Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fada babu gaskiya ba, sannan duk inda ta zauna babu wanda zai ce bai kaunarta haka take, Uwata akwai faɗa." Sunan Hajiyar Maradi ce da ni, wacce tana can matar nan akwai drama, domin akwai Yayun Abba a Maradi can take zuwa ta ce ta gaji da gidan Abba Turai zata kashe ta da miyar barkono. Ita Hajiya Maradi baka iya mata, duk yadda kayi abu matukar bai mata ba, tow zaka kashe ta ne. ---- Tunda ta fita a motar take tsaye a wurin, wayar Mommy Turai tayi cikin rawan murya ta ce mata. "Mommy yau ma naga wannan motar, saura kiris wancan Yar iskan ta ja muyi magana." daga can ta ce mata. "Tow kukan me zaki min? Tunda kin ga motar kin ga wanda yake ciki ne?" "Ban gani ba." "Shi kenan zan duba lamarin, yau ma kin yi fada da ita ne?" "A'a!" "Ai na gaya miki ki fita hanyar ta, kin ki ko rashin miji da kika yi sanadinta ne, gashi nan lokaci guda Uwais ya juya miki baya yana ta dawainiyya da ita." "Mommy kiyi wani abu don Allah!" "Me zan yi? Bayan wanda nake yi kina rusa min " kashe wayar tai Iram ta cire a kunnenta, tana kallon ministry din da zata yi. A hankali take takawa, cikin nutsuwa me fisgan hanklain duk wani mai cikakken lafiya, don ma tana sanye da Jalbab, a hankali ta isa gate din ma'aikatan, shiga tayi cikin girmamawa ta gaida dattawan da suke kofar, sannan ta wuce. Tasan kullum zata wuce sai yi gulmarta. Amma yau sai bata ji sun yi magana ba. Tana shiga cikin ma'aikatan, MD ta fara haduwa dashi. "Good morning sir!" "Morning!" Ya fada ba tare da ya kalleta ba, itama bata wani damu ba ta wuce cikin office din, abokan aikinta na ganinta suka shiga d'aga mata hannu, itama ta musu sannan ta zauna. "Barkan da safiya ya aiki?" "Lafiya lau yau ma kin makara?" Inji daya daga cikin manya a office din. "Aunty Ba laifina ba ne, Ikhlas na tsaya jira!" "Malama kada ki min sharri!" Muryata ta karad'e office din. "Idan zaki gaya musu gaskiya ki gaya musu, ni ban ajiye ki ba, yawwa dazun na ga kamar kin tsaya baki shiga office ba, har Malam Babangida ya kai ni nace ya dawo ni wani abu yana damunki ne?" Mikewa tayi tare da jan hannun, muka fita daga office din, "Wai ke yaushe zaki yi hankali ne?" Cire hannunta nayi tare da cewa. "Yau da yamma!" Na fada ina kallonta. "Iram kada ki kara min karya, kowa yasan cewa idan gari ya waye kafin kowa yasan gari ya waye na gama shirina, na karya kafin nan." Toshe min baki tayi tana faɗin. "Don Allah ki yi hakuri surutu ga ya mace zubda mutunci ne!" Kwace bakina nayi ina mata wani irin kallo. "Iskanci nayi da mutuncina zai zube? Ko an ce miki ni din simi-simi ce irinki? Malama muna cikin 20 century ba zan tab'a zama irinki ba. Dama na ga yadda kika sauka a dame yasa na dawo amma tunda har lafiya lau kike gyata min karya sai an jima." Na juya abina a rayuwata idan akwai wacce nake so Iram ce, ita damuwarta daya ce matuƙar zata samu mafita tow ba damuwarta ba ne ta laka maka sharri. Koda na fito bakin kofar fita ina kallon wani mutum da yake min wani irin kallo. Har zan wuce sai na ji zuciyata bata yarda da shi ba, na