ta zauna acan ba
zata sake dawowa Najeriya ba kuma zata ci
ko Allah Zai sa
ta sami asibitin da suka kware akan ɓangaren
ciwon.
gaba da bincike akan ciwonsaima zata ci
Ya yi mata godiya sosai, Malaika ta zo ta
ja hannunta suka fito, Mama tana biye da su
99 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
tana kuka tana godiya, ya yin da Jalo ya kece
da kuka ya dafe kai ya ji son Nasrin tamkar ya
fasa masa kahon zuciya, amma babu yadda zai
yi ne.
Nasrin ta kwaso kudin Jakarta kakaf ta
bawa Maman Jalo kadan ta rage na motarsu, ta
ce Mama ta yi mata kokarin neman lambar
Account ta turo mata zata taimaka musu da
kuG. Ma'aikata suka rugo da gudu suna yi
mata allama,nan ma ta tuna da wasu kuɗaden
a wani diihun Jakarta ta kwaso ta yi musu
rabon dubu-dubu, sai murna ta kama su.
Nasrin da suka hau acaɓa suka tafiyayin da kuka ya tokare Nasrin, dadi ya
ruftowa Malaika ta shaki iska mai sanyi.
A cikin motarsu dagadda zuwa Abuja ne Nasrin ta bude wayarta ta hau facebook
anan ta ga rubutun Jalo. Tabbas ya yi rubutu
karara akanta suna ne kawai bai ambata ba.
Amma ya suffanta ta da mace ta gari
kuma duk wanda ya aure ta ya yi dace a
duniyarsa da lahira. Daga karshe ya yi mata
addu'a Allah Ya bata dukka alkhairan da suke
cikin rayuwarta ta duniya da lahira.
.
100 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
Nasrin ta tsinci Kanta tana mai
murmushi mai hade da hawaye, Malaika tana
gefe tana harararta dan ita haushi take bataba
tausayi ba.
Kafin su shiga Abuja Nasrin ta yiwa
Zainab waya ta shaida mata sun kusa shigo Abuja ta aiko direba ya zo ya ɗauke ta a tasha.
Dan haka suna sauka suka hango Direba yana jiransu, ya zo da sauri ya ɗauki jakunkunansu ya saka a but suka shiga mota suka nufi gida.
:
Nasrin ta kula Malaika tana ta fara'a tana yi mata hira dan a shinya, amma Nasrin ta gama harka da ita har abada, tasan itama zata guje ta idan Allahya dora mata larura ta rashin
lafiya ko ta talauci. Dan haka Malaika ba abokiyar zama ba é
DAMA NI CE...2
BABI NA GOMA SHA BIYU
ed climb shansind an olay
ABUJA... ediyszust
shunda ght be any
Suka isa gida, Zainab ta tare su da
fara'a tana yi musu tsiya tana
kiransu da aminan juna, ayi faɗa a
sy hose ab as sy transtil
Nasrin ta sha kunu bayan sun gaisa tay
wuce cikin dakinta ta yi wanka ta canja kaya ta
shirya.
fito ta nemi shaya
ta iske Malaik
sha saboda yunwa take ji,
ta yi zubin abinci da karig
uku, sai turawa kawai take yi tana ci tanag
murmushi tana zare ido.
Zainab tata shaidawa Nasrin cewars
Dr.Hala ta dawo daga Amerika shekaranjiya,
Iyayensu sun bada sako ta kawo musu dan
haka ta je ta karɓo musu.
Nasrin ta ce gobe zata je ta karbo musu,
Insha Allah.
Zainab ta sami waje ta zauna a kusa da
Nasrin Wacce take lasar romon farfesu ba tare
102| Jamilu Umar Tanko JUT ufust | For
K
DAMA NI CE...2
da ta iya cin naman kazar ba. Zainab ta shiga
jero mata tambayoyi akan in da suka je?
Nasrin ta yi shiru ta ki yin magana sai
can jimawa sanda ta ga damar bata labari
sannan ta fara bata labarin Jalo, hawaye na
zuba daga idanuwansu su dukka, daman
Zainab uwar tausayi har tafi Nasrin tausayi.
Suka sha kuka,Malaika tanazaune a gefe
tana kallonsu ta na mamakin yadda masu kudi
suke zubar da hawayensu a banza akan talaka.
Da Nasrin ta gama abinda take yi a falo
cewa Zainab ta nunawa Malaika
boskwata(Boy's Quarter) dan batason damu,
ta
ba zata kara zama daki daya da Malaika ba.
Nasrin ta shiga daki ta kulle kanta tabbas
ba zata fito ba sai gobe. Bayan ta idar da sallar
isha'i ta jawo wayarta ta ga kiran Jalo har sau
uku nan da nan ta bi baya ta kira shi. Bayan
sun gaisa ta bashi hakuri akan bata kusa da
wayar ne a sanda ya kira. Ya tambaye ta
gajiyar hanya sannan suka yi sallama suka
kashe waya.
Ta hau facebook akan computer ta, ta
sami lokaci a nutse ta karanta sannan itama ta
103 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
suffanta shi da Miji na gari mai sanin y
kamata ta tura masa.
Ta kira Dina ta bata labarin abinda ya
faru a Jalo da yadda suka iske shi. Sai hankalin
Dina ya tashi matuka ta dauki dogon salati da
kururuwa. Nasrin ta kasha wayar da sauri tana
zubar da hawaye. Ta kwanta ta yi shiru tana
tunani, bata san sanda bacci ya dauke ta ba
saboda gajiya. Bata farka ba sai da asuba bayan
ta idar da sallah ta koma bacci sai karfe goma
sha biyu ta tashi ta yi wanka ta shirya ta fito,
dauke da mukullin mota zata je gidan Dr.Hala,
ta yiwa Zainab sallama ta fice.
Sai ga Malaika ta zaro gyale da gudu ta
biyo bayan Nasrin tana yi mata magana, Nasrin
bata kula ta ba ta shige mota ta kunna sai g
Malaika ta daka tsalle ta shige gidan gaba.
Ta dubi Nasrin ta yi murmushi ta ce,
"Kawata wai har yanzu fushin kike yi min?
Dan Allah ki yi hakuri."
"
Nasrin ta dube ta da gefen ido ta kawar
da kai gefe ta ci gaba da tukinta, daMalaika ta
ishe ta da magana sai ta kure rediyon motar da
karatun kur'ani. Basu tsaya a ko inaba sai a
104 Jamilu Umar Tanko JUT
ya
DAMA NI CE...2
Asokoro kusa da gidan shugaban kasa, gidan Dr.Hala kenan.
Nan fa Malaika ta bude baki tana kallo
fuskarta cike da farin ciki.Suka wuce kai tsaye
cikin katafaren get din gidan amma ba'a bude
masu har sai da aka kira Dr.Hala a waya, ta ji
muryar Nasrin sannan ta yarda a bude musu su
shigo.
Malaika dai bata daina yi da bakinta ba.
Tana faman santi tana kiran "Allahu akbar!
Allahumma arzukuni. Wayyo arziki.'
"
Haushi ya rufe Nasrin ko kallonta ba ta
yi ba ta fito ta shiga gidan, Malaika tana biye
da ita da sauri har suka isa katafaren falo mai
kama da aljannar duniya. Nan fa Malaika ta yi
ta taɓe-taɓe abubuwan da bata taɓa gani ba.
Aka turo 'yar aiki aka ce su shigo daki.
Suka wuce zuwa wani katafaren daki
wanda girmansa ya kusa kaiwa gidan malaika
gaba daya.
Setin gado ne da kujeru a gefe ga kayan
kallo ga sanyin Ac da kamshi ko ta ina.
Sai yanzu Malaika ta gane wacce suka zo
gidanta. Ashe wannan hadadiyar matar nan ce
105 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
likita da suka hadu a Kano. Tabbas mafarkin
ya fara zama gaske gata, ga hadaddiy
dattijuwa. Ta kudiri niyyar ba zata fita daga
gidan nan ba sai ta yi mata kwanaki biyu
sannan ta nemo mata aikin yi koda na kula da
gyaran daki ne.
Su ka zazzauna akan luntsumaluntsuman kujeru suka duka suka gaishe ta Ita
dai Dr.Hala bata ma gane Malaika ba sai da ta
ishe ta da surutu da kwatance sannan ta shaida
ta. Haushin Malaika ya na ta nukurkusar
Nasrin, sannan ta gyara zama ta fara tambayar
Dakta lafiyar iyayenta.Dr.Hala ta fayyacewa
Nasrin farin cikinta yadda Mamarta ta karɓe
ta.Nasrin ta ji dadi da ta ji haka suka ci gaba da
hira.
'Yan hidimar gida suna%.
ta sintiri suna
jere musu kayan marmari na ci dana sha a
gabansu.
Dr. Hala ta duba agogo ta zare gilashin
dake fuskarta ta ce, “bari in yi alwalla. Ku sha
lemo barizan yi sallah.'
"
Tamike a nutse ta tura kofar katafaren
badaki sai kamshi ne yake busowa, Malaika ta
106 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
kama baki tana kallon aljanar duniya, daga nan
ta sake gasgatawa kudi ya yi a rayuwa dan haka ko ta hali kaka sai ta nemo shi.
Ta damu Nasrin da surutu amma ba ta
tanka mataba, lemo ta zuba kaɗan a kofi ta sha
ta ci gaba da karatun jarida, yayin da Malaika
ta yi goho ta dinga aika kayan dadi zuwa ga
birnini tunbinta, Nasrin tana harararta da gefen
ido amma bata yi mamaki ba kauyanci da
jahilci ne babban ciwon da yake damun
Malaika.
Dr.Hala na fitowa daga bandaki Nasrin
ta shiga don yin alwalla itama. Malaika ta
gyara zama tana murna ta sami damar yiwa
Dakta Magana son ranta.
Malaika ta kalle ta, ta yi mata murmushi
ta ce, "sannu ranki ya dade. Ki godewa Allah
dan Allah Ya yi miki komai a duniya, DAMA
NI CE ke."
Dr.Hala ta dube ta ta yi murmushi ta
ce,"Hmmm! Malaika! Ni kuwa tun dazu nake
kallonku ina cewa a raina DAMA NI CE ku,
kar ki yi fatan ki zama ni. Ki tambaye ni me
yaşa nace haka?"
107 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
Malaika ta gyara zama ta na murmushi
kai ka ce anyi mata albisuir da gidan aljanna
saboda tana magana kai tsaye da mai kudi.
Malaika ta ce, "Me yasa kika ce haka?
Dube ni fa talaka, ba ni da ko sisi ciki da waje,
ba ni da gida ko fili balle Motar hawa, ba ni da
kayan sakawa sai tsummokare. Allah Yaba ni
miji talaka, ga yara sun taso a cikin talauci,
iyayena a kauye talakawa ba su da komai....""
Dr.Hala ta yi dariya ta girgiza kai ta ce,
"Allah sarki, 'DAMA NI CE'ke. ... Amma
bari in nuna miki wani abu da za ki tabbatar da
abinda nake nufi. kin gani."
"
Malaika ta juya da sauri ta kurawa Dakta
ido tana kallon abinda ta nuna mata, sai
idanuwanta suka hango mataabinda ya gigita
ta, Malaika ta kwalla ihu ta tafi a guje ta nufi
kofar bandaki wajen Nasrin, suka ci karo da
Nasrin tana fitowa.
Malaika ta rirrike Nasrin jikinta yana
rawa ya yin da hawaye yake zuba daga
idanuwanta.
Muryarta na karkarwa ta ce, "Nasrin! Zo
mu bar gidan nan yau idanuwana sun hango
108 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NICE 2
abinda ban taɓa gani ba. Ashe haka masu kuɗin suke? Gara in koma kauye wallahi bazan
zauna a gidan nan ba. Ke dai ki zo mu tafi zan
fada miki abinda na gani.'
"
Nasrin ma ta gigice ta rirrike Malaika
tana tambaya ta ce, "meya faru? Me kika gani?
Fada min mana."
"
Malaika tana hawaye tana nuna Dr.Hala
hannunta na karkarwa ya yin da Nasrin ta dubi
Dr.Hala ba ta ga komai ba, Dakta dai tana
sallah amma a zaune akan kujera.
Nasrin ta juya ta dubi Malaika, taga har
yanzu jikinta rawa yake kuma ta na ja da baya
ta ki sakin jiki. Daga nan Malaika ta buɗe ɗaki
ta fice da gudu ya yin da Nasrin ta bi ta da
gudu tana so ta damko ta amma ina Malaika ta
wuce falo uku sannan ta keťa kicin, ta gangara
farfajiyar gidan, ta na dankara gudu gami da
ihu ta na neman agaji.
Nasrin tana biye da ita da gudu itama
tana neman agaji tana cewa "a tare-a tare"
Nan da nan ma'aikatan gidan da masu
gadi suka kawowa Nasrin dauki, aka dinga
tsere da Malaika tuni ta yi tsalle ta kama get
109 | Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
tana neman hanyar dira, saboda ta ga halaka.
Haka aka damko ta aka sauko da ita, nan take
ihun da take yi ya karu kai kace ido ake
kwakwale mata.
3
Nasrin ta rasa abinda yake yi mata dadi
Malaika ta kunyata kwarai, koma dai me ta
gani bai kamata ta tayarwa da kowa hankali
haka ba. Tabbas Malaika ta zame mata annoba
a rayuwarta, hawayen takaici ne kawai ya ke
kwaranya daga idanuwan Nasrin. Tana ta
addu'a a zuci Allah ya rabata da Malaika dan
ta zame mata barazana a rayuwarta.
Dakayar aka samu Malaika ta nutsu ta
daina ihu, Nasrin ta kama hannunta suka shiga
cikir falo amma fa Malaika ta ki yarda ta koma
cikin dakin likita saboda tsoro. Nasrin ta shiga
dakin Dr.Hala a sanyaye ta iske ta har yanzu
tana salla a zaune akan kujera. Ta shinfida abin
sallah ta tayar da ikama. Bayan sun idar sun
dade suna ta kwararo addu'oi kowacce
tsakaninta da ubangijita take karanto abinda da
ya dame tana neman agaji a wajen Rabbil
samawati.Bayan sun shafa sai suka kalli juna +
110 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
suka yi murmushi a lokaci guda sannan suka gaisa.
Nasrin ta ce, "Mummy Hala kina jina da
kawata ta firgita ta fita da gudu ko? Me yake
faruwa ne?"
Dr.Hala ta kyalkyale da dariya ta ce,
"ina Malaikar take?"
Nasrin ta nuna da yatsa ta ce,"tana falo ai
ba zata shigo ba."
Dr.Hala ta ce, “mu je falon in bata
labarin rayuwata ko zata daina sha'awata.'
"
Suka fito falo suka iske Malaika ta yi
tagumi, tana ganin Dr.Hala sai ta zabura ta
gyara zama ta sake takurewa.
Bayan sun zazzauna akan kujera
kowaccensu tana kallon Malaika tana dariya,
sai Malaika ta zaci sun shiryo wani abu ne da
za'a cutar da ita ta fára tunanin ma ko a gidan
yankan kai take.
".
Dr.Hala ta dubi Malaika ta kira sunanta
cikin marainiyar murya ta ce, "Malaika! Na fi
sha'awar rayuwarki akan rayuwata shiyasa na
ce kada ki yi fatan ki zama ni. Ga kudi ina da
shi, ga kyau ina da shi amma bana jin daɗin
111 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
rayuwata. Da za'a kwace komai a bani lafiya
kamar ki da na ji dadi, da za'a kwace dukiyata
a bani haihuwa kamar ki da na ji dadi, da za'a
Kwace dukiyata dukka a ba ni miji kamar ki da
na ji dadi."
Sai Nasrin da Malaika suka hada ido
suka juyo gaba daya suka kalli Dr.Hala a
lokaci guda, cike da dimuwa.
Hala ta surnano da hawaye ta sunkuyar
da kai kasa ba tare da ta kara cewa komai ba.
Hankalin Nasrin ya tashi.
Ta gyarazama ta fada cikin harshen
Turanci ta ce,"Mummy ki bamu tarihin
rayuwarki saboda ya zama darasi a rayuwarmu,
musamman Malaika da take ganin kamar kudi
ya fi komai muhimmanci a rayuwa.
LABARIN DAKTA HALA
Ta ce,"sunana Hafsat ana kirana da Hala
kasancewar Mahaifiyata balarabiya ce yar
asalin kasar Turkey, Mahaifina bafillatanin
Adamawa ne.
Ya je karatu can suka hadu suka yi aure
aka haife ni, a wajen haihuwata ta rasu ta barni
112 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
a hannun Mahaifiyarta dan haka a hannun Kakata na girma."
Nasrin ta gyara zama ta langwaɓe kai
cike da tausayi. Ya yin da Malaika ta fara jiyo
harkar Jajayen fata a ta san tabbas Babanta mai
kudi ne.
Dr.Hala ta ci gaba da cewa "Mahaifina
ya dawo kasarsu Najeriya ya yi aure-aurensa
amma ya kan zo ya ganni jifa-jifa nima na kan
ZO.
Na tashi a kasar Turkiya a in da na yi
karatuna gaba day daya, na tashi a cikin rashin
kwaɓa babu tarbiyya, na hadu da saurayin da nake matukar so mai suna Jaddi tare muka yi
karatu a jami'a babu abinda muke yi sai
watsewa, na sha yin ciki ina zubarwa ashe
kwayayen haihuwar gaba daya aaawa na zubar. Na ashe
zama cikakkiyar likita amma babu aure na zaci
Jaddi yana so na ne da gaske kuma zai aure ni
amma ya ki aurena, kullum yana yi min karyar zai aure ni amma daga karshe na ji labarin ya
auri wata a ɓoye. Hakan ya sa na hargitsa na je
na cinnawa gidansa wuta ya kone shi da
amaryar amma ba su mutu.
"
113 | Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
Nasrin da Malaika suka zazzare ido gami
da dafe kirji.
Nasrin ta tambaya "Me yasa kika aikata
wannan danyen aiki?"
Dr.Hala ta yi murmushin takaici ta ce,
"sharrin zuciya, dan haka aka ɗaure ni na
tsawon shekaru dakyar aka samu aka fito da ni
bayan na shekara biyar cur a gidan yari. Dan
daurin shekaru sha biyar aka yanka min da aka
sami canjin Gwamnati na sami alfarma.
Na dawo 'yar shaye-shaye saboda bakin
cikin rayuwa kullum a buge nake hakan ya sa
kowa ya tsane ni, Kakata kadai ke kaunata ko
da yaushe tana yawo a gidan rawa (club) tana
kamo ri dan acan nake kwana a buge.
Watarana nasha na bugu ina tukin mota
na yi mummunan hatsari a take kafata ta hagu
ta tsinke a take ta fita daga jikina. Yanzu haka
bani da kafa sai ta karfe da ita nake amfani."
Ta bude musu kafar ta sa hannu ta
kwance kafar sai ga kafar karfe a hannunta.
Malaika ta daka tsalle ta fado kan Nasrin
ta kankame ta tana salati..
cinud teed
114 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
Hankalin Nasrin ya tashi ta fara
karanto"Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un.
Allah Ka sa mu gama da duniya lafiya. Allah
Ya sa mu yi kyakykyawan karshe.'
"
Dr.Hala ta ɓarke da kuka yayin da
Nasrin da Malaika ma suka rungume juna suna
kuka. Har na wani lokaci.
