shiga taro na zuwa villa,to gaskiya kawata karki wuce group dinnan domin kuwa akwai luxury bag's unique shoe's jewelries iya ganinki,hmm baa cewa komai dai ki shiga idonki ya gane Miki yar uwa*
09
Yadda ya ware idanu cikin kaduwa da tsoro yasa Dodo mage ya ce mishi. "Kai har yanzu da sauran lokaci, ba haka ba ne jininka me karfi ne don haka kada ka damu akan abin da zaka gani ko zaka rasa."
Ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin. "Na razana ne!" Kallon yayi duk jama'ar sun koma halittar da suke so. "Yaku waɗanda suka koma kalar da suke so, ku sani wannan abinda kuka samu kamar kyauta ce daga gare ni, amma ku sani dole ku kawo min tukwaici." Gurnani suka fara yi suna ihu. Sannan ya juya ya koma raminsa, kafin aka juye musu jinin bakiɗaya, wanka suka shiga yi da shi tare da ihu.
Sai goshin asuba suka fara barin wurin,har da Alhaji Nafi'u da Rilwanu Abubakar Yayari. Har zasu tafi Mage ya kara kiransu, juyawa suka yi sannan suka koma gare shi. Zubewa suka yi a gabashi. "Jinin yarinyar nan bai ishe ni ba Nafi'u, ina son jini Rilwanu daga cikin gidanku, akwai wani abu a cikin jinin gidanku. Ina so babba ko yaro, jinjiri ko dan tayi." Shiru yayi kafin ya ce mishi. "An gama!" Alhaji Nafi'u ya sake murmushi ya ce mishi. "Jini zaka same shi, amma Shugaba ya batun bude boyayyen masana'anta na ne?" "Ka kawo min jinin budurwa a kawai da shi zamu ga abinda ya dace da masana'antarka." "An gama!" Mikewa suka yi ya koma raminsa ya boya. Sannan suka bar underworld din. "Rilwanu Abubakar Yayari yanzu ya zaka yi?" "Amaryata tana da tsohon ciki, dan zan bada dama na aureta ne na sadaukar da duk abinda zata dauka ban aureta don tayi ta haihuwa ba." Rabuwa suka yi kowa ya kama hanyar kofarshi, yana isowa penthouse din wutar ya kama wani daki ya nufa yayi wanka. Sannan ya dauki kayansa ya saka, wayarshi ya lallubo ya kira wata number.
"Ina son budurwa mara galihu, a tafi gidan Marayu da F&F a dauko min ita kada na ji kada na gani." Daga can aka ce mishi. "Yallabai duk marayun suna da registrater sannan kullum Malam Junaid yana zuwa ya karya da su, gaskiya a duba wani abu." Shiru yayi yana ji kamar ya ganshi gaban Junaid ya shake mishi wuya,.tashi yayi ya nufi wurin kofar underworld ta bude mishi, tube kayan jikinshi yayi yana nufar can inda suke meeting. "Na dawo gare ka akan lamarin Junaidu!" "Na gaya maka babu abinda zaka iya mishi, kuna dayawa da kuke son ganin bayansa, amma ku sani shi din prey din Gwaska dakare ne matukar kuka tab'a shi zaku yi danasanin haka. Ka je akwai lokaci da zasu ribanci hakurinku. Wata nasara tana biye da kai."
Juyawa yayi yana me barin wurin, yana isa penthouse din wayarshi yana kara. Dauka yayi yana faɗin. "Ya dai?" "Alhaji wani abu ne ya faru na kira na gaya maka, wata yarinya aka kawo ba lafiya amma likitoci sun tabbatar da kodanta ne ya lalace, ko zaka yi wani abu a kai a mata dashen koda haka zai taimaka maka wurin fitar da makomanka" murmushi yayi ya ce PA dinsa. "Ayi kome sannan a tabbatar yan jarida an gaya musu, sannan a gayawa Yaranmu masu aikin nan su fitar da kome."
