ce, "Allah Ya
sa hakan, amma tabbas Shamaki ya yi fushin
da bai taɓa yi ba, ya yi furuci a gaban kowa
furicin da bai taɓa yin irinsa ba. Ya jawowa
kansa bala'ai da tsinuwar ubangiji ta tabbabata
akansa in har ya kara zama da ni, yace ya
hakura da ni in har ya cika dan halas a cikin
uwarsa da ubansa. Na shiga uku na lalace
Nasrin yayazan yi?"
Nasrin ta girgiza kai ta matse hawaye ta
ce, "kada ki damu, ki je kiyi ta addu'a, kuma
ba da baki za ki fada musu kin shiryu ba
124 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
kamata ya yi su gani da idanuwansu su tabbatar
kin canja sai su tausaya miki su yafe miki.'
"
Malaika ta surnano da hawaye ta ce, "ki
yafe min Nasrin na jawo miki zargi da zagi a
wajen Shamaki da iyayena. Gaba ɗaya suna
zarginki da ke kika hure min kunne har suna
kiranki da karuwa mai zaman kanki."
Nasrin ta girgiza kai ta ce,"ba komai
Malaika na yafe miki, na yafe musu suma
kuma In sha Allah za su gane gaskiya."
"
Nasrin ta dauko kudi naira na dukan
Naira dubu ashirin ta bata ta ce ta je ta yi jari,
sannan ta dauko mata kaya kala uku masu kyau
a cikin nata da take sawa ta bata, da yake kirar
jikinsu daya.
Malaika ta yi ta godiya matuka sannan
suka dingumo suka fito zuwa dakin Zainab
suka iske ta a kwance ita kadai. Malaika ta
durkusa ta gaishe ta gami da yi mata sallama.
Zainab ta yi mata fatan alkhairi sannan suka
fito, Narin ta dauki motarta ta kaita tasha ta
shiga mota ta zauna, suna dagawa juna hannu
suna zubar da hawaye da alama kowannensu
tana kukan rabuwa suna kuma kyautata zaton a
125 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
yau wannan rabuwa ta su itace ta karshe ba
zasu kara ganin junansu ba..
Allah sarki sabo turken wawa!
Bayan mota ta cika direba ya tashi mota
suka fara tafiya sai Malaika ta runtse ido
hawaye zazzafa ya fara kwaranya daga.
idanuwanta, kamar daga sama ta ji an mika
mata hankici. Tana daga ido sai ta ga mutumin
da ke kusa da ita ne ya tausaya ya bata dan ta
goge hawayenta. Amma fa ta yi matukar
razana a lokacin da ta yi ido hudu da shi,
Shamaki ta gani fuskarsa cike da damuwa. Ya
kawar da kai gefe dan baya so 'yan cikin motar
su fahimci wani abu. Mamaki mabayyani ne
yake kwaranya daga fuskar Malaika ta kasa
tantance daga in da ya diro. Shin binta yake yi
a baya ne ko kuwa Katari aka yi? Shin daman
Shamaki ya taɓa zuwa Abuja ko kuwa biyo ta
ya yi kawai? Shin sonta yake yi har yanzu ko
kuwa so yake ya damke ta da laifi dan ya
fadawa duniya koi ta wacece?
"
Amsar tambayar tana wajen Shamaki sai
dai kash! Ba ta ga fuskar jero masa wadannan
tambayoyi ba.
126 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
isa garin Kano.
Bai ce mata uffan ba itama haka har suka
*** *** *** ***
Washegari da daddare Zainab da
maigidanta Salis suka kai Nasrin filin jirgi na
Abuja tare da rakiyar kawarta Dinah.
Tabbas Nasrin ta dage sai ta tafi Amerika
amma tana ta kuka kamar an yi mata dole,
Zainab da Dinah ma suna taya ta yayin da Salis
ya dinga basu hakuri amma sun kasa dainawa.
Nasrin tana ji a ranta kamar idan ta tafi
mutuwa zata yi ba zata dawo ba, haka Zainab
ma tana ganin kamar idan ta zo haihuwa
mutuwa zata yi ba zasu sake haduwa ba. Bakin
cikin Dinah kuwa shine ga aurenta ya zo. ba
za'a hada aurenta da na su Nasrin ba dan gaba
daya sun gama ɓaɓewa da Fu'ad an rabu.
