba Mammah ba hatta su Dayyan sai da suka ƙwalalo idanu waje. Lailah da Shariffa kam na haɗa baki wajen faɗin, “Ɗan tsohon shugaban ƙasa fa Yaya!”.
      “To waɗan nan yaran kuma ai inaga shi kansa shugaban ƙasar dake kan kujerar mulki idan tsayawa zai yi bazar da shi zasuyi. Ina ga aikin soja kawai zan kaisu dan al'amarin nasu zaifi armashi a can”.
        “Oh ni A'ishatu ALLAH kana gani, to miyay musu da zafi har takai da sumarwa? Sannan ma wai yaro ne kamar su ko yaya?”.
       “Mammah ina fa sa'ansu, ajin ƙarshe fa yake a makarantar tasu. Kinga ko ai kusan sa'an Mu'azz kenan ake batu”.
      Salati Mammah ta sake sakawa tana zabga tagumi, yayinda su kuma suke cika baki da iska suna hararar Dayyan da Hanoon dake dariya, dan su abin dariya ya basu harga ALLAH. Yara kamar jinin Chaines jama'a.
        “Kun bar wajen ko sai na tashi kan ku”. Daddy Imran ya faɗa yana harararsu gani abinda suke ma su Dayyan. Ɗaki suka nufa sunama su Dayyan ɗin alamar zasu haɗe. Imran ya girgiza kai kawai yana danne dariyarsa, shi wlhy bai san yaya zai yi da yaran nan ba. Jifa ba'a gama kashe wani case ɗin ba suna ma wasu gargaɗi a cikin gida, dole ne a wannan gaɓar itama Ruƙayya a mata aure kawai zai fi samun nutsuwa. Sai da suka gama shigewa ya zayyanema Mammah komai da bayanin da sukayi har Dada yace akai zancen court, sai dai shima bai san dalilinsa na yin hakan ba. Amma yafi ƙyautata zaton kawai yayi hakan ne dan barazana tunda abinda su yaran suka faɗa dole su iyayen yaron zasu so case ɗin ya tsaya iya inda yake a yanzu. Mammah ta gamsu, tare da jera musu addu'ar shiriya. Daga haka shima Imran ya miƙa yay musu sallama dan yace zaije gida ne anjima zai dawo.....

        ★★★★

   Tsoron haɗuwa da Dada ya hana su Nimrah fitowa. Sai da yunwa ta ishesu Nimrah tai ƙundun balar zuwa ga ɗiba musu abinci ta koma. Da yake yau babu islamiyya haka suka cigaba da maƙalewa a ɗakin har akai magriba. Sai bayan sallar isha'i sannan suka fito bayan sun gama leƙowa sun tabbatar da Dada ya wuce sama baya falon, dan idan ya dawo sallar isha'i wani lokacin babu mai sake ganinsa. Su aunty Lailah ma suna sashensu basu kai da zuwa hirar dare ba. Hanoon ce kawai da Afeef yanzu zaune. Mammah ma tunda tai salla bata fito ba. Nimrah na rungume da magenta da in tana gida haka take manne da ita kamar ɗa, ta zube a kujera Ruky kuma ta nufi kitchen ɗiba musu abinci. Afeef da yafi tsanarsu saboda abinda suke musu dan shima fitinanne ne irinsu yaja tsaki yana miƙawa yabar falon. Sarai Nimrah ta jisa, dan haka ta bishi da kallo cikin rai kuwa tana ayyana (shege mai suffar tsaka. Ka rubuta ka ajiye yau da kumburarren baki zaka kwana a gidan kuwa) a fili kam sai tayi ƙwafar data saka Hanoon kallonta, harara ta wurga mata tana zazzare mata manyan idanunta sai kace Hanoon ɗin bata girmesu ba. Dole Hanoon ɗin ta ɗauke kai dan ita tana da tsoro Ba kamar Afeef ba.
     Dai-dai nan Biebah ta shigo falon. Daga gidan Aunty Mimi take tun safe. Da gudu Nimrah taje ta rungumeta. Hakama Ruky data fito plate ɗin abincin ta ajiye tazo ta rungumeta. Har cikin ransu suke ƙaunar Biebah, dan itama tana son su matuƙa. Dai-dai nan Mammah itama ke fitowa a ɗaki. Kamar an saita sai gasu Aunty Lailah da yara duka. Nan fa falon ya kacame aka zagaye Small Mom Biebah dake raba musu tsarabar chocolate da tayo musu.......... ✍️

