har bata gani sosai saboda yunwa.
Ta isa kofar shiga falo, gami da yin
sallama sannan ta daga labulen falon ta shiga.
Maimakon ta ji muryar Zainab sai ta ji wata
murya ta amsa mata. Muryar ta yi mata kama
153 | Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
da muryar da ta taɓa sani amma bata gasgata
ba har sai da ta shigo tsakiyar falon ta kalli mai
maganar sosai ta gasgata ba gezau ba ne
gaskiya ne, ita din ce kuwa.
Malaika Shamaki. ta gani zaune akan
luntsumemiyar kujera ta dora kafa daya kan
daya tana shan AC ga remote din talabijin a
hannunta tana canja tasha yadda take so, ta na
karawa kuma tana rage murya. Ta cokalo
daurin dankwali gaban goshi, gami da saka
wani kwaftareren gilashi baki a fuskarta.
Nasrin ta ji wata gagarimar fargaba ta
dira a cikin zuciyarta, ta ji tamkar aradu ce ta
sauko a kahon kalbinta. Ta ji rugugin takaici
ya taso mata. Ta yi kamar ta dora hannu akai ta
rafsa ihu. Sai ta tuna da cewa duk sanda bala'i
ya diro maka ka lakanci karanta
"Innalillahi wa inna ilaihi raju'un.'
"
Ta fada a lokacin da take kokarin
sulalewa, ta sulale ta zauna akan kujera dan
kafafuwanta ba zasu iya daukarta ba. Malaika
ta taso da sauri cinkin murna zata rungume ta
tana fadin "oyoyo ga kawata ta dawo."
154 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE 1
Jakarlap-top din Nasrin ta sulmiyo daga
kafadarta zata fadi kasa. Malaika ta yi sauri ta
kama mata. Nasrin ta daga mata hannu alamar
kada ta matso kusa da ita.
Nasrin ta zauna ta dafe kai tana ta
jujjuyawa, sabbabin ciwuka ne suka taso mata,
zazzaɓi da ciwon kai suka hadu da yunwa,
gajiya da bakin ciki suka cakuɗe mata.
Malaika na tsaye akanta tana kallo tana
fada a ranta "Tunda na zo bazan tafi ba, ko
zaki mutu wallahi, irin wannan daula da na
shigo kuma in tafi. Ashe ma na zama
sarauniyar wawaye ta shekara. Sai dai idan an
raba ni da raina sannan za'a iya raba ni da
gidan nan, zama a Abuja daram ba zan koma
Kano."
"
Nasrin ta ci gaba da mamakin ta in da
Malaika ta diro, ta shigo gidansu alhali ita bata
taɓa faɗa mata sunan unguwar da take a Abuja
ba. Ta ma daina amsa wayarta ko ta kira ta, tun
ranar da ta goge lambobinsu. Shin Malaika
mutum ce ko aljana?Hakika na ɗauko ruwan
dafa kaina. Lallai na jajiɓowa kaina masifa.
Watakila ma na dauko ajalina da hannuna.
155 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
Yaya zan yi da wannan natacciyar matar, data nace min? Ina zan kai hakkin auren da ta kaso
a dalilina? Ta yaya zan wanke kaina a wajen
Shamaki ya yarda ba ni na ce ta fito ta biyo ni
Abuja ba? Allah Ka ga zuciyata Ka fitar da ni
daga cikin wannan kangin da na shiga. Ka
shiga tsakanin na gari da mugu. Ya Allah kada
Ka bari Malaika ta cutar da mu tunda da
kyakykyawar niyya na karɓe ta." Nasrin take
tambayar zuciyarta kuma tana ta addu'a.
Suna cikin wannan hali sai ga Zainab ta
fito daga kicin da sauri dauke da faranti ta jero
abinci kala-kala wanda ta shirya shi na
musamman domin bakuwarsu Malaika.
Ta sankare a tsaye da ta ga yanayin da
Nasrin ta shiga, ta tambaya a gigice, "Nasrin!
Lafiya ko jikin ne?"
Nasrin ta dago da jajayen idanuwanta, ta
dubi Zainaba cikin sanyin jiki ta ce, “ta ina
matar nan zo mana gida? Ta yaya ta san gidan
nan ta zo, dan ni ban gayyace ta ba?"
