Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 6
da hawaye ya fara kwaranya 49 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 daga idanuwansu su dukka. Lokaci mai tsayi suna kuka sannan ya yi ta maza ya ci gaba da magana cikin sheshshekar kuka. > "Hatsarin ya faru ne da yamma ranar 5/10/2006 a wani kauye da ake kira Dingare, kusa da Yelleman." "Ya salam" In ji Nasrin yayin data mike da sauri ta je ta fada akan gado ta danna kanta a cikin filo ta fara kuka amma wayar tana nanike a kunnenta. Jalo ya share hawaye ya ci gaba da cewa "bayan an taimaka ana cire mu a mota sai na ji tsoron kar motar ta kama da wuta dan an fara cire da Salima,sai Hisham, Umar da direba. Sai ni da Rayyana ne a cikin motar, na hango ta tana ta motsu-mutsu, nace ta taka bayana ta yi sauri ta fita, data taka ni sai na ji kamar ba'a taka ni ba, nan da nan na razana na ce a raina 'ba dai Lakata ce (Spinal cord) ba ne ya tabu. Nasrin ta tashi zaune tana juyi akan gado " zuciyata cike da tashin hankali hawaye ya yi mata kawanya, duk da bata so ya gane kuka take amma sai da ya gane. 50 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Ta zabura ta ce, "in sha Allahu ma lakarka ba ce ta taɓu ba." " Ya yi murmushin karfin hali yace, "Nasrin kin manta labari nake baki? Abinda ná ke fada ya dade da faruwa ai. Koma meye ki bari in kai karshen labarin mana." Ta amsa a gigice "to ina jinka." Ya ci gaba da cewa "Da aka daga motar na yi iya kokarina in fita na kasa sai da aka ciré ni. Na ji kamar an raba ni gida biyu ‘innalillahi wa inna ilaihi raju'un' shi kadai na ke Ambato. Abu kamar wasa sai gamu a asibitin Hadeja, da suka duba ni suka ce ya fi karfinsu sai aka tura mu asibitin Aminu Kano, satina uku anan suka tabbatar mana da cewa abin ya fi karfinsu. " Nasrin ta fasa kuka ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihi rajun. Dakta me ke nan?" Ya surnano da hawaye ya ci gaba da cewa "Mahaifiyata ta na jin labarin na yi hatsari sai ta mike ta nemi ciwonta ta rasa ta bazamo asibiti wajena, a cikinsu ni kadai ne na ji ciwo ana tsaye akaina." 51 Jamilu Umar Tanko JUT. DAMA NI CE...2 Jalo ya kasa ci gaba da labarinsa saboda kuka ya kashe waya. Ta yi ta kira bai dauka ba, haka ta kwana bata rintsa ba. *** *** *** Kwananta biyu tana zagaye a cikin gida cike da damuwa Jalo bai kunna wayaba sai a rana ta uku da sassafe ta kiransa. Ta cika da mamaki jikinta na rawa ta amsa. Ya bata hakuri ya ce ta yi masa uzuri rashin caji ne ya same shi ba da gangan ya kashe wayar ba. Ta yi mamaki yadda caji zai gagare shi har tsawon kwanaki biyu kamar wani dɗan karkara. ya Tambayar da ta yi masa ita ta bashi mamaki ta ce ya faɗa mata in da yake gata nan zata zo. Kafin ya bata amsa ta dinga yi masa magiya har sai da yaya ji hankalinsa tashi. Ta ce ya turo mata cikakken adireshinsa. Sun ajiye wayaba dadewa ta ji sako ya shigo tana dubawa ta ga adireshinsa ya turo mata, tana karantawa ta ji hankalinta ya yi mummunan 52 Jamilu Umar Tanko JUT by DAMA NI CE...2 tashi ta firgita ainun. Ta fara tunanini ta in da zata fara wannan bulaguro. Kamar da wasa ta fita a gigice ta fadawa Zainab cewar zata je Bidda dubiya. Zainab ta shiga jero mata tambayoyin data kasa amsawa. Amsa daya ta fada mata ita ce wajen Jalo zata je ya yi hatsarin mota. Ta koma daki ta hada karamar jakar kayanta ta fito, Zainab ta yi tagumi tana kallonta ta zo ta wuce ta, direba ya kaita tasha ta shiga motar haya. DAMA NI CE...2 l of si BABINAGOMASHADAYAW ME SE _BIDDA w donics niyovi diunt,sand, onoj ali N asrin bata tsaya a ko inaba sai a in da Jalo ya fada mata. Ba zatoCS ba tsammani Jalovaya jiyo muryarta a kofar dakinsus oli simsynd Ya gigice ya ma rasa vad yadda zai fadawa Mahaifiyarsa sai ya cika da mamaki da ya ji Mama ta ambaci sunan Nasrin radai. Ashe tana . biye da su tana Hankalin jin hirarNasrin dwaya yasuke yi yi a matukar tashi a lokacin da ta ga mutuminta a cikin wannan hali, bata taɓa zaton abin har ya kai haka ba. Nasrin a durkushe a gaban Jalo yana kallonta tana kallonsa cike da Mamaki. Kanta ya daure ta kasa gane abinda yake damun Jalo gashi dai a zaune sanɓal amma baya iya tashi. Bayan ta yi sallar azahar ta ce ya bata labarinsa tana so ta san komai. Mama ta tashi ta fice ta je karkashin bishiya ita da wata mata da suka saba suna hira. 54 Jamilu Umar Tanko JUT TULT a list 2 DAMA NI CE...2 *** *** *** CI GABAN LABARIN JALO Ya yi shiru na dan lokaci yana tunani sannan ya bude baki dakyar ya fara Magana cikin marainiyar murya ya ci gaba cewa, "Na fada miki ina asibiti a Kano sun yi iya yinsu abu ya fi krfinsu.Nan da nan labari ya cika garin Yelleman kasancewar ni mai jama'a ne, sai Gwamnan Jiharmu na wancan lokacin ya ji labari, ya aiko aka tabbatar masa da jikina sai ya ce a dauke ni a fita da ni turai, kasar Germany. Miliyoyin Naira aka ba mu. Rayyana da Yayanta Bashar su ne suka raka nican,kudin gaba daya a hannunsu aka damka.' " Nasrin ta mike tsaye tana kai kawo a tsakar daki fadi take "Allah Ya saka sami lafiya." Kuka ya ci karfin Jalo na dan lokaci ya kasa magana sannan ya ci gaba da cewa "Jinya ta Spinalcode mutum baya iya tsayar da bayan 55 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 gida da fitsari haka nake fama sai dai kawai in ji ni na ɓaci.' " Yana fadar haka Nasrin ta sulale ta zauna ta dora hannu aka ta fasa kuka ta ce "Dakta yanzu lakarka (Spinal cord) ce ta taɓu? Lahaula wala kuwwata illabillah. Mai rai ya shiga uku." Su duka sun jima suna kuka kafin a sami wanda ya iya ci gaba da magana a cikinsu Jalo yace, "watarana a asibitin muna zaune da ita na shaida mata jikina ya ɓaci ko zata taimaka ta gyara ni? Ta kalle ni sama da kasa sai ta ja Jakarta ta fice ta bar ni a zaune, da aka jima sai ga ma'aikatan jinya mata su biyu sun shigo. Suka tambaye ni wai matar da ta fito daga ɗakin nan ta ce su zo ina da damuwa. Na fada musu su gyara ni jikina ya ɓaci, bayan sun saka safar hannu suka gyara ni sai suke tambayata waccan matar wacece? Na shaida musu matata ce, sai mamaki ya bayyana a fuskokinsu suka yi Allah wadai da ita, bata damu ba ita. Ita da Dan uwanta Bashar siyayyarsu ce a gabansu suna zagaya gari da makudan 56 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 miliyoyi a aljihun su, ni ina kwance a asibiti. Masifa goma da ashirin. Ga faca da tsawa da take yi min kullum sai na roke ta data harhada kayanta ta koma Najeriya bazan iya ci gaba da zama da ita a haka ba, ta bar ni in ji da ciwo da kaddarar data same ni. Daman haka take so ta kaɗa kai ta yi tafiyarta, yayanta yana ta kwashe mata albarka. Da ni da Bashar muka ci gaba da zama a kasar Germany, ana ta jinya amma jikin dai yana nan yadda yake, aka sake yi min aiki a karo na biyu ba'ayi nasara ba." Kuka ya ci karfin Jalo ya kasa ci gaba da magana sai su dukka suka fashe da kuka. Ya daure ya ci gaba da cewa “Duk da facakar daBashar yake yi a kasar waje da kudin jinya amma ya yi kokari, baya kyama ta, kullum shi yake gyara min jikina ya goge ni, ya fesa min turare ya canja min kayan jikina. Tun da Rayyana ta koma Nijeriyako flashing a waya bata taba yi min ba, balle kira a waya ta ji lafiyata, har muka koma Nijeriya. 