***
Ikhlas
Fushi nayi da kowa na gidan,.don haka ko Maluma fushi nake da ita, dani sai Hajja. "Takwara ayi haka ki ce ba zaki ci abinci ba, tsoro nake kada yunwa su karar da ke, zama gaki abu ba abu ba munafuki yaso tsegumi!" "Na koshi Hajja." Ganin naki kulata ta sake cewa. "Wai takwara bana ganin Irak ina take ne?" "Tana bangarensu." Na bata amsa ina jin kamar na kurma ihu, yunwa nake ji amma bakin halina ya hana ni tashi na je. Ganin bata gane min yasa ta mike tare da barin dakin. Ina jiyo ta tana faɗin. "Ban da mugun hali irin naku, yau kwana biyu kenan babu wanda ya ce takwara ta zo taci abinci, har da kai junaidu kamar baka san Allah ba, haba Junaidu tow wallhi ba zan yarda ba, dama ka saka mata sunana ne don ka azabarta da ita da yunwa? Maza a zuba min abinci na kai mata." Yadda take masifa zaka rantse da Allah ina kwance ne cikin mugun yanayi, nan kuwa dama bana rabuwa abin kwadayi. Kuma su nake ci idan na shiga banɗaki, naci na koshi idan na fito na koma narkewa a idanun Hajja. Ita kuma da bata da hakuri da jure ganina cikin wannan yanayin tayi ta damuwa kenan da damun kanta. Shi yasa nake bala'in son Hajja don tana taya ni abinda nake so.
Shigowa da tire Abba yayi Hajja tana bayanshi, ina ganin Abba ban san lokacin da mike tare da cewa. "Abba!" Yadda na kira sunanshi cikin shagwab'a da rikicin dole yasa shi zuwa min idanu, "Gashi nan!" Ya fada yana mika min, kuka na saka ina faɗin. "Abba kayi hakuri." "Shi kenan, ki shirya zaku tafi jibi!" Dangwara tiren nayi ina faɗin. "Real?" Gyada kai nayi, rungume shi nayi ina ihu "Abba na gode sosai!" Ma faɗa bayan na sake shi, fita yayi can sai gashi dauke da wata gora. Mikawa Hajja yayi ya ce mata. "Maganin baki da farin jini don takwaranki bakin jini ne da ita babu mashinshini!" "Abba ina da saurayi Uwais!" "Kul na sake jin sunanshi a bakinki!" Inji Hajja, kafin ta ce mishi. "Batun auren Irak ba zai yiwu ba, tun bayan ba nake son gaya maka." "Abba ki kyale Baba Malam Umaru ko wancan satin ya gaya min amma abinda zai yiwu nake fatan haka, ita me martaba ya bukata ba wata ba." Murmushi tayi ta ce mishi. "Tunda nake a rayuwata Dan uwana bai tab'a fada min abu bai faru ba, don haka mu barwa Allah ikonsa!"
Kallona yayi ya ce min, "Zaki tafi amma akan one condition!" Kallonshi nayi nace mishi. "Abba one condition?" "Eh ai ke ba yarinya ba ce duk abinda ya faru ki gaya min kin ji ko!" Murmushi nayi nace mishi. "Ok Abba in sha Allah za ayi haka!" Na faɗa ina barinsu dakin na wuce part din Mommy Turai, ina zuwa na ga kofar a rufe, kwankwasawa nayi Tauhid ya bude min, da sauri na shiga dakin da Iram na same ta tana kuka. "Baby Abba ya amince mu tafi?" "Da gaske?" Naji Muryar Mommy Turai, juyawa nayi ina murmushi na ce mata. "Eh! Amma Mommy me ya same ta?" "Akan Abbanku ya ce ba zaki bi mu ba ne!" "Tow ai ya amince, sai ki daina kuka gani nan na gaya miki zan je."
Dakyar Iram ta daina kuka tuni ta ware muka shiga tsara inda za muje. Domin daga Dubai Bangkok zamu tafi na Thailand ta ce Mommy tana da wani abin da zata yi na kasuwanci, sai China inda take odar kayan daki da na kitchen, musamman wanda take sayarwa da kuma na auren Iram din, daga nan sai mu dawo Nigeria.
