Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 6
ta zo ta durkusa ta gaishe ni alhali ni da kafafuwana nake takawa. Abokaina suka dinga sha'awar wannan soyayya ta mu suka d: Ingab ni goyon baya akan in aure ta tana sona kuma wannan ta tabbata mace ta gari." Nasrin ta girgiza kai cikė da tausayi ta ce, "Allah sarki. Soyayya ba karya ba ce.' " Jalo ya yi murmushi ya ce, “haka ne amma za ki sha mamaki nan gaba. Ni dai ina ta tsoro saboda bana son kai kaina gidan masu hannu da shuni. Na fi son in koma garinmu in auro 'yar dangina zata fi yi min biyayya ina tsoron irin matan nan da aka hadu da su a Bariki. 26 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Duk halinda nake ciki sai da na shaidawa Mamana tun ranar farkon haduwarmu da Rayyana. ' Na dinga jan abin dan ina so in gama tantancewa da gaske ina tsoron masu kudi saboda ni dan talaka ne. Da gaske tana so na a yadda ta nuna min ba matsala kuma a shirye take ta yi min biyayya. Ban ɓoye mataba na shaida mata bana son auren masu kudi dan ina da nawa ra'ayin ina da tsare-tsaren da nake so gidana ya kasance. Ta nuna min zata yi min biyayya kuma lahirarta take nema. Nasrin ta yi kabbara ta ji Payyana ta burge ta ta sha yabonta. Jalo " ya ci gaba da cewa Haka abokina sulaiman ya dinga karanto min kyawawan halin Mahaifanta da ita kanta. Har sai da na ji na gamsu da ita zuciyata ta nutsu. Ashekarar nagama makaranta na barta a label2, ina gamawa na fito da aikina aka dauke ni kyarwa a makarantar kasancewar sakamakona ya fi na sauran dalibai kyau. 27 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Sai aka fara shirye-shiryen aure dan a lokacin an sanni a gidansu haka nima kowa ya ji labarinta a dangina. Amma abu daya na lura Babanta kamar baya son auren duk da an shaide shi da kirki amma ni kamar baya sona ya yi ta wahalar da mu dakyar dai ya fara kula ni akan bukatata ta neman auren 'yarsa. Tashin farko ma yace in je in kawo masa gwaji na kanjamau amma bai ce mu je mu yi tare da 'yarsa ba, saboda ina sonta na je na yin na kawo masa. Sai yace in dauko biro da takarda na dauko na mika masa, yace sai na rubuta a alkawari na saka hannu akan a lallai-lallai zan bar ‘yarsa ta kammala karatu sannan ta ci gaba da karatu bayan ta hada digii na biyu kuma zata yi aikin gwamnati. Tun daga nan na tabbatar gidana ba zai yi karko ba, da farko na ki na rubuta saboda ina ganin in har baban matata ya shiga juya gidana akwai matsala sai da jama'a suka taru suka dinga bani hakuri suna nuna min ba komai ba ne harkar manya kuma 'yan boko haka take. Na ga shi matansa uku babu wacce ta yi degree balle mai aikin gwamnati kuma 28 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 iyayensu basa shiga harkar gidansa, yana da cikakken iko akan iyalansa. Dole na rubuta ya saka hannu nima na saka." Allah." Nasrin ta yi ajiyar zuciya ta ce, “ikon Jalo ya yi murmushi ya ce, "Hmmm! Ai kadan kika ji ma.Aka yi aure cikin girma daman su ne masu karfi su suka dauki kusan dawainiyar auren gaba daya haka na yi iya yina, na samo hayar Babban gidan da zata iya zama aka cika mata da kaya amma ni kayan daki ba shine aka burge ni ba fatana ta yi biyayyar aure." " Nasrin ta yi murmushi ta ce, "Allah sarki, ka ji masu arziki masu yi dan Allah.' " Jale ya yi murmushi ya ci gaba da cewa "sun so su bani gidan zama a Lagos, na ce masu zan nemi gidan haya.Na hada lefe daidai karfina da gaba daya abinda al'ada ta tanada . amma a Bauchi aka yi bikin, dangina daga 'Yalleman suka ciko mota-mota suka je biki haka Mahaifiyata itama da tawagarta suka taho daga Lagos. 