Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yaki ci ya ki sha, daga haka ya kwanta bai da lafiya har na tsawon kwanaki." Murmushi Jagaba yayi ya karasa mishi labarin. "Macijin ya hadiye me kiwonshi, banbancin Maciji da kare a bayyane take shi kare baya ciwon ubangidansa. Yunwar wa kake ji na ciyar da kai da jininsa da namarsa!?" Murmushi cikin jin dadi ya ce mishi. "Ka tura yara office din Yan sanda domin rufe case din Joy!" "An gama haka ya maka?" Jagaba ya tambaye shi. "Yayi!" Min inji Musharraf, "Ranka ya dade shi kuma yunwar fa?" "Da lokaci har yanzu ka cigaba da biyayya." Ya fada yana juya ruwan whisky din hannunsa. ** Tsaye yake a gaban window ya harde hannunsa a kirjinshi. Tun safe da ya shiga wurin Mai Babbar daki, ta ce mishi. "Ba laifi ba ne idan bata san al'adarmu ba, amma kuskure ne tana biyewa wasu matan a gefen hanya tana haushi kamar kare, abin kunya ce na d'aga kai nayi magana akan wacece Surukata. Ba laifi zata iya daukar duk wani irin mataki, amma me yasa baka gaya mata tana cikin gidan da ba koda yaushe ake sake numfashi me karfi ba domin akwai daliban sanin halayyar dan adam, don haka na baka lokaci ka nimo y'a daga cikin gidajen Baffaninka ko kawunanka waɗanda zasu iya jure kowacce ihu." "Allah ya huci zuciyarki," wannan shine abinda iya fada, amma tabbas Nadiyyah ta ballo mishi ruwa, bai san yadda zai yi da ita ba, amma da yana da wata hanya da ya dakatar dà haukarta. Yanzu babban damuwarshi zarginta da ake yi mata. "Sun isa gida lafiya?" Inji Faruq da ya shigo dakin. "Hmm!" Ya fada yana tsaye, bayan kamar minti goma ya juya yana kallon Faruq. "File din nan?" "Suna gida!" Gyada mishi kai yayi. Kallon window yana hango zirga-zirgan mutanen da suke wucewa. "Muje gidan ko?" Ya fada bayan ya juya. "Tow Yallabai!" Sai da ya fita Faruq ya haɗa kome ya bi bayansa. Har gida suka isa. Kalaman mai Babbar daki yana kara tab'a shi. "Haihuwa muke bukata, idan da ta haihu da zasu amma bata haihu ba kuma tana irin wannan shirmen bai dace da gidan nan ba." Taya zai gaya mata aurenshi da Nadiyyah babu wannan batun kara auren. Iskar bakinshi ya fesar sannan ya kwantar da kanshi jikin kujeran motar, idanunsa lumshe. Bude motar Faruq yayi ya shiga wurin tukin motar suka asibitin. Lokacin da suka isa gida Nadiyyah ta tafi gantali ita da kawayenta. Dakinsa ya shiga yayi wanka da alola sannan ya wuce masallaci tare da Faruq, ko kafin su dawo Mr Brandy ya gama mishi abincin, ci yayi kafin ya wuce dakinsa sannan ya janyo pillow, ya jefa a kasa ya kwanta cikin sanyin jiki. Tashi yayi zaune da ya tuna bai jima da cin abinci ba ya kwanta. *** Pastor Mathew Yana zaune tare da Alhaji Nafi'u da Malam Imran Bin Daddar. "Wato Pastor Mathew anyi kuskure." D'ago kai yayi ya kalli Malam Imran Bin Daddar. "Malam ba kuskuren ba ne abin dubawa, yadda zamu gyara alakarmu ne, yarinyar Joy ita ɗaya iyayenta suka haifa yanzu ya zamu yi da su?" "Pastor Mathew ka manta waye ni? Shi yasa na tawo maka da Imran don nasan shima abokin cin mushenka ne. Kada ka manta dukkanmu muna karkashin abu daya ne, idan ka so zaka iya hada karamin rigima. An kashe Joy saboda