Reading KIDA A RUWA BOOK2 COMPLETE BY BILLYN ABDUL Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙara girma. Maman Abdull kam dole ne taci ƙyauta ta musamman...........✍️


KIDA A RUWA 2

3

..........Itama dai Nabeeha tun da batun kama Zak-Shadow ya ɓulla hankalinta ya tashi, a lokacin suna umara ita da uwarta. Dan bayan tabar gidan da ita umara suka tafi ita da yaran kaf, wai first lady ce ta biya musu. Hankali tashe ta matsawa uwar suka dawo Nigeria, duk wani tsalle-tsallen tashin hankali da ita akayi sa, kamar abin arziƙi ta dawo gidai, sai dai ana fara bikin su Ja'afar mahaifiyarta ta janye ra'ayinta ta sake barin gidan ta koma gidanta ba'ai bikin da ita ba sam, daga baya kuma ta janyeta suka koma Dubai inda harkokinta sukafi yawa yanzu. Sai bayan da aka yanke ma su Dadan hukunci da fin wata uku ta ɗanzo ƙasar, shima basu wani jima ba ta sake komawa, acewarta bazata iya zama cikin tashin hankali da damuwar tuna Haysam na tsare ba, tsarewar da har lokacin an hana kowa ganinsa kusan shekara ɗaya. Tun daga nan data koma bata sake waiwayen ƙasar ba sai a 2016, sannan Zak-Shadow da Imran nada shekaru uku a gidan yari. A kuma lokacin ne aka saki Imran saboda kai-kawon da matasa suka cigaba da yi har lokacin batare da nuna gajiyawa ba, na Zak-Shadow ne dai yayi tsamari da yawa, shima kuma sunce bazasu sare ba zasu cigaba da gwagwarmaya...

A dalilin dagewar General Yusuf Shu'aibu... Na ganin an saki Dada kamar yanda aka saki Imran akai masa ritaya, dan kuwa ƙungiyar duhu sun fahimci shine ke tsaye kan matasan dake kai-kawo akan al'amarin Zak-Shadow da Imran ɗin, ga shi kuma sunci nasara akan fidda Imran saura Dada, dan haka sukai gaggawar sakawa a daƙileshi dan zuwa yanzu sunyi matuƙar jan hankalin ƴan siyasa a cikin tafiyar tasu fiye da zaton mai hasashe.
Satin Imran ɗaya da fitowa aka sauke General Yusuf Shu'aibu Tafida aka maye gurbinsa da wani. Wannan canji yayi matuƙar kawo ka-ce-na-ce da cecekuce a cikin ƙasa dama kafofin yaɗa labarai, sai dai gwamnati ta toshe kunnuwanta da yin kunnen uwar shegu da komai ta nuna babu gudu babu ja da baya. Bayan ɗaukar lokaci komai ya lafa dole ƴan ƙasa suka amshi sabon canji.
General Yusuf mai ritaya yaji zafin abinda ya faru, sai dai bai nuna ba ya shanye komai tare da komawa gefe kamar yanda akaso. Abu ɗaya ne bai haƙura da shi ba shine ganin Imran ya koma kan aikinsa, duk da shi a lokacin ya nuna baya buƙatar cigaba da aikin soja kuma. Amma Janar ɗin ya tsaya tsayin daka ya fahimtar da shi ammafanin cigaba da aikinsa ne kawai zasu samu taimakon fitowar Zak-Shadow batare daya cika shekaru ashirin da biyar ɗin da aka ɗiba masa ba. Jin haka yasa Imran yarda ya koma kan aiki duk da kuwa a lokacin watansa ɗaya kacal da fitowa a kurkuku...

Tabbas shawarar Janar tayi amfani, dan kuwa komawar Imran aiki ta bashi damar ganawa da Zak-Shadow a karo na farko. A lokacin daya samu umarnin samun wannan damar sai da hawaye suka zubo masa. Imran na matuƙar son Haysam, soyayya irin mara misali ɗin nan da UBANGIJI ne kawai mai tafiyar da ita a zukatan bayi batare da sun san taya take gudana ba......

>>><<•>><<<
21/11/2016

Ranar Litinin ƙarfe goma sha ɗaya na safe Imran ya nufi Special Military Corrections Facility, North Central Command Base inda Zak-Shadow yake. Rana ce da ta fi kowace rana nauyin da sanya zuciya zumuɗi da rauni a lokaci ɗaya a ƙirjin Major Imran Abbas.
A daren jiya bai runtsa ba tunda ya samu tabbacin amincewar zuwan nasa. Kai gaba ɗaya ma kasa zaune kasa tsaye yayi tun da yaga sakon janar mai ritaya ya shigo wayarsa _(An amince. Zaka iya ganin sa gobe. Imran kada ka yi wani abu da zai rikita zuciyarka wannan dama ce muka samu)_ Sai zuciyarsa ta tsaya cak tana mai tsitsinkewa, kai jikinsa kansa tsuma ya dinga yi har sai da Aunty Hafsat ta jeho masa tambaya. Amma sai bai iya bata amsa ba ya girgiza kai kawai. Shekaru uku kenan ba tare da yaga fuskar Haysam ba. Shekaru uku na tambayoyi, na tunani, na laifi da raɗaɗin rabuwa.
Shekaru uku na jin kamar mutuwa mai yankewa ta yanke wannan alaƙar ta har abada. Zaman prison bai jikata zuciyarsa ba kamar tunanin halin da Haysam ke ciki. Cikin dabara ya kai hannu yana share guntayen hawayen da suka taru masa a gefen ido...
Washe gari tunda sassafe ya baro gidansa saboda tsabar zumuɗi, maimakon office kuwa kai tsaye Special Military Corrections Facility North Central Command Base ya wuce. Haka ya samu waje can nesa da prison ɗin ya tsaya zaman kusan awanni uku har lokacin da aka bashi ya cika sannan ya kunna motar ya karasa. A hankali motar sa ta tsaya a gaban babban ƙofar ƙaton gate ɗin. Tsaron wajen ya banbanta da duk wani waje da Imran ya taɓa gani, dan shi ba'a nan aka ajiye shi ba a nashi zaman. Birgedun sojoji biyu a wajen ƙofar, camaras a jikin bango, wasu guards suna sintiri cikin takun da ke nuna horo mai tsauri a wajen.
“Major Imran Abbas?” ɗaya daga cikin guards ɗin ya tambaya.
“Eh, ni ne”. Muryarsa ta yi nauyi kamar anyi masa sarƙa a wuya saboda yanda yake jin kansa da zuciyarsa dake bugawa da sauri-sauri.
“Follow me, sir.”
Kansa kawai ya jinjina, a ƙasan zuciyarsa yana ambaton sunan ALLAH. Ya bi guards ɗin zuwa wani dogon corridor da yake a tsaftace alamar ana kula da wajen sosai fiye da kima. Daga can suka kai shi wani ɗaki da shima yake zagaye da camaras kamar tsiya.
“Ka ajiye wallet, takardu, da belt. Za a bincika ka kafin a shiga.”
Babu wani nuna damuwa Imran ya cire belt ɗinsa dan wannan yasan dokar soja ce. Bai taɓa tunanin zai zo wannan wuri saboda Haysam ba. Bai taɓa hango cewa watarana ƙaddara zata kwaso su zuwa wannan ramin mai tudu da kwazazzabo ba.
Bayan an kammala bincike sa yanda ya dace suka fita a ɗakin, wani ƙaramin ɗakin ganawa suka kai shi, wanda ke da tebur biyu da gilashi tsakanin su. Amma shi an canja musu saboda matsayinsa daga shi har Zak-Shadow ɗin, dan haka aka basu ɗaki na musamman ba tare da gilashi tsakanin su ba.
Wani irin duka zuciyar Imran take tamkar ƙarfen agogo dake bada sakanni na motsawa ne da ita. Minti biyar.. Minti goma.. shiru. Sai zuciyar Imran ta ƙara ƙarfin bugawa kamar bugun gangar yaƙi, dan adadin mintinan da aka saka zai iya fitowa sun cika..

Dai dai nan kuwa aka buɗe ƙofa a hankali. Sojoji biyu suka shigo da Lt. Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi. Sai dai ba irin Zak-Shadow ɗin da duniya ta sani bane a baya. Wannan Zak-Shadow ɗin ya canja da canje-canje masu yawan gaske, musamman a suffa ta soja zuwa wani abu daban, gashinsa ya yi tsawo sosai sama da yadda yake da, fuskarsa ta ajiye saje saɓanin da da babu ko ɗigon gashi a fuskarsa saboda kasancewarsa soja, fuskar sa ta ɗan rame amma kwarijin da cikar kamalar da gizago zaratan MAZAJEN na nan shimfiɗe a kanta. Ga tambarin sallarsa ya sake fita baƙi sosai akan goshinsa saboda hasken zaman waje ɗaya da fatarsa ta sake yi, ainahin haskensa na da kafin wahalar soja ta dusar da shi ya sake bayyana. Idanun nan kam sun wani sake juyewa kamar na kumurcin maciji.
Hannunsa na sanye da ƙananan cuffs saboda dokar prison. Shi dama can bamai ƙiba bane, amma jikinsa a buɗe yake da ginannen ƙarfi irin na masu kulawa da tattali, dan haka ko a yanzu bazakace ya rame na tashin hankali ba, dan daga ganinsa kasan bai daina motsa jikin ba, zaka tabbatar da haka saboda takunsa dai nasa ne na soja mai ji da kansa, ko a cikin jeji, ko a cikin duhu. Ko a cikin bainar jama'a wannan takun ƙasaitar da jarumta baya canjawa.
Ya ɗan tsaya kafin ya zauna. Sai kuma ya kalli guards ɗin da juyayyun idanunsa ya kaɗa kai kaɗan. Su sun san nan ɗin ba wajen wargi bane, dan ko KURA TA RAME TAFI ƘARFIN WAWASON ƘANANUN NAMUN JEJI. Ga shi dai a tsare, amma takashi ko manyan KAYA sun gagara, shiyyasa a tsaren yake amma girmamawa babu abinda ya canja. Ai ko mahaukaci yasan kallon ZAKI sai daga nesa, a nesan ma daga bayan keji, dan ko hannu ya samu zai iya yin wawaso. Yafi ƙarfin kallon banza ma balle ace za'a dake shi. Fitar kuwa sukai da sauri suka barsu su kaɗai.
Shiru ya cika ɗakin. Shiru mai nauyin da ko ƙarar bindiga da harbi bai zama lallai ta iya yankesa ba. Su duka biyun sun zubama juna ido ne kawai kamar masu kallo a cinema. Imran ya ji hawaye sun cika masa ƙwayar ido. Amma ya danne. Zuciyarsa na ƙaraji. Dole ya kauda nasa idanun da kansa gefe yana ƙoƙarin haɗiye hawayen.
ReceivedZak-Shadow ya ɗan girgiza kansa, tare da zama, a hankali ya jingina bayan sa da kujerar. Juyayyun idanunsa suka sauka a fuskar Imran daya sake juyowa kamar yana lissafa duk wani abu da bai faɗa masa ba shekaru uku da suka shuɗe.
Ganin Imran bashi da niyyar yin magana shi ya motsa nashi lips ɗin da sukai jazur cikin dakakkiyar golden voice ɗinsa dake cike da izza da amo ya furta, “Major Imran Abbas.”
Kalmomi uku ne kacal. Amma Imran ya jisu har cikin tsakiyar zuciyarsa da brain. Da ƙyar ya iya dauriyar amsa wa da.
“Sir…”
Muryarsa ta kasa fita gaba ɗaya saboda sabbin hawayen dake cika masa idanu.........✍️KIDA A RUWA 2

4

........Dada dake kallonsa kallo mai cike da ƙauna daga UBANGIJI ya ɗan ɗaga hannunsa yana masa Alamar ka tsaya ka nutsu. Sai kuma ya sake motsa lips ɗinsa kaɗan ya furta “You’re a soldier Imran… but seeing you like this is giving me a headache. What’s happening to you?why are you acting like a woman?”.
Shima ya ɗan kawar da kansa gefe saboda idanunsa na son suyi wani abu saboda hawayen da suka sakko a fuskar Imran sharrrr. Kuka ko ɓacin rai ne shi kansa bai ma san wannene yake ji da ganin hawayen Imran ɗin ba. Cikin dakewarsa, idanunsa na kallon gefe ya sake furta, “Bazan tambayeka yaya kowa yake ba? Dan hakan shine mafi girman abinda zai sosa min ZUCIYA. Na ganka, shi ne abinda yafi komai muhimmanci Imran.”
        Da ƙyar Imran ya tsaida hawayensa. Fuskarsa da murmurshin ƙarfin hali ya ɗan matsa gaba, hannayensa duk biyu ya ɗaura kan teburin. “Munyi ƙoƙari.. Munyi komai… amma suka zaɓi yimana wannan zaluncin Haysam…”
      Dada ya katse shi da murya mai sanyi amma mai ƙarfi da nutsuwa, “Ba zalunci bane. Siyasa ce. Dama kuma ita siyasa ai ba ta rabuwa da jini.”
     Kai Imran ya girgiza. Cikin son ƙarfafa kai ya ce, “Na fahimta, kenan sun kulle ka saboda sun tsorata. Sun tsorata da kai. Sun tsorata da gaskiya. Sun tsorata da abin da ka sani”.
       “Na sani.”
     Dada ya furta a hankali yana ɗan murmurshi. Shiru ya sake mamaye ɗakin kowa da abinda yake tunani, fin sakan goma ya maida kallonsa kan Imran kai tsaye, kallon da ya tattara shekara uku masu zurfi: jarunta, kewa, hikima, da raɗaɗin da ya gama zagaye zuciyar mutum daga mutum ta zama tamkar dutse.
        Imran ya katse shirun da faɗin, “Kurakuraina suka kawo ka nan Haysam, zan sadaukar da rayuwata domin ganin ka fita kuma” ya share hawayen da suka sake silalo masa, batare daya bari yayi magana ba ya cigaba da faɗin, “Bayan rufe mu sun sauke COAS shima, sai dai bai daina gwagwarmaya ba, dan yanzu haka da tsayawarsa nazo nan.”
       Idanu Dada ya lumshe a hankali, batare da kula zancen Imran na farko ba ya furta, “ALLAH ya saka masa da alkairi, dama nasan ba zasu barshi ba shi da duk masu goya mana baya. Imran… ka dawo min nan idan ka samu lokaci. Muna da magana mai tsawo. Kuma kada ka sake jin damuwa. Kai kaɗai ne wanda ban taɓa zargi ba.”
      Idanun Imran suka sake zubo hawaye saboda wannan kalmomi na ƙarshe. Cikin jinjina kai ya ce, “Zak… har abada damuwa bazata barni ba in har kana a wannan wajen. Dan haka bazan taɓa barin ka a nan ba har abada”.
       Dada ya yi murmushi. Ba mai annuri ko farin ciki ba. Murmushi ne kawai irin na jarumta da taurin zuciya. Shi yasan fitarsa a wannan wajen sai wani ikon ALLAH, amma ba abune mai sauƙi ba.
      “Karka damu Imran. Ina a nan ne. Amma ba zan tsaya nan ɗin ba kamar yanda ƙaramin tunaninsu ke basu”. Sai ya jingina da kujera yana ɗan lumshe ido. “Kamar yanda na gaya maka kai ƙoƙari ka dawo. Idan ba haka ba ka fara zargina da guduwa, dan babu gudu babu ja da baya sai na ƙarasa wannan aikin”.
       Tabbas Imran ya tabbatar da alwashinsa cikin idanunsa da suka sake rikicewa, ya kuma san wanene Zak-Shadow ɗinsa, kaɗan daga aikinsa ya aikata dukkan abinda ya ƙudurta. Zama ya gyara cikin sassauta murya dan baya son akai ga matakin da Haysam ke harin saboda komai zai sake jagulewa ne.
      “Dan ALLAH kar akai ga haka MAZAN FAMA. Ina sha ALLAHU zan dawo. Zan dawo duk rintsi, zan......”
       Motsin buɗe ƙofar da ake yi ya katse Imran. Sojojin ɗazun ne suka dawo, hakan ya sasu fahimtar lokaci ya cika. Dan haka kafin ma suyi magana Dada ya miƙe abinsa, sai kuma ya ɗan zubama Imran ido na sakan ɗaya, kafin cikin dakakkiyar muryarsa ya furta, “Imran…”
     Imran ya ɗago kai yana kallonsa fuskarsa cike da damuwa da kewa..
          Ƙaramin murmushi yay masa, tare da furta, “Ka tsare min kanka. Daga yanzu ka saka a ranka sabuwar ƙaddara ta fara motsi.” Daga haka ya juya abinsa yay gaba, ya bar Imran cikin shiru mai nauyin da bin bayansu da kallo, idanunsa cike da hawaye, dan a wannan ƙadamin yama manta da kansa a matsayin soja.......

      <<>><<>><<>><<>>
 Imran ya ɗan sake murmusawa yana shafa kai, cike da girmamawa ya ce, “Sir zan sha ruwan dai, abinci kuwa amin afuwa kada madam tayi fushi nabar nata”.
      Ƙaramar dariya Genaral yayi duk da kuwa shima ba mutum ne mai yawan fara'a ba. Cike da dattako ya ce, “Gaskiya bazan so ɗiyata kam tai fushi ba. Amma duk da haka sai kaci, dan na saka an shirya maka ne na musamman”.
    Babu yanda Imran ya iya dole ya haƙura suka hau teburin cin abincin da aka cika da kayan daɗi. Sai da suka fara cin abincin cikin nutsuwa falon shiru janar ya katse shirun da faɗin, “Ina fatan babu wata damuwa tare da Haysam? Yana cikin ƙoshin kafiya?”.
       Sai da Imran ya haɗiye abincin bakinsa sannan ya jinjina kansa, sai dai fuskarsa ta janza zuwa damuwa. “Alhamdullih Sir. Babu wata bayananniyar damuwa ta zahiri. Dama kuma mun san bayan killacewa babu abinda zai yarda ya ɗauka ga wani na ƙasƙanci in dai Haysam ne. Dan har yanzu JININ MAZA na'a kan FARCE”.
      Sosai Janar yay murmurshi mai faɗi. Ya ɗauki ruwa yana tsiyayawa a kofin gilashi. “Wato Imran da ƙasar nan tasan asarar da tayi na killace Haysam na kwana ɗaya kawai data jima da yima kanta da kanta ALLAH ya isa. Balle ma ace na tsawon shekaru uku da wasu watanni. Irinsu Haysam a ƙasa tamkar hasken diamond ne a tsakiyar sahara. Amma ban san miyasa ba, maimakon aga haskensu anfi kallon wahalar ɗakkosu da gujewa zafin saharar ne da yawanta..”
        “Sir bazasu fahimta ba, irinku ƙalilanne ke fahimta saboda zukata masu ƙyau da ALLAH ya baku. Amma wlhy a tsayin rayuwata ban taɓa cin karo da mutum mai tsananin kishin ƙasa da son cigabanta ba irin Haysam. Mutum ne shi mara tsoro, mai tsayawa akan gaskiyarsa koda kuwa ace zata ƙona shi. Sannan yana so da sauri, shiyyasa yake komai da sauri. Amma na rasa miya tare musu?”........✍️

5

.......Falo ne babban gaske, sai dai gaba ɗaya an kashe fitulun cikinsa sai wasu candles da basufi uku ba kacal aka bari suna ci, suma a cikin kwalba suke dan haka haskensu baida tasiri mai yawa sosai. Yanayin duhun wajen ya ɓoye ainahin fuskokin mutanen dake zaune a cikin falon harma da sirrin tsarinsa, koda yake fuskokinsun ma a rufe suke da facemask ta yanda koda ace akwai hasken wutar baka isa tantance su wanene ba. Cikin wani ɓoyayyen harshe suke magana, harshen da babu makamncinsa a ƙasarmu. Sai ɗan ƙarar kofuna alamar akwai abinda ake sha, sai ko room hitter dake basu ɗumi saboda yanayin sanyi da ake ciki. (Waɗan nan sune manyan munafukan shaiɗanci, kowannen su nada laƙabin suna, dan babu mai amfani da sunansa na yanka balle kasan ainahinsa a addini ko yanki balle harshen yare. Hasalima gamayyace daga ɓangarori ta waje da cikin gida).
          Ɗaya daga cikinsu ne ya ajiye kofin shayin hannunsa, tare da yin gyaran murya. Lokaci ɗaya abokan zaman nashi duk suka nutsu, tare da maida dukkan hankalinsu garesa. Cikin harshen da suke maganar ya furta, “Ya kamata muyi abinda ya tara mu, dan bamu da lokaci isashshe”.
       “Tabbas haka ne Black Spider. Yanzu minene a teburin mu?”.
     Zama Black Spider ya gyara, tare da nutsuwa sosai ya ɗauki remote yana dannawa. Hoton Zak-Shadow ne ya bayyana a jikin ƙaton majigin daya cinye kusan rabin bango, tsayayyen jarumin soja, da ko'a hoton kasan eh da gaske Gwarzan maza ne, dan kuwa a cikin uniform ɗin aiki yake, alamu kuma sun tabbatar yana kan aiki akai masa hoton batare daya sani ba, hakan kuma bai hanashi fita da ƙyau ba kuma tartar har kwarjininsa na dukan zukatan maƙiya koda basu bayyana a fili ba. Amma yanda duk suka ja numfashi a lokaci guda zai baka tabbacin hakan.
      Black Spider ya fara jawabi kamar haka, “Wannan mutumin ya lalata shirye-shiryemu a gabashi da yammaci da yawan gaske da bazasu ƙididdigu ba koda a kintace. Mun ƙyaleshi badan yafi ƙarfinmu ba, sai dan bashi dama ya gama taka irin tashi rawar kafin mu canja masa salon kiɗa. Lokacin mu ya yi a wannan gaɓar. Duk da a baya Target ɗinmu Zak-Shadow ya ci gaba da zama cikas a shirye-shiryenmu. Dabarun mu da yawa sun durƙushe a gabansa. Amma yanzu, lokacin da muke jira ya iso garemu, wato dama ta dawo hannunmu.”
      Cikin wata ƴar iskar dariya Viper ya amshe zancen da murya mai taushi amma cike da shaiɗanci irin ta shaiɗanun azzalumai, “Kamar yanda Black Spider ya faɗa a yanzun nan babu jimawa mun tabbatar da bayanin sirri ta hanyar yaran Dagger. Zak-Shadow ya bar sansaninsa na tsaro domin wata tafiya ta sirri a jejin, sai dai bamu san inda ya nufa ba, amma hakan mu ba damuwarmu bace kai tsaye, duk da dolene mu sani dan aikinmu ya tafi yanda ya dace akansa. Wannan shi ne gibin da ba zai taɓa tsammani ya bari ba a gaɓar da zai fuskanci illarmu mai muni, dan zamu zuba masa dafinmu mai ƙarfi da har abada babu makarin warkewarsa a zuciyarsa”.
      Dariya suka kece da ita a tare, sai kuma suka koma tsitt kowa ya nutsu. Dagger da sam bai dara ba sanda ake dariyar, sai ma danna hannunsa da yake a kan tebur da ƙarfi cike da fusata, dan shi kaɗai yasan adadi tsanar da yayma Zak-Shadow a duniyar nan, saboda shine ya kashe masa ƙaninsa a wani hari na bayanan sirri da basu san yaya akai Zak-Shadow ɗin ya bankaɗo ba a kansu. Cikin kaushin harshe ya fara faɗin, “Sirs! Nayi muku alƙawari gamu mayaƙanku ba za mu bari wannan dama ta sulale ba! Dole mu kafa tarkon da zai karya ƙarfinsa gaba ɗaya. Zan jagoranci ɓangarena da ƙyau kuma da tabbatar cikar buri fiye da baya! Dan ina son da hannuna na gurfanar da shi a ƙasan ƙafafu na cike da ƙasƙanci da wulaƙantarwa. Dolene ya ɗanɗani fiye da abinda na ɗanɗana a wancan karon, da ace zaku bani dama bashi ba kaf ahalinsa sai na shafe babinsu a doron wannan ƙasar, na kuma........”
     Mr Specter ya katse shi cikin jan girma, dan kuwa dukansu Dagger matsayin yaronsu yake, matsayinsa kawai shine shugaban mayaƙansu, hakan na nufin amfani ake da shi domin cimma manufa, kawai dai ita tunkunyar sharri ba'a banbance farfesun kayan ciki a cikinta, haɗawa ake har kashin dabbar da ruwan