Babu yadda zasu yi dan jirgi baya jira
dole suka saki Nasrin ta wuce ciki ta karɓi
(boading pass)na tafiya. Tana tafe tana
waiwayensu suna waiwayenta suna dagawa
127 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
juna hannu, yayin da hawayen da yake
kwaranya ya yawaita.
Allah sarki rabuwa ba mutuwa ba!
*** *** ***
Nasrin ta shiga cikin Jirgi ta zauna kafin
a gama shigowa ta jawo wayarta ta kira
Dr.Jalo, tana jin muryarsa sai ta fashe da kuka.
Shima kukan yake yana mai yi mata nasiha
akan ta zama mai hakuri da tawakkali.
Ya shaida mata yadda yake ji idan ya
tuna rayuwarsa ta baya a lokacin da yake da
lafiya yana takawa kamar kowa dan haka kada
ta zamanto mai yiwa Allah butulci dan Ya
hada su kuma Ya raba su a sanda Ya so. Ya yi
mata fatan alkhairi itama ta yi masa amma ta
roke shi da ya bar cikin dajin ya koma gida ko
asibiti, bata jin dadi idan ta tuno irin masifar
wahalar da ta baro shi a cikin dajin nan. Ya yi
mata alkawarin za su koma gida su zauna su
jira ranar da Allah (SWA) Zai yanke musu
wannan wahala itace ranar da Allah Zai dauki
rayuwarsa. Ya na da tabbacin mutuwa ita kadai
128 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
ce hutu a gare shi. Kuka ya hana su ci gaba da
yin waya sai ta katse.
Ta kira Mahaifiyarta ta shaida mata har
ta shiga jirgi idan sun karaso a zo a dauke ta a
filin jirgi. Hakika Momi ta yi farin ciki da jin
haka ta yi mata fatan Allah Ya kawo ta lafiya.
Daga karshe ta kira Dr.Hala ta shaida
mata yau zata koma Amerika, tana fatan idan
ta shigo kasar zata neme ta. Dr. Hala ta yi
alkawarin yin haka ta yi mata addu'a gami da
fatan alkahairi.
Ta na kashe wayar sai ga kiran Dina,
Nasrin ta amsa da sauri, Dina tana Magana
cikin lallashi ta ce "Nasrin! Ki yi hakuri idan
kin je ku daidaita da Fu'ad ku yi aurenku. Kin
ga wanda kike so din ya nakasa ba yadda zai yi
ya aure ki, Fu'ad ne kadai ya dace da
rayuwarki shine wanda za ki ji dadin zama da
shi dan hutu ke ma 'yar hutu."
Nasrin ta fusata ta ce, "Dinah, Wai shin
kin manta ko waye Fu'ad? Kin manta cin
mutunci da rashin kulawar da yake yi min? Kin
manta da cewa idan na aure shi bakin ciki zai
tula min saboda girman kai da ji da kan da N.
129 Jamilu Umar Tanko JUT
1
DAMA NI CE...2
yake yi min? Kin manta da tulin 'yan matan da
yake da su a turawa da bakaken fata amma duk
da haka ki ce in aure shi? Ba ruwana da abinda
yake da shi in har ba ni da kwanciyar hankali da farin ciki a ransa. Allah shi Ya san dalilin da
Ya hada ni da Jalo kuma ya raba mu. Allah Shi
yasan dalilin da Ya mayar da Jalo nakasasshen da ba zai iya moruwa ba. Na rasa nutsatstsen
saurayi, mai kamala da sanin ya kamata. Na
rasa wanda na ke so kuma wanda yake sona.
Kawata! Ki yi min addu'a Allah Ya ba mu
yadda za muy da ni da Jalo amma ba Fu'ad
ba."
Dina ta yi kasake tana gasgata maganar
Nasrin ba tare da tana da bakin gyarawa ba.
Ta yi ajiyar zuciya ta gyada kai ta ce,
"haka ne kawata, Allah Ya bawa Jalo lafiya Ya
zaɓa miki abinda ya fi alkhairi a rayuwarki. Ina
yi miki addu'a Allah ya kai ki gida lafiya ki
same su lafiya. Ki gaida Mummy da Daddy
dan Allah."
Nasrin ta ce "zasu ji. Amin. Na gode.
