Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 6
a bayan Babur tana baza su, ita a dole katafaren lambu take so ta gani da kyawawan mata. Sai ta dinga hango bukkoki da mutane a dadɗaure kai kace a lahira take ba a duniya ba. Ta sauko daga bayan acaɓa sororo da ita jikin babu laka. Ta ga Nasrin ta koɗe kamar ba itaba, dukka gayun nan babu ta daura zani daban, riga daban. Nasrin ta tsaya suna ta magana da dan acaɓa,falaika tunaninta kw gaba daya ya bata a gidan yankan kai take an gama cinikinta. Nasrin ta bashi kudin aikinsa har ma ta kara masa sannan ta bashi kudi mai yawa ta cè ya sayo mata ruwan roba katan, ya sayo musu biredi (Butter), ta ce ya sayo musu biskit da duk abinda ya gani mai kyau na ci. 75 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Yana murna ya tafi, ran Malaika a ɓace, tana tsaye tana yiwa wajen kallon tara saura kwata. Nasrin ta mika hannu zata karɓi akwatinta. Malaika ta goce ta harari Nasrin ta ce "nan ne lambun Gwamnan?" Nasrin ta tuntsire da dariya ta ce "ba wajena kika zo ba? To anan nake zama yanzu, ke ma anan za ki zauna. Ni kika sani ba Zainab ba kuma ni kike so ba gida mai kyau ba. " Malaika ta harare ta, ta ce, “bazan zauna a gidan yankan kai ba. 66 Nasrin ta kwashe da dariya ta ce, “nan wajen marassa lafiya ne asibitin gargajiya ne.” Malaika ta zabura ta kalle ta, ta ce, "wato asibitin mahaukata kika kawo ni ko? Daman na ga alamar kina yi min kallon marar hankali dan kawai na kashe aurena. " Nasrin ta dafa kafadarta sai Malaika ta ja da baya da sauri dan bata yarda da itaba, gani take wani abu zata shaka mata irin wanda aka ce anan shakawa Mutum idan za'a sace shi. Nasrin ta ce "zo mu shiga ciki ki duba jikin Dr.Jalo shine bashi da lafiya." 76 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Malaika ta zabura ta zazzare ido ta ce "wannan dan gayun kyakykyawa da na ga hotonsa a kwamfiyutarki shine ya zo nan? Daman bashi da hankali?” Nasrin ta ce, “ras yake ya fiki hankali nesa ba kusa ba. Ai kowanne ciwo ana zuwa karɓar magani ba sai mahauka ta kaɗai ba. Malaika ta taɓe baki ta fara bin Nasrin a baya amma fa sanda take yi a tsorace. Suka isa kofar daki Nasrin ta yi sallama sannan suka shiga, suka suka zazzauna akan tabarma bayan sun gaisa da mahaifiyarsa suka jira ya idar da salla, a zaune yake yi kafafuwansa a mike babu sujjada babu ruku’u, sai dai nuni da hannu. Kwalla ta cikawa Nasrin ido yayin da mamaki ya hana Malaika rufe baki. "Tabbas Jalo ne ga kamar nan. Shikuwa wanne irin ciwo yake yi haka a mimmike a zaune haka? Me ya kawo shi nan alhali masu kudi turai suke zuwa ganin likita?"Malaika ta ke tambayar zuciyarta. Da ya idar ya juyo ya kalli Nasrin ya yi murmushi yace “bakuwa muka yi ne?" 77 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Nasrin ta yi dariya ta gyada kai ta ce "eh! Aminiyata ce, sunanta Malaika daga Kano ta zo.' " Sai ya dubi Malaika ya yi murmushi yace "Malaika sannunki da zuwa." Malaika ta yamutse fuska ta yi masa kallon tara saura kwata. Ta amsa da kyar. Wannan abu ya yiwa Nasrin ciwo ta kuma Kudiri aniyyar sai ta koya mata darasi, sai ta nuna mata talauci da talaka ba abin kyama ba ne. Malaika ta yi wuf ta fito ta tsaya a waje tana hucin bakin ciki, yayin da take jiyo ihun mahaukata daga cikin bukkoki daban-daban, ana yare caban-daban. Garin abin :tsoro a tsakiyar dawa suke gaba da baya babu gari, ga duhu. Ta