ta yi leken asiri ta san abinda bai dace kowa ya sani ba me zai hana a haifar da wata yar karamar hatsaniya a dan yi asarar dukiya da rayuka yadda zamu gyara alakarmu. Mu gwara kan addinai guda , idan ka amince ga wannan idan baka amince ba zamu samu iyayen Yarinyar baka san me zamu gaya musu ba " numfashi ya sauke tare sa jan jakar ya bude sabin takardan dollars ne cikin jakar. "A kashe kamar rayukan mutane ashirin a kona kananun shaguna talatin mu kuma anan zamu cusa musu kiyayyar juna. Matuƙar Ubangida yana raye ba zamu bashi kunya ba." Dariya suka saka tare da mikewa suna faɗin. "Ga abu a fili, ka tsaya zaka yi gardama bayan nasan matuƙar da wannan tow ba mamaki kome zai zama me sauki ne a wurinmu." Inji Imran Bin Daddar. Sun isa gidansu Joy Moses, abin tausayi Uwarta sai tashi take tana faduwa an kashe mata yarinya. Sun yi musu ta'aziyar rashinta, sannan suka bada hakuri da abinda ya faru. Alhaji Nafi'u ya ce . "Ni Nafi'u Shaiba nayi alƙawarin biyawa muku zuwa Jerusalem, domin aikin Ibada. Sannan zamu yi magana da gwamnatin jahar nan mai adalci akan ayi adalci akan duk wanda suke da hannu akan mutuwar yarinyar nan, ina me baku hakuri ." Yadda iyayen suke kuka yasa shima share kwalla yana girgiza kai kamar da gaske abinda ya faru kenan. Bayan sun basu abinda suka zo da shi, sannan suka fito. Pastor Mathew ya mikawa Alhaji Nafi'u hannu. "Ka tabbatar yau an tsara kome ni kuma zan yi nawa aikin!" Ya fada yana kallon Imran Bin Daddar. "In sha Allah, nima zamu haɗu da mutanena mu bada goyan bayan da ya dace." Daga haka suka bar unguwar Morocco anan galibin christocin suke da zama da suka bar cikin hausawa suka dawo wannan unguwar sannan akwai daidaikun muslmai a cikin unguwar. * 7:23pm Saka links din rigarsa yake, Faruq ya tashi motar yana jiransui. Wata mota ta shigo da ita cikin gidan, fitowa tayi daga motar tana murmushi. "Na gode sosai, in sha Allah ku yi arrange din kome kafin na zo!" Ta fada tana d'agawa mai motar hannu. Bayan ya fita ta juya idanu hudu suka yi da Prince dinta. Gabanta ne ya fadi saboda irin kallon da yake bin ta da shi. "Prince!" Zuwa yayi ya shiga motar Faruq ta tashi motar. Bai ce mata cikanki ba koda ya dawo ma bai kulata ba, haka tayi ta niman hanyar da zai kulata. Wurin karfe goma na dare ta shiga dakinsa. Yana aiki a laptop. "Aslm Prince!" Bai amsa mata ba. Zuwa tayi gabanshi ta zube akan gwiwarta. "Sorry Babe ba zan kara ba!" Nan ma shiru yayi mata don bata ji tun kafin su iso Najeriya yake gaya mata gidansu ba irin kowani gida bane, baya son ta dauko mishi magana. Amma da yake bata jin magana. Haka ta gama magiyarta bai ce mata cikanki ba. Karshe ta fita ko kallon inda take bai yi ba. File din nan da har yau ya kasa budewa ita ce, yayi kumdunbalar budewa tare da rintsa idanunsa, yana tsoron me zai gani 1990 *BLACK CAT* CULT. Abinda idanunsa ya fara gani kenan a pagen din farko, da sauri ya rufe files din gabanshi yana faduwa, da sauri da sauri sakamakon wani abu da ya shiga kanshi ya mishi Flashing din wani abu da ya tab'a faruwa a wani wurin.... Top_notch season 4 ROYAL POLITICS is not free, pay N500 to get a complete access to the book. *Marubutan TopNotch Writers sun sake zuwa muku da sabon labarai masu ƙayatarwa a tafiyarsu ta Season Four:* *MAI_DAMBU kuwa ta faso muku ne da labarin da ya haɗa da Sarauta, Siyasa da kuma Soyayya, duka a littafin ROYAL POLITICS: An yanka ta tashi.