Hajiya Turai na fita ta nufi daya dakin ta kira Hajiya Layla. Bugu daya tayi ta ɗauka. "Ke dai wallahi baki da mutunci, ina tsaka da jin dadi zaki kira ni." Tsaki tayi ta ce mata. "Banza zamu tawo Dubai don haka ki saka hoton da zan turo miki a kan Apps ko zamu kwashi dami akala."
"Ke wacce kenan?" "Tow!" Ta fada bayan ta kashe wayar ta tura mata hotonan Ikhlas guda biyu.
****
Wherehouse
Gida ne falle can dokar dajin domin ba zaka tab'a tunanin wannan dangun dajin zai samu irin wannan gidan ba, amma son zuciya irin na mutane gandun daji ce dajin Allah aka ware fili aka zuba gida me Bala'in kyau da girma kana aka ware wani shashi na musamman ana aikin sarrafa jikin bil'adama ana fita da su ana sayarwa, musamman koda da zuciya an fi sayansu sama da kome.
Yan mata biyar aka kamo suna ihu suna kome aka wuce da su cikin bangaren nan, aka zubar da su a kasa. Ƙatuwar sufanan babbar motar wani karjejen kato ya makawa daya daga cikin Yan mata ta fadi tana wani irin fisga domin ya same ta ne a tsakiyar kanta. Sauran yan mata hudu tuni tsoro ya kama su. Shigowar wata ƙatuwar Nissan versa 10 2024, baki wulik ta yi parking a daidai kofar mahautar bil adam,wata hamshaqiyar mace ce ta fito daga cikin motar idanunta sanye da tabarau baki, murmushi take ta na faɗin. "A fito da sauran yan matan su dauki darasi akan wanda ya bijire mana."
"Tow Hajiya Layla ikon Allah!" Inji daya daga cikin mutanen, fita suka yi can sai ga yan mata a kiyasti sun kai kusan dari, suka fito aka jera su, suna kallon yar uwarsu aka saka adda aka datse kanta. Jinin ya zuba a jikin kowa a wurin har da Hajiya Layla wacce ta saka hannuna ta laso jinin ya saka a bakinta. "Idan kun gadama ga kofa can a buɗe ku fita daga yau kada a kara rufe kofar gidan nan ko dare ko rana duk wanda yaso ya fita shi ya san yadda zai amshi sakamakon. Ina bata tab'a mu'amala da kowa ba, saka wancan kwaryan ka tari jinin, sannan a ware min Yan mata, kamar shida a musu passport, na Bangkok akwai wasu yan siyasa da suke da wani taro na musamman a can a kai yan matan bangaren yar Chadi a gyara musu jiki. Sannan a kwai wani abu daya a ware min dakin na musamman da alamu zamu yi bakuwa nan da sati biyu anan zata zauna."
Ta fada tana murmushi, kafin ta daura da cewa. "A bani yan mata biyu su min tausa." Ta wuce tana me nufar cikin gidan yan matan suka bita, wayarta ce tayi ƙara bodyguard dinta wata karffafiyar mace ta mika mata. "Allah ya taimaki Madam zaki shigo? Tow Alhamdulillahi bari na saka a zab'a miki yan mata na musamman ina godiya!" Can ta kuma cewa. "A'a ni zan saka a zab'a miki ai nasan baki son ragowar kowa sai naki na ji yanzu haka za ayi!"