fara tunanin inda za'a kwanta, da inda za'ayi wanka da bayan gida anan. Jaloya dubi Nasrin cikin sanyin jiki yace "Nasrin! Saboda me za kikawo matar mutane cikin dajin nan? Banda ni babu wanda ta kama ya shigo nan ya zauna, ke ma dan kin dage zaki zauna dan babu yadda zanyi da ke ne shiyasa 78 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 na bar ki.Bai dace ba, da ta zo sai kice ta jira a gida idan ma dare ya yi gobe sai ki je ki same ta." Nasrin ta sunkuyar da kai kasa ba tare da tasan abinda zata ce ba. Mama ta yi murmushi ta dafa kafadar Nasrin ta ce "Nasrin 'yata! Tana kaunarmu shiyasa take ganin duk mai kaunarta ya zo ya zauna tare da mu ko?" Nasrin ta dago ta dube ta ta yi murmushi ta ce "Mama! Akwai dalilin da ya sa na kawo Malaika nan, ba dan komai ba sai dan ta koyi rayuwa kuma ta kara imani. Bata godewa Allah da gaba daya ni'imomin da ya yi mata. Bata son talaka da talauci.' " Jalo ya Kurawa Kurawa Nasrin Nasrin ido yana mamakin yadda take da hankali da zurfin tunani haka. Malaika ce take kwallawa Nasrin kira, dan haka Nasrin ta fito da sauri. Malaika ta harare ta ta ce, "ɗauko min akwatina zan koma gida, bazan iya kwana anan ba." 79 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Nasrin ta ce "babu abin hawa, kuma a cikin dajin nan ina zaki je ki kwana? Ki tuna doguwar tafiyar da kika yi ki ka dinga hawa motoci daban daban, sannan kika hau acaɓa." Malaika ta yi tsaki ta kama kugu ta daga murya ranta a ɓace ta ce "Nasrin!Bana ciki da iskancin banza. Ta yaya zaki kawo ni gidan mahaukata kice in kwanta?" Nasrin ta cika da mamaki ganin yadda Malaika take yi mata magana babu wannan girmamawar irin na da. Nasrin tace, "ni na ke yi miki iskancin Malaika?" Malaika ta fada a gadarance "Eh! Da ke nake Nasrin.” Daga nan Nasrin ta tabbatar ashe ba dan Allah Malaika ta nace mataba dan kudinta ne da daular da take ciki, yanzu da ba daula ba mutuntawa." " Nasrin ta ja bakinta ta yi shiru, Malaika tana ta kai kawo a kofar daki tana zage-zage a fakaice dai Nasrin take zagi. Sun ci sa'a ma akwai farin wata da ko tafin hannunsu ba zasu iya gani ba. Da aka jima sai ga mai acaɓa ya 80 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 cika alkawari ya siyo dukkan abinda ta zayyana masa. Nasrin ta karɓa ta yi masa godiya ta bashi kyautar kudi mai yawa. Sai Malaika ta daka tsalle ta haye bayan acaɓa ta ce su juya ya mayar da ita in da ya dauko ta. Nasrin ta ce masa "kada ya dauke ta marar lafiya ce guduwa take so ta yi. Kosasshen dan acaɓa ya dakamata tsawa yace ta sauka daga kan babur dinsa kafin ya wurgota, a cikin harshen turanci. Nan da nan ta sauko, ya yiwa Nasrin sallama ya tafi. Malaika ta ɗora hannu aka ta fasa kuka ta na so ta tarawa Nasrin jama'a. Ma'aikatan gidan suka rugo a guje dan suna tunani an kawo musu sabon kamu ne. Da suka karaso suka tambaya, sai Nasrin ta nuna Malaika ta ce sabuwar marar lafiya ta kawo tana so ta gudu. Ba'ayi wata-wata ba aka. damki Malaika aka daure, kamar huhun goro, sannan aka cicciɓa za'a tafi da ita tana ta ihu tana tsinewa Nasrin. Dariya ta kama Nasrin ta toshe baki tana ta tuntsirawa. 