63


.........Mu'azz ya shigo a gajiye, dan daga makaranta yake mashin ɗinsa ya samu matsala a hanya sai da Ammar ya biya ya ɗakkosa, dan haka sukai dare. Sun maida hankali a kansu suna musu sannu da jajanta abinda ya faru Dada ya fara sakkowa daga sama. Dan kafin ma ya bayyana ƙamshinsa ya fara isowa hancinan wasun su da takunsa. Tamkar an saita shima Afeef ya fito daga kitchen ɗauke da tea zai sha. Dan su abinci sai sun zaɓa. Nimrah da hankalinta ke kan kwance ma Afrah kai sam bata ji batun sakkowar Dada ba. Sai hankalinta ya koma kan Afeef. Alƙawarin datai ma kanta na yau sai ya kwana da kumburarren baki ta tuna. Ta kalla dole sai Afeef ya bi ta gabanta sannan zai wuce sai ta saki murmurshin da ALLAH ya tabbatar ma Dada ganinsa sakamakon idanunsa da suka sauka a kanta daga stairscase ɗin da yake sakkowa. Har zai kauda kai sai ya fahimci kallon da take ma ƙafafun yaron nan da ko sunansa bai sani ba. Sam bai kawo tunaninsa akan abinda take shirin yi ba, dan kamar ƙyaftawar ido kawai ta sakama Afeef ƙafa sai gashi kifff a ƙasa shi da kofin shayin nasa. Azaba ta saka shi fasa gigitacciyar ƙarar data saka kowa zabura a falon. Ita ko mai gayya da aiki tuni ta maida ƙafarta ta naɗe yanda take baka isa cewa itace ta aikata ba....

###########

        Tunda fa yau Malam Buba ya buɗe ido ya gansa a gaban shugabannin kungiyar duhu yaji yana neman susucewa, dan kuwa wannan shine karonsa na farko a tsawon fara aikinsa da su shekara takwas. A haka ma iya shugabannin ƙungiyar ne su biyar ba kowa da kowa ba sauran members.
     Daga sama har ƙasa oga Jush ya gama ƙare masa kallo da nazartarsa. Kafin ya fara magana cike da gadarar taƙadaran masu mulki.
         “Miyasa kai ƙoƙarin isar da wannan saƙon kai tsaye garemu bayan akwai Dagger dake jagorantar ka kafin yau?. Duk wani aiki shike baka umarnin sa. Ko akwai wani kuskure ne daka gani a tare da shi da ka ji rashin yarda?”.
       Kasancewar Mole ba jin yaren Oga Jush yake ba Black Spider ya fassara masa. Mole ya sake risinar da kai cike da tsantsar girmamawa yana kuma girgizawa. Shima da yarensa daya iya yay magana black Spider tafinta. Ya tabbatar idan yana son kama kurwar mutanen nan sai ya bisu mataki-mataki, domin kuwa mugu shi yasan makwantar mugu ai.
       “Ranka ya daɗe babu wata matsala shakanina da oga Dagger sai alkairi. Shi mutum ne mai amana kuma yasan aikinsa. Kwana biyu ban samesa bane ga kuma abinda na gani na cimin rai. Na kuma tabbatar kuna buƙatar wannan bayanin da gaggawa saboda matuƙar muhimmancin sa.”
       Koda Black Spider yay ma oga bayani sai oga Jush ya zubama Mole idanu yana sake nazartar sa. Cikin gamsuwa ya ce, “Naji daɗin hakan ƙwarai da gaske. Dan yabon Dagger da kayi ya tabbatar mana kaima mutum ne mai amana. Da kaci amanarsa muma mun san zaka iya cin tamu. Zaka iya bayanin ka yanzu kam”.
       Sosai Mole yaji daɗin wannan yabo, dama kuma irinsa yake son ji. Cikin ƙara kwantar da kai ya fara bayani dalla-dalla akan dawowar Dada. Babu wanda a cikinsu bai rikice ba kam. Dan oga Jush ma har miƙewa yayi tsaye tsabar firgici. Cikin tsawa-tsawa Viper ya ce, “Kasan abinda kake faɗa kuwa? Kai ya akai kasan shi?”.
         “Babu tantama ko kokwanto a maganata oga, duk da a yanzu ya canja kamannin fuska ya ajiye gashin saje bazai layance min ba ai. Sannan taya zan manta da wanda gudan jini na take a hannunsa. Sai da na sake tabbatar da dukkan abinda zan kawo muku sannan na yarda nazo nan. Kuma na baku damar bincikawa kuma, dan kullum suna fita da Imran ɗin nan, sai dai ban san ina suke zuwa ba. Da farko nayi tunanin zai gane ni, sai kuma naga shekara takwas da rabi ba kwana takwas bace ba. Oga ku taimakeni yarinyata ta dawo hannuna nima, dan sun mata asiri bata ko tuna tanada uba. Mun bata video ɗin nan da kuka bada amma babu wani motsi daya nuna alamar ma saƙon da muke ƙoƙarin isarwa ya mata tasiri”.
        Komai babu wanda ya iya sake ce masa a cikinsu. Dan halin da suke ciki a yanzu yafi nashi......

     ★+++++++++++++++★
         Ƙarar da Afeef ya fasa ta daki falon gaba ɗaya. Kowa ya zabura kamar an harba bindiga. Kofin shayin ya watse, ruwan ya zuba a kafet ɗin tsakkiyar falon, shi kuma yana mirgina a ƙasa yana riƙe ƙafarsa yana nishi.
       “Wayyo ALLAHA! Wayyo kaina, ƙafata”.
       “Subhanallah!”
   “Innalillahi!”
Muryoyin su Aunty Shariffa suka gauraye falon. Mammah ta miƙe da sauri tana nufarsa, Aunty Lailah ma ta biyo bayanta. Hakama Biebah da Ruky da har zata nufi kitchen ta dawo. Hanoon da Dayyan sun miƙe tsaye suma a firgice, hakama Mu’azz da sauran yaran su Aheel na tsaye kowa na kallon abin kamar fim.
      Dada ma ya tsaya cak, sai dai baiyi magana ba. Sai idanuwansa da suka sauka a wajen. Kallon farko ya tsaya ne kan Afeef dake kwance yana nishi. Kafin ya maida kan kafar daya riƙe da hannu biyu yana magowa alamar tana masa raɗaɗi. Slowly ya maida kan Nimrah ƙasa-ƙasa ta yanda babu wanda zai ce ita yake kallon.
          Tsaye take. Hannunta biyu riƙe da ƙugu. Fuskarta a haɗe, kamar bata fahimci me ya faru ba, ta wani zuba masa idanu kamar kowa. Idanun kuma darr babu alamar na mai laifi data firgita sakamakon ganin abinda ta aikata. Dada ya ɗan lumshe ido, ya sake buɗe su a hankali, ya maida kallonsa kan Afeef. Sai dai yanzun ma bai da alamar cewa komai.
      “Subahanallahi kaji ciwo ko ruwan zafin ne ya ƙona ka?” Mammah ta faɗa tana durƙusawa kusa da shi da kamo sa jikinta.
        “Zafi nake ji!. Kafa ta…”
    Afeef ya faɗa hawaye na ziraro masa a fuska.
      Biebah ta kalli shayin da ya zube. Cikin nuna mamaki ta ce, “Wai yaya ma haka ta faru? Naga babu komai a hanyar nan dai amma kamar wanda yaci tuntuɓe irin wannan muguwar faɗuwa haka”.
      Afeef ya ɗaga kai, idanunsa na sauka kan Nimrah kai tsaye ya ce, “Ita ce. Ita ta saka min ƙafa.”
      Falon ya ɗauke shiru na daƙiƙa ɗaya. Kafin Nimrah data zazzaro masa idanu ta ce, “Ni?!” ta faɗa cikin kamar ma mai mamaki irin na karya. Sai kuma ta shiga tafa hannaye “Kai! Amma kai mugun maƙaryaci ne. Ta ina zan iya kada ƙaton nan kamar ka to?!”.
     Hanoon da ranta ya ɓaci sosai ta watsa mata harara, sai dai batace komai bata. Ruky data gama sanin wacece Trouble Queen ɗinta ta haɗiye dariyar dake son bayyana a fuskarta saboda Dada. Mu'azz ya taɓe baki yana ƙoƙarin danne dariya shima, dan tsaff ya gane aikin Ninah ɗin ne, haba shekara nawa ana haɗakar tsiyataku a tare.
       Aunty Lailah da Shariffa kam kallon su biyun kawai suke kamar ba su san dawa zasu yarda ba.
      “Nimrah… Mi ya faru?”.
  Mammah ta kira sunanta a hankali, sai dai ta kafeta da idanu.
         Shagwaɓe fuska Nimrah tayi, kafin ya ce, “Ni Mammah sharri kawai yake mun. Kowa ai yana ganin tsifa nake ma Afrah. Yanzu nida ke can, yana nan ƙafar barewa ce da ni balle na iya zunguro shi?. Ƙilama ƙafafun nasa ne basu da kwari, dan gasu nan tsulai-tsulai kamar na talo-talo wlhy”.
        Kafin kowa yace komai Afeef ya harare ta. “Wallahi ke kika saka min ƙafa!”.
       Caraf Ruky ta ce, “Karya kake! Dan ina tsaye ta kusa da ku ni ban gani ba”
     A hasale Hanoon dake hararar Ruky ta karɓe da, “K dama ai bazaki faɗi gaskiya ba bakin ku ɗaya munafuka fitinannun yara! Kawai”.
      “Ke ma fitinanniya! Dan ni da Buddy na albarka kullum Mammah ke saka mana da iyayenmu”. Nimrah ta faɗa tana murguɗa ma Hanoon baki da nuna su Shariffa.
       Hanoon zata sake magana Mammah ta dakatar da su.
      “Ya isa haka. Mu'azz bani first aid kit” Mammah ta faɗa tana kama ƙafar Afeef da cigaba da faɗin. “Bari mu fara ganin kafar yafi wannan gardamar taku.”
        Sai lokacin ta juya ta kalli Dada da tamkar baya ma a falon kamar tana neman taimako. Amma sai gani tayi hankalinsa ma akan wayarsa yake gaba ɗaya. Dole ta haƙura ta maida idanuwan nata ga Afeef.
      Abinda Mammah bata sani ba sarai Dada na lure da kallon datai masan, amma ya fiske. Sai ma mamaki da jinjina ƙarfin halin yarinyar nan da yake a ransa. Dan tsaff ta koma inda ta tashi abinta hankali kwance ta cigaba da ma Afrah tsifarta babu alamar tausayin yaron ko ɗigo. Murmurshi ne yay kamar zai kufce masa amma ya matse.
Sai ma ya nufi ƙofa abinsa yana faɗin, “Mammah sai na dawo”.
        Maganarsa ta saka hankalin su Shariffa dawowa kansa. Sai lokacin suka tuna ko gaishe shi basuyi ba. Aiko cikin sauri suka fara gaishe shin, dole ya dakata yana amsawa.
       Nimrah dake jin idanu masu kaifi a kanta tun ɗazun sai dai ta rasa wake kallon nata ta ɗan motsa kaɗan, zuciyarta na bugawa, amma fuska a tsuke kamar ba ruwanta. Nata idanun ta ɗan ɗago a karo na farko ta saci kallon Dada da kowa ke gaidawa. Cikin sa'a kuwa sai idanun nata suka faɗa cikin nasan. Cikin sauri ta janyesu ta sauke kanta ƙasa ƙirjinta na sake bugawa..
        Dada da shima ya janye nasa cike da basarwa yana sake ɗaure fuska ya ɗan ja numfashi a hankali. Sannan ba tare da ya ɗaga murya ba ya furta “Sai na dawo”.
       Muryar sa ba tai ƙarfi ba. Amma amonta da tasirinta ya ratsa kowa dake falon, musamman Nimrah. Dan kallon da ya sake yi mata kafin ya juya, ya sa zuciyarta ta buga sau biyu. Domin ta fahimci abu ɗaya. Dada ya gani. Kawai bai faɗa ba ne. Sannan bai nuna alamun yama san abinda akai ba. Bai ce Nimrah ba. Bai ce Afeef ba. Bai yi hukunci ba. Sai dai taji tasirin kallonsa na ƙarshe ɗin nan da idonta ya gani, dan bazata iya tantance na baya da bata san wanene ke mata shi ba.........✍️