* *AZIZAT kuma ta tattaro muku rikitacciyar soyayya ne da ya hawo jirgin JayKay ya dira a Kitchen ɗin Ziyada. CHEF ZEEY: Love in the Kitchen* *Account Details:* *5921536136* *RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN* *Moniepoint MFB* *POSTING* *Ɗaya: 500* *Biyu: 1000* *Uku: 1500* *DOCUMENT (da zaran an gama posting zai koma)* *Ɗaya: 1k* *Biyu: 2k* *Uku: 3k* domin tura shaidar biya ko Ƙarin bayani, ku tuntuɓi: *08130269641* Ko *08137311900* Ko kuma *09063467258* [7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: ROYAL POLITICS 🔥 _An yanka ta tashi_ Ramlat A Manga Mai_Dambu TOP-NOTCH SEASON 4 Sadaukarwa ga Auntyna RUKAYYA GOMBE 🥰 🤩 😍 _Na gode sosai da addu'o'inku Allah ya bada lada, idan ta mu tazo Allah yasa mu cika da imani. Allah ya kyautata tamu bayansu Na gode sosai_ 05 #Coincidence "Kai Jigal ku tattara mana kayanmu." ya fada yana kallon Mutumin da yake rike da bindiga. Fadawa ne rike da sanduna, abin ya basu mamaki sai yan taurin cikin fada suma suka fito da bindigar toka, suka zagaye su. Ni dai yau na ga lukutar masifa, domin kuwa abin da yake shirin faruwa. Ina ga kamar rayuwata ce a garari. "Ka sake yarinyar nan ka wuce mu tafi kaga mun kama Yaranka." "Ba zan kyaleta ba, sai dai na kyale gawarta." Motsi nayi naji ya daka min tsawa. "Tsaya min ko na yanke makogaronki." Haka yasa na tsaya kamar ba na raye. D'ago kai mutumin da suke tare da mai bindigar fuskarshi sanye da face mask yayi ya ce mishi. "Tow ka kashe ta bar nan!" Ya fada yana me juyawa abinsa tare da mai bindigar. Wani irin tashin hankali na shiga na ce musu. "Yanzu haka zaku bar ni? Haka zaka kyale ni? Me yasa ? Me yasa rayuwar dan Adam bai daraja ne? Meye amfanin bindigar hannunku. Kashe ni zai yi fa, don Allah ku taimake ni, ku taimaka min kada ya kashe..!" Ni dai ban san me ya faru ba, sai dai na ji wani abu me karfin gaske ya wuce da karfi tare da wani irin huci me zafi , ihun da yayi haɗe da faduwa yasani jin kome ya tsaya min domin nima suma nayi. Faduwar da yayi wnada yayi daidai da zuwan yan sanda yasa aka kwashe su daga shi har Yaransa zuwa state Headquarters na Yan sanda, ni kuma asibitin da yake kusa da Fada aka kai ni, shi kuma wanda suka sara aka wuce da shi babban asibiti da sanda. ------ Bayan an kawo ni asibiti karin ruwa suka min sannan Yeemar ta kira shugaban gidan Radio ta gaya mishi. Tana wayar wata Nurse ta zo, katse kiran tayi ta kalle ta. "Ki zo ana kiranki!" "Tow!" Daga haka ta bi bayan Nurse din, zuwa wurin kiran ganin ba likita ba ne ta kalle shi. "Kace Yeemar Omar ko?" Eh ta fada tana murmushi don ta gane shi, shine wanda ya fara harbin farko. Sai dai wani abu ne ya zo kanta. "Sir amma harbin da aka yi ba kai ne ka yi ba ko?" "Eh mai gida ne yayi, shine na zo a madadinsa na baku hakuri." "Ba kome ai ceton rayuwarta yayi." "Eh tow!" Ya fada yana kallonta. "Ina