dawo abinka da yar jarida. "Malam kallon na mene ne?" Girgiza kai yayi ya ce min. "Babu kome!" Sannan na wuce idan na tuna gidanmu babu wata zaman lafiya sai naji kamar akwai abinda ya dace ma sani. Amma kuma sai nake ganin tunda Iram bata gaya min ba babu ruwana. Lokacin da da na isa wurin aikina Oganmu ne ya zuba min harara cikin masifa ya ce min. "Sai da na gayawa HOD dinku babu abinda zaki iya, amma ya matsa min lamba na dauke ki gashi nan sai yanzu zaki iso." Cikin kunkuni na ce mishi. "Kai dai da katon tumbinka kamar an cika isa, ka fiye takura." "Me kika ce ?" Ya fada a fusace har yana dukar table din gabanshi. "Sir me zance fatan Alkhairi na maka, na ce Allah yasa ka samu promotion har zuwa BBC Hausa!" Na fada ina hade rai. Murmushi yayi ya fara faɗin. "Hmm ai yarinyar nan kina da kyakkyawar zuciya, ke daya ce kike min wannan fatan." A raina na ce mishi. *Da uban sankon kanka zaka BBC Hausa!* A zahiri kuma na sake dariya ina faɗin. "Mutum irinka me amana da adalci ai sai haka!" "Maza wuce ki duba shirin da zaki yi?" "Ok sir;" na wuce, ina fitowa Yeemar ta kalle ni tana dariya. "Yau ma kin hadu da tijarar Yallabai!" "Da katon tumbinsa kamar me cikin wata goma, ai oga yana kuntta min rayuwa wani dagajjaja da shi, ga sanko ga tumbi gashi kamar a rufe da kwandon kayan miya." "Zainab Junaid Gobir!" Wani irin daskarewa nayi ya tako gabana. Yana shafa sankonsa sannan ya daki tumbinsa da alamar kalamaina sun kunttta mishi. " Yallabai!" Na kira sunanshi. Dakatar da ni yayi yana faɗin. "A'a ba sai kin ce kome ba, nasan ni gajere ne, sannan ina da tumbi ga sanko. Amma yaudarata kika yi da kika min fatar aiki da BBC Hausa?" "Haba Yallabai kamata na yaudareka!" "A'a ba sai kin ce kome ba kowa ya koma bakin aikinsa." A yau program din da muke da su, har da hira da Shahararriyar yar gwagwarmayar nan wato Nadiyyah Jamil Chiroma, sai dai shi ba ni ce zan jagoranta ba. Don karfe biyu zata su fara hiran su gama karfe uku. Haka muka yi aikin har karfe daya na rana sannan na yi sanarwar shirin Yancinmu wanda shine da a yi da Nadiyyah Jamil Chiroma, fita nayi Jonathan ya amshi ragamar tafiyar da na'uran, ban daki na nufa na gyara fuskata sannan na fito, wayata ce take kara, na dan juya na dauki wayar a daidai lokacin da naji muryan oganmu yana faɗin. "Ta iso!" " Ban san tana gabana ba, kawai muka yi wani irin karo da ita, wayar hannuna ya fadi ita kuma tayi wani irin baya kamar zata fadi security suka tare ta. "How dare you zaki bangaje Madam Nadiyyah!" "Sorry ba da gangan ba ne!" Na fada ina d'ago kaina. Kamar ance na ankara naji hannunta kiris a fuskata na kauce. Na sake baki galala kafin na kama dariya. "Bayan nace kiyi hakuri? Sannan ki ce zaki mare ni, tow na ture ki, kiyi abinda zaki yi mtseew!" Na bangaje oganmu na wuce. "Wacece ita? Ku kamo min ita!" "Madam ana kallonki, muje daga baya zamu ji da lamarin!" Cizon lips dinta tayi tana faɗin. "Sai na ga iyakarta!" Massalaci na wuce abuna nayi sallah, sannan na koma cafteria naci abinci, sannan na wuce office don haushi ko tsayawa su gama program