Malaika ta koma kan kujerarta ta zauna
ta yi tagumi tana kallon kafar karfen da
Dr.Hala ta wurgar a kasa tana ta godewa Allah
a zuciyarta da Allah Ya barta da kafafuwanta
da hannayenta ba'a gutsiri komai daga jikinta kan
ba.
Dr.Hala ta ci gaba da cewa "a sanadiyyar
wannan bakin cikin ya sa Kakata ta hadiyi
zuciyata ta rasu, na zamanto sai ni kadai a
gidan daman 'ya'yanta da jikokinta sun tsane
ni sai tsanar ta karu suna kirana da wacce ta
kasha musu uwa.
Hakan ta sa suka kore ni na haɗo na
dawo Najeriya garin Babana Babana Adamawa,
Alhamdulillahi! Yana nan a raye tare da
iyalansa matansa uku da yara ashirin da hudu.
115 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
komawa jami'a na zama
Ya yi murna da ganina anan na sake
tabbar likita
(consultant) na fara aiki a asibiti. Na yiwa
kaina faɗa na daina shan komai sannan na
koma ga Ubangijina gaba daya na koma
bautarsa ina tuba akan Ya yafe min kurakuren
dana tafka a baya. Allah mai jikan bayinSa Ya
sa na sami nutsuwa sannan ya hore min arziki
da hanyoyin daukaka da samun kudi. Na yi
tashe a garinmu a babban asibiti saboda na san
abinda nake yi, na san makamar aiki har na
bude asibiti nawana kaina. Daga baya na shiga
harkar siyasa na san manyan gwamnati har na
dawo Abuja da zama na kuma sami sukunin
tafiya Amerika na karo karatu har Allah ya
kawo ni wannan matsayi ina kusa da shugaban
kasa."
2
Akt Akbar Nasrin ! Yaya batun ta langwaɓe aure kuma kai da ta haihuwa ce, "Allahu ?"
Dr.Hala ta girgioza kai ta ce, "Allah bai
sa ina da miji a duniya ba, babu irin kokarin da
banyi ba, haka mahaifina da abokan aikina duk
mai kaunata sai ya yi kokarin hada ni da wani
mu yi aure amma sai Magana ta fara nisa sai su
116 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
fasa. An ce bakin aljani ne, an ce asiri ne
amma ni na yarda da cewa daga Allah ne.
Yanzu ina da shekaru hamsin da hudu ban taɓa
aure ba har na fitar da rai, bana bukatar in yi
auren ma. Na riga na nakasa duk sanda aka
hango kafar karfe sai su gudu ina zargin
wannan ma yana cikin matsalata.'
"
Nasrin ta dora hannu aka zata fasa ihu ta
daure ta sauke hannun, hawaye na zuba daga
idanuwanta.
Dr.Hala ta matse hawaye ta ce "Malaika!
Tun ranar da na fara ganinki na ke fada a raina
DA MA NI CE ke kina da yaranki a gidan
mijinki. Ni na rasa wannan kuma ya wuce ni
har abada, bazan taɓa yin aure ba balle ir
haihu. Ba zan taɓa dawowa daidai ba kamar ki
tunda na rasa kafata na zama gurguwa.
Ba ni da masu gadon uwar dukiyar da na
tara saboda Mahaifina ya tsufa lokaci kawai
yake jira babu abinda zai yi da dukiyata sai dai
yaransa su gada wadanda ba kaunata suke yi
ba ko kadan. Ni kadai mahaifiyata ta haifa ta
tafi ta bar ni. Amma ina tallafawa marayu da
gajiyayyu kuma ina rike su har in aurar."
117 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
Kuka ya ci karfin Dr.Hala har ta kasa ci
gaba da magana. Nasrin ta zabura ta je ta dauko kafar ta
mikawa Dr.Hala ta ce, “ki mayar da kafarki
kada ki damu lilkita na ki mai sauki ne idan
kika ji labarin Dr. Jalo.
Da Dr.Jalo zai ganki da sai yace'DA MA
shine ke, saboda shi baya tafiya, baya iya
tsayar da fitsari da bayan gida, ya rasa Lakarsa
wanda bana tunanin akwai maganin da za'ayi
masa ta dawo dai dai har abada."
"
Dr.Hala ta tsagaita da kukan ta kuarawa
Nasrin ido sanan ta tambaya "waye Dr.Jalo?
Nasrin ta ce, "wani abokina ne da muka
hadu a facebook kuma Allah Ya jarrabe ni da
matukar kaunarsa sai bayan da muka ga juna
sannan na tabbatar da yadda yake. Likita me ya
kamata ya yi ya sami sauki ko kuma ina ya
kamata ya je ayi masa aiki ya warke? Ina son
Jalo zan iya salwantar da duk abinda na
mallaka da wanda iyayena suka mallaka dan in
ceto rayuwarsa.
وو
Malaika ta zabura ta kalli Nasrin cike da
mamaki ta sake gasgata cewar lafiya ta fi
118 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
komai muhimmanci a duniya ba kuɗi ba. Ta.
sake yarda babu abinda ya fi soyayyar gaskiya
dadi a duniya hakika Nasrin tana kaunar Jalo
sona hakika, ba dan kudinsa ba, ba dan
kyawunsa ba.
Dr.Hala ce ta katse tunanin da Malaika
ke yi ta ce, “maganar gaskiya idan Laka ta taɓu
sai dai dibaru,shawarar da za ki bashi ita ce
kice masa idan ya sami kamar awa guda ya yi
kokari ya mike tsaye yana dogara sanduna
yana jan kafafuwan tunda kin ce hannayensa
suna amfani. Ya kokarta ya shiga bandaki ya
sa hannu ya matsa cikinsa da karfi da mararasa
ya turo bayan gida da fitsari su fito sai ya koma
bayan kamar awa gida ya sake komawa ya yi
haka zai yi ta yi. Za ki ga ya daina amfani da
katata kuma zai daina zubowa ba tare da ya
shirya ba.
"
Nasrin tana sauraronta tana gyada kai da
alama ta fara jin farin ciki a kalla dai zai rage
wani abu na alamar samun sauki.
Ma'aikata suna ta safa da marwa suna
jere musu abinciccika kala-kala akan tebur
119 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NICE...2
amma tashin hankali ya hana gaba dayansu ci.
A haka suka yi sallama suka tai.
Dr.Hala ta bawa Nasrin sakon daloli da
iyayenta suka aiko mata da kayan jarirai na
Zainab, ta bawa Malaika atamfa super Holland
kyauta.
Su na godiya suka tafi suna tafe a mota
kowaccensu ta yi jugum babu wacce ta ke iya
magana. Haka suka shiga gidan Zainab sokoko
babu laka a jikinsu, kallo daya Zainab ta yi
musu ta tabbatar suna cikin damuwa amma ta
yi zaton fadan suka tafka a hanya.
Bayan Nasrin ta zazage sakon a gaban
Zainab sai farin ciki ya kama Zainab. Ta
tambaya lafiya ta gansu basa walwala. Nasrin
ta bata labarin Dr.Hala gaba daya, sai Zainab ta
gigice ta daga hannu sama ta na yiwa Allah
godiya da Yaba su rai da lafiya da abinda
lafiyar zata ci.
Gaba dayansu suka yi tagumi ba tare da
wani ya iya ci gaba da magana ba har zuwa
lokaci mai tsayi.
Malaika ta fasa kuka ta ce, “na ko yi
darussa, na lura da cewa damuwar masu kudi
120 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
har ta fi ta mu ta talakawa. Wallahi a zatona
masu kudi ba su da matsalą ko kadan sai na
iske ko da yaushe idanuwansu suna zubar da
hawaye har ma suna sha'awar da DA MA su
ne mu, tabbas lafiya itace komai. Zan koma
gida in zauna in yi hakuri da yadda Allah ya
ajiye ni.'
Nasrin ta matse hawaye ta ce, “nima zan
bar kasar nan jibi in koma gaban iyayena in
zauna bazan iya jira har sai na gama bautar
kasar ba. Na rasa farin cikin rayuwata Dr.Jalo,
na ji gaba daya rayuwata a Najeriya bana jin
dadi. Zan koma in da Allah ya ajiye ni in ci
gaba da addu'a Allah ya hada ni da farin cikin
rayuwa amma kudi ba komai ba ne idan babu
farin ciki babu lafiya."
Su ka yi tagumi ba tare da sun iya magna
ba. Can Nasrin ta mike ta dauki mukullin mota
ta shiga daki ta dauko passport dinta da Jakarta
ta fito da alama wajen sayen tikiti zata tafi ta
fice da sauri.
Malaika ta tashi ta tafi tana haɗa kayanta
a cikin akawati da alama ta yiwa kanta fada ta
ga bala'in da ya fi nata.
121 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
***
Washe gari da safe misalin karfe takwas
na safe Malaika ta tashi ta shirya ta fito da
akwatinta ta bubbugawa Nasrin kofa,
kasancewar Nasrin din ma ba bacci take yi ba
tana ta waya da Jalo tunda asubah. Ta shaida
masa shawarwarin da Dr.Hala ta bayar, kuma
ya yi Amanna.
Daga karshe ta yi masa sallama a kan
washegari zata bar kasar nan ba zata dawo ba,
amma ta yi masa alkawarin yin bincike a game da masu irin larurarsa in har an sami mafita
zata ciko a kai shi zata dauki nauyin yi masa
aikin.
Ya yi mata godiya sosai gami da yi mata
fatan alkhairi. Ya nuna matukar damuwarsa da
ya rasa ta amma ta ce kada ya damu akwai
waya akwai facebook ko da yaushe zasu din ga
haduwa.
Bugun kofar da Malaika ke yi ta sa ta
katse wayar ta je ta bude sai ga Malaika a tsaye
122 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
a bakin kofa da akwatinta da alama ta shirya
tafiya gida.
Nasrin ta yi mata iso ta shigo ta zauna a
sanyaye, bayan sun gaisa sai Malaika ta fara
magana cikin marainiyar murya.
Ta ce "Nasrin! Na gode da kulawarki.
Na gode da jahadin da kika yi akaina har sai da
kika ga na fahimci rayuwa. Ina miki fatan ki
gama da duniya lafiya ki sami rabauta da
aljanna. Na gode da dukka hidimomi da kika
dade kina yi min. Na gode da jajircewa da kika
yi akan kokarin gyara aurena da Shamaki.
Lallai na zalunci kaina, shamaki bai cuce ni ba
ni na cuce shi. Idanna fada miki cin mutuncin
da na yi masa kafin ya rubuta min takardar saki
hakika bana jin har abada zai iya yafe min ya
dawo ya ci gaba da zama da ni."
Malaika ta rushe da kuka yayin da
Nasrin ma hawaye yana surnanowa daga
idanuwanta ta kurawa Malaika ido ba tare da ta
san abinda zata fada mataba. Sai girgiza kai ta
ke tamkar kadangaruwa.
Malaika ta ci gaba da cewa, “abinda ya fi
tayar min da hankali ma shine yadda iyayena
123 Jamilu Umàr Tanko JUT
DAMA NI CE...2
suka tsine min, auren Uwata da Ubana ya rabu
a dalilin na zaɓi in taho Abuja akan na ki yin
biyayya a maganarsu naki yin zaman aure. Na
shiga a uku na lalace, ta inazan fara harhado
rugurgujajjiyar rayuwata alhali ta rugurguje?"
Nasrin ta taso da sauri ta dafa kafadar
Malaika tana lallashi ta ce, “tabbas kin tafka
kuskure amma ba ki makara ba tunda iyayenk:
suna raye kuma Shamaki yana raye na san ba
yi aure ba kuma har yanzu na san yana sonki,
zai yi hakuri da ke saboda yaranki da kuma
kaunar da yake yi miki.'
99
Malaika ta goge hawaye ta