7 An yi biki komai a wadace kuma Mahaifin Rayyana ne ya dauki nauyin komai, 29 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 aka shirya mata gida a Bauchi ba tare da sanina ba ma dan ba'a shawarce ni ba. Anan aka kai Amarya aka watse aka bar Ango aka ce saimunyi sati biyu za mu dawo Lagos, saboda danginta su gama zuwa ganin daki. Daga nan na tabbatar ba ni da 'yanci sai abinda Hajiya da Alhaji suka tsara min. Aka biya mana 'Yankari Game reserɓe'dan mu je mu huta, ni dai ina biye da su ba ni da cewa. " Nasrin ta gyara zama ta ce, “Ikon Allah. Abinda ka ke gudu kuma shi yake shirin afkuwa ko? Ina gidan da ka kama mata na Lagos?" Jalo Ya cije baki ya yi shiru na dan lokaci sannan ya ci gaba da cewa, "gidana na 'Lagos Island' ma an cika shi da kaya kafin ma a taho bikin.” "Yaya aka yi to?" Nasrin ta tambaya cikin zumudi. Ya ci gaba da magana ya ce, “muka dawo gidanmu na Lagos na ci gaba da aikina itama tana karatunta. Amma fa tun ba'a je ko ina ba na fara fuskantar matsala." 30 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Nasrin ta ce "Allah sarki. Wacce irin matsala kuma?" Ya ci gaba da cewa, "Bayan mun tare an yi. farin ciki na amarci kamar na watanni biyu kafin halayar gaskiya suka fara bayyana. Matsala ta farko da muka fara samun damuwa itace yawan zargina, ba damar in je aiki sai ta kira ta ce ta ji muryar Mace a kusa da ni haka idan na dawo gida ta dinga binciken wayata dan taga sako ko kiran da bata gamsu ba ta yi masifa, ban isa in fita unguwa ba sai ta ce zance na je amma duk na ɗauke shi a matsayin so kuma halinsu na mata. Abu dai ya yi ta gaba-gaba na tantance Rayyana ta raina ni bata ganin darajata balle tr ‘yan uwana talakawa idan suka zo, haka abin ya gangaro kan abokaina, dan ta zagin abokina akan idonsa ma ba komai ba ne. Bata dafa min abnci sai dai in fita in saya tamkar ban yi aure ba amma ana ta bani shawara ana bani hakuri an ce idan ta haihu zata bari. Bayan shekara da yin aurenmu Allah Ya bata haihuwar da namiji, sai na ga rashin mutunci kamar ana kara mata, ta kai ta kawo 31 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 m babu abokina da yake iya zuwa gidana saboda tsoron rashin mutuncinta. A 'yan uwana kuwa karwata ceFatima kaɗai ta taɓa zuwa gidana ta yi min kwanaki amma bata ji da dadi ba, suka rabu baram-baram ta koma garin da take aure. Kullum na kira surukata zan gaishe ta sai ta balbale ni da faɗa ta ce ta gaji da halayyata ina wahalar da 'yarta, ba taga amfanin auren nan ba dan bani da hakuri. Ba sa ganin laifin 'yarsu ko kaɗan kullum karana take kaiwa tana ɓata ni. Na yi takaici da da-na-sa-ni ban yi auren nan ba saboda ko daya bata taɓa nuna min halayenta na gaskiya a waje ba, da duk son da nake yi mata da ban aure ta bo. Allah cikin ikonsa wata rana wata matsalarsu ta haɗo ta da Mamarta da yayanta suka zo suka same ta a falo suka yi mata tatas, sai a lokacin mahaifiyarta ta yabe ni cewar ba dan uwa uwa ba ce da bazata iya da halin 'yartaba, dan albasa ba ta yi halin ruwa ba. Yayanta uwa daya, uba daya yace, “da ace matar da zan aura mai irin halinki ce ko na yini daya ba zan iya zama da itaba saboda 32 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 rashin jin maganarki da rashin mutuncinki. Jalo ya yi hakuri da ya iya shekaru da ke.' " Ina jin haka sai na dafe kai nace “innalillahi wa'inna ilaihi raju'un. Allah Ka canja min halin kunci da nake ciki na zama da matar nan. Muka ci gaba da rayuwa a haka watarana na sami wata harka ni da abokaina, ta karamar kwangila na fita tunda safe ban dawo gida ba sai karfe tara na dare, na shigo na same ta ta cika ta batse gaba daya ita a rayuwarta mummunan zato take yi min a tunaninta wajen 'yan mata nake zuwa saboda taga na fita da abokina Yahya shi kuma baiyi aure ba kuma tana ganinsa da ‘yan mata a jami’a. Ita da take da auren ma ina ganinta da maza'yan ajinsu kuma tana karɓar Note dinsu ta zo gida da su amma ni bana zarginta. Na yi mata sallama ta ki ta amsa buɗar bakinta ke da wuya sai ta yi min addua wai 'Allah ya sa in yi hatsari motata ta yi kwarankwatsa da ni.' Kalmar 'Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un.' Na ambata na shige daki na barta. 33 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Haka na ci gaba da zama da ita cikin rashin ‘yanci da fargaba, ina ta takatsantsan dan kada in ɓata mata rai a ce nayi laifi. Idan tana fushi da ni sai ta huce akan ɗana guda ɗaya wanda na ke matukar ji da shi, dan ta fahimci raina yana matukar ɓaci idan ta taɓa masa, sai take hucewa akansa. Watarana tana fushi da ni sai kuwa ta tunkuɗe shi ya fadi akan tiles da ya zo da tsautsayi sai ya karye, muka sha faman zaman asibiti na kashe kudi sosai amma ta fadawa iyayenta wai faɗowa ya yi daga kan gado. Haka har rana irin ta yau ban faɗawa kowa cewar ita ta karya shi ba." Nasrin ta yi tagumi babu abirda take sai girgiza kai tana salati a bayyane saboda tashin hankalin da take zuka a cikin kunnenta. Ya ci gaba da Magana cikin marainiyar murya "Babu wacce ban tuna ba daga cikin jifgin 'yan matan da suka so ni a garinmu Yelleman da na Lagos, na yi da na sanin barin "yan kauye masu tarbiyya nana faɗowa 'yar birni Amma daga baya na saddakar da cewa Allah ne bai so ba amma na tabbata har yanzu 34 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 2 da yawansu suna can suna sona duk da sun yi aure kasancewarwasu dangina ne mu kan haɗu a wata hidimar suna mutunta ni sosai." Nasrin ta ce "Kwarai kuwa komai sai Allah Ya yarda za ayi." Jalo ya gyada kai ya ce, "Tabbas haka ne. Wata rana Rayyana ta tsare ni ta ce Babanta yace baya so ta dinga yin tuki da kanta saboda tana da ciwon ido dan haka duk abinda nake yi na bari na dinga zuwa ina kai taunguwa. Na amsa masa da to. Haka kuma aka yi ko me nake yi sai na bari na zo na kaita unguwa wata unguwar ma kirkiro ta take yi da gangan dan ta wahalar da ni, ban damu ba saboda bana son tashin hankali ko kadan.' و, Nasrin ta bude baki dan mamaki ta ce "abin har ya kai haka? Sun zamar da kai direba ma kenan?" Jalo ya gyada kai ya ce, "Direba ma ai yana da 'yanci bawansu na zama. Rayanna bata zaman lafiya da makwabta ko kadan duk sun ɓata, gashi ni kuma da son mutane karfi da yaji ta sa nake ja da baya da jama'a. Gashi ko dayaushe tana yi min gaba sai muyi sati bata yi 35 Jamilu Umar Tanko JUT 1 DAMA NI CE...2 min Magana. Gaba daya bana jin dadin rayuwata bana samun walwala a kowanne ɓangare, babu in da zan shiga in ji sanyi a raina. " Hawaye ya cikawa Jalo ido haka ma Nasrin suka yi shiru na dan lokaci kowanne yana takaici. Nasrin ta rike baki zuciyarta cike da ɓacin rai ta ce "subhanalla! Wannan bata da ilimin addini amma ko tana da ilimin ma bata amfani da shi." Jalo ya yi murmushi yace, “ke kenan da kika san za'a mutu za'a koma ga Ubangiji ai ita ko salla ma sai ta ga dama. " Nasrin ta dafe keya ta ce, "wayyo Allah mata mun shiga uku." Ya ci gaba da cewa, "bata dade da yaye Hisham ba ta kara samun cikin na biyu. A lokacin na sami tallafi daga gwamnati tafi London karatu a UniversityofBedfordshireLuton Campusanan na yi PHD shekaru uku. (schoolership) na ' Ina zuwa Najeriya akai-akai in gansu suma idan suka yi hutu suna zuwa wajena acan 36 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 London dan a lokacin ta gama karatunta har ta fara aiki. Babu abinda ke tsakani::mu a can London din ma sai fada saboda Allah Ya yi mata mummunan zargi, duk in da na shiga ta dinga kira na a waya ta ji ko ina tare da wata, idan kuma ban amsa wayarta ba sai ta yi ta turo sakonni na zagi tana kira na mazinaci. Alhali Ubangijina shine shaidata ban taɓa yin zina ba tunda nake a rayuwata." " Nasrin ta ji kwalla ta cika mata ido ta ce "Allah sarki.” Ya sharce kwalla ya ci gaba da cewa "Idan na zo Najeriya daga London ɓacin rai ne, idan na ce su zo da fada za'a rabu; idan basu zo ba a waya zagi ne, idan na ki amsa wayarta ta yi ta turo sakonni munana. Da na ga ɓacin ranta ya na kokarin ya taɓa karatuna na share ta na daina kula damuwarta na ci gaba da karatuna dan in fito da sakamako mai kyau. Amma duk da haka sai ta je ta huce akan mahaifiyata da kannena duk da ma Mahaifiyata tana ɓoye min amma wasu daga cikin kannena suna kira su fada min a 37 |Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 ya boyc. Idan raina ya yi dubu sai ya ɓaci sai na kira Mahaifiyarta na shaida mata, bab kara haka zata bi bayan ‘yarta karara. Na zaci dan ita Mace ce, sai na faɗawa Babanta abin bani tsoro dan shima karara ya bi bayan 'yarsa, ni ma suke bawa laifi wai bana kulawa da ita na fi kula da kannena da mahaifiyata. Tun daga nan na yi alkawarin na dai fada musu komai kawai dai zan yi addu'a Allah Ya zaɓa mana abinda ya fi alkhairi amma bana son yin saki saboda darajar yarana. Ina can na ji an ce an bawa mahaifinta Minister dan haka sun kaura sun koma Abuja. Ba izinina Rayyana ta rufe gida ta kwashi yara ta canja aiki ta canjawa yara makaranta ba tare da ta faɗawa Mahaifiyata ba ta bi iyayenta, sai da kannena suka je gidan suka ganshi a datse, kwana da kwanaki da na kira na tambaye ta take fada min hukuncin data yanke. Na rabu da suna ci gaba da karatuna har Allah Ya sa na kammala na fito da sakamako mai kyau na zama cikakken Dakta. Na so in yi zamana acan in fara aiki dan Jami'ar sun so su rike ni na ji ina kishin bayar da ilimin da na 38 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 samu a turawa, ina kishin kasata Najeriya yadda gwamnati ta biya min PAR BAUER ta biya min ya kamata su more ni, ina so in zauna kusa da Mahaifiyata da 'yan uwana dan in taimake su suna cikin wahala. Haka zan so ina kusa da deman taimake su suna cikin yarana in kula da tarbiyyarsu dan ban yarda da tarbiyyar Rayyana ba daga ita har iyayenta. " JellA Nasrin ta langwaɓar da kai dan tausayi ta ce, Allah sarki.” shuvanagh nim i STS BA bududs. Ya ci gaba da cewa "Na kunso kudina da yawa na zo na biya kudin gidana da nake hay daman sun yi min magana idan ina so in saya, duk da gida na da tsada aLagos sun yi min ragi sosai kuma duk da haka ban gama biyansu ba amma na biya su fiye da rabi. Mun i da su zan dinga biyansu a hankali har in gama. Gidan wata Allaja ce mai kirki wacce take sona da alkhairi, mijinta ya rasu ya barta da dukiya mai 80 yawa. stsWIBVox ab adsy to i 2014.I Na je Abuja na zauna da waliyinta da Waliyina aka yi Magana sosai akan yadda zaman auren zai kasance, na shaida musu a tambayi Can Rayyana in har ta gaji da War la gaji da auren ta bani yarana in sauwake mata, ni ban fadi abubuwan 39 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 da take yi min ba amma mahaifinta ya zakalkale yana ta zano sharri wanda ban san an yi ba. Gaba daya wajen suka ga laifina bana sc: in yi masa musu ko in karyata shi sai da yagama fadar nasa sannan na kalli Rayyana nace ta rantse idan haka aka yi, da yake bata tsoron Allah ta rantse dan haka na bar ta da Allah. Na gyara Zama na fara karanto abubuwan da suke yi min daga nan kawunan waliyanmu ya kulle suka rasa mai gaskiya a cikinmu kin san manya sai suka ce abar zancen kuma a cire maganar rabuwa a sulhunta. Ni dai ina kan bakana ko ta biyo ni Lagos mu zauna ko ta bani yarana in tafi da su, Ta rantse ita ca Mahaifiyarta ba za'a ba ni yara ba sai dai nima in dawo Abuja a ba ni wani aikin mai kyau. A lokacin ne na fada musu karara bazan iya yin aiki a karkashinsu ba yanzu, na fi son in koma Lagos in ci gaba da koyarwata. Nan dai suka nuna basa son saki kuma aka amince zata dawo Lagos nan da watanni uku idan yara suka yi jarabawar canja aji. Aka bani hakuri na amince na dawo Lagos na zauna 40 |Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 ni kadai har tsawon watanni biyar sannan ta dawo." Tausayinsa ya kama Nasrin sai hawaye ne kawai ke fita daga idanuwanta, tana ta faman girgiza kai. Ta jawo Computer ta ta kunna ta nemo hotonsa a Facebook ta zuba masa ido tana kallon kyawu ido da hanci kamar balarabe, ga ililmi ga nutsuwa amma Rayyana take wulakanta wannan kadarar. Ta ce "Allah sarki, yi hakuri dan uwana jarabawa ce kowa da irin tasa kai kuma irin taka kenan." Jalo ya daga robar ruwa ya sha ya ci gaba da cewa "haka ne sosai kuwa. Na yarda da kaddara mai kyau da marar kyau. Rayyana ta dawo da sababbin salo na rashin kunya, bata raga min duk da bana daga ido in kalle ta amma bata kyale ni ba. Zargina take ina bin mata a jami'a dan haka ma bana kusantarta kullum addu'arta Allah Ya ragargaza ni a mota a hanyata ta zuwa wajen . Nasrin ta dafe kai ta runtse ido ta ce, "Wa'iyyazu billah." 41 Jamilu Umar Tanko JUT NDAMA NI CE...2 Jalo ya girgiza kai yace, “kadan ma kika ji daga cikin mugayen jafa'in da take jawo min. Kullum ta ce min ina takama da kyau da ilimi sai na yi rugu-rugu, kyawun ya disashe a kwabo ma babu mai dauka ta." 99 Nasirin ta gyara zama ta ce, "amma wannan ba kaunarka take yi ba. Subhanallah!" Jalo yace, "na dade da gane haka bata kauna ta ko kadan.' 99 Nasrin ta ce, “meyasa ta dage sai da ta aureka? Kuma sun fi ka kudi balle ace kwadayi ne. " Jalo yace, "ina ga saboda kyawuna take sona, ko ilimi, kuma tana son auren talaka ta taka shi ta yi abinda take so ni kuma na ki: binta in yi wasu abubuwan. Duk abinda shari'a ta hana bana yi. Koda yaushe Rayyana addu'arta a gare ni kenan Allah Ya kwace aikin nawa ma taga yadda zanyi takama. Dan haka zaman gidana ya fara gagarata kullum daga wajen aiki sai gidanmu wajen Mamana ita ke dafa min abinci, tana mai lallashina da bani baki akan in yi 42 Jamilu Umar Tanko JUT MAMAN DAMA NI CE...2 hakuri in daina damuwa. Allah Yana tare da mai hakuri⠀⠀⠀⠀⠀880 ht Yarana suna sona basa bacci sai na dawo haka zaá mumu viyi was wasa da tsalle-tsalle, zan kai su makaranata in ɗauko su. BBB R (BO suals A haka muke har watarana and de mana hakamuke harwatara штаби Allah ya aiko slide oqush Seb Ed yajaikums da hatsarin mota ni, ita,yaranmu ,direbana da kanwarta.' "BYD ORAMA BY Nasrin ta firgita ta mike tsaye gami da dafe kirji ta ce, "hatsari fa ka ce Yaya Jalo?" Ya surnano da hawaye yace, "hatsari ***** muka yi kanwata.” solst ou slud sisw Nasrin ta langwaɓe kai ta koma ta zauna ta jingina da bango ta ce "Allah Ya sa ya zo muku da sauki.' BIE headmet gashi 66 Jalo ya ci gaba da cewa amma yau shi baki sanni baba baadhi baki t:ɓa ganina ol ba amma kin yi min adaddu'a. Ya Allah ina rokonKa da ka 8082262 Tube 90 61 162006. amsawa Nasrin bukatunta na duniya da lahira Asobi sebel 6 Sai Nasrin ta zare ido ta cika da mamaki Rosli ina nols exp BOUL BWSIE J dub zuciyarta cike tambayoyi masu dinbin har ma bata san ta in da zata faraba. greet of overand U16 Bawa b 60 Bbat cl6x sbaids 43 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 "Dakta Jalo ban fahimce kaba, kana nufin kunyi hatsari har ka ji mummunan ciwo matarka bata yi maka saanu ba?” Bai bata amsa ba sai ya kashe waya da alama baya son maganar. Nasrin ta sake kiransa, wayar tana shiga amma bai dauka ba, data dame shi da kira sai ya kashe wayar gaba daya. *** *** *** Nasrin ta fito falo a gigice gami da yaye wata hula data tuma a kanta ta wurgar a kan kujera saboda gumin da ya keto mata. Kamar daga sama ta ji murya ana tambayarta "lafiya?" Ta daga ido ta dubi mai Magana, Zainab ce, sannan ta sassauta ta ɓoye damuwarta amsar ita ce "babu komai, ina jin zafi ne?" Zainab ta daga ido ta kalli Ac dake kunne sanyi ya cika falon sai itama nasrin ta dubi AC suka kurawa juna ido. Nasrin ta juya da sauri ta shiga daki ta rufe ba tare da tasan abinda zata faɗa ba. 44 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 YEARS Zainab ta faca a bayyane "Allah Ya baki lafiya toh." Nasrin ba ta ma san har karfe ɗaya na dare ya yi ba sai da ta duba agogo, dan haka ta kwanta zuciyarta cike da damuwa. Asuba ta gari! *** *** *** a Da safe ma ta gwada kiran Jalo bata shiga ba har yanzu bai kunna waya ba. Labarinsa ya na ta yi mata zagaye kwakwalwa tana so ta ji ci gaban wannan abin tausayi. Tana mai matukar son ya karɓi bukatarta shine ya yarda ya so ta ya ga yadda ake kula da miji. Ta ji tana son Jalo amma tana tsoro ko zai sake yarda ya auri yar masu kudi saboda ya sha wuya a baya. Ta na kallo ana ta kiranta daga ofis amma ta ki amsawa ta san ana matukar bukatarta amma ko ta je ta san ba zata moru ba damuwa ta buwaye ta. 45 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Ta ga kiran Shamaki da Malaika ma ta ki amsawa dan ta san wata damuwa zasu kara iza mata. Dinah ceke ta kiranta ta ki ta amsa sai da ta ga kiran ya yi yawa sannan ta amsa wayar. A tunaninta hakuri dina zata bata dan ta ɓatamata rai jiya sai ta ji akasin haka. Dina ta balbale ta da fada akan maganar Fu'ad daga nan ta tabbatar Fu'ad ya yada ta har ma ya kara da sharri dan wasu abubuwan ma ba'ayi ba. Ba ta da lokacin sauraren wadannan maganganun dan haka ta kashe wayarta ba tare da ta cewa Dina uffan ba. Dina ta fusata ta ci gaba da kira Nasrin ta ki ta amsa, ta fito falo ta gaishe da Zainab ta iske ta tana cin kwadon zogale ta zauna suka ci tare ba tare da suna yin hira ba. Da suka gama Nasrin ta fita farfajiyar gidan tana shawagi hakika huhunta yana bukatar iska mai sanyi dan ya cushe da takaici. Ta gaji da shawagi ta shigo falo suka hau kallon kallo da zainab har ta shige daki bas u y 46 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Magana ba, da alama Zainab ta gaji da ɓata yawun bakinta wajen tambayarta. Nasrin tana shiga daki ta iske kira rututu amma na Dr.Jalo dana Mahaifiyarta ta fi damuwa da kira. Ta fara kiran Mummy sun jima suna Magana da alama Zainab ta kai kararta haka Fu'ad. Hankalin mahaifiyarsu a tashe tana zargin Nasrin bata da lafiya dan haka ta umarce ta ta bar bautar kasar ta dawo Amerika ta yi jinyarta. Nasrin ta yi amfani da duk wata kalma ta turanci da ta Hausa da ta sani wacce za ta iya gamsar da Mahaifiyarta wajen ba ta hakuri amma Mahaifiyarta ta ki amincewa, daga karshe ma kashe wayarta gaba daya. Nasrin ta gigice ta fito falo a fusace ta sami Zainab a kicin tana mai nuna ɓacin ranta akan abinda ta yi mata gashi ta jawo an ce ta bar bautar kasa ta koma gida. Zainab ta fada cikin isa da gadara ba tare da tsoro ba, ta ce Eh ta fada dan tana kaunarta ba zata zauna ta zuba mata ido ba ta je ta kashe kanta saboda damuwa, tunda ta ki fada mata gaskiya ai dole ta fadawa wacce ta haife ta. 47 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Nasrin ta koma daki a fusace hawaye yana zuba abin mamaki tana shiga kiran Jalo yana shigowa. Ta mika hannu da sauri ta amsa gami da yi masa sallama sannan ta gaishe shi. Ya sake neman gafarar ta dan ya kasha mata waya jiya. Ta yi murmushin karfin hali ta ce ba damuwa' tana fatan yau zai daure ya karasa bata labarinsa har karshe. Ya yi mata alkawarin hakan, ta sami kujera ta zauna ta ci gaba da sauraronsa. CI GABAN LABARIN JALO Jalo ya ce, "Wata rana Mahaifiyata ta tafi garinmu Yalleman da niyyar ganin gida sai ciwo ya kwantar da ita acan. Ina zaune aka yi min waya mahaifiyata bata da lafiya sosai ko wanka ma sai anyi mata. $Y Hankalina ya tashi na yi magana da abokina Saifullahi a Kano nace ya tanadar min direban ofishinsu idan na zo Kano a jirgi sai direban ya zo ya kai ni Yelleman. Rayyana ta 48 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 ce itama zata je amma da alama taṇa so ta tsaya bikin kawarta a Kano dan na san dai ba Mahaifiyata take son ta dubaba, ta fake da haka. Nan da nan na amince, a lokacin kanwarta Salima ta zo wajenta hutu. Muka tsayar da ranar da zamutafi, mu ka dunguma mu biyar ni, Rayyana Salima, da yarana biyu muka hau jirgi zuwa Kano kafin mu iso direban Saifullahi ya zo yana jiranmu, ya so ma ya kaimu gida mu ci abinci kamar yadda abokina ya umarce da ya yi, na ki nace gara mu wuce Yelleman kawai dan hankali ya tashi sosai Mamana kawai nake so in ga yadda jikin yake. Sai dai a waya na kira Saifullah na bashi hakuri." Nasrin ta ji gabanta yana ta dukan ukuuku dan fargabar abinda zai faɗa nan gaba. Fadi take "Allah ya kawo da sauki. Allah ya yi muku afuwa." _ Jalo Jalo ya ci gaba da labara, “Ahanyarmu ta Yalleman ne Allah ya aiko mana da mummunan hadari." Nasrin ta runtse ido ta takure jikinta tana ta salati yayin

Chapter 2 of 6