*_Typing📲_*






*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_GENERAL FICTION_*

_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._


*_BOOK 2_*
_Chapter 6_

__________________

_A KANO KI KE…? Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da MANDI RICE, GRILL CHICKEN, CHICKEN BIRYANI, FUNKASO, ALELEN GWANGWANI, BREAD POCKET da sauran su. Fannin abin sha akwai natural ZOƁO mai zaƙi, wanda aka yi shi da ingantattun kayan marmari masu ƙara lafiya, akwai wanda bashi da zaƙi domin masu ciwon sugar da masu gudun ƙiba._



_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram ko TikTok domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._

INSTAGRAM
👇🏻👇🏻👇🏻
https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr
CALL/WHATSAPP
👇🏻👇🏻
wa.me/2349030398006

TIKTOK
👇🏻
https://www.tiktok.com/@leemars_delicious?_t=ZS-90ZQJ2mNJKc&_r=1




Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida.❤️❤️🫶🏻
__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

..........“Ku fara da gaskiyar Ojo. Akwai wani abu da bai dace ba. Kuma akwai hannaye da yawa da suka fi mu ƙarfi har a cikin gida. Sai dai fuska biyun su tasa sun zame mana masu lulluɓin biri”.
    Shiru ya cika ɗakin. Wani irin sanyi ya ratsa zuciyar Imran. Cikin kasa haƙuri ya furta, “Idan kuwa har akwai masu fuska biyu zan kasance mai tsoro da shakkar mu'amulantar kowa?”.
       “Wannan shine gaskiyar magana, amma a ciki akwai ɗaya tamkar da dubu. General Yusuf Shu'aibu Tafida. Col. Haydar Galadima (Faro), Brigadier General Abraham Yohana, yaranmu Dabo, Yusuf. Amma saura duk ka ajiye kowa. Akwai saƙo a ɗakina na ajiye maka, idan ka haɗa da wannan zai baka abinda nake buƙatar ka fahimta. Dan na tabbatar daga yau bazasu sake barinka ka ganni ba.”
     Da ƙyar Imran ya iya furta, “Janar ya shiga SIYASA...”
         Cak numfashin Zak-Shadow ya tsaya, hakama bugun zuciyarsa kafin su dawo a tare. “SIYASA?!”. Ya furta yana tsatstsare Imran da idanu.
      Kai tsaye Imran ya jinjina masa kai. Sai kawai Dada yayi murmurshi tare da wani ɗan lumshe idanu sannan ya sake buɗesu luuu akan Imran. “Na amince kayi aiki da shi Imran....”
     Cikin tsatstsareshi da idanun shima Imran ya ce,

Please Login or Register in order to submit comment