64


..........Babu wanda ya sake furta komai a ɗakin sai babbar jakar dake gefen oga Jush yay ma Mr Specter nuni da idanu. Mr Specter ya jinjina kai da tura jakar da ƙafa gaban Mole. “Ga wannan kaje da ita zamu nemeka idan buƙatar hakan tashi.”
     Wani irin daɗi ne mai barazanar fasa zuciya ya daki zuciyar Mole. Duk da yaji damuwa da shirunsu bayan maganarsa ta ƙarshe, dan yaso ace sun tattauna fiye da haka domin su ƙara yarda da shi fiye da yanzu. Amma ko hakan ma ai tafiya tayi riba, dan ya tabbatar maƙudan kuɗi ne irin wanda aka saba bama Dagger yana tsakura musu yanda yaso, shima yau gasu an bashi matsayin nashi. Lokacin gina sabuwar rayuwa yayi, dan yana son sanda Nimrah zata dawo hannunsa tasan shi cikakken uba ne da zai mata gata....
  
       Bayan sun sallami Mole ƙofar ɗakin ta maida kanta ta rufe. ɗakin ya sake komawa wani irin yanayi na shiru. Ba hayaniya. Ba motsi. Sai na ac. Shirun da kan gitta tamkar mutuwa ta ziyarci waje. Shirun da yake sa zuciya ta dinga tambaya kafin harshe.
      Oga Jush ne na farko da ya motsa. Ya gyara zama a kujerarsa a hankali, kamar wanda ke sauke nauyin wani tunani mai tsanani. Bai dubi kowa ba. Sai teburin dake gabansa.
        “Zak-Shadow…”
    Ya faɗa sunan cikin murya ƙasa-ƙasa. Black Spider ya ɗaga kai kaɗan ya kallesa, sai dai bai ce komai ba.
        “Na zata an gama da shi.”
   Oga Jush ya ƙara faɗa, wannan karon muryarsa cike da ɗaci da zafin rai daya kasa dannewa.
         Iska mai kauri Viper ya furzar. Cikin nashi yanayin ɗacin ya furta, “Oga dama mutane irinsa nada taurin rai saboda taurin kansu. Gadararsu ta banza da wofi kansa su dinga jin ba su gama ba. Su kan ɓace ne kawai da maimaita kalmar zasu dawo koda da cika baki ne.”
         Ƙwafa mai ƙarfi oga yayi, ƙwafar dake nuna babban ƙudirin dake tafasa zuciyarsa a wannan gaɓar. Sai kuma shiru ya sake ratsa ɗakin, kowa da irin tunanin da yake yi. Dan su sun ma fi oga Jush shiga cikin razani.
      Oga Jush ya sake katse shirun nasu. “Tambaya ya kamata muyi ma kammu yanzu, ba dawowarsa kawai ba.” Ya ɗaga kai ya dubi kowan nen su a jere. Kafin ya cigaba da faɗin, “Tambayar ita ce… me ya dawo domin yi?”
       Tamkar ya dakesu a zukata ne da wannan kalma, dan babu wanda baiyi motsi irin na mai cizon cinnaka ba. Black Spider da ya jingina da bango, muryar sa na shaƙewa a naƙoshi ya amsa da, “Idan har ya sake kafa gida, to yana nufin yana da abin karewa.”
       Viper ya ɗan yi murmushi mara daɗi. “Ko kuma ita ribar ƙafar ba, dan ina ji a raina riƙonta a garesa da manufa. Karfa ku manta yana da wayo, yana da target.”
     Oga Jush ya lumshe ido na daƙiƙa kaɗan. Kafin a hankali ya ce, “Tabbas maganarka gaskiya ce. Musamman idan muka kalla Mole. Tana kusa da shi. Kuma ba ta san komai ba a kansa.”
        Black Spider ya ɗan jinjina kai da furzar da numfashi mai nauyi. “Wannan ne mafi haɗari. Ku duba, mun bata video ɗin nan, amma babu wani motsi…”
        Shiru ya sake mamaye ɗakin kamar an kashe iska. Kowa ya nutsu cikin tunani, ba don rashin amsa ba, sai don girman barazanar da ke gabansu.
       Viper ya gyara zamansa da faɗin, “Idan har yarinya ta iya jure irin wannan barazanar, to tabbas tana da ƙarfin zuciya da dole sai mun sake nazartar ta… ko kuma tana cikin shakka da wasi-wasi. Kuma dole mu gaggauta......”
       Oga Jush ya ɗaga hannu da alamar yarda da zancen Viper ɗin.
    “Yarinyar ba matsala bace,” Oga Jush ya furta yana zuƙar sigari, sai da ya fesar da hayaƙin da sake gyara zaman ƙasaitarsa yana kakkaɓe tokar sannan ya cigaba da faɗin, “Matsalar ita ce wanda ke kusa da ita. Ku sani Zak-Shadow bai dawo domin zama ba. Idan har ya sake takun zahiriyya, to lallai ya dawo ne domin ya gama abin da bai kammala ba a baɗini.”
        “Kenan oga hakan na nufin idan yarinyar bata motsa ba, zamu tilasta mata ta motsa dole?.”
    “A’a. Ba da gaggawa ba.”
  Ya yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya saki wani murmushin mugunta mai armashi da ban tsoro. Sai kuma ya haɗe fuska da ƙarasawa da,
    “Amma daga yau… ta zama hanyar shiga.”
       A tare suka bubbuga tebirin gabansu alama na amincewa. Babu dariya. Babu tambaya. Babu jayayya.
Shirun da ya biyo bayan maganar ya fi kowace hukunci nauyi. Wannan shirun ya fi kowace tsawa firgita.....