*** ***
130 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE2
Jirgi ya lala sama yayin da Nasri ta
rutse ido sai hawaye ya surnano mata, kamar
daga sama ta ji an nanika mata hankici a
hannunta tana bude ido ta dubi mutumin da ya
ke zaune a gefenta ne ya bata, tabbas ta firgita
ta gigice a lokacin da suka yi ido hudu da
Fu'ad.
A
Sai ta zazzare ido saboda mamaki gami
da fargaba mai tsanani. Da alama yagama jin
wayar da duk ta yi da su Jalo, ya gama jin
wayar da ta yi da Dinah. Sedeg nen sonsand
Ta dube shi sai ya yamutse fuska ya
kawar da kai gefe ya sha kunu ransa a ɓace.
Lallai dole ransa ya ɓaci da jin irin wadanan
munannan kalamai da ta furta akansa.(TUL)
Abin tambaya shine caman Fu'ad yana
kasar amma bai zo ya neme su ba kuma bai
faɗawa kowa yana nan ba? Shin me ya kawo
shi kasar, uzurinsa ne ya kawo shi ko bibiyarta
yake yi?
Rigiji gafji! Wani kaya sai amale!
Basu kara cewa juna uffan ba har suka
isa kasar Amerika.
131 | Jamilu Umar Tanko JUT Txost rem!! ulims!|
DAMA NI CE...2
Kash!
Anan zan dakata mu hadu a littafin
DAMA NI CE... Kashi na 3
Mu ji yadda zata kasance.
*Tsakanin Nasrin da Dr.Jalo
*Tsakanin Malaika da Shamaki da
Iyayenta.
*Tsakanin Nasrin da Fu'ad.
*Tsakanin Nasrin da Mahaifiyarta. *Yaya rayuwar
kasance nan gaba? kowannensu zata
Ku biyo ni ku sha Labari.
Ta ku har abada
Jamila Umar Tanko.
(JUT)
DAMA NI CE...2
A DADE ANA YI SAI GASKIYA.
Ina makaranta da 'yan kasuwa? Ina
masu sayen daidai ko sari? Inamasu neman
littattafan JUT gaba daya tun daga kan
'KWANA ASHIRIN DA HUDU' zuwa
'DA MA NI CE' marmaza ku garzayo
shagona mai suna
'ADON DAWA BOOKSHOP' da
yake layin layin ''yan littatfai littatfai
SABON GARI KANO.
KASUWAR
Farashi cikin sauki.
Abubakar akan
A tuntubi
wannan lamba
08060267571 domin neman karin bayani.
Sai kun zo.
133 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2.
MATA ADON GARI IN BA KU BABU
GARI, IDAN KUN YI YAWA GARI YA
BACI.
*Idan kina neman shawara akan zamanki na
aure.
*idan kina da matsaloli ta kowanne ɓangare.
*Idan ki na da korafi.
*Idan mai gida baya jin daidai.
*Idan fatar jikinki tana neman gyara.
*Idan ki na so ki rike kamshi na ciki da
waje.
*Idan abubuwa sun motse ki na so ki ciko.
*Idan ki na bushewa.
*Idan kina so ki zama marubuciya.
*Idan ki na neman shawara akan sana'a dan
taimakon kanki da kanki.
134 Jamilu Umar Tanko JUT
1:
DAMA NI CE...2
MACE SAI DA GYARA
Ka da ki bari ki zama bora, ka da ki bari
Oga ya raina ki, ka da ki bari kishiya ta
raina ki. Yanzu ba'a kishin fada sai dai a yi
kishin gyarada kyautatawa Mai gida.
Ga wata dama ta samu JUT ta bude
kofar ba da shawarwari da bada
gudunmawar abubuwan gyara, a tuntuɓe ni
a wannan layi 08037196708.
TSARABA:
Ki nemi tumatur mai kyau ki raba
gida biyu ki goga a fuskarki kafin ki shiga
wanka. Ko ki matse tumatur a cikin 'peak
milk' sai ki goga a fuska da wuya. Ki bari
bushe sannan ki murje tas. Idan kin shiga
wanka kada ki wanke fuskar da soso, kada
ya
135 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
ki saka ruwan zafi idan za ki wanke fuska
da sabulu da ruwan sanyi za ki wanke.
Za ki ga yadda fuskar zata din ga
gyalli kamar tangaran. Fuska bata son
jagwalgwalo da yawan taɓawa. Haka a guji
dafke-dafken mayuka daban daban a fuska.
Masha Allah!
Allah Ya sa mu dace. Amin!
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels