ta yi kamar itama ta barke da kuka.
127 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
Da yake Malaika 'yar dangice jama'a
daga Muntsira suka yi ta diddikowa suna zuwa
gaisuwa, haka dangin Shamaki da abokansa na
Bichi da na BUK suka yi ta zuwa matansu da
Mazansu.
Anan ne Malaika ta ga Fatima Giwa.
Duk da an yi mata mutuwa amma sai da ta
jinjina kyau da kudi irin na Fatima, farar shuwa
kal. Ta kawo musu buhunhunan shinakafa biyu
da Kudi naira dubu goma. Malaika ta dauko
kwaraɓɓiyar wayarta ta karɓi lambar Fatima
Giwa abin takaici kowa ya gane, bata karɓi
lambar wayar kowa ba sai ta mai kudi..
*** *** ***
Bayan kwanaki bakwai sannan kowa ya
watse aka bar Malaika da Shamaki sai sauran
yaransu guda biyu, su kaɗai jugum, sai a
lokacin mutuwar ta dawo musu sabuwa fil.
Malaika bata da aiki sai kuka Shamaki yana ta
lallashinta. Yana ta lallaɓata duk wani abu da
zai kwantar mata da hankali shi yake yi. Sun
sassami kudi amma duk ya tattara ya damka
128 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
mata dan ta ji sanyi a ranta dan ya san ita
masoyiyarsu ce.
Vayayi sanyi kalau da
alama ta fara saduda da kyalkyalin duniya.
Ba'ataɓa yi mata mutuwar da ta ji a jikinta ba
sai wannan karon, kasancewar Uwa da uba da
wasu kakaninta duk suna raye haka 'yan
gidansu wajen su talatin suna nan da rai, da
wayonta babu wanda ya taɓa mutuwa. Haka
shima Shamaki bayan Mahaifinsa da yamutu
yana karami bai san shi ba.
Kakansa da 'yan uwansa duk suna raye dan
haka sai yanzu aka fara yi masa mutuwa.
Sun yi kuka sun gaji Ahmad ya tafi ba
zai dawo ba. Allah ya kyautata karshenmu.
shi ba. Mahaifiyarsa,
vidid
net
Malaika jikinta
Nasrin ta yi kokarinzumunci danmullum
sai ta kira Malaika kala ta yi mata ta'aziyya jumata taʼaziva idan
Shamaki na kusa ta ce a bashi shima. Malaik
ta mika masa shima ta yi masa taʼaziyya. Ta yi
mata alkawarin idan aiki ya yi sauki zata shigo
Kano ta yi mata ta'azivya azıyya. melicu sist
UCH IV:
Malaika ta ji dadi kwarai da wannan kulawa ta
sharariyar mai kudi da take yi mata.
62800s at out a omum
stop det oM Schuede ennem a ovadonat
129 | Jamila Umar Tanko (JUT) Us | 020
DA MA NI CE...
BABI NA BAKWAI
RANAR ASABAR. .ABUJA
au asabar ce, da misalin karfe
goma sha daya na safe, Nasrin
tana zaune a falo da kofin shayi
a hannunta. Dakyar take kurɓar shayin saboda
yanayin zazzaɓin da take ciki. Ita kadai ce a
gidan daga ita sai wayarta da take karancekarance a facebook.
Ta ci karo da sababbin rubutun Dr.Jalo tana ta
bibiya amma bata yi niyyar tofa albarkacin
bakinta ba. Kamar daga sama ta gan shi ya hau
(online) bata yi masa magana ba dan bata
shirya kwasar takaicin shariya ba, ta kanta take
yi yau.
Sai ta zaci mafarki take da taga ya yi
mata sallam. Ta amsa, ya sake gaishe ta. Nan
da nan ta gyara zama ta ji sanyin da take ji ya
fara gushewa dan har zufa ta fara feso mata. Ta
cika da murna a take ta amsa masa. Ya
tambaye ta menene tambayarta? Me take so ta
130 | Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
koya daga gare shi da take cewa tana so ta
zama kamar sa?
Nasrin ta kaikaice ta yabe shi, ta koɗa
shi, ta jinjina masa, sannan ta ce yana birge ta
ne haka kawai.
Da alama ya ji dadin kalamanta shima
sai ya yi mata godiya data sami dama takebiye
da shi.
Ta nemi ya fada mata mafita game da wata
matsalar aure dan taga rannan ya yi magana
akantaɓarɓarewar auren Bahaushe. A takaice
ta bashi labarin Malaika, sannan ta bashi
labarin Shamaki kamar yadda suka bata. Ta
shaida masa ta yi hira da mijin ba tare da matar
ta sani ba haka ta yi hira da matar ba tare da
mijin ya sani ba, kowannensu abinda ya faɗa
daban ne ta rasa mai gaskiya a cikinsu.
Dr.Jalo ya yi murmushi ya rubuto mata
bayanai a tsare daki-daki, ya jero matsaloli ya
jero mafita. Daga bayanansa ta fara samun
mafitar matsalolin auren Shamaki da Malaika.
Ta ji dadi sosai ta yiwa Dakta godiya daya bata
dama da lokacinsa yau. Shima ya yi godiya ya
sauka.
131 Jamila Umar Tanko (JUT)
CE... 1
Sai Nasrin ta nemi zazzaɓi ta rasa, ta
ware ragas, ta yi tsalle ta dire tana ta rawar
murna ita kadai a cikin falo.Hakika mahakurci
shine mawadaci.
Ta jwo wayarta da karfin gwiwarta ta kira
DA MA NI
wayar Malaika.
Malaika ta amsa amma tana ta magana
kasa-kasa cikin rada, da alama ba ita kaɗai
bace a in da take tana tare da mutane Malaika
ta shaida mata ta fito unguwa ne sai ta koma
gida zata kira ta.
Nasrin ta kashe waya tana kashewa ta
kira wayar Shamaki da karfin guiwarta tana,
murna ta samo masa mafita, Shamaki na ganin
kiran Nasrin sai ya ji ransa ya ɓaci, yayi jagejage da garin fulawa yana kicin yana kwaɓin
danwake, yara suna ta kuka suna jin yunwa.
Malaika ta fita unguwa bada izininsa ba.
Gaba daya yana zargin Nasrin dasake
ɓata masa Mata, dan ta turo mata katin dubu
uku jiya shi ta siyar ta sami kudin hawa A-daidai-ta-sahu ta shiga gari.
Ya na kallon wayar ya ki dauka sai a
karo biyu data sake kira, ya dauka a fusace
132 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
yana huci, Nasrin ta yi sallama sai ta ji ya ja
dogon tsaki ya katse.
Ta cika da mamaki bata tunanin hakan
yake nufi dan haka ta sake kira, ya dauka tana
gaishe shi sai ya yi mata tsawa “Menene
kuma? Kawar ta ki bata nan.
Ya kashe wayarsa ma gaba ɗaya.
Nasrin ta sankare a zaune tana ta
mamaki da takaicin abinda Shamaki ya yi
mata, lallai ya wulakanta ta, ba'a taɓa yi mata
irin abinda ya yi mataba a yau, ta fuskanci
haushinta yake ji. Ta shiga zulumi shin ko dan
bata zo musu gaisuwar mutuwa bane? To su a
suwa da za zasu kullace ta dan bata zo gaisuwa
ba? Yaushe suka santa ma da zai zama laifi?
Gaisuwar data yi musu a waya ma ai ta isa.
Kai! Ba wannan ba ne. Anya Shamaki bai fara
kishi badan ya gaMalaika tana yawan zancenta
da nemanta a waya?Dole da daya daga cikin
wadannan abubuwan da ta zaiyano a ranta.
.
Nasrin ta damu da wannan yankwanawa
da Shamaki ya yi mata,gashi shi ba kowan
kowa ba. Amma ta kudiri niyyar ko ya kira ta
ba zata sake ɗauka ba, itama har abada ba zata
133 | Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE...
sake kiransa ba. A fusace ta goge lambarsa
tana ta faman hucin takaici, ta rasa wanda zata
faɗawa wannan mummunan labarin, ta ji sanyi
a ranta.
Ta jawo wayarta a sanyaye ta kira
lambar Jalo, cike da fargaba kada ta sake
haduwa da wulakanci irin wanda Shamaki ya
yi mata. Tana kira ta ji Mace kamila ta amsa,
sai gabanta ya fadi ta yi kamar ta katse wayar
sai ta daure, ta san dai matarsa ce tabbas.
Cikin ladabi Nasrin ta gaishe ta sannan ta
shiga in-ina wajen gabatar da kanta.
Matar ta yi murmushi ta ce, “bari akai
masa wayar. Ga Jalon can."
"
Tana jin karar tafiyar matar har ta isa in
da yake ta mika masa wayar, sai Nasrin ta
shiga kogin mamaki gami da jinjina ga wannan
mace ta gari marar kishi. Hakika ilimi ya yi a
rayuwa rashin ilimi ke sa mata yin taɓargaza
da sunan wai kishi. Haka kawai sai su binciki
lambar mace a wayar mijinsu su kira suna
zaginta, shima miji a tutsiye shi ayi ta rigima.
Dr.Jalo ya karɓi waya bayan ya duba
sunan mai kiran. Ta ji kamar a dakile baya
134 | Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
walwala a yadda yake amsa gaisuwar, dan haka
sai ta shiga damuwa.
Nasrin ta ce, "na kira in gaishe ka ne
kawai, sorry ban san kana gida ba ina fatan
banyi laifi ba, uban gidana?"
Ya yi dan murmushi ya girgiza kai
'
yace
"ko kaɗan bakiyi laifiba, za ki iya kira
kowanne lokaci.'
"
Nasrin ta lumshe ido ta ce,"haba dai
kowanne lokaci, ai ko Madam bata damuwa
idan taga kiran ya yi yawa zata zargi wani
abu.'
"
Ya girgiza kai yace, "Madam babu
ruwanta.
"
Nasrin ta gyada kai ta ce, "amma ina jinjina ga
wannan gwarzuwar Mace ta gari, ta fahimci
mijinta yadda ya kainata."
Ya yi murmushi ya ce, "da Mamata kika
yi magana yanzu ba da Madam ba.”
وو
Sai Nasrin ta sake tsunduma cikin sabon
kogin mamaki tana linkaya.
Ta tambaya a cikin zuciyarta "Me yasa
mahaifiyarsa ta dauki wayarsa ta amsa sannan
135 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... ↑
kuma bashi ya zo ya karɓa ita ta tafi ta kai
masa? Lallai dan gata ne, ya cika sarauta."
"
Nasrin ta yi ajiayar zuciya ta ce "daman
maganar ma'auratan nan ne nake so in baka
labarin yadda muka yi, na kira su ɗazu zan
basu shawara kamar yadda kace in basu sai aka
sami matsala.'
"
Yace "mu koma online mu yi bayani na
fi kaunar rubutu (chats)."
Sai ta amsa masa cikin ladabi, suka
.
Nasrin da Jalo sun dauki awanni biyu cur
suna hira a rubuce,idan ta fadi matsala sai ya
faca mata mafita. Har ta gangaro matsalarta da
wanda zata aura Fu'ad, ta fada masa halayɩnsa
wanda take ganin aure da shi ba zai yiwu ba,
yana da yawan fushi sai ya yi wata guda cur
yana yi mata gaba. Jalo ya bata shawarwarin
yadda zata bi ta gyara shi.
Tabbas ya shaida mata Shamaki ya fara
jin haushinta yana zargin kudin da take bawa
matarsa yana kara jawowa ta raina shi.
"Meye mafita?" Nasrin ta tambaya
136 | Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
Jalo ya bata karfin guiwa ta ci gaba da
jajaircewa zata sami lada. Kada ta yi fushi
kuma kada ta gajiya.
Wayar Nasrin ceke ta ruri tana dubawa
taga Malaika ce ta tabbatar ta dawo daga
unguwa sai ta amsa da sauri. Da yake da
computer take hirar da Jalo, tana waya tana
bashi amsa.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajun." Nasrin
ta faɗa a lokacin da ta ji Malaika na kuka
kamar ranta zai fita.
Nasrin ta tambaya "yaya aka yi?"
Malaika ta shaida mata Shamaki ya sake
ta har yayi mata watsi da kaya.
Sai ta ji jiri ya fara daukarta ga Jalo a
Computer yana ta jero zancen mafita, nan
kuma aure ya taɓarbare.Sai ta kurawa rubutun
Jalo ido babu abinda zata iya yi a yanzu.
Nasrin ta katse waya tana ta huci ta sake
gasgatawa Shamaki mugun bawa ne shi yake
cutar da Malaika, tabbas shine makaryaci,
labarin duk da ya bata karya ne. Yana da kudi
yake ɓoyewa yake bin karuwai.Duk da ta goge
137 | Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NICE
lambarsa dazu, amma ta na da ita ala
'dailledcalls' da ta kira shi dazun. woorisjej
Nasrin ta kira wayarsa a fusace daman da
haushin wulakancin da yayi mata ɗazu sai ta
hada ta cashe masa.assislaM syst
☐ yana Shima ya amsa a fusace tashuciny
ace "menene kuma? Ai ta faru ta kare, sai ta
kaura Abuja wajenki ta zauna, saboda ke ta ki
zaman aure ta raina mijinta.
92;
aires Nasrin ta fusata ta ce, "baka da adalci,
baka san darajar aure ba.. Me ya kawo maganar
saki?" siit is inT TEMES
Yace "au har ta kira ta fada miki na sake
99
ta? To ni ban sakin matata ba idan burinki
kenan." ayed sb fetsw stem iyey isd st
Bol Sai Nasrin ta yi kasake ta kasa gane kan
wannan matsala. Ta kashe wayarta ta koma ga
Dr. Jalo ta iske ya sauka baya kusa. Nasrin tá
sulale ta kwanta tana mai tsananin damuwalda
shiga rudani. Mafita daya itace ta fita daga
harkar Malaika da Shamaki kawai. Daman bata
sansu ba balle matsalarsu ta zame mata
matsale. Bata da hawan jini samma da nalama
agog et ab oluⱭ.iswi aid exsy swayed by
138 | Jamila Umar Tanko (JUT)) oxosT U slime | TEI
DA MA NI CE... 1
Shamaki da da Malaika zasu saka mata. Toh
wai me ya yi zafi ido zai ci wuta?
*** *** ***
Da daddare misalin karfe goma da rabi
na dare taga Dr.Jalo a facebook ta gaishe shi ya
amsa amma sai ta ji ya ambace ta dawani suna
wanda ya bata mamaki.
Nasrin Abdul Nasir (kueen), bata yi
mamaki mai yawa ba dan dai bata rubuta
wannan sunan akan Username dinta ba. Ta
tabbatar ya yi bincike akanta, yau ya gano
kowacece Nasrin kuma me yasa take ta bibiyar
rubutunsa tana so su saba. Sai yanzu ya gane
da wa yake magana ashe da cikakiyar ‘yar
jarida yake magana, wacce take daya daga
cikin mata 'yan jaridar da suke burge shi
wadanda suka san makamar aiki.
Dr.Jalo ya jero mata waɗannan manyan
kalamai na jinjina. Sai ta ji tamkar a mafarki
take ganin wadannan kalamai nasa, ta tabbatar
yanzu ta zama mutum sosai a wajensa tun da
andzadad ng joint enou
139 jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
har ya damu ya bincika ya san ko ita wacece,
lallai ta sami shiga.
Ta yi masa godiya, sun kai karfe sha
biyu na dare suna ta magana a facebook, .
sannan suka yi sallma kowa ya sauka, bata
damu da kwanciya da wuri ba saboda gobe
lahadi babu aiki.
Tana duba wayarta ashe Malaika ta
kikkira ta da yawa, bata ji ba saboda ta saka
wayar a silent tun da yamma da suka ɓata mata
rai. Tana gani ta yi tsaki ta turo baki kafin ta
ankara Malaika ta sake kiranta. Nasrin ta danna
a fusace tana jira ta ji abinda Malaika zata
ce,sannan ta yi mata wankin babban bargo.