>>>>>>>%<<<<<<<

       Fitowarsa ya saya Imran dake tsaye jikin mota yana duba wayarsa kamar wanda ke jiran lokaci ɗagowa yana kallonsa. Shima kallon nasa yake, koda suka haɗa ido sai ya ɗauke nasa, kai kace baiga Imran ɗin ba ma. Dan kai tsaye gaban motar ya buɗe ta gefen mai zaman banza ya shiga abinsa. Imran dake binsa da kallo yay murmushi yana ɗan taɓe baki, kafin shima ya zagaya gefen driver ya shiga ya zauna..
       Sai da ya tada motar ya ɗan kallesa da faɗin, “Ni harna fara tunanin binka ciki ma, jin shiru bayan kace gaka nan fitowa”.
      Dada bai amsa ba. Ya daidaita zamansa ne kawai, ya jingina da kujerar, yana mai lumshe idanunsa. Sai da suka fice gaba ɗaya a gidan sannan Dada ya ɗan saki numfashi, tare da motsa lips kaɗan, cikin murya ƙasa-ƙasa ya furta,
     “Hmm.. yaranka basa ji.”
Imran ya ɗan juya kai ya kallesa, sai kuma ya saki murmushi da maida hankalinsa a titi sosai.
       “Oh, su ne suka tsaidaka kenan? Mi ya faru?”
    A nan ma shiru yay kamar bazaiyi magana ba. Irin shirun nan na manya, wanda baya nufin babu abin cewa, sai dai ana tattara abin faɗar ne saboda ɗabi'ar rashin son magana. Imran yasan halin kayansa, dan in kaji doguwar magana a bakin Zak... Ɗinsa ɗayan biyu ne. Kodai akan aiki, ko yana tare da Mammah ko da shi randa yaso hirar. Sun riga sun fice daga unguwar, har sun shiga babban titi, Imran na kallon hanya cike da natsuwa.
      “Wai bazaka gaya min ba, sai na sauke ka a hanyar nan?”.
    Idanu Dada ya ɗan buɗe yana harararsa, Sai ya kauda kai gefe, kamar yana kallon wani abu a waje, ya ɗan taɓe baki, murmushi yana ƙoƙarin kufce masa amma ya haɗiye kayansa.
      “Kana son bani ciwon kai ne kawai kai da su Imran. Tsabar mugunta yaron nan kawai ta sama ƙafa ya kife a ƙasa shi da kofin tea. Ta kuma fiske abinta baka isa cewa ita ta aikata ba, harda kiransa mai ƙafar talo-talo”.
      “ALLAH ya shirya min Ninah”
Imran ya faɗa yana ƴar dariya. Dada ya juyo ya watsa masa harara.
     “Oh abin ma sugar yay maka kenan? Idan taji masa ciwo kuma fa?”.
     “In banyi dariya ba kuka kake son nayi. Indai su Nimrah ne kaɗan daga aikin su ka gani.”
           Shiru ya sake ratsa motar. Amma wannan karon shiru ne mai ɗauke da dariya a ciki. Dan Dada gintsewa kawai yake, amma yanda ta saka ƙafar yaron ya kife kifff kawai ke dawo masa cikin rai. Yana buɗe file ɗin daya ɗauka a gaban motar ya sake furta, “Na shaida hakan yau kam, dan ƙiri-ƙiri Ruƙayya ta bata kariya bayan yaron ya tabbatar ita ce ta kada shi, Mammah kuma ko faɗa bata musu ba fa.”
       Imran ya saki dariya sosai har yana ɗan dukan sitiyari. Sai da yay mai isarsa, Dada da ya kallesa ya girgiza kai kawai.
        “To wai wanene aka kada? Nasan dai ba zasu ma Mu'azz ba”.
    Dada ya lumshe ido na ɗan lokaci, sannan ya ce cikin sanyin murya, “Cikin yaran mutum nan ne. Dama na fahimci ƴar tsama suke da su”.
       “Kaji fitina, yaron da a tsaye ya fisu sau biyu!” Imran ya furta yana dariya.
           “Ba ku kuke ɗaure musu ƙugu ba, ba Mammah ɗin ba, ba kai ba balle Uncle's da Auntys ɗin nasu. Abinda suka aikato a school yau banji wani yace musu dan mi ba, ƙarshe ma Mammah na gayama su Ma'aruff dariya na jiyo sunayi Bilal harda musu kirari”.
     Imran ya sake kallonsa, wannan karon da nishaɗi sosai. “Ba wani ɗaure musu ƙugu da muke. Dole akwai abinda ya aikata musu shima, dan duk ƙiriniyarsu basa faɗan rashin gaskiya. Ɗazu ma lawyer ɗin nasu ya kirani yana min bayani wai yaron ya farfaɗo, amma iyayen sun kawo lawyer suma, da farko da sun dage sai an sake maido su station ƴan sandan suka nuna masa basu cika 18years ba, basu da hurumin riƙesu anan.”
    “A’a. Ba da gaggawa ba.”
  Ya yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya saki wani murmushin mugunta mai armashi da ban tsoro. Sai kuma ya haɗe fuska da ƙarasawa da,
    “Amma daga yau… ta zama hanyar shiga.”
       A tare suka bubbuga tebirin gabansu alama na amincewa. Babu

Please Login or Register in order to submit comment