81 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Mama ta fito a gigice tana tambaya, Nasrin ta bata labaria abinda ke faruwa, Mama ta ce su kwance Malaika lafiyarta kalau, Nasrin - ma ta yi Magana sannan suka kwance ta, suka tafi. Suna juya baya Malaika ta cakumi Nasrin tana narka mata ashar, Nasrin bata iya dambe ba, bata ma taɓa yi ba. Mamaki ya hana Nasrin yin motsi tayi kasake tana kallon ikon Allah tamkar a mafarki. Tabbas ta gasgata Malaika ce ta cuci Shamaki ko tantama babu. Mama ta shiga tsakaninsu ta raba dakyar, amma ta kasa sa Malaika ta yi shiru da bakinta har yanzu zage-zag take yi. Nasrin ta shiga daki ta zauna a gefe tana kuka ya yin da Jalo ya kasa magana ya zuba ido yana kallonsu ba tare da ya san abinda zai ce ba. Mutum ne mai nutsuwa bai cika son yin magana ba. Kukan Nasrin ne yake yi masa ciwo a cikin zuciya, can da aka jima ya girgiza kai ya yi Magana cikin sanyayyiyar murya "Nasrin! Kada kiyi kuka, wannan abu bai isa ya ɓata 82 JamiluUmar Tanko JUT DAMA NI CE...2 miki rai ba.Idan kika tuna ni’imomin da Rabbi Ya yi miki.Babbar ni'ima ita ce da ya baki lafiya, Ya yi ki musulma, Ya baki ilimin saninSa kuma kina bauta maSa. Gobe ki ja ta ku koma gida. Kin ji?” Ta sharce hawaye ta gyaɗa kai. Mama ta lallaso Malaika dakyar suka shigo cikin ɗaki suka zazzauna jigum, kowa ya yi tagumi. Da aka jima Mama ta ce "ga ledojin purewater can ku sha, abincinmu shayi ne da garin kwaki ga su can a jakar bacco ku jika ku sha.' " gefe. Malaika ta harari jakar ta kawar da kai Nasrin ta mika hannu ta jawo ledojin da dan acaba ya yi mata sayayya. Manyan kifaye ne gassasu masu zafi yanzu aka sauke daga kan wuta, ga ruwan roba da biredi da butter. Ta tura gaban Mama ta ce ta raba. Mama ta dauki kifi daya ta basu ɗaya, ita da Jalo suka ci daya kuma Nasrin da 83 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Malaika suka ci saboda girmansu sai da kowa ya koshi sannan ya sha ruwa. Mama ta fara bayanin wajen kwanciya yadda za'a yi tsarin, ta ce ba zai yiwu su cakuɗa a cikin daki daya ba amma Nasrin ta je ta sami ma'aikata ta faɗa musu su bude mata ɗaki daya su yi musu shinfida sai su je su kwanta, dan taga alamar ma'aikatan suna girmama Nasrin sosai. Nasrin ta amsa ciki ladabi ta tashi ta bude Jakar kayanta ta daukozanin gado ta juya ta kalli Malaika ta ce ta taso su tafi. Malaika ma ta bude Jakarta taɗauko zaninta guda daya. Suka yi musu sallama suka fice, har sun fita bakin kofa Nasrin ta dawo ta dauki jakar ledar pure water ta fita. Suka isa wajen maʼaikata Nasrin ta yi musu bayanai jikinsu na rawa suka amsa mata saboda tun da safe take yi musu ruwan naira. Komai ma na musamman aka saka a dakin, sababbin tabarmi da fitilar kwai sabuwa an cika ta da kananzir. Bayan ma'aikatan sun tafi Malaika ta zunɓuro baki ta tambayi Nasrin bandaki, tana so ta yi alwalla. 84 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Nasrin ta ce ta zagaya baya duk ida taga ya yi mata ta tsugunna kawai. Ga purewateman ta yi alwallar da shi. Malaika ta daɗe tana hararar Nasrin, ita kuwa ta yi kamar bata san tana yi ba, ta ci gaba da daddana wayarta. Malaika ta fusata ta dauki ruwa leda 2 ta fice. Ba jimawa ta shigo ta tayar da Sallah. Abin Mamaki sai ga Jalo a facebook ya turo Sako (Post) ya yi Magana akan bayin Allah masu kaunar juna saboda Allah, ya haɗa da addu'a Allah Ya sakawa masu kaunar mutum saboda Allah. Aka yi ta sharhi da Amin, Amin. Dadi ya rufe Nasrin tabbas ta san daita yake wannan Magana. Bata san sanda ta fara murmushi ita kadai ba har da daga hannu sama tana addu'a. Malaika ta juyo tana harararta tana mamakin yadda har take farin ciki a