A cikin yan mata shida da zasu tafi Bangkok aka kara ware yan mata uku, aka fara musu wanka da kayan kamshi wankar a aka musu na karshe dafaffiyar madara ce aka zuba mata kayan kamshi suka shiga cikin suka zauna sai da suka jima a cikin sannan saka fito aka basu wani irin ruwa suka yi wanka wanda saboda kamshin ruwan sannan suka fito aka shiga goge musu jiki da wani audiga daga yadda ake gyara musu jiki kowacce ta sha jinin jikinta bakuwar su mai muhimmanci ne, bayan sun gama aka kai su dakin, wurin karfe biyar na yamma aka ce bakuwar tazo. Amma da tazo meeting dinsu suka shiga yi, basu fito ba sai karfe goma. Jagora Hajiya Layla ta mata sannan ta rufe kofar, tana shiga yan matan da dama sun san aikinsu suka rufe ta tare da taimaka mata ta cire kaya, sannan suka rufe hannunta zuwa ban daki suna masu riketa har ta shiga wanka, suna taimaka mata har ta fito sannan suka daura mata towel suka riko hannunta, zuwa dakin kafin suka cire mata towel din, kwanciya yayi suka fara mata tausa da goge mata jiki, dukkansu babu wanda zai ce yasan fuskantar, domin wutar dakin babu haske sosai mai duhu ne, suna cikin mata ta kamo daya daga cikinsu ta fara masha'a da ita duk sauran suka rufa mata.
Bata bar dakin ba sai karfe biyun dare, don ta gaji yaran ma sun mata kokari duk da sabin hannu ne nufar waje tayi ta saka kayanta. A babban parlourn ta hadu da Hajiya Layla tana shan wine. "Dazun kin ce min Turai ta turo miki hoto ina yake?" Mikewa tayi ta dauko tap din ta mika mata. Hoton Ikhlas ce tsaye kanta babu dankwalin sai tulin gashin kanta, riga da skirt ne a jikinta. "Akwai wata da take son mace irin wannan a nan nahiyar Afirka, sai dai ban kai ga samu ba sai ga shi kin samo min ita nawa ta saka domin nima tayi min akwai wani abu na musamman a tattare da ita nawa ne?"
"Hajiya Turai tace last 2 million dollars!" Juya idanu tayi tana faɗin. "Shekarunta nawa?"
"19yrs tana karatu a bangaren Jarida " "bana bukatarta." Ta fada tana mikewa.."Hajiya akan me?" "Tayi wayo dayawa yaran da basu kai matakin secondry school nake bukata wannan duk inda muka kaita a duniya zata dawo kuma ita ba abin yarda ba ce ki gayawa Turai kada ya saka rayuwar sana'armu a hatsari. Wai ma a ina ta samo ta?" "Yar kishiyarta ce!" Takaici ya rufe matar daka mata tsawa. "Hauka kuke yi? Idan Uwar Yarinyar tana addu'a lalata mana kome zata yi, don haka kada na ji labarin ko Bangkok ta ketara da yarinyar domin haka zai iya saka a kama yan team dinmu kin ji dai!" Daga haka ta bar parlourn, ita kanta ta san wacece Hajiya Suhaima!
Lauya ce da takai matakin SAN, duk wani ta'addanci da ake ayi a garin Zanzabira ita ke bawa kowa mafakar siyasa ko ta shara'a ba a tab'a nasara akanta ba, sannan ita kanta kasungurman matsafiya ce, tana cikin hadaddiyar kungiyar Matan alfarma da suka ga duniya sannan kafin ina shiga kungiyar sai an ga wani irin value kake dashi. Kungiyar tana da tasiri sosai musamman yadda suke bin ƙauyuka suna tallafawa mata, sannan suna janyo marayu suna basu ilimi a baki, a zahirin gaskiya kuma safara da fataucin sassan jikin mutane suke yi, a karkashin wannan kungiyar akwai kungiyar karuwai matan aure da yan mata, duk wani kazamta suna da ita,.amma bayan nan basu yarda da mata ta dauki yar kishiyarta ta ce zata saka a harkan ba domin akwai wani barazana da suke ganin zai iya faruwa akan haka. Fita tayi tana jadaddawa kada a fara kuma kada ta ji labarin haka. Ai kuwa tana fita Hajiya Layla bata koma cikin gidan ba, ta kira Hajiya Turai. "Ke ki dakatar da tafiya da Yar kishiyarki domin akwai matsala." "Na saka buri akanta ko ban bawa kowa ba sai na saka an lalata min ita domin ina jin ciwo na bude idanuna na ga Iram da ciki You know what I mean, sannan You know how much I love Iram don haka ba zan." "Tow SAN ce ta ce a gaya miki!" Ajiyar zuciya ta sauke ta ce mata. "Shi kenan zan tafi da ita amma ba da wannan manufar ba! Amma na bude idanun na ga abinda yake faruwa da Iram wai tana laulayin cikin wani shege ji nake kamar na bindigeta!" "Amma ba ita ba ko?" "Tow ya zan yi kowaye ya mata ciki Allah ya tsine mishi albarka domin ya zalunce ni!" "Ke ba mamaki sau daya ne, idan aka zubar da shi ai kome ya wuce sai a mata gyara ciki da waje." Murmushin takaici tayi ta kashe wayar. "Shegiya me wayo kin ci kudin budurcin yarki ai! Ai zuru bata ci zuru ba." Wato a wannan harkan ilimi ake yi.
****
Murmushi Turai tayi ta ce a ranta, "Layla kin yi kuskure zan rama, kamar yadda kika nuna min ba kome nima na dillantar da Nadra ai rama cuta ga macuci ibada ce." Ta taso daga gadonta ta dauki Tap dinta ta shiga gallary na tap din, hoton wata yarinya ce da bata wuce 19yys ba ya fito. Daukar wayarta tayi ta kira wani waya. "Lucky ga yarinyar nan ba tura maka ta wancan mail din, ka tabbatar an yi daga-daga da Virgin dinta, ni zan bawa Yarinyar lasisin shiga bariki, kafin nan ka nima min Anaconda ina da babbar harka."
****
Salmanu Faris
Juyawa yayi yana taku a hankali. Kafin ya juya ya ce mishi. "Kai da Abba na lura kun mai dani Dramaandra ko? Ko Amita bacha wanda zai kawo a gaji idan al'umma sun shiga wata masifa." Ya fada yana me nad'e hannu a kirjinshi. Sannan ya ce. "Faruq ni ne Bahubali dinsu nake tsammanin!" "But sir is too harsh, ka duba lamarin...
*Hajiata indai kinsan kina Neman jaka da takalmi na fita kunya na alfarma na shiga taro na zuwa villa,to gaskiya kawata karki wuce group dinnan domin kuwa akwai luxury bag's unique shoe's jewelries iya ganinki,hmm baa cewa komai dai ki shiga idonki ya gane Miki yar uwa*
Top_notch season 4 ROYAL POLITICS is not free, pay N500 to get a complete access to the book.
*Marubutan TopNotch Writers sun sake zuwa muku da sabon labarai masu ƙayatarwa a tafiyarsu ta Season Four:*
*MAI_DAMBU kuwa ta faso muku ne da labarin da ya haɗa da Sarauta, Siyasa da kuma Soyayya, duka a littafin ROYAL POLITICS: An yanka ta tashi.*
*AZIZAT kuma ta tattaro muku rikitacciyar soyayya ne da ya hawo jirgin JayKay ya dira a Kitchen ɗin Ziyada. CHEF ZEEY: Love in the Kitchen*
*Account Details:*
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
*POSTING*
*Ɗaya: 500*
*Biyu: 1000*
*Uku: 1500*
*DOCUMENT (da zaran an gama posting zai koma)*
*Ɗaya: 1k*
*Biyu: 2k*
*Uku: 3k*
domin tura shaidar biya ko Ƙarin bayani, ku tuntuɓi:
*08130269641*
Ko
*08137311900*
Ko kuma
*09063467258*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: ROYAL POLITICS 🔥
_An yanka ta tashi_
Ramlat A Manga
Mai_Dambu
TOP-NOTCH SEASON 4
Sadaukarwa ga Auntyna RUKAYYA GOMBE 🥰 🤩 😍
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HYpizDjKAkJB4QClSeLTvw
*Hajiata indai kinsan kina Neman jaka da takalmi na fita kunya na alfarma na shiga taro na zuwa villa,to gaskiya kawata karki wuce group dinnan domin kuwa akwai luxury bag's unique shoe's jewelries iya ganinki,hmm baa cewa komai dai ki shiga idonki ya gane Miki yar uwa*
10
Bude baki yayi da niyyar magna amma Nady ta kira shi, share kiran yayi can ta kara kiran shi. "Babe ka manta ne yau zamu fita cin abinci a waje?" A kowacce karshen wata suna fita waje cin abinci. Shafa kanshi yayi yana jin wani irin yanayi kafin ya ce mata. "Ina hanya!" Sannan ya kashe wayar, ya kalli Faruq sannan ya juya tare da barin parlourn. "Na yarda da kai yasa na gaya maka, har da Iram a tafiyar kuma ita ce Mai Martaba ya zab'a domin a daura aurensu." "Kamar Ya? Auren Iram take da Mai Martaba mata hudu gare shi." Gyara tsayuwar shi yayi ya ce mishi. "Ya tabbatar da ya ba da wani sako a cikin gidan, ban san waye ya bawa sako ba, amma ya ce sakon zai iso ana saura kwanaki ƙalilan daurin auren." kallon Malam Junaid yayi yana me dauke kai ya fita daga cikin parlourn. Koda suka fito waje kallon Faruq yayi, murmushi Faruq yayi ya ce mishi. "Kayi hakuri ka duba lamarin." "Akan me? Ba Matarshi ba ce me yasa ba zai iya dakatar da ita ba?" "A wannan rayuwar dayawan mutane suna ji suna gani basu da abinda zasu yi, kuma idan suka ce zasu yi dole su fuskanci wata rayuwa. Babban damuwarshi Yaranshi mata, gaskiya Malam Junaid na Uba ne na gari!" Tab'e baki Dr Faris yayi ya kwantar da kanshi a jikin motar yana jin kamar yayi ta rusa ihu. Haka suna cigaba da tafiya har zuwa gida, ganin motar asibiti ta shiga Yayari Estate, yasa shi kallon kofar. "Na je na duba ne?" "Hmm!" Ya fada yana gyara kwanciyar shi a jikin motar. Can mansion dinsa aka wuce da shi, "Zaka iya tafiya!" "An gama!" Inji Faruq, yana parking ya fita ya bude mishi, shima ya fita sannan Faruq ya dauki kayan bukatar shi ya kai mishi cikin gidan, kafin ya dawo yayi mishi sallama.
***
Kasancewar kasuwar ta yamma ce ana ci har dare, a wannan lokacin Jigal bai da aiki sai dai ya fita yayi amsar kudaden mutane, wanda dayawan mutane tsoronshi suke ji, haka ya bawa Kamal dama ya nufe shi da wani irin sauri ya suka mishi wuka ta baya sai da ya fito ta gaban cikinsa, abinda ya saka shi fasa ihu, ya sake cire wukar ya kara caka mishi, sai da ya kara fitowa ta cikin shi, jini ne yake malala ya durkusa akan gwiwarshi yana dafe ciki, cikin rashin imani ya saka wukar yanke wuyar Jigal sannan ya fadi a nan wurin yana kakarin mutane mutane kan sun gudu babu kowa a wurin. Lashe jinin yayi yana shafawa a fuskarshi, sannan ya bar wurin da gudu. Kai tsaye gidan Jagaba ya nufa, yana zuwa ya same shi da Yara zasu fita. Ganin shi cikin jini yana haki. "Na kawar maka da abin harin saura waye?" "Kashe Jigal?" "Oga kira ka ji labari!" Ai kuwa kafin ya kira wani dan sanda ya kira shi ya gaya mishi, abin da ya faru. Murmushi yayi ya ce mishi. "Muje yau zaka bar garin nan domin akwai shara."