din ban yi ba, na bar radio station din na dawo gida, inda na samu Mommy Turai taba bala'i. "Ya Nuraim meke faruwa?" "Wai akan maganar auren Iram da Abba ya gabatar ne ashe mai martaba za a daurawa auren a turata can Germany." "Mai Martaba Mutumin da yayi jika da ita haba shi kuwa Abba, gaskiya ko ni ce Mommy Turai abinda zan yi kenan kuma fa akan." "Tafi can sakarya!" Shiru nayi na wuce part dinmu. "Wallahi idan na yarda Allah ya tsine min idan ban saka wuta ta kona kowa ba har ni da ita yar mu mutu zaka san dani kake zancen, na baka zabi zaka dawo ka same ni!" "Allah ya kyauta muka ce!" Amma ya kamata Abba ya sani Mommy Turai bata fadar abu ta kasa aiwatar da shi sai dai idan bata yi niyya ba. *** DAUSAYI Nan ne gidan gonar Sarki Attahiru Shehu Yayari,shiru kowannensu yayi kafin Malam Junaid ya mika mishi wasu files guda uku, ya nuna mishi daya. "Wannan ita ce asalin yarjejeniyar da muka yi tsawon shekaru talatin da wani abu, wannan kuma shine na kasuwancinmu, wannan kuma shine na mafarin raba kanmu. Amma ni da Mahaifinka mun ajiye wannan shaidar ce na ko karta kwana. Sannan abu na gaba da zan gaya maka batun auren Mai Martaba." D'ago kai yayi kafin kalman Baba Salama ya dawo mishi. "Malam ban gane auren Mai Martaba ba? Ko maganar da mutane ke yi kana yaki akan dukiyar nan ce?" Murmushi Malam Junaid yayi ya ce mishi. "Duk yadda ka ce!" "Mai Martaba da bai da lafiya, sannan a shekarun irin ta shi za a hada shi da mace? Yarinya da ya ribanya shekarunta kamar biyar? Mallam bayan Abba da Baba Saddam waye target dinka?" Murmushi yayi a karo na biyu ya ce mishi. "Kai ne harina na gaba?" Sai kuma ya sake dariya irinta manya. " Nasan ba za a tab'a kashe ni ba, sai kwanana ya kare amma kuma zan yi ƙoƙarin tayaka tafiyar da baka san inda zata bulle maka ba, ka nutsu da kyau tun kana yaro ka gaya min kana mafarkin kuraye a zagaye da kai suna son kai maka hari. Amma akwai wasu garken zakuna da suka zagaye ka." Dafe kan Salmanu Faris yayi saboda sara mishi da yayi. Wani irin zufa ce take karyo mishi. "Sannu a hankali zaka fahimci kome. Faruq zo ka ɗauke shi!" Da sauri Faruq din ya iso, d'aga mishi hannu yayi ya dunkule hannunsa tare da mikewa ya kalli Malam Junaid. "Yawwa kaga na manta, wannan ita ce file da na kiraka domin ita duk wani abu yana cikin nan ka duba, Allah ya tsare." Tunda suka bar gidan gonar, wayarshi take kara kamar zata idanunshi a lumshe ya ce. "Faruq dauka!" Dauka yayi yana faɗin. "Ma kina son magana da shi ne?" "Ina yake ?" Ya fada cikin hayagaga. "Yana jinki." "Prince kana ina ne? Kazo ZR station wata Yar iskar kyankyaso ce ta min rashin kunya ni zata bangaje." "Look Nady ki dawo" cikin masifa da Bala'i. "Taya zan dawo bayan anci mutuncina? Don ni bare ce a garinku? Dama abinda ake ta nuna min kenan?" "Faruq muje!" Ya sani ba zata tab'a barin wurin ba matuƙar ba a nimo yarinyar an mata kashedi ba. Tafiyar minti goma ya kai su, bude mishi kofar Faruq yayi ya samu masu tayata da wasu abubuwan suna waje, office din MD din ya nufa. Duk inda ya shige gaishe shi ake. A hankali ya tura kofar tana zaune ta harde kafa. Kuka ta saka mishi cikin rigima irin nata. "A kore ta a wannan gidan rediyon din, sannan a kuntatta mata." Ta fada tana kallon shi. Durkusawa yayi a gabanta ya ce mata. "Kin gamsu ayi haka?" "Idan aka mata haka tazo har office dina ta bani hakuri." "Ok MD Wacece ita?" "Zainab Junaid Gobir Khlash!" D'ago kai yayi yana kallon MD. "Aiki take ko me?" "Tana sanin makaman aiki ne." Idanunsa cikin na Matarshi. "Ka dakatar da ita sannan ta rubuta sakon ban hakuri ta kawo har office dinta!" "Tow Sir!" "Haka ya miki?" " A kore ta har a jami'a." Ta fada tana share kwalla da yake zubo mata. "Nady akwai line din da bamu isa tsallakewa ba, Babanta shine shugaban jami'ar da take karatu, Please a bar maganar a nan." Da wani irin takaici ta mike suka dawo gida, amma tabbas ya yarfata a sonta ayi ta ta ƙare, amma haka zata yi hakuri tunda ya ce ta hakura. *** Nightmare Sake glass cup din hannunta tayi jikinta yana wani irin rawa. Abin da kowa yake mata gudu ya faru ita yau Faris zai kalli idanunta ya ce an mishi mata saura sati biyu aure? Wani irin juyi kanta yake ta nime wuri ta zauna tare da dafe kanta. "Please Nady i don't mean to hurt you, nima auren nan Abba...." "I laugh aure on my foot!" Ya fada muryanta na rawa. "Why Dr? Why aure now? Dama kayi haka ne domin ka ci zarafina? Kasan yadda nake sonka? Kai ka min alƙawarin ba zaka tab'a kallon wata Y'a mace ba, why you broke your promise? Dama ka hadu da Banzayen zuriaraka da suka yi abondan dinka ne don ka yi aure?" "Nadiyyah ya ishe ka haka aure na fada babu fashi....." "Idan ina raye babu macen da zata hada kafada dani, kuma sai na kashe ta kowaye Ubanta." D'aga hannunshi yayi kamar zai mare ta farko daga munnunar mafarkin da take, zuciyarta tana wani irin gubawa. Kallonshi tayi yana barci, kasa hakuri tayi tana me tashinsa. "Prince tashi nayi mafarkin wai zaka kara aure da gaske ne? Please tashi!" Bude idanun yayi yana kallon yadda gigice duk da sanyin Ac amma zufa take kamar ta hadiye kunama. "Kwanta babu maganar aure ni naki ne har abada?" "Ya maganar yarinyar da ta min rashin kunya tow? Zuba mata idanun yayi kafin ya ce mata. "Amma tun jiya muka gama wannan maganar ko?" "But!" "Nady dare yayi fa barci nake ji." Ya koma ya kwanta. *** Cikin Gida. Dare mahutan bawa, amma a wannan lokacin masu shiri da shirinsu. Masu nima da shirinsu suke nima. Wasu mutane ne guda uku suka fita daga cikin gidan gaban wata mota suka nufa, kasancewar wurin akwai duhu me tsananin gaske. Wata mace ce ta fito ta kofar gabasa aka bude mata motar. "Saura kwana nawa Gwaska dakare ya fito?" Tayi maganar cikin wata irin murya wanda ya nuna alamar ta saka abu a bakinta. A cikin motar aka ce mata. "Tsakanin watanni ciki da haihuwarsa!" Inji mutumin ya faɗa. "Ina ga madadin ayi haihuwar guzuma da Junaid me zai hana shima a rufe mahaifarsa." Ta fada tana murmushi. "Na ci suna mikiya ne ba wai don ban san yadda zan yi ba amma abu me muhimmanci shine a sakawa gafiya hayaki domin ya fito daga rami.... Top_notch season 4 ROYAL POLITICS is not free, pay N500 to get a complete access to the book. *Marubutan TopNotch Writers sun sake zuwa muku da sabon labarai masu ƙayatarwa a tafiyarsu ta Season Four:* *MAI_DAMBU kuwa ta faso muku ne da labarin da ya haɗa da Sarauta, Siyasa da kuma Soyayya, duka a littafin ROYAL POLITICS: An yanka ta tashi.* *AZIZAT kuma ta tattaro muku rikitacciyar soyayya ne da ya hawo jirgin JayKay ya dira a Kitchen ɗin Ziyada. CHEF ZEEY: Love in the Kitchen* *Account Details:* *5921536136* *RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN* *Moniepoint MFB* *POSTING* *Ɗaya: 500* *Biyu: 1000* *Uku: 1500* *DOCUMENT (da zaran an gama posting zai koma)* *Ɗaya: 1k* *Biyu: 2k* *Uku: 3k* domin tura shaidar biya ko Ƙarin bayani, ku tuntuɓi: *08130269641* Ko *08137311900* Ko kuma *09063467258* #Top-notch4 [7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: ROYAL POLITICS 🔥 _An yanka ta tashi_ Ramlat A Manga Mai_Dambu TOP-NOTCH SEASON 4 Sadaukarwa ga Auntyna RUKAYYA GOMBE 🥰 🤩 😍 02.. Suicide "Kana tsammanin za a barshi ne ya cigaba da yadda yake so?" "Je ki!" Ya fada duk da duhu ne amma ta kara kallonshi. "Me haka yake nufi?" "Irin wannan abin Gwaska dakare ya aikata ya fada matsala idan kika yi wani abu tow da hannuna zanta yankar naman jikinki!" A rude ta ce mishi. "Kana nufin kashe ni zaka yi?" "Fita!" A hankali ta fito kafin ta ce mishi. "Shi kenan sai mun hadu kenan!" Ta fada tana me komawa cikin gidan sannan yar tsohuwar motar bar kofar gabas din. *** Khlas. Duk da part dinmu yafi kusa da na Mommy Turai, haka bai hana ni jin yadda take kuka tana magiyar rokon Abba ba, gaskiya Abba yaso kansa taya zai dauki Iram ya bawa Abokinsa da tsufa suka ci mishi, tsaki nayi ina nazarin program dina ta ce mishi. "Kaso kanka Junaid kada ka manta nima y'ata ce, taya zan yarda ka lalata mata rayuwa da auren matacce!" Rintsa idanuna nayi tare da bude su sakamakon amsar da Abba ya bata. "A'a gawa ne, idan kika fusata ni zaki ga b'acin raina." "Tow idan kuwa baka kyale min y'a ba wallahi zan maka ka kotu, akan me? Baga Zainab ba me yasa ba zaka bashi zainab ba?" "Ai hadin ma ba daya ba, Ita Iram din dai na zab'a domin ita Ikhlas har yau bata da hankali. Sannan da kike magana ita Ikhlas din kin tab'a jin labarin tana da wani saurayi ne? Sannan dukkansu Yayana ne, don Allah kada ki cigaba da raba min kan Yarana!" Ya fadi haka, tashi zaune nayi ina me kashe laptop dina domin fadarsu hana ni barci yake tunda da karfi suke na dauki bargona, na nufi bangaren Umma knocking biyu nayi ta bude min. "Khlas lafiya?" "Lau Umma yau ni daya zan kwana shi yasa na dawo bangarenki!" Kallona tayi kafin ta ce min. "Shigo tow!" Na wuce ta, aikuwa ta rufe kofar na wuce dakin da aka ware na daban na jefa pillow na a gadon. Sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na kwanta ina jin kamar na sauke min nauyi. Wayata da na shigo da ita ce tayi wani irin ƙara, dauka nayi na ina kallon sunan wanda ta kira wayar. Joy Moses, dauka nayi ina fada mata "fine girl." "Zeey Juh babu lokaci, I'm in danger, yanzu haka ina farautar rayuwata. Please zan bar miki sako duk abinda ya faru kiyi kokarin bincike. Domin zasu zo niman drive din." "Joy ban gane ba?" Cikin gaggawa ta ce min.."Zeey Juh ki duba gadona da kyau." Karar da na ji na ce mata. "Joy lafiya!" Katse wayar tayi koda na kira wayar bata dauka ba. Haka nayi ta kiranta amma bata dauka. Joy Moses abokiyar fada ta ce, saboda tana da kwazo amma a haka bai hana mu abota da juna ba. Domin tun kwazonmu ne yazo daya. Ita din iyayenta Christian ne, sannan makarantar mu daga secondry school tare muka yi, koda muka hadu a jami'a department ya rabamu ita suna bangaren Law ne ni kuma na dauki bangaren Mass communication, haka yasa haduwarmu a jami'a sai ya zama kamar ya mai damu abokai ne, Joy kyakyawa ce wacce ake kira da Fine girl. Duk da bana shiri can amma duk wani abin da ya shige mata kai tana tuntubata. Sannan tana yawan bani labarin cewa. "Zeey Juh akwai wani boyayen al'amari a cikin makarantar nan, i think Dad ɗinki bai sani ba, sannan ina kan bincike ne ni da wasu mutane, idan bincike na ya zama daidai kece yar jarida zan fara bawa labarin ke kuma ki isar da shi ga inda ya dace." Kallonta nayi na ce mata. "Me yasa kike fadar haka?" "Saboda!" Sai ta mike tare da faɗin. "Manta kawai zamu haɗu." Yau wata biyu kenan da muka yi maganar sai ga kiranta, kusan har gari ya waye ban wani yi barcin kirki ba, sannan bani da wani kuzari abinda na sani raina ba dad'i. Kitchen na nuna Mama Zuwairah me yin aikin Mommy Turai tana ta jefa dan wake, ni kuma a duniyata na tsani aikin Mama Zuwairah. Wucewa store nayi na dauki kwai da indomitable guda biyu. "Ikhlas dauka da ni."inji Iram "Ke kuturwa ce?" Na tambaye ta, murmushi tayi tana cewa "ko daya amma nasan dole zaki dafa da ni." Tsaki nayi na wuce kitchen. "Ekilas ga dan wake ina yi ki ce zaki dafa wani abincin? Gaskiya zan gayawa Hajiya Turai ta san abinda zaki yi." Shiru na mata na kunna gas na cigaba da aikina babban abinda yake ƙara bani haushi bata iya fadar sunana ba, sannan tun tashina na ganta a tare da Mommy Turai. "Ke wacce irin mara kunya ce ga abinci amma sai kin dafa wani." "Mommy kin san bana cin mangyada kuma Abba ya fada idan za'ayi dan wake ko shinkafa da mai da yaji na nime abinda zan ci, shi yasa na dafa indomie sannan ai bani daya ba ce zan ci har da Iram!" Ina fada haka sai ta sake fuskanta tana kallon Mama Zuwairah. "Bana son kananan magana!" Sannan ta juya tare da barin kitchen din, kallon Mama Zuwairah nayi na ce mata. "Mama shi fa wannan rayuwar baka da iko ka hana mutum yadda zai yi, sannan kin san dai ba kawo ni aka yi gidan nan ba gidan Ubana ne. Sannan ni ban ga dalilin da kome muka yi zaki je kina hada mu da Mommy Turai ba, ita mun fi kusa da ita domin uwa ce a gare mu, ki ga yadda Mama tasalla take rayuwarta babu ruwanta da kowa, sannan dukkan mu yan gidan nan muna girmamata. Ban san wani abu kike bukata ba, amma matukar baki kula da harkokin ba zaki bar gidan anan." Na fada bayan na dauko wani gasashen nama, na bude domin tun safiyar jiya Abba ya bani amma na saka a frijin kitchen din nasan za a iya wani abin da bai ba, juyawa nayi a cikin indomie din na zuba kayan dandanon, sannan na bar bude tukunyar tea, na diba daidai cikina kafin na hada madara da cadbury, sannan na jera a tire na nufi dakinmu, anan na samu Iram tana kuka. Kallo daya nayi mata na cigaba da cin abincina. "Baki damu da halin da nake ciki bane?" " Akan me zan damu? Abu daya na sani Abba ya yarda da halayenki ne yasa yayi choose ɗinki, sannan ya tabbatar ba zaki kunyata shi ba yasa yake da Yakini akanki auren nan fa ba yanzu zaa yi ba, da sauran lokaci idan ke da Mommy kuka cigaba da matsawa kin san Abba kuma kin san waye shi da abinda zai iya." "Ikhlas idan kece ya zaki yi?" "Biyayya zan yi daidai gwargwado,amma fa ba sauki ina da wanda nake so!" "Amma ai Abba bai sani ba!" "Eh ba kome ake fitowa da shi fili ba, kowa yana da nashi sirrin nima nawa sirrin Ya Uwais ne." Na fada ina mikewa daga flat din na nufi bangaren Malama. Da sallama na shiga tana lazimi, daki na wuce nayi wanka na shirya cikin riga da zani na atamfa, tsayawa nayi na kashe dauri sannan na dauki babban mayafi na yafa, kasancewar wancan dakin mu na yan mata ana shiga kuma ana dan zare mana abubuwa sai muka bar shi kawai a na kwananmu, sauran abubuwan kuma zamu dawo dakin iyayenmu, sai mu shirya. Kuma da jiya bangaren Maluma na dawo na kwana na rantse sai ta kwad'a min mari, domin zata ce na je ina jin gulmar fadar Mommy Turai da Abba, ina gama shiri na dauki jakata na wuce dakin Umma na dauki wayata da na ga miss call rututu. "Iram na tafi fa!" Na fada ina sauri. "Gani a bangaren Abba!" Ta fada, kallon shigar da nayi na kuma. Yanzu Abba sai ya ce na sauya shiga. Tsaki nayi na shiga bangarenshi. "Ina kwana Abba!" "Lafiya lau!" Na nime wuri na zauna. "Kin ji labarin ne?" "Wani labari kuma?" Na tambaye shi ina kallon Iram. "Na mutuwar kawarki!" "Kawata kuma? Wacce kenan?" Na tambaye shi a karo na biyu.."Joy Moses!" Rufe bakina nayi da hannuna biyu idanuna a buɗe. Jikina ya dauki wani irin rawa. Kamar xan sake fitsari. Hawaye ne ya zubo min sharr. "Ana tsammanin daren jiya ta mutu." Mikewa nayi da sauri zan fita Abba ya ce min. "Jira nima zan fita sai na ajiye ku a wuraren aikinku." "A'a Abba zan je na ga Joy ne ni ce last call dinta!" Na fada ina fashewa da kuka. "Abba ta kirani tana bukatar taimakona Abba wallahi ta kirani ka ga kiran?" Na mika mishi wayar. Kallona yayi kafin ya ce min. "Zainab!" "Na'am Abba!" "Bana son ko Mahafiyarki ta ji wannan labarin, sannan kema Iram ki rufe bakinki. Kada na ji kada na gani." "But Abba why?" "Case din kashe kanta tayi?" "A'a Abba kashe ta aka yi, na rantse kashe ta suka yi!". "Nace kiyi shiru! I believe what you saw not what you hear, kin ji ko baki ji ba?" Na ji nace ina shashekar kuka. "Ki wanke fuskanki muna jiranki!" Bayan na fita Iram ta ce mishi. "Abba Ikhlas bata karya, sannan ka ce mu rufe idanunmu akan abinda ya faru Joy kawarmu ce idan muka yi haka bamu ci amanar zaman tare ba?" Shiru yayi ya goge kiran sannan ya mika mata wayar. "Ba kowani abu ake bukatar magana akai ba. Kin fahimta?" Ya

Chapter 2 of 13