cikin wannan surkukin dajin. Nasrin ta zankaɗo sharhi ta tura, tana mai sake jaddawa cewar Aljannar masu kaunar juna dan Allah daban ce, sai ga Jalo ya tsinci 85 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 kansa yana mai murmushi. Bai ce komai ba bayan ya karanta sai ya sauka. Nasrin ta jira ta ga bai dawo ba sai ta hakura ta rage fitila ta kwanta suka yi kai da Kafa Malaika tana ta habaici tana tsaki akan an cuce ta duniya da lahira da aka kawo ta daji aka jifge, tana addu'a Allah Ya gaggauta yi mata sakayya. Nasrin bata kula ta ba dan ta fi kowa taship hankali bata san yadda bacci zai dauke nan, babu gado, babu AC. mu dalla ta banAi kuwa ba ‘a jima ba munsharin Malaika ya fara tashi da alama daman ta saba da kauye amma Nasrin ta kasa. Wayar Nasrin ce ta dauki kara abir ya razanata kuma ya bata mamaki, tana dubawa ta ga sunan Jalo, dadi ya rufe ta jikinta na rawa ta amsa, ubbe anct Yana Magana cikin rada yace, "Nasrin ! Ba ki kwanta ba ko? Daman na san ba za ki iya bacci badan ba ki sababa. Na damu da yawa na san ba zaki iya ba. Dan Allah ku koma gida gobe ba dan na gaji da ku ba sai dan kawai bai ohet sy 9o audeb HallA neb so 86 |Jamilu Umar Tanko JUT Toldot ( | 28 un DAMA NI CE...2 dace ku cutu ba. Na gode da kara da kaunar da kika nuna min." " Hawaye ne yake kwaranya daga idanuwansu su dukka, Nasrin ba ta iya magana ba saidai sheshshekar kuka. safe. Ya kashe waya bayan ya yi mata sai da Nasrin ta tashi ta zauna tana rusa kuka tana addu'a Allah Ya bawa Jalo lafiya. Malaika ta juyo ta harare ta ta ja tsaki ta juya keya ta ci gaba da baccinta. Yadda Nasrin ta ga rana haka ta ga daretana duba agogo tana soshe-soshe sauro da kwari suna cizonta. Da asuba ta dauki ruwa ta fita ta yi alwalla ta zo ta yi ta tashin Malaika ta ki ta tashi. Nasrin ta yi sallah ta daga hannu sama ta na ta addu'a amma Jalo kawai ta ke yiwa addu'a akan Allah Ya bashi lafiya, ya gyaru kamar yadda ya ke ada kuma Ya masanya masa da mace ta gari. Kuka ya hana ta ci gaba da addu'a ta yi kuka har ta godewa Allah. Kukanta ne ya tashi Malaika, ta mike a fusace ta dauki ruwa tana gunguni. 87 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Tana mamakin yadda Nasrin ta ke damun kanta a kan matsalar wani talaka, bayan Allah Ya yi mata ni'iaomi ta dukiya da lafiya. Bayan gari ya waye tangararai Nasrin tr ce da Malaika su zo su dauko ruwa, Malaika ta harare ta, ta ce ba inda zata je. Nasrin ta kwallawa garadan ma'aikata kira, nan da nan suka rugu da gudu, suka duka suna jiran su ji dalilin kiran. Nasrin ta juya ta dubi Malaika ta ce "ko ki tashi mu je ko in sa su saka ki a turu in ceke mahaukaciya ce.' " Malaika ta mike cimak a fusace suka ɗauki jarkoki suka fara tafiya. A hanya suka hadu da masu zamar jinya da yawa, wasu suna tafiya wasu kuma sun ɗauko suna dawowa. Tafiya mai nisan gaske a cikin daji ba gida gaba babu baya. Haushin Nasrin ya cikawa Malaika zuciya ta fara tuhumar kanta akanshishshigi da kwadayinta ne suka ja matashigowa dajin nan sannan Nasrin in ba neman suna a wajen Jalo ba ta sa wadancan ma'aikatan su dauko musu ruwan mana sai sun je da kansu. 88 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Suka isa da kyar bayan sun galabaita, suna isa Nasrin ta zauna ta dafe kirji tana sheshsheka, Malaika ta kudiri niyyar ko zata mutu ko sannu ba zata yi mata ba ita ta jawowa kanta ba wani ba. Da Nasrin ta huta ta karasa ta ciko jarkarta sannan Malaika ma ta je ta debo suka nada gammo amma Nasrin ta kasa ɗorawa akai, gashi gaba daya abokan tafiyar ta su sun dauka sun tafi. Malaika ta yi tsaki ta nuna ta da yatsa ta ce, "bazan ɗora miki ba kuwa saboda ke kika jawo mana wannan jarabar." Nasrin ta fusata ta buge hannu Malaika ta ce "kada ki sake nuna ni da hannu." Malaika ta fusata ta wawuro Nasrin sai ga Nasrin a kasa saboda bata da kwari, tuwon dawa bai ratsa ta ba. Malaika ta zauna a ruwan cikin Nasrin ta danne ta, ta daga hannu zata kai mata naushi, ta tuna wani abu ta fasa dukan ta, amma ta ja mata kunne akan kada ta kara marmarin nuna mata hannu balle ta doke mata hannu. 89 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 a Mamaki da tsoro ya hana Nasrin yin magana, Malaika ta daga ta ta dauki ruwanta akai ta yi tafiyarta ta bar Nasrin anan tsugunne tana kuka. Sai da ta yi kuka ta gaji Allah ya kawo wasu mata zasu ɗauki ruwa, ta roke suka dora mata ruwan akai ta tafi, wuyanta kamar zai ɓalle dakyar ta iso. Ta iske Malaika har ta shiga wanka wato ba ba kenan. dan marar lafiya ta dauko ruwan Nasrin ta isa kofar dakin su Jalo ta yi sallama Mama ta fito, ta sauke mata tana yi mata godiya. Nasrin ta duka ta gaishe ta sannan ta shiga ciki ta durkusa a gaban Jalo ta gaishe shi ya amsa cike da fara'a. Yana dauke da laptop akan cinyarsa yana karatu da alama ya na kan facebook ne. Ta cika da mamaki ashe daman duk posting din nan da yake a cikin kungurumin dajin nan yake yi? Nasrin ta fito ta sake daukar wata jarkar zata dauko wani ruwan, ta ce Mama su yi amfani da wannan. Ma'aikaci daya ya karɓa yace zai dauko mata dan daga gani ba tambaya ansan 90 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 galabaita ba ta sababa. Duk da a ɓoye ya tafi ba'a yarda su bar mararsa lafiya ba. Nasrin tana zaune daga karkashin bishiya tana hango Mama tana faman shiga da fice dauke da katuwar roba tana tsaftace jikin ɗanta, sai ta fara kwaranyar da hawaye tana sake jinjina kaunar Uwa akan ɗanta. Nan da nan taga Ma'aikaci ya dawo da jarka cike da ruwa, ta yi masa kyauta har sai da ya yi mamaki yana ta godiya. Ta sake kai ruwan bakin kofar ɗakin su Jalo, Mama ta fito da fara'a tana godiya. Mama ta diba a bokiti ta je ta yi wanka data fito sannan Nasrin ta je ta yi wankan itama, gaba ɗaya tsikar jikinta ta tashi, borin jini ya fito mata dan bata taɓa wanka a cikin kazanta haka ba. Ta koma gefe tana ta susa tana kuka ba tare da ta bari kowa ya sani ba. Tana ta addu'a har Allah Ya yaye mata. Ta zo ta dauki jakar kayanta ta koma ɗakinsu ta iske Malaika ta yi wanka ta canja kaya tana kwance tana girgiza kafa da alama a fusace take. 91 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Nasrin bata kula ta ba ta shirya tsaf da wata atamfa doguwar riga da dan mayafi ta hada kayanta gaba daya. Sannan ta juya ta harari Malaika ta ce "in kin ga dama ki tashi mu tafi.' " Malaika ta yi zunbur ta mike har da murmushin dadi, su na fitowa suka ga mai maganin yana zagaye daki-ɗaki yana bada magani, Nasrin ta kalle shi sama da kasa ta kamanninsa sak na Bokaye ko riga babu a jikinsa sai fata da gashin kaza a ko ina da a jikinsa, guru da laya a hannu da kafa, daga shi har makarbansa abin tsoro. Tabbas babu alamar musulunci anan, sai tafara tunanin yadda aka yi Jalo ya yarda ya zo nan neman maganai da iliminsa da komai. Ta kudiri niyyar sai ta yiwa jalo magana akan wannan. Nasrinda Malaika suka nufi dakin Jalo suka shiga da sallama, abin mamaki sai ga Malaika tana washe baki ta ji za'a tafi gida, ta gaishe su da fara'a ta jawo kayanta tana hadawa. Nasrin ta mika musu Biredi da butter Mama da Malaika ne suke ci suna korawa da 92 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 lemo da ruwa. Jalo ya na azumi bai ci ba, Nasrin kuma ta ce ta koshi. Gaba daya hankalinta a tashe yake babu abinda take sai kallon Jalo tana ganin idan suka rabu yanzu har abada ba zasu kara haduwa ba. Ya kula da haka sai ya zare farin gilashin da ke fuskarsa ya dube ta ya yi mata lallausan murmushi ya ce, "Nasrin! Na san abinda ya ke damunki. Kada ki damu Ubangijina Yana tare ta ni, Shi ya ɗora min Shi zai yaye min. Ya fi ki sona kuma ko dukka duniya zasu taru akaina bazan ji sauki ba in dai ba Shi Ya so in warke ba." Nasrin ta surnano da hawaye ta ce, “Zamanku anan ne ya fi damuna, kuma yanzu na ga Mai baku magani sai nagan shi da siffar Bokaye.' " Jalo ya gyada kai yana kallonta yace "Nasrin! Magani kawai yake bani sassake ne babu wani abu bayan wannan kuma ga Mama nan ita take kuka idan na ce ba zan zo ba. Kar ki damu Insha Allah ba zan ɓace hanya ba.' Nasrin ta gyada kai sannan ta langwaɓe kai hawaye na zuba, kuma bakinta yana ta " 93 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 rawa da alama tana so ta yi wata magana ta kasa. yana kallonta Nasrin ta zura masa ido tana kallo shima hawaye ke Zuba daga idanuwansu su dukka. Sai suka juya suka kalli Mama wacce tashin hankali ya hanata ci gaba da cin abinci. Mama ta tashi da sauri ta fice tana hawaye ta basu waje, amma kuma ta laɓe a inda zata dinga jiyo abinda zasu ce. Malaika tana zaune tana cin biredi tana kallonsu da alama itama tana jin tausayi duk da bata san ciwon da Jalo yake yi ba, ta ga alama dai baya iya tashi tsaye. Can jimawa Nasrin ta sunkuyar da kai kasa tana tunani, sannan ta sake ɗagowa ta dube shi cikin sanyayyiyar murya ta ce, “Dr. Jalo!in tambaye ka wata alfarma zaka yi min?". Ya dago da sauri ya dube ta cike da mamaki ya yin da kwakwalwarsa ta kasa tuno masa alfarmar da zai iya yi mata yana zaune a cikin kashi da fitsari. S 94 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Nasrin ta dago ta dube shi ta yi magana cikin sanyayyiyar murya ta ce, "Za ka taimake ni ka aure ni?" Sai ya ji gabansa ya fadi, ya zazzare ido ya na kallonta. Ta sake cewa “ina sonka a yadda kake Jalo." Sai ta fashe da kuka shima hawaye ya na zuba daga idanuwansa. Ya girgiza kai yace, "Nasrin! Ina tunanin har yanzu baki gane halin da nake ciki ba, ai babu maganar aure a tare da wanda lakarsa ✓ bata aiki.' " Ya ɗaga mata ledar fitsari da take jikinsa, wato katata. Ta yi sauri ta sunkuyar da kai kasa ta fashe da kuka. Yayin da Malaika ta kura ido tana kallonsa sai yanzu ta gane abinda yake faruwa. Nasrin tarusa kuka ta faɗa cikin ɗaga murya "ina sonka a haka, na yarda zan zauna da kai a haka. Jalo ban san soyayya ba sai da na hadu da kai tun ma ban taɓa ganinka ba. Haka kuma da ka kula ni na ji farin cikin da 95 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 ban taɓa ji ba. Da na same ka da larura babu abinda ya canja, ina sonka" har yanzu.' Ya girgiza kai yana kuka ya ce, "Nasrin! Na gode. Ba zan taɓa mantawa da ke ba a rayuwata ba. Ke ce mace ta farko da kika taɓa sona na tsakani da Allah ba dan kyawuna ba, ba dan kudina ba, ba dan martabata ba. Na fi bola abin tsantsani amma duk da haka kika ji kina kaunata.' " Kuka ya ci karfinsa yayin da Nasrin ma kukan take. Mahaifiyar Jalo tana laɓe a bakin kofa tana rusa kuka dan duk tana jin abinda suke cewa. Mamaki ya hana Malaika rufe baki jira take ta ji Jalo ya amince ta tashi ta rike Nasrin ta ce baza'ayi wannan taɓargazar a gabnta ba. Sai Allah Ya sa bai amince ba sai ta ji dadi, amma tà fara tuhumar Nasrin da ciwon taɓin hankali tunda take son mai larura kuma talaka duk da kyau da dukiya da Allah ya yi mata. Nasrin ta sharce hawaye ta ce, "tun da nake a rayuwata ban taɓa ganin mutumin da ya taɓa birge ni irinka ba, a koda yaushe ina cewa 96 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 'DAMA NI CE Jalo, da ma in zama kamar ka, Da ma in kasance tare da kai.. . .” Ya yi sauri ya katse ta yala magana cikin kuka ya ce, “ni nake sha'awar DA MA NI ne Nasrin, dama in zama ke, Dama ni ne nake da lafiya kamar ki. Kada ki yi fatan ki zama ni. " Nasrin ta ce, "Allah Ya na sonka kuma Allah zai baka ladan tawakkali. Ka yarda in kasance tare da kai Jalo, na yarda na hakura da komai na jin dadin rayuwa." kuka. Mahaifiyarsa ce ta shigo da sauri tana Ta rungume Nasrin ta ce, "Nasrin ina kika shiga tuntuni, baki hadu da Jalo ba? Da ace mun san ki ada da bai auri Rayyana ba. 'DA MA ke ce' uwar 'ya'yansa mun san zaki zauna da muda amana, nasan za ki zauna da mu a cikin kowanne irin hali muke ciki. Mun gode da kauna, amma Allah bai ga damar ku zauna tare ba tunda kun hadu a kurarren lokaci a sanda Jalo ya zama hoto." " Su dukka ukun kuka suke yi. 97 Jamilu Umar Tanko JUT CAMA NI CE...2 SER Nasrin ta kara kankame Mama ta ce, "Kada ku hana ni zama da zaɓin rayuwata, ui na zabe shi a haka zan zauna da shi har lokacia mutuwata."" Mama ta girgiza kai ta ce, “mu ma bamu ki ki ba amma shi kansa Jalo ba zai yardaba, haka nima ba zan yarda ba balle iyayenki. Haba Nasrin kada ki makance alhali kina da idanuwa, kada ki zama kurma alhali kina ji da kunnuwanki, kada ki haukace da gangan alhali kina da hankali. Ba kya ganin halin rashin lafiya da yake ciki?Ba ya bukatar mace yanzu ma da a rayuwarsa. Mun godewa Allah Yabashi dama ya yi aure aure ya haifi biyu kafin ya zama haka. Ni ce ya zame min dole ni uwara, na kashe aurena dan in zo in zauna da shi. Ina addı:'a Allah kada Ya dauki raina da wuri dan in zauna da dana in ci gaba da kula da shi. Ina addu'a kada Allah Ya dora min ciwon da zan kasa kula da Jalo." Jalo ya rike kai ya yi kuka ya gaji, ya dago ya dube su ya ce, "Allah kada ka fara kashe Mamana kafin ka dauki raina." 98 Jamilu Umar Tanko JUT DAMA NI CE...2 Mamaki ya hana Malaika rufe baki da alama itama ɓurbushin tausayinsu ya rufto mata. 5 Ta tashi tsaye ta fita da akwatinta ta dauko jakar Nasrin ta fito da ita sannan ta fita ta tare Masu acaɓa biyu dan suna ta shigowa da mararsa lafiya. Ta yi ta kwallawa Nasrin kira ta zo su tafi, amma Nasrin batagama yin sallam? batana tare da su Jalo. ya h Nasrin ta durkusa a gaban Jalo takudi. bata account number sa zata turo masaidi yana Ya girgiza kai yace baya bukat yiwa 'yan siyasa rubutu suna nsa yadda ya kamata. Addu'arta kawai ke bukata shima yana nan yana yi matatan alkhairi ta sami miji na gari. Nasrin ta shaida masa gara ta koma Amerika wan mahaifanta

Chapter 4 of 6