57 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Bashar a ranar yace zai wuce gidansu Abuja ba zai zauna da ni ba, na yi zaton kaunata da yake yi a kasar waje ta gaskiya ashe saboda kudi ne. Na yi kuka na share hawaye na ci gaba da zuba ido in ga yadda Allah zai yi da ni. " Nasrin ta girgiza kai ta sharce hawaye ta ce “Allah sarki. Rayuwa da wuya. Allah Ya baka lafiya." Jalo ya gyaɗa kai yace, "Amin nagode.Babu ruwan Rayyana da ni, koda yaushe tana cikin dakinta tana kallon setlite bata kula ni. Sai abokina Muhammad ne yake zuwa ya gyara ni ya bani abinci. Ko sati guda banyi bana kira Mahaifiyata ina neman taimakonta akan ta zo ta yi zaman jinyata dan matata ta kasa. Mahaifiyata da mijinta sun Yelleman tun wannan rashin lafiyar bata koma Lagos ba, bata da karfi kuma gata a karkashin wani dole sai ya bata izini zata taho, bayan na fada mata sai da ta dauki tsawon sati uku sannan ta zo kafin nan Makwabta suka yı shawara a kai ni Teaching Hospital na lagos kauro 58 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 don in sami kulawa, sai suka dauke ni suka kai ni. Mahaifiyata da kaninaAbubakar suka zo dagaLagossuka same ni a asibiti,Mama ce take wuni da ni da daddare sai ta koma gidana ta kwana, kanina yake kwana da ni. Bayan tsawon watanni biyu Rayyana ta ce ta gaji da dafa abincin da take yi tana kawo mana asibiti dan bata son warin asibiti, sai kanina yake zuwa yana dauka ita ta daina zuwa, duk da haka ta ce ta gaji da dafa abincin. Abin ya kai sai MaKwabta ne suke kama-kaman kai min abinci saboda na zauna da su lafiya. "Innalillahi wa’inna ilaihi raju’un” kawai nake kira hawaye kuwa idanuwana basu taɓa bushewa ba, haka mahaifiyata daga ta kalle ni sai ta runtse ido ta zubar da hawaye dan tausayi." Hawaye ya hana Jalo ci gaba da Magana. Cikin kalaman tausayi Nasrin ta ke magana "ka yi hakuri Allah Yana sane da kai....' " Kuka ya hana ta ci gabada magana itama. 59 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Jalo ya ci gaba da cewa "Yau da ba mutuwa da sai in ce na lalace, ko da a ce jinya ba ibada ba ce da sai in ce nayi hasarar kai. Na ga wulakanci dukka-dukka watanina shida da fara jinya sai dai kawai na yanke shawarar yin hakurida komai don Shi Allah ba Ya kuskure. Watarana ina zaune a asibiti sai ga Rayyana ta shigo da tsohon saurayinta wai ya zo ya gaishe ni, na yi mamakin ganinsu tare. Ko dan na zama haka shine ta fara nemo samarinta na baya, ko daman suna tare ni ne ban sani baoho? 66 Saurayin ya kalle ni a yamutse ya ki zama ma yace, yanzu Rayyana haka zaki ci gaba da zama da wannan mijin na ki? Ai bashi da wani amfani." " Sai ran mabaifiyata ya ɓaci ta fusata ta ce masa"yaro! Da shi da yake kwance da kai da ke tsaye waye ya san gawar fari? Abin duk na Allah." Ya yamutse fuska ya fice.ita kuma Rayyana ta tashi ta bi shi a bayansa, suka fice ni da mahaifiyata muka yi kuka har muka lallashi kanmu.Kin san ya yi mana haka da 60 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 kwana uku, ya yi hatsari ya rasu a take. Rayyan ta sha kuka a gabana babu kunya.” Nasrin ta rike kai ta ce "wayyo Allah. Allah abin tsoro ne. " Jalo ya matse hawaye ya ce, "Kullum muna zaune a waje daya jiki dai yana nan yadda yake, sai dai ana ta kawo mana labaran wajen masu maganin gargajiya aka ce ana warkewa. Ba mu da zaɓi sai muka tafi Bidda akwai wani kauyen nufawa mai suna Gayko, cikin kauye kayayau mota ma bata shiga sai bukkoki. Daga inda muke da in da ake zuwa ɗauko ruwa tafiya ce mai nisan gaske haka abinda zaka saya ma ka ci babu, rogo da gyada muke ci." Nasrin ta langwaɓe kai ta girgiza kai ta ce, "Allahu akbar! Allah Ya sa kaffara ne." Jalo ya ce, “amin. Sai da gorin makwabta ya yiwa Rayyana yawa sannan ta nemi kauyen da muke ta zo, da jakar kayanta. Ta tsaya kawai tana kallon yadda muke rayuwa tabbas na san ba zata iya ba saboda rayuwar da muke yi ma a Lagos ta raina balle a nan. A daddafe dai muka yi kwanaki biyu tare 61 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 da ita. Mahaifiyata ceke ta faman dauko ruwa, har wata Mata mai suna Aisha ta fara tausayawa tsohuwa, sai ta karɓi jarkar ta je ta ciko mata da ruwa ta kawo kofar dakin nan ta dan ajiye,kafin Mama ta ta kasafta ruwan cancanawa muke yi Rayyana ta dauke dukka ta je ta yi wanka da shi. Sai Mama ta yi mata magana ta ce, "yanzu ruwan wankan mutane uku kika dauka ki ka yi wanka da shi dukka? Alhali ke ba daukowa kike yi ba,ni ba karfi ne da ni balle in jido, makwabciya ta tausaya min ta ɗauko min kuma ki ɓata gaba daya." " Budar bakin Rayyana ke da wuya sai ta ce “eh ba zan ɗauki jarka in je in debo ruwa ba dan a gidanmu ba mu saba dauko ruwa ba. 66 Sai na shiga maganar nace Rayyanakada kiyiwa Mama rashin kunya, na san zamanmu anan ba zai yiwu ba, ki dauki jakar kayanki ki koma in da kika fi wayo." Nan da nan ta dauki kayanta ko sallama bata yi manaba ta juya ta yi tafiyarta. Duk da halinda nake ciki anaba ni albashina kuma a ciki nake cewa ta ciri kudin abinci dana 62 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 makarantar yara, amma ta ɓoye bata fadawa iyayenta gaskiya ba, nuna musu take bana bata komai su suke ta aiko mata da kudi suna tausaya mata." Nasrin ta girgiza kai ta cė, "Tir da halinta, bata ci wannan suna ba Rayyana." Jalo ya ce, "Ga magani ana ta yi amma abu sai kara muni yake sai aka kai ni TeachingHospital na Maiduguri, a inda aka yi min tiyata na mafitsara." Nasrin ta dube shi cike da tausayi ta ce "Allah Ya sa anyia sa'a "." Jalo ya ce, "toh Alhamdulillah kawai za'ace. Gidan da nake ciki kinsan na ce ansayar min zan dinga biya a hankali,Mai gidan Alaja Allah Ya yi mata rasuwa dan haka yaranta suna son cikon kudinsu da gaggawa ko su siyarwa wasu, dan haka sai hankalina ya tashi na cewa Babanta ko zai saya saboda a ganina zai iya sayawa 'yarsa Rayyana ko jikokinsa guda biyu da yake matukar so, wato 'ya'yana. Amma sai ya aiko min miliyan daya, sannan ya je ya biya masu gida cikon 63 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 kudinwanda suke bina, shikenan gidan ya zama nasa. " Nasrin ta buɗe baki tana mamaki ta rasa me zata ce. Hawaye yana kwaranya daga idanuwan Jalo ya ci gaba da cewa "abin ya yi min ciwo sosai saboda mun yi da wani abokina zai bani miliyan biyar, kuma sannan ya cika musu kudin da suke bina. Amma ban damu ba dan na san ko ba komai dai ba zai kori ‘yarsa da 'yayanta daga cikingidan ba." Nasrin ta cije baki dan takaici ta ce, "Allah Ya sawake. " Jalo ya ci gaba da cewa "Ba'a dade da yin haka ba sai Babanta ya turo min kannensa suka zo suka duba ni a Asibitin Lagos. Sannan suka faɗa min wai yau shekarata daya da watanni biyar da kwanciyata ciwo, ko a kotu alkali shekara daya yake bawa marar lafiya idan ba'a warke ba sai a bada karin watanni biyu, idan mutum bai sami sauki ba kotu tana raba aure. Haka alwalina ya saka ni a gaba yace in sake ta saboda sun daɗe suna damunsa da maganar saki.” 64 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Nasrin ta zazzare ido tana mamaki, ta sunkuyar da kai kasa sai hawaye ya surnano daga idanuwanta. Jalo ya surnano da hawaye ya ci gaba da cewa "ina hawaye na rubuta mata takardar saki daya, ba kukan rabuwa da ita nake yi ba sai kukan yadda so saboda Allah ya yi karanci, na kuma tausayawa yarana da muka haifa tare. Rayuwarsu abin tausayi kasancewar Mahaifinsu na zama abin tausayi.". ni Nasrin ta runtse ido ta surnano da hawaye ta dago ta dube shi cike da tausayi ta ce, "Allah Ya musanya maka da wata mafi alkhairi. Yanzu ina Rayyana da yaran suke?” Ya girgiza kai ya ce, "tunda muka rabu basu taɓa tunanin kawo min yarana na ganni ba, duk da damunsu da suke yi da maganata." Allahu Akbar!~ *** Nasrin ta mike tsaye ta fito waje a gigice inda ta ci karo da Maman Jalo ta na laɓe tana 65 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 jinsu ta yi kuka har ta gaji. Nasrin ta rungume ta suka daɗe suna kuka. Mama ta sharce hawaye ta ce, "mun gode da kauna amma ki zo ki koma gida da wuri kada a neme ki." Nasrin ta girgiza kai ta ce "a gidan yayata nake amma na faɗa matazan kwana ana ta ji labarina ta ji labarin Jalo.". Mama ta yi shiru tana tunanin yadda rayuwar 'yar gayun nan wacce babu tabo a jikin ta zata kasance a cikin kauyen nan.Shin me zasu bata ta ci? A ina zata kwanta ma. Ta yaya zata iya doguwar tafiya zuwa rafi dauko ruwa? Yaya zata yi da mahaukata da kutare da ake taruwa waje daya idan mai magani ya zo ganin marassa lafiya?" Nasrin ta katsewa Mama tunanin da take yi ta ce, “Mama yanzu me za'ayi in taya ku? Dauko ruwa ko shara?" Mama ta kalle ta da jajayen idanuwa wanda ta sha kuka ta ce, "Babu wani aiki Nasrin, sai dai muna zuwa dauko ruwa, yanzu zan je in dauko, ki kula da shi har in dawo." 66 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Nasrin ta ce, “mu je tare Mama idan na ga wajen sai in ci gaba da zuwa ni kadai ke sai ki huta.' " Mama ta dauki jarka daya ta bata ɗaya suka tafi, Jalo yana zaune daga daki yana jin su yana mamakin yadda halin Nasrin ya ke. Ya ji a ransa dama lafiyarsa kalau da ya sami matar kirki. Amma ya san komai da sanin Allah Ya ke faruwa. Sun sha wahala sosai a tafiya haka a dawowa har kamar Mama ta fi Nasrin kokari dan Nasrin bata saba ba ta jigata sosai.Sai da aka taya ta saukewa wuyanta ya kage. Jalo ya kwalla kiran Nasrin ta shiga fuskarta cike da murmushi Ya dube ta ya yi murmushi yace "sannu da aiki. Kada ki damu ki zo ki tafi gida na gode da kulawarki." Nasrin ta girgiza kai ta ce "kada ka damu zan zauna tare da Mama." " Ya girgiza kai yace, "za'a neme ki a gida." Ta girgiza kai ta ce, "'yan gidanmu sun san zan zo nan. " 67 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Ya daɗe yana tunani ya ce mata "ga wayarki nan tana ta kara a cikin jakarki." Ta zabura ta dauko ta duba abin mamaki sai ta ga sunan Malaika, ta kira ta ya fi sau goma. Sai da Jalo ya gane ta shiga wani yanayi na mamaki. Ya zabura ya tambaya "lafiya kuwa?" Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "wata kawata ce." Ta na rufe bakinta sai wayarta ta sake yin kugi, tana dubawa ta ga sunan, Zainab. Bata yi mamaki ba dan ta san ya kamata daman ta neme ta. Ta danna sannan ta yi sallama, Zainab ta amsa bayan sun gaisa. Zainab ta tambaye ta ya bata dawo gida ba har yanzu? Nasrin ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Kada ki damu Anti Zainab ina cikin koshin lafiya kamar yadda na fada miki na zo Bidda dubaDr.Jalo.' " Zainab ta zazzare ido ta ce, "Bidda? Yaushe zaki dawo?" 68 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Nasrin ta yi shiru can ta ce, "zan kwana biyu. Lafiya dai ko?" Zainab ta ce, "kawarki ce Malaika ta dawo ina tsoron zuciyarki nace ta zo ta tafi kafin ki dawo. Ta ce da gaske mijinta ya sake ta, gata ma ta taho da takardar saki. Ni fa bazan iya wannan rigima irin ta ku ba, gata da naci. Nasrin ta yi tsaki ta kashe waya. " Zainab ta sake kira sai Nasrin ta kalli Dr.Jalo ya kura mata ido da alama abinda ya ke tunani ma daban ne ba ya ma gane abinda suke cewa. Hakika ransa ya sarkafu da son Nasrin musamman da ya tabbatar da gaske take sonsa. Ciwo ne bana karau ba da babu abinda zai hana ya kasance tare da ita. Ya ji kwalla ta cika masa ido har Nasrin ta fara ganewa ya na cikin halin damuwa. 22. Ta yi murmushi ta mike da sauri ta ce "yi hakuri minti biyu, zan fita in amsa waya. Ya gyada mata kai ba tare da ya iya Magana ba. Tana fita Mahaifiyarsa ta shigo da katuwar roba wacce zata zuba kayan kazanta 69 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 m idan ta gyara masa jikinsa. Ta kara kofa dan kada Nasrin ta dawo idanuwanta su gane mata. Tana can gefe tana amsa wayar Zainab da Malaika. Idan rayukan Nasrin da Zainab ya yi dubu yau ya ɓaci, saboda Malaika matsala ce. Ta dage ita ba zata koma Kano ba anan Abuja zata zauna, zawarcinta karakaf a gidan zata yi har sai Allah Ya bata miji ɗan Abuja. Zancen karatu da aiki ma ta ke yi. Idan suka takura sai ta tafi sai ta ɗauki kuka irin na mutuwa ta ce "ko wanke-wanke ne su bata za ta yi mata, an tsane ta a gidansu. Nasrin ta yi wani tunani sai ta ce Zainab ta bawa Malaika waya zata yi mata magana. Kuka kawai malaika ke rusawa. Nasrin ta lallashe ta ta ce shiru su yi magana.Malaika ta tsahirta da kuka tana sauraron Nasrin. : ta yi shiru Nasrin ta ce "Malaika! Tabbas kina kaunata kuma bazan guje ki ba. Sannan ban iya wulakanta dan adam ba. Kin zame min dole amma baki zama dolen Zainab ba, tunda bana 70 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 gidan ki biyo ni ki zo ki same ni a Bidda tunda babu nisa da Abuja.' " Malaika ta washe baki ta yi dariyar dadi ta ce "ina ne Bidda? Gidan wa?" Nasrin ta yi murmushi ta ce, "Minna ne.Gidan Gwamna ina tare da matarsa acan zan kwana biyu. Ki zo kawai." Malaika ta ji kamar ta yi ihu dan murna. Nan da nan ta hau godiya. Nasrin ta ce ta bawa Zainab waya zasu yi magana. Zainab ta karɓi waya ranta a ɓace dan ta gaji da lamarin Malaika da Nasrin. Nasrin ta yi murmushi ta ce, "ki sa direba ya kai ta tasha yanzu,asaka ta a motar Bidda yanzu muna waya har ta karaso in da nake kada kice mata fa a wajen masu magani muke." ta kashe waya. Nan da nandireba ya kai Malaika tasha da katuwar akwatinta ta shiga mota.Farin ciki ya cka mata zuci tana tafe a mota tana murna, kawai hango ta take a gdan Gwamna ta baje, sannan ta hango ta a motar Gwamna ana yi Zainab ta amsa sannan 71 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 mata jiniya. Babu abinda take hangowa sai rayuwarta ta da Shamaki cikin kunci, yanzu kuma ta hango rayuwarta yadda zata kasance a cikin ni'ima.Bata san sanda ta kyalkyale da dariya ba a bayyane. Har mutanen cikin mota suka juyo suna kallonta, sun fara tunanin ko ta zare ne. Suka isa Bidda, Malaika ta kira Nasrin a waya ta ce gata a tasha, a turo Motar gidan Gwamna ta dauke ta. Nasrin ta ji dariya ta turnuke ta ta toshe baki ta yi dariya sannan ta ce "ki nemi motar garin Agay, daga nan ki hau Motar Goyko kina sauka sai ki tarimai acaɓa ki hau ki bashi wayazan fada masa in da zai kawo.ki." " Malaika ta zabura, ta zazzare ido ta maimaita ta ce "Acaɓa fa kika ce? Cabdijam! Au har wasu motoci zan shiga nan gaba?”. Nasrin ta kunshe baki ta kyalkyale da dariya ta ce, "ga mu nan a lambun Gwamna, muna tare da matarsa muna ta shan kayan marmari, sai da magriba za mu koma gidan Gwamnati. Ki yi sauri." 72 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 " Malaika ta yi dariya ta amsa"yauwa ga motar can ma na ji ana cewa Agay." Ta tafi da sauri ta shige, bata daɗe da shiga ba ta cika suka kama hanya. Tafiya mai nisan gaske sannan suka isa. Suna Isa ta kira Nasrin ta sake tuna mata sunan daya garin wato Goyko. Malaika ta nemi motar Goyko ta shiga suka tafi, da ta isa ta kira Nasrin ta ce ta nemi mai acaɓa ta bashi waya zata kwatanta masa. Malaika ta zunɓura baki ta ce "Ga dan acaɓa ma ya zo,ki kwatanta masa. Malaika ta mikawa dan acaɓa waya ya karɓa Nasrin ta yi masa bayani sosai nan da nan ya gane dan garin ba ɓoyayye bane. Ya dauko Malaika niki-niki da kaya suka fara tafiya, ashe ma tafiyar da ta yi ma a baya wasace lungu da sako sai yanzu suka surkumo. a Hankalin Malaika ya tashi kwarai tun tana hango hango girman lambun Gwamna zuciyarta har ta fara hango kabarinta. Ta fara zargin ko siyar da ita Nasrin take shirin yi. 73 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA Idan ta kalli keyar dan acaɓa nama dumu-dumu sai taga ya yi mata kama da ɗan yankan kai, gashi baya jin Hausa dukka tambayoyin da take yi masa baya ganewa. Ta kwajiɓa turanci ta ce ya tsaya. Su kaɗai a dokar daji babu gida gaba babu gida a baya. Ya shaida mata akwai 'yan fashi a hanya idan ya tsaya zasu fito su kama su ko su kashe su, musamman suna ganinta da katuwar akwati. NI CE...2 Idanuwan Malaika kawai zaka dinga hangowa a bayan acaɓa, kai kace Mujiya aka jefa a rami. Salati take yi a bayyane tana kiran sunan Iyayenta na yanka akan su yafe mata rayuwarta ta zo karshe. Nasrin kuwa tsinuwa take sha ba adadi yayin da dan acaɓa yake shan asharai da tofi a keyarsa. Ta tofa masa addu'ar aljanu ta ga bai ɓace ba, ta tofa masa ta neman tsari daga azzalumai ta ga bai razana ba. Aikinsa yake kawai yana shirga gudu fatansa ya kaita ya karɓi 'yan canjinsa, addu'arsa idan ya kaita ya samo masu fita ya fito da su riba biyu kenan. Malaika ta kira Nasrin a waya, Nasrin ta amsa da sauri sai ta ji Malaika tana kuka tana 74 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 yi mata bayanin dokar dajin da suke ketawa. Nasrin ta kwantar mata da hankali akan ba guduwa zai yi da itaba haka hanyar take. Gonar tana karshen garin ne. Malaika ta ji dan sanyi a ranta, suka ci gaba da tafiya basu iso ba sai da daddare. Nasrin tana tsaye a farfajiyar gidan tana jiransu, sai ga idanuwan Malaika

Chapter 3 of 6