take?" "Tana cikin dakin!" Shiru yayi kafin ya sosa kanshi yana murmushi. "Ki gaishe ta!" Wayarshi ce tayi ƙara ya ciro a aljuhun gaban rigarshi, Sir ya gani da sauri ya juya yana d'aga mata hannu. Sake baki tayi tana kallon yadda yake gudu, can ta tab'e baki ta shiga cikin dakin. "Ja'ira." Ta fada tana make ta. *** Headquarters of police Minti goma da kawo su, sai ga Kwamishinan yan sanda, hankalinsa a matuƙar tashe. "Wani dan iskan ne ya kamo su?" Shiru sauran officer din suka yi, yayi fada kamar zai dake su. Shigowar inspector Mu'azzam Adnan ya shigo office din, "Waye ya kamo Yaran nan?" "Sir ni ne?" Juyawa yayi ya kalle shi kafin ya ce mishi. "Waye ya baka izinin kama su?" "Sir daga kofar fada aka bada izinin kama su." Ya fada a hankali, "Wani dan iskan ne zai baka iznin kama su?" "Ni ne!" Ya furta daga bakin kofar shiga office din, inji Salmanu Faris da ya shiga office din, Faruq yana take mishi baya duk da haka babu wanda zai ce ya ga fuskar shi domin cikin face mask yake amma da alamu CP yasan kowaye shi. Kwarjinin da cika idanu da yayiwa CP yasa lokaci guda ya cire hularsa. "Mai martaba kai ne da kanka? Ai da ka gaya min da nayi maganin abu, ba sai ka zo ba. Yaran nan sun cancanci a kama su sannan zamu mika su ga kotu ta hukuntasu." Juya kai yayi kafin ya ce mishi. "Shi kenan idanuna yana kansu!" Daga haka ya juya suka bar office din. Mikewa Goga yayi ya ce mishi. "CP kasan dole na bar office din nan domin mutumin Jagaba na tab'a idan na kara awa daya a wurin nan tabbas Uwata sai dai ta haifi wani. Don haka ka bude ni da Yarana mu tafi! Sannan ka ga jinin da nake zubarwa." Hararansa yayi yana me barin wurin. Bayan kamar minti goma, sai ga daya daga cikin jami'an gwamnati wanda kowa yasan shi shahararren dan bangan siyasa ne. "Bana kashe rigimarka da jagaba ba? Me yasa zaka dauki doka a hannu?" "Zuciyata ce ta kasa samun nutsuwa shi yasa na farmake shi!" Wucewa office din CP yayi, bayan kamar minti goma suka fito aka bude shi, da Yaransa suka bar Headquarters din. ---Karfe hudu na yamma na farka gidan muka wuce da Yeemar MD sai kiranmu yake yana son jin meke faruwa,tunda na amsa na ce mishi don Allah kada ya kara kira lafiya nake. Da muka isa gidan ma ba kwanciya nayi, Maluma take tambayar me ya faru Yeemar ta ce mata. "Jiri ne ya kwashe ta muna aiki!" "Hmm bata ji wasa take da cikinta ba dole ta fadi ba!" Ta wuce daga haka murmushi nayiwa Yeemar na ce mata. "Na gode sosai!" "Nima haka xan tafi office nayi report." A hankali na ce mata. "Na gode sosai!" Bayan tafiyarta Abba ya dawo ya kalle ni, yadda nake tsakuran abincin ya ce mim. "Yau me ya faru?" "Fadar Daba ce ta ritsa da mu!" "Me kika je yi?" D'ago kai nayi nace mishi. "Mun je aiki." "Ikhlas a kodayaushe ina son ki gane bana son shigarki rigimar da babu ruwanki." "Abba baka yarda ba ne?" "Na yarda dake mana." Daga haka ya mike tana faɗin. "Nuraim ya je dauko Hajja!" "Alhamdulillahi Drama Queen ta dawo." Na faɗa ina dariya. *** Unguwar ganuwa Unguwa ce ta talakawa da duk yadda za a kwatanta maka tow da gaske sai ka nutsu zaka fahimci yadda unguwar yake, saboda yadda unguwar yake kamar irin zamanin da can, har gara zamanin da akwai cigaba amma wannan unguwa babu wani abin more rayuwa, domin tsohuwar unguwa ce a ta haura shekaru dari, asalin gine-ginen da suke cikin unguwar ta irin ta jar kasa ce, wanda ka gani yayi ginin zamani Yaranshi ko shine yayi kokarin fitar da kanshi daga old model. Gidan Malam Adamu, gida ne babba wanda me dauke da mata uku da Yara sama da goma sha daya. Maza da yan mata, galibinsu kanana ne kuma gidan ba karamin fitina ake ba domin kuwa kishi ake a gidan har da na hauka. Dan Uwar gidan mai suna Kamal ne.ya fito matashi ne da bai wuce dan shekaru goma sha Bakwai. Yadda ya fito daga dakin kwanansu mika yayi yana zare idanu kamar wanda aka mishi karya. "Yanzu Kamalu baka yi sallah safe ba don Allah?" Inji Rakiya matar Babansa ta uku. Ita ce mai dama-dama, domin ita har islamiyya Malama tabawa tana zuwa, Yaranta kuwa suna da sauki rashin jin magana. Cikin rashin mutunci irin na wanda aka daurewa kugu ya kalleta ya ce mata. "Maman Mujahid babu ruwanki da ni, munafuka kawai." Ya fada yana nufar kofar dakin Uwarsa. D'aga labulen dakin yayi ya hango uwarsa tana sharar barci ya ce mata. "Iyah!" Firgit ta farka tana faɗin. "Dan nan Lafiya?" "Iya ki shiga tsakanina da kishiyarki don wallahi sai na burmeta." Ya fada yana sauke labulen da sauri ta sauka a kan gado me rumfatar ta fito waje. "Wai Rakiya ina ruwanki da Dan nan ne? Yaron nan." "Malama dakata min ba fa wani abu na mishi ba, fisabiilillahi taya za ace sai yanzu karfe bakwai zai tashi yayi sallah asuba? Laifi ne don na mishi magana Alh ya baki hakuri." Ya cigaba da haɗa wutar abin karyawan da take don ita ce da Malam Adamu, yana kwance yana jinsu amma bai da wani katabus musamman da ya kasance jiya da yau duk Rakiyar ce take musu abincin dare da na safen yau, Malam Adamu dan kamusho ne, a tasha yake aikin lodi sannan ya samu na cefane, tow da sauki ma idan da cefanen yake idan ya samu kuɗin wurin mai shayi da indomie yake zuwa a soya mishi kwai hudu, da gefen mai shayi akwai me tukuban tsira da tukunya a zuba a cikin kwan shayi kuwa madara rabin gwangwani ake zuba mishi, sai cadbury sachet biyu shayin tayi kauri har tana danko danko, su kuma gidan ya haɗa su da dubu daya, da wata muguwar masara da kwari suka cinyeta, ita zaa jika a wanke sannan a baza ta sha iska, kafin a kaita injin a nikota ta datsa. Azo a ba zata tayi ta shan iska, na dare kenan na rana kuwa Gero mata zata sayo rabin mudu da tsamin kanti sai ashfati, a kawo yan matan gidan su surfa su wanke sannan a kaita nika daga ita sai yar citta mai ra'ayi a cikin s u kenan, wata kan ma haka zaa nikota a kawo a taceta da rariyar tankade, sai a damata a zubawa kowa a kwanon sha a mikawa Uwarsa ya je can su ta fama. Kwana biyu kasuwar ta ja baya saboda karin kudin mai da aka yi matafiya ma sun dan jinkirta tafiye-tafiye da suke. Haka yasa ko ya fita baya wani samun sai dai dan wanda zai kashe. Kullum haka yake koda ya samu baya iya kashe dukka domin matan shi yan bala'i ne, Rakiya ce bata da matsala domin tana sana'a awara da taliya, da yamma ake cika gidan ana sayan awara da taliya. Kasancewar Uwargidansa Iyar Kamal daga kauyensu ya auro ta, wacce suke kira Kande, sai Barirah wacce itama dai yar unguwar ce ya aure ta. Itama Rakiya yar gari ce amma ba a unguwar take ba, daga wani unguwa ya auro ta. Amma yar talla ce a tasha suka hadu, Rakiya tana da zafin nima domin ta taso gidan nima ne Uwarta har kwanan gobe tana sayar da abinci a gidanta da masu tayata aiki. Shi yasa Rakiya itama bata yarda ta zauna haka domin tana shiga gidan ta fara bude haihuwa da Yan mata. Barirah kuwa bata shiga harkan kowa dilaliya ce, ta dauko kayan jagwal a biyo ta a kamata, ita dai Kande ce bata sana'a sai zaman banza da kishin ita ce mai Yara. Yaran Kande biyar yayinda Barirah take da Yara hudu, Rakiya kuwa Yaran biyu ne da ita ga karamin cikin na uku. Daga Barirah har Kande burinsu kowacce ta samu cikin nan domin su haihu kada Rakiyah ta rigasu haihuwa. Kamal shine babba Yaron Kande, kasancewar Unguwar yana hade da yara marasa jin magana shima ya shiga cikinsu ya saje, Yaran basu zuwa makarantar boko da na islamiyya, Yara ne kanana amma fitinarsu tafi ta manya, domin kuwa sune sace-sace dabbobin mutane, shiga gidan mutane dauke musu tukwane ko fasa gidan sabuwar amarya a kwashe mata kayan aurenta. Sai shaye-shaye da fadar dabba. Babban burin Kamal ya shiga tawagar Jagaba, amma duk lokacin da yayi yunkurin shiga sai Jagaba ya kore shi. Ko daren jiya sai da ya je amma Jagaba ya mishi koran kare. Yanzu ma yana farkawa ya wuce unguwar tabkin A, duk da nisan unguwar bai hana shi tafiya ba. Yana zuwa ya samu ana sallah jana'izar Smolli. Jagaba yana can gefe sai busar wiwi yake yana yi yana kallon inda gawar take ana idar da sallah aka ɗauki gawar. Hango Kamal yayi ya kira shi da hannu, zuwa yayi ya ɗan durkusa. "Ina abokanka?" "Suna gida!" Shiru yayi kafin ya ce mishi. "Ga wannan ka dauko su zamu yanzu!" "An gama shugaba" ya bi bayan masu tafiya kai gawa. Bayan an binne shi ya tafi ya dauko abokanshi. Zuba musu Idanu yayi kafin ya ce musu. "Wannan kudin naku ne, da na iyayenku, aiki zaku min sannan zan san yadda zan fito da ku. Ku zaku yi kai kuma ga wannan wukar ka farke min cikin Jigal na hannun damar Goga zaka iya ko ba zaka iya ba?" "Shugabana na zata zaka ce na yanko maka makogaronshi ne?amma haka ma cauuu ce." Dariya yayi idanunshi jajjur ya ce. "Idan ka iya min wannan aikin ni da kaina zan saya maka abubuwa." "Shugaba idan kuma wuyar goga na yanke fa?" Zare idanu Jagaba yayi ya ce mishi. "Hauka ka fara? Goga ko ni karon battarmu bata kyau don lizami tafi ƙarfin bakin kaza ka gane. Ku zamu tafi kai kuma ka san yadda zaka yi ka nimo inda Jigal yake domin shine kawai zan tab'a Goga yayi kuka." "An gama" Kamal ya faɗa, amma shi a burinsa ya datse wuyar Goga. Daga nan Office din Yan sanda ya saka Yaran nan, suka mika kansu a matsayin sune suka kashe Joy Moses, don haka aka fara bincikensu. ** Pastor Mathew A yau Laraba service din yamma da aka yi, ya yi kira da duk wani dan kungiyar da suke zaune a gabanshi. "Kuna tsammanin wannan abin zai wuce ne? Tow ba zai wuce ba kome zasu biya mu, lokaci yayi da zamu dauki fansa don haka ranar Friday zamu dauki mataki garuruwan