An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
Adon Dawa Publishers
JAMILA
UMAR
TANKO
DA MA NI CE
DAMA NI CE...2
HAKKIN MALLAKA(M): JUT
COPYRIGHT(C):JUT
SHEKARAR BUGAWA:
2015
NA'URA MAI KWAKWALWA:
JUT
Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
BABI NA TARA
BAYAN KWANAKI UKU
RANAR ASABAR.....ABUJA
Wayar Fu'ad ce ta tashi Nasrin
da sassafe cikin magagin
bacci take amsa masa kuma
alamar tana fushi da shi, dan yau wata guda cur
baikira ta ba,saboda yana fushi da ita. Ta in da
yake shiga ba ta nan yake fita ba. Nan da nan ta
ji baccin da take ji ya gudu, idanuwanta sun
wartsake gaba ɗaya, ta bude baki kawai tana
mamaki. Ta saki kunne tana zukar bakaken
maganganun da yake jero mata daga gani
damanya shirya su dan fita suke kawai babu
gargada ko kame-kame.Kuma da alama bai yi
shawara da kowa ba kafin ya kira ta ya faɗa
mata irin wadannan munanan maganganu dan
da ace ya yi shawara da koda shugaban
gaɓayen shekarada zai fada masa bai dace ba
koya ragwanta mata.
3 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
Yana fada yana ta nanatawa auren nan
ba dole ba ne dan taga yana sonta ne shiyasa
take ja masa aji, in dai mata ne gasu nan farare
da bakake suna binsa, dan haka ta je ta yi
tunani ta kira ta fada masa idan bata yi shi ma
baya yi.
Da yagama ya yi tsaki ya kashe waya,
batare da ta iya ce masa komai ba.
Malaika ce ta zuro da kanta daidai
fuskarta ta ce "Nasrin!da wa kike waya?
Dr.Jalo ne?"
Haushi ya rufe Nasrin ta yi tsaki ta juya
mata keya ta ci gaba da tsiyayar da hawayen
takaici, ta rasa wanda zata fadawa maganar nan
ta ji sanyi a ranta, dan idan ta fadawa Zainab,
kara ɓata mata rai zata yi dan su ne 'yan goyon
bayan Fu'ad. Ga Dr.Jalo yau sati guda ke nan
baya amsa wayarta bata ma sake sake ganin
sababbin rubutunsa ba. Ta damu tana dai
tunanin ko jikin ne, dan taga alamar bashi da
lafiya, ba dai ya son ya fada mata ne kawai.
Rayuwa ta tsananta a gare ta babu abinda
take tunawa ta ji dadi a ranta, aikin ma da take
yi tana sha'awa duk ya fita a ranta.
4 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
Cikin sanyin jiki Nasrin ta jawo wayarta ta kira aminiyarta Dina, tabbas ta san Dina bata
tashi daga bacci ba amma dole ta sa ta tashe ta
dan ita ma tashinta aka yi.
Dina ta na layi tana magana dakyar
amma data fara jin jerin rugugin bakaken
maganganunda Fu'ad ya fada sai ta ji ta
wartsake, dan da farko ta zaci ma a mafarki
Nasrin take fada mata.Sai Dina ta dauki salati
tana yi tana nanatawa.
Hawaye ya surnano daga idanuwan
Nasrin ta ce "ya zama sirri a tsakanina da ke
kada ki fadawa ma Ahmad ki bar ni da shi
kawai. Ni wallahi ban taɓa jin ina son Fu'ad ba
fa, darajar magiyar iyaye da kuma nacinsa ya
sa nake sauraronsa kuma halinsa bai yi min
ba."
Dinah ta yi ajiyar zuciya ta ce, “na san
da haka Nasrin mu ci gaba da addu'a.”
"
Su ka yi sallama suka kashe waya.
Malaika ta sake tasowa daga kan
katifarta ta rarrarafa kan gadon Nasrin.
5 | Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
Ta ce, "au haka Fu'ad ya yi
miki?Gaskiaya gara ki auri Jalo, amma dai
kamar Fu'ad ya fi kudi tunda a turai yake."
Nasrinta ji kamar ta shake Malaika tà,
dan ta ma manta tana cikin ɗaki da ba zata yi
magana da Hausa ba, ko da yake turancin ma
tana ji.
Nasrin ta yi alkawarin daina tankawa
Malaika ko me zata ce dan ta ga abin nata ba
mai karewa ba ne komai sai ta tsoma baki.
Nasrin ta ja dogon tsaki ta, ta rufe kanta da
bargo.
Malaika ta sake rarrafawa ta koma kan
shinfidarta ta kwanta.
+2
Wayar Malaika ceke kara, ta zabura ta
tashi a gigice ta jawo wayar sai ta dauki salati
da karfi kai kace mutuwa aka yi, tun kafin ta
amsa wayar take salati. Gaban Nasrin ya dinga
faduwa ta yi firgigita ta yaye mayafin data
lulluɓa tana kallon Malaika cikin fargaba.
-
Malaika ta amsa waya a gigice ta ce,
"Baba ina kwana. "
Baban Malaika yace, "ko ki dawo gida
ko in tsine miki albarka. Gidan uban wa kika
6 | Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
je? Dan ance wai kina Abuja. Wa kika sani a Abuja? Karuwa zaki zama?"
Malaika ta zabura ta tashi tsaye a gigice, ta ɗora hannu aka ta ce, "Wallahi Baba sharrin
Shamaki ne ya san in da na tafi, kawata ce fa
mai aiki a NTA ta gayyace dan ta yi hira da ni, ni zan wakilci kano kuma an ba ni Woman
leader ta Kano gaba daya. Ga Nasrin din ma dan ka tabbatar ba yawan banza na tafi ba a gidansu nake."
Malaika ta taho da gudu ta nanikawa
Nasrin waya a kunne, Nasrin na fusgewa har sai da ta tsaya ta rike wayar tana sauraro, ba tare da ta yi magana ba.
Nasrin ba ta ankara ba ta ji Baba tsoho
yana ambaton sunan Nasrin yana gunzumawa iyayenta asharai, daga baya ya hada sunan Malaika da Nasrin din ya mulmule ya cakuɗe
ya danna musu asharai. Nasrin bata san sanda
ta yi wurgi da wayar ba a kasa, wayar ta
tarwatse a kasa.
Malaika ta zabura ta dafe kirji ta ce,
"Nasrin!yaya kika yi min wurgi da wayar da
7| Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
nake ji da ita? Baban nawa kike wa wurgi da
waya? Me yace miki ne?"
Nasrin ta yi ruf da ciki ta juya baya sai
hawaye zafafa suka dinga kwaranya daga
idanuwanta.
Ta fara karanta Istigfari tana ta tunanin
laifin da ta yi wa Allah Ya jeho mata.
dunkulalliyar masifa wacce take azabtar da ita
wato Malaika. Ta na neman gafara Allah ya
yafe mata, ko zata ji saukin bala'in nan shine
Ya janye mata Malaika daga kusa da ita.
Malaika ta haɗa wayarta ras ta kunna sai
ga kira wannan karon Mahaifiyarta ce.
Malaika ta dauka a gigice ta ce, "Iyata!
Lafiya na ji kina kuka?"
Iya ta sharce hawaye ta ce, "Malaika,
yanzu haka za kiyi min, ki jawo min abin gori
a gari? Yanzu gashi kin ja aurena ya mutu a
sanadiyar tafiyarki shiga duniya. Babanki yace
ni nake zuga ki ya sake ni."
Malaika ta dafe kirji ta ce,"Baba ya sake:
ki? Toh ki rabu da shi kawai ki koma gidanku
zan samo mana kudi idan na fara aiki sai in zo
8 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
in kawo ki Abuja mu yi zamanmu ke ma ki rabu da rayuwar wahalar nan kauye ta wahala."
Iya ta bude baki tana mamaki ta ce,
"Malaika kina da hankali kuwa? Ki dawo gida
a yau din nan ko in daga miki Nono. Ga
Shamaki a zaune ya yi rantsuwa shi bai sake ki
ba, amma kika yi karya kika ce ya sake ki, ya
yi miki watsi da kaya, ya yi miki korar kare.
,,
Malaika ta dora hannu aka ta namagana
cikin ɗaga murya har sai da kwakwalwar
Nasrin ta fara tafarfasa dan bata saba jin irin
wannan tankiya haka ba.
Nasrin ta sa hannu ta toshe kunnuwanta
dan bata so ma ta ci gaba da jin abinda Malaika
take fada. Ta ji dai ance an saki uwarta, ta ji an
Ice Shamaki yace bai sake ta ba.
Nasrin bata ankare ba, ta ji dirar Malaika
a bayanta tana nanika mata waya a kunne, tana
yi mata Magana cikin rada "ga Iyata ki faɗa
mata ke kika ce in zo.'
"
Nasrin ta yi kasake tana sauraron abinda
Iya take fada, hankalin Nasrin ya kara tashi.
Iya ta na kuka tana fadin "Malika kin
cuce ni, kawarki ta cuce ni. Yanzu gidan marar
9 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
mutunci marar aure za ki koma ki tare? Duk
ismatar da aka co tanzania Abuja na diki
tana zaman kanta a kisan bata da matad
ce
yin wargi
(20 st Nasrin to finish idosa hawaye
sitsiyayo, tana jimuryar Shafakfa gefe yana ta
sibayani akan Nasrin yana cewa iface sila, ita
intake aiko mata da kati waya da Azurdun
skudi har ta hure mata kunne ta ja ta zuwa Abuja Nastin tasak li da
skwaraɓaɓɓiyar wayar nan ta sake wargajewa.
Iswlsw Malaika taskwalla Kará ta dafe Kirita
ncé, “Haba Nasrin❗Wayar tawà zäkì zaki få¸ããã fasa, da me
zan dinga jin lafiyar 'ya gidan W Juara tana kwashewa tafa gunguni
sdomm wayarta istashi, wannan karofita flfaku
qdatyawatiswi ise as ons isb it &T.sbst exist Nasrin ta fima añá kūkā kðacy [!? a
sdünk min Kukuñéia yanke
sakan Malaika dan ba zata datiWand sin
fdan su sukuba bæ‚ybææaif a gu Malaika suna zarginta nan Malaika a re
saba
ha
sta barcio ta takurawa rayuwágába ya bata da sukuna tabby, kxle. aid exileM" afbet sast sжlux sa st syl
TEISM ashig UNY in
10 Jamilu Umar Tanko JUT
a win
TULOжNGT 16U ulimet e
ta.
CanyonkaseyDAMA NI CE...2
Idan Malaika bata bar gidan nan ba ayau to ita
zata bari.
Nasrin ta mike tsaye tana sharce hawaye
ta bude durowarta ta dauko kayan sakawa seti
uku leshi daya, atamfa (super ) da material,
masu kyauwun gaske, ta mikawa Malaika sai
mamaki ya hana Malaika rufe baki.
Ta tambaya "me zan yi da shi?"
Nasrin tana Magana dakyar ta ce, “na ki
ne na baki kyauta."
Malaika ta yi shewa ta yi tsalle tana
godiya.
Nasrin ta dauko Jakarta ta bude ta zaro
kudi Naira dubu goma ta mikawa Malaika,
Nasrin ta sake zaro Naira dubu biyar ta sake
mikawa Malaika.
Malaika ta karɓa cikin sanyin jiki ta
tambaya "wannan fa na meye?"
Nasrin ta ce, “"dubu biyar kiyi kudin
mota dubu goma ki je ki ja jari ki zauna a
gidan mijini kada iyayenki su tsine miki a
banza."
Malaika ta sulale ta zauna a kan kujera ta
girgiza kai ta ce, “gaskiya bazan tafi ba, dan
11 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
wallahi bazan iya sake yin rayuwa da Shamaki ba, Mugu ne."
Nasrin ta fusata ta fara faɗa, tun tana
da Hausa har Hausar ta kubce ta juye turanci.
Oho Malaika ma bata san me take cewa ba sai
kallon bakinta kawai take yi ita dai a ranta ta
Kudira ba in da zata je yau ko da kuwa garin
Abuja sai yi girgiza.
Nasrin ta yi magana ta karshe ta ce, “ko
ki tafi a dadin rai ko in kira masu gadi
(security) su fitar min da ke da karfin tsiya.
.99
Malaika ta zaci wasa ne, bata tabbatar ba
sai da ta ga Nasrinta jawo waya ta kira John, ta
kuma fada masa su zo gidansu zasu fitar mata
da wata mata da ta ki tafiya.
Sai Malaika ta mike da gudu ta nufi
dakin Zainab da Salis tana ihu, suka firgita
suka mike da gudu suna salati sun zaci gidan
ne ya kama da wuta, Suna bude kofa suka ga
Malaika tana kuka ba ma sa gane abinda take
cewa saboda kuka ya ci karfinta.
Hankalinsu ya tashi aka dingumo wajen
Nasrin suka iske Nasrin ta fito mata da
12 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
akwatinta falo, ga security a bakin kofa suna
jiran a basu izini su karaso.
Zainab da Salis sun ga rashin kyautawar
Nasrin suna tausayawa Malaika amma takaici
ya hana Nasrin yi musu bayanin komai sai
faman huci take yi. Ta gama Magana ta ce, ko
ita ko Malaiaka sai dai su zaɓi ɗaya, idan sai
Malaika ta kara kwana a gidan nan to ita zata
haɗa kayanta ta tafi kuma ita da su har abada.
Zainab ta salami security, suka
tafisannan ta zauna ta yi musu sulhu ta ce
Nasrin ta bar Malaika ta yi wanka ta karya
kumallo, direba ya kaita tasha ta tafi a nutse.
Nasrin ta amince amma tana zaune a falo
tana jiranta, Zainab ta bawa Malaika kayan
sakawa tsala-tsala kala biyu, Salis ya bata kudi
Naira dubu goma. Malaika ta haɗa kan kuɗi ta
damke tana murna da wannan dukiya amma
tana takaicin tafiyarta. Da ta zo zata tafi sai da
ta sake yiwa Nasrin magiya tana bata hakuri
akan ta bar ta ta zauna, Nasrin ta ji kamar
tausayinta zai kama ta amma ta tuna taʼasar da
Malai̟ka ta yi sai ta kawar da kai gefe. Malaika
tana kuka, Zainabma hawaye take a haka suka
13 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
rabu, direba ya kaita ya sakata a motar Kano,
sai da ya tabbatar Mota ta cika ta tafisannan ya
dawo gida kamar yadda Nasrin ta umarce shi
da ya yi.
Zainab da Salis suna matukar mamakin
yadda Nasrin ta zama marar tausayi kuma
mafaɗaciya, da nada basu santa da haka ba
amma sun kasa ce mata komai, dan sun ga
alamar ranta a ɓace yake tun sanda Malaika ta
zo gidan nan bata yi musu magana, haka ba su
sake ganin dariyarta ba.
Tafiyar Malaika tasa Nasrin ta ji tamkar
ta yarda kwallon magwaro ta huta da kuda,ta ji
iska sanyayyiya tana busa ta, ta ji ta rage
takaicin da suka taru suka addabe ta.
**
Wayar Nasrin ce ta dauki kara tana
dubawa ta ga sunan Dina sai ta tabbatar da
akwai magana dan haka ta danna ba tare da ta
yi magana ba, ta kasa kunne tana saurarenta.
Dina tana magana cikin ɓacin rai da alama
14 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
BABI NA GOMA
RANAR LAHADI.
N
.ABUJA
asrin ta na zaune akan kujerar
dake tsakiyar dakinta tana shan
shayi, bata cikin walwala kwatakwata, ta jawo wayarta ta kira lambar Dr.Jalo
shi kaɗai ne bata yin fushi da shi. Tana kira ya
ɗauka sai ta yi mamaki data ji muryarsa garau
cikin farin ciki.
Ta fada cikin sanyayyiyar murya “inaka
shiga fiye da sati ban ji ka ba? Kullum sai na
kira ka bana samunka kuma na daina ganin
rubutunka. Hankalina ya tashi na zaci jikin ne.
Yaya jikinka?"
Ya lumshe ido ya yi murmushi yace,
“jikin ne amma na sami sauki. Na gode.
Nasrin!shiyasa wani lokacin na kan yi kuka
domin matar da nake da ita Rayyana ban taɓa ji
ta yi min addu'a ba itace kuma uwar ‘ya'yana,
kuma auren soyayya muka yi sosai. "
16 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
Nasrin ta bude baki sororo tana saurare cike da mamaki, ta tambaya "kamar yaya ban fahimce ka ba? Ba ni labarinka."
"
Jalo ya yi murmushin karfin hali ya girgiza kai yace, “kin tabbata kwakwalwarki
zata iya daukar abinda zan fada? Labarina yana
da matukar tsauri mai hade da damuwa da
jimami. Za ki iya ruguza farin cikin da kika
gina na baya a rayuwarki, zaki iya haɗuwa da
damuwar da zata iya hana ki bacci har cikin dare."
Ta yi dan murmushi ta ce, “mace mai
kamar maza kwari ne babu, haka ne taken da
Daddy na yake yi min. Ina da dauriya ba ni da
tsoro, kada ka damu na saba jin abinda ya fi
haka ma.
"
Jalo ya gyara zama yace," ina da
tabbacin cewa baki taɓa jin labari mai
firgitarwa kamar nawa ba."
Sai ya kashe waya ba tare da ya yi mata
sallama ba.
Hankalin Nasrir ya tashi ta sake kira,
wayar tana shiga amma bai amsa ba, da ta ci
gaba da kira ma ta ji ya kashe wayar gaba ɗaya
17 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
ma. Daga nan ta ji ranta ya ɓaci ta fara tuhumar Jalo da laifin wulakanci bistasm ab ɔtɔ
Ta fara bawa zuciyarta hakuri, tail
alkawarin daina shishshige masa, ta hakura da
nemowa zuciyatta farin cikin da take faman yia
amma baya samuwa, ta yi sallama da farin ciki,
tassan Ubangijinta mai jin kai ne zai musanya
mata rayuwarta da wasu masoya na daban.
Hawaye ya surmano daga idanuwanta ta koma
ta jingina da kujera tana karanto innalillahi wab
inna ilaihi raju'un. " .916b
ism A haka ta wunia daki cikin bakin ciki
dan ma ta yini tana karatun ku ani shiyasa ta ji
sanyinas ranta ba dan haka ba da zuciyarta
bindiga zata yi. Shayi da biskit ne abincinta sait
a waya suka gaisa da Zainab dan ta rufe kanta ad
daki ta ki fitowa ta ci abinci,syg sy olst
"
ism Zainab kuwa ta shiga tsoronta har ta fara
tunanin kiran mahaifiyarsu tas sanar mata halin
das Nasrinske ciki.Dan tasfara tunanin in har
ba'a jefe ta ba a wajen aiki to kuwa ta yirgamo?
da bakin saljanid Dangaba daya halinta ya
canja, wannan aba Nasrin dingda suka sani
adaba cedeg isуs das byBY its sm six sb sdsg
18 Jamilu Umar Tanko JUT TUL 0xa6T 16U ulims
DAMA NI CE...2
Da misalin karfe tara na dare Nasirin
tana kishingide akan kafet tana jan carbi tana
kallon 'Sunnah TB' da alama wa'azin nan yana
shigarta dan kamar da ita ake yi ana lallashin
wanda aka ɓatawa rai a rayuwa, akan ya yi
hakuri Allah Ya na tare da mai hakuri.
Wayarta ce ta yi kara tana dubawa ta ga
sunan Dr.Jalo. Ta yi matukar mamaki da ganin
kiransa haka ta yi farin ciki. Jikinta na rawa ta
danna sai ta ji ya na magana cikin sanyin
murya, hakuri yake bata akan kashe mata waya
da ya yi, ya shaida mata kuka ne ya ci karfinsa
tun ma kafin ya fara bata labari.
Hankalinta ya. tashi sai ta gyara zama ta
dafe kirji ta fada in lallashi. "Dakta! Ka yi
hakuri ka bani labarinka ni zan zama abokiyar
shawararka in har zuciyarka ta nutsu da ni
kamar yadda tawa ta yarda da kai tun ban taɓa
haduwa da kai ba."
Dr.Jalo ya yi murmushin karfin hali ya
girgiza kai ya ce, “damuwar da kika yi da ni ta
sa na ji kamar duk duniya babu mai kaunata
kamarki, baya ga mahaifiyata wacce a koda
yaushe ta ke kusa da ni, bata daina rainona ba
19 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
har yanzu kamar yaro dan goye. Allah Ya
bawa Mahaifiyata gida a aljanna madaukakiya.
Allah Ya bawa Nasrin gida à cikin aljanna
madaukakiya itama. Amin.
Nasrin dai har yanzu hannunta na rike da
kahon zuciyarta gabanta na ta faduwa, ta amsa
da “Amin Jalo. Me yake faruwa ne?"
Jalo ya gyara zama ya matse hawaye ya
cije baki ya yi shiru yana tunanin ta in da zai
fara bata labarinsa yadda hankalinta ba zai
tashi da yawa ba.
LABARIN JALO:
"Sunana Kabir Hassan Jalo,amma an fi
kirana da Jalo. Ni Bafillatani neɗan asalin wani
gari da ake kira Yalleman, a karkashin
hukumar Kaugama cikin Jahar Jigawa.
Allah Ya azurta garin Yelleman da
manyan mutane masu arzikin gaske, masu
ilimi, Matansu kyawawa,haka matasanmu
masu nutsuwa ne.
Garin Yelleman ya kasu kashi-kashi,
akwai'Yelleman Tijjanai' su ne Hausawa.
20 Jamilu Umar Tanko JUT
•
DAMA NI CE...2
Sannan akwai 'Yelleman Fulani' su kuma sun kasu kashi-kashi ko wanne dangi(Family) akwai sunansu misali akwai 'Yottore', akwai
na sarauta sune ake kira 'Tal', akwai 'Gajos"
sune wadanda suka yi yake-yake ada kenan,akwai 'Bal', akwai 'Jah' akwai ‘Lamin',
akwai 'Njay', akwai 'Sise', akwai ‘Kulbari',
akwai 'Bah', akwai 'Dem', akwai ‘Khan Jallo',
"Sise wan', akwai ‘Magasa', akwai ‘Barros', akwai 'Nyam', akwai 'Sidi', akwai 'Bal' da
sauransu.
Mu na da yawa a Lagos saboda mu na
yin sana'ar canji sosai yawanci a Idiyarba,
Agege, Lagos Island da Yaba mu ka fi zama.
Mahaifina ya rasu ten ina dan karami
shekaru hudu, ya bar mu mu shida, matansa
biyu mahaifiyata da uwar gidanta Umma.Mu
uku ne a wajen mahaifiyata, Amadu ne
babba,sai ni, sannan'yar autarmu ta goye
Fatima. A can ɗakin kuma manyan yayyanmu sun grime mu sosai maza uku Iliya,Umar,
Muhammadu.
Mahaifina bashi da kudi talaka ne, ya rasu bai bar mana komai ba. Dan haka mun
21 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
dandani talauci tun muna yara tun ma ba'a je
ko inaba. Mahaifiyata tana yaye kanwata
Fatima, ta sami mijin aure kasancewarta tana da kuruciya sosai, a lokacin shekarunta ashirin da huɗu, dan haka ta yi aure ta bar mu a hannu kishiyarta ta tafi Lagos da miji amma ta tafi da kanwata Fatima. Zama na amana da mutunci
kishiya da rikon ‘ya'yan kishiya duk da
tsantsar talaucin da ake ciki.
Umma ta rike mu kamar ‘ya'yan cikinta,
da kanta take fita kauyukan kusa da mu irin su
Askandu, walawa, Dingare, Burtali ko Wailari ta nemo kudi.Yayyena ma su fita su nemo
mana abinda zamu ci.
Umra ta rike ni tamkar dan cikinta tana
so na sosai kasancewar ta daɗe bata haihu ba
bata da karmin da.'
"
Nasrin ta gyara zama ta gyada kai ta ce,
"Allahu Akbar! Allah ya jikan Baba Ya kai
rahma kabarinsa."
99
Ya yi ajiyar zuciya yace, "Amin Nasrin."
66
Ta ce, Yaya rayuwarku ta kasance
kuma?"
22 Jamilu Umar Tanko JUT
Ya yi murmushin karfin hali ya ci gaba NICE...2
da cewa na shiga Makarantar Madarasa
firamaren da wani ɗan garin ya gina sunansa
Modibbo. Anannagama, na far fara sakandire
kenan Allah Ya yiwa Umma rasuwa ade
999
dole
DAMA AMA
Mamana amana ta zoo ta dauke nini na komama wajenta a
Lagos.A unguwar Agege suke acanna zauna
bhar na gama sakandire. Du har na gama sakandire. Duk da a can dinm ma'
sala, wadata, mijin ɗan canji ne amma bashi da
jari sai dai ya karɓi kudin wasu (dallars) ya
sayar musu ya sami riba ya biya haya da kuɗin
makaranta a ci abinci. A nan ma ta haifi yara
uku dukka maza Umar usman da Abubakar.
Kuma daga kanta ya fara samun haihuwa ya yi
aure-aure da dama suna rabuwa bai taɓa samun
haihuwa ba."
153
BILA
"
BY TSVIQgis ablo sbet sT
babu
Ya nista rufe bakınsa wayar ta mutu,
Nasrin ta yi sauri ta kira sai ta ji a kashe ta yi
ivZaton sharrin network ne amma ta gwada fiye
da sau ashirin bata shiga ba. in said band ismox aim
falo tana ta zufa
hankalinta a tashe. Sai katse gumi take daga
goshinta tana ta salati a cikin zuciyarta. Kamar
daga sama ta ji magana
SVSO BI SE UIST SY ED SUS
"saitis?
23 Jamilu Umar Tanko JUT
W DAMA NI CE...2
"Nasrin lafiya?"
Ta juya da sauri sai ta ga Zainab.
Та wayence ta sassauta damuwar da take
ciki ta ce "zafi nake ji.'
"
"Zafi kamar yaya ga fanka ga Ac?" inji Zainab.
Tabbas tambayar nan bata da amsa sai ta
sulale ta koma daki babu shiri ta saka mukulli
ta datse. Ta jawo wayarta ta ci gaba da gwada
kiran Jalo bata shiga ba har yanzu a rufe.
BAYAN KWANAKI 2
Abin mamaki tana zaune da yamma sai
gashi ya kira da kansa, Nasrin ta yi sauri ta
masa cikin zum”di.
Ta fada cikin marainiyar murya, "Allah
ya huci zuciyarka da alama na yi maka laifi, ka
yi hakuri."
Ya girgiza kai ya ce, "wallahi ba kiyi
min komai ba kanwata, damuwa ce ta hana ni
amsa miki. Tuna labarin da ya faru da ni a baya
tamkar gyambo ne ake fama min a cikin
zuciyata. Na yi kokarin amsawa sai kuka ya ci
karfina.'
"
24 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
"Subhanallah! Wannan wanne irin
mummunan al'amari ne ya faru da rayuwarka
haka? Nasrin ta fada a gigicé.
Ya matse hawaye ya fara magana cikin
marainiyar murya.
CI GABAN LABARIN JALO
Jalo ya ce, "rannan na shaida miki
mahaifina ya rasu, Marikiyata ta rasu ko?Sai a
wajen Mahaifiyata na karasa karatu Mijinta ya
rike ni tamkar dansa na cikinsa ko?"
Nasrin ta koma kan gado ta kwanta ta ce,
"Eh ka fada min haka. Allah Ya albarkaci
zuriyarsa. Allah ya bashi ladan rikon maraya
da ya yi."
,,
Jalo ya ce, "Amin. Da na gama sakandire
na ci sosai sai na shiga Jami'a ta Lagos anan na
yi digiri dina na karanci ‘'Political science' ina
gamawa na ci da yawa na wuce na yi masters
akan 'International relation."
A shekara da zan gama Masters na hadu
da matar da na aura a jami'a, a lokacin ta na
shekarar farko a digiri.
25 Jamilu Umar Tanko JUT
DAMA NI CE...2
A lokacin mahaifinta ya na shugaba
Jami'ar mu mun je gidan ni da wani abokina
ɗan uwansu anan auka hadu, Na ji ta burge ui
saboda takarramawar da ta yi mana, ta karɓi
lambobin wayoyinmu, har ma na manta da ita
take kira na akai-akai muna gaisawa har ta kai
ta kawo nima ina kiranta mu gaisa. Idan na
haɗu da ita a cikin jami'a duk da gatanta da
tsaleliyar motarta haka zata fito daga mota