Malaika tana ta kuka har yanzu ta ce
"Nasrin! Ki taimake ni ina cikin wani hali.
Shamaki ya kore ni kuma ya bani kwana daya
in kwashe kayana, na je gidanmu ana ta zagi
ana cewa basu da inda zasu saka ni da kayana,
sai dai in san na yi. Ki taimake ni ki bani
adireshinki in taho a Abuja wajenki tunda bani
da goyo kuma ya kwace 'ya'yansa.'
"
Nasrin ta ji tamkar Malaika ta caka mata
wuka a kahon zuci na takaici, ga hausshin
140 | Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE...
Shamaki gami da tausayin Malaika, ga haushin
jin danyen hukunci da Malaika ta yanke na
zuwa wajenta.
"Ta zo wajena Abuja ta zauna akan me?
Meye hadinna da ita?" Nasrin ta faɗa a cikin
zuciyarta.
Nasrin ta dakatar da ita, ta ce, "in takaice
miki mijinki yana zargina da kashe muku aure
gani yake ni nake zuga ki saboda ina turo miki
katin waya, dan haka Malaika kada ki sake
nemana a waya balle kice za ki zo gidanmu.Ki
je iyayenki da iyayansa su yi muku sulhu ku
zauna lafiya, babu in da zaki je ki zauna ki yi
daraja wanda ya wuce gidan mijinki, ki
rungumi 'ya'yanki dan babu mai rike miki su
ki ga daidai idan bake da kanki ba. Dan Allah
Malaika ki cire ni daga cikin mutanen da kika
taɓa sani a rayuwa, matsalar gidanki ta dame ni
ta tsaye min a rai, gashi ta jawo min zargi da
wulakanci daga Shamaki.'
"
Nasrin ta tsiyayo da hawaye ta katse
wayar, tana katsewa ta yi sauri ta goge lambar
Malaika daga cikin wayarta. Ta kashe wayar
141 | Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE...
gaba ɗaya ma dan taga Malaika tana ta sake
kiranta.
Ta rubutawa Dr.Jalo sako ta ce, “daga
karshe wannan auren da muke kokarin ceto
rayuwarsa Allah ya yi masa cikawa a yau da
yamma.
"
Ta rufe computer ta, ta kwanta cikin
gagarumin ɓacin rai.
DA MA NI CE... 1
BABINA TAKWAS
RANAR TALATA ABUJA •
au Dr. Jalo da Nasrin sun daɗe suna
a facebook kasancewar ta ga
wadansu sakonninda abokansa su na
tura masa suna yi masasannu da jiki. Ta
tabbatar bashi da lafiya, dan haka ta damu tana
ta tura masa sakonninfatan samun lafya cikin
gaggawa. Ya yi mata godiya saboda kulawarta
ya nuna ya ji dadi. Amma ta matsa ya faɗa
mata abinda ya ke damunsa, sai bai ce mata
komai ba ya ma canja hirar. Gudun kada ta
ɓata masa rai sai ta bar zancen, dan taga alamar
baya son yawan tambaya.
Daga nan ta shaida masa tana yawan
zazzaɓi da ciwon kai kwanan nan. Ta tambaye
shi wanne irin magani ya kamata ta sha dan ta
warke?
Ya jima bai ba ta amsa ba, daga baya
yace ta je asibiti mana. Ta ce tana so ta je
amma aiki ke hanata zuwa, kasancewar
143 Jamila Untar Tanko (JUT)
DA MA NI CE 1.
zazzabin dare ne kafin safe ya sauka sai ta manta ta fita ofis.
4
ХАТ АЙШАЯ Sai yau yau ya tabbatar mata shi ba likitan
asibiti ba ne likitan karatu ne kawai. Nasrin ta
yi mamaki matuka dan ya yi mata kama da
cikakken likita mai farɗe mutum ya dinke. Sai
ta ji ta rage mamakin yadda ya zama kwararren marubuči, rubutu masu masu mama'ana ' ashe likitan
karatu nesanlods sbainnolsa p2ebsw
ST Yashaida mata ya karanci English
Litraturëb yana koyarwa a jami ar
Lagos. Nasrin ta ji dadi kwarai da ta fara sanin
wani abu nasa bodsa syibog stem by Y swaggsy
SY BUGSY sbstas y mamaki da ta ji yace ta bashi
2010 2:
bride sisu karanta
16 FT 8260 sted
tarihiin rayuwarta yana so ya sani.Ta
sakon nan daya daya tura tura,, yaya fi sau biyar dan ta
tabbatar haka din yake nufi nufi dan kada ta fara
zuba alhali bai ce ba. Ta gasgatanewer haka yake sys
nufis sai ta gyára zama. Ta rubuta ta tura masa ta ce idan bazai damu bazatakira is shi bidsvess su yı new ida magana a waya, zai fi dadiidan suka yi magana
baki da baki, ta shaida masa kada ya damu bata
biyan kudin katin waya.Nan da nann yay bata
izinin, żata iya kira ba damuwa. Farin ciki ya
woman swusstened
144 Jamila Umar Tanko (JUT) (TU) of
DA MA NI CE... 1
rufe ta kafin ta kira shi sai da ta kira Dinah ta
bata labarin yadda suka yi da Dr.Jalo, ta
tabbatar mata yanzu ma zata.kira shi su yi
labari.
Dinah ta yi mamaki ta kuma ta taya ta
murna ta tabbatar mata ita ma ba zata yi bacci
ba har sai sun gama wayar, tana jiran ta kira ta
fada mata yadda suka yi, Nasrin ta yi mata
alkawari zata kira k ta fada mata komai.
Dinah ta yi mata alkawarin zata dauki
jarbi mai dubu ta taya ta da addu'a Allah Ya sa
atattauna abubuwa masu alkhairi.
Maganar Dina ta bawa Nasrin dariya
kwarai, dan haka ta yi ta dariya ta kashe waya.
Ta fada abayyane "Dina shakiyiyar
yarinya ce wallahi." Ayaw Gab
Nasrin ta tashi ta buce firij ta dauko
lemon kwali da kofi ta dawo kan gado ta zauna
ta nutsu sannan ta kira lambar Jalo, bayan da ta b
karanto kula'uzai ta tottofa a kowacce 5
kusurwa ta dakin, ta na neman Allah ya tsare ta
da ɓata masa rai ko ta faɗamasa abinda zai sa
ya janye daga gare ta.
145 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
Data buga bai dauka ba har ta katse sai a
karo na biyu aka dauka, maimakon ta ji
muryarsa sai ta ji muryar matar nan data dauka
ran nan, wacce yace mahaifiyarsa ce.
Nasrin ta zabura ta dukar da kai ta gaishe
ta, cikin fara'a ta amsa gami da cewa ki kira
nan da mintina goma idan yagama abinda yake
yi. Nasrin ta amsa cikin ladabi sannan suka
kashe wayar. Sai mamaki ya hana Nasrin rufe
bakinta, ta duba agogo taga karfe goma
shaɗaya da minti goma sha daya na dare amma
Jalo yana tare da mahaifiyarsa.
"Ina matarsa ne? Ko irin mutanen nan ne
masu son uwa, har yanzu yana nanike da ita?
Daga gani baya ɓoyewa Mahaifiyarsa komai
dan wayarsa ma yawanci a wajenta ta ke.'
Nasrin ta ke tambayar zuciyarta.
"
Tana cikin mamaki sai ta ji kira, tana
dubawa ta ga shine ta ki amsawa, sai bayan
data katse sannan ta kira saboda bata so ta ci
masa kudin waya. Tana kira sai ta ga ya katse
kiranta, sannan ya kira ta.
Ta amsa cikin ladabi ta gaishe shi.
146 | Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
Yace “me yasa za ki kira ni? Ai ni ya
kamata in kona katin wayata ba ke ba. Kada ki
damu nima katin wayar zai isa mu kwana, mu
yini muna hira bai kare ba."
likita.'"
"
Nasrin ta yi dariya ta ce, “na gode kwarai
Ya yi dariya ya girgiza kai yace, “kada ki gode
min ki godewa Allah da Ya hada mu, gashi
muna ta zumunci muna karuwa da juna. Yau
ma na ga rahotanninki a gidan shugaban kasa
(Billa), a labarai aka nuna, sannu kina kokari
fa har kin fi wasu tsofaffin maʼaikatan sanin
makamar aiki."
Nasrin ta yi dariya ta sosa goshi ta ce,
"haba dai muna ta koyo dai, ai ku ne gwanayen
magana. Da ma zan iya ganinka in yi hira da
kai ka wanke mana 'yan kudu da suke yiwa
'yan arewa gani-gani."
99
Ya yi dariya yace,“rufa min asiri ni asu
wa?"
Ta yi dariya ta ce, "kai kuwa kai ne komai,
amma sannu a hankali zan sanka, na yi
alkawari sai na haska ka a duniya, gaba daya
147 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
sai an sanka. Kuna da amfani a cikin
al'umma."
Ya yi murmushi ya canja hira,yace,
"Nasrin, ba ni labarinki. Ina so in san ko ke
wacece?"
Ta gyara zama ta yi farfari da ido ta yi
gyaran murya.
LABARIN NASRIN:
Ta ce "Sunana Nasrin Mahaifina kuma
sunansa Abdul Nasir, sunan mahaifiayata kuma
Hajja Khadija. Gaba dayansu daga tsatso daya
suka fito 'yan uwan juna ne kakanninsu ɗaya,
jikokin wani shahararren sarki ne mai karfin
mulki a arewacin Najeriya. Dan haka jinin
sarauta ne.
A daki daya aka rike su, da suka
kammala karatun sakandire sai aka daura musu
aure daman su na son junansu, aka tura su
karatu America, acan suka zauna. Bayan sun
kammala karatun jami'a ma basu dawo ba suka
fara aiki acan.
Haihuwarsu ta farko aka haifi yayata
Zainab wacce nake gidanta anan Abuja,nice ta
148 | Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE
biyu sannan aka haifi dan autanmu Nafi'u yana
can tare da su shima ya shiga Jami'a. In takaice
maka dai Mahaifina shine ambasadan Amerika
da yake wakiltar Nigeriya.”
Dr.Jalo ya yi ajiyar zuciya yace, "da
kyau. An daɗe ana neman ilimi a duniya
ashe?"
Nasrin ta yi dariya, ta ce "gidansu gaba
daya 'yan boko ne abin mamaki kuma duk sai
da suka sauke ku'rani tun kafin a saka su a
makarantar firamare ma, dan haka hafizai ne,
mu ma haka suka yi mana. Akwai wasu
ustazan larabawa a Amerika su suka koyar da
mu tun muna kanana."
Jalo yace,
ni kwarai."
"masha Allah amma sun birge
Nasrin ta yi ajiyar zuciya ta sa hannu ta
jawo kofi ta tsiyayi lemo ta kora ta ci gaba da
cewa, "A Amerika muka yi firamare, muka yi
sakandire da jami'a. Amma ni ina yawan zuwa
Najeriya akai-akaiduk hutu, wajen
kakannina.Amma na fi zuwa a lokacin da
Zainab ta yi aure a Najeriya. Yanzu haka
bautar kasa ce ta kawo ni. Idan na kammala
149 | Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
zan koma Amerika sai in yi masters da
PHDdina, dan ina so in zama Dakta a fanni
jarida. La so in zama kamar ka.
Suka yi dariya su dukka.
"
Ya ce "in sha Allah Nasrin sai kin fi ni
ma dan irin karatuna da naki ma ba daya ba ne,
mu da mu ka gama karatu a Najeriya kasar da
ake yawan yin yajin aiki, ga wahala. Ku kuwa
karatunku babu wata damuwa, kun yi kun kare
cikin nutsuwa.
99
Nasrin ta yi dariya ta ce,"abin ai a
kwakwalwa ne, ga shi kuwa a wajenka mu ke
koyo."
Ya ce "kin gama zayyano min karatu
amma ban ji kin ambaci aure ba. Ina labarin
Fu'ad?"
Nasrin ta yi dariya ta rufe ido da
hannunta ta ce "Fu'ad dan gidan Yayan
Babana ne, A gidanmu aka rike shi, dan haka
gidanmu daya, yana can tare da Baba a
Amerika, yana aiki a karkashinsa. 99
Ta ji muryar mace tana yi masa magana
cikin yaren fulatanci, shima ya bada amsa cikin
harshen Fulatanci, sanna ya dawo kan Nasrin.
150 | Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE
S
"
Ya yi dariya yace, "sorry! Muna magana
da ke na juya ina magana da Mamata. Ta ce
min in je in kwanta haka dare ya yi.”be iam os
Nasrin ta yi mamaki ta juya da sauri ta
kalli agogo, karfe goma sha biyu saura mintina
biyar. end men ofbud
3d stTa ce "Allah sarki da gaskiyar Mama
dare ya yi."
new Jalo yace, “to za
gobe." ayaw sismios
ad cams iguaz et ab cust
mu yi magana sosai
que fabi at six stas
Nasrin ta yi dariya ta ce, "na gode, Allah Ya
tashe mu lafiya." To adeown) sy loosd
Su ka kashe waya.
Gaba dayansu suka kwanta cikin farin ciki da
tunani muryoyin juna, da alama muryar Nasrin
ta yi matukar tafiya da hankalinsa, haka itama
muryarsa tana burge ta matuka.
st husYana ta nanata labarinta yana juya shi a
ransa. Ya tabbatar Nasrin ba karamar 'yar hutu
bace, ko ba'a faɗa maka ba daga ganin suffarta
da maganarta ba tashin nan bace. imen st danis
90 st Ita kuma tana tamamakin yadda
Mahaifiyarsa take tare da shia koda yaushenA"
"saspason nojsw s saitisl
151 | Jamila Umar Tanko (JUT) on muslims SI
DA MA NI CE... 1
"Ina matarsa da yaransa ne? Ban taɓa jin
muryar yara a cikin gidan ba. Ko irin uwar nan
ce mai saka ido akan 'yayansu su hana su
zaman lafiya da matansu? Ko kuwa matar ce ta
yi tafiya kasar waje kasancewar ‘ya'yan masu
kudin nan haka suke basa kula da mazansu?
Oho!" Nasrin na ta tambayar kanta da kanta ba
tare da ta sami amsa ba.
Ta ma manta ta yiwa Dinahalkawarin
zata kira ta idan sun kammala waya da Jalo,
haka ita ma Dina tuni ta yar da carbi gefe,
bacci ya kwashe ta.
Asuba ta gari!
Nasrin ta dan makaraam mata yi sauri ta
shirya ta fito falo, ta iske Salis ya riga ta
fita.Zainab kaɗai ta iske a falo, bayan sun gaisa
Zainab ta nemi da Nasrin ta zauna ta ci abinci.
Nasrin ta duba agogo ta girgiza kai ta ce
"Antimi,yau na makara sosai na san saina amsa
laifina a wajen manajana."
152 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE T
Zainab ta harare ta ce, "kin kwana kina
hira da kawaye ko in ce da Mutanen ɓoye su
Jalo ko?"
Nasrin bata amsa mataba, ta fice da sauri
tana saɓa jakar Lap-top a kafaɗa.
Zainab ta bita da kallo cike da tausayi,
saboda wahalar da take sha akan aikin nan data
ɗorawa kanta, dan ba dan kudi take yi ba
saidan sha'awa da neman suna.
*** ***
Nasrin bata dawo gida ba sai da yamma
likis karfe biyar na yamma. Tafiya take tana
jefa kafa dakyar saboda gajiya ga yunwa.
Banda lemon kwalba guda daya babu abinda ta
saka a cikin cikinta yau.
Burinta ta ganta a kwance akan gadonta
kawai, amma yau ta kudiri niyyar cin abinci da
yawa dan