Zainab ta cika da mamaki ta ce,
"Malaikarki ce fa wacce kike ba ni labarinta
kullum. Ko ba ki gane ta ba ne? Kin manta
156 | Jamila Umar Tanko (JUT)
re
DA MA NI CE... 1
wayarki a cikin daki, kina fita na ji ana ta kira
na je na dauka, ta ce gata nan zata zo Abuja
kun yi za'a bawa direwa waya a fadi kwatance
ya kawo ta har gida,na rike waya a hannuna
muna ta waya har ta karaso. Da ta isa tasha ta
kira, na yiwa direba kwatance ya kawo ta.",
Nasrin ta ja dogon tsaki ta harari Zainab
ta juya ta harari Malaika sama da kasa, ta tashi
ta shige daki a fusace gami da bugo kofa da
karfi ta datse, yayin data yi arangama da wata
dankareriyar tsohuwar akwatin Malaika a
tsakiyar dakinta wato kaurowa ma ta yi gaba
daya, babu ranar tafiya tunda ta hankaro kaya
haka.
Nasrin ta ji wani ɗaci ya taso daga cikin
makoshinta har zuwa bakinta, ta fara zaton
ɗacin ajali ne ya tunkaro ta gadan-gadan. Sai ta
dau salati ta sulale ta zauna a gefen gado ta
dafe kai.
Malaika ta langwaɓe kai,wai nan ita abar
tausayi, ta zare bakin gilashin da yake makare
a fuskarta, sai hawaye ya sirnano daga
idanuwanta, ta sulale ta zauna akan hannun
kujera ta yi tagumi.
157 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
Hankalin Zainab ya yi matukar
tashi,kunya ta kamata, ta tafi kan tebur din cin
abinci ta ajiye farantin abinci. Ta taho da sauri
ta dafa kafaɗar Malaika tana lallashi, ta kamo
hannunta ta kaita kan tebur din cin abinci ta
zaunar, tana bata baki akan ta daure ta ci abinci
ko kaɗan ne kada ta sa abinda Nasrin ta yi
mata a rai ya dame ta.
Sai Malaika ta kyallare ido ta hango
dankareriyar kaza guda sukutun, bayan kayan
ciki, kai da kafafuwan da aka cire ba'a cire
komai a jikinta ba, a haka aka gasa ta a gashe
tana kamshi. Malaika ta sake kanne daya idon
ta kyallaro shinkafa, ta zama koriya ga karas,
wake gwangwani, gami da hanta da koda duk
an jere a ciki, gefe kuma salad haɗɗade ya ji
kwai. Ga lemuna kala-kala da kofi a kusa gaba
daya nata ne.
Nan da nan ta ji ta fara fita daga cikin
hayyacin dan dadi, ta fara tunanin ko jirgin
tunanin nan nata da ya saba daukar ta ya kaita
duniyar karya ne ya danno.
Zainab ta juya baya za ta shiga ɗakinta,
sai Malaika ta yi mata gwalo, ta saita masun
158 | Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE 1
yatsunta ta kaiwa kazar nan hari 'CAK' ta
kafa mata hannu. Ta raba cinyar nan da gangar
jikin, ba tare da ɓata lokaci ba ta kai mata sara
ta cake ta da hakora, ta yaga ta ci gaba da
taunawa.
Kan kace kwabo dadi ya kaiwa
kunnuwanta hari, nan da nansuka dauki zugin
dadi 'zuuuu' dan tunda take bata taɓa cin
abinci mai dadi irin wannan ba.
Ta na ci tana fada tana nanatawa a
bayyane tamkar karatu, ta ce, "Nasrin! ko za ki
mutu ba zan bar gidan nan ba, sai dai ayi duk
wacce za'a yi wallahi. Karen hauka ne ya cije
ni da zan koma Dorayi?"
Kash!
Anan zan dakata.
Mu hadu a 'DA MA NI CE. . . .' littafi kashi
na 2
Mu ji yadda zata kaya:
*Tsakani Malaika da Nasrin
159 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE..
*Tsakanin Dr.Jalo da Nasrin.
*Tsakanin Fu'ad da Nasrin.
*Tsakani Shamaki da Nasrin.
*Tsakanin Shamaki da Malaika
Ta ku
JAMILA UMAR TANKO (JUT).
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels