Reading KIDA A RUWA BOOK2 COMPLETE BY BILLYN ABDUL Chapter 18 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kukan da tayi.
      Ba ƙaramin mamaki Mammah tayi ba da jin batun damuwa dana kuka. Amma sai batace komai ba tabar doctor yay aikinsa. Allurori yayi cikin drip ya saka mata, kasancewar akwai masu saka barci a take barcin yay galaba a kanta.
Mammah bata sanarma kowa abinda likita ya faɗa mata ba, ta bar komai a hannunta zata saka ido kan Nimrah ɗin harta fahimci damuwar tata..........✍️46


.........Kwana biyu Nimrah na jiyyar zuciya da jiki ko muce sunayi ita da Hassanar tata Ruƙayya, dan itama dai duk ta zama sukuku da ita. Sannan komai Nimrah tace tana so zata tashi tai mata cike da kulawa. Ita Biebah har dariya ma suke bata kamar ba waɗanda suka gama shan faɗa ba a daren ciwon Nimrah ɗin. Uncle's ɗinsu kam da su Aunty Shariffa kowa ƙoƙarin tattalinta yake, bare kuma Mammah da suka dawo ɗakinta ma kwana tare da ita, dan tace har Nimrah ɗin ta samu sauƙi sannan.
     To Alhamdullah sauƙi ya samu, dan yau juma'a ma har cewa tai zata makaranta Mammah ce ta hanata tace dai Monday, amma taso zuwa kodan ta samu hanyar samun wayar da zatai kiran number ɗin can da aka faɗa mata a video ɗin. Dan duk yanda take yaƙin ture abun a ranta da hakan kanta yin abinda suka ce ta kasa. Kamar wadda ake mintsini da azalzalarta haka take ji. Dan ma bata samun sukunin yin tunani saboda Mammah bata barinta koda yaushe tana tare da ita musamman idan du su Ruky sun tafi makaranta. Amma yau da Mammah ta hana tabi su Ruky makarantar ta gama yankema kanta shawarar koma ta yaya sai ta samu tayi magana da mutumin nan a cikin weekend ɗin nan su haɗu a tahfiz. Da wannan tunanin ta kasance har su Ruƙayya suka dawo daga makaranta. Mazan gidan sukai shirin massalaci suka fita..

       ★Ammar ya fito a mota zaije massalacin juma'a shi da su Abees da Mu'azz sai ga Adeel a hanya shima zai je a ƙasa, sai kawai Ammar ya tsaya suka ɗaukeshi. Mu'azz dake gaba ya koma baya Adeel ya shiga. Haka sukaje Central mosque ɗin tare, bayan idar da salla a ƙa'ida sukan wuce gaishe da Baffan su Imran da Hajjo, dan haka tare da Adeel sukaje, acan kuma suka samu su Yaya Ja'afar da Ma'aruff. Ammar ya gabatar da Adeel matsayin abokinsa makwafcinsu. Su mutanene masu daraja ƴan adam, babu wanda ya nuna komai akan Adeel sai mutuntawa, sukaci abinci a gidan akasha hira duk da shi Adeel baya jin Hausa sai turanci, dan haka hirar duk sai ta koma da yaren nasara.
     Sai da a gaɓar da Baffa ke ma su Yaya Ma'aruff nasiha akan batun Uncle ɗinsu Tasi'u daya koma Lagos akan su manta da komai suyi hakuri su karɓesa kamar yanda Mammah ta hakura ne ya koma Hausa. Ya kara musu nasiha sosai duk da kuwa randa su Nimrah suka zo gidan suka samu Uncle Ammar ya fita da shi sun haɗu ne a gidan Uncle Nasiru dama sun musu faɗa akan batun Uncle Tasi'u ɗin. A ranar dai sun ce komai ya wuce, amma basuce sun yafe masa ba. Shine ya koma Lagos ɗin da nufin zai kawo yaransa gidan Mammah ɗin, washe gari ya tafi. Shine yanzu Baffan ya sake musu nasiha shi da hajjo. Daga haka suka koma batun kasuwanci. Dan shima Baffa ɗan kasuwa ne da sukaci zamani a lokacin ƙuruciya....

     ★★★★★

A kusan dai-dai wannan lokacin Nimrah ce ta faki idon su Mammah datai baƙi Ruky kuma na barci ta nufo gate. Ƙanin Baba maigadi kawai ta samu zaune yana latsa ƴar wayarsa rakani kashi harda ƙyauro a jikinta. Sallamar da tai masa ya saka shi ɗagowa yana kallonta, dan tunda yazo gidan magana bata taɓa haɗasu ba daga ita har Ruky. Saboda kallon marasa ji da rashin kunya yake musu ma shiyyasa bai taɓa fatan wani abu ya haɗasu ba.
      Amma mi, a mamakinsa sai ta masa sallama, baima san lips ɗinsa ya fara rawa wajen amsawa ba. Bata damu ba ta ɗora da gaishesa. Nan ma mamaki ya kama shi. Cikin kasa haƙuri ya ce, “Hajiya kina son wani abu ne?”.
        Nimrah ta ɗan sauke numfashi da waigawa ta kalla hanyar cikin gida, har yanzu babu alamar kowa kamar yanda tai fata, sai sabon driver data hango can wajen mota yana fitowa daga ciki alamar wani abun yake yi wanda ta san bai wuce goge motar ba dan ɗazun taga suna wankewa shi da Sanda ɗin. Kauda kanta tai daga kallonsu dan bazai yiwu yaji maganarsu ba daga inda suke, kuma taga hankalinsa gaba ɗaya baya a kansu ma.
        “Waya zaka ara min”.
    Tai furucin idonta akan wayarsa. Shima da mamaki ya kalla wayar sannan ya sake ɗagowa ya kalleta. “Hajiya waya dai? Kalli fa wayar tawa yanda take.”
        “Karka damu ba wani abu zanyi da ita ba.”
    A zuciyarsa ya furta (wannan yarinyar kuwa anya ba zargina take ba, dan na fahimci shegen wayo ne da ita. Ko kuma wani ne dai ya turota gareni a cikin gidan...)
      “Malam Sanda”.
  Nimrah ta katse masa tunani. Firgigit ya dawo hayyacinsa. Ganin yanda ta tsatstsare shi da manyan fararen idannunta baima san ya miƙa mata wayar ba.
     “Na gode”.
  Ta faɗa a hankali tana barin wajen. Da kallo ya bita, kamar yanda Malam Buba driver ke binta da kallon gefen ido, dan tun ɗazun dama hankalinsa a kansu yake duk da baya iya juyo abinda suke faɗa. Ganin ta amshi wayar Sanda ya sashi fahimtar mi take shirin yi, da sauri ya koma cikin motar kamar bai gama abinda yake ba, ya zaro tashi ƙaramar wayar ya shiga neman layin Dagger daya san zai iya samunsa da gaggawa. Aiko babu wani jimawa ya ɗaga shima daga can, dan kwanakin nan gaba ɗaya cikin ƙaguwar jiran kiran Nimrah yake yi, amma shiru kake ji, sai da ma Molen ke sanar masa bata da lafiya ne kwana biyu sannan. Ko gaisuwa basu yi ba Mole ya fara sanar masa, “Oga ka kasance cikin shiri na tabbatar kai zata kira. Dan gata can ta amshi wayar Sanda ta nufi bayan ɗakin janareton su.”
     Sai da Dagger ya sauke wata wawiyar ajiyar zuciya sannan ya ce, “Mole waye Sanda kuma?”.
       Cikin ƙaguwa Mole ya ce, “Wannan ƙanin Almu ɗin fa da nake gaya maka sunzo ranar daya dawo tare”.
      “Oh-oh na tuna, bara na ɗaga inaga gata tana kira.....”
    Bai jira amsar Mole ɗin ba ya katse kiran.....

      A ɓangaren Nimrah data zagaya bayan ɗakin Gen... Ɗin gidan kuwa da sauri ta fara loda number wayar data kwafe a jikin ƙaramar takarda, sai da ta danna kira ta tabbatar ya shiga sannan ta nema waje ta zauna dan ta tabbatar babu mai zuwa nan a cikin ƴan gidan balle yay tunanin tana nan. Sai dai ma'aikatan gidan irin su maigadi, kuma sai da ta leƙa ta tabbatar babu kowa a ɗakin dan dama maigadi ne bata gani ba acan waje, shiko ƙaninsa Sanda da Malam Buba tunda sun ganta tasan baza su zo b......
       Sallamar da akayi ce ta katse mata tunaninta. Duk da yanda muryar mai maganar ke a buɗe ba daɗin ji dai ta daure ta amsa. Daga can Dagger ya sake matse murya shi a dole yau yana waya da masoyiya, dan jikinsa har tsuma-tsuma yake yana dannewa da ƙyar. Saboda yanda muryar Nimrah ɗin ta dakesa ji yay kamar zai shiɗe....
       “Kana magana da Naja'atu Nimrah ne? Dan ALLAH waye kai?”.
     Da ƙyar Dagger ya iya dannewa ya daidaita yanayin sa ya bata amsa da, “Sani na a yanzu ba shi bane mai muhimmanci, ina ya kamata mu haɗu ya dace ki nema kawai. Dan lokacin da kike da shi a gareni bashi da wani yawa, zan iya ɓace miki a kowane lokaci.”
       Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, tare da faɗin, “Shi ke nan a ina zamu haɗun? Yau she kuma? Amma ka sani ina son ganin ka da gaggawa”.
     “Baki da matsala indai ni ne. Kamar yanda nai niyyar sanar miki gaskiya ba zan guje miki ba. Na baki damar ki faɗi a indai zai miki sauƙin mu haɗun batare da ko ƴar uwarki ta sani ba, saboda gudun kar a cutar miki da ita”.
      Ba tsoro Nimrah ke ji ba, tsoronta kawai kada a taɓa mata lafiyar kowa a ahalinta ne. Dan haka ta ce, “Ni bani da inda na sani bayan gidan mu, kuma ba'a barina fita ni kaɗai”.
       “Okay na gane, makaranta fa?”.
   “Makarantar bokon mu ma baza'a bari na fita ba, sai dai mu haɗu a tahfiz gobe, shima lokacin da ake kawo ma ɗalibai abinci”.
       “Ta yaya kenan?”.
   “Zan ma drivern gidanmu magana”.
“Amma nace miki bana son kowa ya sani ko? Shi drivern baƙya tsoron ya bamu matsala?”.
     “To ni ban san yaya zan yi ba, wannan hanyar gareni kaɗai gaskiya. In dai ba ita ba sai dai a haƙura....”
     Da sauri Dagger daya fahimci zata ƙwaɓa masa aiki ya ce, “Karki damu bar komai a hannuna zan san yanda zanyi. Goben kawai ki saurare ni”.
     Kanta ta gyaɗa tana ɗan juyawa jin kamar motsi, sai kuma ta sauke wayar a kunnenta. Ganin babu komai ta sauke ajiyar zuciya tare da goge number ɗin daga cikin wayar ta muƙe zata bar wajen. Da sauri Sanda dake laɓe jikin window ɗin bayinsu dake ta wajen ya duƙe dan duk yana jinta.47


..........★Anan kam su Ammar sai da akai la'asar suka baro gidan Baffa, daga nan gidan Uncle Nasiru suka je shima gaishesa, kuma nan ma Adeel ya bisu bakuma suce masa komai ba. Dan a ganinsu ma ya ɗanyi yawon buɗe ido tunda ya sanar musu abinda yazo yi kasar kenan a gidan Baffa. Sun samu Uncle Nasiru bai kai ga shigowa gidan ba saboda sune dai keta gwagwarmaya akan kafa gwamnatin Janar Yusuf kowa ya sani. Amma Ummy ta musu tarbar girma kamar yanda ta saba. Yaran duk sun zo sun gaishesu, anan ne ma Mu'azz ke takalar Bintu da cewar ƙawayenta nacan zasu yawon juma'a tazo su tafi da ita. Shine take dariya da bashi amsar ai Mammah ta hana su fita. Tace Ninah harda kuka.
       Su duka dariya sukai, sunan Nimrah da Imam ya ambata ya saka Adeel jin zuciyarsa na motsi, da kyar ya iya dannewa baice wani abu akan sunan ba, dan ya tabbar Nimrah ɗinsa ake nufi. Suna nan Uncle Nasiru ya shigo gidan, haka sukai zaman hira da shi shima har gab da magriba, shima kuma bai ce komai akan Adeel ba bayan bayanin da sukai masa da alaƙarsa da Ammar.
     Sun dawo anguwarsu anan sukai magriba, Mu'azz ne kawai ya shiga da su Aheel gida saboda sun gaji ansha gantali. Bayan an idar sai Adeel yaji kunyar binsu gida, da kyar ya daure yace zaije gida shima ya huta ya gaji, koda sukai masa tayin shiga sai ya kanne yace karsu damu watarana zai shiga yanzu dai su masa afuwa ai sun sha yawo. Dole suka barsa suka shige shi kuma ya shige yana danne ransa da kyar, amma tunda dai aka fara samun wannan damar yasan nan gaba za'a samu wadda ta fita ma. Damma zai ƙara tafiya ne kan uziririnsa, amma yasan yanzu kam ya ƙulla da wannan ƙasar kenan. Batun mijin Nabeeha kan tuni ya ajiye sa gefe bai ko sake tunashi a cikin manyan ayyukansa ba, ba kuma hakan na nufin ya ƙyale Nabeeha ɗin bane ba, yana son ya ƙarasa abinda ke gabansa ne kawai kafin ya sake waiwayenta.....
        
<<<<<。⁠◕⁠‿⁠◕⁠。>>>>>

         Washe gari asabar duk da Mammah ta hana Nimrah zuwa tahfiz ta dage da shagwaɓa da magiya, har sai da Bilal yasa baki yace ta barta. Babu yanda Mammah ta iya ta ƙyaleta sukai shiri suka fita harda su Ayyan driver na jiransu. Kamar yanda suka saba Mu'azz na gaba da su Aheel, su kuma da Aunty Biebah suka shiga baya. Malam Buba na saukesu suka nufi shiga gate, tsayawa Nimrah tai tare da juyawa da baya tana faɗin, “Kai nayi mantuwa a mota. Kuje bari na amso kada ya tafi”.
    Babu wanda ya kawo komai a ransa suka shige, dan Ruky na riƙe da Afrah ne a hannu. Nimrah ta iso Malam Buba na ƙoƙarin barin wajen, duk da dai shima hankalinsa na kanta dan yanda suka tattauna da Dagger a jiya ya sanar masa yanda sukayi ya tabbatar zataso yin magana da shi. Ilai kuwa sai gata. Glass tai masa knocking, ya sauke shi ƙasa. Suna gaɗa ido tai saurin janye nata saboda yanda tsikar jikinta ta tashi. Cikin dauriya ta ce, “Baba dan ALLAH wayarka zaka ara min”.
      Kalmar Baban nan ba ƙaramin dukan ƙirjinsa yayi ba, ya danne da ƙyar yana gyaɗa mata kai, wayar ya miƙa mata har hannunsa na ɗan rawa kaɗan. Da yake hankalinta ba'a nan yake ba ma bata lura ba ta amshi wayar ta saka number ɗin jiya. Kamar jiranta ake bugu ɗaya aka ɗaga. Kai tsaye bayan sallama ta sanar masa Nimrah ce, ta cigaba da faɗin, “Number ɗin drivern gidanmu ce, idan ka tashi sai ka kirashi nan da ƙarfe sha biyu”.
      Daga can Dagger ya ce, “Okay bashi wayar naji yanda zamuyi da shi. Ke kawai ki shige ciki”.
     “Okay”.
  Ta faɗa kawai tana bama Malam Buba wayar. “Baba kayi magana da shi baƙona ne, zuwa anjima in zaka kawo abinci ka bada sunana zan fito amsa”.
       Kasa magana Mole yay sai jinjina kai. Ita kuma ta wuce kawai abinta....
    Da kallo ya bita har sai da ta ɓacewa ganinsa sannan ya ce, “Kana jina?”.
     Daga can Dagger yace, “Eh.......”
   
<<%>><<%>><<%>>

           “Ka bani tsoro fa, miya faru kake so mu haɗu da gaggawa haka?”.
  “Wani abu ne ya rikita min lissafi, shiyyasa nake son ganinka da gaggawa. Ko Almu bai san zan zo nan ɗin ba, dan nace masa ne kawai zanje sayo kati ne”.
       “Miya faru?”.
   “Cikin yaran nan biyu dake gidan ƴammata akwai alamar tambaya akan ɗaya daga cikinsu fa”.
     “Wacce a ciki?”.
“Baƙar. Kamar ita naji suna kira Nimrah. Jiya tazo ta amshi aron waya a hannuna, ta koma can baya domin yi, sai kawai naji na tsargu da tunanin ko zargina take zatai wani bincike ko kuma wani ne ya sata.”
       “Ka bata wayar?”.
    “Na bata, amma na bita a baya ta cikin toilet sai naji tana maganar kamar zata haɗu da wani ne a makaranta”.
      “Wani?”.
   “Tabbas”.
“Number data kira ɗin tana wayarka?”.
“Tana bani wayar ita na fara dubawa, sai dai ta goge ta, kasan yarinyar nada wayo matuƙa.”
       “Kai mi kake tunani?”.
    “Ɓoyayyar alaƙa da saurayi, ko wani abu akan mutanen gidan”.
“Nafi yarda dana farko”.
“Zamu iya sakankancewa ya zama na biyu kuma”.
     Shiru wancan yayi alamar tasirantuwar maganar Sanda ɗin. Kusan mintina biyu ya furzar da iska kaɗan yana jinjina kansa. “Kaima kazo da magana. Amma dole muyi abu ɗaya a yanzu, kaje ka saka mana ido a kanta sosai, idan munga zatai mana amfani sai mu jawota muma. Dama tsintacciyar mage ce ai a gidan” .   
      “Ban gane hausar ba fa”.
    Dariya wancan yayi da taɓe baki, sai kuma yace, “Tunda ba yarenka bane taya zaka gane.”
      “Kai kullum gorin yare, naga nima dai ina da yaren, kuma yanzu ba iya yaren naku ai”.
     Ƴar dariya waccan yayi da faɗin, “Haka ne, gashi ma harka zama Sanda”.
    Dariya suka bushe da ita a tare.....
       

      •••••••••••••••••••••
    ★TAHFIZ★     

        Gaba ɗaya yau Nimrah bata wani nutsu a karatun da akai ba duka. Sai ma yawan duba agogo data dinga yi har Ruƙayya ta gaji ta jefa mata tambaya. Sai ce mata tai kawai ba komai. Haushi Ruky taji sai kawai ta shareta. Dan kwana biyun nan abubuwa da yawa ta fahimci Nimrah bata son ta sani idan tanayi, tun ma bata maida hankali har ta fara ranta na sosuwa a kai. Sai dai bata taɓa mata magana ba ko damuwa da bibiyar son sanin abinda take ɓoyewar ma.
     Ƙarfe sha biyu da ashirin Nimrah ta miƙe, inda malamin dake koya musu karatu a yanzu haka yake ta nufa, sanar masa tai zata bayi. Bai hanata ba dan hakan ba wani abu bane. Koda ta fita bayin ta fara zuwa, bata ko shiga ba aka kaɗa ƙararrawa, alamar lokacin amsar abinci yayi an kuma tashi yara daga ƴan aji ɗaya zuwa uku. Da sauri Nimrah ta fito ta nufi gate. Cikin sa'a ta faki idon securitys ɗin gate ɗin dake ƙoƙarin amsar sunan wanda zasu amshi abinci, ɗayan kuma zai fara fida yara da aka tasa.
     Waige-waige ta fara na neman motar gidansu....
     “Hajiya gamu ta nan”.
Taji muryar malam Buba a bayanta. Da sauri ta juya inda yake, yana tsaye a jikin motar, duk da yanda taji faɗuwar gaba sai ta fuske. Shima bai sake magana ba ya nuna mata motar kusa da shi. Motar ta kalla kamar mai nazari ko tsoron shiga, sai da ya maimaita mata, “Baƙon naki ne a ciki Hajiya” sannan ta saki ajiyar zuciya mai nauyi. Dai-dai nan kuma aka buɗe mata gaban motar, sai kawai tai addu'a sannan ta shiga ƙirjinta na dukan ɗari-ɗari na rashin sabo. Sai dai abinda take buƙata ya danne wannan a zuciyarta.
     Tana gama zama Malam Buba ya rufe motar, sannan ya buɗe ta gidansu ya fara kwasar abinci. Ɗauke ido Nimrah tai daga kallon malam Buba a karo na farko ta kalla wanda ke cikin motar da suke dan har yayi reverse zai bar wajen. Ido suka haɗa da Dagger, sai taji tsigar jikinta na tashi har sai da ta karanto addu'a. Gashi dai cikin shigar mutunci dan manyan kaya ne a jikinsa. Shadda fara harda hula, sai dai fuskarsa da jajayen idanunsa zuwa lips ɗinsa dake baƙi sosai alamar shaye-shaye sai wankan ya banbanta da kalar tasa. Shi ko wani shegen daɗi yake ji yau gashi ha kyakkyawarsa Nimrah, duk yanda yaso kamewa ya kasa sai sakin murmurshi yake....
Received at 5:07 PM        Kallon juna Ruƙayya da suma nasu jikin ke rawa a yanzu sukai. Tuni hawaye sun wanke fuskar Ruƙayya, ta rungume Nimrah da gaba ɗaya ita kukan yaƙi zuwa mata. Dan kuwa a wannan gaɓar hankalinta ya rabu gida biyu ne. Ba komai yasa hakan ba sai zancen mutumin can da tun randa suka haɗu bata sake bi takan al'amarinsa ba balle binciken da yace tayi, kenan da gaske yake Dada na prison ne ba ƙasar waje ba kamar yanda suka ji ƴan gidan na faɗa?. Tabbas a yau ta zama cikin ruɗani na kasa banbance waye mai gaskiya tsakanin shi da ƴan gidan to. Shin kukan murna zatai itama kamar kowa? Kona baƙin cikin sakin wanda bata da tabbacin shine ya kashe ahalinta ɗin ko ba shi bane?.
       Bata da mai bata amsa, hasalima hawayen sun gama wanke mata fuska batare data farga ba. Dan a duniya kukan Mammah yana jerin farko na karya lagonta. Matuƙar so takema tsohuwar nan a cikin jininta da ɓargon jiki. Bata jin kuma koda ta tabbata mutumin nan shine ya kashe mata iyaye hakan zai shafi soyayyar da take ma Mammah duk da mahaifiyarsa ce. Ta saka a ranta shi da laifinsa daban, alaƙarta da Mammah daban. Yanda laifinsa bazai hana alaƙarsu ba, soyayyar Mammah bazata hanata hukuntashi ba in har ta tabbata shi ɗin ne ya kashe mata zuri'a.
       Tuni ita da Ruƙayya da Biebah ma sunje sun rungume Mammah dake kuka sosai saboda karanto mata abinda suka karanta da Mu'azz yayi. Bayan tayi sujidar shukur ta ɗago harda Uncle's nasu suma. Hakama su Shariffa da suka shigo, sun haɗu sun zagayeta kowa na kukan farin ciki mara misalin ƙididdiga.........✍️
          “Ba gaisuwa ƴammata”.
   Ya katse mata tunani. Maimakon ta gaishesan sai ta ɗan yamutsa fuska. Dan duk da turaren daya bulbula a jikinsa ita jitai kawai kamar dai bata shaƙar iska mai nagarta. “Bana son yin nisa samu waje anan”.
      Maimakon yaji haushi sai yay murmurshi, kai tsaye ya furta, “Yanda kike so haka za'ayi ginbiya”.
    Nan ma bata tanka masa ba, ya samu ƙasan wata bishiya yay parking, gefensu kaɗan da shaguna na saida abubuwa kala-kala. Hakan sai ya ɗan bata nutsuwa. Cike da son birgewa Dagger aka wani gyara zama yana kallonta, ita ko ta sake haɗe rai, cike da nuna halin tsiwa da rashin kunyar tata ta ce, “Kaga nifa bana son kallo wlhy. In dai kana son mu shirya kaja girmanka naja ƙanƙantata”.
      Ƙaramar dariya yayi anan ma, yana jin tana wani bala'in sake burgesa. Ya ce, “Okay duk yanda kike so haka za'ayi. Nasan kina buƙatar na fara miki bayanin waye ni, sai dai ba zanyi hakan ba saboda rashin lokaci, dan ina son ki koma kafin ƴar uwarki ta farga da rashi ki. Yanzu dai duk videos kin gansu ai ko?”.
       “Eh na gani”.
   “Kimin duk tambayar dake ranki zan baki amsa”.
       Kai ta jinjina masa tana gyara zama sosai. Bata son kollonsa, amma bata da zaɓi a wannan gaɓar, dan haka kai tsaye ta kallesan da faɗin, “Ni wacece?”.
      Kallonta yay da ƙyau shima yana jinjina shegen wayonta da basira. Amma sai ya shanye kai tsaye ya bata amsa da, “Naja'atu Nimrah mana”.
       “Nasan wannan ai. Ina nufin asalina. Sannan minene alaƙata da su Mammah?”..  
     Ba wannan tambayar yake buƙatar tai masa ba, dan bashi da amsarta kai tsaye sai nan gaba. Dan haka yace,........✍️



........“Zaki san wacece ke nan gaba kaɗan Naja. Su kuma mutanen nan baki da wata alaƙa da su face riƙo”.
       “Riƙo!?”.
    “Tabbas riƙo. Shi sojan nan da kikaga ya kashe mahaifiyarki nan da tsohon nan Kakanki ya kuma bada umarnin a kashe yaran nan a kuma tayar da bomb a cikin gidan shine ya kawoki gidan. Bari na fito miki a mutum. Sunansa Haysam Abdul-rasheed Shehu, soja ne mai muƙamin Lieutenant Colonel a lokacin da waɗan nan abubuwan suka faru shekara takwas kenan.......”
      Tsaff ya kwashe labarin komai ya bata shekaru takwas da suka wuce. Sai dai labarin ya bata shi ne a yanda suka tsara ba'a yanda yake gaskiya ba. Daga ƙarshe ya ɗora da faɗin, “A dalilin wannan kisan gillar da yay ma nahaifin Ummanki da Ummanki da danginku da mahaifinki ne aka kamashi aka rufe a prison. Shine har yanzu yake can a ɗaure....”
     Cikin matsanancin ruɗani Nimrah ta furta, “Taya zan yarda da kai. Bayan su sunce su yana ƙasar waje? Mutanen nan fa sunmin komai a rayuwa, fiye da yanda wasu iyayen na kema ƴaƴan da suka haifa. Ban kuma taɓa jin an faɗi wani mugun hali na Dada a gidan ba sai alkairansa”.
       “Babu wani ƙasar waje Naja, suna ɓoye gaskiya ne saboda ke. Amma daga shi har Imran akan haka aka rufesu. Daga baya shi Imran saboda babansa mai kuɗi ne ya shiga ya fita aka fiddoshi a shekara uku. Kada kuma kiyi mamaki dan sun miki gata ai, saboda abinda ya tsara suyi miki kenan dan a binne miki wannan gaskiyar da nake faɗa miki a yau. Zak-Shadow ya wuce duk yanda kike tunani, kuma komai tsanani mutanen gidan nan har mahaifiyarsa da Imran bazasu yi abinda ba umarnin Zak-Shadow ɗin ba. Amma na baki dama kije kiyi bincike a hankali daga nan har wata ɗaya. Nasan zaki sake nemana da kanki, duk da nasan zasu iya canja miki labarin saboda su ɓoye miki gaskiya akan kashe miki iyaye da yayi. Amma maimakon su ki tambayesu

Please Login or Register in order to submit comment