Ciki suka shiga ya saka yayi wanka sannan ya nufi wani daki ya kwaso kudi da abubuwa dayawa ya ce mishi. "Zaka tafi kayi shekara daya a can, iyayenka zamu ji dasu kai kuma ka zauna a can idan lokaci yayi da kaina zan zo daukarka"
"Godiya nake" dafa kafad'arshi Jagaba yayi ya ce mishi. "Kada na ji labarin ka farmaki wani sannan ka jira sakona a koda yaushe, ka fara sana'a kada ka yarda a rena ka, kada kuma ka yarda yan sanda su saka maka idanun ka shiga cikinsu ta haka ne zaka zama ɗan gida." Haka ya dauke shi sai wurin wani drivensa suka bar garin.
--- Labarin mutuwar Jigal ya sami Goga tana gaban Khalifa Nafi'u Shaibah da Ahmad Rilwani Yayari, mikewa yayi da sauri ya fita a gidan yana gudu yana faɗin. "Kada ka mutu, kada ka mutu don Allah ka jira ni." Har ya isa inda abin ya faru wanda ba karamin nisa ba ne da wurin, yana zuwa ya sami gawar Jigal, zubewa yayi a kasa tare da fashewa da kuka, wanda rabonsa da yayi tun rasuwar Mahaifiyarshi, yau gashi duke gaban gawar Jigal Yaron nan Maraya ne, shi ya fara saka shi a wannan harkan gashi yau an kashe shi ba tare da ya kare rayuwarshi ba, yadda yake kuka sai ya baka tausayi domin akwai wata irin shakuwa a tsakaninsu, wanda yasa yake jin Yaron kamar jinin jikinsa. Haka aka ɗauki gawar yana ji yana gani suka nufi asibiti. Koda yau zai bar daba sai ya rama wannan wulakancin da aka mishi.
***
Mr and Mrs Faris.
Babban hotel mafi girma da daraja suka nufa domin cin abinci, tun aurensu haka suke yi. Koda suka isa yadda yake kaf-kaf da ita yasa ta kara nutsuwa akan shi domin tana son irin wannan soyayyar balle kuma akanshi gani take da tana da yadda zata yi da ta cire abinta ta saka mishi a cikin aljuhunsa yayi ta yawo da ita, waiter har mutane biyu ne suka zo kansu, mika mata menu na abincin aka yi ta fara zab'a, bayan ta gama ta nuna musu. "Beb duba ka gani." Amsa yayi yana kallon Waite din ya kara miki mishi, zuba mata idanun yayi sai lokacin ya lura da shigar da yake jikinta. Ranshi ya b'aci sosai kasa kasa ya ce mata. "Me yasa kika yi irin wannan shigar?" "Kai Babe meye illar shigar? Na ga dai ba wani abu ne." Ta fada tana murmushi. "Illa ce domin ke matar aure ce!" Cire coat dinsa yayi tare da mikewa ya saka mata, wayarshi ya zame kasa, bin wayar tayi zata dauka ta ga sako ta email dinsa na ya samu ticket din Dubai. "Beb Dubai zaka?" "Na zata Germany zaka?" Bai saka ranshi ya amshi wayar ba, don kada ta daura zargi a kanshi. Don haka ya saka mata rigar sannan ya koma ya zauna ta cigaba akan wayar tasan kome na akan wayar ganin Booking da yayi daga shi sai Faruq yasa ta zuba mishi idanunta masu shegen kyau. "Babe kaɗai da wancan punk din zaku tafi? Wai Beb me yasa ka damu da shi ne. " Abincin aka kawo ya gyara zamanshi ana ajiye abincin shi babu ruwanshi da wani zance. Kallon yadda take son d'aga mishi hankali ya mika mata hannu, ajiye mishi wayarsa tayi ta dauke kai kamar zata yi kuka. Ihun mata da ta ji a can gefensu yasa ta juyawa matan wani dan siyasa ne suke fada shima dan siyasan gashi zaune. Daya na cewa karuwa yar iska me bin maza, bata tsaya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 13