da suke wajen gari na muslmai zamu far musu ranar juma'a yadda suka zubar da jinin yar uwarmu ba zai tafi a banza ba,.muma Zanzabira garinmu ce bata muslmai kaɗai ba." Haka suka yi ta shirya yadda zasu farmaki muslmai. *** Knock din kofar dakin karatun yayi sau biyu, gyara murya Salmanu Faris yayi. "Assalamualaikum!" "Waalaikumunsalam!" Ya amsa hankalinsa yana kan laptop dinsa. "Sir Yaran nan an sake su." Shiru Faruq yayi. Yana cigaba da aikinsa domin yaji ba wai ban ji ba. "Tun jiya aka sake su!" Ya fada yana me d'ago kai ya kalli Faruq. Gyara tsayuwa Faruq yayi sannan ya labarta mishi labarin da ya samu. Murmushi Salmanu Faris yayi ya ce mishi. "Allah ya kyauta." Tunda aka sake wadancan Yaran babu abinda zai iya yi domin kuwa akwai masu kaunar aikata miyagun laifi a cikin garin. *** Alhaji Nafi'u Shaibah Gidan shakatawa ce babba, duk ba kowa ya san da gidan ba, amma kuma Alhaji yana yana zaune yana wani aiki mace ce a gefenshi. Wisky ce riƙe a hannunsa yana jifanta da wani irin kallo da yake bayyana asalin abin da zuciyarsa ke rufewa, yanayinta ya yi masa, sai ya ji ya ƙara ƙaunar yin mu'amala da matan aure domin sun fi test da waye, da iya soyayya, mu'amalar aure, a kan ta ya ji cewa zai samu cikar duka muradansa. "Kin sani? Ko taɓa ganina? Ko jin labarina? Ko ganin poster ɗina in anywhere?" "This is the first time dana sanka, Yallaɓai?" Ya dubi laɓɓanta, ba ta yi kala da matan aure ba, ko talaka take aure? Irin matsiyatan talakawan nan? "Yaranki nawa?" Rausya kai tayi cikin wani irin yauki da yanga me fisgar hankali ta ce mishi. "Biyu!" Mikewa yayi ya dauko wani jan kyale ya shimfid'a a gadon, murmushi yayi mata sannan ya ce mata. "Ina da ka'ida, kwanciya da mace ta baya da gaba, kowanne da furashinsa." Gabanta ne ya fadi ta tsaya tana kallonshi kafin ta ce mishi. "Gaban nawa ne?" Murmushi yayi cikin jin dadi da kwaikwayon muryanta. "Gaba dubu dari biyar ne,.baya kuma 1M nake ba yarwa duk awa daya!" Gyada kai tayi tana faɗin.."amma babu wani abun da zai samu bayanan ko!" Da dan tsoro a tambayarta. Murmushi yayi yana faɗin. "An cigaba ba zan yi haka kawai ba, yan matana" ya ja wani drower baby lotion da Baby cream da baby oil ya ciro, durkusawa yayi a gabanta yana mai kai hannunsa kan kirjinta da suke dan cike. "Kina goyo kenan?" Gyada kai tayi tana faɗin. "Eh shi yasa nake son na koma da wuri." A hankali yake shafawa yana faɗin.."idan kika yi hakuri zaki tafi! Ina son mace Mai goyo dama!" Ya fada yana kai bakinshi kan abincin Yaronta, abinda take son ace mijinta yana mata kenan amma ya kasa sai dai ya ce ta kwanta ya hau ya sauka. Shima minti biyar baya yi ya sauka ya gama. "Yaushe rabonki da Mijinki?" Wannan tambayar ya dawo da ita daga duniyar da ta shiga. "Wata biyar!" Ta bashi amsa, cire bakinshi yayi yana kallon yadda take nishi.."ban gane ba?" "Eh driven Babban mota ne, tun kafin na haihu ya tafi bai dawo ba." Dariya yayi ya ce mata. "Amma kuma kike hakuri?" Shiru tayi domin dan dattijon nan ya kure mata lissafi. Domin da bayanta ya fara bayan shafa mata mayukan da ya fito da shi har da wani me danko, awa biyu ya dauka

Chapter 5 of 13